Uncategorized

Tubali Book 1 Part 10 Complete Novel

 

NA
AISHA ALIYU GARKUWA

 Da sauri ya miƙe.
Idanunsa ya d’an zazzaro tare da sanya hannu ya dafe forehead d’insa,  bakomai ne ya sashi yin hakan ba kuma, face ganin Barrister Kabir da  ya shigo cikin gidan. 
“Wannan mutumin Again? to me yazoyi? Kardai akan wancan magananne mai kama da tatsuniya ya biyoni har gida? gaskiya Indai hakane bazan iyaba, gwara ma tunda wuri naje na dakatar dashi.”
Ya fad’i maganar cikin sauri, batare kuma daya tsaya wani jinkiri ba kaitsaye ya juya, ya nufi asalin cikin sashinsa, Domin dole saiya sauko kasa, kafun zai iya dakatar da Barrister Kabir din. 
Barrister Kabir kuwa Koda ya gama dai-dai-ta parking din motar, budewa yayi ya fito.
Ahankali ya juyo tare da nufo inda Baba Maud’o ke tsaye, idanu Baba Maud’o ya zubawa, fuskar mutumin da yaga yana tunkarosa, babu ko kyaftawa, Yayinda ajikinsa yakejin wani irin yanayi na girgizar kwanya.
“Assalamu Alaikum Barka da aiki.”
Barrister Kabir ya fad’a yana me mik’awa Baba Maud’o hannu, alaman suyi musabaha.
Hakan kuwa shi ya katsewa Baba Maud’o d’an guntun tunanin da yakeyi, hannu ya mik’awa Barrister Kabir din suka gaisa.
Saidai kuma duk yanda Baba Maud’on yaso dauke idanunsa daga Kallon, mutumin dake tsaye agaban nasa ya kasa. 
Barrister Kabir kuwa Dan gyara tsayuwarsa yayi, kana cikin sakin fuska yace.
“Ni bak’one kuma nasan baka shaidani ba, amma Dan Allah ko zaka iya yimin sallama da maigidan?” 
Still idanu Baba Maud’o ya zuba masa, saidai kuma jin yace Yayi masa sallama da mai gidanne, yasa shi d’an sauk’e ajiyar zuciya.
Kai Baba Maud’on ya jinjina, cikin kuma gamsuwa da yaji acikin zuciyarsa yace. 
“To Kajirani anan, ba matsala bari nayi masa magana.” 
“To Masha Allah nagode sosai.”
Barrister Kabir ya fad’i hakan, yana murmushi.
Yayinda shi kuwa Baba Maud’o kaitsaye ya nufi cikin gidan. 
Aikuwa yana fara tafiyanne hankalin Barrister Kabir gaba d’aya ya tattare ya tafi kanshi, inda ya zubawa bayansa idanu baya ko k’yaftawa.
 Musamman tafiyan mutumin, yaso tuna masa da wasu  abubuwa.
Saurin girgiza kansa yayi, tare kuma da ture duk wani tunani da yazo cikin k’wak’walwarsa, saboda yasan ma ba hakan bane, maybe yanayi ne kawai yazo d’aya.
Sannan babban abunda yake gabansa ayanzu ma yafi karfin wannan tunanin. 
Shikuwa Baba Maud’o Koda ya k’arasa jikin k’ofar babban falon gidan, tsayawa yayi tare da soma dan k’wank’wasa kofar.
Abba kuwa dake zaune acikin falon, Jin ana buga kofarne yasashi, d’an d’ago da kansa, tare kuma da bada izinin shigowa. 
Jin anbada izinin shiga ne kuma yasa Baba Maud’o d’an tura k’ofar, ahankali ya saka kansa acikin falon bakinsa d’auke da sallama. 
Ganin Baba Maud’o ne kuma yasa Abba dake zaune saurin mik’ewa, lokaci daya kuma ya saki fuskarsa tare da cewa.
“A’a Baba Maud’o yau kaine da kanka, shigo daga ciki.” 
Murmushi Baba Maud’o yayi, tare kuma da d’an girgiza kansa, kana murya asake yace.
“A’a ai bama sai na shigo ba, yanzuma daliline ya kawoni, wani mutumi ne yazo yananan awaje, ya kuma ce Kai yakeson gani.” 
Kai Abban ya d’an jinjina, tare kuma da danyin shiru na.
 Dan wasu sakanni, saboda duk a iya saninsa baiyi da wani akan cewar za’azo nemansa ba. 
Watsar da tunanin dake zuciyar tasa yayi, cikin kuma sakin fuska yace. 
“To Baba Maud’o ace masa ganinan zuwa.” 
Abban ya fad’a yana me gyara zaman babbar rigar dake jikinsa.
Kai Baba Maud’o ya jinjina, batare da yace komai ba kuma, ya juya ya fice daga cikin falon.
Dai-dai lokacinne kuma Rayyern ya gama sauk’owa cikin falon. 
Ganin da yayi kuma Abban nasa na shirin fita ne yasashi, dan Sosa k’eyansa, cikin yanayin inda-inda yace.
“Abba fita zakayi ne?”
Juyowa Abba yayi ya d’an kalleshi tare da cewa.
“Eh yanzun nan Baba Maud’o yake cemin wai wani mutumi awaje yana son ganina.” 
Kansa yad’an shafa still, kana cikin yin k’asa da murya yace.
“No Abba basai kajeba ai, ba bak’on ka bane bak’onane, kuma nasan ni yake nema.” 
Idanu Abban yad’an tsura masa, cikin rashin gamsuwa da hakan yace.
“To kuma Idan ba bakona bane yace kuma yana nema na? Bari dai naje naji ko menene.” 
Saurin d’ago da kansa yayi ya kalli Abban nasa, lokaci daya kuma ya marairaice fuskarsa tamkar karamin yaro.
“Abba dan Allah ka zauna, Zanje naji ko menene.” 
Ya fad’a yana me kokarin fita wajen.
Kallonsa Abba yayi kana cikin rashin bai yarda da hakan ba yace.
“Anya kuwa Rayyern To waye ne, lafiya dai kam ko?” 
“Eh Abba Lafiya kalau, bari naje na sameshi.”
Rayyern din ya fad’a cikin d’an sauri, tare da gudun kada Abban nasa yace Lallai shi da kansa  zaije. 
“Da kata Rayyern, koma dai wajen waye yazo, ai dai yanzu kam ni ya buk’aci gani ko, To barni naje na sameshi.” 
