Hausa novels

Yar Aikin Karuwa Book 2 Page 66-70 By Asma Baffah

Yar Aikin Karuwai Book 2 Complete Document

🌼’YAR AIKIN KARUWAI 2🌼
MATAFIYA

BOOK 2

66-70

Official

By
AsmaBaffa

 

SADAUKARWA GA
ZAINAB USMAN

 

Adashin kudi kamar haka
20k kwasa 200k
Slt 1 2 4 7 8 9 10

30k kwasa 150kslt1 2 4 6 8 9 10

50k kwasa 500kSlt1 2 3 4 5 7 8 10

10k kwasa 100k Slt2 3 2 4 7 9 10
Mebukata yaneme wannan numbern👇
09049197049

Munayin adashi kamar haka👇
Kayan daki set na kujera da gado
Kayan kitchen
Freezer fridge
Injin wanki
Gas
Dasauransu
09049197049

 

Page naku ne

Ummu Minnah
Ummu Annur
Aunty Nurse Zariah
Princess
Maman Ahmed
Mrym
Maman Aslam an Abdul
Mamar Bintou
Ummey Muhammad
Maman Murtalah
Sumayya Auwal
Ummu Lateefah
Mommy Sadiq

Ummin Sadeeq
Ina gaisuwa

Also Download FARRAH Hausa Novel Complete Document By Maman Shuraim

Santana sai safa da Marwa yake kamar matarsa,yace yanzu ba dama a shiga,Nawwar ya watsa masa wata uwar harara ba Shiri yayi mukus,Mami har Salma ta Koro waje,duk suna waje,na danji dama dama tace a turo min su Wise, kunyar nake ji suruka zata kalleni ni gwara su Wise,ciwo yana dawowa nace ni bana son surukata ta ganni,Mami tace ashe kuwa sai in baza ki haihu ba su sun San haihuwa ne,Rabi ni dai sai tattale kafafu nakeyi,na mike daga kwanciyar na sakko kasa nayi goho nace a haka zan haihu irin tamu ta gargajiya,naji wahala nace wallahi ta asibiti zanyi na dawo na kwanta akan gadon ina bude kafa,ban San sanda ma na cire kayan jikina ba ina tattale kafa,kan yaro ya taho yaki fitowa sai ya fito ya koma,likitoci suka zo suka agaza har ya fito,sai kuka inya inya,Su Wise suna ji sai shewa yeeeeeeeeeeee,Nawwar ya harare su yace ai Kwa bari dai aji lafiyarta ko, nan da nan aka gyara Miracle ba kayan komai a jikina wahala tasa na cire,ta hada gumi sharkaf duk,na manta ma da suruka na nan,sai da aka gyarani tsaf aka gyara dakin neat nurse tace Hajiya sai a sa kaya ko,kunya ni Miracle naji Mami an goge jariri an nade shi aka Mika mata,ta mika min zani tace gashi maza ki daura daki za a canja mana sai ki wanke jikinki mu tafi,nan da nan aka canja mana daki,abinka da private komai Kal Kal yana kamshi,Mami tace ruwan zafi fa,na fara wani yarfe hannu Mami ta fita ta Kira Wise da Star suka shigo tace kuje ciki ni kunyata take ji ku tabbar ruwan zafi ta sa,Ai kuwa suka shiga sai kace Yan iska a tsaye ma
Nayi wanka na danyi gashi sama sama nace sai anje gida na fito,bani da karfi sosai,Abaya Wata Maroon me kyau Mami ta bani na Sanya na shirya kaina sosai na kwanta a saman gadon ina huce gajiya,Mami ce ta fito tace Zaku iya shigowa.

