Uncategorized

The Governor Wife Book 1 Page 3 Complete Novel

 

…… MATAR  GWAMNA….

 *©Azizat Hamza*

Washegari Asiya ba ta shirya da wuri ba dan sai takwas da rabi ma ta fita daga gida. So take MD ya tura Comrade Faisal da CY gidan Gwamna amma kash! MD ya nace sai ita ɗin zata je. Yau kan maimakon riga da wando data saba sakawa Atamfa ta saka riga da skirt da ƙaton mayafi daya kai mata gwiwa. Shikansa MD sai da yai wa Asiya kallon mamaki ganin shigar da ta yi, rabon da Asiya ta yi shigar Atamfa zuwa office har ya manta. Suna tafiya a hanya CY  ya dinga tsokalarta wai tayi shigan matan aure. Asiya bata kulashi ba dan gaba ɗaya gabanta faɗuwa yakeyi, ta rasa dalilin hakan kuwa.

Koda suka isa gidan Gwamnati ƙarfe goma saura minti shabiyar. Wajen da aka ajiyesu jiyan dai nan aka sake zaunar dasu.  Basufi minti goma da zuwa ba fitsari ya kama Asiya, cikin ranta sai dana sanin shayin da ta sha kafin su fito take. Ƙarshe data ga abin zai dameta ta miƙe ta tafi wajen wata mata da ke da office a corridor ɗin lobby ta tambayeta ina ne banɗaki, matar da keta tauna cingam kamar zata haɗa da harshenta tayiwa Asiya kwatance tana haɗe rai, Asiya ta wuce tana mamakin matar da fiskarta ya gama soyewa saboda bleaching.

**

“Na san ka san matsayinka a wannan Jaha. Kuma ka san baya daga cikin ayyukan ka abinda ka aikata”

“Your excellency…”

Gwamna ya ɗaga masa hannu ya cigaba “kar hakan ya ƙara faruwa Mr Lamara Damana. Matsayin Chief of Staff zai iya faɗawa hannun kowa nan gaba. Ina fata ka fahimta”

“Yes your excellency. Hakan ba zai sake faruwa ba da yardar Allah”

“Good. Now ka duba min ko kwamishinan ayyuka ya fara aikin da aka bashi”

Lokacin da COS ya fita Gwamna ya jawo takardar da ya ajiye ya kekketata sannan ya watsar. Ba zai taɓa lamunta da wannan ba. Fitar COS keda wuya Sakatare ya shigo ya sanar da Gwamna cewa ‘yan jaridan jiya sun dawo.

COS na shiga office ɗinsa ya cillar da file ɗin hannunsa takardun ciki suka watse.   Ya dunƙule hannunsa kamar mai shirin dambe, ya kira sunan Gwamna da ƙarfi “Saifuddeen Kachallllaaaaah!”

Yana cikin huci ya tuna da wani abu nan da nan yai saurin lalubo wayarsa a aljihu ya shiga danna kira, ba aɗauka ana farko ba sai a kira na biyu.

“Akwai matsala Kachallah” abinda ya fara furtawa kenan da kakkausar murya. Bai bari wanda yake maganar ya ƙarisa ba ya katse shi da cewa  ” har Gwamna zai yi iƙirarin cireni a matsayina. Ya manta ne? Ya manta ne?”

Yai shiru yana sauraron bayani daga ɗaya ɓangaren  sannnan ya ɗaura da cewa 

 “idan har bai san yadda akayi aka ɗaura shi akan kujera ba to kuwa lallai ƙaddarar da ta hau tsohon Gwamna za ta sameshi. Ta inda aka hau tanan fa ake sauka Kachallah… eh inaji…. sai dai abu ɗaya na sani idan har Saifuddeen ya cireni a matsayina saina gayawa duniya cewa Saifuddeen Sa’ad Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna…”

Saura kaɗan recorder da ke hannun Asiya ta faɗo saboda firgita da tayi.  Tayi saurin toshe bakinta saboda kar mutumin da take naɗan maganarsa ya jiyo nishinta. Ta fito daga banɗaki kenan za ta koma inda aka ajiyesu ta hango Chief Of Staff ya zo ya shige wani lungu a bircike. Curiosity nata na ‘yar jarida ya sa ta bi bayansa. Wani office taga ya shige hakan ya sa ta bi bayansa da zimmar ko za ta iya gano dalilin fushinsa tunda hanyar da ta ga ya fito tanan ne office ɗin Gwamna, koma minene ya ɓata masa rai yanada nasaba da Gwamna ɗin.

Ihun da ta jiyo COS yayi yana kiran sunan Gwamna yasa ta laɓe ta fidda ƙaramar recorder ɗinta ta fara naɗan maganar sa.

Ganin yayi shiru yana sauraron bayanin da ake masa ya sa tayi saurin jan jiki ta bar bakin ƙofar.

Ba ta ji ƙarshen maganar sa ba.

“Eh…ina sane amma… shikenan zan kiyaye sai dai gara a nuna masa cewa mune muka buɗa masa hanya har ya samu ya hau kujeran, idan aka cigaba da ninke shi a baibai zai yi abinda zai jawo masa dana sani… to shikenan zamu haɗu idan na tashi a office”

Da ƙyar Asiya ta iya komawa wajensu CY dan a tsorace take, abinda ta jiyo ya girgizata matuƙa yayinda tsanar Gwamna Saifuddeen ya dira a zuciyarta, dama ya aka ƙare balle kuma…

Ta samu CY na faman saita camera, shi da Sunusi suna taɗi shiyasa hankalinsu bai kai gareta sun lura da chanjawar yanayinta ba.

Bayan minti biyar sai ga Gwamna ya iso fiskarsa ɗauke da annuri. Kallon tsana Asiya ta bishi da shi tana ji a ranta kamar ta shaƙeshi ya mutu kawai.

Maimakon jiya da za a naɗi shirin sannan a editting na shi kafin a ɗaura a tasharsu yau kam live za a saka shirin a gidan talibijin na su.

Yau kam ba kamar jiya ba babu tsoro ko fargaba a tattare da Asiya, cike da nitsuwa ta fara gabatar da shirin. Tambayoyin da aka amince ta masa su takeyi sai da aka kai tsakiyar shirin sannan ta sako zancen tsohon Gwamna wanda ba Gwamna kaɗai ba hatta CY sai da ya sha jinin jikinsa da tambayar

“Gwamna Saifuddeen duba da yadda mutuwar tsohon Gwamna ya zo bagtatan ko za ka iya sanar damu yadda mutuwarsa ta zo maka?” Tambayar offscript ne baya cikin jerin tambayoyin da akace za a masa shiyasa ya ɗan ji abin banbaraƙwai amma ya dake ya amsa da cewa.

“Kowanni halitta dake doron ƙasa sai ya ɗanɗani mutuwa. Dukkanmu lokaci muke jira. Haƙiƙa mutuwar tsohon Gwamna ta girgizani matuƙa saboda yadda ya zo mana lokaci guda…”

“Excellency baka ganin ya kamata a duba mutuwar tasa kodai akwai lauje cikin naɗi duba da cewa Gwamna nada ‘yan adawa dayawa”

Ba dan shirin kai tsaye aka ɗaura shi ba da CY tuni ya katse ɗaukan shirin saboda yadda Asiya take chanja alaƙar shirin nasu.

Gwamna ya kalleta cikin zargi amma bai bari hakan ya bayyana a fiskarsa ba yace ” Malama Asya mutuwa koda ciwo ko babu ciwo sai anyita. Likitoci sun tabbatar da cewa hawan jini ne yai ajalin tsohon Gwamna Allah ya jiƙan rai”

“Ya yanayin alaƙarka da shi kafin rasuwarsa?”

“Munyi zama na amana da shi, Allah ya gafarta masa kurarensa da ma namu gaba ɗaya”

“Amin”

“Tambayata ta gaba ko miyasa Gwamna ya zaɓi Alhaji Bala Yamai a matsayin mataimakinsa duba da cewa ana zarginsa da cin hanci da rashawa har ma shekarun baya hukumar EFCC sun kama shi?”

Kafin Gwamna ya bada amsa daga chan ma’aikatarsu aka katse shirin aka saka talle saboda a samu daman katse ɓaranɓaramar da Asiya ke yi.

“Jesus! Aseey lafiyanki kuwa?”

CY ya faɗa da ɗan ƙarfi, kafin ta bashi amsa MD ya kirata tana ɗauka ya shiga surfa mata masifa kaman zai zo wajen ya bindigeta. Tana ajiye wayar tareda sauke ajiyar zuciya ta haɗa ido da Gwamna. Duk da tsanar da take masa hakan bai hana tasirin kallon sa gareta ba.

“Yaudara na ɗaya daga cikin abubuwan da na ke ƙyama. Miss Asya na yarda da wannan interview ne saboda babu maganar siyasa a cikinta, kar ki manta da wannan”

A yadda ransa ya sosu da abinda tayi niyyarsa ya miƙe ya bar wajen saidai idan har yai haka ya sani daga lokacin ‘yan jarida zasu murɗa labarin da cewa Gwamna ya ƙi amsa tambaya saboda bashi da gaskiya. Ya sani Alhaji Bala Yamai ba shine candidate ɗin daya so ya zama mataimakinsa ba sai dai kamar yadda Alhaji sani ke yawan faɗa masa cewa a siyasa dolene ka yi abinda bature ke kira compromise. Ba zai manta lokacin da Alhajin ya kirashi ya ce masa mataimakinsa shine Alhaji Yamai ba. Ya faɗi maganar kamar bashi da zaɓi, kamar ba shine mai ikon naɗa duk wanda yakeso ba.

“Alhaji Yamai yanada record na rashawa, Baba” ya faɗa da murya mai sanyi.

“Ka zo gida muyi magana” Alhaji Sani ya faɗa. Koda ya sameshi a gida bayani ya masa wanda hakan ya birkita shi har sai da asthma ɗinsa ta fara barazanar tashi.

Ya sani tun kafin ya kawo wannan matsayi Alhaji Sani Kachallah yana ɗaya daga cikin wanda suke riƙe ko yace suke juya jahar Congo. Tun zamanin mulkin soja ake damawa da shi har aka dawo mulkin farar hula.

“Mutane huɗu ne keda alhakin zaɓan Gwamna da Mataimakinsa. Wannan karan ɓangarena ne da Gwamna, ɓangaren Mataimakinsa yana hannun ɓangaren Yellow Group kuma sun zaɓi Alhaji Yamai. Kar ka damu, Alhaji Yamai hoto zai zama kawai” yadda Alhaji Sanin ya faɗi kalmar hoto sai ya tuna da yadda shima watannin baya yake kamar hoto a matsayinsa na mataimakin Gwamna. Ya so yaja da hakan amma bai samu ƙwarin gwiwar yi ba. Tun lokacin da Alhaji Sani ya gabatar da shi a jam’iyyarsu ya sanar dashi ma’anar tutar Jahar Congo. Kalar Baƙi da ta fi yawa a jikin tutar ita ke ɗauke da kaso 45% wanda Yallaɓai ke shugabanta yayinda kalar Blue ke ɗaukan 25%, kalar Red ta ɗauki 18% sai Yellow 12%.

  kalar blue ta Alhaji Sani Kachallah ne hakan na nufin da shi ake damawa a Gwamnati, hakan na nufin Saifuddeen ba shi da ikon yin komai sai da yardar sa.

Yanzu da aka dawo daga tallen da aka saka wanda ta kai kusan minti takwas bai ɓata lokaci ba ya amsa tambayar Asiya da cewa ya zaɓi Alhaji Bala Yamai ne a matsayin mataimakin Gwamna saboda an riga an wanke sunansa daga laifin rashawa da ake tuhumarsa da shi shekarun baya, ya haɗa da cewa Alhaji Yamai yanada experience a harkar siyasa fiye da shi shiyasa ya zaɓe shi. Lokacin da ya gama bayanin lokacin da aka ɗibarwa shirin ya ƙare dan haka Asiya bata sake wata tambayar ba ta ƙarƙare shirin.

CY na cewa Cut Gwamna ya miƙe ya tafi yayinda muƙarrabensa suka bi bayansa cikin sauri.

“Aseey kin fuck up Wallahi” CY ya faɗa yana girgiza kai yayinda Sunusi yake jimamin yanzu ɗan alkhairin da za a basu ya wuce tunda gashi ran Gwamna a ɓace ya bar wajen su.

