NA
AISHA ALIYU GARKUWA
Cikin tsananin tashin hankali da ruɗani ya iso garesu.
Tare dasa hannunsa ya jawota jikinsa yana mai cewa.
“innalillahi wa innailaihi raji’un Janna Meya sameki?”.
Karkarwa jikinta yakeyi kamar zata zube ƙasa, kana ga yunƙurin yaƙi tsayawa, wata iriyar fitinenneyar zuface mai ƙarfi ta keto mata.
Har yanzu kakarin takeyi amman aman yaƙi zuwa.
Da sauri ya ruggume ta a jikinsa, bayanta ya fara shafawa tare da cewa.
“Yah Salam Janna meke damunki gaya min”.
Narkewa tayi a jikinsa dan gaba ɗaya ƙarfinta ya tafi ji takeyi kamar zata faɗi.
Ramadan ne ya ja musu kujera tare da cewa.
“Hamma zaunar da ita”.
Cikin tarin damuwa yace.
“Ramadan zata faɗi kaga bafa yadda takeyi, Please ka duba min ita, Abba zo kaga yadda takeyi fa innalillahi wa innailaihi raji’un Jannaaaaaaaaaa”.
Yayi mgnar cikin raunatacciya kuma gigitacciyar Muryar da tasa Abba zuwa da sauri.
Gaba ɗaya ya gigice ita kuwa har yanzu yunƙuri da kakarin aman takeyi gwanin ban tausayi.
Cikin damuwa Abba yace.
“Subahallahi, Rayyern ajiye ta. Jannart meke damunki? Ramadan maza ɗauki akwatin taimakon gaggawa”.
Da gudu Ramadan ya nufi side ɗinsu.
Mamy kuwa da sauri ta kamo hannun Jannart ɗin tare da cewa.
“Ya ilahi Jannart kiyi mgn meke damunki gayamin”.
Cikin azabebben kakari da yunƙurin da takeyi ta nunawa Mamy miyar kasen daketa tururi har yanzu tace.
“Mamy a rufe miyar nan wari yakeyi”.
Cikin tsananin mamaki Mamy ta rufe kular tare da cewa.
“Jannart wari kuma?”.
Wani dogon numfashi ta fara ja mai tsawo jin an rufe miyar ta fara jin sauƙin tururin dake shiga hancinta, cikin sauƙe numfashi ta manna bayanta da jikin Rayyern ɗin tana mai maida numfashin.
Kai Mamy ta jinjina tare da sauƙe numfashi a hankali tace.
“Ayyah Jannart sannu Rayyern yanzu haka take fama da amai?”.
Kanshi ya jujjuya mata yana mai sharce mata zufan dake goshinta yace.
“A’a Mamy ni ban taɓa ganin tana amai ba”.
Gyara zamanta tayi still dai hannunta na kan hancinta.
Dawowar Ramadan ne yasa Abba ɗan ja baya tare da cewa.
“To gsky muje asibiti kawai zaifi”.
Cikin sauƙe numfashi tace.
“Abba aman ya tsaya ai, ba matsala”.
Tayi mgnar cikin rauni da kasala.
Cikin kulawa Abba yace.
“Anya kuwa Jannart”.
“Da gaske bana jin komai Abba”.
Shi kuwa Rayyern juya kujerar yayi ta fuskanci washing hand baby ɗin cikin yanayin mai cike da tsantsar kulawa, ya wonke mata hannunta.
Da bakinta, sai kuma ya tare ruwa yasa mata a baki, kuskure bakinta tayi, kana ya wonke cikin wurin.
Sannan ya juyo kujerar, kan table ɗin.
Ganin abin nasa azimun ne yasa Abba juyawa ya koma falo.
Ramadan kuwa da yanzu ya iso, cikin kulawa yace.
“Aman ya tsaya?”.
Murmushi Jannart tayi tare da cewa.
“Eh ya tsaya zo kaci abinci.”
Cike da mamaki duk suka zauna suka sata a tsakiya.
Suna kallon yadda take sauƙe numfashi.
Cikin kulawa Mamy ta jawo filas cup ta ɗauka mai ɗan girma, kunun gombawa ta tsiyaya cikinsa kana ta miƙa mata.
Da sauri ta amsa tare da kai cup ɗin bakinta dan wani irin masifeffen kwaɗayin kunun taji wanda a take yawun bakinta ya tsinke, lumshe idanunta tayi sabida jin dadinsa.
Da sauri Ramadan ya ɓalle maganin amai kwara ɗaya, ya miƙa mata, ba musu ta amsa ta haɗiyeshi sabida taji azabar kakarin yasata yin laushi.
Shi kuwa Rayyern gaba ɗaya ya gaza yin komai sai kallonta yake cike da mamaki, shi kansa sai yanzu yake ganin wani irin matsanancin farin da tayi har wani yellow-yellow tayi, ko dan acan yana ganin turawane yasa baiga tsananin farintaba, ko kuma dan yanzu Mamy dake ba fara sosai bace na kusa da ita koma dai menene farinta yayi yawa yayi kamada dana masu ɗanyen jiki.
Ita kuwa Mamy plate ta ɗauka pepper chicken ɗin ta zuba masa tare da soyyam arish kaɗan. Sai kuma ta haɗa masa tea mai zafi.
Jan plate ɗin yayi gabanshi jin Mamy na cewa.
“Ungo maza kaci kuje ka dubata a asibitin”.
Fork ya ɗan ɗauka tare da soka tattausan tsoka da arish kana ya nufi bakinta dashi.
Da sauri ta jujjuya mishi kai kana tace.
“A’a nifa kunun nan ya isheni”.
Ta kare mgnar tana toshe hancinta.
Haka kuwa akayi duk abinda aka ce mata gashi sam taƙi.
Ramadan kuwa juyawa yayi ya dawo falo don maida kaya aikinsa.
Abba ne ya nuna masa jakkunan da sunan Rayyern ke liƙe a kai yace.
“Kai masa su ɗakinsa”.
Ba musu ya ɗaukasu.
Yana sauƙowa kuma Abba ya nuna masa na Jannart ɗin tare da. Nuna mishi ɗakinta, haka ko akayi ya ɗauka ya kaisu kana ya wuce dinning area.
Sukaci abinci,
Suna fitowa falon Mamy ta kalli Jannart tare da cewa. “ Shiga side ɗinki, ki samu ki ɗan watsa ruwa zakiji ƙarfin jikinki”. Ta ƙare mgnar tana nuna mata ƙofar ɗakin nata, haka yasa Jannart ta
nufi inda tasan nanne ɗakinta.
Shi kuwa Rayyern ido ya zubawa Mamy.
“Kai me kake kallonta haka?”.
Abba ya faɗa cikin tsare gida.
Shi kuwa Rayyern cikin kwaɓe fuska yace.
“Babu”. Yayi mgnar kamar wani abun tausayi.
Ita kuwa Jannart a hankali ta fito Bathroom ɗinta, cikin yanayin kasala.
Tana mamakin abinda yasata amai, da kuma sauyin da ta samu a jikinta tunda tayi aman take jinta wata iriya a haka dai tayi ta ɗan shafa mai, kana ta sauya kaya sannan ta kuma fitowa. duk suna falon sai Abba dake can waje wurin Baba Mauɗo.
Hira sukeyi cike da kewar juna.
Ɗikunan bikin da akayi musu.
Mamy ta fito musu dashi.
Suna kallo, cikin jin daɗi Jannart tace.
“Masha Allah Mamyna mun gode”.
Sai kuma suka kalli Rayyern da ya amsa kiran da Riyyam-nsra ke tayi masa.
“Barka da isa lfy Hamma Rayyern”.