Sun Riga me abin shiga ma Nawwar ya tsaya yana kallon ikon Allah yace sai kace Dan su to ku gama ni na shiga kowa yana daukan jiririn Kato da shi yana masa Addua,Inna da Seraline suka iso suma har da abinci lafiyayye a manyan flasks,Star tace kice girki kika tsaya yi,tace wlh shi na tsaya yiwa Me jego harda tea yaji hadi aka zuba min na shanye nan take sabo da yunwa, Mami ganin Nawwar shuru bai shigo ba ta fito masa da jaririn ya karba yana murna kamar zai tashi sama kafin ma ya masa Addua yace Mami ya take? tace abinci ma fa take ci kalau take fes da ita kawai karfi ne bata da shi sosai kuma wannan dama Idan mutum ya haihu yana jin hakan sai a hankali a dawo dai dai,sunyi mata Allurai da magunguna gasu ka siyo mata,ta Mika masa takardar, Mami iceko sun mata wannan abun Wanda ake kwashewa mace jinin dake mararta ni bana so a dade ana wani jini abu yaki ci yaki cinyewa,Mami tace to fitsararre marar ta Ido abinda Kai kasa nurse suka mata ai sun fada mana,dariya Nawwar yayi yace Mami sauki na nema mata fa,kaga yiwa yaro Addua ni,Nawwar ya masa Addua sosai yanda addini ya koyar sannan ya mikawa Mami yace kice su fito dan Allah ni zanga Matata wannan masifa haka duk Auta ne ya jawo da ya Kira su,Sai ga Auta ya dawo da ledojinsa na kayan marmari da nama da su Madara tarkace dai,dama yana kawo Nawwar ya bar asibitin,Nawwar ya kalle shi yace Auta ikon Allah ,Murmushi yayi kadan yace sai Aunty ta haihu zanyi dariya,yace ai kayi Da Autan Mami ta haihu tun yaushe kana can gantali,Auta yace haba ana ganinta? Yace ae mana an canja mata daki ma har taci abinci,Auta yace nayi Da shike nan na zama Daddy ya shiga ciki da Sallama suka Amsa,yace Masha Allah Aunty ya jiki? tana cin abinci tace Alhmdllh Nawaf,ya karbi yaron a Hannun Mami ya masa Addua yace kamar Yaya Nawwar kamar Aunty miracle suka yi dariya,Santana ma ya shigo yaga jariri ya tafi, sai da suka gama rubibinsu Mami tace duk su tafi gida suka fito suka tafi Banda Salma yar anace kamar danta ta karbe shi harda jijjiga shi,tsokanar Rabi tayi tace bari a masa rawa,da sauri na nunata da yatsa ina karkadawa uhm..uhm..uhm wai kar ta sake tayi masa,Auta yace to anyi da Kuma ba Saban ba,Nawwar ne ya shigo suka mike suka fito duka har Mami,ni kuwa na durfafi abinci sai yi nake,ya kalleni kawai yace sannu ya jikin? Nace da sauki na ajiye plate tass na cinye abinci,na bude ledar Auta na dauki yogurt sai da na kusa shanye roba guda,na dakko fruits nan ma naci wannan naci wancan sai da naji na koshi sannan na sha ruwa Faro nace Alhmdllh,sai lokacin na Kalli Nawwar dake tsaye yana kallona,nace zauna mana,ya sake cewa ya jiki nace da sauki lafiya nake,nace Baby local government ta fafe Yasin ta afka ai wani ruftawa tayi Kai naga bala’i,dariya Nawwar yayi, na dafa kafadarsa nace kaiiiiiii haihuwa da wahala yanzu su Wise nake tausayawa zasu dandana kudarsu, Nawwar ya zuba min Ido kawai, ina uban bashi labari na nuna kugu na nace aka rike ni ta nan,aka damki nan,aka tattaro marata aka yamutsa aka yamutsa sai naji kamar kasusuwana sun watse, Subhannallahi sai yanzu nake jin kunyar Mami tsirara nayi a gabanta,dariya Nawwar yayi yace shike nan ai kayan danta ne dan ta gani ba komai ai Larura ce,duk da haka da kunya Allah,itama ai mamanki ce ko? Nace ae mana,Allah yasa an mana hutun school Nawwar yace ai naji dadi nima,ki Kara hutawa zuwa yamma a sallamemu bari na Kira Umma,na Kira Umma ta daga nace Umma na haihu,Umma tace Masha Allah me aka samu? Namiji Umma,tace to Allah ya raya bari gobe su Omaira su taho ko kafin manyan su zo,nace to zan turo musu kudin mota,Umma tace akwai kudi fa,nace ai baza a kwashe naki ba Umma zan tura musu,to Allah yayi Albarka Ina me gidan, nace gashi bari na bashi ta mikawa Nawwar waya,ya karba suka gaisa ta masa Allah ya raya yace Ameen Ameen Umma.