Lokacin da aka katse shirin aka saka talle COS ya zame jiki ya wuce office ɗinsa. Abu ɗayane ya zo masa wato Asiya taji abinda ya faɗa idan ba haka ba babu yadda za ayi ta kawo maganar mutuwar tsohon Gwamna. Tunda aka bashi matsayin Chief of staff lokacin Gwamna Saminu Bacci ya saka CCTV a office ɗinsa saboda shiga masa office da akayi ba da izininsa ba aka bincika masa wasu takardu. Ya kori sakatariyarsa a lokacin amma ya sani ba da saninta aka yi hakan ba, bai jima ba kuwa ya gano wanda yai hakan. Babu wanda ya san yanada ɓoyayyiyar camera a office ɗin nasa. Kasantuwar Sakatariyarsa Jennifer bata desk ɗinta sanda ya shigo ya ƙara tabbatar masa da cewa Asiya ta ji wayar da yai tun ma kafin ya duba CCTV footage ɗin. Bai sha mamaki ba da yaga Asiya laɓe a bakin ƙofarsa da ‘yar ƙaramar na’ura da yake da tabbacin recorder ce lokacin daya kalli footage ɗin.

Asiya tana waya da Ubayd wani security ya iso ya ce ta biyo shi. CY da Sunusi suka zaro ido tareda tambayar lafiya. Bai ce musu komai ba yai wa Asiya jagora suka bar wajen. Asiya ta tsorata amma ta dake bata nuna ba saboda kar ta bada kanta, yau duk yadda za ayi sai dai ayi amma bazata taɓa fito da recorder ɗin nan ba.

Office ɗin Chief of Staff ya kaita kamar yadda tayi hasashe. Tayi mamaki da taga Sakatariya a office ɗin farko wanda ɗazo da ta zo babu ita. Lokacin da ta shiga office ɗinsa Mr Lamara Damana yana tsaye ya haɗe gira.

Jakarta security ɗin ya ce ta miƙo tana miƙa masa ya zazzage kayan ciki a walaƙance. Powder, lipstick, hankerchief, jotter, biro da earpiece ne a ciki. Wayar hannunta security ɗin yace ta kawo ta miƙa masa ba musu tana kallon COS da shima ya zuba mata ido yana mata kallon tsana. 

Wata na’ura da ke detecting devices security ɗin ya bi ya zagaye jikin Asiya da shi amma bai detecting komai ba.

COS yace ya miƙa masa wayar Asiya sannan ya basu waje. Bayan fitan security ɗin COS ya kalli Asiya ya ce “na san ba a waya kika ɗauki maganarba dan haka ki fito da recorder ɗin”

“Ikon Allah, ina tunanin ka manta cewa ni ‘yar jarida ce, wannan cin zarafi da kake min zai ja maka matsala” Asiya ta faɗa a kausashe.

Wani murmushin gefen baki COS yai wanda idan ba lura kayi ba baza ka gane murmushin yai ba saboda yadda gefen bakin ya tattare kamar mai shirin kuka.

“Asiya Shahidah Faruƙ Baba. Na san kina sane da haɗarin da ke tattare da wuce gona da iri a cikin aikin ku”

“Are you threatening me?”

“You know better”…

Lokacin da ta isa wajen su CY ko magana ba ta musu ba ta wuce gaba suka bi bayanta suna tambayar miya faru. Sai da suka shiga mota Asiya ta karɓi jakar camera da ke hannun CY ta buɗe wani ƙaramin zip ta ɗauko recorder a ciki ta damƙe shi a hannunta, yadda ta damƙe shi har sai da hannun ya fara rawa. CY kallonta yake yi cike da tambayoyi a harshensa amma ya yi gum da bakinsa tunda tace musu kar wanda ya mata magana.

Maimakon office gida tace Sunusi ya sauketa. Tana shiga ɗaki ta samu Umma na wanki a tsakar gida, ganin Ummanta duƙe tana wanki ya tuna mata da washing machine da ta ce zata siya tun watan daya gabata. Rashin lokaci ya sa take bada kaya a wanke mata sai ta haɗa dana Umman amma tunda Umman ta ce ba ta son a fita mata da kayan wanki waje ya sa duk weekend indai tana gida take wanke kayan mahaifiyarta.

A tsanake ta gaisheta  tace mata ta zo ɗaukan abune dan kar ta firgitata. Tana shiga ɗaki kai tsaye laptop ɗinta ta buɗe ta fara ƙoƙarin tura abinda ta naɗa zuwa Laptop ɗin. Maganganun COS sun ɗan razanata amma idan ta tuna itama tanada abinda zai iya wargaza mulkinsu sai ta tausashi ranta.

Kafin ta gama abinda take wayarta ta shiga ruri. MD ne ta sani kuma ba zata kulashi ba sai ta gama abinda takeyi. A ƙalla ta kai awa ɗaya da rabi a gida kafin ta shirya ta koma office.

Ta ɗauka MD zai mata faɗa kaman yadda ya yi a waya amma sai ta ji ya tausasa kalmominsa gareta “Asiya ban san mi kika naɗa a gidan Gwamnati ba amma ina so ki sani cewa zaki iya taka Gwamna ki kwana lafiya amma Lamara Damana ba zai barki haka ba”

“MD kana so kace…”

“Asiya na san kinada ƙoƙari sosai wajen dukkan ayyukanki amma ki sani ana iya barin halak saboda kunya”

Za tayi magana ya ɗaga mata hannu sannan ya cigaba ” already mutane sun fara reacting wa interview da kikayi amma nan da kwanaki kaɗan komai zai lafa, saidai idan kika sake bijiro da wani abun Asiya ba ke kaɗai fitinar za ta shafa ba idan ba ki ji ta ma’aikatarmu ba to ta iyayenki fa?” 

Jikinta yai sanyi ta kasa cewa komai.

“Asiya you are a field reporter not investigative reporter, kada kiyi aikin da ba naki ba. Faɗa da ‘yan siyasa ba abu ne da ake ƙareshi ta daɗi ba”

“Sir, kana nufin na watsar da gaskiya na rungumi ƙarya kenan?”

“Ban san mi kika sani ba Asiya amma koma minene ki yiwa Allah ki haƙura dashi saboda mutuncin ki. Lamara Damana ba mutumin da za ki iya ja da shi bane”

“Shikenan na ji” 

Bayan Asiya ta bar office ɗin. MD ya sauke ajiyar zuciya. Kashedi Chief of staff ya masa ɗazu daya bugo akan in har aka fitar da wata magana da ta shafeshi Hill TV za ta rasa matsugunni a Jahar Congo. Ba wannan ne matsalar ba. Jin ya ambaci sunan Asiya ya sa shi fahimtar dalilin dayasa Asiya ta yiwa Gwamna tambayoyin da tayi, duk da bai san takamaimai mi Asiyar ta jiyo ba amma yanada yaƙinin abune da ya shafi mutuwar tsohon Gwamna. Duk wanda ya ke bibiyar siyasar jahar ya san cewa Lamara Damana shine shugaban munafukan gidan Gwamnati masu hana ruwa gudu. Mr Damana ya fara aiki daga Sakatare ne a hankali ya dinga shiga cikin manya ya zamana anyita ƙara masa matsayi har ta kai lokacin Gwamna Saminu Bacchi aka bashi muƙamin Chief of Staff. Tunda aka koma mulkin farar hula babu Gwamnan da Mr Damana bai yi aiki da shi ba.

“Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta naɗi abinda yafi ƙarfinta, idan ya fito waje bana tunanin za ta sake yin rahoto da bakinta” kashedin COS na ƙarshe kenan.

Yana son Asiya tun farkon zuwanta ma’aikatar lokacin da tazo yin bautar ƙasa. Ya nemi soyayyarta ta ƙi shi, wanda yanzu ya riga ya haƙura tunda yaji ance an kawo kuɗin aurenta.

 Duk da COS bai buɗa ba ya fahimci mi yake nufi sarai dan ba yau ya fara aikin jarida ba. Ba zai taɓa mantawa da wani ogan sa edita Mr Simon da suka fara aiki tare lokacin yana Lagos ba, shima kamar Asiya taurin kai ne da shi, indai a wajen bayyana gaskiya ne to baya jin tsoro. Ranan da gidan jaridarsu ta wallafa shafi akan wani asiri da Mr Simon ɗin ya jiyo na wani fitaccen ɗan siyasa ranan bai kwana duniya ba domin yana hanyar dawowa daga office motarsa tayi bindiga ta kama da wuta.

 Ba zai manta da wani abokinsa Ja’afar ba. Ja’afar Bello investigative reporter ne daya binciko yadda wata Matar Minister ke safarar ‘yan mata karuwanci zuwa ƙasashen waje. Yanada isassun evidence a kanta har an fara shari’a haka kawai aka nemi Ja’afar Bello aka rasa, ko sama ko ƙasa. Yanzu shekaru shatara kenan babu labarinsa.

Yana tsoron kada taurin kan Asiya ya jawo mata fitina.

Asiya koda ta koma office tunanin maganganun COS da ta MD ta dinga yi, a wani ɓangare kuma tana tunanin bazata taɓa bari Gwamna Saifuddeen yaci bulus ba. Ta sani cewa abinda ta naɗa bai kai evidence da za a iya kama Gwamna ba amma idan har maganan ta fito zai jawo cecekuce har a fara bincike, koda ya sha yanzu lokacin zaɓe abokan adawa za su yi kamfen da maganar su hana mutane zaɓanshi, ko kuma idan har akabi komai da gaskiya to dole ne ayi impeaching ɗinsa. Babu abinda take ganin yanzu zai faranta mata rai a rayuwa sama da taga an tsige Gwamna Saifuddeen Sa’ad Kachallah …

***

A office Asiya ta dinga jayayya da zuciyarta akan ko ta bi shawaran MD tayi shiru da abinda ta ji ko kuma dai ta fitar da shi ta tada fitinar da zai jawa Gwamna matsala. Shawara ta yanke akan idan Ubayd ya zo hira za ta nemi shawaransa ta ji mi zai ce. Daga baya ta kasa haƙuri har zuwa lokacin ta kira numbarsa tace ya hau whatsapp akwai abinda za ta gaya masa. Sai bayan minti shabiyu ya hau saboda yana duba wani patient ne a lokacin da sukayi waya.

A tsanake ta masa bayanin komai da kuma abinda MD ya faɗa mata. Bai tsaida ita ba har sai da ta gama bayani ta ce miye shawaransa gareta.

” Asiya Shahidah na roƙe ki da girman Allah ki haƙura da abinda kike shirin yi domin ba zai haifar da ɗa mai ido ba. For God sake! we are getting married soon. Kina so rikicin siyasa ya jawo miki wata fitinar ne? Idan har abinda kika ji gaskiya ne then you are not safe Aseeya ba ke kaɗai ba hatta ‘yan uwanki ba su tsira ba. Asiya ina za ki iya rikici da Lamara Damana?, Please ki mayar ma sa da recorder ɗinnan ki nuna masa ba za ki taɓa fitar da maganan da kika ji ba”

Tana gama karanta rubutun ta sauka tareda jan dogon tsaki. Wai sunata maganan Lamara Damana, Lamara Damana, shi waye da za ta ji tsoronsa. Idan har ba za a fitar da labarin a ma’aikatarsu ba ai akwai social media. Ringing ɗin wayarta ya dawo da ita daga tunanin da takeyi. Koda ta ɗauki wayar Ubayd cigaba da roƙonta yayi yana cewa ta masa alƙawarin ba abinda za tayi, da ta ga ya dameta tace mishi ta ji za ta yi shiru sai dai chan ƙasan ranta ta san ba haka bane.

Lokacin da suka tashi CY ne ya nemi ya kaita gida saboda yana son jin labarin miye dalilin sauya tambayoyi da tayi, sannan miye dalilin da yasa COS ya nemi ganinta.

“Na san gulma ne ya kawoka Clement kuma ba za ka ji komai ba”

“Ahn-Ahn, Aseey Darling ya zaki fassarani haka, jiya ma fa ni na kai ki gida”

“Ahaf, ka gama kame-kamen naka dai ka dawo hanya, magulmaci”

CY yai dariya ya wuce gaba.

Suna fita daga ma’aikatar Obinze Maigadi ya ɗaga waya jiki na rawa ya kira wata number ya ce yanzu Asiya ta fita daga ma’aikatar tasu ya haɗa da cewa tare take da abokin aikinta akan machine kafin aka katse kiran.

CY na tuƙi yana yiwa Asiya taɗin budurwarshi mai suna Evelyn da ta ce masa dole sai ya koma ɗariƙar Katolika (catholic) kafin ta iya auren shi, Asiya tana masa dariya. Ba suyi aune ba dai-dai za suyi kwana wata babbar mota da basusan daga ina ta fito ba ta zo ta mangajesu hakan yasa Asiya tsalle sama ta faɗi gefe yayinda motar tabi ta kan machine da ta danne CY ta wuce da bala’in gudu…*THE GOVERNOR’S WIFE*

…… 

“Darling” Bilkisu Kachallah ta kira da fake American accent ɗinta wanda kunnen Saifuddeen ya kasa banbance “Dolin” tace ko kuma “Durling”. Ya dai ɗago ido ya kalleta ba tareda ya furta komai ba. Ya sani ya kamata ya ce mata tayi kyau ko kuma yace jan lingerie (rigar bacci) data saka ya amshi jikinta sosai amma bai ce komai ba.

