Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 67 Complete Novel

ASM Bk2067*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

………Tana zuwa bakin corridor ta hango shi zaune akan L-shape inda Haisam ke zama, da sauri ta maida idanun ta k’asa ganin ya zuba mata ido, a d’ayan side d’in ta zauna sai lokacin ta d’ago ta kalle shi still kallon ta yake a sanyaye ta gaishe da shi ya amsa, shiru suka d’an yi kafin taji ya fara magana, “dama mun had’u da H,Zakee a Airport ne ban ga kin rako shi ba har nike tambayar shi kina ina yace kina gida shine nace bari in zo mu gaisa” d’an d’agowa tay ta kalle shi da k’ak’alallen murmushi bata ce komai ba, shiru suka d’an k’ara yi ganin yanayin ta yasa shi cewa “Mom Zarah ko akwae wani abu ne u look abnormal” k’walla ne suka taho mata da sauri ta maida fuskarta k’asa had’i da girgiza mashi kai alamar babu komae, bin ta da ido yay kaman mai nazarinta can ya kira sunanta ta amsa ba tare da ta kalle shi ba yace ta d’ago, saida tay d’an jimm kafin ta d’an d’ago suna had’a ido k’wallan suka zubo mata sharr kawae sai tasa mashi kuka ta kai hannu ta rufe bakinta, a d’an rud’e yace “Subhanallahi, Mom Zarah Mike faruwa ne pls tell me” girgiza mashi kai ta hau yi cikin kukan tace mashi ba komae bata lafiya ne, tambayar ta yay Mike damunta tace kan ta ke ciwo, shiru ya d’an yi yana kallon ta ya cije lower lip d’in shi can yay sigh yace “ba gaskiya kika fad’a man ba Mom Zarah, in har baki lafiya na tabbatar H,zakee bazai tafi ya barki a halin ciwo ba koda kuwa baki fad’a mashi cewa baki lafiya ba nasan zai yi noticing don yana d’aya daga cikin Mutanen da suka karance ki sosae kusan ma zan iya cewa yafi kowa karantar ki, so don’t hesitate ki fad’a man in akwae wata matsala” cire hannun data rufe bakin tay ta fara goge k’wallan tana yi tana kallon shi tana d’an bud’e baki, gaba d’aya tama rasa to mi zata ce mashi bata san ta ina zata fara ba,

 