Abban ya fad’a cikin serious, wanda hakanne kuma yasa duk jikin Rayyern din yin lak’was, kansa yad’an langwabar gefe, cikin kuma yanayin sanyi yace.
“Shikenan To Abba Dan Allah muje tare.” 
Kai Abban ya jinjina masa alaman to.
Inda Abban yayi gaba shi kuma Rayyern ya biyoshi abaya, Yayinda acikin zuciyarsa yakejin babu dadi, saboda baisan da wacce maganan Barrister Kabir din ya kuma zuwa yau ba.
Saidai koma meye yana fatan ace sab’anin waccan magananne da sukayi last Friday acikin mota. 
Koda suka fito compound din gidan, Barrister Kabir dake tsaye ajikin motarsa, yana hangosu ya fadada murmushi da kuma fara’ar dake kwance akan fuskarsa. 
Bayan sun k’arasone kuma Abba’n ya mik’a masa hannu sukayi musabaha, kana Rayyern ma ya bashi hannu suka gaisa. 
D’an Kallon Barrister Kabir din Abba yayi, cikin yanayin sakin fuska yace.
“Sannu bawan Allah saidai kuma gaskiya ban shaida fuskar taka ba.” 
Murmushi Barrister Kabir din yayi,  tare da gyara tsayuwarsa, still kuma fara’a fad’ad’e akan fuskarsa yace.
“Eh gaskiya bazaka shaidani ba, Domin wannan zuwan nawa, shine zuwana na farko cikin gidanka, sunana *Barrister Kabir Saleh Dakata!!”*
Dammmmm dammmmm haka zuciyar Baba Maud’o tayi wani irin bugawa, a lokacin da yaji sunan mutumin dake tsaye agaban nasa.
 A hankali ya lumshe idanunsa sabida jin zuciyarsa na wani irin harbawa da karfi, tamkar zata faso kirjinsa ta fito. 
Abba kuma kai ya jinjina nawa Barrister Kabir alamun gamsuwa.
Rayyern dake tsaye agefensu kuwa, Dan lumshe idanunsa yayi, cikin kuma yanayin kosawa yace.
“To Barrister mungode k’warai da ziyara.”
Ya k’arasa maganar tasa atak’aice Domin Sam bayason daga haka mutumin ya sake fad’an wani abu kuma.
Barrister Kabir kuwa fahimtar hakanne yasa shi, sakin murmushi, batare kuma daya lura da shock din da suke ciki ba yace.
“Alhaji wajenka nazo Idan babu damuwa kozan iya samun lokacinka muyi magana.” 
Saurin girgiza Kai Rayyern yayi, lokaci daya kuma gaba daya mood d’insa ya sanja. 
Kallon Barrister Kabir din yayi, kana cikin dagiya yace. 
“Mun gama magana dakai tun a wancan ranan.
To yanzu kuma ai inaganin babu buk’atar kace lallai saika yi magana da Abbana, Dan Allah kaje kawai.” 
Dr. Rayyern din ya k’arasa maganan, cikin son kin bawa Barrister Kabir din dama. 
Shikuwa Barrister Kabir murmushi yayi, batare kuma daya ce komai ba, ya sake gyara tsayuwarsa. 
Abba kuwa wani irin boyayyar ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da d’an juyawa ya kalli Rayyern dake bayansa, wanda yayi kicin kicin da fuska. 
Tabbas zuciyar Abban ta raya masa wani abu.
Hakanne kuma yasa shi dawo da kallonsa ga Barrister Kabir d’in.
“Shikenan badamuwa Barrister Kabir Saleh Dakata mushiga daga ciki.” 
Abban ya fad’a yana me juyawa, kaitsaye, Barrister Kabir kuma ya rufa masa baya. 
Rayyern kuwa idanunsa ya rumtse, cikin haushi da takaici ya d’an ciji Labb’an bakinsa, sam kwata kwata ba haka yaso ba, yaso ace Barristern bai samu attention din Abban nasu ba. 
Juyawa yayi shima asukwane yabi bayansu. 
Yayinda Baba Maud’o dake zaune akan d’an bencinsa kuwa duk yabisu da idanu.
Acan cikin falon kuwa, suna shiga Abba ya nunawa Barrister Kabir din wajen zama.
Bayan duk sun zaunane kuma, Abban ya kalli Rayyern, da yake shigowa yanzu.
Kuma shidinma waje ya samu acikin falon ya zauna, saboda ya fiso duk wani abu da Barrister din zai fada ya jita acikin kunnensa.
Abba da Barrister Kabir din kuwa sake gaisawa sukayi,  kafun duk sukayi shiru na d’an wasu sakanni. 
Still Abban ne kuma da har yanzu zuciyarsa bata daina bugawa da karfi ba, ya kalli Barrister Kabir din, tare da cewa.
“Barrister inajinka meke tafe dakai?” 
K’akk’afar ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauk’e, lokaci daya kuma duk wani mood d’insa ya sanja, tsananin rauni da kuma karyewar zuciya ne suka bayyana akan fuskarsa, Yayinda zallan damuwa ta fito tayiwa fuskarsa kawanya.
Gyara zamansa yayi ahankali, cikin kuma sanyin murya dake bayyana tarin fargaba hadi da damuwarsa yace.
“Tabbas ni mabuk’aci ne awajenku, sannan kuma banzo dan komai ba, saidan saka rai da kuma fatan cewa watakila zaku dubeni..”
Dan Jim yayi kana cikin k’ank’an dakai yace.
“Taimakon had’i da  Alfarma nazo nema awajenku, Dan isar Allah da Manzonsa idan zaku iya.” 
Shiru gaba d’aya falon ya d’auka, Yayinda kuma har yanzu zuciyar Abba keci gaba da bugawa,  saidai kuma jin abunda Barrister Kabir din ya fad’ane yasa shi, sauk’e ajiyar zuciya, tare da kallon Barrister Kabir din cikin, kuma rashin gane inda kalamansa suka dosa yace.
“Inajinka Barrister wacce irin taimako kake nema awajenmu, Allah Dai yasa zamu iya sabida yadda ka haɗamu dashi da fiyayyan halitta in ban iya maka shiba zanji ciwo a raina.” 
Idanunsa da suka d’an ciko da hawaye lokaci daya ya lumshe, cikin sanyin da jikinsa yayi ne kuma ya d’an zamo jikinsa daga kan kujeran, batare kuma dasu Abban sun farga ba, sai ganinsa sukayi ya durk’usa guiwowinsa biyu agaban Abban.
