Halysaah Page 161 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 161…Khaleesat na shiga dakin Nenne siblings dinta suka taso da gudu suka rungumeta cike da murnan ganinta, Khaleesat ta ja kunnen Islam tana murmushi tace “Shi ne kika ki zuwa Bauchi ko” Dariya Islam tayi tace “Umma ce tace kar in bar ta ita kadai fa” Nenne dake ta kallon Khaleesat tace “A’a karya take, ina ruwan wata Umma da ita tunda ba nono zata bata ba” Khaleesat na murmushi ta karasa kusa da Nenne ta zauna tace “Ina yini Nenne?” Nenne tace “Lafiya qlau Khaleesat, Alhamdulillahi hankali ya samu, har kun dawo daga tafiyar?” Khaleesat ta wani kalleta tace “To da bani da hankali?” Nenne tace “Atoh, naga a nutse kika shigo ne ai shi yasa, ko da yake tun a Bauchi ina ta mamakin nutsuwarki da muka je lokacin” Khaleesat dai murmushi kawai take, Nenne tace “Ina Yariman?” Khaleesat na wasa da gyalenta tace “Yana masallaci” Nenne tace “Maa sha Allah, wani kasar ku ka je halan? Ko da yake ni da kika yaudara za a tafi Amurka da ni ashe karya kika tsula min, Allah ya so ban gaya ma kowa ba balle aga ban tafi ba ayi min dariya inji kunya” Dariya Khaleesat tayi tace “To wa yace maki wataran baza aje da ke ba? Kin fiye azarbabi ne” Nenne tace “To Allah ya kawo wannan lokacin dai” Khaleesat tace “Baba na parlonsa ne Nenne?” Nenne tace “A’a sun kai kaya Lakwaja, wani babban mutum ne da ya saba aiki da shi da dadewa ya damka masa kayan ya taimaka ya kai masa Lakwaja don kayan kudi ne ba kadan ba….” Khaleesat tayi shiru, sai kuma a hankali tace “Amma ni bana son Baba ya ci gaba da wannan sana’ar fa Nenne” Nenne tace “To hauka ake Khaleesat? Taimako kawai yayi wannan saboda an yarda da shi aka basa kayan ya kai, kuma yana matukar jin kunyan mutumin, bai ma dade da dawowa kasar ba mutumin, da yana nan kilan da ya tsaya ma Ali a sanda aka dauresa, to ko sisi baban naki ma yaki karba a kyauta zai kai masa kayan, mu kam yanxu ai kuma Alhamdulillahi babu abinda za mu ce ma Allah sai godiya, ba mu rasa komai ba, muna cikin wadata sosai wallahi kamar ba ayi rayuwar talauci ba, Allah yayi ma Ahmad da mijinki albarka don duk su suka fiddo mu daga kangin talauci, sannan sarki ma ya taba ba Ali miliyan goma ya ja jari, duk fa ba a dade ba Ali ke fada mana, kin san sa da zurfin ciki” Khaleesat ta sauke idonta a hankali tace “To Allah ya saka da alkhairi” Nenne tace “Ameen, ke kam kin kawo mana arziki gidan nan, Allah ya maki albarka Hauwa, Allah ya baku zaman lafıya da mijinki ya azurta ku da yara masu albarka” Cikin sanyin Khaleesat tace “Ameen” Nenne tace “kinsan an kawo kudin auren er uwarki Lamisa kuwa?” Khaleesat ta bude ido tace “Haba dai?” Nenne tace “Wallahi kuwa in gaya maki, yaron abokin babanku Salihu ne ya fito yana sonta, da naga nutsattse ne kuma ya samu karatu babu laifi nace to a basa kawai, nan da wata shidda biki, sunan yaron Kallamu” Khaleesat tace “Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya kai mu lokacin lafiya” Nenne tace “Ameen, sannan uwar Ahmad ta zo gidan nan yau kwana uku in gaya maki” Khaleesat ta dan yi shiru sai kuma tace “Wani Ahmad kuma?” Nenne tace “Jewe ku ke ce masa ko me, Ahmad dai dan uwan mijin ki, Ahmad dan albarka yaron kirki” Khaleesat ta dan bude ido da mamaki tace “Da gaske Nenne?” Nenne ta gyara zama tace “Wallahi in gaya maki, ta zo har nan ta bamu