“Ko mun fara 6oye ma juna abu ne?” Cikin muryar kuka tace “ba kai ne ka fara ba, ka 6oye man cewa shi miji nane” d’an shaking kan shi yay tun a Asibiti ya fahimci bata ji dad’in abun ba, “am very sorry for dat Mom Zarah, kaman yadda na fad’a maki haka aka tsara so bai kamata ace na fad’a maki ba tunda bamu san yadda Al’amarin zai kasance ba, duk da muna fatan auren ya d’ore ba lalle hakan ya faru ba kuma kinga in kika sani sai kin fi shiga mawuyacin hali fiye da farko, da naga bai sake ki ba kaman yadda aka tsara lokacin na fara sama rai na auren zai d’ore, a lokacin da abu ya shiga tsakanin ku da ace kin fad’a man da tabbas zan bayyana maki komai ne to amman sai baki sanar man ba kema kika 6oye man har abu mara dad’i yazo ya faru, amman nasan haka Allah ya k’addaro komae ba mu isa mu canza ba, yanzu shikenan abar shi a munyi ma juna laifi, kiyi hakuri nima kuma nayi hakuri sai muci gaba kaman farko, in kina da wata matsala feel free ki fad’a man ta yuwu in iya taimaka maki ko yaya ne, kinsan ance a Problem shared is a problem half solved” idon ta a kanshi tana ta kikkifta su a kokarin ta na ta dakatar da cigaba da yin kukan, ce mata yay yana Jin ta ta fad’i mashi Mike damun ta ta fara motsa baki cikin karyayyar murya tace “ba wani abu bane Ya Abbas, kawai dai na fahimci Ya Haisam bai sona ne, ya za6i yaci gaba da zama dani ne don dalili biyu, ko don abunda ya faru tsakanin mu ne yana ganin in bai cigaba da zama dani ba bai man Adalci ba ko kuma k’ilan Hajiya ce ta matsa mashi amman ba wai don yana son yin rayuwar Aure dani bane” da k’yar take tattaro kalaman take fad’i mashi, shiru yayi daga Maganar da tayi ya fahimci komae dama kuma tafiyar Haisam d’in tasa shi kokonton in wani abu ya shiga tsakanin su, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yama rasa ta ina zai fara shi kanshi ya rasa gane ma Haisam d’in game da auran, jin yayi shiru yasa Fatuu cigaba da Magana a sanyaye “I decided to get out of his life tunda ba son zama yake dani ba ni bazan so in zame mashi matsala ba, yayi man dukkan Alkhairi a rayuwata bai kamata in hana mashi kwanciyar hankali ba” girgiza kai Abbas yay “kar kice haka Mom Zarah nasan dole ki shiga damuwa game da hakan amman ina ganin mu bashi lokaci tunda kinga duka sati guda kenan da kasancewar ku tare” da alamun bacin rai tace “to Ya Abbas wane lokaci zamu bashi abunda komai a bayyane yake da yana sona ba zai tafi ya barni ba, koda ta kama ma ya tafin ai a k’alla zai man bayani kan dalilin tafiyar da kuma lokacin da zai dawo, amman fa jiya da daddare kawai yace man wai zai koma kuma yau d’in yay tafiyar shi” idanunta ne suka kawo ruwa da alama abun ba k’aramin 6ata mata rai yay ba, hannu ta kai ta goge k’wallan tace “gara mu rabu kawai tunda na gane his heart belongs to his wife alone ni na hak’ura, da ai har na hak’ura dashi na amince ai man auran abun yay turning haka, ni yanzu ya Abbas ka taimaka man kasa ya sake ni kawai, dama yace duk abunda nike so in maka magana, to ka fad’i mashi ya sake ni don Allah kaga sai suci gaba da rayuwar shi da Matar shi cikin farin ciki ba tare dana takura su ba, kaga bama sai ya dawo ba” fuska a kwa6e ta k’arasa Maganar Abbas dake kallonta ya d’an yi guntun murmushi don ba abunda ke acikin Maganar tata face sheer jealous, sigh yay “kar muyi saurin yanke mashi hukunci Mom Zarah, mu dai k’ara bashi lokacin kiyi hakuri, ina d’aya daga cikin Mutanen dake fahimtar shi sosae amman da yawan lokutta is very difficult to understand him completely, ni raina na bani shima yana son ki don kuwa H,Zakee adalin Mutum ne zan iya rantsuwa akan hakan, indai yasan zai aure ki ya takura rayuwar ki bazai ta6a amincewa yaci gaba da zama dake ba so mu bashi lokaci, in har ya dawo komai bai canza ba na maki Alkawarin da kaina zan je wurin Hajiya in fayyace mata komai game da zaman ku na tabbatar zata raba ku bazata goyi bayan a cutar da wani ba” shiru tay taji ta amince da Maganar ta shi, tambayar ta yay hakan yayi mata ta d’aga mashi kai, lallashinta ya shiga yi yana kwantar mata da hankali har ta d’an saukko, tambayar ta yay yaushe zasu yi exam ne tace mashi kafin Azumi yace to ta dage tunda Azumin ya taho kar tasa damuwa a ranta har tazo ta samu matsala tace mashi to,

 

shiru suka d’an yi can ta mik’e tace bari ta kawo mashi lemu ya dakatar da ita yace daga gida ya fito yaje Airport bai jin k’ishi tace to bari ta kawo mashi cincin nan ma yace mata ta barshi ai an basu da yawa sun ci sosae, duk da hakan saida ta tafi tana fad’in bari ta kawo mashi ya kaima su Abdul ta nufi hanyar corridor yabi ta da kallo har ta shige sannan ya d’an girgiza kai a fili ya furta “DESTINED HEART”, bada jimawa ba ta dawo ruk’e da leda ta d’aura akan c-table ta koma ta zauna, rok’on shi tayi kan ya kawo mata Abdul ya zauna na wani lokaci ya nuna mata yanzu in ya kawo mata shi aiki zai zamar mata tunda ba hutun school akayi ba kuma itama gashi tana zuwa Makaranta amman ta bari in akayi hutu yayi mata Alk’awari zai kawo mata shi har hutun ya k’are ta ce to, shiru ta danyi sai kuma tace “yace duk abunda nike so kai zan tambaya yanzu in ina son fita fa?” D’an murmushi yay yace ina zata ne tace a’a tana nufin in fita ta kama ko zuwa gida haka, still murmushin yake yace ba wani abu duk inda take so ta je tunda yasan bazata je inda bai kamata ba, daga baya ya mik’e yay mata Sallama yace zai je su gaisa da Hajiya tace ya gaida su Aunty Feenah, bayan tafiyar shi d’aki ta koma ta kwanta rub da ciki ta fad’a duniyar tunani wanda kusan duk na Haisam ne, can ta mik’e ta d’aukko wayarta ta shiga cikin gallery, tsofaffin hotunan su ta shiga gani wanda yawanci duk shi ya tura mata a ranta ta rink’a jin inama ace irin rayuwar nishad’in da suke har yanzu kenan, a hankali take kai hannu tana goge k’wallan dake zubo mata daga baya ta kife wayar tay lamo akan gadon, tana haka har Magrib sannan ta mik’e don tayi salla jikinta duk jin shi take kaman na wadda ta tashi daga ciwo.