Cikin wata irin muryar dake bayyana karyewar zuciya da kuma tsananin damuwarsa yace.
“Dan Allah Dan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam. kuyimin taimako, da kuma alfarma kamar yanda na buk’ata a farko, saboda tseratar da rai da kuma lafiyar y’ar Adam.” 
Again gaba d’aya falon shiru ya dauka, babu abunda ke tashi acikinsa kuwa face bugawan zuciyoyi, Yayinda kwakwalwar kowanne daga cikinsu ke kawo masa tunani na daban.
Bama kamar Abba da gaba d’aya kalaman Barrister Kabir din suka d’aure masa Kai, tare da juya masa tunaninsa izuwa wani waje na daban.
Yayinda shikuwa Rayyern gaba daya ya dauke kansa gefe, tare da hade fuskarsa.
Kallon Barrister Kabir din Abba yayi, cikin kuma rashin fahimta da kasa sanin makaman kalaman nasa, hadi da rudun daya samu kansa aciki yace.
“Barrister har yanzu dai ban fahimci inda kalaman naka suka dosa ba, bamusan me kake nufi ba? Rayuwar waye zamu tseratar, sannan me hakikanin zancen naka yake nufi?”  
Idanu Barrister Kabir ya d’an lumshe, sannan kuma murya araunace yace.
“Tana tsananin buk’atar taimako, Tabbas Jannart tana buk’atar Garkuwa, had’i da ingantaccen mafaka, tana buk’atar haske acikin rayuwarta, wanda yake dauke da sarkakiya maitarin yawa, gaba daya duhu da bakinciki sunyi tasiri acikin rayuwarta, hakika tana buk’atar taimako, da kuma samun ceto daga irin azabar da d’an uwanta yake gana mata, Dan Allah ku taimaka ku bata mafaka, ku taimaka ku tayani inganta rayuwar marainiyar da Allah kejin kanta akoda yaushe.”
D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare da d’ago kansa akaro na barkatai ya kalli Abba daya zuba masa ido.
Saidai kuma awannan karon irin Kallon da yakeyiwa Abban ya banbanta dana sauran lokutan.
Bakinsa ya bud’e Ahankali cikin kuma fata da addu’an cikar burinsa yace.
*”Dan Allah Ina meneman alfarma agareku, Ina nemawa y’ata auren d’anka Dr. Rayyern Mai-nasara!!” zan bashi ɗiyata bisa yarda da gamsuwa da tarbiyarshi da gskyarsa da amanarsa*
Wani irin bugawa maitsananin karfi zuciyar Abba tayi, wanda kuma harsaida rud’u da kuma mamakin daya shiga ya kasa b’uya akan fuskarsa. 
Idanunsa ya d’an zazzaro waje, da tsananin mamaki al’ajabi hadi da tu’ajjudi, yake Kallon Barrister Kabir din, saboda zai iya yin rantsuwa cewar maganan da Barrister Kabir din ya fad’a, ta daki zuciyarsa sosai, Yayinda kuma ta rarraba masa tunaninsa zuwa wani waje na daban.
Rayyern dake zaune kuwa idanunsa ya rumtse da k’arfi, adai-dai lokacin da maganan Barrister Kabir din ta daki dodon kunnensa. 
“Aure! Aure!! Aure kuma!!!” Abba ya fad’a cikin bayyana tsananin mamakinsa, saboda shidai zaice tunda yake bai tab’ajin anyi irin hakan ba, sai awasu k’asashen kamar India, koda ma kuwa anan din anayi to ya sani ba acikin zuriyar Hausa Fulani ba gidan mata suje nemawa yarsu auren gidan maza. 
Barrister Kabir kuwa Kai ya jinjina, fahimtar da yayi kuma cewar sun yiwa maganan nasa wata kalar fahimta ne yasa asanyaye yace.
“Kuyi hakuri banzo da maganar dan yin kaina, ko kuma wani abu na daban ba, saidai halin matsalar da nake ciki da kuma wanda nake shirin fuskanta yasa nazo muku da wannan buk’atar,  nasan bakusanni ba baku kuma San komai akaina ba, amma Idan har buk’ata ta bazata samu ba, Dan Allah kuyi mini alfarma na kawo Jannart gidanku, ku b’oyemin ita, ku bata kariya kuma ku zame mata Garkuwa, ta yanda baza’a tab’a sanin cewa tana nan ba, kamar yanda na fad’a muku a farko, Jannart Marainiyace, marainiya kuma wacce take tsananin buk’atar taimako, amatsayinku na y’an uwa musulmai Dan Allah kuyi min wannan taimakon, ku zama kariya ga Jannart!!”
Barrister Kabir ya kare maganar yana me had’e hannayensa duka biyu waje d’aya, alaman rok’o. 
Wani irin doguwar ajiyar zuciya Abba ya sauk’e, tare dasa hannunsa ya dafe zuciyarsa, da ayanzu ta rage yawan harbawan da takeyi tun lokacin da yaji sunan Barrister Kabir, maida bayansa yayi ya jingina da jikin kujerar da yake Kai.
Idanunsa ya lumshe, Yayinda yake amsar duk wani tunani da ke yawo acikin k’wak’walwarsa, wanda kuma har yakeji tamkar zasu hautsuna masa k’wak’walwa.
Tabbas ayanzu duk wani nazarinsa ya tsaya cak.
Yayinda Rayyern kuwa dake can gefe, idanu ya tsurawa Abban nasa zuciyarsa na bugawa, saboda sam bayason Abban nasa ya aminta da maganar Barrister Kabir din.
Domin shi agaba daya rayuwarsa babu maganan wata Mace acikin tsarinsa, ba kuma yajin zai iya auren wata, balle kuma ya karb’i wani ajiya ji rainin hankali wai ajiya!? Kamar a garin gaɓa-gaɓa.
Abba kuwa kusan mintuna 5 kenan yanzu da ya nutsa acikin duniyar tunanin da yake.
“Lallai Wannan shine k’arin dama, abubuwa nata kusantowa, nesa na matsowa kusa, Yayinda haske ke shirin bayyana ya mamaye duhun duhuwan daya danne kekkyawan Tubalin da yake gine tun da dadewa.” 
Abban ya fad’i hakan acikin zuciyarsa, adai-dai lokacinne kuma ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi.