Karanta>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Bacci na kwanta na fara shakar uban bacci tun safe bayan na haihu har 5pm sannan na tashi,Mami tace dama ke muke Jira ki tashi an sallame mu,nace to na mike a hankali ina yatsina fuska,Salma tana wajen ta kalle ni tace rauni kika ji a wajen? Mami tace shegen baki kamar kinci aku,dariya Salma tayi tace Mami yanzu ai kuna so na ko? Mami tace dama muna sonki ai horaki aka yi dauki kayan mu tafi,Nawwar ya dakko flasks da sauran tarkacen Itama Salma ta dauka suka dawo gida abinsu,bangaren Mami a sama aka bawa Rabi daki,Suka shiga na zauna a gefen bed da kyar ina yatsine fuska,Mami tace ai ruwan zafi Zaki shiga gashi Zaki na sosai shine Zaki samu afwa,Wise ta hada min ruwan zafin harda zuba shegun magungunansu na tsumi a ciki,na tafi toilet naga magani a ruwan nace Wise ni yaushe zan koma wajen Nawwar a sake abin nan,Wise tace hehehe sanda Zaki koma ma ku zuba sex wa ya sani,wlh Idan baza ki shiga ba zan Kira Mami sai ya Huce abin haushi ke ba Salma ba bare nace zan Kira Baso,nace zan rama wlh ai kema Zaki haihu so soon,da kyar na shiga ruwan ina zama na Kwalla ihu tare da mikewa,Nawwar yace kinji Mami ta Kone,rabu dasu wanka take fa,na sake zama zan mike Wise ta danne min kafadu kamar zan mutu haka nake kuka sabo da zafi,sai da ya huce sannan na mike,Wise ta wanke min gashina tas da shampoo me kamshi ta barni ciki nayi na sabulu da kaina na shirya kaina na fito daure da towel da karami a kaina ina tsanewa,Nawwar yana gefen gadon a zaune shi kadai,nace Ina Mamin? ta tafi yiwa jariri wanka,ya taso a hankali yace shike nan na zama Gwauro ya rungume ni ta baya,hannu ya dora a kaina yana tsane min gashin, Mami ce ta shugo ta zuba masa harara tace a gaskiya ka dame mu ka tafi mana haka tunda kaga jaririn kaga lafiyarta,yace irin wannan shi yasa ba a son a bar mace ta tafi gidan Iyaye,ya mike ya fice yana cewa mutum da matarsa kawai sabo da ta haihu sai a Hana mutum sukuni,Miracle nace ka kwaso kayan jaririn nan daka siyo a kawo nan,yayi tafiyarsa gida ma gaba daya,wanka yayi ya shirya cikin kananan kayansa hadaddu purple ya kwaso kayan jaririn ya kasa zama a gida shi kadai ya dawo gidan,lokacin anyiwa yaro wanka an shirya shi cikin fararen kaya,nima na saka doguwar rigar material readymade me siririn hannu na shafa turaruka masu tsada ni da yaron sai kamshi muke me dadin shaka,dakin Salma tazo ta gyara ta dame bed din ta kwashe tarkacen fitarwa ta fitar dasu komai neat daki yana kamshi,Auta ne ya shigo ya sha gayu zai fita yace Hajiya Aunty me jariri inyeee ba Saban ba anyi da mun shiga uku Kuma, Yaya Nawwar ya kenan naga karyar maita yanzu gwara ya karo aure kawai,na harare shi ina dariya nace ya karo mana Idan ya Isa,ai sai ka auro masa wata mu gani dan iya Kai da ka kasa komai wlh ka bani kunya Auta Kai da muke ta Jira yarinyar nan sarkin giringidishi kayi mana maganinta ka kasa duk son aurenka,Auta yace sannu sannu dai Aunty a sannu sannu sai Kun kaita asibiti an mata dinki,Allah ya shiryeka Auta Dan Iska a baki,dariya yayi yana kallon Kansa a mudubi, Salma ce ta dawo cikin yar fitted gown dinta me dogon hannu itama an sheka kyau harda kwalliya,tazo ta ture Auta daga jikin mudubin matsa Nima na Kalli kaina,Auta ya kalleta yace to baki kyau ba,a boye Kuma yana kare mata kallo yana yiwa Rabi signa da Ido yana nuna duwawun Cele da hannu yace harka iya harka,Rabi ta sheke da dariyar iskancin Auta,Salma ana ta faman gyara kwalliya bata San me suke ba,Wise ce ta shigo taga Abinda Auta yake tayi dariya tace yau na shiga uku,Salma ce ta juyo tace me ya faru Aunty tace ba komai,Auta fita zaiyi yace nikam sai dare,Salma da sauri tace Ina zaka je Kuma,yawo ya furta,ka tafi dani,yace a’a ni Ina ni Ina ke ai ke sai Baso ki zauna ki karbi Yan barkar jariri ya bude kofa ya fice,Salma ta biyo shi da gudu tabi steps da uban gudu,da Mami suka ci Karo,tace ke Kam Salma bakya rabo da gudu Ina Zaki haka,tana haki tace Abu na manta ta fice,Auta har yayi nisa ta cin masa tana hakki tace wallahi Idan ..Idan ..ka kula wata bazan yafe ba,ta juya ta dawo kafin Auta ya juyo har tayi nisa,baki ya tabe ya wuce ya shiga mota abinsa.

Karanta>>> Furar Kashi Chapter 1 By Billyn Abdul

Nawwar ne ya shigo ya iske Salma da Wise a dakin suna hira,Salma tace sannu da zuwa Yaya ya farincikin an Baby,dariya ta basu ta mike ta fice,itama Wise ta fito,Salma wajen Mami ta dawo tace ki kawo jaririn a Kai shi ga Babansa can Yazo,Mami tayi dariya tace sai yace a Kai masa abinsa? tace ae yace son ganinsa yake bai karewa dansa kallo ba,Mami tace sannu zubaida wai yau kinwa Auta girki ma kuwa? tace banyi ba muna ta cuku cikun haihuwa,Mami tace to tafi kitchen ki Dora girki ba iya na Auta ba kowa da kowa,Hamra gobe zata dawo daga gidan su Aunty Rukayya a Katsina ta dinga tayaki aikin,tace to Mami ta wuce,Mami ta shiga da jariri ta iske Nawwar a zaune nace ai har naji sauki da nayi gashin nan,wani karfi naji,Mami tazo ta Miko min jaririn na karba tace bashi nono ya sha yunwa yake ji,Miracle na wani jawo bargo na lulluba wai a ciki zata bashi kar a kalle mata Nono,Mami tace a haka ake bawa jaririn nono a kwance cikin bargo baza ki fito ba,na mike zaune na jawo mayafi me kauri na lubbe nononta da jaririn,Mami tace hmm ta juya ta fita,tana fita nace sa key a kofar Baby, Nawwar ya Saka key kuwa ta bude nononta da jaririn.