 

Haisam ya sauka lafiya tuni dama yaje ne don ya duba jikin Mahaifin shi kafin ya wuce, ya iske ya samu sauk’i sosae dama ciwo ne kawai Allah ya kawo mashi don mutum ne mai cikakkar lafiya don ko hawan jini bai da shi hakan yasa ma wasu sukai tunanin ko Asiri ne ba kamar da yake d’an siyasa ne saidae shi yace ya d’auke shi ciwo ne kawai Allah ya kawo mashi, da daddare suna cin Abinci ne Mom d’in shi ke tambayar wai ko har yanzu bai lafiya ne taga still da rama a fuskar shi gashi kaman baida kuzari yana d’an murmushi yace mata ya samu sauk’i sosae Dad d’in shi yace ai bai cin Abinci sosae gashi ya yi ciwo dole yay ta zama hakan, shidai d’an murmushi kawai yake, bai ci wani Abincin kirki ba ya mik’e Senator ya kalli Mom d’in shi yace “you see, taya zai maida jikin shi da wuri” d’an 6ata fuska tay tace mashi ya zauna ya k’ara to shi bai iya gardama ba ba kamar kuma da iyayen shi kawae sai ya koman ya k’ara ci daga baya ya tashi ya nufi upstairs idanun Mahaifiyar tashi a kanshi, bayan ya haye ta maido idon ta kan Senator tace bai lura kaman yana cikin damuwa ba ya d’an watsa hannu yace ba lalle ba tunda gane mashi nada wuya, haka ta bar Maganar amman a ranta tana ganin kaman akwai abunda yake damun shi.

 

Daren ranar baccin Fatuu ragagge ne, Washe gari bayan tayi sallar Asuba Al’qur’ani ta d’aukko ta fara karatu, ta dad’e tana yi bayan ta gama ta nufi toilet don tayi wanka, tana cikin sa kaya Saude ta kawo mata breakfast, bayan ta gama Part d’in Hajiya ta nufa ta isketa a d’aki suka gaisa tay mata ya kewar mai gida ita dai d’an murmushi kawai tayi, nan ta bata hak’uri tace mata daga wurin aikin shi ne suka buk’aci ya koma tasan bai rasa fad’i mata, tace ai sun ma yi mashi mutunci suda basu wasa da aiki don ma yana yi masu wani daga nan, ita dai Fatuu shiru tay daga baya tace zata je wurin Aunty Saude, tare sukai aikin Abincin rana, gaba d’aya ta koma sukuku da ita ga tunanin Haisam da ya addabi zuciyar ta komi take shike mata yawo a rai har Saude ta lura da yanayin ta ta tambayi ko har yanzu ciwon kan take tace mata a’a da Sauk’i, anan taci Abincin rana tare da Hajiya bayan sun gama suka koma falo suna kallo saidai ita idanun nata na kan tv d’in ne ba don tana fahimtar mi ake ba wani lokacin sai ta sauke idanunta tay shiru, Hajiya da ta lura da yanayin ta tace “Fateema anata kewar miji ko?” d’an firgit tay ta kalli Hajiya lokacin idanunta na k’asa tay Maganar ta d’an k’ak’alo murmushin yak’e ba tare da tace komai ba,

 

