Karfe A Wuta Chapter 34 By Ayshercool
Abunka da zuciya, dumm haka ƙirjin Jauhar ya buga, da ƙarfin gaske, take wani abu da ba ta san menene ba ya taso mata.A ranta ta ce “Saboda haka dama ku ka aura mini Al’amin, dan rusa aurena da Alhaji mu’zzam?”‘kul jauhar, Al’amin zaɓin Allah ne a gare ki, babu wanda yake da ikon canzawa wani ƙaddararsa, dama haka Allah ya tsara miki’Cikin sauri ta ce “Ahh haba, amma ba a gaya mini ba, ga shi muna waya, ina yi muku magana ta what’s app, Anty ke ma ina da lambarki, amma ba a gaya mini, ko dan kar in haɗa lefen na zo na ɗauki kayan kwalliya ne ya sa ba a gaya mini ba?”Anty Zakiyya ta ce “A’a kar a gaya miki ki ji wani abu a ranki ne, dama Allah bai ƙaddara mijinki bane”Jauhar ta ce “Haka ne, mijin wata baya auren matar wani, idan an gama haɗawa ni dai zan zo a bani kayan kwalliya”.Surayya ta ce “Au, ashe fa ba ayi miki lefe ba ke ko?”Jauhar ta girgiza kai ta ce “A’a kin manta an yi mini sayayyar kaya?””Duk da haka wannan ai ba lefe bane ba”Wayar jauhar ta fara ringing, ta cirota daga jakarta ta ce “Master””Fito mu tafi””To gani nan””Bari na tashi yana jirana, idan an saka lokaci sai a gaya mini”Hafsa ta ce “An saka bayan salla da sati uku ne””To Allah ya sa zamu gani, a gaishe mini da baba, sai kuma Allah ya kaimu salla, Anty walida ku kuma na gaji da roƙonku ku zo gidana, ko sau ɗaya babu wanda ya taɓa yi mini kara ya zo”.Hafsa ta ce “Ke fa babu wanda zaki gani a gidanki, muna yayyenki zamu din ga zuwa gidanki, ko so ki ke mu zo mijinki yayi mana illa?””Haba dai, ba fa mahaukaci ba ne, da zai yi muku illa, da ban kawo yanzu tare da shi ba, sai anjimanku”Zuba mata ido yayi, har ta ƙaraso, sai dai ya lura da jikinta a sanyaye yake, bai ce mata uffan ba, ya kunna babur ɗin, ya karkata mata ta riƙe shi ta hau suka tafi.Sai yanzu ta ƙara gane dalilin yin amfani da yi mata sharri, wurin aura mata Al’amin, ba wai tana baƙin ciki da auren hafsa bane ba, ta san haka Allah ya ƙaddara kawai mamakin tsananin ƙin da suke yi mata take yi, ta san ko da kuɗi ba za su yadda su aurawa ‘ya’yan su mutum irin Al’amin ba, saboda kar ta huta shiyasa suka yi mata wannan muguntar.Kallon bayan Al’amin take yi, a ranta ta ce “Kai Allah ya zaɓa mini, kuma in sha Allah sai na yi kyakywar rayuwar aure da kai master’.Da haka suka ƙaraso gida, sai dai yana ankare da yadda walwalarta ta gushe, take komai jiki a sanyaye babu kuzari.Ɗan muzurunta na ta kewayata, yana yi mata ɗan kuka, amma ta kasa kula shi, wanda da tana cikin walwala da tuni ta ɗauke shi tana yi masa rawa, da ma shi ba shiri yake yi da muzurun ba, dan dana sanin kawo mata shi ma yake yi, saboda yadda take tsananin ba wa muzurun kulawa, kamar ya jefar da shi haka yake ji wasu lokutan.Ya zuba mata ido, tana ta yi wa wani mayafi ado da beads, na kayan sallar mutane da take ta yi, sai dai a saɓule take aikin.Muzurun ma ya gaji, ya koma gefe ya kwanta, saboda ta kasa kula shi.Har aka sha ruwa, ko surutun yau ba ta iya yi, abincin ma cakalarsa kawai take yi, ta kasa ci ta ajiye ta tashi tayar da sallar taraweeh.Ta cigaba da aikin beads.”Ssss, Ji mana” ta ɗaga kai ta kalleshi.”Zo mana”ta ce “To” ta yinƙura ta tashi, ta ƙaraso gaban sa, tana