Nawwar ya kalleni nace zafi zafi wlh in yana ja,yace ai baki Saba ba ne shi yasa,Nawwar yana ta kallon dansa yace wannan yaron Allah me Iko yanzu da nine nake sha da yanzu kin zauce ko? nayi dariya nace ae ma Idan Dan uban ne ba ajin komai amma da uban ya sa baki wayyo sai sweet,Nawwar yace hukuncin Allah kenan to na bashi aro ya zanyi,aka juya jariri daya barin nan ma ya sha nace ya koshi kai gashi har yayi bacci.

Sai da na gama gyarawa ya bude kofar su Sultana Amare anzo,Jamcy ma a ranar Santana ya kawota,Mandula da Yar zabil duk laulayi suke sunzo suma da mazajensu sunga jariri,Star kuwa Malam ya kawota da dare again ta Kai masa jariri ya masa Addua yace saura namu,Star tace kwana nawa ne wai star da ya wohoho ta karbi jaririn tana masa Addua Karka sake kayo Halin mamanka na fada maka Ameen,nace amma baki da mutunci ni halin tsiya ne da ni? Masifar wai take nufi ayi mata afwa cewar Malam Abhulkair harda fada da kalar tausayi.

Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document

Wise da Salma sune Yan zaman barka suna makale, washe gari su Omaira suka dira a gidan,Omaira, Raheema da Rahma,Salma ba zaman lafiya ganin Yan mata sunzo suma Kuma kyawawa, gashi Auta nasu ne dama,Auta suke ta nema kawai,ni kuwa Ina satar kallon Salma yanda hankalinta ya tashi,nace Omaira kuje kuyi aiki fa ana baki wa zai dinga abinci duk da akwai masu aiki dole kuyi min,Omaira tace to suka fita,suna fita nace Salma tace Na’am nace ya kamata ki fara gyaran jiki,murmushi tayi tace wa zan wa? Nace in Zaki fara ma ki fara kinga dai ke baki da Uwa a gaban Namiji kika girma, ni Ina da su ba siya zakiyi ba zan baki ana Shan na Infection sabo da tsaro da na niima da sauransu,Salma tace Idan da Zaki zan sha ni bana son magani,tsaki nayi nace Wise ce fa zata hada Miki komai ki dinga zuwa wajenta zata baki munyi zancen,Salma tace to na gode.

Kamar muryar Auta taji a kasa da sauri ta fita,nayi dariya nace wannan yarinya ta fada son Auta bata sani ba,fitowa tayi taga shine suke ta labari da su Omaira suna dariya,kishi me tsanani ya kama Salma ta sakko kasa,Auta yana kallonta sai da gabansa ya fadi shi Kam har tsoron Salma yake ta ganshi da mata, Salma cikinsu ta shiga aka ci gaba da hirar da ita tana hararar Auta a boye, tashi tayi ta rike Hannun Auta tace muje,Omaira tace Auta ango gaskiya Amarya kina ji da Autan Mami,Salma tace ba dole ba aje ayi min awon gaba da shi,suka yi dariya su Basu San ma kishi take ba,ta ja Auta cikin bedroom dinsa tace zauna ya zauna tace me zaka ci? Auta shi mamaki ma yake matar da watarana Idan zata bashi abincin ma sai da masifa,yace yau na koshi ya furta