hakuri gwanin ban tausayi har da hawayenta, har sai da ta sa ni kuka nima, gaskiya matar nan mutum ce….” Khaleesat ta sauke idonta lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, sanda suke Tanzania sau biyu Ajay ya kira Mami kuma duk sai da tace ya bata wayan, Nenne tace “Ta ce tayi da ta sanin abinda ta aikata mana ayi hakuri a yafe mata, da yake kusan magariba aka kawota a katuwar motar har Malam Ali sai da suka gaisa shi ma ta basa hakuri baiwar Allah, ai haka ake son mutum yayi kuskure ya gane kuskurensa ya nemi gafara tun a duniya, lallai ta cika musulmar kwarai, kuma nasan ba komai bane sharrin shaidan ne abinda tayi da kuma zugan yan masarautar nan, ko matar sarkin nan ma ta isa ta zugeta ta kai ta ta baro” Khaleesat ta sauke ajiyar zuciya, Nenne tace “Ga kuma wani abu da ake ta boye maki, duk da lokacin kin koma Amurka bayan aurenku da Yarima, Awdul dai zuwansa biyu gidan nan yana gaishe mu in gaya maki, mu dai a tsorace muke Ummanki ce kadai ke basa fuska, ranan farko da ya zo ya ba yan biyu dubu hamsin su raba, zuwansa na karshe ma haka, kudaden na nan mun ajiye babu ruwanmu wallahi, amma kuma sai naga kamar shiriyar Allah ce fa ta samesa, don ya dawo wani nutsattse wallahi, amma kuma sai naga kamar shiriyar Allah ce fa ta samesa, don ya dawo wani nutsattse wallahi, tausayi ma yake ban” Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba, bayan few seconds ta mike tace “Ina zuwa Nenne tace “Ina kuma za ki?” Khaleesat tace “Zan duba ko ya idar ne” Nenne tace “To yi maza ki tafi gaskiya” Nenne ta bi ta da kallo har ta fita, sai kuma ta rike haba cike da mamaki tace “Ikon Allah, to Allah mun gode maka da ka saita mana er nan tayi hankali tasan ciwon kanta” Mikewa Nenne tayi ta fita parlor don ganin su waye a parlor ta korasu tace bako zai shigo, a Parlon ta tarar da Aunty Farida ta kunna turaren wuta ta kunna Ac bata dai ce ma su Mama Zubaida komai ba, don yanxu magana daya biyu sai su fashe da kuka wai ana masu gori ana hantarar su, Nenne tace “To ke Parida ba sai kice su fita daga parlon ba bako zai shigo a gaisa?” Nenne bata rufe baki ba su Mama Zubaida suka mike duk suka bar parlon, Nenne tace “Don ma dai sanyi ya fara shigowa banda haka ai da parlon nan ya dume yanxu da warin mata, haka kawai mu ji kunya tunda bakon kunya ne Ita dai Aunty Farida bata tanka Nenne ba ta tafi ta ajiye kaskon turaren wutan can wajen dinning area, Khaleesat na fita gate ta tarar da Ajay tsaye jikin mota yana danna wayarsa, ta karasa kusa da shi tace “Yaushe ka fito masallacin?” Yace “Just now” Tace “Ohk na zata ka dade da fitowa Ya girgiza mata kai yace “Not at all” Tace “To ka shigo ku gaisa da yan gidan” A hankali yace “Amma bamu kawo masu komai ba Jeeddah” Ta dan yi murmushi tace “Mu da muka dawo daga wata kasar Yayi shiru bai ce komai ba, ta dan bi unguwan da kallo ganin babu kowa ta kama hannunsa zuwa cikin gidan, Nenne na zaune parlor tare da Aunty Farida suna jiran shigowar Ajay, ga lemo da ruwa ta jido masa daga dakinta don har da Fridge gareta a dakin, tun bai karaso ya zauna kasan carpet ba Nenne tayi saurin cewa “Don Allah ka zauna kan kujera kar kace zaka zauna kasa Yarima” Ya dan yi murmushi bai dago kansa ba yana karasawa ciki, Khaleesat a dan zaman da tayi da Ajay ta lura yana da kunya a inda ya kamata, kuma tasan bazai zauna kan