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauk’e, tare kuma da dawo da kallonsa ga Barrister Kabir dake zaune agabansa.
Kwarai ya aminta da shawarar da zuciyarsa ke basa, ya kuma yi Na’am da hakan domin akwai wani ƙulli a tsakani.
Numfashi me zafi ya fesar, cikin kuma yarda da kai hadi da gamsuwa yace.
*”Ni Alhaji Bashir Abban Rayyern na amince da buk’atar da kazomin dashi Barrister Kabir, saboda haka na amincewa d’ana Auren Jannart!!” bisa tsarin Musulunci mu zamu nemi aurenta*
Tamkar rugugin tsawa asararin samaniya haka Rayyern yaji fitan kalaman Abban nasa, hakanne kuma yasa shi mik’ewa tsaye agigice, hankalinsa amatukar tashe yake Kallon Abban nasa baya ko k’yafta idanunsa, wanda lokaci daya sukayi jajur.
Barrister Kabir kuwa idanunsa ya lumshe, zuciyarsa cike da matsanancin farinciki, hadi da jin dadi marar misaltuwa, saboda tsabar farincikin da yaji acikin zuciyarsa ne kuma, yasa wasu irin hawaye suka gangaro kan fuskarsa. 
Hannayensa ya had’e waje guda, tare dayin shiru Dan yama kasa sanin da wacce irin kalmace zai godewa Abban.
Rayyern kuwa da gaba d’aya jikinsa ya d’auki rawa, kansa ya soma girgizawa cikin, wata irin murya dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace.
“A’a Abba Dan Allah kada…..”
Saurin dakatar dashi Abban yayi, ta hanyar d’aga masa hannu, mai dauke da alamun dakatarwa,  wanda kuma hakan shiya tilastawa Rayyern din yin shiru tare da haɗiye ragowar mgnarsa. 
Idanunsa ya rumtse da karfi, tare da taune jajayen labb’ansa, haka yakejin kansa na wani irin juyawa, arayuwarsa kwata kwata bayason jin wata magana da ta shafi mata, Babu mata atsarin rayuwarsa, saboda ya aminta cewa, zai iya rayuwa ko babu Mace a kusa da shi, Domin ko a addinance Aure bai zama dolen dole ba, matuk’ar zaka iya kare kanka daga aikata Zina da fasikanci toh shi bai kawo mace a rayuwarsa ma bare wani abu ya kwashesa. 
“Kabamu wuri!!”
Abban ya fad’a atak’aice fuskarsa babu alaman wasa ko wargi.
Idanunsa da sukayi ja sosai ya bud’e ya kalli Abban nasa, saidai kuma yanayin da ya gani akan fuskar Abban nasa, yasa shi juyawa cikin sauri ya nufi stairs din dazai sadashi da part d’insa, ransa amatukar jagule.
Barrister Kabir kuwa ganin Rayyern din ya tafi ne, ya sashi juyowa ga Abba.
Kansa ya d’an sunkuyar fuskarsa dauke da tsananin farinciki yace.
“Tabbas Alhaji Bashir kayimin halacci, kayi min abunda bakowane zaiyi minshi ba, nagode matuka na gode sosai da sosai, nagode Alhaji Allah Ubangiji ya biyaka ya sanya farinciki mai dorewa acikin ahalinka.” 
Kai Abban ya d’an girgiza Barrister Kabir din, tare da cewa.
“Bakomai Barrister Kabir ai duk yiwa kaine,  Fatana da kuma burina shine Allah yasa hakan shine sanadiyar kawo haske acikin rayuwar da gaba da bayanta ke dauke da duhu da kuma rashin sani.” 
Kai Barrister Kabir din ya jinjina, batare kuma daya zurfafa tunaninsa akan maganan da Abban ya fad’a ba ya ci gaba da yi masa godiya. 
Haka dai suka dauki kusan 30mn suna maganganu irin tasu ta manya. 
Kafun daga bisani Barrister Kabir ya mik’e da niyar tafiya.
Har bakin kofar falon kuwa Abba ya rakosa, ba tare kuma daya tsaya yaga tafiyarsa  ba, ya maida kansa cikin falon. 
Juyowarsa cikin falon kuwa yayi dai-dai da fitowar Mamy dake cikin kitchine, wanda kuma tun d’azu take tsaye tana sauraran maganganun da suke fad’a.
Kallon Mamyn Abban yayi, Yayinda ita kuwa Mamy keyi mishi Kallon mamaki.
Fuskarta d’auke da damuwa sosai tace.
“Duk naji abunda kuka tattauna Alhaji, amma kwata-kwata banajin hakan dai-dai ne, tayaya zaka amincewa mutanen da baka sansu ba? Tayaya zaka dauk’o wasu daban ka sakosu acikin rayuwar mu?  Wayesu mene hadinmu dasu, da har ka amince akan Rayyern ya auri y’arsu?” 
Ajiyar zuciya mai k’arfi Abban ya sauk’e, kana Ahankali ya shiga takowa har zuwa inda take.
Batare kuma daya amsa mata duka tarin tambayoyin nata ba, ya kama hannunta kaitsaye suka nufi  falonsa dake cikin main parlor din.
Koda suka karasa falon nasa kaitsaye bedroom d’insa suka wuce, still kuma har yanzu yana rik’e da hannunta.
Suna karasawa cikin dakin kuwa, ya maida kofar ya rufe tare da murzawa kofar key. 
Numfashi ya d’an fesar, kana Ahankali ya d’ago Kai ya kalli Mamyn, wacce har yanzu takeyi masa Kallon mamaki.
K’asa-k’asa yayi da muryarsa, yadda yasan koda akwai wani adakin To bazai tab’a iya juyo abunda yake fad’a ba, sai ita d’in kawai. 
“Kiyi k’asa-k’asa da muryarki Ruk’ayya, kinsan komai babu wani abunda baki sani ba, Dama ce ta samu, hakika naji ajikina cewar komai yana gab da had’uwa waje d’aya, da yardar Allah abubuwa suna ta had’uwa waje d’aya.” 
Idanu Mamyn ta zuba masa cike da d’an d’aurewar kai, cikin kuma muryarta da yayi sanyi sosai tace.
“Har yanzu bangane abunda kake nufi ba, meke shirin faruwa ne?” 
Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e tare da sake rik’o hannunta da kyau. 
Again kuma Cikin yin k’asa da murya yace.
“Kintuna Barrister Abdulkarim Saleh Dakata?”  