Kallonsa tayi da sauri tace me? na koshi yau ya sake fada,Salma tace ai kasan Ina maka girki ko shine kaje ka fita Kaci a waje wa ya sani ma ko wasu Yan matan ka Kai joint to sai Kaci ko cikinka zai fashe Allah ta juya ta fice,Auta ya zaro wayarsa yana dannawa yana murmushi,tana fitowa tace Omaira an kusa bikinki ne? Omaira tace a’a ni dai Ina da Wanda nake so amma ba lallai a barshi ya aureni ba iyayensa sun ce yayi yarinta Kuma fa wallahi ya ma fi Auta shekaru,Salma tace ke karki yarda duk yanda za ayi ki auri Wanda kike so,ke aure akwai dadi ni dake ne wannan zancen sabo da ni kin min a rayuwa jininmu yazo Daya,Omaira tace Nima Ina sonki,Salma tace ke tun wuri kiyi aure kiji dadin da ake ji kema,soyayya akwai dadi ki dafa abinda kike so kici kiyi iko da mulki a gidanku yarinya Malam sai ma dare yayi,Omaira itama yarinya ce bata gane Salma wayo take mata ba wai kar ta so Autanta tayi aurenta kawai,Omaira harda mikawa Salma hannu suka tafa tace ke Allah kice akwai harka? Salma tace ta gaske karki bari kanki ya kulle,tace kin ganni sakata nake na Wala,Omaira tace shegiyar gari ai gashi nan kuwa kin kwace Auta ke kinga irin kallon da yake Miki nace jar Uba kina fama,Salma tace ai missing dina yake shi yasa kwana daya baiji Industry ba,Omaira itama harda washe baki tace ke karki sake a kwace Miki shi ki tarairayi abinki,Salma ana kasa da muryar irin munafuncin nan low down your voice abeg surukata tana nan,Omaira tace tsiyar zama da suruka waje daya kenan,tace Dan ma mun samu ta kirki ai Mami ta waye tsakaninmu da ita sai Addua,kinga bari na Kai masa abinci,Omaira tace iceko kin hada juice? tace tuni ma ai no kidding,Salma yau a abinda ma ta zubawa Auta abincin na daban ne ya sha kyau,Omaira tace gantsare Baby chest ya yo waje baya ma out,kin san kan gari dole muyi kawance,su Rahma ne suka shigo Omaira tace Kai ku fita zancen manyane muke Yara sai shegen son zance ana zance kuna kallon bakin mutane,Raheemah tace dama munyi waya da Umma tace Cele ta dawo a fada muku zata zo ma suna,Omaira tayi murna tace tab ni wallahi tsoronta nake ji tunda ta fasa min Kai fada da ita baya mutuwa tana zuwa na shiga uku,da su Aunty Bilkisu zasu zo ai bata Isa ba,Celen lallai to Cele ba Wanda ta dagawa kafa,Rahma tace Kuma Umma tace tana nan da bala’inta inda kisan bata zaga dakin Allah ba,Omaira tace Ina ga shedan ta jefa ya rama suka yi dariya tace muje wajen Aunty Rabi,tace cab mijinta ya manne da shi ake karbar barka wannan bala’i wallahi zai mata wani cikin da wuri, Mami ma tayi fadan ta gaji,to muje muyi kallon tv.

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Salma ce ta shiga dakin Auta dauke da abinci sai da ya bi flasks din da kallo ya sha mamaki,ta zuba a plate tace to zan baka a bakin? Auta harda shagwaba nace na koshi fa,itama fuska ta shagwabe ta kwaikwaye shi tace nifa wlh sai ka ci harda shure Shure,Auta bai san sanda ya fashe da dariya ba,Mami ce tayi knocking taji suna ta faman dariya ta juya ma bata shugo ba Kuma basu Bude ba sai driver ta aika ya siyowa Rabi wani nama me Dadi.