“ko kije gida nasan in kika ga Dije Kya rage kad’aici” sosae taji dad’in Maganar a hankali tace mata to ta mik’e, har zata tafi Hajiya tace taje Kitchen ta zuba Abinci ta kai mata nan ma ta amsa da to ta nufi Kitchen d’in, Yau ma data je gidan saida gwaggo tayi mata fad’a kan miyasa zata rink’a zaryar zuwa a sanyaye ta fad’i mata yadda sukai da Hajiyar, duk a zaton ta bata san Haisam d’in ya tafi ba amman sai taji tace ai yazo yayi mata sallama kafin ya wuce jiya ma harda kayan Abinci Tk ya kawo, ta d’ora da fad’in ai dama yakamata ya koman tunda bada shirin zama yazo ba, gwaggo ta lura da yanayin ta amman bata ce komai game da hakan ba sai kawai ta nuna mata tayi mashi Addu’a da fatan Alkhairi in ya samu lokaci tasan zai dawo ne Fatun ta d’aga mata kai kawai, jefi jefi suke yin fira nan Fatun ta rok’i gwaggo kan ta d’aukko Mino yanzu sai ta taya ta zama, cikin wasa tace kenan ma ita zata d’aukko ma ita, a sanyaye tace a’a ko kwana ne sai ta rink’a taya ta tace ta kusa zuwa ai, sai bayan isha ta koma gida a part d’in Hajiya taci Abincin dare lokacin da zata koma part d’in su Hajiyar tace mata in tana so ta kwana anan tace to don a tunanin ta in anan ne k’ilan ta samu tayi bacci sosae ba kamar jiya ba, komawa tay part d’in nasu ta shiryo sannan ta dawo, a d’akin Saude ta kwanta da yake ita ba anan zata kwana ba, Washe gari bayan sallar Azahar tana part d’in Hajiya sai ga kiran Fauzy bayan ta d’aga tace mata bata nan ne gasu sun zo da Aunty Mareeya amman ba kowa a part d’in, da sauri tace mata gata nan tana part d’in Hajiya ne, tana shigowa parlon ta nufi Aunty Mareeya da yar sassarfa ta fad’a jikin ta sai kuka, rarrashinta ta shiga yi tana d’an bubbuga bayanta daga baya ta washe, sosae ta shiga bata baki tana kwantar mata da hankali ta nuna mata sam bata ji dad’in halin da take ciki ba amman in sha Allahu komai ya kusa zama labari, fira suka shiga yi daga baya Fatun tace bari ta d’aura masu girki suka ce suda daga gida suke sun ci Abinci ta kafe kan ai anjima sai suci in ta dafan, ta fad’i masu bata ta6a yin girki ba sai yanzu Aunty Mareeya tace ah lalle taje tayi masu su ci girkin Amarya harda cewa Allah yasa akwae sauran man shanu tana yar dariya tace eh akwai ai bata ma wani amfani dashi, tare da Fauzy suka fara yin aikin girkin wanda Fried rice ce zasu yi, suna cikin yin girkin Aunty Mareeya ta shigo Kitchen d’in tay masu sannu da aiki kafin ta nufi drawer din da ta saka mata magunguna ta bud’e, wasu daga ciki ta fiddo tace mata zata tafi dasu don kar su lalace in buk’atar su ta taso daga baya zata aiko mata da wasu, d’an tura baki tay tace ita tama kwashe su duka tana dariya cike da tsokana tace karfa daga baya ta kirata tana mata yar muryar Aunty Mareeya dama Maganar Magungunan nan ce, duk sukai dariya tace ita bazata k’ara amfani dasu ba, bayan sun ci Abincin duk in suka ce zasu tafi sai Fatuu ta marairaice kan su bari sai anjima a haka har dare yay sai da akai sallar isha sannan suka tafi bayan sun je part d’in Hajiya sun gaisa, Washe gari tana yin shirin zuwa Makaranta a ranta ta raya ko wama zai rink’a kaita, k’arshe ta yanke in ta gama shirin kawae ta tafi ta hau abun hawa, bayan ta gama shiryawa a parlor ta zauna tana yin breakfast da Saude ta kawo mata tana cikin yi aka k’wank’wasa kopa ta bada izinin a shigo, Tk ne ya shigo yana ganinta ya fara mata dariya ya shigo ciki, akan armchair ya zauna har suna had’a baki wurin gaishe da juna yace mata dama zuwa yayi yaga in ta shirya nan ta gane shine zai rink’a kaita kenan, yana zaune har ta gama taje ta d’aukko jakarta da takalma suka tafi.

 

A Ranar wadda ta kama Monday Haisam ya tafi U.S, Bayan ya isa Fanan ta d’aukko shi ta sha kwalliyar k’ananan kaya, gaba d’aya Farinciki ya cikata har fuskarta bata iya 6oyewa, tun a Mota ta fara nuna mashi tayi missing d’in shi don ma ita ke driving d’in, bayan sun isa gida zo kaga tarairaiya har wanka ita tayi mashi, haka Abinci ma a baki ta rink’a bashi, bai dakatar da ita daga yi mashi duk abunda ta saba mashi ba, ita kanta saida tayi Maganar fad’awar da fuskar shi tayi da har yanzu bata ciko ba, cike da nuna damuwa ta shiga tambayar ko har yanzu bai lafiyan ne yace mata ya warke nan ta yanke harda stress tace ya tashi daga ciwo bai huta ba ya tafi wani aiki, sosae ta bashi dama ya huta don har saida ya d’an yi mamakin hakan harda su massage aka mashi, daga baya ne bayan ya huta sosae abu ya shiga tsakanin su a lokacin kuma ta nuna mashi how badly tay missing nashi to shima d’in bai yi k’asa a gwaiwa ba wurin sauke mata abunda ya tara, daga baya suka cigaba da gudanar da rayuwar su yadda suka saba.