ƙoƙarin zama a ƙasa, ya nuna mata kusa da shi, ta zauna tare da sunkuyar da kanta.”Kin ga muna zamanzamanmu, ki ka kwashe mu, muka je wurin mutanen nan, gashi kin je an yi miki wani abun kin kasa sukuni, shiyasa tun farko na ce kar mu je, ki ka dage, kin dawo kin kasa nutsuwa, me aka yi miki?”Ta girgiza masa kai ta ce “Bakomai”Ya ce “Bana tambaya sau biyu””Ka yi haƙuri dan Allah, babu komai, zuwa da safe zan wartsake in sha Allah”.”Ba ki da juriya, kin fiye rauni, da wuri ake ganin gazawar ki, ki ƙara ƙoƙarin zama jaruma, ko dai ayi miki ki shanye ko shirya ramuwar gayya sama da abun da aka yi miki. Ki ajiye wannan abun da ki ke yi, ki tafi ki je ki kwanta”Ta jinjina masa kai ta ce “To master, na gode sosai” ta tashi jiki a sanyaye ta tafi ta kwanta.Sai dai bacci ya gagari idonta, ta din ga tunanin, meke damunta kishi ne ko hassada. Sai dai ta tabattar wa da kanta ba kishi bane ba, saboda ta riga ta zama matar wani, ko ba komai a yadda yake ɗin nan, ta fara appreciating yanayin zaman na su yanz saɓanin da, dan haka tana matar wani ba zata yi kishi a kan wani ba.Hakazalika ba hassada ba ce ba, ba ta ji ta damu dan hafsa zata shiga cikin daular da, da ita ce zata shiga, ta san wannan nufin Allah ne, kawai tana jinjina yadda suka shiga suka fita, suka aura mata Al’amin dan kawai kar ta auri Alhaji mu’azzam.Wannan gillin ɗabi’a ce ga zuciya, da duk yadda ɗan adam ya kai ga dannewa sai yayi tasiri, ta din ga istigfari da roƙon Allah ya sanyaya mata ranta, ta manta ta fuskanci Rayuwarta.Yanayin yadda Al’amin ya fara nuna damuwarsa a kanta, ya ke sanya wa ta ji tabbaci da ƙwarin gwiwar cewa wataran za ta ji daɗinsa, tun da dai babu duka ko zagi a tsakanin su, shaye-shayen sa da nema rigimarsa ne babbar matsalarta, gashi yanzu cefane ma yana yi ko ba kullum ba.A cikin kwanakin da ta dage da addu’a, sai ta fara jin sassauci ta fara mantawa, ta cigaba da mayar da hankali a kan sana’arta, da yi musu Addu’a babu dare babu rana.Al’amin ya fara rage yin shaye-shaye a gabanta, sai ta yi bacci, sai ya fita tsakar gida, ko ƙofar gida yayi, duk da wasu lokutan idan ta shiga ta tarar da shi yana yi, mazewa yake yi ya haɗe rai ya cigaba da shan abun sa, amma sosai yake rage abun da zai yi, wanda zai sanya ta shiga damuwa.Ya mayar da ita asibiti, likita ya tabattar da jininta ya sauka, kuma ya dakatar da ita daga shan magani, na wani ɗan lokaci.Saura sati guda salla, gidan jauhar mutane ne kawai ke shiga suna fita, masu mayafai, masu ɗinkuna da zata yi wa stone work, masu kitso da lalle, a haka kuma tana kasa kayanta, na shirin dutse, sarƙa abun hannu, jigida, ga kayan lemo, masu zuwa kitso suna yi mata ciniki. Ta zama very busy, idan yamma ta gabato, ga aikin abinci, sai dai garin Allah yana wayewa, ya fice ya bar gidan, saboda mutane.Sai dai ana shan ruwa take sallamar kowa, ta ce sai gobe, za ta kula da mijinta.Yana falo a zaune, ya gama shan ruwa ya kasa tashi, wata mata tayi sallama, tayi ta yi wa jauhar magiya, wai tana son ta turo yaran, ta wanke musu kai, tayi musu kitso, kowace yarinya ɗari da hamsin, su huɗu.Jauhar ta ce “Haba Maman Nana, ki bani ɗari bibbiyu mana, ga wanke musu kai, ga kitso?””Taimakawa zaki yi