“Barka dai Riyyam-nsra, ina Mammy yaushe zaku taso?”.
Yaya tambayar a jere.
“Mammy na gida ni kuma ina wurin surkarka ne, zan sallameta, in sha Allah gobe uwar haka ai tuni mun iso”.
Cikin kula yace.
“Toh Allah ya kawo mana ku lfy”.
Amin yace kana ya bawa Jannart wayar kamar yadda Riyyam-nsra ɗin ya buƙata cikin jin dadi tace.
“Ga nan ɗikunan ka dana Zaiton hardama Mammy an mata ɗinki Allah yasa dai suyi mata”.
Cikin sauri yace.
“Zasuyi ai Hamma Ramadan ya haɗata da telan sunyi video call ya ganta”.
Cikin zaƙuwa tace.
“To Allah ya kawoku lfy”.
Amin yace kana sukayi sallama.
Su kuwa Anan sukayi ta hirar yadda bikin zai kaya har zuwa wani ɗan lokacin.
Jannart ce zaune gefen.
Mamy data bata cup ɗin kunu ganin yanzuma taƙi cin abinci.
Amsa tayi tare da cewa.
“Nagode”.
Da sauri Mamy tace.
“in akwai abinda kike son ci ki gaya min in dafa miki”.
Da sauri tace.
“Ba komai Mamy yanzu kam na ƙoshi in nasha kunun sai kuma da safe.”
Ta ƙare mgnar tana amsa kiran Barrister Kabeer daya shiga wayarta.
“Masha Allah ɗiyata ta dawo”.
Cikin jin dadi tace.
“Abbana na dawo, a kawo min su Hafeez mana”.
Da sauri yace.
“Kada ki damu in Sha Allah da safe zan kawo miki su”.
Cike da jin daɗi tace.
“Alllah ya kaimu”.
“Amin ɗiyata, ki huta gajiya, zamuzo harda Auntynki”.
Cike da jin daɗi take.
“Kai Alhamdulillah naji daɗi na”.
Daga nan sukayi sallama.
Rayyern kuwa da Ramadan, tuni suka wuce Mai Nasara hospital.
Lungu da saƙo suke zagayawa, yayinda ko ina yake fes-fes haske kamar rana.
Jinjina kai Rayyern yayi tare dafa kaɗan Ramadan kana yace.
“Alhamdulillah Ramadan kayi ƙoƙarin naga dukkan majinyatanmu cikin Kekkyawar kulawa ta musamman komai yana tafiya dai-dai bitsa tsari, naji daɗi haka, nasan ko yanzu na barka da aikin asibitin zakaji da komai”.
Cike da jin dadin ya yaba masa da akayi ya buɗe musu ƙofar Office ɗin Rayyern ɗin kana suka shiga ciki yana cewa.
“Amman dai za’a bani hutun amarci ko”.
Tsaresa da ido yayi hakan ne yasa yayi ƙasa da kansa.
Sai kusan ƙarfe goma harda wasu mituna suka fito.
Daga asibitin kai tsaye gidansu Raihana ya wuce ganin sha ɗaya bata cikaba sabida jarabebben naci.
Shi kuwa Rayyern daga asibitin gidansu Usman PA ya wuce.
Nasir ƙanin Usman ɗin da Mahmoud abokinsa daya fara bawa Jannart bayanai a kan Rayyern ɗin ya samu a ƙofar gidan.
Ganin sa yasa Naseer saurin buɗe masa ɗan madaidacin gate ɗin.
Yana mai cewa.
“Masha Allah Hamma Rayyern Barka da dawowa, mu isa ciki”.
Cikin ɗan sakin fuska yace.
“Umma na nan ko?”.
Ya gyaɗa mishi tare da cewa.
“Harda Yah Usman ɗin ma”.
Suna shiga falon suka samu, Umma da Usman ɗin suna zaune.
Ganin uban gidan nasane yasa Usman miƙewa da sauri tare da cewa.
“Kai Sir mai abin mamaki baka gajiya dayi mana bazata”.
Cikin alamun shaƙuwarsu yace.
“Umma wurinki nazo in gaidaki duk da naga dare yayi”.
Ya ƙare mgnar yana zama gefen Umma, shi cike da jin dadi Umma tace.
“Aiko naji daɗi Rayyanu na, ya hanya ina surkar tamu tana lfy dai ko?”.
“Alhamdulillah Umma”.
Sai kuma ya miƙa wa PA hannu wanda shima hannun ya miƙa masa musabiha sukayi kana sukaci gaba da hira.
Harsu Naseer.
Sai kusan ƙarfe sha ɗaya da kwata kafin ya sallamesu, ya tafi.
A gida kuwa, hira sosai Mamy keyi da Jannart tana bata labarin rawan kan Ramadan dariya sosai takeyi harda kerkerta.
A can gidansu Raihana kuwa, Daddynta ne ke tsaye jikin window ɗakinsa dake sama, cikin yanayin nazari da zurfin tunani ya zubawa Ramadan dake zaune gefen Raihana yanayi mata wani irin kallo mai kama dana maita, kallone da duk wanda ya gani yasan na cikekkun jarababbune, ya lura gaba ɗaya jikin yaron rawa yake kamar mazari.
Numfashi mai nauyi yaja tare da sake labulen ya koma ya zauna yana kallon time.
Shi kuwa Ramadan sha ɗaya da rabi dai-dai ya sallami Raihana,
har gaban mota ta rakasa, cikin narkewa yace.
“Baby wlh ji nake kamar kada in tafi, gani nake dararen suna yimin tsawo”.
Cikin jin kunya tace.
“Saida safe”.
Tana faɗin haka ta juya ta tafi.
Cike da zumuɗi yaja motar ya tafi.
A falon ya samu Mamy da Jannart suna hira, haka yasa ya zauna akaci gaba da hira Jannart na mishi tsiya.
A hankali Mamy ta sauƙe numfashi ganin Jannart ɗin nata hamma da lumshe idanunta, cikin kulawa tace.
“Jannart jeki kwanta dare yayi naga kina ta hamma. Gashi har sha ɗaya da rabi tayi gota”.
Murmushi tayi tare da lumshe idanunta.
Cikin tsokana Ramadan yace.
“Gsky kam Mamy bare ma masu ƙaramin ciki da bacci”.
Cikeda mamaki ta juyo ta kalleshi sai kuma ta kauda kao ganin dariyar tsiya yake mata.
Shi kuwa miƙawa tsaye yayi tare da cewa.
“Uhmm ni bari inyi ciki in Kira tawa masoyiyar”.
Ya ƙare yana haurawa sama.
Itama Jannart miƙewa tayi a kunyace, dan Ramadan ya kumyatata,
A ranta tace.
“Wa ciki yoh ni ina ni ina ciki? Indai ba’a ruwa ake shansaba.”
A fili kuwa kai a sunjuye tace.
“Mamy sai da safe”.
Cikin jin dadi Mamy da dama tuni kallon mai ciki takeyi mata tace.
“Toh Allah ya bamu al’khairi ɗiyata”.
Amin tace tare da wucewa ɗakinta, kana ta maida ƙofar ta rufe.
Ita kuwa Mamy dake falo da sauri ta juyo ta kalli Abba da ya shigo falon, gefenta ya zauna tare da cewa.
“Kawo min coffee ɗina nan”.
“Toh yau kuma a falo za’a sha kenan”.
Tace tana nufar kitchen tana mamakin hakan.
Dai-dai lokacin kuma Rayyern ya turo ƙofar ta shigo tare da sallama a bakinsa.
Amsawa yayi cikin yanayin tsare gida, gefen Abba nasa ya matso cike da son ganin wulgawar Jannart ɗin ya fara jujjuya idanu kana a hankali yace.