 A mafiya lokuta idan ta yi shiga irin wannan tana buƙatarsa ne, ba kawai buƙata ba domin daga ƙarshe idan ta kwanta gefensa tana shafa gashin ƙirjinshi a hankali za ta bijiro masa da wata buƙatar ne, mafiya yawanci abubuwanda take tunanin ba zai mata su ba idan ta tambayeshi kafin ta shigo turakarsa su take tambaya.

Rabonsa da ita tun ranan farko da suka tare a gidan Gwamnati. Ba wai baya buƙatarta bane amma rashin nuna damuwarta gareshi yasa yake haƙuri da ita, ƙila saboda a koyaushe baya son takura mata ne. She’s not yet 40 amma kuma lamarin sex life ɗinsu ya lalace tun lokacin da ta haifi Junior.

Takardu yake dubawa ta tura takardun gefe ta shiga kissing ɗinsa, farko daga goshinsa, kunnensa kafin ta kai bakinsa. Ba a jima ba ya tureta yace ” ki bani minti goma na ƙarisa aikin dana ke”

“Haba Darling, ka san yaushe rabonka da ni kuwa? Aiki can wait please” ta faɗa tana zunɓura baki.

So yake ya ce mata laifinta ne idan bai nemeta ba tsawon kwanakin nan, saboda duk lokacin daya samu free time yake buƙatar kulawarta baya samu, amma bai faɗi hakan ba sai yayi mata murmushinsa mai shiga rai yace ” kar ki damu, ba zan jima ba”

Bilkisu ta kwanta gefen gado tana kallon ceiling yayinda ya cigaba da duba takardun da idan bai duba yanzun ba bashida lokacin duba su gobe.  Kusan minti talatin da uku kafin ya gama komai lokacin har Bilkisu ta fara gwarti. Ya je ya ajiye takardun acikin wani file ya saka a briefcase.

Bai tashi Bilkisu ba saboda ya san a gajiye take yau tace masa ta fita duba gidan marayu bai san details ɗinba kuma bai tambayeta ba.

“Shine baka tasheni ba” ta faɗa lokacin da ta tashi da Asuba. 

“You’re tired”

“Still” ta faɗa tana haɗe rai.

“To barin dawo daga masallaci” 

 Lokacin daya dawo daga sallar Asuba ta riga tayi wanka ta chanja kaya, ba rigar bacci ta sa ba amma shima kamar na jiya guntu ne mai hannun spaghetti, rigan ya kamata sosai, ya bayyana ƙaton tumbinta da yake a taƙune.

Kamar yadda yai hasashe yana shirin miƙewa ya je yai wanka ta faɗa masa buƙatarta na son buɗe Bilkisu Kachallah Foundation dan tallafawa marayu. Ajiyar zuciya yai sannan yace “Allah ya sanya alkhairi” ya wuce banɗaki tda sauri…

Meeting biyu ya shiga daga zuwansa office, yanzun ma wani meeting ɗin zai shiga nan da minti talatin. Yana duba report ɗin da aka kawo masa. Sakatare ya shigo da wasu takardu a hannunsa. 

“Your excellency na samu COS ya reschedulling ziyarar da za ka kai ƙaramar hukumar  Antu zuwa jibi laraba”

“Ok”  Gwamna ya faɗa yana cigaba da duba takardun da ke gabansa.

“Excellency kafin na manta. ‘Yan jaridar da suka zo jiya sun yi hatsari”

“Asya!” Gwamna ya ɗago kai da mamaki

“Ita da abokin aikinta suna komawa gida wata babbar mota ta afka musu…”

“Is she alive?” Ya faɗa da tsananin damuwa a tattare da shi

“Na ji labarin dukansu suna raye. Ita Asiya ance nata da sauƙi amma shi ɗayan kam rai a hannun Allah”

“Hasbunallah! Keep me posted akan labarinta” ya faɗi labarinta kamar ita ɗaya akace tayi hatsarin.

Bayan fitan Sakatare daga office ɗinsa ya ɗaura haɓarsa akan hannunsa yana tuna siririn ushiryar dake tsakanin haƙoranta wanda yake ƙara mata kyau idan tana murmushi.

***

Umma ne a gefen gadon da aka kwantar da Asiya lokacin da Ubayd da Abba suka shigo. Abba ya tambayeta ko Asiyan ta tashi tace masa bata tashi ba. Lokacin daya zauna ta tambayeshi jikin abokin aikin Asiya Abba yace ance musu har yanzu bai farfaɗo ba. Ubayd ya ƙurawa Asiya da ke kwance ido bai san lokacin da hawaye ya fara zubo masa ba. Ba dan kariyar Allah ba da ita ne ke halin da CY yake ciki ko kuma ace da yanzu an jima da bisineta. Yai saurin goge hawayensa dan kar Umma ta gani. Alhamdulillah ya furta a ransa kafin ya yiwa su Umma sallama ya fita.

Ba a jima ba Asiya ta farka a karo na biyu tun safiyar yau. Da farko data farka   kuka ta dinga yi tana faɗin a kaita wajen CY. Yadda ta birkice musu sai da aka mata alluran bacci.

Wannan karan ma data farka sunan CY ta kira. “Abba CY ya mutu ko?, sun kashe shi ko?”

“Kwantar da hankalinki Shahidah. Yana nan da ransa”

Da bata faɗa gefen titi ba, da ba wannan zancen akeyi akanta ba. Gefen goshinta, kunnenta da kafaɗarta sai kuma gwiwarta da ya kurje su kaɗai ne ciwon jikinta, sai dai saboda irin faɗuwar data yi duk jikinta ciwo yake mata.

Asiya ta sauke ajiyar zuciya hawaye na zubo mata.

“Abba idan CY ya mutu bazan taɓa yafe musu ba. Kuma sai na…”

“Asiya!” Ya kira sunanta da ƙarfi har sai da ta tsorata.

“Ba abinda zakiyi, kina jina? Nace ba abinda zakiyi. Zan mummunan saɓa miki idan kika sake maganan mutanen nan”

“Abba…”

“Zamuyi magana idan munje gida”

Ta kalli Abba da mamaki, ba yadda za ayi yai wannan maganar sai dai idan har yasan wani abu. Kenan Lamara Damana ya tuntuɓeshi.

Da yamma da Ubayd ya dawo ta tambayeshi ina CY yace mata CY na CUTH (Congo University Teaching Hospital ) an ɗaura shi a na’ura saboda ya shiga coma.

“Mutuwa zai yi ko?” Ta tambaya murya na rawa

“Mine mutuwa a hannun Allah take. Ki masa addu’a amma he’s in a very bad shape infact an yanke masa hannu ɗaya”

“Ya Allah!” Ta riƙe baƙi.

‘Yan wajen aikinsu sun zo sun gaisheta. MD shi kaɗai yazo da yamma lis kuma bai jima ba saboda lokacin ɗakin nata akwai mutane. Lokacin daya fita Abba ya bi bayansa da sauri. Bayan sun samu waje sun keɓe sannan MD ya bashi takardar dakatar da aiki na Asiya. Abban ne ya nemi hakan shiyasa yana karɓa ya masa godiya ya koma cikin Asibitin.

MD ya girgiza kai yana fata wannan ya zamowa Asiya mafita saboda ta tsokano tsuliyar dodo. 

Kwanan Asiya biyar a Asibiti aka sallameta har lokacin kuwa ba suyi maganar abinda ya faru da kowa ba saboda Abba ya hanata. Kamar yadda kowa ya ɗauka cewa tsautsayi ne ya kawo hatsarin da suka yi Asiya ta san ba haka bane kuma ta san Abba da Ubayd ma sun san ba hakan bane. 

Kafin su wuce gida ta roƙi Ubayd da ke tuƙi akan ya kaita taga CY. Da farko ya ƙi amma data takura sai Umma tace ya kaita itama tana son zuwa dubashi.

 Lokacin da taga CY kwance an jona masa wasu na’ura a jiki sai kawai ta fashe da kuka. Da Allah yayiwo CY mace da zata iya cewa har abada ba za ta iya samun ƙawa kamarta ba saboda yadda jininsu ya haɗu kuma suka fahimci juna, sai dai CY namiji ne shiyasa abotar tasu take da iyaka.

Sun gaisa da mahaifiyarshi inda take jadaddawa Asiya cewa Gwamna ya biya   kuɗin aikin da za a masa a ƙasar waje takardunta da ake processing yasa basu tafi ba sai wani sati. Jin Josephine mahaifiyar CY ta ambaci sunan Gwamna yasa zuciyar Asiya ta cunkushe, tsanar mutumin ya sake sauka mata. Munafuki ta faɗa a ranta, shine ya jawo wannan matsalar sannan  yake ƙoƙarin rufe bakin mutane da maganar biyan kuɗin aiki. Ita Asiya ba zata yi shiru ba, tayi alkawari.

Sanda suka isa gida Abba ya zaunar da ita ya mata bayani.

“Abinda ya faru Asiya ki ɗauke shi a matsayin ƙaddara. Ki riƙe bakin ki da zargi domin ba abinda hakan zai jawo sai fitina. Na saka an dakatar dake daga aikin ki, daga yanzu babu ke babu aikin jarida. Ban sani ba idan kin koma ƙarƙashin ikon Ubaydullah ko zai barki kiyi amma iya watannin daya rage miki ƙarƙashin kulawata, na dakatar da aikin ki”

Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa

“Waɗanda kika samu saɓani da su sun zo sun karɓi laptop ɗinki na gida da wajen aiki dama wayarki amma sun dawo da wayar taki jiya. Sun bayarda saƙo a baki *ki cigaba da rayuwarki kamar komai bai faru ba, hakan zai sa su manta da komai*”

“Abba ya zaka min haka?” Ta ma rasa haushin wanne ɗaya za ta ji. Na halin da CY ya shiga saboda ita ne ko kuwa dai na aikin da ya hanata ne ko kuma na ɗauke laptop ɗinta da COS ya sa akayi. Abin takaicin ma a laptop ɗin kawai ta tura recording ɗin ba ta riga ta tura a wani wajen ba.

“Asiya ki yiwa Allah ki manta da komai. Bana so ko da Umman ki kiyi  wannan maganar saboda kar hankalinta ya tashi”

“Abba dafa na mutu yanzu, dafa…”

“Ki godewa Allah kawai ki riƙe bakin ki Asiya”

Abba bai bata daman magana ba sai kawai ta fashe masa da kuka, da tayi mai isarta ta miƙe ta bar falon.

Tuwon shinkafa miyar taushe Umma ta zubo mata bayan  tayi sallar Isha, ta haɗa mata da zoɓo mai sanyi. Duk yadda take marmarin ci kafin a girka yanzu ya fita mata aka saboda rasa recorder ɗinta da tayi, koya akayi suka samu recorder ɗin ma oho, dan a ƙasan katifar Umma ta saka bayan ta gama kwafan abinda ke ciki zuwa laptop ɗinta. It means bata da wani evidence kenan.

Umma ta katse mata tunani da cewa ta ci abinci 

“Umma ki bani a baki” ta faɗa da yaren kurame. Umma tayi murmushi ta wanke hannu ta fara bata a baki.

Ƙarfe shabiyu na dare tanata juyi a kam gado ta kasa yin bacci. Wayarta da Abba ya bata an share komai na kai kamar sabon waya. Tunanin rashin imani irin na Gwamna ya tsaya mata a rai, ita yanzu ta daina ganin laifin COS ma dan gani take da umurnin Gwamna ya aiwatar da komai. 

Ƙarshe ta jawo wayarta ta sake downloading twitter da facebook da aka goge. Tana saka gmail da password ɗinta na da ta samu access zuwa ga tsohon account ɗinta nan da nan ta shiga rubuta dogon article a blog website nata, data gama ta kwafa ta kai shi twitter ta jerasu a dogon thread of tweets . Ta kai facebook ma ta posting a wall nata. Tana ganin duka rubutun ya hau tace “Excellency yanzu aka fara wasan”

Yadda ake fama da talauci da wasu matsaloli wannan rubutu nata tabbas zai jawo hankalin mutane kan Gwamna and this is good. 

 Kalaman ɗan jarida suna da kaifi, kalaman da ke iya kunna jita-jita tsakanin al’umma ya maida gaskiya ƙarya sannan ƙarya ta koma gaskiya.