kujeran ba saboda Nenne, hakan yasa ta dau darduman da Aunty Farida ta ajiye a parlon ta shimfida masa ya zauna a kai sannan ya gaida Nenne, Nenne ta amsa da fara’a tana masa sannu da zuwa, ya maida dubansa kan Aunty Farida suka gaisa ita ma da fara’arta, ba a dau lokaci ba Umma ta fito parlon ita ma suka gaisa da shi ta juya ta koma daki, su Islam da Stepsisters dinta duk suka fito su ma suka gaishesa, su Mama Zubaida ma duk suka leko a gaisa, Khaleesat dai sai kallonsa take don gaba daya he is uncomfortable, Nenne tace “To ki kai sa parlon Ali a zubo masa abinci” Ajay ya daga kai yace “A’a kaka mun ci abinci, yanxu zan koma gida ne, sai gobe in sha Allah zan zo” Nenne tace “To ko ruwa baza ka sha ba Yarima” Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, Nenne tace “To Allah ya kai mu goben Yarima, Allah ya huce gajiya” Sai kuma ta kalli Khaleesat tace “Ki dauko jakarki ku tafi ko” Khaleesat ta sauke idonta sai kuma ta mike ta tafi dakin Nenne ta dauko handbag dinta, sai da ta fara shiga dakin Ummanta, Umma tace “Za ku tafi Khaleesat?” Khaleesat ta sauke ido tace “Eh sai gobe da safe in sha Allah Umma” Umma tace “To Allah Ubangiji ya kai mu, amma abinci fa? Ko zaki tafi maku da shi?” Khaleesat ta girgiza kai tace “Akwai abinci a can Umma” Umma tace “To Allah ya tashe mu lafiya” Juyawa Khaleesat tayi ta fita daga dakin ta koma parlor ta tarar har Ajay ya fita, tayi ma Nenne da Aunty Farida sallama, Nenne na cewa “Maza ki tafi kin bar sa a waje” Khaleesat ta leka dakin Mama Shatu ganin bata nan ta fita daga parlon tana daga ma Aunty Farida hannu, Aunty Farida dai ta kasa daina mamakin Khaleesat. Khaleesat na fita kofar gida ta tarar da Ajay cikin mota har ya tada motar, ta bude front seat ta shiga tana kallonsa, yayi kasa da murya yace “But nace ai ki kwana fa Jeeddah” Tayi shiru tana kallonsa, ya sauke idonsa yace “It’s somehow mu koma tare ai yanxu” Ta jingina da kujeran motar ta tura baki tace “To bayan duk na masu sallama sai aga na koma” Murmushi yayi yace “Naga alama dai ke baki jin kunya” A hankali tace “To kunyan me zan ji? Bayan an san mijina zan bi” He couldn’t stop smiling yana kallonta yace “To ke idan baza ki ji kunyan ba ni dai zan ji” Ta wani kallesa tace “To ba kace za mu dawo gobe ba?” Yace “In sha Allah” Tace “Idan muka dawo sai in kwana tunda kace za mu yi kwana biyu” Yace “Ohk then Milady” Reverse yayi suka bar unguwan, sannan yace “Kaka tace min Baba ya tafi Lokoja da kaya ko?” Khaleesat ta gyada kai, yayi kasa da murya yace “Amma da baba ya hakura da driving haka yayi concentrating a business dinsa, ko ya kika ga?” Khaleesat tace “Ba aiki yaje ba, kawai kaya ya kai ma wani mutum da suka saba, amma ai baya driving yanxu, kyauta ma ya kai masa kayan Lokoja” Ajay ya gyada kai yace “Ohk na gane, but still dai it’s best yayi ignoring driving idan ba within Kano ba” Khaleesat dai tayi shiru bata ce komai ba, after almost 10 mins of silence ta daga kai ta kallesa a hankali tace “Me za ka ci? Nasan ba lallai ka ci abinci a can gidan ba shi yasa ban taho da shi ba” Murmushi yayi yace “Ke zan tambaya me zan siya maki for dinner Milady?” Tace “Hotel za mu je?” Yace “A’a, gida za mu je” Tayi shiru bata ce komai ba, yace “Ban fiye zaman hotel a Kano ba since akwai gida a nan, although wani lokacin ina lodging hotel din, but for now