jauhar, idan ki na son gobe mu kawo miki coustomers, kin san yadda garin yake, ubansu bai bani ko sisi ba, ni nake wahalata dan yaran su fito fes, ko hankici bai yi mana ba”Jauhar ta ce “To shikenan, bari na sallami master, gobe in Allah ya kaimu akwai mutane sosai, turo su yanzu a wanke musu kan, in dafa ruwa a heater tun da da wuta, gobe in Allah ya kaimu da sassafe sai ayi kitson””Ke, na hana kitson, kwashi yaranki ki tafi wani wurin ayi miki” ta ji muryarsa a ƙofar falo.Jauhar ta ce “Master meyasa?”.”Na hana kitson, duk wannan wahalar da ki ke wuni kina yi a ɗari da hamsin? Dama wuni ki ke wahalar banza, saboda aikin yi yayi miki ƙaranci? Get out malama kwashe yaranki ki fita, iyayen son banza”.Kamar jauhar ta yi kuka ta ce “Master dan Allah…”Shhh” yayi maganar yana ɗora yatsansa a kan laɓɓansa.Matar ta fita ta kalleshi kamar za ta yi kuka ya ce “Na ga aiki ne yayi miki ƙaranci, mu je ina da aikin da zan baki ni, ki zauna ki wuni kina wahala, a ɗari da hamsin, ina zaki kai kuɗi ne wai? Duk kin rame saboda kin saka azabar son kuɗi a ranki” Yayi maganar yana kallon ta, tana tsaye tana tura baki.Ya fizgota gabansa ya ce ya kai hannunsa wuyanta ya ce “Wannan ƙashin na wuya da ki na shi? Duk kin yi wuri-wuri ga azumi ga wahala” da sauri ta ɗan kama jikinta, saboda unexpected ya saka hannunsa a wuyanta.Maimakon ya sauke hannunsa, sai ya miƙar da hannunsa zuwa kan maƙogwaronta, ya fito da dogon harshen sa har wurin haɓarsa, ya lanƙwasa shi, sannan ya mayar cikin bakinsa ya ce “Na ga kina motsa baki, me zaki ce?”Jauhar ta ce “Ai shikenan ka korar mini coustomer, kuma ka shaƙeni zaka kasheni ka huta. Kuma sai ka biyani kuɗin wanda ka korar mini, ɗari shida””Bana son ganin wannan ƙashin, kwana uku kawai na baki ya koma” yayi maganar yana sake shafa wuyanta. Riƙe hannunsa tayi, tana kallon idonsa, da abun da yake yi matan ko a jikinsa.Ɗan muzurunta ne, ya yo tsalle yana yakushin ƙafar Al’amin, saboda riƙe wuyan jauhar da ya yi, yana kuka.Al’amin ya kalli muzurun, yayi cilli da shi, ya ce “Na kusa mayar da abun nan in da na ɗauko shi, ya fiye zaƙewa, zo ki yi mini aikina”Ta biyo shi tana mitar ya korar mata coustomer’s , ya nuna mata kujera 3seater ya ce ta zauna.Ta nemi wuri ta zauna, ya kwanta ya miƙe ƙafafuwan sa a kan cinyarta ya kaɗa mata yatsunsa, alamar tayi masa tausa.Ta ji haushin yi mata asarar ɗari shidan da yayi, shi kuwa ko a jikinsa, sai dai ƙasan zuciyarta mamaki take yi, ashe yana kallonta har haka da ya gane ta rame.Iya ƙarfinta ta saka tana jan yatsun ƙafarsa, tana son yayi magana, amma ko a jikinsa.Tun tana yi da marmari, har ta fara gajiya, dama gashi wuni tayi aiki, tun tsakiyar azumi rabonta da baccin kirki.A take ta fara gyangyaɗi, bacci mai ɗan nauyi ya yi gaba da ita, kamar a mafarki ta ji abu yana taɓa cikinta, ta buɗe idonta ta ga menene, babban yatsansa ya saka yana taɓa cikinta.Da sauri ta ɗame cikinta, ta kalle shi, ya rufe idonsa kamar mai bacci. Ta riƙe ƙafarsa, ta sake kallonsa, amma ya saka ɗayar ya cigaba.Ta saka duka hannunta biyu, ta rirriƙe ƙafafunsa, tana ajiyar zuciya kamar mara gaskiya.A hankali ya buɗe idonsa, yana kallonta, ta sake ɗaga kai ta kalleshi, suka haɗa ido, tayi