Kusan minti goma shabiyar kafin ta fara ganin comment na ‘yan tsirarun mutanen da suka gani. Tana bin comments ɗin tana murmushi idan taga wanda ya yabi Gwamna kuma sai ta yi tsaki. 

Asiya bata kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi, dake Umma a ɗakin Abba ta kwana yasa bata samu mai tashinta da Asuba ba sai ƙarfe shida saura minti biyar da Umma ta shigo ɗakin ta tasheta sallah…

***

Chief of Staff Lamara Damana yana kwance kusa da matarsa ƙarfe huɗu da rabi wayarsa ta shiga ƙara. Bayan ya ɗau wayar miƙewa yai ya bar kan gadon dan wanda ya kira ɗin special agent ɗinsa ne mai kula masa da hidimominsa a yanar gizo.

“Ina jinka Felix” ya faɗa lokacin daya zauna a kujeran dake falonsa.

“Asiya again?” Ya faɗa yana cizen leɓe. Lokacin da aka tabbatar masa Asiya bata mutu ba sannan  bata ji ciwo sosai ba yaso ya sa a ƙarisata a Asibiti amma daga baya ya chanja ra’ayinsa. Beside ita macece dole taji kashedin iyayenta.

Yanzu da Felix ke karanto masa abinda ta ɗaura yayi mamakin ƙarfin halinta.

“This girl! Yanzu dai kasa a blocking accounts nata, sannan ka controlling duk wata jarida da zata yi sharyi akan abinda ta rubuta”

Lokacin da Asiya ta idar da sallan Asuba  ko Azkar bata yi ba ta jawo waya ta fara duba twitter account ɗinta sai dai kash! An riga an banning account ɗin tun misalin ƙarfe biyar na Asuba, ta zaro ido waje tareda duba website nata cikin sauri sai dai shima an blocking na shi, facebook ma haka.

Tayi ƙoƙarin searching article ɗin a google amma an sauke shi gaba ɗaya babu ko mai kama da shi.

“Nooo” ta faɗa tana kaiwa sallayar da ta ke kai duka…

Gwamna na zaune a office wayarsa ta shiga ƙara yana dubawa yaga sunan Baba.

“Saifu mi yake faruwane? Yanzu nake jin wai Umaru Kwom yayi wata magana a twitter akan abinda wata ‘yar jarida ta ɗaura”

“Bani da labari Baba amma yanzu zan tabbatar”

“Nayi magana da COS amma ka tabbatar da adviser ɗinka ya kashe duk wani hayaniya da za ayi a yanar gizo akan maganar”

Gwamna na ajiye waya ya kira mai magana da yawunsa a yanar gizo.

Umaru Kwom abokin adawar Saifuddeen Kachallah ne saboda lokacin yana tareda Alhaji Sani Kachallah ya so ya zamo mataimakin tsohon Gwamna Saminu Bacchi amma Alhaji Sani ya ƙi ya tsaida Saifuddeen, tunda aka tsaida shi kuwa ya fice daga jam’iyyarsu ta CDA ya koma Q party.

Lokacin da Special adviser Ahmad Tanko ya shigo ko kaɗan Gwamna bai ji daɗin yadda aka ƙi sanar dashi abinda ya faru ba.

“Mi Umaru Kwom ya ce?”

“Excellency an riga an cire duk wani tweet ko post na ‘yar jaridar amma awa biyu da suka wuce Umaru Kwom ya tweeting wasu maganganu daga ƙarshe ya haɗa da screenshot na tweet ɗin ‘yar jaridar”

“What did he say?” Gwamna ya faɗa da ƙarfi.

Ahmad ya fito da wayarsa ya fara karanta tweet ɗin “inada tabbacin ‘yar jaridan nan tayi gaskiya duba da yadda Gwamna ya biya kuɗin aikin  da za ayi wa Clement Yohanna a ƙasar waje. Idan ba a manta ba Clement da Asiya sune suka je interview ranan, idan har babu lauje a cikin naɗi ba abinda zai sa ayi yunƙurin hallaka ‘yar jaridar a ranan da tayi maganar mutuwar Gwamna Saminu Bacchi. Bisa wannan, muna so mu gayawa Gwamnatin SSK cewa duk abinda ya sami Asiya  ‘yar jarida nan gaba zamu yi ƙaran Gwamnati. #a binciki mutuwar tsohon Gwamna”

SSK ya sauke ajiyar zuciya kafin yace Ahmad ya miƙa masa wayar yaga rubutun da Asiya tayi.

Bayan ya gama karantawa ya miƙa masa wayar yace ya fita masa daga office ɗinsa.

Ba yadda za ayi Asiya tayi wannan iƙirarin idan har ba wai ta ga ko ta ji wani abu ranan da suka zo bane. Dole ne ya gana da ‘yar jarida Asiya Shahidah…

***

“Shikenan ai tunda kinyi gaban kanki, kin nuna cewa ba nina haifeki ba”

“Abba ba haka bane, Wallahi ba haka bane”

“Kinyi gaskiya Asiya, ba nina haifeki ba  ban kuma manta da hakan ba.Tunda ban isa na baki shawara ki bi ba shikenan Allah ya baki sa’a. Kije kiyi magana da Umaru Kwom daganan ku wuce kotu ku bi wa Marigayi Saminu Bacchi hakkinsa”

Asiya ta kalli Abba tana zaro ido. Kenan Ubayd ya gaya masa komai.

“Tashi ki tafi”

“Abba…”

“Tashi ki tafi kawai”

Jiki a sanyaye ta fice daga falon.

Ɗazu Umaru Kwom da kansa ya kirata yace yana son haɗuwa da ita saboda su tattauna iƙirarin da tayi a yanar gizo. Ya tabbatar mata yana tareda ita ɗari bisa ɗari. Bata ɗauka Abba zai fassara maganar haka ba. Abba bai taɓa faɗin magana makamancin wannan ba hakan na nuna ba ƙaramin fushi yai da ita ba. Ubayd ma tun safe daya kira ya gama balbaleta da masifa bai sake waiwayanta ba, koda ta kirashi dan ta sanar dashi kiran Umaru Kwom ƙin ɗaukar wayarta yai.

Lokacin da zata shiga ɗakinsu ta ji Hindatu na mata habaici wai ‘karyar ‘yan siyasa’ bata tanka mata ba ta shige ɗaki. Rasa ma mi zatayi tayi dan yadda ran Abba ya ɓaci bata jin zata iya zuwa wajen Umaru Kwom.

Da yamma lis tana kitchen tana haɗawa Umma zoɓonta na siyarwa Ubayd ya shigo da sallama. Kasa amsa sallamar tayi saboda wani tsoro da taji ya taso mata lokaci guda. Umma ba ji take ba bata ma san anyi sallamar ba tana faman tuƙa tuwon Masara.

“Inna Yaha ina Asiya?” Ubayd ya faɗa bayan ya leƙa ɗakin Umma bai ga kowa ba.

Inna Yaha dake ƙullin gyaɗa ta kauda kai gefe tace “kaban ajiyarta ne?”

Bai ma gama jin mi take faɗa ba ya wuce kitchen.

Suna haɗa ido da Asiya ta ji gabanta ya faɗi. Idon Ubayd ya kaɗa yayi ja.

Sama-sama ya gaishe da Umma yace da Asiya ta biyo shi.

 

“Yaya Ubayd miya faru?” 

Bai kulata ba ya fice daga kitchen ɗin cikin sauri.

“A dai bi a hankali har yanzu ba a shafa Fatihan ba” Inna Yaha ta faɗa tana tauna gyaɗa.

Da Asiya da Ubayd ɗin duk babu wanda ya kulata suka shige falon Abba.

“I’m disappointed in you Asiya. Ban ma san mizan faɗa ba. Tunda attension kike nema kin samu yanzu. Congratulations! Gwamna zai zo wajenki yau da dare”

“Gwamna kuma?” 

“Abinda kike nema kenan ina, kin samu sai mi ya rage kuma”

Zuciyarta ne ya tafaso. Taya zai zargeta da neman suna.

“Kar ka gaya min magana, idan baza ka tayani neman hakkina ba baka da ikon zargina”

“Asiya kar ki kawo mana rikicin siyasa gidan nan. We are happy the way we are”

“Ni ban san mi kake nufi ba. Ni ba harka nake son yi da ‘yan siyasa ba i just wanted to…”

“A gaban Gwani aka mari Abba” maganarsa ya katseta.

“Mari?” 

“Yes Asiya. Abba bai gaya miki yadda komai ya faru bane saboda baya so ya ɗaga miki hankali, amma ke ba abinda kika sani sai kanki.  Ranan da suka zo karɓan Laptop ɗinki Gwani na wajen shi ya faɗa min komai. Asiya yaron da bai kai sa’an Habibu ba ya ɗaga hannu ya mari Abba saboda ke…”

“Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’oun”

“Ko kin san Lamara Damana yayiwa Abba kashedi da kashe ni da ke da su Habibu? Ko kin san saboda hakane ya je ya samu MD ɗinku akan ya sallameki?. Ofcourse ke ba ruwanki tunda kinada irinsu Umaru Kwom da zasu goya miki baya idan wani abu ya same ki.

“Asiya end this thing once and for all Dan Allah. In har da gaske kina sona ki ajiye maganar nan, idan ta kama ma ki rubuta cewa abinda kika faɗa ƙarya kikeyi indai hakan zai kawo maslaha to kiyi. I’m having bad feeling about this Asiya”

Bai jira amsarta ba ya fice daga falon ya barta tsaye tana hawaye.

Da Abba ya dawo daga sallar Isha ya kirata ya sanar mata Gwamna zai zo wajenta anjima. Bata nuna masa cewa Ubayd ya gaya mata ba saima haƙuri data shiga bashi kan abinda ta jawo masa…

***

Daga office bai wuce gidan Gwamnati ba asalin gidansa ya wuce ya chanja kaya daga office suit zuwa riga da wando da face cap duka baƙaƙe ya haɗa da baƙin glass saboda yaiwa fiskarsa kariya dan kar a ganeshi. Daga nan ya ɗauki tsohon drebansa yace ya kaishi layin ‘yan dabino. Sakatare ya riga ya kira dreban ya masa bayanin gidansu Asiya dan haka bai tsaya ko’ina ba sai ƙofar gidan. 

Lokacin da aka tsaya yayi kusan minti biyu kafin Gwamna ya kira numbar Abba ya sanar dashi gashi a ƙofar gida. Ko minti ɗaya bai cika ba Abba ya buɗe ƙofar falonsa dake fiskantar ƙofar gida ya fito jiki na rawa. An riga an kashe wutan ƙofar gidan shiyasa da akwai ɗan duhu. Yana ƙarasowa Gwamna ya buɗe ƙofa ya fito kafin kace me sun shige falon Abba.

 Sai da Gwamna ya zauna kafin Abba ya zauna yana risinawa duk da zai bawa Gwamnan shekaru kusan goma shatakwas amma girma girma ne.

A tsanake suka gaisa kafin Abba yace masa bari ya kira Asiya.

Asiya na ɗakin Umma ta takure waje guda Abba ya shigo da sallama.

“Yana jiranki”

“Abba” ta faɗa a hankali kamar mai ciwon baki

Abba ya samu gefen gado ya zauna ko kallon Asiya bai yi ba har ta fice daga ɗakin sanye da dogon hijabin sallarta.

Ƙanshin turarensa ya game falon dan tana buɗe ƙofa ƙanshinsa ne ya mata marhaban. Kallon tsana ta bishi da shi har ta zo ta zauna daura da shi. Har lokacin data zauna bai ɗago ya kalleta ba, idonsa na kan wayarsa. Ganin bashida niyyar magana yasa Asiya tace ” akwai abinda nake yi kafin na fito, zan koma”

Har ta fidda ran zai amsa tana shirin miƙewa ta bar masa falon taji yace “miyasa kike zargina? Mi kika sani?”‘

Da ita mai ashariya ce da ta ɗura masa ƙazamar ashar a wajen.

“Ji wani tambayar rainin hankali a nan. Your excellency na san komai, na san abinda ka aikata amma kuma zan yi shiru ne kawai saboda Abbana. Sannan ka sani akwai Allah “

Lokacin daya ɗago ido bataga ƙwayar idonsaba saboda face cap ɗinsa ya tare. 

Sai dai duk da haka sai da taji bugun ƙirjinta ya chanja.

” na yaba da jajircewarki sai dai zargi babu shaida matsalace Asya. Umaru Kwom zai yi amfani dake ne ya yar, you are too young for that

“Idan kinada shaida akan abinda kike iƙirari kuma, kina iya gabatar min yanzu”

Wani abune yazo ya tokare mata maƙoƙaro dai-dai lokacin da take ƙoƙarin kurma ihu. Ita Gwamna zai rainawa hankali bayan shi ya aiko akazo aka ɗauke recorder da laptop ɗinta.

