Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 40 Hausa Novel

Tunda ta fara zuwa aiki kuma sai aikin gida da na yara suka kara taruwa suka yiwa Naja yawa. Domin sai ya zama kullum idan Khadeeja zata fita da hafsa take fita saboda rike mata Hammad a wajen aiki. Gani haka ya sa Naja ta saka Mustapha a gaba sai da ya bari ta dauki mai aiki wadda take zuwa kullum tana tafiya da yamma; tunda ya ce ba zata rabawa su Afaf wanke-wanke da gyaran gidan su dinga yi idan sun dawo daga makaranta ba.Babu yanda bata yi da shi ya mayarwa da Khadeeja kwananta ba amma ya ki; saboda ki-fadi. Duk da shi dinma yanzu zai so ace sun fara kwana bibbiyun tunda yanzu yana son shiga harkar Khadeejan; amma dai ya san Khadeeja ba zata karbi kwanakin nan da ta bayar ba tare da son ranta ba sai ta saka masa ciwon kai.Ita kuma ta so ta yiwa Khadeejan magana amma ba zata yi ba, saboda kusan tunda ta zo gidan ba wata magana da take hadasu da Khadeejan bayan gaisuwa; da yake ma Khadeejan ba mai son fitowa bace sai ya zama idan dai ba aiki zata je ba to zasu iya kwana biyu ma basu hadu ba.Haka suka cigaba da rayuwarsu.………Ranar Juma’a ce ta kama ranar da Khadeeja ta cika arba’in. Duk wani shiri ta gama yinsa, ta gama gyaran jikinta kamar yanda duk wata maijego take yi. Sai dai bata sa rai zai bata kwanan ba kuma ta ci alwashin ba zata taba kai masa kanta ba sai dai shi ya kawo kansa.Bayan ta idar da sallar asuba sai ta sake bin gado ta kwanta tunda ta san Hammad ba zai taba wuce karfe takwas yana bacci ba zai tasheta. Bata san iya tsawon lokacin da ta dauka tana bacci ba bugun kofar da ake mata ne ya tasheta, a tare suka farka da Hammad wanda ya sa kuka. Ta lalubo wayarta ta duba lokaci inda taga 8:30am; nan da nan ta mutssike ido don ya kamata ace kafin karfe tara ta fita ta tafi gidan rediyo. Sai da ta dauki Hammad sannan ta mike ta bude kofar. Hafsa ta gani a tsaye; bayan ta gaisheta tace ‘Anti na gama aikin gaba daya na ga baki fito ba kuma jiya kin ce min na shiya da wuri zamu fita.’‘Hmm! Bacci ne ya kwashe ni. Zauna ki jirani na shirya Hammad na miko miki shi nima na shirya mu tafi.’Nan da nan ta shirya Hammad ta mikashi wajen Hafsa suka zauna a parlor sannan ta koma dakin ta shiga wanka.A gurguje tayi wankan ta fito daure da karamin farin tawul dinta, tana rike da wani tawul din tana goge jiki. Mustapha ta hango yana zaune a gefen gadonta ya mike kafa yana kallo a waya. Ba karamin mamaki tayi ba domin gaba daya ta kasa tuna me yake jira. Ba wai baya shiga dakin bane amma dai tunda Naja ta tare bai zauna a dakin ba sai dai ya shiga ya gaya mata abinda zai gaya mata yana daga tsaye ya fice. Ta dan tsaya kadan ta kalleshi sannan tace ‘Ina kwana.’Ya ajiye wayar ya amsa gaisuwar tata da fara’a. Ta karasa gaban mudubi tana goge jiki yayinda shi kuma Mustaphan ya mike tsaye ya nufota. Ya karasa ya tsaya a bayanta ya rungumota ta baya, ta kalleshi ta cikin mudubin suka hada ido tace ‘Fita fa zan yi ka ga ma na makara.’Yayi murmushi ya saka bakinsa a kan kunnenta yace ‘Nima fita zan yi, amma diai kin san yau kinyi arba’in yau ko.’Ta dan motsa saboda yanda yake kara shigewa jikinta tace ‘Um.’‘Ok, ki karbi kwananki yau sai ki ajiye min dinner.’Murya kasa-kasa tace ‘Toh.’Ya sumbaci gefen wuyanta sannan ya saketa ya juya. Har ya kusa zuwa bakin kofa kuma sai ya juya ya dawo, kafin ya karasa inda take itama ta juyo don haka ya tsaya a gabanta. Cike da damuwa ya kirawo sunata, bayan ta amsa yace ‘Bana jin dadin yanda kuke zama da Naja kamar kuna gaba, please ki dinga dan zama a parlor din kasa saboda ku saba.’Ta dan yi murmushi tace ‘Ba wata gaba da muke yi tunda muna gaisawa, kuma duk abinda ya kama na magana ai muna yi.’Ya kalleta suka hada ido sannan ya rike kwayar idonta yana cewa ‘Duk da haka dai ki dinga dan zama a can kuna hira. Kinga idan kina nan ba zata shigo ba itama sai tayi ta zama a parlor dinta inda ke ba kya shiga.’Bata son ta ja zancen saboda bata son ta makara, don haka tace ‘To shikenan.’Ya sake tsattsareta da ido sannan yace ‘Please!’Tayi