Hausa novels

Halysaah Page 192 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 192Khaleesat ta rufe bakinta da sauri ganin yanda Safiyyah ke kallonta, Mikewa Safiyyah tayi ta wuce dakin da ta sauka ta bar mata parlon, Khaleesat ta ci gaba da dariyarta don sosai abun ya bata dariya, she just can’t imagine Safiyyah and Musty as couple, dama ita tun da dadewa ta fara zargin Ya Musty don kiran da yake mata idan bata gida is extraordinary, after a while ta mike tana murmushi ta bi bayan Safiyyah, bude kofar dakin tayi a hankali tana leka taga bata dakin alamar ta shiga bandaki don it’s time for Magrib, murmushi Khaleesat tayi ta jawo mata kofar ta wuce dakinta, sai da ta jira aka idar da sallah tunda ba sallan take ba ita sannan ta dau hijab dinta ta saka ta fita zuwa part din Mami zata dau abinci ta kai ma Ajay, yawanci Mami ce ke masa girkinsa yanxu, wani lkcn kuma Hajja tayi masa da kanta, ita iyaka ta je ta dauka ta kai masa part din Jay, tana shiga parlon ta samu Mami tare da Hadiyah a kusa da ita tana nuna mata message a waya, suka amsa sallaman Halysaah, Mami tace “Duk yau ban ga bakuwar ki ba, ko ta tafi ne Halysaah?” Khaleesat ta girgiza kai tace “A’a tana nan Mami, yau bata jin dadi ne” Mami tace “To Allah ya bata lafiya, in kin kai abincin ki dawo ki amshi sakon ki” Halysaah tace “Toh Mami” Kitchen ta nufa ta dauko abincin da Mami tayi ma Ajay, leaving the fruit salad bowl behind don bazata iya daukar su dukka a lkci daya ba, tana fitowa Mami ta kalli Hadiyah tace “Ki dauko mata fruit salad din ki rike mata, wai kina ma zuwa duba yayan naki kuwa Hadiyah?” Khaleesat ta kalli Hadiyah tana jiran jin abinda zata ce don tun da Ajay ya koma part din Jay ta dena zuwa duba sa, Hadiyah tace “Eh jiya da safe mun dubasa tare da Hajja” Mami tace “To dauko fruit salad din ki rike mata” Hadiyah ta mike ta tafi kitchen ta dauko bowl din ta dawo parlor, Khaleesat ta nufi kofa Hadiyah na biye da ita suka fita daga parlon Mami, a hanya Hadiyah tace “Kin amshi kayan ki kuwa?” Khaleesat ta kalleta tace “Kayan me fa?” Hadiyah tace “Baki san anyi anko for tomorrow ba?” Khaleesat ta ɗan yi shiru, can ta girgiza kai tace “Wallahi ban sani ba” Hadiyah tace “Hankalin ki na wajen mijin ki ta ya za ki san abinda ke faruwa a gidan” Khaleesat tayi murmushi kawai, Hadiyah tace “Lace su kilishi suka fitar da atamfa, na tarban amarya gobe, an yi ma kowa dinki, naki yana wajen su….” Khaleesat tace “To amma ai ba a san size dina ba ni” Hadiyah tace “To kin fi ni ne?” Khaleesat tayi murmushi tace “A’a ni ban ce ba” a haka har suka isa bangaren Jay su shiga ciki, babu kowa parlon Khaleesat ta nufi Bedroom dinsa Hadiyah na biye da ita, bakin kofar ta tsaya tayi sallama, ita dai Hadiyah na tsaye gefe, Jay ya amsa sallaman after some seconds ya bude kofar dakin, Khaleesat tace “Ina yini Ya Jawwad” Yace “Lafiya lau Halysaah” Ya koma gefe yana kallon Hadiyah da taki kallonsa, Khaleesat ta shiga cikin dakin da sallama Hadiyah ta bi bayanta da sauri, Ajay na zaune kan kujera ya dora kafa kan table yana cin Apple din hannunsa yana kallon football ya sha head warmer din Jay kamar yana kasar waje, tun da Khaleesat ta shigo ya maida idonsa kanta yana kallonta yana cin Apple dinsa a hankali, ta karasa har inda yake zaune ta ajiye abincin sannan ta kallesa, kashe mata ido yayi, tayi murmushi ta zauna kan carpet, Hadiyah