Bata san ya akayi ta samu ƙwarin gwiwa ba, ƙila tsanarsa da tayi ne ya bata wannan ƙwarin gwiwa, ƙila kuma saboda marin da Ubayd yace anyiwa Abba ne.

Jug ɗin ruwa da aka ajiye a tsakiyar centre table ta ɗauka ta buɗe ta watsawa Gwamna a fiska.

“Wannan shine shaidar ka, Azzalumi”

Tana tsaye riƙe da jug ƙirjinta na bugawa da ƙarfi kamar zai ɓallo, ta kasa ko motsawa a wajen.

Ya kai sakan arba’in kafin Gwamna ya iya cire hular kansa ya buɗe manyan idanunsa. Loƙacin da ƙwayar idonsa ya shiga cikin na Asiya tsabar tsoro saida fitsari ya tsirto wa Asiya.

Yai shirin buɗe baki yai magana amma ya fasa kawai sai ya miƙe tsaye, bai gama miƙewa ba Asiya ta fece da gudu ta bar falon…*THE GOVERNOR’S WIFE*

…… 

“Jiya na yi bacci da wuri ban san yaushe ka shigo ba”

Gwamna bai kulata ba ya cigaba da kurɓan shayin dake hannunsa a hankali

 “gobe zan wuce China, idan na gama siyayya a chan zan wuce Dubai”

“Na ɗauka wata uku uku kike zuwa sari” ya faɗa yana kallonta

“Manager yace ana buƙatan sabbin kaya, ka san latest goodies nake shigowa da shi”

“Ok”

Bai sake cewa komai ba ya cigaba da cin abinci a hankali.

Jiya bai shiga gidan da wuri ba sai kusan ƙarfe biyu saura na dare. Baccin awa biyu yai ya sake miƙewa dolene ya je office da wuri saboda wani exco meeting da zasu yi ƙarfe takwas na safe.  Har yanzu bai bar mamakin abinda Asiya ta masa ba. Gaskiya yarinyar tanada ƙarfin hali.

 Jiyan Asiya na fecewa yai murmushi dan abin dariya ya bashi. Yana fita cikin sauri ya je ya shige mota Dreba ya wuce da shi gidansa. A nan ya chanja kaya ya ɗan huta kafin ya shiga rubuta waƙa, kafin ya ankara ƙarfe ɗaya tayi dan haka ya tattara komai ya koma gidan Gwamnati. Sai daya leƙa ɗakunan yaran kafin ya je ya kwanta. Ya lura da cewa Nana da Zunairah sun rugume juna cikin bargo amma bai ɗauke shi komai ba. Mahirah kuma da alama karatu take bacci ya ɗauketa dan ga littafin nan gefen gado yana shirin faɗowa. Ya ɗauki littafin mai suna Americanah ya ajiye a gefen side drawer yai murmushi domin Mahirah ce ta ɗauko son karatunsa, bayan ya kashe wuta sannan ya wuce ɗakinsa inda Bilkisu ke kwance ta jima da barin nahiyar Africa…

Ta sani abinda tayi bai dace ba, shiyasa lokacin data fito banɗaki ta shige da gudu. Bata fito ba kuwa sai da Inna Yaha ta fara ƙwanƙwasa ƙofar. Lokacin data isa ɗakin Umma, Abba baya nan dan haka ta fara ƙoƙarin chanja kaya ƙirjinta na wani irin dokawa kamar wanda tayi tsere.

Washegari kasa zuwa gaida Abba tayi tana zaune a ɗaki ta kasa leƙa ko ƙofar ɗaki tunda tayi Alwalar Asuba.

Ɗumamen da ke gabanta ma turashi gefe tayi dan ba iya ci zatayi ba.

Shigowar Abba ɗakin da sallama yasa ta miƙewa a firgice,  tun jiya take jimamin shirun Abba.

Shiga ta musamman yai, yasa babbar riga kamar mai zuwa ɗaurin aure.

“Ina kwana Abba” ta faɗi tana rusunawa

“Lafiya Asiya Shahidah”

“Abba kayi haƙuri, wallahi ban san ya akayi na watsa masa ruwan ba”

“Ba tarbiyyan gidan nan bane. Ba kuma tarbiyyan Gwani bane Allah ya jiƙan rai.  Girmama na gaba koda ba Shugaba bane tarbiyyan musulunci kenan, tarbiyyan da nake da yaƙinin mun miki kenan Asiya. To amma…”

“Abba ka yafe min”

Shi kansa Abba tun jiya ya kasa yarda Asiya ce tayi haka sai yanzu da ta jaddada masa. Jiya ya ji gudun Asiya zuwa banɗaki bai kai minti ɗaya ba kuma ya ji ƙaran tashin mota hakan ya sashi zuwa falon nasa da sauri.

Jug ya fara  gani a ƙasa,  wajen da Gwamna ya zauna kuma akwai alaman ruwa a wajen. Ya duba ƙasan wajen nan ma akwai ruwa a malale.  Wajen baiyi kamada kwaɓewar ruwa bisa tsautsayi ba yafi kama da cewa watsashi akayi.

Kasa gaskata cewa Asiya ce ta aikata hakan yayi. Ya so kiran Gwamna amma rasa abinda zai faɗa masa ya sa ya fasa kiran. Ya kwana da tunanin mi zai yi, daga baya ya yanke shawaran zuwa wajen Gwamna ya bashi haƙuri. Lokacin daya tura saƙo wa Gwamna da bai ga reply ba tsoro ya shige shi. Bayan kamar minti arba’in Gwamna ya masa reply akan ya zo ƙarfe goma da minti shabiyar.

“Zan je na bawa Gwamna haƙuri dan gidana ba gidan da ake walaƙanta baƙo bane balle baƙo kuma shugaba. Kamar yadda na faɗa kiyi duk abinda kika ga dama”

Yana juyawa yai kiciɓis da Umma. Allah Sarki ta jima a wajen amma dake bata ji bata san mi suke tattaunawa ba. Ta shiga tambayar Abba miya ke faruwa amma yace mata kar ta damu idan ya dawo zai mata bayani.

Bayan fitar sa Umma ta tsare Asiya da tambayoyi. Daga ƙarshe dai sai da Asiyar ta faɗa mata abinda tayi. Umma ta kama baki tana zaro ido…

Abba na fita waje Ubayd na ƙoƙarin tsaida motarsa. Bai gaya masa abinda Asiya tayiwa Gwamna ba ya dai ce ya zo ya raka shi wajen Gwamna.

Haka suka wuce gidan Gwamnati kowa da abinda ke ransa.

Daga waje Ubayd ya nuna ID card ɗinsa amma duk da haka sai da masu gadi suka kira suka tabbatar da ana tsammanin zuwan su kafin aka barsu suka shiga ciki.

Wani security ya musu jagora har ofishin Sakataren Gwamna bayan ya sanar da Gwamna zuwansu sannan yace su shiga ciki.

Kwarjini Gwamna ya ƙara yiwa Abba. Kunyarsa ta gama cika shi lokacin da Gwamna da kansa ya miƙa masa hannu sukayi musabaha sannan ya jagorance su zuwa wajen kujeru inda yake zama ya tattauna da baƙinsa.

“Ranka shi daɗe, ba zan iya bayyana maka yadda raina ya ɓaci jiya ba. Ina roƙon ka dan Allah kayi haƙuri ka yafe mata. Asiya…”

“Ba komai Malam Nuhu, ya wuce a wajena. Infact na yaba da ƙarfin gwiwarta. Sai dai ina tausayin mijin da zata aura kar watarana yai laifi ya sha ruwan zafi” yai maganar yana dariya

Abba ya dara yayinda Ubayd ya sunkuyar da kai yana kallon fiskar wayarsa wanda hoton Asiya ne a wayar, bai ɗago ba sai da yaji Abba yace ” ka ji abinda Gwamna yace ko Ubaydullahi, sai ka zage damtse”

Gwamna ya kalli Ubayd sannan ya kalli Abba hakan yasa Abba yai saurin cewa “ɗana kenan Ubaydullahi wanda zai aureta nan da watanni kaɗan masu zuwa”

“Allah ya musu jagora”

Abba ya amsa da Amin. Ko sakan talatin ba ayi ba Sakatare ya shigo ya ce da Gwamna lokacin tafiya yayi. Gwamna ya miƙe yai wa su Abba sallama dan fita zasuyi da tawagarsa zuwa wani ƙauye da akace za a buɗe firamare school na farko a wajen…

Gwamna yana ƙauye Alhaji Sani Kachallah ya kira shi akan yana son ganinsa idan ya dawo.

A ofishin Gwamna suka tattauna sabon batun daya ɓullo wai Matar tsohon Gwamna tana son shigar da Gwamna Saifuddeen ƙara.

“Umaru Kwom ne da wannan aiki. Shegiya ko idda bata gamaba tana maganar shiga kotu” Alhaji Sani ya faɗa da ƙarfi.

“Ko sun shiga kotu Baba ba abinda zasu samu sai baƙin ciki. Saminu Bacchi died a natural dead. Ni da likitan mun tattauna kuma ya gaya min jininsa ne ya hau sosai, stress ya sa shi faɗuwa har…”

“Na san wannan Saifu. Abinda nake gujewa shine wannnan maganar zata ɓata maka lokaci. Zaka ɓata ƙarfinka wajen biyewa shirmensu sannan alokacin Kamfen zasu dinga ɓata maka suna da zancen. Mutumin da ke karkara idan aka ce masa Saifuddeen Kachallah ne ya kashe tsohon Gwamna ba zai nemi gaskiyar magana ba. Abinda zai yi shine shi da iyalensa ba zasu zaɓi Saifuddeen Kachallah ba. And kasan ƙarfin ƙuri’un ‘yan ƙauye kuwa ?”

“Baba inaga gara su shiga kotun a gama maganar kawai sab…” sai yai shiru tunowa da yai yadda Abba ke ƙoƙarin risinawa lokacin da yake bashi haƙuri. Idan aka shigar da maganar nan kotu Asiya za ta shigo ciki kuma za ta iya zuwa kurkuku ko ta biya tara mai yawa idan bata iya kare iƙirarinta da shaidu ba.

“Kar ka damu zan yi maganin matsalar. komai zai warware”

***

Musababbin zuwanta China ba dan saro kaya bane sai dan ta ga Malamin taurari wato Tsu Zhang. Shekaru ishirin da suka wuce a garin New Haven, Connecticut ta ƙasar America lokacin tana karatu a Jami’ar Yale wata Ƙawarta mai suna Paula ta gayyaceta wani taro da za ayi na mabiya addinin Buddha, inda aka gayyaci Malamin addini wato Monk Tsu Zhang ya zo ya yi mu su Lakca. Bayan an gama lakcan Paula da saurayinta Simon wanda basu jima da shiga addinin Buddhancin ba suka nemi ganawa da Malami Tsu Zhang, ya ba su lokaci da adreshin wajen da zasu sameshi.

Bilkisu ba ta bisu ba lokacin da suka je ganinsa amma ga mamakinta da suka dawo Paula tace mata Tsu Zhang ya faɗi saƙo a bata.

“Yace kinada ƙaddarar matar babban mutum yace tauraronki zai haska tareda ta mijinki”

“Haka yace? Taya ya sani?” 

Tambayoyinta kenan lokacin da Paula ta sanar da ita saƙon Tsu Zhang. Bata tuna da wannan batu ba sai ranar da aka rantsar da Mijinta a matsayin Gwamna. Godiya take son yiwa Tsu Zhang shiyasa ta nemi ƙawarta Paula wacce take aure a ƙasar Brazil. Paula ita ta bata addreshing Tsu Zhang a China.

Bata sha wahalar samun inda Tsu Zhang yake ba sai dai kuma sai da ta booking lokaci saboda yanzu Tsu Zhang ya tsufa baya karɓan baƙi sosai. 

A wani tafkeken temple (wurin bautan gumaka) Bilkisu ta samu Tsu Zhang. Lokacin da aka kaita wajensa ta jima zaune tana jiransa saboda meditation da yake yi. Lokacin daya buɗe ido bai juyo gareta ba, daga inda yake zaune yana fuskantar ƙaton gunkin Buddha dake ɗakin yace ” akwai wani tauraro daya fito a gefen tauraron mijinki. Yadda tauraronki ke haskawa tareda ta mijinki haka wannan tauraro zai dinga haskawa tareda shi har sai tauraron mijinki ya haskaka fiye da tunaninki. Idan kikayi ƙoƙarin disashe wannan tauraro babu makawa da taki tauraron data mijinki haskensu zai dinga disashewa. Ki sani taurari uku a waje ɗaya suna bada haske na ban mamaki “

“Ban gane ba…”

Hannu ya ɗaga mata hakan ya sa tayi shiru. An riga an gaya mata cewa Tsu Zhang idan yai magana baya ƙarawa sannan baya maimitawa.