Kai Mamyn ta jinjina, cikin sauri kuma tace.
“Natuna shi mana, har abada kuma bazan manta shiba.” 
Kai Abban ya jinjina cike da gamsuwa, yace.
“To wannan bak’on da yazo wajena k’aninsa ne, shima kuma Barrister ne, sunansa Barrister Kabir Saleh Dakata.” 
Idanu Mamyn tad’an zaro cike da tsananin mamaki, tace.
“Ikon Allah, Allah mai iko, mai kumayin duk yanda yaso, Lallai Tabbas kuwa na amincewa maganarka, Nesa na matsowa kusa, kuma haske zai bayyana Insha Allah.” 
“Insha Allah kuwa.”
Abba ya maimaita cike da k’warin guiwa.
Acan b’angaren Rayyern kuwa…!
Acan b’angaren Rayyern kuwa, koda ya koma part d’insa, gaba daya kasa zaune yayi, Domin kuwa abubuwa da yawa ne keyi masa yawo acikin tunaninsa.
Direct kuma saman balcony d’insa ya koma, yana nan tsaye ne kuma yaga Barrister Kabir din ya fito.
Hakan yasa cikin sauri ya juya, tare da nufan falon k’asan nasu kaitsaye. 
Koda ya fito falon, rashin Ganin Abba acikin falon Yayi masa dadi, wanda kuma hakanne ya bashi daman nufan waje kaitsaye. 
Fitowarsa compound din gidan, kuwa yayi dai-dai da mik’awa Baba Maud’o hannu da Barrister Kabir din yayi.
Cikin aminci suka sake gaisawa, inda Baba Maud’o yace.
“Masha Allah har kafito zaka tafi, To mungode sosai a gaida gida.”
Murmushi Barrister Kabir din yayi, tare da cewa.
“Nima Nagode Baba.” 
Dai-dai ya juya zai shiga cikin motarsa ne kuma, Rayyern ya k’araso wajen. 
Kallon-kallo suka danyi da Barrister Kabir din, Yayinda Barrister Kabir din ke kallonsa cikin sakin fuska. 
Shikuwa Rayyern yaken dole yayi, kana anutse yace.
“Har zaka tafi?”
Kai Barrister Kabir din ya jinjina masa alaman.
“Eh.”
Shikuwa Rayyern kaitsaye bud’e murfin motar yayi, b’angaren mai zaman banza ya shiga ya zauna.
Ganin hakanne kuma yasa Barrister Kabir yin murmushi, tare da bud’e murfin motar shima ya shiga ya zauna. 
saboda Lallai yasan cewa akwai magana.  
Yana zama kuwa Rayyern ya fuskancesa.
Cikin muryar dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace.
“Bansan me kake nufi ba, Bansan me kake nema da rayuwata ba, Bansan wani k’ulline kuke nufina dashi, kaida y’an uwanka da kuma abokan kasuwancinka akaina ba, inayiwa fuskarka kyakkyawan gani , da kuma kyakkyawan zato, amma why zakayi min haka?  kayi min bayanin yarinyar, kuma na saka baki anbata taimakon daya kama ta a Hospital dina? To yanzu kuma me kuke nema awaje na?  Meyasa dole saini zaku zab’a mainayi muku? Ina da yakinin Akwai dubbannin mutanen, da zasu iya taimaka muku akan matsalarku, bawai dole sai lallai niba, To Meyasa kuke son takuramin? Meyasa kuke bibiyata? Meyasa zaka zo da wannan maganan mai kama da tatsuniya?  Wanda ko’a labarai ko a fina finai babu irin wannan al’amarin,  ni    nakan cire kaina acikin duk wani abu danasan babu ruwana,  Meyasa kukeson sakani acikin abunda baidace dani ba??”.
Juyowa Barrister Kabir din yayi, ya kalli Rayyern d’in.
Domin kuwa acikin kalaman da yaji sun fito daga bakinsa babu wanda bai fahimta ba ya fahimci Rayyern yanayi musu kuɗin goro shi dasu Alhaji Idi Saleh Dakata dasu Dr Lukman da Abdu Tababa. 
Ajiyar zuciya mai karfi ya sauke tare kuma da kamo hannun Rayyern d’in, cikin fuskantar juna yace.
“Rayyern! Rayyern ka yarda dani, Rayyern ka aminta dani, bazan tab’a cutar dakai ba har abada, wallahi babu cutarwa tsakanina da kai,  saidai ina tsananin neman taimakon ka, Ina neman taimakonka.
 Dan tsiratar da ran Jannart, Jannart marainiya ce,  Dr. Rayyern ba zaka gane halin da nake ciki ba,  ba ni kuma da isashshen lokacin da zanyi maka bayanin da zaka fahimceni,  fatana ayanzu shine Jannart ta kasance ak’ark’ashin inuwarka,  ba naso asan ma tana tare dakai, Domin Kuwa auren da zakayi da ita, Aurene na sirri, haka kuma aure ne da zai zamo auren manufa, Dan Allah Rayyern ka amincewa buk’atata, ko badan niba Kodan maraicin Jannart..”
*”Manufa? Auren manufa Wanne irin manufa kenan?”*
Rayyern din ya tambaya, yana me tsare Barrister Kabir da ido.
“Manufa saboda ceto Rayuwarta, da kuma manufar fidda gaskiyar da take b’oye tsawon shekaru ashirin da biyu.” 
Idanu Rayyern din ya lumshe, akaron farko cikin kuma halin ko inkula yace.
“To ni meye had’ina da wannan? Meya shafeni da hakan?”
Ajiyar zuciya Barrister Kabir ya sauk’e.
Kana cikin sanyi yace.
“Baka da had’i dashi, amma kuma abad’inance kana da had’i dashi, Domin idan kataimaketa Allah Zaibaka lada, kuma kayi taimakon musulunci.”
Barrister Kabir din ya fada idanunsa na ciko da k’walla.
Lips d’insa ya cije, tare da sake rumtse idanunsa, cikin yanayin dake nuna Kosawa da da maganan yace.
“Har dai yanzu bangane inda komai suka dosa ba.”
Still ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya sake saukewa, kana ahankali yace.
“Nidai fatana shine ka amince, Idan ka amince ninasan yanda zan gudanar da komai.”
Kai Rayyern din ya girgiza Cikin kuma rashin gamsuwa, da abunda Barrister Kabir din ke fad’a yace.