“Abba Barka da dare”.
“Yauwa Barka dai”.
“Uhm Abba yau kuma kai kaɗai inasu Mamy”.
Kanshi ya juyo ya kalli Mamyn dake shigowa.
“Babana ka dawo ne”.
Mamy ta faɗa cikin kulawa.
Kanshi ya ɗan jinjina tare da kallon ƙofar falon Jannart a karo na barkatai yace.
“Eh Mamy ya mai jikin?”.
Cikin kulawa da yanayin da yake ciki tace.
“La Alhamdulillah ba komai bata sake aman Bama, tun ɗazuma hira mukeyi da naga tana jin baccine nace taje ta kwanta”.
Kanshi ya jinjina kana ya kuma kallon Abba daya tsare fuska.
Miƙewa yayi tare da cewa.
“Bari inje in ɗan watsa ruwa”.
Da sauri ya kalli Abba da yace mishi.
“Toh saida safe”.
Yi yayi kamar bai jisaba ya haura saman.
Shi kuwa Abba coffee ɗinsa da Mamy ta haɗa masa ya fara sha,
ita kuwa Mamy gefenshi ta zauna tana ɗan mishi hira.
Bayan kamar 30 minute, Abba ne ya juyo kansa a hankali ya kalli steps ɗin sauƙowa, sabida jin takun mutun. Rayyern ya gani cikin wata tattausar jallabiya maroon collor mai shaƙi.
Shima Rayyern Abban ya zubawa idanu cike da mamakin ganinsu a falon har yanzu.
Cikin kauda kai ya ɗan sosa sajensa da bayan hannu kana ya ƙarasa sauƙowa ƙasan.
“Babana bakayi bacci bane?”.
Cewar Mamy. Fuskarsa ya ɗan kwaɓe tare da kallon ƙofar ɗakin Jannart wanda hakan yasa Abba jinjina kai tare da tsareshi da idanu shi kuwa, cikin sanyi yace.
“Eh da..ma”.
“Dama me?”. Abba ya faɗi still idansa na kansa, da sauri yace.
“Uhmm Dam Chocolate na nazo karɓa”.
Yayi mgnar cikin inda-inda da kallon ɗakibta,
Shi kuwa Abba gyara zama yayi tare da cewa.
“Naga ai ɗazu Ramadan yasa wasu a Fridge je ka duba”.
Kwaɓe fuskarsa ya kumayi kamar zaiyi kuka.
Allah ya sani bazai iya bacci ba tare da itaba.
Yana begen ɗumi da ƙamshin jikinta, cikin ransa yace.
“Abba bazaka gane bane”.
Asheko bai san mgnar ta fito fili ba.
“Bazan ganeba kamar yaya? To ai sai ka ganar dani”.
Abba ya faɗa a daƙile.
Da sauri ya nufi kitchen ɗin yana cewa.
“Eh Abba babu irin wanda nake sone a Fridge ɗin shiyasa”.
Sai kuma ya juyo ya haura saman.
Shi kuwa Abba kanshi ya jinjina tare dayin mgnar zuci.
“Mara kunya da bai san kawaici ba, ka kalli tsabar idon mutumin daya baka kyautar mace ba tare da sanin ko kai wayeba kace mishi wai baka son yarsa bazaka kuma taɓa sontaba, harda cewa auren yarjejeniya ne zaka saketa, uhumm ɗan yau”. Ita kuwa Mamy cikin mamakin take kallonsa ganin yayi nisan zangon a tunani.
A can cikin ɗakin kuwa, kasan cewar, Ramadan ya bawa, Jannart mgnin amai tasha, shiyasa tana kwanciya sai bacci.
Shi kuwa Rayyern cikin takaici yake zirya a falonsa,
A karo na uku ya kuma leƙowa, jin falon shirune kuma an kashe wuta yasashi, sauƙowa da sauri.
Yana isa tsakiyar falon ya tsaya.
Ganin an haskashi da hasken waya, da sauri ya juya baya, ganin Abba ne zaune bisa 3 str.
“Yah Salam”. Yace tare da dafe kansa yayi maza ya koma baya.
Yana mgnar zuci haka ya haura sama.
Shi kuwa Abba maida kai yayi ya kwanta.
Shi kam Rayyern ranar jk yayi kamar yayi ta kurma ihu.
Haka yake jinsa duniyar babu daɗi.
Sai kusan ƙarfe uku kafin bacci yayi nasarar ɗaukesa.
Washe gari bayan suna dawo daga masallacin sallan asuba, a jere suka shigo falon, Abba ne a baya ya sasu a gaba.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Abba.
Shi kuwa Abba tsaresa da ido yayi, a falon suka zauna.
Suka sha tea kamar yadda suka saba.
Miƙewa Ramadan yayi ya wuce side ɗinsu.
Shi kuwa Naan kan kujera ya hau tare da niyar kwanciya.
“Kai tashi ka tafi ɗakinka, ka fara shiri, bakwai dai-dai zamu tafi Company”.
Cikin sanyi yace.
“Toh kana ya miƙe ya tafi.”
Yana mgna ƙasa-ƙasa.
Ƙarfe bakwai da kwata dai-dai ya fito cikin wasu tattausan yaɗi mai masifar kyau, fari ƙal, sai baza ƙamshi yakeyi, kansa babu hula.
A tsakiyar falon ya tsaya tare da zubawa Jannart dake fitowa falon idanu kamar ya shekara bai gantaba.
Cikin tsananin bege da kewa, ya buɗa mata hannu alamun tazo, da sauri ta zaro idanunta tare da jujjuyasu ta nuna masa hanyar kitchen da corridor fitowa side ɗinsu Abba kana ta jujjuya mishi kai alamu a’a.
Cikin sauri ya tako zuwa gabanta, hannunta ya riƙo ya jawota jikinsa, tare da ruggume ta, cikin sassayan murya mai fallasa sirrin zuciya yace.
“Allah ya hanani sake ganin irin Daran jiya, domin yayi min tsoro, na rayu babu daɗi sabida rashin ɗuminki a kusa dani, na gaza bacci, na gaza samun salama Janna jiya kawai naji kamar shekara gudane Bama tare”.
Cikin yar dariya tace.
“Sorry Naanu sakeni to kada Mamy ta fito”.
Mamy kuwa dake tsaye a dinning area, kai ta juya da sauri ta koma cikin kitchen tare fara fasa kwan da zatayi amfani dashi.
Shi kuwa Rayyern hannunsa yasa ya tallabo haɓarta, cikin kulawa yace.
“Kina lfy dai ko? Baki sake yin Amai ɗin bako?”.
Da sauri ta gyaɗa mishi, kai tana ƙoƙarin kauda kanta ganin yana sunkuyo da kansa.
Shima da sauri ya ɗan ja baya kaɗan jin gyaran muryan da Abba yayi.
Shi kuwa Abba hango yadda yake riƙe da itane yasa, yayi gyaran muryan tun kafin ya iso.
Da sauri ta matsa can nesa, tare da rusunawa, ta gaidashi, shi kuwa Rayyern kitchen ya nufa.
Shi ko Abba waje yayi yana cewa.
“Hamzarta ka fito mu tafi kaga yau jumma’a mu samu mu dawo da wuri”.
“Toh Abba gani nan zuwa”.
Yace tare da kallon Mamy.
Kana ya juyo ya ɗan kalli Jannart dake bayansa.
“Barka da safiya Mamy”.
“Barka dai Babana ya gajiyar hanya?”.
“Alhamdulillah, Mamy na tafi”.
“Toh Allah ya bada sa’a ya kiyaye hanya”.