saurin kawar da kanta.”Dambe zamu yi ne ki ka rirriƙe mini ƙafa? Tausa fa na ce ki yi mini”.Kamar ta yi kuka ta ce “Na gaji bacci nake ji””Eh da aikin banzanki ne, ba zaki gaji ba ai, kin ga yanzu kya samu lada sama da ɗari shidan da ki ke yi mini ƙunƙuni a kanta”A shagwaɓe ta ce “Ni ba ƙunƙuni nake yi ba fa, ka yi haƙuri to” ya janye ƙafafuwan sa daga kan cinyarta, ta tashi da sauri, muzurunta ya bi bayanta, ta saka hannu ta ɗauke shi ta nufi ɗaki.Baba ya ji daɗin abun da ya tarar jauhar ta kai masa, ya din ga murna da sanya mata albarka, tare da yi mata addu’a iri-iri.Ganin hankalin Jauhar yana kan ‘yan kuɗaɗen da take samu, na sana’ointa, ya sanya ya ƙyaleta, baya son yawan takura mata.A goman ƙarshen nan, haka ta din ga damunsa, a kan yawaita ibada, dan azumin kawai yake yi, ba sauran ibadu. Da ƙyar take saka shi yayi salla cikin dare ko raka’a biyu ce.Dama idan aka sha ruwa, ya ƙoshi sai ya je dabar su, sun yi shaye-shaye tukuna ya dawo gida.Ana jibi salla, ta saka shi a gaba da naci, da magiya, su je ayi masa aski saboda gabatowar bikin salla ƙarama.Ya ce na za shi ba, ƙarshe ita ta zauna, ta wanke masa kan, ta rage masa sumar da almakashi, tayi masa gyaran fuska da shaver, tamkar ɗa da uwa.Ana gobe salla, ta yi masa list dai-dai na talaka, ta ce ya sayo, za ta yi abincin salla, dan abubuwa da dama idan ba ta ce masa yayi ba, ba zai yi ba, idan kuwa ta ce ya sayo zai sayo, idan ba shi da hali kuma zai gaya mata ba yanzu ba.Da sassafe ƙarfe bakwai, ta shigo ɗakinsa da mp ɗin ta, an sako kabarbari da ake yi yayin tafiya idi, tana maimaitawa.*Allahu Akbar, Allahu Akbar la’ilahaillala**Allahu Akbar, Allahu Akbar walillahil hamd**Allahu Akbar kabiran**Walhamdilillahi kathiran**Wa subhanallah bukratan wa asila*”Master, kar mu makara sallar idi fa, ka tashi” ya motsa a hankali yana yamutsa fuska.Ta miƙa masa hannu ta ce “Barka da salla? Ina fatan ka yi sallar idi lafiya”Yayi miƙa tare da hamma, ta ce “A’uzibillah, Alhamdilillahilazi ahyana, ba’ada ma amanatana wa ilaihil nushur. Ga ruwa mai zafi can, ka zo ka karya mu shirya””Sai na karya tukuna””To taso ka yi brush, ko sai na ɗauke ka ne, sai ƙara maƙalewa ka ke yi a katifa”Kukan ɗan muzurun nan ne ya sanya Al’amin shi tashi zaune ba shiri, ya biyo jauhar yana yi mata ɗan kuka.Ta kalli muzurun ta ce “Sweetheart, mu je na baka abinci” Al’amin ya tashi ya bar ta da muzurunta, saboda zaƙewar muzurun ta fara yawa a kan matarsa.Ya fito daga wanka, ta shigo ɗakin da wata leda, ta saka dogon hijjabi light blue, sai zuba ƙamshi take.”Master yi sauri zamu makara”Ya shafa mai, ta buɗe ledar ta fito da ɗinkakkiyar shadda light blue, da hula, ga agogo sai takalmi soso na ta da nasa, iri ɗaya na ta na mata na sa kuma na maza.Turus yayi yana kallonta, cikin tsananin mamaki.”Ungo saka, bari na je na rufe ɗakina kan ka gama”Kamar soko ya kasa karɓar kayan.”Ko ba ka so ne?” Tayi maganar a sanyaye.”A ina ki ka samo wannan kayan?”Ta ce “Dama ana samo kaya ne? Neman kuɗin da ka ke cewa na saka a gaba ne, ka san wata nayi ina yi mana tarin nan? Hmm saka kayanka ina zuwa bari na ɗaukko wayata da darduma” ta ajiye masa ta fice.Kallon kayan ya din ga yi yana jujjuya su, har da