“Wannan tatsuniya ne, ko kuma nace mafarkin da bazai kammala ba har gaban abadan, well yanzu me kaje ka fad’awa mahaifina mai kuka tattauna dashi?.”
Murmushi Barrister Kabir din yayi.
Kana yace.
“Idan ka tambayeshi duk zai gaya maka na tabbatar da hakan.” 
Kafad’ansa yad’an d’age, batare kuma daya sake yiwa Barrister Kabir din wata, tambaya ba ya bud’e murfin motar ya fice.
Hakanne kuma yasa Barrister Kabir sakin murmushi,  tare da dan juyawa yana kallonsa. 
Harsaida Rayyern din ya b’a cewa ganinsa, kafun ya yiwa motar key kaitsaye ya fice daga cikin gidan.
Rayyern kuwa kaitsaye part d’insa ya koma, gudun kada wasu banzayen tunanin abunda basu da muhimmanci arayuwarsa su dameshi ne kuma yasa shi, daukan laptop d’insa ya soma shigar da wasu bayanai. 
Acan b’angaren Barrister Kabir kuwa, zuciyarsa cike da tsananin farinciki ya Baro gidan su Rayyern din. 
Koda ya isa inda zaije kuwa ansoma kiraye kirayen sallan la’asar, bayan yayi sallan ne kuma ya ci gaba da sabgoginsa. 
Yayinda acan b’angaren Jannart kuwa, yau din kusan wuni tayi tana bacci, kasancewar acikin magungunan da aka bata a asibitin Mai-nasara’n, akwai way’anda suke sa bacci sosai,  babu laifi kuma tana samun kulawa mai kyau, daga wajen Momy da kuma k’aninta Abdull. 
10:00 pm 
Aunty Dijat ne wacce Tasha wanka cikin night gown, ta turo kofar dakin mijinnata, Ahankali Yayinda bakinta ke dauke da sallama. 
Saidai kuma ganin abunda mijin nata keyi ne, yasa taja ta tsaya tare da kura masa ido.
Domin kuwa shigowarta cikin dakin, yayi dai-dai da dirowar Barrister Kabir din k’asa, wanda kuma fitowarsa daga cikin silin kenan. 
Idanu Aunty Dijat din ta d’an zaro, cikin kuma yanayin mamaki tace.
“Barrister, yana ganka haka cikin silin fa ka shiga?” 
Kansa ya jinjina mata alaman Eh. 
Batare kuma daya motsa bakinsa ba, ya koma ya zauna, tare da baje tarin takardun dake hannunsa ak’asa, wanda duk sukayi kura ya soma kad’ewa. 
Ganin hakanne kuma yasa Aunty Dijat din cewa.
“Barrister lafiya kuwa, way’annan tarin tsofin takardun duk na meye?”
Juyowa yayi ya kalleta, cikin kuma son samun nutsuwa yace.
“Dijat dan Allah kid’an hakurtamin, Domin ayanzu bani da amsar da zan baki, bincikene akan abunda ya shafi aikina, please kije anjima zanne meki, yanzu Idan kika tsaya zaki iya disturbing dina.”
Ya fad’i hakan yana me Dan tausasa muryarsa.
Aunty Dijat kuwa sanin irin yanayin aikin nasa ne yasa batare da ta musa masa ba, ta juya ta fice daga cikin dakin, saboda tasan watarana Idan tension din aiki Yayi masa yawa, To kwata kwata bayason damuwa. 
Shikuwa Barrister Kabir Ganin Dijat din tatafi ne, yasa shi soma bubbud’e takardun dake zube agabansa. 
Yayinda kowacce takarda Idan ya bud’e, sunan Barrister Abdulkarim Saleh Dakata ne ke bayyana, da kuma sa hannunsa.
Yayinda acan gefe guda kuwa, kan wani file me kaman document aka yi rubutu da manyan bak’i.
*”Bashir Muhammad Mai-Gaskiya”*  shine abunda ke rubuce ajikin file din.
Ajiyar zuciya Barrister Kabir din ya shiga saukewa akai akai, Yayinda kuma yake ci gaba da kimtsa takardun awaje daya. 
Saida hakan kuwa ya d’aukesa kaman tsawon 30mn kafun ya kammala.
Kana anutse yasake maida takardun inda ya d’auko su, ma’ana cikin mab’oyansu na musamman.
Acikin zuciyarsa kuwa wani irin k’warain guiwa yakeji, tare da sake yiwa Allah Godiya, saboda ayanzu yasan kowanni shaida yana hannunsa.
Bayan kuma ya kimtsa wajenne, ya shige toilet kaitsaye alwala ya dauro, bayan ya fito ne kuma ya shumfud’a sallaya, tare da tada sallah ya d’anyi nafilfilu,  hade da sake godemawa Allah.
Koda ya idar da sallan hannayensa ya d’aga sama.
Kana cikin aminci yace.
“Alhamdulillah Allah Nagode ma, daka bani Aron raida lafiya, har kuma ka kawoni tsawon wannan lokacin, da ake gab da samun nasara akan Jannart, da kuma ida bunne duk wata hujja, kuma ya Allah kataimakeni kabani sa’a, in tono duk wata hujja na bayyanata, gaskiya tayi halin ta..”
Shafa addu’ar tasa yayi, bayan wasu yan mintuna ne kuma ya tashi kaitsaye ya nufi dakin Dijat d’insa. 
              *Washegari* 
Tuesday.
Jannart 8 am dai-dai ta bud’e Idanunta Ahankali, tare kuma da tashi ta mike zaune.
Tabbas taji karfin jikinta sosai yau din, tasan kuma hakan bai rasa nasaba da magungunan da Tasha. 
Cikin kuzarin data dan samune kuma ta mik’e tare da fad’awa bathroom tayi wanka.
Koda ta fito, mai kawai ta shafa, batare da ko powder ta kuma mutstsukawa fuskarta ba, ta bud’e drawer dinta,  hade da zaro wata Brown din jallabiya na mata,  mai kyau da Tsushi ta zura ajikinta. 
Sosai kuwa rigar tayi mata d’as ajikinta.
Normal perfume din da ta saba shafawa, ta shafa ajikinta, batare kuma da ta tsaya wani jikiri ba, ta d’auki wayarta kaitsaye ta fice daga cikin dakin.
Direct falon k’asa ta nufa.
Koda ta karasa cikin falon, Momy da Abdull kawai ta samu akan dining table suna breakfast.
Ganinta ne kuma yasa dukansu sakin murmushi.
