MAFARKIN TASHI SAMA
Ma’anar Mafarki
Asslamu alaikum mafarki gaskiya ne kuma hanyace da ake sanar da Bawa wani al amuran rayuwansa mai kyau Ko marassa kyau, mafarki baiwane wadda Allah yake yiwa bawansa a barci amma akwai mafarki wadda shedanu ke sanyawa bawa don saka shi cikin wasi-wasi.
Tajallin mafarki
Shine samarda mafarki a yayin kwanciya da sananin tsoro ko kwanciya da tunanin Abu ko son abin,kamar masoya sukan kwanta da tunanin son junan Su hakan ke sa mafarkan Su Bai cika Zama gaskiyaba.
Mafarkin abin da ka kwanta Dashia Rai Bai cika Zama gaskiya .
Wanda yayi mafarkin yana tashi sama to, Matsayine da daukaka,
Idan Dan kasuwa yai mafarki yana tashi sama zai sami riba mai yawa cikin kasuwancinsa.
Idan malami yai mafarki yana tashi sama za a daga darajar sa.
Idan mai sarauta ko mukami yagani cikin baccinsa yana tashi sama mulkinsa ko masarautarsa zata daukaka,
Idan dalibi yai mafarki yana tashi sama zai sami ilimi mai amfani.
Idan mai Neman wani biyan bukata kota wani aiki addu a ko magani sai yayi mafarki yana tashi sama bukata zai biya.