 

Ba k’aramin yak’i da zuciyar ta Fatuu ke yi ba, ta matsa mata da tunanin Haisam gaba d’aya ta koma sukuku da ita gashi tunda ya tafi basu yi waya ba ko text message balle kuma chat, sosae take daurewa a haka har yayi sati guda da tafiya, a ranar wadda ta kama Friday bayan ta dawo daga Makaranta tana cikin Bedroom ta fito daga wanka tana shiryawa taji wayarta ta fara ringing ta nufi bakin gado inda take ajiye ta d’auka, har saida gaban ta ya fad’i ganin Haisam ne ke kira, tamke Fuska tay wata zuciyar ta bata kar ta d’aga ta bi kiran da kallo har ta yanke, zama tay a bakin gadon nan da nan mood d’in ta ya canza damuwa ta bayyana a kan fuskar ta a ranta ta shiga raya ace tunda ya tafi bai kira ta ba sai yau a haka za’a ce wai yana son ta Abbas da bata had’a komai dashi ba kullum sai ya kira yaji ya take wata rana ma sau biyu yake kiran nata, tana ta zancen zuci wani kiran ya sake shigowa ta k’ara bin screen d’in da kallo, har ta kusa yanke wa wata zuciyar ta raya mata hakan ba daidai bane tunda shi ya kira ba ita ta neme shi ba ta d’auka, picking tay ta kai wayar kunne jin shiru yasa can k’asan makoshi tay sallama, amsa mata yay daga haka tay shiru shima shirun ya d’anyi sai kuma taji ya tambayi yadda take k’asa k’asa ta bashi amsa da lafiya lau, sake tambayar karatun ta yay nan ma tace lafiya lau, jin sun yi shiru yasa tace mashi sai anjima yace Ok, bin wayar tay da kallo fuska a kwa6e bayan ta cire ta daga kan kunnan ta, can ta cillar da ita ta kife fuskarta a saman gadon.

 

***** ******

 

Ranar Friday da ta kama satin Haisam biyu da tafiya daidai, Misalin k’arfe sha biyu da rabi na rana Jirgin su Senator da Hajiya Maryam ya sauka a Airport d’in Katsina don amsa kiran da Mahaifiyar su tayi masu kwana ukku da suka wuce, tun ranar data kira su ta sanar dasu tana son ganin su suka hau tambayar ta lafiya tace masu Kada su tashi Hankalin su lafiya lau sai Alkhairi kawae tana son ganin su ne in sun samu lokaci, shine daga baya suka kira Junan su suka yanke ranar da zasu zo, gaba d’aya sunyi shiga ta Alfarma Senator na sanye da babbar rigar shadda haka takalman shi ma fararen cover ne da hular shi hannun shi sanye da dankareren agogon diamond yayin da Hajiya Maryam ke sanye da rantsattsiyar bak’ar shadda data sha aiki golden takalmanta ma golden ne masu d’an tudu haka jaka da gyalen jikinta duk golden ne tsadaddun gaske to coge d’aurin kallabi, tun daga kan kunnan ta da wuyan ta da kuma hannunta kerarrun gold ne, dole ma ka kalle ta ko bakai niyya ba sai faman baza k’amshi suke ba kamar dai Senator d’in, in ka kalle su zaka ga basu kama saidai kamar jini don shi mahaifin su ya biyo ita kuwa Hajiyar Sanata ce sak, A dankareriyar Jeep aka d’aukko su Motar Escorts na biye da su suka nufi gidan Hajiya, bayan sun isa cike da Farinciki Hajiya ta tarbi y’ay’an nata abun Alfaharin ta itama ta ca6a adon leshi, kan kace mi kopar gidan ya cika da Jama’a Mutanen Senator, a nan Parlor suka zauna suna gaisawa daga baya wasu daga cikin Mutanen Senator d’in Abokan shi na hannun daman shi da suka zo yi mashi sannu da zuwa su kuma gaida Mahaifiyar tashi suka shigo a bisa Umarnin shi, nan fa hira ta 6alle baka jin komai sai dariyar manyan mutane masu tumbin Naira, Saude da wata da aka d’aukko don ta kama mata aiki suka shigo masu da abubuwan sha da na ta6awa kafin lokacin cin Abinci yayi, daga baya sukai ma Hajiya sallama bayan sun mata Alheri irin nasu na manya Senator yace mata zaije Government House su gaisa da Governor, bayan tafiyar su ya rage daga ita sai Hajiya Maryam, hannu ta kai ta kamo na Hajiya da yake a kujera d’aya suke 2 seater da murmushi tace “Hajjajutah fatan dai kina lafiya?” itama murmushin take tace mata tana lafiya Alhamdulillah,

