Mijin Marigayiya Page 41 Hausa Novel
Yana shiga parlor dinta ya kai hankalinsa kan dining table, yanda ya ga wajen a jere da kwanuka ya tabbatar abincin ne ta dafa ta ajiye masa. To me yasa tayi hakan? Ya karasa kan tanle din ya bude kwanukan ya ga abinda ta dafa, sannan ya taba flask din ruwan zafi ya jishi a cike; tabbas ya san shayi ta dafa masa. Ya gyada kai ya juya ya nufi dakinta.Duk da ita ba mace ce mai son mu’amala ta turaren wuta da humra ba amma dai tana son kamshi, tana da hadaddun turarkanta na jiki da nakaya wadanda idan dai ta zauna a waje sai ka ji kamshinsu. Yana tura kofar dakin nata kamshin turarenta yayiwa hancinsa maraba. Fitilar dakin a kashtake sai dai dim-light wadda take ajiye a kan durowar gefen gado itace a kunne; ga alama bacci ne ya kwasheta ba tare da ta kashe fitilar ba. Ya karasa kan gadon inda take kwance, ya leka fuskarta; bacci takeyi hankalinta a kwance gashi yanayin baccin ya yiwa fuskarta kyau. Kamar ya kyaleta sai kuma ya canza tunani, ya zauna a hankali a gefen gadon daidai inda kafafunta suke, ya daga abinda ta rufa dashi ya sosa mata tafin kafa a hankali. Ta janye kafarta da sauri sannan ta bude ido a hankali hankalinta gaba daya yana kan Hammad wanda yake kwance a cikin gadonsa na baby a gefen gadon nata.Yayi dariya a daidai lokacin da ta ganshi, ya lakace mata hanci yana cewa ‘Yanzu mutum daya ne a rayuwarki wato Hammad ko? Ke na taba amma ba abinda ya tabaki kike nema ba yaronki kike nema kada a taba miki shi.’Ta yi murmushi ta mutssike idonta tana gyara zama sannan tace ‘To ina laifi, nice gatansa kaga kuwa dole na kula da amanar Allah.’‘Hakane. To a taso a bani abincina yunwa nake ji sosai.’Ta zubo kafafunta daga kan gadon ta mike tana cewa ‘Bari na wanko baki.’Ta wuce ta gabanshi ta nufi bandaki.Ya bi bayanta da kallo yana yaba yanda jego ya karbeta. Ya dade bai ganta a haka sanye da rigar bacci kamar wanna ta jikinta ba sai yau kuma tayi matukar burgeshi. Yana nan zaune yana lissafi ta fito daga bandakin suka fito parlor din.Sai daya zauna a table din sannan ta zuba masa abincin ta ajiye a gabansa, ta koma ta hada masa shayi kamar yanda yake so shima ta ajiye masa ta koma ta zauna a kujerar kusa da shi.Tun kafin ta zauna ya fara cin abincin saboda da gaske yunwar yake ji; bayan ya cinye lomar bakinsa ya dubeta yace ‘Ke kin ci abincin ne?’Tace ‘Um, mun ci ni da yara mun koshi tun dazu.’Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yana cin abincinsa yace ‘Wai me yasa baki saka abincin a parlor na ba kika kawoshi nan?’Ba tare da wata damuwa ba tace ‘Ba komai, kawai dai nan din ya fi min kusa da kitchen saboda saukin aiki ko?’‘Um hakane. Ki dinga sakawa a parlor din kawai kin ji can din zai fi yanda duk wanda yake son yaci zai iya diba.’‘Ok, next time in sha Allah.’Suka sake yin shiru na dan lokaci, jimawa kadan ya ajiye cokalinsa ya fara shan shayin. Bayan ya kurba ya ajiye kofin sannan yace ‘Kuma na ga baki gyara mana dakin ba, yanzu zaki gyara kenan ko a haka kike so mu kwana?’Ta kalleshi da mamaki tana dan zare ido ‘Duk gyaran da nayi kuwa? Ko dai baka kalli dakin ba? Koda yake baka kunna fitila shi yasa ba zaka ga dakin sosai ba amma na gyara sosai fa.’Ya kula da tana maganar hankalinta yana kan kofar dakinta kamar dai ta zata dakinta yake nufi bata gyara ba, yace ‘Ba fa dakinki nake nufi ba, dakina nake nufi tunda ai a nan zamu kwana.’‘Oh,..’ sai kuma ta dan sunkuyar da kai kamar dai ta kasa fadin abinda take son fada ne. ya kurbi shayi ya bita da kallo yana jira ta karasa fadin abinda ta fara fada.