“Amin Ya Allah”. Yace yana mai juyowa ya, sauƙo.
Juyowa yayi ya kalli Mamy ganin baya ta basu, yasashi manna mata kiss a goshi, wanda sautinsa yasa Mamy juyowa, shi kuwa da sauri ya wuce waje tsaye ya samu Abba da Baba Mauɗo gaisawa sukayi kana ya shiga mota ya tafi.
Ita kuwa Jannart a kunyace ta shigo kitchin din tare da cewa.
“Mamy sannu da aiki”.
“Yauwa sannu Jannart”.
Ta ƙare mgnar tana kaɗan kwan data fasa.
Da sauri Jannart tasa hannu ta rufe hancinta tare da juya, baya wurin sink wani irin yunƙurin amai ta fara kamar maƙoshinta zai tsage.
“Ya Salam”. Shine abida Mamy ke faɗi tana ƙara matsota.
Ita kam Jannart yunƙuri kawai take, babu abinda take haraswa, to me taci da zata har.
Da sauri Mamy ta kamo hannunta tare da cewa.
“Sannu ko, muje waje”.
Cikin haɗa zufa suka fito dinning area,
numfashin ta fara sauƙewa tare, da danne yunƙurin dake taso mata, amman ina abin yaci tura, kasan cewar hannu Mamy da ɗan ƙarnin ai yunƙurin takeyi har jikinta na rawa tuni hawaye da zufa suke zubo mata dan yunƙurin yaƙi barinta,
cikin azaba tace.
“Mamy ki wonke hannunki ƙarnin kwai”.
Da sauri Mamy ta saketa ta juya tana wonke hannun tare da cewa.
“Allah sarki, kiyi haƙuri Jannart am na cuceki, kiyi haƙuri”.
Cikin hawala ta fara maida numfashin tare da cewa.
“A’a Mamy ba komai, nima bansan meyasaba naketa amai ni dai ƙarnin kwai baya sani amai fa”.
Kamota tayi tare da cewa.
“Muje falo, ai dama dole ki samu sauye-sauyen abubuwa, sai kuma in kinyi sa’a in ya rika zaki koma dai-dai sannu ko Jannart”.
Ta kare mgnar tana ajiyeta kan 3 str.
Da sauri ta kwanta sabida jirin da yawan kakarin ya jaza mata, lumshe idanunta tayi tare da fara sauƙe numfashi.
Gyara mata kwanciyar Mamy tayi tare da cewa.
“Banda zuwa kitchen na yafe, sam bana son tayin aikin ki bari zanyi komai dama wannan aiki nane”.
Ita dai Jannart shiru tayi sai zufan dake keto mata.
Ganin ta nitsune yasa Mamy komawa taci gaba da aikinta.
Ƙarfe takwas da rabi Ramadan ya sauƙo cikin shirin fita, zama sukayi a dinning table.
Amman duk yadda akayi taci abinci sam ta gaza, haka nan takejin bata son komai sai kunun nan, haka yasa shi kaɗai tasha.
Bayan sun gamane shi ya fita, su kuma suka dawo falo.
Rayyern kuwa A companyn suka samu Usman PA.
Dadi sosai Abba da Rayyern ɗin suke ciki ganin tarin ci gaba da kuma yadda hada-hadar ma’aikata da kuma yan kasuwan ke tafiya, kai Rayyern ya jinjina ganin yadda aketa cika manyan tirelili da kayyakin masarufi, wanda kasuwanni zai je, da kuma wasu jihohin wasu motocinma har ƙasashen maƙotanmu kamarsu Niger, Kamaru, Chadi. Zasu nausa.
Sune basu bar cikin campanyn ba sai ƙarfe biyu saura kwata, tuni anata huɗuba a masallatai wasuma sunyi salla.
Suna cikin mota ne ya kira Ramadan.
“Ni kam kunyi mgn dasu Riyyam-nsra kuwa?”.
“Eh Hamma Rayyern muyi mgn dasu kafin su taso”.
“Toh Allah ya kawosu lfy, kada kayi nisa zamu je Airport yanzu kana ina?”.
“Ina asibitine”.
Daga nan suka kayi sallama.
Shi kuwa Rayyern a hankali yake nazartan Abba da tun jiya ya kula dashi, time to time yana dafe ƙahon zuciyarsa alamun yana jin wani abune.
Cikin kulawa yace.
“Abba meke damunka ne?”.
Ajiyan zuciya yaja tare da cewa.
“Ba komai kawai dai ina yawan jin tsinkewan zuciya ne, tun shekaran jiya bansan me yasaba”.
Da sauri yace.
“Toh sai munyi salla mu wuce, pharmacy in gwada bp’nka”.
Daga nan dai suka wuce masallaci.
A gida kuwa dai-dai lokacin Barrister Kabeer ya sauƙe Aunty Dijat dasu Hafeez a ƙofar gidansu Rayyern ɗin kana, yace.
“Yauwa to ku, shiga ni zan wuce masallaci, sai an idar zan taho,”.
Ai tuni Hafeez da Hafiza kam sunyi cikin gidan.
“To Allah ya kiyaye hanya”.
Aunty Dijat tace, tare da bin bayan yaran.
Shi kuwa jam motar yayi ya fita, dan ganin Ari na tsaye alamun shima fita zaiyi, yasa suka tafi tare.
Da sauri Jannart ta miƙe tsaye tare da cewa.
“Laaaa Allah sarki Hafeez Hafiza”.
Sai kuma ta buɗe musu hannu tare da nufarsu.
Aifa da gudu suka faɗa jikinta, suna dariya cike da jin dadi suke cewa.
“i miss u so much Aunty Jannart”.
“Miss you to”. Tace tana sakesu da sauri ganin Aunty Dijat da yanzu ta shigo.
Mamy kuwa ido ta zuba musu tana murmushi.
“Allah sarki Aunty na, Ina kewarki, kai yau naji daɗi na Mamy ga Aunty Dijat matar Abba na da yaransa”.
Cikin karramawa Mamy tace.
“Masha Allah, sannunku da zuwa ku iso, marhabin lale da zuwa”.
Ita kam Aunty Dijat sai kallon Jannart take cike da so.
Zama sukayi bisa kujeru gaba ɗaya Hafiza ta kanainayeta, sai tsalle takeyi.
Mamy kuwa dinnin area ta nufa, Fridge ta buɗe tare da ɗebo musu, kayan sannu da zuwa.
A gaban Aunty Dijat ta ajiye, cike da kulawa tace.
“Bissmillah, yau kam Barrister ya cika mana alƙawarin”.
Cikin sakin fuska suka gaisa suna ta yabon sauyawar Jannart.
Kana suka sha ruwa.
Hafeez kuwa baisha komaiba, cikin kulawa Jannart ta miƙa mishi Appul tare da cewa.
“Ga mutuminka”.
Kai ya jujjuya tare da cewa.
“Uhum”.
“To me kakeso?”.
Da sauri yace.
“Aunty Jannart kiyi mana a logoi-logoi”.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
“Kace muyi hana baba tashi”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Mamy kuwa cewa tayi.
“Ai kuwa kam bari inyi wata ƙil kema kici,”.
Da sauri tace.
“A’a Mamy zanyi mana kekam ki huta”.
Hannunta Hafiza ta fara ja tana cewa su tafi.
Cikin Faɗa Aunty Dijat tace.
“Ka da Allah ki nitsu ku barmu, mu gaisa shegen iyayi”.
Kwaɓe fuska Hafiza tayi alamun zatasa kuka, haka yasa Jannart kamo hannunta da sauri tare da cewa.
“Ayyah my Aunty ki barmu, zo mu tafi”.