gida za mu je, masu aiki ne kawai a gidan in ba wani occasion ake yi a Kano ba a hankali Khaleesat tace “Ohk….” A wani eatry ya tsaya ya siya mata abinci ya fito, tana ganin leda daya bayan ya shigo motar tace “Tare za mu ci ko?” Yace “A’a, ni tea zan sha” Bata kara cewa komai ba, wajen karfe tara da yan mintuna suka iso gidan, gida ne babba with many rooms, Ajay yayi parking a parking space, yana kara amsa gaisuwan Mai gadi da masu share sharen gidan dake gaishesa a compound, tuni suka sauke boxes din dake booth suka yi cikin gidan da su, Ajay na rike da ledan takeaway din da yayi ma Khaleesat ya nufi entrance din shiga gidan tana biye da shi a baya, ya tura kofar parlon ya shiga Khaleesat na biye da shi, zaune ya ga Jay a parlon yana danna wayarsa yana shan fruit din dake gabansa, sau daya Jay ya kallesu ya ci gaba da shan fruit dinsa at the same time yana amsa sallaman Ajay, Ajay ya karasa cikin parlon ya zauna, after some seconds yace “Good evening Jay” Jay yace “Evening Junaid, fatan kun dawo lafiya” Ajay yace “Alhamdulillah” Jay yace “Maa sha Allah” Daga haka ya maida hankalinsa kan abinda yake yi a wayarsa yana shan fruit dinsa, Ajay yace “Ka dade a Kano kenan?” Jay yace “Not at all, 3 days ago na kawo Mami” Ajay yace “Ohk, tana nan ne?” Jay yace “Bata sauka nan ba” Ajay yace “Ohk” Jay bai kara cewa.komai ba daga haka, Ajay ya dan kalli Khaleesat dake tsaye tana kallon katon hoton Mai martaba dake parlon, mikewa yayi ya nufi stairs ta bi bayansa, sai a sannan Jay ya bi ta da kallon side eyes, Ajay ya bude dakin da yake yawan zama idan ya zo gidan ya shiga ciki da boxes din da workers din gidan suka ajiye bakin kofar dakin, the room was neat and smelling fresh kasancewar ana gyarawa ko da yaushe, ya bi Khaleesat da kallo ganin ta nufi kan gado ta zauna gefen gadon tana cire mayafinta, kulle kofar dakin yayi calmly yace “Jeeddah me yasa baki gaida Jay ba?” Ba tare da Khaleesat ta kallesa ba tana cire jewelries din jikinta tace “Yayi kamar ya gan ni ne da zan gaishesa? Didn’t you see he ignored me? Ae bai yi kamar ya gan ni ba” Ajay yace “No Jeeddah, bana son haka, i wasn’t happy da baki gaishesa ba….” Khaleesat tayi shiru tana kallonsa, sai kuma ta mike tana tafiya a hankali ta nufesa ta kamo hannunsa cikin sanyin murya tace “To kayi hakuri don Allah, bazan sake haka ba in sha Allah, ko yayi kamar bai gan ni ba zan dinga gaishesa yanxu” Ajay yayi shiru, sai kuma ya zame hannunsa a nata ya tafi ya zauna kan kujera, marairaicewa tayi ta bi sa ta zauna kusa da shi kamar zata yi kuka tace “Baka hakura ba Dear?” Yayi mata side hug murya can kasa yace “Na hakura wife, ai bana fushi da ke, just that you should have greeted him, he is elder than me” Dan murmushi tayi tace “Am so sorry Mi Vida, in sha Allah bazan sake haka ba” Ya gyada mata kai a hankali yace “Thank you Jeeddah” tayi pecking lips dinsa tace “Let me take my bath” Ya sauke Idonsa yace “Ohk, Milady” Mikewa tayi ta rage kayan jikinta, sannan ta bude box dinta ta dau abubuwan da zata bukata ta shiga bandakin, Ajay ya dafe kansa a hankali don suna shigowa cikin gidan kansa yayi masa nauyi, Yana ta zaune gefen gado yayi nisa tunanin da yake har Khaleesat ta fito wanka, mikewa yayi yana cire shirt din jikinsa, Khaleesat dai kallonsa kawai take ganin har sannan mood dinsa bai dawo dai dai ba, sai