Inda Cikin tsananin kulawa Momy tace.
“Masha Allah Jannart tayi sauk’i, Alhamdulillah hinyau Lallai kinji karfin jikinki.” 
Murmushi Jannart din tayi, adai-dai lokacin da ta karaso dining table dinne kuma tace.
“Good morning Momy, Alhamdulillah naji sauki sosai.” 
“Alhamdulillah ai haka akeso, dazu na shiga ai naga kina bacci shiyasa kawai ban tasheki ba, amma tunda kintashi yanzu zoki zauna kici abinci.” 
Momyn ta fad’a cikin kulawa.
Abdull kuwa Kallon yayartasa yayi, kana fuskarsa dauke da murmushi yace.
“Sannu Aunty Jannart ya jikin naki, Ina fatan ace yanzu kin gama warkewa har tsere zaki iyayi.” 
Dariya duk sukayi Yayinda Jannart din tace.
“Momy Daddy fa?.”
Ajiyar zuciya Momyn ta sauke, kafun daga bisani tace.
“Yau ai Daddynku tun sassafe ya fita, yace yana da ayyuka sosai.”
Kai kawai Jannart din ta jinjina, batare kuma da ta sake cewa komai ba, ta soma cin soyayyen chips and ketchup din da Momy ta saka mata, hadi kuma da fruit salad. 
Bayan sun dan tab’a hira ne kuma, Abdull ya mik’e ya tafi makaranta, saboda yau din yana da lecture 10 am.
Itakuwa Jannart falo ta dawo ta zauna, tana falonne kuma Aisha Lawal da kuma Salman suka zo duba ta.
Har cikin falon kuwa ta shigo dasu, sosai kuma zuwan nasu ya debe Mata kewa, Yayinda Momy kuwa tayi musu tarba ta mutumci.
Ita dai Jannart kam yau tana cikin farinciki, saboda har yau Junaid enemy dinta baidawo gidan ba.
Acikin hirar tasu dasu Aisha Lawal  dinne kuma, take tambayar Salman, ko wannan mutumin ya kirasa. 
Numfashi Salman din yadan fesar, kana Cikin son kwantar mata da hankali yace.
“Har yanzun dai baikirani ba, amma nasan zai kira Insha Allah, karki damu ai daganinsa yasan muhimmancin alkawari, kuma ko yanzu ma da zamu taho saida muka biya wajen wasan polo’n, nayi tunanin zan hadu dashi kamar wancan ranan, amma kuma saidai ko mai kama dashi bangani ba.” 
Ajiyar zuciya ta d’an sauk’e, tare da karyar da wuya cikin, sanyi tace.
“To Allah Yasa ya Kira.”
Da “Ameen.” Suka amsa dukansu.
Ganin yanda Jannart din ta damu ne kuma yasa, Aysha Lawal dafa kafad’anta, cike da son bata kwarin guiwa tace.
“Please Jannart karki damu kanki, Insha Allah komai zai tafi dai dai, kuma Koda ma ace baku samu ganinsa yanzu ba, ai ba matsala saboda MD yace ya k’ara miki one week, saboda rashin lafiyarki, kinga before nan ma kin sake warwarewa.”
Jin abunda Aishan ta fad’ane yasa, Jannart sauke Ajiyar zuciya mai karfi.
Cikin Jin dadi tace.
“Alhamdulillah, amma duk da haka nafison naganshi nan kusa, saboda muyi hira dashi asatinnan,kinga hakanne kad’ai zai karamin nutsuwa.”
Kansu suka jinjina dukansu, tare da sake bata kwarin guiwa akan cewar Lallai zata ga DR. Rayyern Bashir Muhammad Mainasara. 
Haka dai suka ci gaba da hira, saidai kuma basu wani jima sosai  ba, sukayiwa Jannart din sallama suka tafi.
Bayan tafiyar tasu ne kuma Jannart din tabi Momy kitchine Dan Tayata aiki. 
Ganin Jannart din acikin kitchine ne kuma yasa Momy cewa.
“A’a Jannart bazaki fara aiki daga yanzu ba, kwata kwata ma yaushe ne kika samu sauki, ki koma ki zauna ni zan karasa komai.” 
Jin abunda Momyn ta fad’ane yasa ta k’wab’e, fuska cikin sigar shagwab’a tace.
“Dan Allah Momy kibari nayi aikin ko kad’anne Allah naji sauki sosai.”
D’an Jim Mamyn tayi, saidai kuma ganin yanda Jannart din ta matsa yasa, ta bata bleending na pineapple.
Haka kuwa suka shiga yin aikin suna hira.
Bayan sun kammala ne kuma Jannart ta koma daki koda tayi sallahn Isha kwanciya kawai tayi.Acan b’angaren Dr. Rayyern kuwa gaba daya sabgogin gabansa yake, musamman ma yau din da duk baisamu zama ba, Domin gaba ɗaya wuninsa acikin Hospital yayi sa, saboda wasu patients da aka kawo masa, masu heart attack yayi musu operation.
Adangane da batun Barrister Kabir kuwa, tuni ya watsar da duk wasu maganganun da sukayi da Barrister din acikin kwandon shara, impact ma shiya manta da wani batun maganan aure da aka fara. 
Domin ko yanzu daya dawo gida, bayan yayi sallan isha ko dinner bai tsaya yiba, kaitsaye ya wuce bedroom d’insa.
Bayan ya sake wankane kuma ya dauro alwala, tare da kimtsa kansa cikin wasu tausassun fararen kaya. 
Chocolates d’insa masu dadi yaci har kusan Leda uku dake ledan ƙananane, kafun ya daura da ruwa. 
Ko takan laptop d’insa bai kuma biba, baccin gajiya ya daukesa. 
Ahakama Acan b’angaren Riyyam-nsra, duk wunininsa na yau acikin dakin hotel din Tahir Guest Palace yayi sa.
Yayinda yake manne da wayarsa tsawon awanni kenan yanzu daya ke bad chat da wata sabuwar babe yar k’asar Morocco daya samu.
Kwata kwata yarinyar bata da kunya, da kamun Kai.
Wanda hakanne kuma yasa gaba daya Riyyam nsra ya susuce akanta,  tare da b’ata duk wasu lokutansa na yau din akan yarinyar. 
Domin kuwa Koda Ramadan ya kirasa akan yazo suyi dinner, cewa yayi sai Gobe da safe zaizo suyi breakfast, saboda yau din bacci yakeji sosai. 