gajeren murmushi ta daga kai.Ya fice bayan tayi masa a dawo lafiya.Ta ja tsaki bayan da ya fice; bata jin zata iya rabar Naja, ta tsaneta. Watakila hakan yana da alaka da yanda Mustaphan ya bata mata rai a kan Najan tun kafin aurensu da kuma maganganun da ta gani a wayar Afaf da suna chatting da Naja. Gaskiya ba zata iya hira da wata Naja ba, gahi kuma bata iya munafurci ba balle taje ta yi na karya. Shi dai da yaga Naja yana so ya aurota suje can su karata.Cikin sauri ta karasa shiryawa suka fice ita da yaranta.Tun kafin Magriba ta gama abincin dare, don haka Habib yana shigowa daga masallaci sallar magriba ta turashi ya kirawo kannensa a wajen Naja. Nan suka zauna a parlor dinta suka ci abinci inda ta dafa macaroni da miyar hanta da salad. Suna gama cin abinci Afaf wadda dama bayan sallama bata ce mata komai ba ta tashi ta fice daga parlor din. Sauran yaran kuma suka zauna a nan aka cigaba da hira ana kallon TV. Wajen 8:30pm duk suka fara jin bacci don haka da kanta ta tashi ta rakasu dakinsu, ta shirya shukra sannan ta tsaya Nasreen ma ta shirya suka yi brush suka kwanta sanna ta koma nata dakin. Shima Habib yayi mata sai da safe sannan ya wuce nashi dakin.Har zuwa lokacin Mustapha bai dawo ba, sai dai yayi mata waya ya sanar da ita sun fita da Alhaji don haka sai ta ganshi.Don haka bayan tayi wanka tayi shirinta na bacci sai ta koma ta jera masa abincinsa a table din parlor dinta sannan ta wuce dakinta ta kwanta.……….Sai wajen 9:30pm sannan ya shiga gidan. Kai tsaye bayan ya kulle gidan parlor din Naja ya shige tunda itace a kasa.Tana zaune a kan kujera tana shan cornflakes ranta a bace. Ya karasa bayan ta amsa sallamarsa ya sumbaci kumatunta sanna ya zauna a kusa da ita yana cewa ‘Cornflakes kike sha a daren nan?’‘Um. To me gidan ce da girki kuma bata bani nawa abincin ba shine na hada cornfakes nake sha tunda ban saba zama da yunwa ba.’ Ta fada tana kara shan kunu.Ya dan shiga duhu, yace ‘Umm, Khadeeja bata yi abinci bane?’‘Ta yi, amma nan ta turo aka kirawo yara suka je samanta suka ci abinci. Da suka gama cin abincin ma a can suka yi zamansu Afaf ce kawai ta sauko ta tayani hira.’‘Um! To ai na zata kowaccenku dama girkinta zata dinga yi ko?’Ta harareshu sanna tace ‘A ina ake haka? Tunda wadda take da girki itace zata dinga kula da yara ai gikin ma gaba daya zata dinga yi. Shi yasa nima idan nayi abinci nake fitowa dashi nan parlor din inda kowa zai iya diba, itace bata fitowa ta diba saboda bata son ganina.’‘Wa ya gaya miki? Ba haka bane. Bari zan yi mata magana in ya so sai ta dinga yi da ke, kema ranar naki girkin sai ki dinga yi da ita kun ma ragewa kanku aiki.’Ta zumbura baki ‘Ah to don ni dai haka na san duk masu mace sama da daya suna yi.’Yayi mata sallama ya wuce sama. Bata taba sanin idan Khadeeja ta karbi kwana abun zai sosa mata rai ba sai a wannan lokacin. Gaba daya zucuyarta tayi kunci, haka tabi bayansa da kallo har ya fice daga parlor din ya rufe mata kofa. Nan take hawaye ya wanke mata fuska; ta ajiye kofin da yake hannunta akan tebur ta hada kai da gwiwa ta sa kukan da ta kasa gane me ya kawo shi. Haushin Khadeeja ta karbi kwana ko kuwa haushin an barta da yunwa?………..Yana karasa shiga parlor dinsa ya kalli dining table, bai ga alamar abinci ba. Kamar ma ko taba wajen ba ayi ba tunda ya fita da safe. To me Khadeeja take nufi? Duk wannan dokin da yake na zuwa wajenta ita ashe bata gama fushin ba kuma bata gaya masa ba?Cikin sanyin jiki ya karasa ya shiga dakinsa. Ga mamakinsa dakin ma ba a gyara ba. Yanda Naja ta fita ta barshi da safe yana nan a haka, babu ma alamar da take nuna mutum ya shiga dakin bayan fitarsa. Khadeejan ma da yake sa ran zai gani a dakin bata ciki. To ina take? Me take nufi bayan ya sanar da ita yau itace da kwana? Gaba daya ranshi ya gama baci; baya son fitnar Khadeeja don ita rigima da ita ba ta karewa, musamman a yanzu da yake da bukatarta.Har ya juya zai fita kuma ya fasa, ya tsaya ya canza kaya ya shirya sannan ya dauki wayarsa ya fito ya nufi dakin khadeejan…

Back to top button