Daga nan suka wuce kitchen din.
Sauri-sauri ta haɗa komai na a hana baba tashin.
Ta sannan ta fara, tuya.
A ɗigon forko da ƙamshin ya bugeta, tayi saurin juyawa, tare da toshe hancinta.
Tuni yunƙuri ya taso.
Jin yadda ƙamshin ke ƙara rufetane, yasa tayi maza ta fito.
Da sauri Mamy ta miƙe tana cewa.
“Subahallahi Jannart aman kuma?”.
Ina ba mgn sai amai take zugawa, a duk kunun da tasha take keleyar dashi.
Tanayi harda shaƙuwa.
A tare Aunty Dijat da Mamy suka iso.
Hafeez kuwa da sauri ya kashe gas ɗin.
Kana suka fito, sannu suketa jera mata.
Amman babu bakin amsawa,
Tallabeta Aunty Dijat tayi cike da kulawa tasa mata ruwa ta wanke bakin ta da fuskarta.
Sai rawa jikinta keyi kamar mazari.
Falo suka dawo, Mamy kuwa gyara wajen tayi.
Sannan tazo ta zauna gefenta, tana mai kiran Ramadan a waya, yana ɗagawa tace.
“Kana ina?”.
“Asibiti”.
“Maza yanzu kazo wallahi aman nan fa yaƙi tsayuwa yau sau biyu tanayi”.
Da sauri yace.
“Toh Mamy bari in duba abinda ya dace in zo mata dashi.”
Su kuwa Aunty Dijat ne faɗa ta kama yiwa yaranta.
Jim kaɗan kuwa sai ga Ramadan ya shigo.
Da leda a hannunsa.
Gabanta ya ɗan tsuguna, cikin kulawa tace.
“Sannu my Aunty”.
Ya kare mgnar yana zaro ɗan ƙaramin ledan ruwan da yazo dashi, Alkurai ya ɗan haɗa kana, yace.
“Bari in sa miki ruwan nan zakiji ƙarfin jiki da kuma sauƙin aman zaki samu kuma kici abinci”.
Kai kawai ta jinjina mishi, sabida harga Allah tana son taji sauƙi dan zuwa yanzu, gaba ɗaya duniyar ba daɗi take jinta.
Hannunta ya kamo ya ɗan ɗaura mata robar nan, kana ya samu jijiya ya cusa allurar.
“Wachh”. Tace da ɗan ƙarfi.
“Sannu”. Sukace mata baki ɗayansu.
Haɗa mata ruwan yayi tare dasa alkuran.
Gyara mata kwanciyarta Aunty Dijat tayi.
A waje kuwa dai-dai lokacin Abba suka shigo cikin gidan, yayinda motar Barrister Kabeer ke biye dasu a baya.
Abba waya yakeyi da Baban Raihana.
Haka yasa suna fita, shi ya jingina da jikin motar shi kuwa.
Rayyern motar Barrister ya zubawa ido har yayi parking ya fito.
Gaisawa sukayi cikin mutuntaka.
Shima Abba ya gama wayar hakan yasa suka gaisa.
Baba Mauɗo daya nufosu ne Abba ya kalla kana ya juyo ga Barrister Kabeer dake cewa Rayyern.
“Eh gida lfy lau, duk gidan nawa ma ai suna ciki, ɗazu na sauƙesu kafin in wuce masallaci”.
Ɗan guntun murmushi yayi tare da cewa.
“Ah lallai kam mun gode kuwa”.
Juyowa sukayi suka kalli Abba da yace.
“Baba Mauɗo zamuje gidan Surkan Ramadan ne, sunce suna son ganinmu”.
“Toh Allah yasa lfy dai ko?”.
Cewar Baba Mauɗo.
Kai Abba ya gyaɗa kana yace.
“Allahu alamu.
Barrister muje harda kai”.
Da sauri Barrister Kabeer yace.
“Ayi haka kuwa?”.
“Ah ba komai muje”.
Baba Mauɗo yace.
Haka yasa suka shiga motar shi Barrister Kabeer ɗin kana yaja suka tafi.
Shi kuwa Rayyern ciki yayi.
“Dai-dai lokacin kuma Ramadan ya gama haɗa mata komai ya koma gefe, yaja Hafiz da Hafiza.
Da sauri Rayyern ɗin ya ƙaraso tsakiyar falon, cike da alamun tambaya yake kallon Jannart dake kwance da ƙarin ruwa.
Gefenta ya iso, yana mai cewa.
“A’a Janna amanne Kuma?”.
A hankali ta buɗe idanunta tare da gyaɗa mishi kai.
Aunty Dijat kuwa, ɗan matsawa gefe tayi ganin yadda yake matsowa.
Hakan kuwa yayi masa daɗi, hannunsa ya kife kan goshinta kana ya gangaro dashi zuwa.
Kan wuyanta, cikin tsananin kulawa, tausayawa, yace.
“Baby kuma babu zazzaɓi fa”.
Still kai ta gyaɗa masa.
Mamy ce ta ɗan harareshi tare da cewa.
“Toh ai dai ka gaida surkar taka ko?”.
Cike da kunya ya ɗan sosai ƙeyarsa kana ya kalli Aunty Dijat sannan yace.
“Barka da yamma Aunty Dijat”.
Cikin jin daɗin kulawar da yake bawa Jannart tace.
“Barka dai Rayyern kun dawo lfy”.
Alhamdulillah yace yana zama bisa hannun kujerar da Jannart ɗin ke kwance.
Ramadan kuwa, whatsApp nashi yake dudduba akai-akai, dan ko zaiga saƙon Riyyam-nsra aikuwa yana dubawa yaga ya turo masa saƙonni har shida.
Aunty Dijat kuwa cikin sanyi tace.
“Toh amman dama haka take fama da amai hakane?”.
Da sauri Mamy ta jujjuya kai tare da cewa.
“A’a Wlh sukace batayi a can sai dai tunda suka dawo, in dai tururin wani abun mai ɗan mai da al’basa ya bugeta sai tayi ta amai, kin san sha’anin mai ƙaramin juna sai a hankali”.
Da sauri cike da tsananin mamakin Rayyern ya kalli Mamy jin wai mai juna.
Ita kuwa Jannart ƙara rufe idanunta kawai tayi.
Ita kuwa Aunty Dijat cikin jin daɗi tace.
“Allah sarki gsky ko zata rainin cikin da wahala, duk laulayi babu mai daɗi amman cikin dake sa amai yafi jikkatarwa”.
Shima kam Rayyern kamar gaula haka yake binsu da ido.
“To wai su a zatonsu cikene da ita Dako hakane da naji dadin duniya. Toh inama ta yarda na kusanceta bare in bata ciki yarinya da sai kwalele ta iya min ta barni in shiga muhallinka taƙi saidai ta dakatardani a bakin ƙofa”.
Sai kuma ya ɗago kansa da sauri jin Ramadan na cewa.
“Masha Allah, Alhamdulillah Hamma Rayyern su Riyyam-nsra sun iso yanzun nan yace jirginsu ya sauƙo”.
Cikin farin ciki yace.
“Masha Allah”.
Sai kuma ya kalli Mamy da tace.
“Toh maza kuje ku ɗaukosu”.
Da sauri kuwa Ramadan ya miƙe.
Shima Rayyern miƙewar yayi bayan ya shafa fuskarta.
Waje suka nufa.
Ganin la’asar tayine yasa, suka tsaya sukayi salla.
Kana suka wuce Airport.
Suna shiga cikin jama’a suka rinƙa kutsawa, tare da jujjuyawa.
Suna neman ta inda zasuga su Riyyam-nsra ɗin.