Har ta bar temple ɗin hankalinta bai kwanta ba. Wani irin tauraro ne ya shiga tsakaninta da ta Saifuddeen?…

***

Abba daya dawo bai gayawa Asiya komai ba, ya dai yiwa Umma bayanin komai, tareda faɗa mata yadda Gwamna ya tarbesu da mutunci suka rabu ana raha. Ubayd kam ko gidan bai shigo ba dan har yanzu fishi yake da ita.

Umma ta bata shawaran ta je ta bawa Gwamna haƙuri amma har yanzu bata yanke shawaran zuwa ba. Gani take idan ta je kamar ta ƙasƙanta kanta a wajen Gwamna ne.

Haka dai ta dinga saƙa da warwara har dare. Ƙarfe takwas da minti Arba’in Ubayd ya kirata yace ta sameshi a waje. Da murna ta fita dan a ganinta ya sauƙo kenan.

“Kin ji cewa Sha’awanatu Bacchi zata shigar da ƙara akan kashe mijinta da aka yi?” Ya faɗa yana tsareta da ido.

“Na gani a newsline”

“Kin shirya shiga kotu dan kare kanki kenan?”

“Ya Ubayd…”

“Tambaya na miki”

” ban so haka ta faru ba”

“Abinda kike so kenan Asiya. Ina so  ki sani cewa shari’arku ta tsaya a wajen gidan nan. Nothing should happen to my family Asiya, kada abinda ya samu Abba ko wani acikin gidan nan. Rigimarku ta siyasa ta tsaya chan nesa da mu”…

Washegari ƙarfe shaɗaya ta shirya ta wuce gidan Gwamnati. Indai baiwa Gwamna haƙuri shi zai sa Umma da Abba da Ubayd suyi farin ciki da ita to za tayi. Wunin jiya ko kallon kirki Abba bai mata ba. A duniyar nan babu Uban da take da shi daya wuce Abba. Ale Faruƙ haihuwarta kawai yai amma Abba shine Ubanta.

Tunda ta fito daga keke Napep zuwa shiganta Gate sai ɗaukan hotonta ake ta yi. Ta turawa Sakatare text jiya da dare bayan ta bar wajen Ubayd akan tana son ganin Gwamna  kuma shi yace ta zo ƙarfe shaɗaya na safe.

Tana isa wajensa yace ta shige ofishin, Gwamna yana jiranta. Gwamna ne zaune tareda Alhaji Sani Kachallah lokacin data shiga ofishin.

” ‘yar jarida mai ƙwazo” Alhaji Sani ya faɗa yana murmushi.

Asiya tayi saƙeƙe tana kallonsa.

“Bismillah, zo ki zauna ai wannan zama naki ne”

Ɗan ɗosanuwa tayi a bakin kujera ta dinga kallonsu ɗaya bayan ɗaya yayinda ta sha jinin jikinta saboda kwarjini da suka mata.

Alhaji Sani ya ɗauki kofin shayin da ke gabansa ya kurɓi kaɗan kafin ya kalli Asiya yace ” akwai saƙon da za ki gani gobe. Tukwici ne daga gareni. Ina fata idan kin ga saƙon zai faranta miki rai sosai”

Haƙuri ta zo bawa Gwamna amma kuma ta kasa furta komai. Bata gane inda maganar Alhaji Sani ya dosa ba.

Da ƙyar ta iya haɗa kalmomi biyu tace “ban gane…”

“Idan kinje gida ki gaishe da mahaifinki”

Ba sai ya ƙara magana ba ta sani managarsa na nufin ta tashi ta tafi.

Gwamna baishe da ita uffan ba sai ma kauda kansa da yai gefe…

Daga gidan Gwamnati shagonsu ta wuce wanda tunda sukayi hatsari rabonta da wajen. Tana wajen Umaru Kwom ya turo mata saƙo akan ya kamata su haɗu

su tattauna. Ta tura masa saƙo akan yai haƙuri ba zata iya taimaka masa ba.

Saƙon Alhaji Sani Kachallah ya isowa Asiya ƙarfe takwas na safe lokacin tana shirin fita shago tunda yanzu ta bar aiki a Hill TV. Aliyu ne ya shigo ɗakinsu da gudu sanye da uniform ɗin makaranta.

“Miya sa baka tafi makaranta ba Ali?” 

“Anty Shahidah wai kije yanzu-yanzu inji Abba” ya faɗa sannan ya ruga da gudu.

Hijab ɗin Umma dake kan gado ta saka sannan ta wuce falon Abba da sauri.

Tana zuwa ta ganshi ya ƙurawa TV idanu.

Baice komai ba dan haka itama ta maida hankalinta kan talabijin ɗin. Bayan minti uku sannan aka fara karanta labarin daya sakata riƙe kai. Hotonta aka nuna tana magana da wani security a bakin gate ɗin gidan Gwamnati sannan ga tanan tana ƙoƙarin shiga office ɗin Gwamna daga nan kuma sai aka nuna hoton wasiƙa zuwa ga Gwamna wanda sunanta da sa hannunta ke ƙasa. Mai karanta labaran yana karanta wasiƙar hawaye na zubowa a idon Asiya yayinda ilahirin jikinta ya ɗau rawa.

Cin mutuncin da za a mata kenan a ɓata mata suna.

Abba ya rage volume ɗin TVn sannan ya juyo ya kalli Asiya.

“Abba wallahi ban rubuta wata wasiƙa ba”

“Wanda bai ji bari ba ai zai ji hoho ko Asiya. Kin dai ji yadda ‘yan siyasa suka juya labarinki”

“Na shiga uku”

“Kiyi addu’a Allah ya sa ya tsaya a iya haka. Idan kuma taurin kai da kika saba za ki yi to Bismillah”

Kafin ƙarfe goma na safe ko ina ya ɗauka ‘yar jarida Asiya Shahidah Faruƙ Baba ta yiwa Gwamna tayin soyayyarta ne shiyasa ta yaɓa masa baƙin fenti da bai amince da ita ba. Hatta cikin rahoton data kawo tana aibanta SSK lokacin daya ke mataimakin Gwamna sai da aka nemo aka dinga yaɗawa.

Kowa a jahar sai tofa albarkacin bakinsa yake yi akan zancen. Wasu suce Asiya irin matan nan ne masu bibiyar ‘yan siyasa amma shi Gwamna SSK babu ruwansa da harkan mata. Wasu kuma suce neman suna take yi saboda ta fitar da labarin da zai yi fice da ita a duniya amma dake Allah ba azzalumin bawa bane shiyasa asirinta ya tonu. Wasu kuma cewa suke akwai lauje a cikin naɗi ƙila an yiwa Asiya barazana ne shiyasa ta rubuta wasiƙar nan. Wasu kuma suna ganin ‘yan adawa ne suka biyata dan ta ɓatawa Gwamna suna. Maganganu dai kala-kala.

Maganar shigar da ƙara da ake ta raɗe-raɗin Matar tsohon Gwamna za ta yi kuwa sai ya zo ya bi ruwa.

 Lokacin da Likitan tsohon Gwamna yai bayani a gidan talabijin tareda fitar da report na gwaje-gwajen da akayiwa Gwamna Saminu Bacchi bayan rasuwarsa hatta Umaru Kwom sai da ya ji jikinsa yayi sanyi domin babu yadda za ayi ya samu nasara kan tuggun daya shiryawa SSK duk da kuwa ya yarda koda SSK bai sa an kashe Saminu Bacchi ba to Alhaji Sani Kachallah zai iya aiwatar da hakan.

A ranan wani Malamin addini ya fito yai bayani akan yarda da ƙaddara mai kyau ko marar kyau. Yai maganar cewa yana cikin rashin yarda da ƙaddara mutum ya fara bibiyar dalilin mutuwar wani. Gwamna Saminu Bacchi lokacinsa ne yayi shiyasa Allah ya ɗauki ransa abinda al’umma za su yi shine a cigaba da yi masa addu’a da shi da duk wanda suka riga mutuwa. Ita kuma Asiya Allah ya shiryeta.

A rana ɗaya tal sunan Asiya ya chanja zuwa maƙaryaciya.  Washe gari da safe wani mawaƙi ya shiga studio ya sake waƙa yana yabon Gwamna yana aibata sunan Asiya.

Sai da Asiya ta gama shirya kayanta tsaf kafin ta wuce falon Abba, baya nan dan haka ta tura masa saƙo akan cewa zata koma gidan Baffa Malam.

Idonta yayi jaa duk sun kumbura saboda kuka. Umma ta goyi bayan shawaran data yanke data ce zata je ta zauna a gidan Baffanta har sai saura sati biyu bikinta kafin ta dawo…

***

“Your excellency inada magana”

“Bismillah Malam Baffayo”

“Yarinyar nan Asiya rayuwarta na cikin haɗari”

Gwamna ya zaro ido cike da mamaki.

” na samu labari daga majiya mai ƙarfi cewa mutanen Umaru Kwom suna son kasheta saboda a tada sabuwar fitina tunda wancan ta mutu”

“How could they, ina kaji wannan magana?”

Sakatare yace ” Excellency a bar kaza a cikin gashin ta”

Lokacin daya bar office kai tsaye Kachallah house ya wuce wajen Alhaji Sani.

Bayan ya yiwa  Alhaji Sani bayanin da Sakatarensa ya masa sai kawai ya ga ya ɓigire da dariya har da kakkautawa.

Ya sake baki yana kallon Baffan nasa.

“Wani lokaci Saifu kaman baka san mi ake nufi da siyasa ba. Ba abin mamaki bane idan sun yi niyyar kasheta saboda wata manufarsu, sai dai duk ta inda suka ɓullo ina nan ina jiransu. Har yaushe ma Umaru ya girma da zai ce zai ja dani”

Wani abu ya daki zuciyar Saifuddeen. Ana maganar kashe ran yarinyar da bata ji ba bata gani ba amma yana dariya. Ba zai taɓa bari a hallaka rai a rikicin Gwamnatinsa ba.

“Baba ba zan bari su taɓa lafiyarta ba balle ma har su kasheta matuƙar ina raye”

Alhaji Sani ya kalli SSK da alamar tambaya a bakinsa amma bai furta ba sai yace ” kenan zaka aureta?”

“Baba ban gane ba” Gwamna ya faɗa cikin rashin fahimtar manufar Alhaji Sani Kachallah.

“Hanya ɗaya da zaka iya kareta kenan Saifu” Alhaji Sani faɗa yana cigaba da dariya.

WAIWAYE…8[27/05, 6:40 pm] +234 803 916 8182: *THE GOVERNOR’S WIFE*

…… 

*WAIWAYE*

Abu ne da muka sani cewa Allah zai iya jarrabtar mu ta kowani fanni na rayuwarmu. Zai iya  jarrabtarmu ta wajen dukiya, lafiya, ‘ya’ya, mata, ‘yanuwa, iyaye da sauransu.

Asalin iyayen Lukman Fulanin Baroroji ne wanda basa zama waje guda su jima.

Lukman yaro ne da aka haifeshi da ƙusumbi (hunchback). Yana shekara uku mahaifiyar sa ta rasu wajen haihuwa. Matar uban sa da ake kira da Gaji ta ce ba za ta iya riƙe shi ba, shiyasa Uban sa ya damƙa shi wajen Yayar mahaifiyarsa mai suna Habbi. Yana cika shekara biyar a wajenta ta ɗauke shi ta kaishi wajen Malam AbdulWahab Falke Almajiranci wanda ya kasance Kawu a wajen mijin ta.

Tunda aka damƙa Lukman wajen Malam kuwa Mahaifin sa bai taɓa waiwayan sa ba har Allah ya ɗau ran sa,  shekaru biyar bayan rasuwan Asiya mahaifiyar Lukman ɗin. Itama Inna Habbin sau ɗaya ta je ta duba Lukman daga nan ba ta sake zuwa ba har rai yai halin sa.

Malam Falke ya zamewa Lukman Uwa da Uba sannan Malami. Duk cikin Almajiran Malam, Lukman ya fi ƙoƙari da hazaƙa. Ya maida hankali sosai wajen karatu. Ɗan sarari da su ke samu da sauran ke watayawa cikin gari shi yana amfani da wannan lokaci ne yai ta ƙoƙarin rubutu a Allon sa.  