 

“Ya k’afafun da Sauk’i dai ko” cike da nuna kulawa tay tambayar tare da d’an kallo k’afafun Hajiyar, nan ma ce mata tayi da Sauk’i sosae da taimakon sandar ta ba inda bata zuwa, “Ma sha Allah haka muke so, Allah ya k’ara maki lafiya da nisan kwana our Heartbeat” Hajiya na yar dariya ta amsa da Amin,

 

“Sai muka ji kira kina neman mu, nifa har hankali na ya d’an tashi kawae don kin ce ba komai sai Alkhairi yasa na d’an kwantar da hankali na amman duk da hakan naji na k’agara in zo in ji miye” still da fara’a a fuskar Hajiya tace mata in sha Allah Alkhairin ne kaman yadda ta fad’a masu tace to ta fara fad’a mata kafin Yayan ya dawo, tace “Saurin mi kike, ki bari ya dawo kaman yadda kuka zo tare sai muyi Maganar tare ko yau zaku koma ne?” tana yar dariya tace mata a’a kawai ta k’osa taji ne nan zasu yi mata Weekend,

 

“Shine don rowa ko a taho man da d’aya daga cikin mazajen nawa ko k’awayen nawa koma a kwaso man su duka” dariya ta saka da yar kakkausar muryarta tace “Wllh kuma sun so biyo ni k’in tahowa nayi da kowa hakanan kai ta yawo da yaro tunda saida na je Abuja sannan muka taho nan” Hajiya tace to miye tunda ba’a k’afa za’ai yawon ba tace a’a in suna so in akai masu hutu sa zo,

 

“Amman dai nasan banda uwar ji da kai aka nuna ana son zuwa ko” still dariya take tace “Wai Farha, aikuwa kaman kin sani ko in gaida ki bata ce ba” ta6e baki Hajiya tay “taji da shi, nima ba son tace tana gaida nin nike ba tunda inada wanda suke gaida nin ta rik’e kayanta ban so” haka suka cigaba da hira cike da raha. Duk wannan abun Fatuu na Makaranta bata dawo ba daga can ma Hostel zata wuce sai Fauzy ta shirya zasu taho tare a sauketa a gidan Aunty Mareeya sai ta dawo tunda akai Break dama ta kira Tk ta sanar dashi don Kada yazo in an tashin shima kawai sai ya wuce cikin gari bai ma san su Senator d’in sun zo ba, tare da Hajiya Maryam d’in suka tafi Masallaci sallar juma’a, bayan an gama nan fa aka fara tururuwar zuwa gaishe dasu da yake da yawa sun santa wasu kuma sai sun zo gaida Hajiyar suke sanin wacece wasu ma ba sai an fad’a masu ba tunda ga kama nan, bayan sun dawo ne suka zauna cin Abinci, suna cikin ci Senator ya dawo ya nufo Dining area d’in Hajiya tace ya zauna su ci Abinci yana murmushi yace mata sunci Abinci tare da Governor, d’an 6ata fuska tay tace to itama sai yaci nata tunda don su akai yana yar dariya yace tuba yake zai ci ba sai ta 6ata rai ba yaja kujera ya zauna duk sukai dariya,

 