Riyyam-nsra kuwa dake bayan Mammy da zaiton ƙasa yayi da murya tare da cewa.
“Mammy bari mu gani ko jini da nono zaiyi musu jagora su ganeku”.
Rayyern kuwa idanu ya zubawa Mammy da Zaiton dake liƙe da niƙabi a fuskokinsu.
Cikin wani irin sassayan daɗi da yaji ya ziyarceshi ya saki murmushin mai haɗe da dariya cikin tarin jin daɗi yace.
“Mammy!”. Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya Mammy ta sake mai ƙarfi tare da yaye niƙabin.
Kawai sai ta ruggume shi, wani irin sanyi mai masifar ɗadine ya rufesa yana maijin wata iriyar fitinenneyar iska mai daɗi na ratsasa.
Ita kuwa Mammy hannu tasa ta jawo Ramadan da ya zuba musu idanu.
Ruggume su tayi tsam-tsam a jikinta kawai sai taji hawaye na kwaranyo mata.
Zaiton ma yaye nata niƙabin tayi, tare da ruggume Mammynta ta baya.
Shi kuwa Riyyam-nsra cikin tsananin jin daɗin ya farayi musu video tare da cewa.
“Ko yau ko yanzu na mutu, na mutu da cikekken farin ciki, Mammy na cika miki burinki, na haɗaki da mafarkinki a zahiri”.
Sai kuma ya ruggume Ramadan da Rayyern ta bayansu.
Wani irin farin cike mai tarin yawa ya rufesu.
Da yawa mutane tsayuwa sukayi suna kallonsu.
Wata matace da tazo wucewa gefensu tace.
“Masha Allah uwa da ƴaƴanta”.
Kai Mammy ta jinjina mata tana mai sharce hawayen ta,
Kana ta sakesu gaba ɗayansu.
Su kuwa cikin tarin farin ciki suka ruggume Riyyam-nsra kana a ladabce Rayyern da baiji mamaki ko rashin dai-dai a ruggume su da Mammy tayiba ya kamo hannun Zaiton tare da cewa.
“Muna farin ciki da ganinku”.
Cikin jin dadi suma sukace haka.
Daga nan kuma Ramadan da Riyyam-nsra suka jidi jakkunan su, suka kai cikin mota, shi kuwa Rayyern bayan motarsa ya buɗe wa Mammy tare da cewa.
“Mammy shiga nan ban yarda da tuƙin Ramadan ba ya cika rawan kai”.
Cike da fara’a ta shiga kana ya maida ƙofar ya rufe.
Kana ya jawo hannun Zaiton kuma yasata a gaban motarsa.
Sannan ya zagaya ya shiga yana cewa.
“Ku kuma iyayen rawan kai ku tafi a hankali dai”.
Dariya Riyyam-nsra yayi tare da cewa.
“Yah Ramadan nine zan jamu”.
Haka kuwa akayi suma nufi gida cikin farin ciki.
Su Abba ma acan gidansu Raihana sukayi sallan ganin lokacin yayi, kana suka kama hanyar gida.
Suna isa, gida Baba Mauɗo yayi side ɗinsu.
Abba da Barrister Kabeer kuwa cikin gida sukayi.
A falon kuwa tuni Mamy ta cirewa Jannart ruwan dan ya ƙare kuma Alhamdulillah kuzarinta ya ɗan dawo dan har da tashi zaune suna hira.
Mamy ce ta ƙarasa musu suyan ta kawo musu sunaci suna hira.
Alhamdulillah kuma itama Jannart ta ɗan samu taci.
Tattare Wurin Mamy tayi.
Dai-dai lokacin kuma su Abba suka shigo.
Nan suka gaisa.
Cike da farin ciki Barrister Kabeer ya kalli Jannart da kyau tare da cewa.
“Eyyyeh masha Allah Mascow ta amshi ɗiyata ga yadda kika zamma balarabiya”.
Cike da kunya tayi murmushi.
Dai-dai lokacin kuma su Ramadan suka shigo farfajiyar gidan.
A can sashin Baba Mauɗo kuwa, fitowarsa da bayan gida kenan da alamun al’wala yayi, qura’an ɗinsa ya ɗauka, kana ya zauna kan sallayarsa ba tare da ya naɗa rawaninsa ba, suratul Khaf ya fara karantawa cikin dadɗan sauti.
Su kuwa su Riyyam-nsra, yana gama parking ya fito da sassarfa waige-waige yake yana cewa.
“Baba Mauɗoooo”.
Ganin babu alamunsa a wurin ne yasashi juyawa da sassarfasa ya
nufi cikin gida yana mai cewa.
“Mamy! Aunty Jannart!! Abba!!!”.
Dariya sosai Hadi da Ari sukeyi, dan su kansu sunyi farin cikin ganinsa.
Rayyern kuwa buɗe wa Mammy motar yayi tare da cewa.
“Mammy bisimilla mu shiga”.
Ramadan kuwa Hadi da Ari ya kalla tare da cewa.
“Yauwa ku shigo da kayyakin nasu”.
To sukace kana suka amshi key ɗin motocin.
Rayyern kuwa jagora yayi musu, yana gaba suna binsa a baya.
A can side din Baba Mauɗo kuwa, cikin ƙarfin hali yake karatun sabida wani irin masifeffen harbawa da zuciyarsa keyi.
Yayinda haka take a wurin Abban Rayyern ma.
Cikin murmushi Abba yake kallon ƙofar falon jiyo yadda Riyyam-nsra ke auna musu kira.
Mamy kuwa da sauri ta fito daga kitchen da taje ɗaukowa Barrister Kabeer ruwa.
Dai-dai lokacin kuma ya shigo.
Sai kuma ya isa gaban Abba yana ɗan sosai ƙeya yace.
“Oyoyo Abba”.
Murmushi Abban yayi tare da cewa.
“Har lau dai baka sauyaba”.
Kai ya jujjuya kana ya juyo ya kalli Mamy cikin sauri ya isa gabanta tare da cewa.
“Allah sarki Mamy na”. Sai kuma ya juyo ya kalli Jannart dake cewa.
“Uhum ina ka baro mana Mammy da Zaiton”.
Da sauri yace.
“Oho My Aunty ai bam ganekiba nayi zaton balarabiyar Saudia ce”.
Dariya sukayi baki ɗaya dai-dai lokacin kuma Rayyern ya turo ƙofar tare da shigowa kana yace.
“Mammy shigo mana.
A hankali tasako ƙafarta ta dama cikin falon.
Haka yayi dai-dai da wani irin harba da zuciyar Abba tayi wanda yasashi sauri ɗago kansa.
Ita kuwa Mammy a nitse ta kutso kanta cikin falon hakan ya bawa Ramadan da Zaiton damar shigowa.
Da sauri Jannart ta miƙe tsaye, ganin yadda Abba yayi wani zabura ya mike tsaye cikin tsananin kaɗuwa da zaro idanu a ɗimauce.
Mamy kuwa ganin yadda suka miƙa baki ɗayasu ne yasa ta ɗan tako zuwa gefen Riyyam-nsra daya ɗan tareta kaɗan.
Idanunta ta sauƙe kan fuskar Mammy da tun a airport data cire niƙabinta bata maidashi ba.
Wani irin zazzaro idanu Mamy tayi tare dajan wani numfashin mai haɗe da tarin al’ajabi, tsoro, kaɗuwa, da girgiza cike da ruɗani tace.
“Heeeehhhhh Addaaaaaa Aichaaaaaaa”.
Kawai sai luuuu ta tafi ƙasa a sun…!
Tubali Book 3 Page 1
Tubali Book 3 Page 2
Tubali Book 3 Page 3
Tubali Book 3 Page 4
Tubali Book 3 Page 5
Ta tafi ƙasa luuu a sume,
Kusan a tare duk suka mimmiƙe tsaye baki ɗayansu.