ta ajiye fruit din hannunta tace “Yaya ina yini” Yace “Lafiya lau” Tace “Ya jiki?” yace “Alhamdulillah” Tace “Allah ya kara lafiya” Ya gyada mata kai, ta ɗan kalli kofar dakin taga Jay ya fita ya koma parlor, Khaleesat na kallonsa tace “A sa maka abincin yanxu?” Ya girgiza kai yace “Sai can anjima” Ta dinga kallonsa, ita dai Hadiyah idonta na kan TV tana son barin dakin amma ta kasa fita sanin Jay na nan parlor, after some minutes Hadiyah ta mike tace “Allah ya kara lafiya Yaya, sai da safe” Yace “Allah ya tashe mu lafiya” Kofa ta nufa tana ɗan leka parlon, Khaleesat dai kallonta kawai take tana murmushi, har dai daga karshe ta fita daga dakin, Ajay na kallon Khaleesat yayi kasa da murya yace “Ummi…” Ta daga idanuwanta ta kallesa, gefensa ya nuna mata, ta sauke idonta ta mike ta tafi kusa da shi ta zauna, ya jawota jikinsa a hankali yace “Duk yau kin barni ni kadai saboda kawarki tana nan ko?” Tana murmushi tace “To ba ga Ya Jawwad ba yana taya ka zama” Yace “Wannan cika ni yake da surutu me sa ciwon kai” Khaleesat tayi dariya tace “Ai ko sai na gaya masa” Shi ma murmushin yayi yana kallonta kasa kasa, sai kuma ya kai bakinsa kunnenta kamar me rada yace “Kin gama period din kizo ki kwana nan?” Dariya ya bata, ta kauda kanta taki cewa komai, yana shafa lap dinta a hankali yace “Jeeddah….” Cike da shagwaba tace “Dama kwana hudu nake period din?” Yace “To na sani ko ya canza” Ta kwantar da kanta kan shoulder dinsa a hankali tace “Yana nan yanda yake, just that yanxu ina skipping months ban yi ba” Shiru yayi yana kallonta, ya kamo hannunta yace “That’s not normal My love, ba ki je asibiti ba?” Tace “Mun je da Mami, sun ce ba wani matsala” Yayi kasa da murya yace “Za a kara maki sadaki kenan” Murmushi kawai tayi, shi dai kallonta kawai yake baya ko kiftawa, tace “Kai da baka son cin abinci very late me yasa baza ka ci ba yanxu?” Yace “A’a ki dai dawo can anjima sai ki ban in ci” Tace “To shikenan, zan je in kai ma Safiyyah abinci” Yace “Alright My love, Ina jiran ki karfe goma da rabi” Zaro ido tayi ta mike tana kallonsa, yace “Baza ki zo ba?” Ta langwabar da kai tace “I don’t want us to inconvenience ya Jawwad” Jin bai ce komai ba ta kwantar da murya tace “Toh zan zo in sha Allah” Ya lumshe idonsa ya bude yace “I will be waiting…” Ta gyada masa kai sannan ta juya ta fita daga dakin, babu kowa a parlon ta nufi kofa ta fita. Khaleesat na komawa part dinta wajen karfe takwas da rabi sai ga kilishi ta shigo, shi ma ta zo wucewa ne ta leko ciki, Khaleesat ta gaisheta Kilishi ta amsa tace “Ke ya baki zo kin amshi ankon naki ba Halysaah” Khaleesat tace “Yanxu zan je dama” Kilishi tace “To zan tafi sashin Hajja, ki bari sai can karfe tara ki zo ki amsa kafin nan na dawo, size din Hadiyah aka maki don kuna asibiti da Mami ranan da aka aika Measurements, Allah sa yayi maki dai” Khaleesat tace “Zai yi Aunty, anjiman zan zo in amsa” Daga haka Kilishi ta fita daga parlon, Khaleesat ta tafi dakin da Safiyyah take taga bata taɓa abincin da ta kai mata ba, Khaleesat ta zauna gefen gado tana kallonta tace “Sophie….” Safiyyah ta ki kallonta, Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya tace “To yanxu ki gaya min menene matsalar ki da auren Ya Mustapha? Is it because of his wife?” Safiyyah ta wani kalleta ta mike zaune tace “In don ta wannan matar ce ai da tuni na auresa ko don musguna