Auta yace bani dai naci kadan ta dire gwiwoyinta a kasa yana bakin bed tana bashi a baki yana ci,Baso ne ya dinga Kiran Salma ta Kalli wayar my love bata canja suna ba,Auta ya kalla ya sake lekawa cokalin da zata bashi abinci ya bige yayi fatali da shi da abincin gaba daya tayi watsa watsa a dakin ya mike ya fice,Wayar Salma tana ta ringing ta dauki wayar a fusace ta danna wajen kashewa da karfi tana jijjiga wayar kamar zata fasa ta tace Dalla Malam Daina Kirana ta ja tsaki ta jefa wayar a kan gado ta kwantar da kanta a saman bed ta fashe da kuka.
Mami suna Palo da baki Auta ya fito fuuuuuu kamar zai tashi sama ya fice,Mami ta kalle shi kawai,da Nawwar suka hadu a hanya ya wuce shi rai a bace,Nawwar hannunsa ya rike ya juyo da sauri,yace Auta lafiya ne wai? Auta kamar zaiyi kuka yace wannan yarinyar ce Yaya can you imagine tana da aurena tana sawa wani my love a wayarta mahaukaciyar Ina ce ita,Nawwar yace Baso ne fa,Bason banza Bason wofi ni wlh inda kasan mutuwata haka na tsani Baso,Nawwar yayi dariya yace Soyayya ta kama Auta fa, Auta in love,Auta yace Allah ya kiyaye na so wannan yarinyar ko zan fara sonta sai na roki Allah ya yaye min wannan wacce irin jarfa ce, Nawwar yace calm down su fa mata ba a musu haka ba da fada ake samun soyayyar mace ba Auta,wannan Kai ka dakkowa kanka tunda kasan tana son wani,wlh tayi kokari ma yarinyar nan ka duba horon da aka mata ko Yan aikin gidan nan basu aiki haka,ta tura gate ta karfi ta zama me gadi,aka bata duk wani aiki na gidan nan,aka canja mata abubuwa da yawa na wahala Idan wata fitsararriyarce zata yi wannan Kuma tasan bata sonka,Amma bata taba Raina wani naka ba ko Abu zata maka sai dai Kai da ita,Ka duba yanda bata gajiya tana girmama iyayenka da duk Wanda ya shafeka wallahi lokacin da na dakko miracle Idan itace baza tayi ba duk da tana girmama mutane amma rashin kunya ma ta Isa a kyaleta,yanzu bata yi kokari ba,sabo da iskanci abinci ma a baki ake sawa ta baka tana da kunya ba a nan ta taso ba haka ta daure take maka har kace sai ana shafa maka gashi ,Sabo da kawai kaga ta sawa Baso My love,Iyaye ma suna sawa yayansu my love,lovely Mum,wayata fa Sweetheart na sawa Mami, Auta yace ai Baso ba muharraminta bane kuma kasan sonshi take ta ya zaka ce hankalina ya kwanta,Ka fara sonta Auta itama naga Alama tama fika kamuwa,mace ce Mai rauni sai anyi hakuri shine auren ai,Yanzu ka koma ko baza ka kulata ba kawai ka koma kayi hakuri,haba Autan Mami duk mun zaci I yanzu ta samu ciki ma,me kakeyi ne wai baza kaji dadin ba,tuntuni ka dame mu aure aure kace ka balaga tuni ko ba haka ka fada mana ni da Baffa ba? Auta yace hakane ai Kuma na balagan ko ban balaga ba Kalli gemuna ya kusa fin naka ma,Nawwar yayi dariya yace to aini banga balagar ba Auta kaje ka bata Service,Auta yace Yaya wlh har tsoron yarinyar nake ji fa,ba dama nayi sukuni,Nawwar ya dinga sheka dariya yace kwailar? Yace ni naga sharrin kwaila wallahi sunfi manyan gyara Namiji, kana gani Yaya ya bigi kirjinsa ni Auta Autan Mami gyarani take tsaf,bana jin kunya da fargabar kowa amma ni yanzu Yaya bana so mace ta rabeni kar ta gani,a school ta sa min Ido ta hanani sakewa sai sawa take Ina batawa da Yan mata duk sai sharara Mari nake kawai a school fas fas, yanzu duk Mata sun kiyayeni Allah Yaya.

Karanta>>>> Sanadin Labarinah Chapter 2 By Hafsat Rano

Nawwar ya gyara kujera ya zauna yana tuntsira dariya,Auta yace hmmm shima ya zauna yana gyara wandonsa da yake ass down da shi yana zazzagowa,ya daki kafadar Nawwar yace Yaya ka gane ko? Auta ya shafa gemunsa da sajensa yace kasan Glory ko kaga yanda muke good time da ita da tausayi ya karasa maganar a sanyaye yace wallahi Yaya rannan na gwaura mata Mari itama,Chima nan tawa yarinyar nan akwai kirki amma ya sake sanyaya maganarsa yace amma itama na fesa mata Mari wlh hagu da dama,Yaya sai da ka fada min gaskiya naki ji ka Cece ni,Nawwar yayi dariya kamar cikinsa zai ciwo ya buga kafa sosai yana sheka dariya,Baffa ne ya dawo daga ganin Jaririn ya wuce su suna hira suka masa sannu ya wuce,Nawwar yace dama maganin irinku kenan Babu rainin da baka yiwa mata ba,kanwar Rabi ma cewa kayi zasu mallakeka yanda aka min,Auta yace ai ni yanzu so nake ma wannan ta mallakenin amma yar jakar Uba sai kayan haushi zan mata baki Yaya,Nawwar yayi dariya kamar me yace Autan shagali Allah yayiwa Salma albarka Karka yi mata baki kaji sai ta sake lalacewa,Auta yace saura kadan kuwa.