aiki a jikin kayan, shi bai yi mata kayan salla ba tayi masa?.Ya saka wandon, ya tsaya yayi shiru yana kallon rigar, har ta dawo ɗakin.”Master saka mana” ta karɓi rigar tana ɓalle botiran jiki, ya karɓa yana sakawa ta ce “Alhamdilillahilazi kasani haza saub, waraƙatani min gairi haulin minni wala ƙuwwa”Ta saka masa hula, ta saka masa lence ɗin hannun rigar, ta ɗaura masa agogo, tare da saka masa farin glass na maza.Tayi wani irin murmushi ta ce “Tubli wa yuklifllahu ta’ala. Wallahi kana da kyau master, ka ga yadda ka yi kyau kuwa? Subhanallah saka takalmin mu ke falo na yi maka hotuna” gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, ashe matan ma sunan suka tara? Wace irin mace ce jauhar.”Master ka yi dariya mana, sai hoton ya fi kyau”Ta gama yi masa hotunan, ta riƙo hannunsa, ita ma ta saka nata gilashin fari, suka fita sallar idi.Musulunci mai daɗi, al’ummar musulmi na ta ɓarkowa ta kowane angle zuwa masallacin idi.Shi rabonsa da zuwa sallar idi ma, har ya manta lokacin, amma yau albarkacin auren mace ta gari, ta saka shi a gaba har zuwa masallaci.Aka idar da sallar idi, suka haɗu a wani gate ɗin daban, bisa koyi ga sunna, jauhar ta bawa wata wayarta, ta ce dan Allah tayi mata hoton first eid with habinbi.Ta ɗauka zai ce baya so, bisa ga mamakinta, sai ta ga ya saka hannu, ya dafo kafaɗarta jikinsa, yana kallonta, ta saka hannu ta zagaya a ƙugunsa kasancewar da kaɗan ta wuce ƙugunsa, ta kalleshi ita ma tana murmushi. Hotunan sun yi kyau sosai, banda wanda ya yi wa Al’amin kyakkyawan sani, ba zai gane shi ba, sai ya zama very decent and calm.Har suka dawo gida, hannunta na cikin nasa, cike da shauƙi da nishaɗi.Ya karɓi mukulli ya buɗe musu gida suka shiga, jauhar baba ta fara kira, ta yi masa barka da salla, ya ce mata idan mijinta na da account, ta tura masa ya saka mata barka da salla.Ta kira yaya saifu ma, haka ta din ga bin family tana yi musu barka da salla.Ta kalli Al’amin ta miƙa masa wayarta ta ce “Saka mini lambar baba, mu yi masa barka da salla””Bani da ita” ya bata amsa.Ta marairaice ta ce “Dan Allah master”Ya ce “Sai kuma ki yi”Haka ta haƙura ta tashi ta ƙyale shi, ta tafi ɗakinta, ya din ga kallon kayan jikinsa, yana sake jinjina ƙoƙari da ƙarfin hali irin na jauhar, wai shi ta yi wa kayan salla.A status ɗin ta, ta yi posting “Alhamdilillah first eid with my amazing Habibi, Allah ya ƙara wa zamaninka tsayi, ya maimaita mana”Surayya ce ta fara ganin status ɗin, ta din dariya tana nuna wa ‘yan gidan, suka din ga cewa pretending ne, na lallai sai ta nuna wa mutane tana cikin kwanciyar hankali, sai dai suna tsaka da gulmar, ta sake saka hotonsu riƙe da dadduma a filin idi, wanda hakan ba ƙaramin girgiza su yayi ba da ba su mamaki.Master ya kai mintuna goma sha biyar yana zaune, ta fito sanye da leshinta da ta saka ranar ɗaurin aure, ta shafa powder da jambaki, ta saka kwalli, ta kwantar da gashin gaban kanta, da gel, ta yi ɗauri mai kyan gaske, gashi ta kaiwa Suwaiba tela ta gyara mata ɗinkin, dai-dai jikinta.Har ya tashi zai shiga ɗakinsa, ya waiwayo ya ganta ta fito, mp ce a hannunta, tana bin waƙar da aka saka, a cikin nishaɗin barka da salla.Cikin waƙar m sharif *Farin gani kai ne