Akasin hakan kuwa saida yakai 2 am a online inda suke vedio chat da yarinyar ta Instagram.
Wanda ko kaya babu ajikinta.
Haka take zaune agaban wayarta single, Yayinda shi kuwa Riyyam keta susucewa akanta, Koda suka fara video sex chat, kusan gigicewa yayi, saboda yarinyar ta fisa tsaurin ido da iya iskanci sosai. 
Saboda zaucewar da Riyyam din yayi kuwa, harji yayi inama da ace yayi  tsuntsuwa ya gansa a Morocco, manne ajikin abokiyar tab’ewar tasa. 
Haka dai ya hana idanunsa bacci. Har sai 3am kafun bacci ya daukesa ba kuma ibada yakeyi ba. 
        *Washegari.*
Kamar kullum kuma kamar Koda yaushe. 
8 am dai-dai gaba ki dayansu zaune suke akan babban dining table din.
Abba, Mamy, Rayyern, Ramadan da kuma Riyyam nsra wanda kallo daya zakayi mishi kafahimci cewar bacci bai ishesa ba, saboda yanda idanun nasa sukayi luhu-luhu. 
Rayyern kuwa da tun zamansu awajen yake lure da yaron, tass ya fahimci cewar yaron baya bacci da wuri, saboda wani dalili dayayi imani cewa ba dalili mai kyau bane. 
Abinci sukeci cike da nutsuwa.
Yayinda Abba kuwa ya dago kansa ahankali ya kalli Riyyam-nsra.
Cikin kuma son sake sanin da wanda suke tare.
Ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.
“Riyyam”.
Da sauri ya amsa tare da kallon Abban.
Shi kuwa Abba cikin tsareshi da ido yace.
 “Mahaifinka yana raye? shima Acan ethopian yake da zama ne?.”
Abban ya kare maganar yana me kafe yaron da ido.
Riyyam kuwa daya Kai loman abinci bakinsa, Jin abunda Abban ya tambayeshi ne yasa shi d’ago kansa Ahankali.
spoon din dake hannunsa ya ajiye, lokaci d’aya kuma idanunsa suka cicciko da hawaye.
Labb’an bakinsa ya motsa ahankali, cikin sanyi yace. 
“Mahaifina ya rasu.”
Gaba daya dagowa sukayi duk suka kalleshi.
Tare dajin wani irin matsanancin tausayin sa, musamman ma Rayyern da hakanan yaji wani iri acikin jikinsa. 
Riyyam-nsra kuwa da gaba daya zuciyarsa tayi rauni, hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunsa.
Wanda hakan yasa Ramadan share masa hawayen, cike da tausayawa yace.
“Kayi hakuri kaji Riyyam, Allah yajikansa da Rahama, amma kadaina kuka, addu’a zaka nayi kaji.”
Kai Riyyam-nsra din ya jinjina, kana cikin sanyi yace.
“Insha Allah.”
Ad’an fakaice kuma ya kalli wayarsa da tun dazu take aiki, saboda kiransa da Mammy d’insa tayi, sai kuma ya d’aga ab’oye batare daya fad’awa kowa ba. 
Daga can cikin wayar kuwa Mammy duk taji abunda yake faruwa.
Wanda hakan yasa hawayen dake cikin idanunta gangarowa kan fuskarta,  haka ma Zaiton dake gefenta, hawayene kwance akan fuskar ta, saboda itama taji abunda akace, Dan Mammyn nasu a hands free ta saka wayar. 
Shikuwa Abba har yanzu idanunsa akan Riyyam din yake.
Sake gyara zamansa yayi, tare kuma da duban Riyyam din.
Cikin sanyi da kuma dan bugun zuciyar da yakeji yace.
“Allah ya jiƙanshi da rahma?”
Idanu Riyyam din yadan lumshe, still cikin zubar da hawaye yace.
“Amin Amin. Ameeeeeeen ya rabbil izzati ngd matuƙa da addu’arga.” 
Ayanzu kam gaba daya tsananin tausayi da kuma raunin yaronne ya rufe musu zuciya.
Hatta Abba kuwa saida yaji zuciyarsa ta raunana. 
Nandai sukayiwa Baban Riyyam din addu’a, bayan sun kammala cin abincinne kuma kowannesu ya watse zuciyarsa cike da tausayin Riyyam-nsra. 
To ayau din dai kam gaba daya Riyyam din tare da Ramadan suka wuni har dare kuma suna tare. 
Inda washegari laraba ne kuma, Jannart  taji saukin jikinta yasa ta shirya zuwa aiki, bayan ta gaya wa Daddyn nata cewa zata biya ta gidan Abba Kabeer.
Daddy kuwa Ganin cewa Jannart din bata da wani ishashshen lafiya sosai ne, yasa bai hana ta zuwa gidan Abba Kabeer dinba. 
Jannart din kuwa Koda ta fito daga gidan nasu, kaitsaye gidan Abba Kabir ta nufa. 
Koda ta isa gidan tarba maikyau ta samu daga wajen Aunty Dijat, bayan sun gaisa ne kuma.
Aunty Dijat din ta sanar mata cewa.
Abba Kabir din na kiranta.
Akaron farko kenan  a iya tsawon rayuwarta, da taji wani abu mai kama da faduwar gaba, saboda Abba Kabir din ya kirata.
Sunan Allah ta soma ambato acikin zuciyarta.
Lokacin da ta isa bakin kofar bedroom din nasa ne kuma tayi knocking daga ciki aka bata izinin shigowa.
Ahankali ta tura kofar dakin ta shiga bakinta dauke da sallama. 
Bayan Abba Kabir din ya amsa mata sallaman ne kuma yayi mata alama akan tazo ta zauna. 
Babu musu kuwa ta karaso ta zauna agabansa, Yayinda shikuwa yake zaune akan gado.
Koda suka gaisa kuwa Almost 5 minutes haka suka zauna shiru. 
Ahankali kuma Barrister Kabir din ya gyara zamansa.
Cikin kuma muryar dake bayyana iya gaskiyarsa, da kuma abunda ke cikin zuciyarsa da alamun umarni yace.
*”Jannart Aurenki ya kusa fa zanyi miki Aure!”*
Ya fadi mgnar cikin serious 
Wanda hakan yasa Jannart cikin wani irin yanayi mai rauni.
Da harbawar zuciya cikin sauri Jannart din ta D…….

Back to top button