yanzu Yaya kune Manyan,au yanzu ka yarda? Yace ah na yarda kuje da girmanku Allah ya kara girma,Salma ta gama kukanta ta wanke fuskarta ta zo ta share dakin ta goge ta gyara komai ta dauke kwanikan ta kwashe Rabin abincin ta kulle a Leda ta jefa a shara tace Allah na tuba nayi barna,Mami ce shigo tace wai fada kuka yi da Autan? Salma ta kirkiro fara’a tace a’a Mami akan nace sai ya ci abincin da yawa shine yayi zuciya wai shi ya koshi kinga Dan Wanda ya ci ta Bude flask,Mami ta leka tace ba sai ki kyale shi ba, ki Daina biye masa,Salma zuciyarta ta karye ta fashe da kuka,Mami tace to kiyi hakuri Salma aure sai hakuri haka kowa yake hakuri da nasa,Salma tana kuka tace Mami ya Auta zai dinga min haka sabo da Allah,Mami tace ke karki sake ki masa kuka ba a yiwa Namiji kuka zai Raina ki Idan ya gani shike nan zai samu lagonki karma ki bari ya San kinyi kuka wanke fuskarki,Salma da sauri tawanke fuskarta a sink,tace yayi? Mami tace ae je ki shafa powder bari naje wajensa,Salma tace karki masa zancen Dan Allah zai ce na fada Miki kinga bazai ji Dadi ba zai ce Ina hada shi da iyayensa,irin dai Dan nasiha Zaki masa a Dan wayence kin gane ai,Mami tayi dariya sosai wai ita Salma zata koyawa duniya,tace ashe dai Salma da hankalinki wallahi kina da hankali kin Kuma birgeni,tayi dariya tace ai sai ma nan gaba sai nafi kowa hankali a gidan nan zaku gani Mami,Mami tace oh jama’a Ina da surukai a gidan nan baga Rabi ba ga Salma,ta fice,tana fita Salma ta hau tsalle tana furta yes yes.
To yau Salma za a fara kwana a dakin Auta sabo da Baso yace,Mami bata sani ba ma,bata San ance ta dinga taya Auta kwana ba,sai da ta bari kowa ya kwanta tayi Shirin baccinta cikin kayan bacci ta lallaba Sadaf Sadaf kamar zata dauki kayan wani tana zuwa kofar Auta ta Murda ta fada ciki da gudu,Auta yana cikin bargo tana fushi wai an mata dole ta janye bargon da Auta ya lulluba ta shimfida a kasa ta ja pillow daya tayi shimfida ta kwanta abinta,Auta yana jinta bai ko kulata ba,magana ta shiga yi tace shike nan mutum sai fushi,ba dama ayi abu sai fushi ai ba haka ake rayuwar duniya ba.
Auta yana kwance kamar bacci yake yace Aljanna dai Idan naga dama kafa zansa na take ko na tsinewa mutum, Kuma sai dai kiyi ta kwana a kasa baki Isa kin hau min gado na ba,tace ai Nima Ina da gadon ganin damata ce tasa nazo,suna ta carcar baki har bacci ya kwashe su.