jikinta yayi sanyi tana ganin ta bata masa rai, bandakin ya shiga, ta zauna gefen gado feeling guilty, after some seconds ta mike ta shirya cikin kayan bacci, har zata koma ta zauna sai ta tuna yace zai sha tea, ta kalli kofar dakin sai kuma ta bude ta fita zata dubo kitchen tayi making masa tea, tana sauka downstairs taga Jay baya parlon, karasawa dinning area tayi ta bude kofar da ta gani a wajen don tana zargin kitchen ne, tsaye taga Jay a sink yana wanke bowl din da ya sha fruit salad, tace “Good evening” Sai bayan seconds biyar yace “Tsoron gaisheni kike a gaban mijin ki kenan” Khaleesat bata shiga kitchen din ba tana tsaye bakin kofar tace “Not at all” Komawa gefe tayi ganin zai fita, har ya fita ya wuce sama sannan ta shiga cikin kitchen din zata yi abinda ya sakko da ita kasa, bayan ta gama hada shayin ta koma sama ta shiga daki, Ajay na tsaye ya daura towel yana goge gashin kansa da karamin towel ya daga kai yana kallonta bayan ta shigo dakin, tana murmushi tace “I made you a cup of tea My prince” Yace “Thank you Jeeddah” Ta ajiye shayin kan table ta bata fuska kamar zata yi kuka tace “Wai har yanxu fushi kake da ni dear?” Ya buda ido yace “No wife, i am just tired….” Ta karasa gabansa a hankali tace “Ko in maka tausa?” Murmushi yayi yace “Zaki iya?” Ta sauke idonta tana murmushin ita ma tace “A gwada a gani mana” Yace “To zo ki gwada mu ga” Kan gadon dakin ya tafi ya kwanta yana kallonta, ta rage hasken dakin sannan ta karasa ta hau gadon ita ma, yace “Da Hijab ake tausa?” Tayi murmushi ta cire hijab din ta ajiye sannan ta matsa kusa da shi ta hau kansa tana shafa kirjinsa a hankali har zuwa cikinsa, Ya lumshe ido kamar me jin bacci yace “Down there too Slushie” ita dai murmushi kawai take tana ci gaba da shafa faffadan kirjinsa slowly, ya jawota jikinsa yana magana can kasa kasa yace “To baki cire towel din ba ta yaya zaki yi tausan da kyau wife?” Rufe fuskarta tayi jikinsa tana wani murmushi, sai kuma ta fara…….kofar tace “Not at all” Komawa gefe tayi ganin zai fita, har ya fita ya wuce sama sannan ta shiga cikin kitchen din zata yi abinda ya sakko da ita kasa, bayan ta gama hada shayin ta koma sama ta shiga daki, Ajay na tsaye ya daura towel yana goge gashin kansa da karamin towel ya daga kai yana kallonta bayan ta shigo dakin, tana murmushi tace “I made you a cup of tea My prince” Yace “Thank you Jeeddah” Ta ajiye shayin kan table ta bata fuska kamar zata yi kuka tace “Wai har yanxu fushi kake da ni dear?” Ya buda ido yace “No wife, i am just tired….” Ta karasa gabansa a hankali tace “Ko in maka tausa?” Murmushi yayi yace “Zaki iya?” Ta sauke idonta tana murmushin ita ma tace “A gwada a gani mana” Yace “To zo ki gwada mu ga” Kan gadon dakin ya tafi ya kwanta yana kallonta, ta rage hasken dakin sannan ta karasa ta hau gadon ita ma, yace “Da Hijab ake tausa?” Tayi murmushi ta cire hijab din ta ajiye sannan ta matsa kusa da shi ta hau kansa tana shafa kirjinsa a hankali har zuwa cikinsa, Ya lumshe ido kamar me jin bacci yace “Down there too Slushie” ita dai murmushi kawai take tana ci gaba da shafa faffadan kirjinsa slowly, ya jawota jikinsa yana magana can kasa kasa yace “To baki cire towel din ba ta yaya zaki yi tausan da kyau wife?” Rufe fuskarta tayi jikinsa tana wani murmushi, sai kuma ta fara kwance masa towel din a hankali…..