min da ta dinga yi a Maryland ta maida ni mara galihu, kawai ni dai a matsayin yayana uwa daya uba daya na daukesa, gida daya fa muka tashi tun ina yarinya, haba ni wallahi ban ma taɓa ganin inda aka yi haka ba gaskiya, shi bai ji kunyata ba yace zai aureni” Khaleesat tayi murmushi tace “Kunyan me zai ji? Kema ana auren duk zaki manta da duk maganar nan da kike yi yanxu, kuma wallahi babu wanda zai iya ma fitinar ki sai shi din, tunda yasan halin ki, meye a ciki don kun yi aure, kawai migrating za ku yi daga yaya da kanwa zuwa husband and wife….” Safiyyah tace “Kin ga kar kiyi provoking dina Khaleesat, wallahi nafi karfinsa, ni da nake masa kallon mace ma, ko ni da nake mace na fi sa zama namiji wallahi, nan nan nan yaje ya durkusa shi da Jawwad suka dinga ba Aymaan hakuri abinda Ajay bazai taɓa yi ba har duniya ta nade, to don Allah me mutum zai yi da irin wannan mijin matsoraci, duk ranan da ka kwaso fadan ka ai sai dai ayi maka duka, gaskiya bazan iya auren Mustapha ba don ni ba gantalalliya bace….” Khaleesat bata san sanda ta fashe da dariya ba tace “Is all this necessary Sophie? Ki bari dai ayi auren sai ki gane ko mace ne shi ko namiji, i mean in every aspect” Safiyyah ta dinga mata wani kallo, Khaleesat dai bata fasa dariyar da take ba ta mike tace “Nima nan nan nan kika dinga zaunar da ni kina min nasiha inyi accepting aurena, har da tula min maganin mata, wallahi nima na miliyan daya zan maki order, har da su special kunun aya sai na siya maki” Khaleesat na kai wa nan ta fice daga dakin tana dariya. Kamar yanda Kilishi tace mata karfe tara ta nufi bangarenta don amso nata ankon, mutane sun kusa sha biyar ta gani a part din Kilishi duk kawayenta ne sai Hajiyah Habibah da Hajiya A’isha, ashe taro sosai suka shirya ma gobe, ita dai ko sani bata yi ba don duk hankalinta na wajen rashin lafiyan Ajay, ankon ma banda Hadiyah ta gaya mata da bazata sani ba, lace ne me shegen tsada an dankara masa lafiyayyen dinki, har da head din da za a daura a kai, ga atamfa shi ma me tsada an dinka, Kilishi tace “Atamfar za a saka da safe, leshin kuma na tarban amarya ne da yamma” Khaleesat ta amshi kayan tayi mata godiya ta mike ta nufi kofa zata fita, Kilishi na nuna ma manyan kawayenta Halysaah tace “Kanwar Baabarta ce amaryar Mai martaba, yanda ku ka ganta haka ita ma take….” Wata kawar Kilishi tace “Kai haba, ikon Allah ki ce Fulani Hafsat za ayi hawan jini idan aka dawo daga jinya, buzuwa ce amaryar kenan” Duk suka kwashe da dariya har da shewa, Hajiya A’isha tace “Hawan jini ma ai me sauki ne, ba tana ganin tayi kane kane shekara da shekaru ta hana a auro wata a cikin gidan nan ba, to alkadarinta dai ya karye yanxu don ga amarya son kowa ƙin wanda ya rasa, aminiyar tata Hajiya Nafisah ma mun yi waya daxu tace zata zo kallo gobe, har ita bata gaya mata abinda ke faruwa a masarautar nan ba, mun ce kar wanda ya sanar mata idan ta dawo ta gani da idonta, ba dai Mukhtar yace gobe za su dawo Nigeria ba, shekara talatin kenan ta hana Sarki kara aure….” ita dai Khaleesat ta fita daga parlon zuciyarta cike da mamaki, wai Kilishi da Hajiya A’isha ke murnan an yi ma Aunty kishiya duk yanda suke da Aunty, shi ne har da gayya suka yi masu tarban Aunty Faridah. Sai da Khaleesat ta fara kai kayan ankon nata bangarenta sannan ta tafi part din Mami zata amso sakon da tace ta zo ta karba, Mami ta