Malam Falke Allah bai bashi ‘ya’ya dayawa ba. Yaran sa biyar ne kacal sai kuma ‘ya’yan da ya ke riƙewa. Huɗu daga ciki mata ɗaya kuma namiji. Kafin a kawo masa Lukman ɗansa namiji ya jima da rasuwa, dan shekaransa shida ya rasu bayan wata ƙaramar jinya.

Dayawa mutane sukan ɗauki Lukman a matsayin ɗan Malam ne saboda irin kulawar da Malam ke bashi.

A hankali da ya dinga lura da baiwar karatu da Allah ya bawa Lukman sai ya zamana ya fara ba shi karatu na musamman. Duk wani ilimi da ya ke da shi to yana ƙoƙarin ya ga cewa Lukman ya samu, yana ma sa tanadin zama magajin sa. Koyaushe baya rabuwa da yiwa Lukman Du’a’ul Fahmi.

Lukman yana shekara tara yai saukan ƙur’ani (tartil) yana shekaru shahuɗu yai haddar ƙur’ani kuma cikin watanni bakwai ya rubuta ƙur’ani da ka. 

A hankali ya dinga haddace manya-manyan litattafai na addini. Yana shekara shabakwai Malam ya tura shi Borno wajen wani Babban Malami. Bai dawo ba sai da yai shekaru huɗu a chan. A sanda ya dawo ne kuwa ya tarar da Malam ya aura masa wata ‘yarsa.

Rumaysa’u wacce aka fi kira da Tabawa ita ce auta cikin ‘ya’yan Malam. Ita ce kuma Allah ya jarrabce shi da ita.

Saɓanin sauran yayyanta da su ka yi karatu sosai har su ka yi sauka tun ma kafin ya aurar da su ita fir ta ƙi karatun.

  Bayan nan, ƙiriniya da yawace-yawace da ta tsirfata da tara samari ya sa ya ce zai haɗata  aure da wani Almajirin sa. Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa ta ce ba za ta auri Almajiri ba.  Yayi yayi da ita ta ce ba za ta aure shi ba. Ƙarshe ma ta kai ƙarar sa wajen Maigari. 

Malam ya haƙura ya aura ma ta wanda ta kawo ta ce tana so. Da ke babu albarkan iyaye auren dudu wata biyar su ka yi ya rabu ta dawo gida ta fara zawarci. Kafin kace me sunan Tabawan Malam ya sake zama tamkar waƙa a wajen samari da bazawarai.

Lokacin da Malam ya ce ta fito da miji sai ta nuna Chukudi a matsayin wanda ta ke so. Kasuwanci ya kawo Chukudi garin, ɗan kuɗin da ya ke kashewa Tabawa shine ya tsole ma ta ido har ta zaɓeshi a matsayin wanda za ta aura, duk da addinin su ba ɗaya ba, al’adar su ba ɗaya ba, uwa uba ba asan minene asalin sa ba.

 Wannan karan da Malam ya hanata auren sai wayan gari aka yi aka ga ta gudu daga gidan. Ita da Chukudi aka neme su a gari aka rasa. Wannan cin mutuncin har kwantar da Malam yai, kamar ma ba zai  tashi ba sai kuma bayan ya sha jinyar watanni sai gashi ya samu sauƙi amma baƙin cikin da Tabawa ta ƙunsa ma sa yana nan yana cinsa, kullum addu’ar sa gareta Allah ya shiryar da ita. Ya sha tsayuwar dare akan lamarinta sai dai ita ɗin wata jarrabawa ce da Allah ya ma sa.

 Shekara ɗaya da rabi kafin Tabawa ta dawo gida. Ranan da ta dawo mutanen gidan da ƙyar su ka ganeta saboda lalacewa da ta yi. Bayan ta bi Chukudi zuwa ƙauyen su ashe niyyansa shine ya tsafeta yai kuɗi da ita. Da ƙyar Allah ya kuɓutar da ita daga kaidinsa, sai dai tunda ta bar ƙauyen ta rasa gane kanta. Ta jima tana garari kafin ta samu ta warke ta dawo wajen Babanta dan ta san nan ne kawai gatan ta.

Malam ya karɓeta ne da sharaɗi guda, za ta zauna tsakani da Allah da duk wanda ya aura ma ta. Kaman da gaske ta ce ta amince.

A take ya ɗaura ma ta aure da Lukman ya kuma tura wasiƙa akan Lukman ya dawo gida idan Malaminsa ya sallameshi. Bai samu dawowa ba sai bayan wata uku.

Kafin ya dawo Malam ya gyara ma sa ɗakuna biyu cikin gidansa inda anan za su zauna da Tabawa.

Lokacin da Malam ya sanar da Lukman maganar auren da yai masa ya sha mamaki sosai. Ya san halin Tabawa sarai kuma duk abinda ke faruwa babu wanda ba shi da masaniya akai. Ba wai ba zai karɓi zaɓin Malam ba ne amma yana tunanin anya kuwa Tabawa za ta zauna da shi?

Tsoronsa kuwa ya tabbata  domin lokacin da Malam ya haɗa su zai mu su nasiha Tabawa ta ƙeƙasa ƙasa akan ba za ta auri Mai ƙusumbi ba. Ita duk zaman nan ta ɗauka ɗaya daga cikin manyan Almajiran Malam aka aura mata, bata san Lukman Maiƙusumbi ba ne.

“Baba ba zan zauna da Maiƙusumbi, Miskini, marar asali ba. Duk cikin Almajiranka ba wanda ba sa zuwa wajen ‘yan uwan su lokaci zuwa lokaci amma wannan bai taɓa zuwa wajen na shi ba. Ƙila ma ɗan shege ne”

“Rumaysa’u!”

“Baba zan auri kowa amma banda shi Wallahi”

“Na fi ƙarfin Miskini” ta ƙara jadda masa kafin ta fice daga ɗakin Malam ɗin.

Duk ƙoƙarin da Lukman ya ke akan kada yai hawaye agaban Malam sai da hawaye su ka zubo ma sa. 

Dai-dai yana gogewa da gefen hannun rigansa Malam ya ce “Lukman ka tashi ka je za a kawo maka ita yanzu”

“Malam ka yi haƙuri Dan Allah, tunda ba ta so a bari na sawwwaƙa ma ta”

Ran Malam cike da ƙuna ya ce ” ka san Allah idan har Rumaysa’u ba ta karɓi auren ka ba sai na tsine mata”

Lukman ya zaro ido waje.

“Kai ne aka cuta da na haɗaka aure da mace kamar Rumaysa’u, na yi haka ne dan ko Allah zai shiryar min da ita ta hanyar ka”

A chan cikin gida kuwa Tabawa ta dinga faɗa wai a rasa wanda za a aura ma ta sai Maiƙusumbi. Wata Gwoggon ta da ke gidan ta fito ta dinga surfa mata masifa. 

Yadda ta dinga kiranta da butulu shiyasa jikinta yai sanyi. 

Duk da tarin laifuffukanta itakam ta ƙwammace ta zauna ba aure da ta auri Lukman Maiƙusumbi. Kusan shekaru biyu kawai Lukman ya ba ta. Tun suna yara ta tsaneshi. Yadda Malam ya ja shi a jiki ya maida shi ɗansa na dole ba ƙaramin ɓata ma ta rai ya ke yi ba.

Bayan Gwoggo ta ƙare mata faɗan ita da  Kulu yayar Tabawan suka tarkaɗata zuwa sashen da aka gyarawa Lukman. Tabawa ta sa a ranta zata zauna ne zuwa abubuwa su lafa, nan da lokaci kaɗan za ta rabu da shi ko da ta ƙarfi ne.

Har ta fara bacci Lukman ya  shigo ɗakin jikin sa a sanyaye. Umurnin Malam na ƙarshe kafin ya taho ne ya dagula ma sa lissafi.

“Wallahi idan har ba ka tare da matarka daren yau ba. Ban yafe karatun da na koya maka ba”

A gigice ya bar wajen saboda bai ga alaman wasa a wajen Malam ɗin ba.

Da lallami ya nemi Tabawa amma ta ƙi bashi haɗin kai wannan ya sa shi binta da ƙarfi ya karɓi haƙƙin sa. Ya sha tsinuwa a wajen Tabawa kam kafin ya gama saboda da farko ta rena ma sa kan  cewa za ta iya ƙwatan kanta a wajen sa. Ƙaramin ruwa gareshi shiyasa ta ke ma sa kallon ƙashi da rai ba ta san yadda ya ke a bushe haka ya ke da ƙarfi ba.

Tun daga ranan kuwa ba abinda ya sake  shiga tsakanin su. Iya kyautatawa yana yi ma ta amma itakam kullum cikin zagi da tsinuwar sa ta ke, tareda cewa ya saketa indai shi ɗan halak ne.

Awata na biyu da auren ta gane ciki gareta. Ta yi kukan baƙin ciki sosai dan haɗa iri da Lukman mugun abu ne a wajenta.

Wasu ƙulle-ƙullen magani ta nema ta sha wai dan cikin ya fita. Ba ta jima da shan maganin ba ta cika gidan da ihu. Iyaji Mahaifiyarta ta zo ta sameta cikin jini. 

Kwanan ta uku a Asibiti kafin aka sallameta. Sai da su ka dawo gidan ne ma Iyaji ta tabbatar ma ta da cewa cikin jikinta na nan.

Ta sake shiga damuwa dan da ƙarfi ba ta son abin cikin ta. 

Ƙarshe Sheɗan ya kaɗa mata kai ta aiwatar da abinda ya zo ya rabata da Mahaifinta har abada.

Guba ta zubawa Lukman a abinci akan idan ya ci ya mutu sai ta yi takabar sa ta huta da auren baƙin ciki.

Lukman ya zo ya fara cin abincin kenan ko loma biyar bai yi ba wani jikan gidan ya leƙo akan ya je Malam na kiran sa. Ya  wanke hannu ya fita.

Yana wajen Malam suna magana cikin sa ya fara murɗawa tun yana daurewa har ya riƙe cikin yana murƙususu a ƙasa. Malam ya ɗauke shi aka yi Asibiti da shi bayan ya bashi zumar daya tofa ayoyin shifa a ciki. A chan ne aka ce mu su maganin ɓera ya ci.

Ko tantama Malam bai yi ba ya sawa ransa Tabawa ce da wannan aikin. Sawa yai a kira ma sa ita. Lokacin da ta zo yana tare da Lukman da ke zaune gefen sa yayi wani fayau da shi saboda a yau ɗin ne aka sallameshi daga Asibiti. 

Ko gaisuwarta Malam bai amsa ba ya umurci Lukman ya saketa. Takardar da Malam ya miƙo ma sa ya karɓa hannunsa na rawa.

“Ka rubuta ma ta saki na ce” ya sake maimaita ma sa da ɗan karfi.

Alƙalamin da ke gefen Malam ya ɗauka ya rubuta wa Rumaysa’u saki ɗaya da rubutun Ajami.

Yana rubutun Tabawa na murmushi.

Malam ya dubeta ya ce “Bayan Lukman bana tunanin za ki samu wani namijin ƙware da zai sake neman auren ki Rumaysa’u”.

Magana ce ya mata amma kasancewarsa Uba gareta sai abin ya zame mata baki.

Abin mamaki ko Wata ba’ayi ba da rabuwar su Malam ya aurawa Lukman ‘yar uwarta wadda su ke ‘ya’yan Baffanu (cousins).

Indo budurwace mai ƙarancin shekaru amma ta yi biyayya ga zaɓin Malam ta zauna da Lukman tsakani da Allah.

Cikin Tabawa na wata takwas Malam ya rasu mutuwar da ya girgiza su sosai.

Sati uku da rasuwan ta haifi ɗa namiji. Sunan Baba ta so sakawa amma saboda jinin Lukman ne sai ta ƙyamaci hakan. Da kanta ta samu Lukman akan sunan ɗanta Faruƙu. Ranan suna kuwa bai chanja ɗin ba aka sawa yaro Faruƙ.

Tunaninta ta rabu da auren Lukman za ta buɗe da wani auren mai kyau sai kuma duniya ta juya mata baya.

Halayyar ta na baya su suka bayyana wa kowa da ke son zuwa aurenta.

Tabawa ce dai da ta gudu da wani Arne na kusan shekaru uku. Tabawa ce dai da ta kai ƙaran mahaifinta wajen Maigari, Tabawa ce dai… Tabawa ce dai…

Tun tana zaune ba ta komai, da abubuwa su ka fara kwaɓe ma ta ɗan sauran kuɗin da ta samu na gadon Malam ta fara sana’ar tuyar ƙosai. Wasa-wasa sai da Faruƙ ya shekara shida kafin ta samu miji ta yi aure. Aure ta yi amma ɗan ƙaran wahala  take sha a cikinsa ko da wasa Ƙaura Mafarauci bai ɗauketa da daraja ba. Tana zaune da matan sa biyu amma duk ciki ta fi su wahala. Bayan duka da ya ke mata da har ya zame mata jiki ‘yan kuɗaɗen sana’arta duk shi ya ke karɓa ya sha giya da su. Ƙarshe jari ya ƙare. Ta yi zagin ta yi faɗan duk dan ya saketa amma ya ƙi.