Download>>> Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

Cele suna sauka a airport ta Kira Ahsan ta sanar masa sun sauka lafiya yayi murna,taxi suka shiga da kayansu gaba daya duk sun zo,Kaka yace to jaraba mun dawo tsiya sai kwazazzabo titin ma baza kaji luwai ba haba,kaka ya Kalli Kasuwa za a wuce yace Cele ji wai nan sababbin kaya ne ake siyarwa,Cele tace ji wata Vest a rataye kamar gwanjo,Kaka yace ai nan Sabuwa ce Kuma? tace ae fa wai gashi nan ma rubibinta akeyi,Kaka yayi dariya yace Kalli mutane Dan Allah duk sunyi baki sai jijiyoyi kamar masu cutar yunwa,ai nan a koshe suke Kaka baka gani har yanga suke ba ,Kaka ya Kalli wata mace yace Jita yar kutun Uwa to ba Madara tana tafiya kamar bata da jini,Cele tace yo ba protein,haka suka Isa gida,Cele ba Sanya dama akwai Almajirin da suka bari a gidan gashi da tsafta duk yana gyara gidan babba ne,Cele ta sake gyara gidan tayi wanka tace Kaka Allah toilet dinmu kamar ta akuyoyi,kaka Yace da kyar na iya fitsari, muje wajen Umma na matsu na gansu cewar cele,suka fice suka tafi tsohon gidan suka je,Cele taga Abba a kofar gida a Sallaya yayi tagumi,Cele taji tausayinsa abinka da mahaifi,tace Abba abin mamaki sai yayi murmushi yace Rufaida saukar yaushe tace Abba dazu dazu tace Abba kalleni me ka gani? Yace kin hadu ga kakan naki ma yayi Jajir da shi yayi kiba,Kaka ya Mika masa hannu suka gaisa yace Zauna zauna Haladu,Kaka yana mamaki Shima mutumin da baya kulashi yake gaba da shi,Cele tace Abba Umma fa? Abba da tausayi yace ai sun bar gidan nan uwarku da Yan uwanku sun ware ni kamar bani na haife su ba,Rabi aka gani yar uwarki wacce aka haifeku tare,Cele tace Allah amma naji Dadi dama itace Rabin kasan Allah Abba wata ta Dade tana tareni tana ce min Rabi to kasan ni ba mutunci naci ubanta amma naji dadi, na sake ganinta a Makkah kuwa matar naki kulata,amma da Alama a kauye ta girma naji Rabi gatsal Ina laifin Rabiat,Abba Ina da aure fa yanzu labarin sai an zauna,Abba yace gaskiya Cele kin Kara hankali,Cele tace Abba ai aure nayi shi yasa dole a Dan nutsu albarkar aure ce,Abba sai soyayya nake ta yi,amma ya za ayi su wareka Abba gaskiya Basu kyauta ba,Amma laifinka ne Kai ka jawo,badan zuciyar Musulunci da Kuma Uba ubane fa to Abba wallahi da baza mu kulaka ba,kaifinmu ne da muka zo a mata? ita Uwa da tazo a mace wani ne yace tazo a mace ba Allah ba,Abba kuka ya saki yace shike nan ni ba inda zanje naji sanyi kowa sai ta fada min abinda taga dama,Cele tace Abba bafa zuwa nayi ka min kuka ba gaisheka nazo bani kwatancen Umma,Yace bazan fada ba kema tafiya zakiyi wajenta ki barni,Cele tace Abba kasan duk da Ina maka wasu abun na bacin rai amma kasan Kai ka jawo Kuma ina da tausayi,Cele ta karkace ta zaro kudi sun Kai dubu ashirin tace ungo Kaci albarkacin macen da baka so,Abba ya karba yace kamar kin san banci komai ba tun safe dama uwarku itace take San mana abincin Idan Kun kawo mata Kuma Rabi ta auri me kudi,Cele tace me kudi ne? Yace na gagara ma Cele saurayi matashi kamar bature idan kika Ganshi ga hankali,Rabi ma ba sauki da masifa tayi mana Sallama,Cele tayi dariya tace wooo woo jinina a lafiya dai Rabi ai dole naje gidanta,Abba yace ta haihu ma yau kwana biyu,Cele tace Masha Allah da ni za aci suna,Abba yace Dan Allah duk da ta rigaki Shan iskar duniya ki mata fada ta dinga kula da Mahaifinta,Cele tace zata ci ubanta zanje tana min rashin kunya zan gurje bakinta,ta girmeki Cele da kusan awa Daya,Cele tace yo aini ko sa’ar Umma ce bana tsoro,Bari naga Uwa,Abba yace Allah sarki yau tun safe kunu ne a ruwan cikinta sabo da yunwa,Cele ta shiga tace kina inane ke Uwa fito ko yunwa ta Miki Illa ne? Uwa ta fito tana washe baki tace Cele,Cele tace kalleki abin in masge duk kece kika ja mana bala’i baki iya tarbiyya ba da ace kinwa danki tarbiyya yasan addini ai bazai yi haka ba, ta zaro dubu biyar tace ungo sabo da Allah,Uwa tana murna tace na gode dama tun safe kunu na sha,tace kyaji da shi ni kinga tafiyata Uwa kin shiga uku da gori wlh har ki mutu ko kina kabari Ina binki da gori,akan Zaki sace ni sai Umma ce ta bawa Kaka ni da yanzu Ina wani kauyen,Uwa kiji tsoron Allah tam,ta juya ta tafi,Abba yaji dadin kudi sai yayiwa Cele kwatancen gidan suka tafi da kaka,Umma sai jin Cele tayi tana kwalawa Umma Kira Umma fito yarki ta dawo na ragargaji shedan, Umma ta fito suka rungume tace Alhmdllh kin dawo lafiya Ina ta Miki Addua Allah ya tsare min ke,Cele tace kaji Uwa ta gari,Umma ban mu tafa, Umma ta harareta tace Ina su Omaira? Suna can kudu wajen yar uwarki Rabi,Naje wajen Abba ya fada min,Umma haka Abba yayi laushi? Cele ta hau bawa Umma labari har komai da ya faru a Makkah,Umma tace Allah ya rufa mana asiri baki haihu ba, wai da munji kunya,Umma ma ta bawa Cele labarin Rabi kaf,tace Allah sarki ashe Rabi har dandi aka yi,Umma tace bafa tayi ba Allah ya amsa adduata ya tsare min Yata dama Ina ta mata Addua,Cele tace gaskiya ta sha wahala daga baya dole muje gidan Dagaci ko yar magana ce in jajjefar masa duk da ya tuba wallahi sai na fadi baka,Kefa halina dake kenan,ki dai shirya zuwa suna sannan ki fadawa Mijinki Idan ya amince tace wayyo Umma ai wani Alhaji Salmanu ne zai amince ,Umma sai murna take Cele tayi aure,kaka ya shigo Shima yayiwa Umma murna,Umma ta dinga yiwa Kaka godiyar rike Amana.

Download>>> Mijin Malama Complete Document

Duk Cele ta zaga Yan uwa da abokan arzuka ta raba tsaraba sosai.
Masu zuwa suna Yan uwan Rabi sunyi Shiri ciki harda Cele da su Bilkisu,za a tafi,ana gobe suna suka taho gaba dayansu banda Umma.
Salma tayi Shirin school Mami tace nawa kika kudin littafin? Salma tace Haushin kare,Mene haushin kare Kuma? dariya tayi tace Mami wan wan Ina nufin one one dubu Daya da dari Daya,Mami tayi murmushi ta girgiza Kai tace a wajen Baso kika koya wannan abin sai Yan Daba.
Ba Wanda yasan za a zo da Cele har ni Miracle sun boye min wai surprise za a mana,sun cewa ma su Raheemah da suka sani sunce Cele ta fasa zuwa,naji haushi a raina nace lallai bata da mutunci sai naci uban yarinya.

Click Here To Read Book 2 Page 71-75

Back to top button