tauraro, ko a cikin samari, mai ji da ni ba ka yin ƙwauro ka sa na wuce gori, na ɗau takarda na riƙe biro, kai na saka a fari, kai zan ba dawakai, kowanne da silkai, matsayinka ya kai ba zan yi ma kishiya ba…….Da haka ta ƙaraso gabansa tana rawa, tana yi masa fari da ido.Tsayawa yayi yana kallonta yana murmushi, sai dai bai tsinke da lamarin na ta ba, sai da ta ƙaraso gabansa ta riƙe hannunsa wai sai ya yi rawa.Karo na farko da ya buɗe haƙoransa talatin da shida yayi dariya.”Ba dariya zaka yi ba, ka yi mini liƙi ko ka yi mini rawa” ya buɗe baki ya ce “You are not serious””Am serious mana, rawa ko liƙi, biyani ɗari shida ta ma da ka korar mini coustomer’s” ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu da ɗari uku ya ce “Suke nan nake da su, uwar son kuɗi””Ungo dubu ɗaya, sauran bari na bayar da ayata a markaɗo mini, na haɗa da snacks da tuwon salla na raba. Ba ka ce ma na yi kyau ba, ka taɓa ganin mace da tayi kwalliya tayi kyau kamar yadda na yi yau?”Yayi murmushi ya ce “Ni da ba kallon mata nake yi ba, ya za ayi na sani, ni dai ba ki yi mini kyau ba, kamar babyn roba haka ki ka zama” yayi maganar yana matsa kumatunta.”Daga Angela zuwa ‘yar madara, yanzu kuma babyn roba?””Eh, irin na wasan nan ba”Jauhar ta ce “Kyau nayi maka ne”Ta fice tsakat gida, tabbas tayi kyau kam, tayi fresh farar fatarta ta karɓi baƙin leshin sosai da sosai, kwalliyar ta yi mata kyau.Tana tsakar gida, wasila ta shigo ta kawo mata tuwon salla, suka gaisa tare da yi wa juna barka da salla.Wasila ta ce “Jauhar iyayen soyayya, mu matan layin nan, tare muka haɗa kai muka tafi idi, a hanya muka hango ku, an maƙalƙale hannun master ana yashe baki, kai jauhar a ji tsoron Allah”Jauhar ta ce “Anty wasila kina saka mini ido wallahi, ki sa ka in ta jin kunya””Ke ba wata kunya, riƙe abunki wallahi, abunku gwanin sha’awa, kafin lokacin ya wuce, ba kowane namiji ne yake jure ayi ta soyayya ba”.Al’amin ne ya fito, Wasila tayi tsit dan ba ta san yana nan ba, ta gaishe shi ya amsa ciki-ciki.”Master ina zaka? Kunun aya ka san baya daɗewa””Nura ne a waje ya kirani, ba nisa zan yi ba”Ta ce “Ok to”Daga jikin gate guduma ya ce “Antynmu barka da salla”.Jauhar ta ce “Yauwwa malam nura, ina fatan ka je idi?””Eh na je, na biyo mu gaisa sannan ki bani tuwon salla”.Jauhar ta ce “Aikuwa ka samu, amma sai ka kai mini markaɗen aya, ka sayo ƙanƙara sai na haɗa maka da tuwon”Ya ce “Ba case matar babban yaya”Al’amin bai sani ba, har gidansu jauhar ta aika da abincin salla, guduma ne ya kai ya kai na gidan su ita ma.Ta zuba wa Al’amin, ya tafi da shi, tun da ya shiga wurin na su, Liti da sauran yaran suke bin sa da kallo.Liti ya ce “Maza, wannan shuɗiyar audugar ruwan sararin samaniya fa, waye ya sayeka cikinta?””Ban sani ba”Walid ya ce “Abun a tambaya ne, ni fa tun da na sanka sau ɗaya na ga ka saka manyan kaya, ranar da aka zarga maka uku, ina nufin igiyar sunnar ma’aiki da bint laban ɗin ka, wato madam ‘yar madara”Ya tsuke fuska ya ce “Mai laya”Walid ya ɗaga masa hannu ya ce “Tuba nake, na kiyaya wannan ma’adanar abincin fa?”Al’amin ya ajiye musu kwanuka, suka dirarwa abincin nan da ci babu ji babu gani.Baba kuwa yaya saifu ya aiko, aka kawo mata fulasanta, da