Ga shi shekaru bakwai tare amma ko ɓari ba ta taɓa yi ba, shiyasa ma ta kasa miƙawa Gwani Lukman ɗansa Faruƙ lokacin da ya buƙaci hakan. Duk yadda ba ta son Ubansa haka ta ɗaurawa Faruƙ tsananin so. A shekara ta tara da auren Ƙaura ya rasu. Ta yi farin ciki da mutuwar sa sosai. Tana ƙarisa takaba ta dawo gida lokacin ba wanda zai ganta ya ce zai waiwayeta saboda yadda ta tsofe ta lalace.

Bata yi niyyar sake Aure ba amma ganin Indo da Gwani Lukman suna zaune lafiya ya sa ta kasa zaman gidan nasu. Lukman shi ya gaji Malam, tun bayan rasuwan sa Makarantar Malam ba ta watse ba. Wani fili da ke gefen gidan Malam wanda tun Malam na raye ya ba shi kyauta ya samu ya fara ginawa, cikin shekaru biyu kuwa ya kammala shi da Indo su ka tare a gidan da yaransu guda biyu maza AbdulWahab da su ke kira da Malam sai Zakariyya da su ke cewa Zakari.

Cikin shekarun nan Allah ya ɗaukaka sunan Gwani Lukman Baba fiyeda ta Malam Falke. Babu wanda ke duba ƙusumbinsa sai tarin Ilimin da Allah ya bashi. Daga garuruwa daban daban ana zuwa ɗaukan karatu wajen sa. Tuni sunan sa ya koma Gwani Baba.

‘Ya’yan sa Malam da Zakari kuwa sun zama abun kwatance cikin gari. Ga tarbiyya ga karatu.

Kukan Lukman kullum akan Faruƙ ne wanda Tabawa ta janye shi daga jikinsa. Tun yana yaro idan ya sa shi ya zo wajen sa karatu yake guduwa. Da ya fara masa duka sai ya dena zuwa kwata-kwata, Tabawa ta ɗaure ma sa gindi har da samun Lukman akan ya bar ma ta ɗa ba lallai ne sai ɗanta ya zama Malami kamar sa ba.

“Ba a chanjawa tuwo suna Ruma. Duk lokacin da ki ka kalli Faruƙ na san fiskata kike gani a tasa. Ki bani ɗana Allah ya taimakeni na ɗaura shi akan tarbiyya mai kyau”

Ruma ta ce ba ta san zance ba.

Lokacin da ta koma gida haka ta titsiye Faruƙ a gaba tana kallo wani abu na sukanta a zuciya.

Kallo ɗaya za ka yiwa Faruƙ ka san jinin Gwani Lukman ne. Idan ka cire ƙusumbi da bashi da shi komai na Gwani ya ɗauko, hatta da murmushi idan yai sai ka ɗauka Gwani ke yi.

Ta sani Lukman kyakyawane sosai, Ƙusumbin da ke bayansa da kuma ƙaramin jiki da Allah ya bashi shine kawai naƙasu da Allah ya mishi.

Bayan ta gama  takaba da shekara ɗaya ta auri Saleh. Ganin Saleh babban mutum ne dan ya ɗara shekaru hamsin alokacin kuma shine sarkin noman Doka wani garin da ke maƙotaka da su ta yi tunanin samun lamuni a auren.

Da Faruƙ ta tare duk da kuwa alokacin yana kusan shekaru shashida a duniya ya ƙi karatun Arabi ya ki ta Boko. Ko Primary bai gama ba ya dena zuwa.

Ta ɗan samu zaman lafiya na ɗan wasu watanni kafin asalin halin Sarkin noma ya bayyana ma ta. A gidan Sarkin noma ne ta ƙwammaci tun asali da ba ta rabu da Lukman ba. Bayan munanan halinsa kuma ga uƙubar kishiyoyi. Lokacin da ta fara Sana’a tana ɗan samu abun rufawa kanta asiri ɗaya daga cikin kishoyinta ta je aka mata surkulle kasuwan ƙosai da ɗanwake da ta keyi ya lalace ga uwa uba ciwo da aka sa ma ta. Ko shekara Faruƙ bai yi da ita ba ya tafi Birni neman aiki, bai sake waiwayanta ba. Haka ta zauna cikin ƙunci ita kaɗai.

Dama tunda ta rabu da Lukman zumuncinta da ‘yan uwanta ya yi rauni. Lokacin da ta koma Doka da zama da abubuwa ke mata daɗi ba wanda ta waiwaya a cikin su.

A shekara na uku da rashin Faruƙ wata rana da Adda Karime ta kawo ma ta ziyara. Ashe Allah yayiwa mahaifiyar su Iyaji rasuwa kusan wata biyar da su ka wuce ba ta sani ba. An aikawa Saleh lokacin mutuwar amma bai gaya ma ta ba. 

Tabawa ta yi kuka sosai. 

Lokacin da Adda Karime za ta tafi ta roƙeta da Allah akan ta faɗawa Gwani ya nemo ma ta Faruƙ tunda Karimen ta faɗa ma ta suma rabon su da Faruƙ ɗin tun bayan tarewar ta.

Addu’a sosai Gwani ya sa gaba akan Allah ya dawo ma sa da Faruƙ gida tunda Tabawan da ya ke tunanin yana wajenta ma tace ba ta san inda ya shiga ba.

Allah maji roƙon bawa a cikin wata na huɗu sai ga Faruƙ ya shigo gari. Idan ka ganshi ba za ka ce ɗan Malam kuma jikan Malami bane. Ya tara uban gashi yana sanye da wando na yayi wanda ta matse daga sama daga ƙasa kuma ta buɗe.

Cikin ikon Allah da Gwani yai ma sa maganar aure sai ya amince.  Ɗan kuɗi da ya zo da shi da kuma abinda Malam ya haɗa mi shi da shi yai jari ya fara kasuwanci.

A hankali kuma Allah ya sa ma sa albarka a ciki, cikin lokaci kaɗan ya samu rumfar kan sa a kasuwa.

***

A wani madaidaicin gida kuwa wata budurwa ce ke aikin wanke-wanke. Kwanukan yawa garesu, kuma yawancin su robobi ne madaidaita hakan zai sa ka kira su da kwanukan saida abinci.

Daga yadda budurwar ta duƙa tana wanke-wanken wani yaro wanda ba zai wuce shekaru goma ba ya ɗira ma ta dundu a baya. Budurwar ta juyo a zabure tana zare ido.

“Kurma ki je inji Mama” ya faɗa yana nuna mata dai dai barandar da ɗakuna uku su ke jere reras.

Maimakon ta ɓata rai da abinda ya mata sai ta masa murmushi. Ta goge hannunta ajikin zaninta ta wuce ɗakin Mama Asabe.

Tana ɗaga labulen ɗakin sai da ƙirjin Mama Asabe ya buga saboda ta ɗauka mijinta Malam ne.  Ganin Kurma ce ya sa ta ɗan sauke ajiyar zuciya.

Cinikin da su ka yi da safe da kuma na rana ta ke irgawa.

“Yawwa Kurma zo ki je ki auno min shinkafar gobe wanda ya rage ba zai kai ba”

Ta ƙarisa maganar tana miƙa mata wani dunƙulen kuɗi da ta ajiye a gefe.

Bayan da Kurma ta karɓi kuɗin a hannunta ta cigaba da yi ma ta bayani da hannu ta yadda za ta gane. Tun tana shekara huɗu aka kawo mata ita kuma cikin shekaru goma ba abinda ba ta iya ba a yaren kurame.

Yadda ta jaddada ma ta cewa a rumfar Ale Faruƙ ta ke so ta siyo ma ta shinkafar hakan ya sa ta yi saurin zuwa ta ƙarisa wanke wanken da ta ke yi dan daga gidan su zuwa rumfar Ale Faruƙ aƙalla sai ta yi tafiyar minti shabiyar  zuwa ishirin.

Lokacin da za ta fita daga gidan ne ta ci karo da Malam a zaure. Ta ɗan risina ta gaida shi kafin ta wuce.

Malam Sabo Yayan Mahaifinta ne. Bayan rasuwan mahaifiyarta lokacin tana watanni bakwai da haihuwa Mahaifinta Malam Inusa bai ƙara aure ba har Allah ya ɗauki ran sa shekaru uku bayan rasuwan matar sa. A wajen Inna Talatu  Zainab kurma take tun rasuwan mahaifiyarta amma bayan rasuwan Malam Inusa, Yayansa Sabo ya karɓota ya kawota wa matar sa Asabe. Da niyyar zai ɗauki nauyin marainiyya ya karɓeta amma ba wannan ne gaban sa ba irin gadon gona da gida da ƙanin sa ya bari. Ba ayi shekaru biyar ba ya cinye komai, ya siyar da gida ya siyar da gonan duka sun bi ruwa babu ko ɗaya yanzu.

‘Ya’yan Mama Asabe Maza huɗu ne shiyasa ta ke moran Zainab Kurma son ranta tun tana ƙarancin shekaru.

Yau rumfar Ale Faruƙ a cike ta ke da mutane magidanta da zawarai. Benchi uku aka jera kuma duk sun cika da mutane. Yankan farce akewa Ale Faruƙ lokacin da ya ɗaga ido yaga Kurma na tahowa rumfarsa kanta a ƙasa saboda kunya.

Yana ganin yaron shagonsa Iro ya miƙe yai saurin miƙewa ya ƙariso wajen.

Da hannu ta ke nunawa Iro daron shinkafar da ke kan teburi tana nuna ma sa yatsunta biyar alamun mudu biyar zai auna ma ta. Ba yau ta fara zuwa ba shiyasa Iro ya fahimci bayanin ta. Zai fara aunawa kenan Ale Faruƙ ya dafa kafaɗan sa ya ce ya koma ya zauna zai auna ma ta.

Mudu biyar ta ke so, Iro ya faɗa kafin ya bar wajen dan ya san halin Uban gidansa indai ya ga mace to hankalinsa ya tashi kenan.

Sai da Ale Faruƙ ya auna mudu biyar zai  zuba na shida Kurma ta yi saurin kai hannunta dan ta dakatar da shi aka ci sa’a hannunta ya taɓa nashi. Dama tuni kyakyawan fiskanta ya riga ya zautar da shi balle kuma yanzu da ya ji sanyin hannunta akan na shi. Ta yi saurin ɗage hannun tana yi ma sa bayani akan mudu biyar ta ke son siya. 

Ya san biyar ɗin ne yana so ya ƙara ma ta mudu ɗaya ne saboda neman guri a wajenta.

” ‘yan mata ai ba a hana Ihsani. Idan na kyautata miki na san Allah…”

“Maigida kurma ce fa” Muryan Iro ya katse shi.

Ale Faruƙ ya wangale baki yana kallon Iro da mamaki. Yana kallo Iro ya karɓi kuɗin hannun Kurma ya miƙa ma ta ledar da aka zuba shinkafan bai iya cewa komai ba.

Sai da Kurma ta yi nisa ya samu daman tambayar ko ita ɗin ‘yar gidan waye?. Wani cikin abokansa ya ce ” shege mutumina, yanzu kuma kan Kurma za ka koma kenan” yana maganan yana dariya.

Kafin a tashi a kasuwa Ale Faruƙ ya samu duk wani bayanai da ya ke so gameda Kurma.

Ya san  marigayi Malam Inusa, balle uwa uba Baffanta wanda abokin karawan sa ne, yanzu haka yana bin Malam Sabo bashin kuɗi ma su yawa.

Ya so haƙura zuwa washegari kafin ya je ya samu Malam Sabon amma kuma zuciyar sa ta kasa nitsuwa, kyakykyawar fiskar Kurma ce ke ta ma sa gizau. Kusan ƙarfe tara da rabi ya nemi babban riga ya saka ya wuce gidan Malam Sabo.

Tun a daren suka gama magana. Tunda Ale Faruƙ ya ce ya yafewa Malam Sabo bashin da ya ke binsa ya fara washe baki saboda ya san ba haka kawai Ale Faruƙ zai yafe ma sa kuɗi ba sai dai idan akwai wani abu na shi da ya ke so ne. Da farko dai ya sa a ransa indai maganan Injin niƙan Asabe ne to kuwa za ayita dan ya san halin Asabe sarai. Sai kuma ya ji zancen akan ‘yar wajensa ce Zainabu Kurma, indai ita ce ba shi da matsala da wannan.

Back to top button