Riyyam-nsra ne yayi wani irin juyi cike da hanzarin ya tarota ta faɗa jikinsa.
Ramada da Rayyern kuwa a guji sukayi kansu.
Barrister Kabeer kuwa, Abba ya nufa, ganin yadda ya tsaya ya tamkar an dasashi ya zubawa Mammy idanu tamkara ƙwayar idanunsa zasu faɗo ƙasa, wani irin azabebben karkarwa jikinsa ya kamayi tamkar mazari.
Kana fuskarsa ta cika da tsananin kaɗuwa, mamaki, tsoro, firgici, al’ajabi, da tarin ɗimuwa sam baibi ta kan Mamy da ta saki ƙara ta faɗi sumeba kana bai bi ta kan Rayyern da Ramadan da keta jijjigata suna auna mata kiraba.
Zaiton kuwa, cikin tsananin rawan jiki itama ta saki kuka tare da bin bayan Mammynsu data nufu kan Mamy.
Cikin Sauri Barrister Kabeer yayi hamzarin riƙo Abba ya ajiyesa.
Jannart kuwa a gigice ta saki kuka ganin yadda gaba ɗaya Mamy ke kwance kamar matacciya.
Wani irin tsorone ya rufeta, jin Rayyern yana cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji’un Abba, Mamy bata motsifa, Ramadan ka duba mana Mamy, Mammy ki taimakemu”.
Gaba ɗaya ma shi ya mance cewa, shi likitane.
Shi kuwa Ramadan kuka kawai ya saki da azaban karfin sauti yana jijjigata.
Hakan ya tsananta kukan Jannart, yayinda kukan Jannart ɗin kuma yasa su Hafeez saki kuka da karfi.
Ita kuwa Mammy kitchen ɗin su ta nufa sa sauri.
Aunty Dijat kuwa kamo Jannart tayi tare da ruggume ta, tana maimaita.
Innalillahi wa innailaihi raji’un.
Riyyam-nsra kuwa yau shine ya zama na miji
Domin dama can shi yanada zaton hakan zai iya faruwa, hakan yasa cikin ƙarfin guiwa da ƙarfafawa su Rayyern guiwa yace.
“Hamma Rayyern Mamy fa tana raye, Please ka nitsu, ka dubata, tana da raye, sumane tayi”.
Ina gaba ɗaya falon ya dibke da koke-koke duk gidanma ya hargitse.
Dai-dai lokacin kuma Hadi da Ari, suka shigo riƙe da jakkunan su Mammy.
Ganin yadda gaba ɗaya suke a hargitse ne, yasa, Ari sakin jakukkunan Hannunsa, a guje ya koma baya.
Side ɗinsu ya nufa, a matuƙar gigice.
Yana tafe yana aunawa Baba Mauɗo wani irin hargitsestsen kira.
“Baba Mauɗo innalillahi wa innailaihi raji’un Kazo kaga halinda Alhaji da ahlinsa sukeciki, Baba Mauɗoooooo!!!!!”.
Cikin tsananin gigita Baba Mauɗo ya ajiye ƙura’an ɗin hannunsa kana miƙe tsaye a hargitse.
Dai-dai lokacin kuma Ari ya shigo.
Ganin yadda Ari yake a matuƙar gigicene, ya sashi.
Ƙara kiɗiminewa cikin tashin hankali yace.
“Kai Ari meke faruwa”.
Cikin hargitsi Ari ya fara nuna muna masa, hanyar cikin gidan yana cewa.
“Rayyern! Ramadan! Riyyam-nsra! Jannart! Namynsu”.
Innalillahi, jin yadda ya jera masa kiran sunayen su Rayyern shine tashin hankali mafi muni a garesa.
Allah ya sani da wani mugun abu ya samesu gwara ya samesu.
Wannan dalilin yasa gaba ɗaya ya firgice jikinsa ya ɗabi wani irin mazari.
Ba tare daya tuna baisa rawanin da yake kare surar fuskarsa ba, ya nufi cikin gidan a hargitse.
A can cikin gidan kuwa, cikin Hanzarin Mammy ta ɗauko ruwan sanyi a Fridge ɗin data samu a dinning area.
Tana ɓalle marfin goronan, ta iso inda Mamy ke kwance kan cinyar Riyyam-nsra.
Da sauri ta watsa mata ruwan a fuska, cikin Sa’a watsawa ɗaya, Mamy taja wani irin firgitacen numfashi tare da yunƙurawa a zabure ta miƙe zaune kamar wacce zata arta a guje, ganin hakane yasa.
Rayyern yin wani irin zabura ya kamota ya ruggume ta a jikinsa da ƙarfi cikin gigita yace cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji’un Abba Mamy na, Mammy Help me”.
Cikin tsananin sauri Mammy ta sunkuyo kan Mamy hannunta ta kamo ta riƙe da karfi, cikin tsananin rauni tace.
“Ruƙayya ki buɗe idonki, kada ki zauce, nice Adda Aichanki ki buɗe ido, kinga Rayyanunnki ya shiga ɗimuwa, kalli Ramadan ɗinki yadda yake kuka”.
Wani irin zurawa Mammy idanu tayi, wasu hawaye masu azabar zafi nankwaranyo mata.
Abba kuwa har yanzu ya gaza daina kallonta.
Barrister Kabeer dai na riƙe dashi.
Yayinda Aunty Dijat ma ke riƙe da Jannart.
Dai-dai lokacin kuwa Baba Mauɗo ya kutso kansa cikin falon, yana mai cewa.
“Rayyanu! Ramadan! Meke faruwa”.
Jin sautin muryarsa ne, yasa Mammy dake durƙushe, wani irin zabura tare da miƙewa tsaye,
Ido cikin ido sukayi da Baba Mauɗo.
Cikin tarin kiɗima, gigita, hautsunewar tunani, ta fara nunashi da yatsa murya can sama a hargitse tace.
“Ya ilahi ya mujibattada’awati ya hayyu ya ƙayyum birahamatika astaƙisu. *Mujed* ta kira sunan da yasa jikin Baba Mauɗo sakin wani irin masifeffen karkarwa.
Ita kuwa Mammy luuu tayj
Ta faɗa kan Ramadan a sume.
“Innalillahi wa innailaihi Mammy!”.
Zaiton ta saki azabebben kuka.
Abba kuwa ganin fuskar Baba Mauɗo ne, yasashi yin wani irin zabura ya kwace hannunsa da riƙon da Barrister Kabeer yayi masa.
Kawai sai yasa hannunsa duka biyu ya riƙe kansa da azaban ƙarfi cikin hartsewar murya cike da kuka yace.
“Ya Allah kada in rasa hankalina, ya Allah idan mafarki nakeyi, ka farkar dani ka kuma tabbatar min da mafarkina ya zama gsky al’farmar Annabi da al’ƙur’ani dan girman zatinka”.
Shi kuwa Riyyam-nsra da sauri shima ya zubawa Baba Mauɗo ido, wanda ya gane sanadin ganinsa ne ya sumar da Mammynsu.
Goran ruwan dake hannunta yazare.
Tare da yayyafa mata.
Amman ina bata farfaɗoba
kuma yayyafa mata yayi da ƙarfi, cikin Sa’a ta farfaɗo da wani irin maraitaccen kuka mai cushe numfashin, ta meda kanta jikin Ramadan.
Shi kuwa Baba Mauɗo zamewa yayi ya zauna a tsakiyar falon bisa carpet cikin wata iriyar fitinenneyar murya mai cike da ababe masu tarin yawa yace.