Bayan sun gama cin Abincin suka dawo parlor nan Hajiya Maryam tace mata tunda Yayan ya dawo sai ta fad’a masu abunda yasa ta buk’aci ganin su, numfasawa Hajiya tay ta gyara zaman glass d’in fuskarta sannan ta fara Magana a nutse “Farko dai muyi ma Annabi salati” gaba d’aya suka amsa da sallallahu alaihi wa sallam, bayan kowa yayi taci gaba “dalilin kiran ku abu ne ya taso wanda dole kuna da buk’atar sani ko ba don komai ba don halin rayuwa, ta wata fuskar ba lalle ku kalle shi a matsayin abun Alkhairi ba amman ina fatan ku natsu kuyi amfani da hankalin ku ku kar6e shi a matsayin Alkhairin domin duk abunda kaga Allah yayi to mai kyau ne” dakatawa tay tana maida numfashi duk sun natsu suna sauraronta Hajiya Maryam na gefen ta yayin da Senator ke facing d’in su acan d’ayan bangaren, Maganar da tayi yasa duk suka k’osa su ji miye abun da take son sanar da su d’in, kasa hak’uri Hajiya Maryam tay tace “muna jin ki Hajjaju” sauke yar ajiyar zuciya Hajiya tay ta d’aura “Haisam ne yayi aure, kuma yanzu haka da nike maku magana Matar tashi na zaune a gidan nan acan part d’in nashi” har saida Hajiya Maryam ta d’an zabura ta d’ago sosae idon ta akan Hajiya da alamun d’aurewar kai tace “Mi kike fad’a haka Hajjaju, Wane Haisam d’in yayi AURE!!!” tace mata wane Haisam ta sani banda d’an su, da tsananin mamaki akan fuskar ta tace “To ni ban gane mi kike nufi da yayi aure ba, ai dama duk mun san da yayi aure ko” d’an ta6e baki Hajiya tay kafin tace “dana ce yayi aure baki ji nace Matar na a cikin gidan nan ba, ko dama nan yake zaune da Matar tashi da kuka san ya aura?” da alama bakunan kowannen su ya mutu, shi dai Senator bin su da ido kawai yake ya jingine bayan shi da kujera yatsun hannun shi na had’e cikin na juna, Bayanin Yadda Al’amarin ya kasance Hajiya ta shiga yi masu tiryan tiryan har ta gama ba wanda ya katse ta sannan furiously Hajiya Maryam tace “kenan don uban shi har ya isa yayi aure without our Knowledge, Saboda bamu da amfani a wurin shi bai d’auke mu da daraja ba ko mi!!!” a tsananin fusace tayi Maganar har huci take, kallon Senator tay tace “Yaya kana ji fa, wai yaron nan har ya kai yayi aure bada sanin mu ba!” d’an girgiza kai kawai yay still bai yi magana ba, “ke kuma Hajjaju ya aikata wannan d’anyen aikin har ki goya mashi baya kisa ya zauna da ita, tunda matsayin taimakon ta yayi to miyasa bazai saketan ba zaki bashi dama suci gaba da zama” a fusace idanunta akan Hajiya tay Maganar, Hajiya data kwa6e fuska tace “to miye amfanin sakin nata tunda abu ya shiga tsakanin su har rabo ya shiga tsakani….” A zafafe Hajiya Maryam ta katse ta don da ta ambaci rabo tamkar ta watsa mata ruwan zafi taji cikin k’unar zuciya tace “Don Allah ki daina wannan Maganar Hajjaju, wane rabo ba kince ya zube ba to cigaba da zama da itan na minene???”

 

“Amman dai kinsan in aka saketa ai ba ai mata Adalci ba, da ya aure tan ai matsayin zai taimaka mata akai dashi ba’a yi dashi wani abu zai shiga tsakanin su ba ko, to tunda har hakan ya kasance sai a rungumi Al’amarin ai fatan ya zama Alkhairi ta yuwu dama Allah ya k’addara auren ba don su rabu bane” girgiza kai Hajiya Maryam ta shiga yi tana cigaba da yin huci can tace “Impossible wllh, bazai cigaba da zama da ita ba, duka yaushe yay Aure da za’a ce wai har ya k’ara, k’arin ma na wulakanci da kaskanci, dole mu nuna mashi bashi ke iko da kan shi ba akwae masu iko dashi da zai je yayi gaban kan shi, in ba iskanci ba da ya raina mutane a ina na ta6a jin irin wannan taimakon” idanunta har sun sauya kala tsabar 6acin rai, kallon Senator tay “Yaya kana jin rainin wayau ko, dole ma a raba su wllh kawai a kira shi ya saketa!!!” tana rufe baki Fatuu ta sawo kai cikin parlon da sallama tana sanye da jallabiya ta yafa veil d’inta duk suka maida idanun su kanta, nan take ta ja ta tsaya tana bin su da ido itama, da hannu Hajiya tay mata alamar ta k’araso ta nufe su a d’arare don kuwa duk ta gane su, tana zuwa bakin kujerun ta toge duk tasha jinin jikin ta ganin yadda suke bin ta da ido ba kamar Hajiya Maryam wadda bacin rai ke kwance k’arara akan fuskarta, Hajiya ce tace “ki k’araso mana Fateema” shiga tay duk ta kame kanta, nuna mata kujera Hajiya tay alamar ta zauna maimakon ta zauna samanta sai ta duk’e saman carpet daga d’an nesa da Hajiyar, fuska a sake tace “an dawo?” Kai ta d’aga mata,

 