‘Gaskiya mu kwana a dakina, in ya so duk ranar kwana kai sai ka dinga zuwa dakina muna kwana.’Da mamaki yake kallonta yana dariyar yake ‘Khadeeja a ina kika taba jin miji ya bi matarsa dakinta kawai saboda su biyu ne? shike nan yanzu duk wacce take da kwana nine zan je dakinta kenan?’Ta dan bata rai ‘Nifa ba haka nace ba, ita idan tana so ta dinga zuwa dakinka bani da matsala da hakan amma ni dai sai ka dinga zuwa dakina.’Dariya ma maganar tata taso ta bashi; tunda yake bai taba jin inda maigida yake bin dakin matansa ba sai dai a inda bashi da dakin saboda kankantar gidan ko kuma agidan haya. Amma ya za ayi yana da gida kamar wannan ga dakinsa da parlor dinsa amma ace shine zai dinga bin mace dakinta? Allah ma dai yasa Khadeeja wasa kawai takeyi.‘Tunda kike don Allah kin taba jin inda aka ce maigida kamar wannan yana bin matansa daki saboda kwana madadin su suje dakinsa?’ Ya tambayeta yana nuna gidan, sannan ya cigaba ‘Kuma ma a wanne karatun aka biya miki haka bayan ga yanda kika taso kika ga ana yi?’Ta kalleshi ta marairaice da fuska tana cewa ‘Don Allah ka bari mana, na ga dakin nawa ma duk gidanka ne ai meye don ka kwana a ciki. Itama Najan idan tana bukatar hakan ba sai kaje dakinta ka kwana ba?’‘Oh, nine ma zan dinga binku ina kai muku kwanan kenan?’‘To meye a ciki, abu ne fa wanda ya zo a tarihi ma.’Ya dan zaro ido yana kallonta ‘Wanne tarihin Khadeeja? In ce ko dai tarihin tsumburbura ne?’Ta kula dai so yake ya raina mata hankali, kuma idan bata yi da gaske ba so yake ta dinga zuwa dakinsa kwana. ita kuma gaskiya bata jin zata iya kwanciya gadon da ya kwanta da wata matar ko da kuwa ba Naja din bace. Gara kawai ya dinga zuwa dakinta. Ta kara bata fuska tace ‘To a islamiyya dai tunda ake buya mana sirah sai dai ace Annabi SAW ya je dakin Aisha, ko yaje dakin Hafsa da sauransu, duk bayanan da aka yi mana sun nuna shi yake zuwa dakin kowacce. Kuma tunda dai auren nan shi ake kwaikwayo SAW ai ba zai zama matsala ba idan an kwaikwayi wannan din ma.’Bude baki yayi kawai yana kallonta; ya rasa yanda aka yi Khadeeja take lale shi haka har take samun damar gaya masa duk maganar da ta ga dama. Ya jijjiga kai yace ‘To idan nace ba zan zo ba fa sai dai ke ki zo dakin nawa?’Tayi murmushinta wanda yake kara bashi mamaki; kana cikin magana da ita fuska murtuke sai kuma ta koma murmushi har kaga kamar da zuciyarta take murmushin, haka ma kuma idan tana walwala lokaci guda zata sha kunu ka zata kamar bata taba murmushi ba.Muryarta ce ta katse masa tunanin tana cewa ‘Na san ma ba zaka ce hakan ba, kai da gidanka. Abinda ko a parlor ka kwana babu wanda zai nuna maka yatsa balle don ka kwana a dakin matarka?’Binta kawai yake da kallo yana jijjiga kai, yace ‘Toh tsarani Khadeeja.’Tayi dariya tana mikewa tsaye tana cewa ‘To ina laifi, yaushe rabon da a tsaraka.’Kasa magana yayi kawai ya dinga binta da kallo har ta gama kwashe kwanukan. Bukatar ta yakeyi saboda shi kansa ya san yayi kewarta, don haka ma baya son yaja rigima a wannan daren da yake son ya huce gajiyarsa. Gashi sai kaiwa da kawowa takeyi tana kwashe kwanuka tana juya jikinta kamar da gayya, ya ma rasa me zai ce mata.Bayan ta gama kwashe kwanukan ta dafa kafadarsa tace ‘Sai ka shigo.’Bata ko saurari amsarshi ba wuce dakinta ta barshi a nan.Sai yau ya tabbatar Khadeeja ta raina shi; tunda yake bai taba ganin matar da idan tayi niyyar abu sai tayi shi ba ko da tsiya ko da tsiya-tsiya sai Khadeeja. Anya kuwa ba wani abu Khadeeja tayi masa ba; idan taga dama ta gwada masa taurin kai da fitan idan kuma taga dama ta mayar da shi kamar wabi sakarai tayi masa wayo? Amma dai gaskiya ba zai juri binta dakinta ba dole ta hakura tayi yanda aka saba wato duk mai kwana ta bi miji dakinsa.Babu yanda ya iya da yake shine yake da bukatarta dole ya tashi ya bita dakinta; kafin yaje ma bacci ya riga ya kwasheta. Don haka sai da ya tasheta ta sake lallabata sannan ya sami biyan bukatarsa.………..