kuɗi dubu goma, kasancewar ba ta tura account number da ya ce ba a matsayin barka da sallar ta.Da daddare da ya dawo, yana shigowa ta ji warin sigari, dan da alama ma a cake yake, bai kulata ba, ya tafi ɗakinsa ya baje a kan katifa, ta bi bayansa har cikin ɗakin, cikin matsananciyar damuwa ta ce “Haba master, shi ne ka je ka sha da yawa, kalli a yadda ka dawo fa, gaba ɗaya ka ɓata mini ɗan farincikin da na tsinci kaina a ciki yau” yayi shiru yana sauke numfashi.Ta ƙaras ta ce “Tashi a cire kayan to, sai ka saka wasu””Get out””Ai zan tafi amma……”I said get out” yayi maganar cikin tsawa.Ta tashi a razane, ta bar masa ɗakin, cikin azumi dai Allah ya taimaketa ya ɗan nutsu, saboda baki a rufe yake, ba ya shaye-shaye sosai, yau da ga sallacewa ya koma ruwa.Saboda tsabar takaici, ko baccin kirki ba ta yi ba.Da safe kamar ba shi ba, ya tashi ya fito abun sa, ya sayo abun karyawa, sai share shi take yi, amma ya nuna ko a jikinsa. Kasancewarta mai matukar raunin zuciya, sai kuma ta sake.Suna karyawa, Hafsa ta kira ta a waya, jauhar ta ɗaga tayi mata sallama ta ce “Amarya ba kya laifi””Mhmm, dama anko ne mama ta ce sai an nuna miki, shi ‘yan gida za su yi da bikina, zan turo miki ta what’s app lace ne dubu goma sha biyar sai atamfar kamu dubu tara, na san ba lallai ma ki yi”Jauhar ta yi murmushi ta ce “Anty hafsa kenan, aikam dai kun san mijina talaka ne, zan sako dai abun da Allah ya hore mini na zo, in sha Allah””Dama na sani ai, mama ce ta takura a turo miki kar abun ya zama surutu, a ga kin fita daban. Allah ya sauwwaƙe tisya””Ba tsiya ba ce anty hafsa, idan ruwanka bai isa alwala bane sai ka yi taimama Allah ya kaimu bikin lafiya” ba shi aka gaya wa ba, amma sai ya ji maganganun hafsan tamkar direct da shi take, wani irin haushi da takaici ya kama shi. Sai dai ya basar ya cigaba da karyawa abun sa.Ya kammala ci, ta tashi ta yi aikace-aikacenta, yau ma wata kwaliyyar ta yi da abun da Allah ya yassare mata.Ya ce “Babyn roba”Ba ta kalle shi ba ta ce “Saura ta rodi” “Zaki gama kumbure-kumburen naki ki sace”Ta share shi, tana shafa muzurunta d take cewa boti.”Ina magana ki ka share ni, kina wasa da wannan abun da nake dana sanin kawo shi?””To me zan ce maka? Kawai ka je ka sha abun da ka sha, daga yi maka magana ka hantare ni” tayi maganar idonta na cika da hawaye, saboda takaici.Maimakon ya damu, sai yayi murmushi ya saka hannu ya matsa kumatunta a hankali ya ce “Abun wasa na, you are like a toy to me, wani abu mai ɗan bani nishaɗi wasu lokutan”Galala take bin sa da kallo, ita ce ma abun wasan.”Kin daɗe kina yi mini abubuwa, abun da ki ka yi mini jiya ya tsaya mini a rai, ki ka ɗinka sutura sukutum ki ka bani, Allah ya suturtaki ranar da bayi za su tsaya a gabansa babu sutura. Na gode Allah ya baki miji nagari”Da sauri ta sake kallonsa, sakamon abun da ya faɗa na Allah ya ba ta miji nagari.”I still mean it, haryanzu ina kan bakana na rabuwa da ke a duk lokacin da ya dace, kina takura mini da yawa”A fusace ta saka hannu, ta buge hannunsa da ya riƙe kumatunta, ta waiwaya tana kallon gefenta.Ya ce “Idan ki ka kuskura ki ka jefe ni, yau ni da ke ne” tashi ta yi tana kuka, ta nufi ɗakinta.
Ayshercool 08081012143