“amman ya akai baki shigo tun d’azu kin ci Abinci ba?” Cikin rawar murya tace “a..ai yanzu na dawo, na tsaya a Hostel ne wurin Fauzy mun yi Assignment” da k’yar ta k’arasa sakamakon mugun kallon da Hajiya Maryam ke jefa mata don kuwa ta santa tasan itace Matar Haisam d’in, tuni zuciyarta ta hau bugu da k’arfi da k’arfi, kai Hajiya ta jinjina sai kuma ta sake cewa “baki gaida bak’i ba to, kin gane su?” Kai ta d’aga mata alamar eh ta kalli Hajiya Maryam cikin rawar murya ta gaida ta tay mata banza, juyawa tay kan Senator dake ta kallon ta shima ta gaida shi ya jinjina mata kai kawai, juyowa tay kan Hajiya Maryam ta k’ara gaishe da ita aikuwa ta zabga wani uban tsoki ta mik’e ta nufi hanyar barin Parlon a fusace da sauri Fatuu ta fara k’ok’arin matsawa saidai ko kafin ta bata hanya ta cimmata aikuwa ta ham6are ta gefe ta wuce Fatun ta bugi kujera sosae aikuwa nan take ta fashe da kuka don ba K’aramin buguwa tayi ba, yamutsa fuska Hajiya tayi ta bi Hajiya Maryam d’in da kallo har ta shige Corridor sannan ta girgiza kai ta maido idon kan Fatuu ta mik’a mata hannu alamar ta matso ta jawo jiki tana cigaba da yin kuka tana gogewa da gyalen jallabiyar ta da ya zame daga saman kan, rarrashinta ta shiga yi tana bata hak’uri hannun ta guda a saman shoulder d’inta ta d’agota ta zaunar da ita akan kujerar kusa da ita tana cigaba da rarrashin ta, tana cikin goge k’wallan ta kai idonta kan Senator suka had’a ido kawai sai gani tay yay mata alamar tazo da kan shi, dakatawa tay tana kallon shi ya d’aga hannu ya k’ara kiranta Hajiya da ta gani tace taje ana kiranta ta mik’e a d’arare ta nufe shi, bayan ta isa gaban shi tana k’ok’arin zama akan carpet ya nuna mata kujerar kusa da shi yace ta zauna, zama tay tana cigaba da goge Fuskar ta tana yar ajiyar zuciya, a nutse cike da dattako ya fara magana,

 

“Kiyi hak’uri kin ji, ranta ne a 6ace shiyasa tay maki hakan amman Kada ya dame ki, nasan ba ki rasa sanin cewa in rai ya 6aci mutum na iya aikata komai ko?” Kai ta d’an jinjina mashi, d’an murmushi yayi “Good, a wani School kike ne?” Still muryar ta rawa take don wani irin kwarjini ne dashi ta bashi amsa, jinjina kai yay “da kyau, kinyi nisa a Karatun ne?” tace “Eh ina aji biyu kuma mun kusa yin Exam” nan ma kan ya jinjina yace “sai ku shiga aji ukku kenan, ai kaman daga nan ma zaku gama ko don nasan kaman karatun 3 years ne” kai ta d’aga mashi a sanyaye tace eh, “kice watarana in bani lafiya za’ai man Allura kenan, koma har kin iya yanzu?” ya d’an bud’a mata ido sak irin yadda Haisam ke yi dabarbarcewa tay don bata tsammaci ganin hakan daga gare shi ba tace eh ta iya, wani kallo yay mata irin na baka yarda da Mutum ba yace “kai, ki fad’a man gaskiya fa, ko don Kada ince baki da k’ok’ari kika ce hakan” da sauri tace “Allah da gaske nike na iya harda sa drip ma da d’inki” jinjina kai yay yana murmushi yace “kice Daughter d’in nawa mai k’ok’ari ce kenan” d’an waro ido tay baki a d’an bud’e take kallon shi ya d’age mata gira yace ko bata da k’ok’arin da sauri tace tana da shi, kai ya jinjina taji yace taje taci Abincin da sauri tace to ta mik’e ta nufi hanyar barin cikin parlon duk suka bita da ido Hajiya na d’an murmushi dama tunda suke Magana dashi take kallon su tana murmushi, Ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannu ya shafi fuskar shi yana kallon Hajiya yace “She’s so cute” Hajiya dake murmushi tace mashi haka take sai ma ya zauna da ita tana da dad’in zama sosae, nan ta shiga bashi labarin rayuwar da sukai da Haisam a baya, Maimakon ta shiga Kitchen d’aukko Abincin sai ta zille ta bi ta kopar baya ta fuce, bata bi ta 6angaren da d’akin Hajiya yake ba tabi ta d’ayan 6angaren tana tafiya cikin sauri ta d’an d’age kasan rigarta tana yi tana waigen bayanta ta nufi part d’in su………

 

_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button