fito daga bedroom dinta don har ta kwanta, tace “Nayi tunanin ma sai gobe za ki zo da naji shiru baki zo ba tun daxu Halysaah” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “A’a Mami, yanxu na gama abinda nake ne” Kitchen Mami ta tafi ta dauko mata wani package babba, ta sake shiga bedroom dinta ta dauko wani package din, lokaci daya wani fitinannen kamshi ya daki hancin Khaleesat wannan yasa ta gane ledan da Mami ta dauko a daki na turarruka ne, Mami ta fara mika mata package din da ta dauko daga kitchen tace “Ga su nan Halysaah, wa enda zaki saka a fridge sai ki saka, idan kin gama period sai ki fara amfani da su, kar ki yi wasa kin ji, zaki ga wani a babban roba shi wannan ki fara sha tun yau” Khaleesat ta kasa kallon Mami, don ta ma gane kayan mata ne Mami ke bata, kanta a kasa tace “Nagode Mami, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya kara girma” Mami tace “Ameen Halysaah, yaushe zaki gama period din?” Khaleesat bata dago kanta ba tace “Jibi” Mami tace “To kina gamawa ki yi amfani da su, yanda zaki yi using dinsu duk yana nan a rubuce jiki” Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Mami ta mika mata ledan turaren tace “Wannan kuma turarruka ne, idan kin koma sashin ki sai ki dubasu duk zaki ga yanda zaki yi using dinsu” Nan ma dai Khaleesat kai kawai ta gyada ma Mami, Mami tace “Allah ya tashe mu lafiya” A hankali Khaleesat ta kara yi ma Mami godiya sannan ta mike ta fita daga part din ta koma bangarenta…. A dakinta ta bude turarrukan ta shafa kadan a hannu taji dakin gaba daya ya gauraye da kamshi, azababben kamshin turaren ne yasa ta kasa komawa bangaren Jay. Washegari shagali sosai aka yi a masarauta na tarban Amaryar sarki, gidan ya cika da baƙi da abokan arziki masu zuwa taya murna, tun safe Hajiya Nafisa aminiyar Aunty kuma Cousin dinta ta iso gidan da wata kawarta suka shige cikinsu Kilishi da Hajiya A’isha da tawagarsu, sosai su Kilishi suka yi gayya, ga abinci iri iri da abun sha, kowa ya cakare cikin ankonsa na atamfa ga masu kidan kwarya suna ta kida a farfajiyar gidan sarki, da yamma kuma duk aka canza zuwa leshi aka sha gwala-gwalai bayan sun tabbatar amarya na hanya, Khaleesat dai a bangaren Mami ta wuni ranan sai dai hankalinta gaba daya na can gun mijinta, saboda su Mukhtar da friends dinsa na part din Jay ne yasa bata sake zuwa ba tun breakfast da ta kai da safe, amma duk da haka she just can’t wait su Aunty Farida su iso gidan and she is very happy yanda taga kowa na ta jiran isowarsu ana ta shagali da ciye ciye, karfe biyar dai dai su Hajiya Zaliha da manyan frnds dinta hudu da Baaba Gaje, Aunty Murja, sai Mama Shatu, da kawar Umma Maman Salame har da sha’awa da wata kawar Aunty Farida da ta taho tun daga Lagos, sannan ga wasu Neighbors dinsu biyu masu rufin asiri a nan Tudun Yola da suka rako Aunty Farida duk suka iso Emirate cikin Convoy, ko wannensu cikin shiga ta alfarma, frnds din Hajiya Zaliha da ita kanta sun sha gwala-gwalai, Neighbors dinsu na tudun Yola su ma duk sun sha gold, har Mama Shatu da Sha’awa ma shigar alfarma suka yi sosai, Baaba Gaje ma leshi me tsada ne jikinta da mayafi wanda Nenne ta bata, Sha’awa da Maman Salame kuwa duk Umma ce ta siya masu kaya da mayafi masu tsada, duk cikinsu babu wanda zaka kalla ka raina, uwa uba Aunty Farida da idan ka kalleta sau daya sai ka sake kallonta….

Back to top button