“Ya Salam, Yau a raye nake ko a mace? Ya Allah mafarkine ko zahiri? Aicha a mafarki nake ganinki ne kamar kullum koko ido biyu ne?”.
Ya kare mgnar yana sakin kuka kamar yaro.
Wannan al’amarin ya magaga ya kuma dunguzuma tunanin kowa,
Barrister Kabeer kuwa kai kawai yake jinjina yana nanata kalmar.
“Alhaji Bashir Muhammad Mai Gaskiya! Ya salam, inama ace nima zanga yah Abdulkareem a wannan duniya da nake ciki”.
Sai kawai ya saki kamo Jannart dake kuka ya ruggumeta cikin sautin kuka yace.
“Kiyi kuka Jannart, bazan hanaki yin kuka a wannan ranarba, kiyi kukan da ba’a barki kin yishi ba tsawon rayuwarki.
Jannart kiyi kuka domin kece kikafi cenccenta dakiyi kuka fiye da kowa a yau”.
Ita kam Jannart zuwa yanzu kanta ya fara juyawa.
Ita kuwa Mammy rarrafe ta farayi kamar yarinya.
A haka ta isa har gaban Baba Mauɗo, kawai sai ta kife kanta, bisa sawunsa.
Cikin wata iriyar sassayar murya tace.
“Nice Mujed nice, Aucha nice, ɗin dai”.
Hakan ne yasa Baba Mauɗo ɗaga Hannunsa sama tare da cewa.
“Alhamdulillah alakulli halin, Aicha gaya min Riyyam-nsra ɗanane?”.
Cikin zubda hawaye ta gyaɗa masa kai tare da cewa.
“Eh shida da Zaiton duk yayanka ne Mujed yayankane na cikinka kuma na halattatu”.
Jin wannan kalmar ce, tasa, Riyyam-nsra janye jikinsa daga jikin Mammy da rarrafe shima ya taho jikin Baba Mauɗo.
Shi kuwa Baba Mauɗo, hannu ya miƙawa Zaiton tare da cewa.
“Zo nan Mamana zo nan Aicha kin cika min burina”.
Aifa cikin kuka Zaiton ta faɗa, jikinsa, ita da Riyyam-nsra duk sun gane, cewa Baba Mauɗo shine mahaifinsu tun daga fuskarsa, dan sun mishi farin sani a hoto.
Da sauri suka juyo duk suna kallon Barrister Kabeer dake kuka ruggume da Jannart, cikin sanyi Abba yace.
“Barrister kayi haƙuri, ni nasan kukan me kakeyi, amman dan Allah kayi haƙuri”.
Da sauri cike da mamaki Barrister Kabeer ya tsagaita da kukan yanayiwa Abba kallon tambaya.
Kai Abba ya jinjina masa.
Alamun “eh na sani”.
Rayyern kuwa a hankali ya miƙe dinning area ya nufa, gororin ruwan sanyi ya ɗebo masu yawa.
Yana dawowa, ya ɓalle marfin goro ɗaya, yasawa Mamy a baki, ba musu, ta amsa, ajiyan zuciya ta fara sauƙewa bayan ta gaba shan ruwan.
Abbansa ya kuma bawa, sannan ya bawa Mammy amsa tayi tasha, sannan ya bawa Baba Mauɗo.
Haka sai ya basu baki ɗayansu.
Kana a hankali ya kamo hannunta janyeta yayi daga jikin Barrister Kabeer.
Bisa kujera ya ajiyeta.
Ɓalle marfin goro yayi tare dasa matashi a bakinta.
Yadda takejinta a gigice yasa ta amshi ruwan.
Shi kuwa Rayyern jawo Hafeez da Hafiza yayi ya mannasu a jikinsa yana shafa kansu.
Hakan da yayi musu yasa gaba ɗaya nitsuwa ta fara sauƙar musu.
Kallon Jannart yayi cikin tattausan murya yace.
“Kiyi haƙuri ki dena kukan haka nan kinji, kinga baki da lfy”.
Meda kanta kawai tayi ta jinginar a kujera bayan ta zame ƙasa.
Abba ne yayi gyaran muryan tare da kallon Mamy dake sauke ajiyan zuciya.
Cikin sanyi yace.
“Ruƙayya kinga ikon Allah ko?”.
Kai ta jinjina masa kawai.
Shi kuwa Barrister Kabeer, wayarshi ya zaro.
Alhaji Bala tambari ya kira, yace yana son ganinsa a gidansu Dr Rayyern.
Kana ya kira Dr Sajo.
Sannan su kuma falon kab, ɗinsu kowa ya koma mazauninsu.
Riyyam-nsra kuwa murmushi kawai yake tayi.
Gaba ɗayansu a ƙasa suka Zazzau na.
Babu abinda ke tashi sai sauƙe ajiyoyin zuciya.
A hankali Abba ya matso gaban Baba Mauɗo cikin tarin girmamawa mutuntawa, sunkuyar da kansa yayi ƙasa murya a raunace yace.
“Kafin ince komai, in kuma yi komai.
Zan fara da neman afuwarka a bisa ajiyeka da mukayi a matsayin maigadi, a muhallinka, wallahi bamj ganeka ba, ka gafarceni ubangidana, da kai tsaye zan iya kiranka da ubana”.
Da sauri Baba Mauɗo ya fara jujjuya mishi kai tare da cewa.
“Bashiru dan Allah kada kace komai, domin da duk al’ummar duniya kowa zai samu mutun mai amana irinka ahlinsa to da tabbas da babu wani batun cin amana da zai rage a duniya, Bashiru kai mutun ne managarcin da samun irinka zaiyi wuya, domin irinku suna ƙaranci a duniya, to Ni kuma Bashir me zanyi maka takwarana da zan iya biyanka a duniya, ka cika ɗan halas”.
Mamy kuwa a hankali ta iso gaban Mammy cikin rauni da kuka tace.
“Adda na kuma uwata kin min komai a duniya, ni kuwa me zan miki?”.
Da sauri Mammy ta rufe mata baki tare da cewa.
“Ai ni kika yiwa komai a duniya, bani da abinda zan biyaki dashi tabbas jin cika amintacciya”.
Cikin rauni Ramadan yace.
“Mamy ki dena kuka, koma menene abarshi sai mun gaisa dasu”.
Hakan ne kuwa yasa duk suka rinƙa gaisawa da juna.
Dai-dai lokacin kuma Dr Sajo da Alhaji Bala Tambari suka shigo a tare. Dr Sajo kam yayi masifar kaɗuwa da ganin fuskar Baba Mauɗo, yayinda Alhaj Bala Tambari kuwa yaketa murmushi.
Nan aka gaggaisa dasu. Kana duk suka Mamy ta gabatar musu da ɗan abin taɓawa. Amman ina babu wanda yayi iya cin komai.
Musamman Rayyern da Ramadan dake cikin kaɗuwan son sanin Meya firgita musu iyaye harda suman wasu, irin Rayyern da Abba tun safe babu abinda sukaci.
Gyara zama sukayi tare da fuskarta Abba da Barrister Kabeer ya jefa masa tambayar da amsoshinta keda yawa.
“Abban Rayyern, su waye waɗannan da ganinsu ya gigitaku ya firgitaku har ya kai iyalinka da suma? Sannan me alaƙarku dasu? Sannan ya akayi Alhaji Bashir Muhammad Mai Gaskiya, da akeda cikakkun rahotannin rasuwarsa shekaru ashirin da biyu zuwa da uku ya kasance a nan a gidanku kuma cikin bada kamanni?”.
Kai Baba Mauɗo ya jinjina tare da saurin cewa.
“Ƙannena su”.
Da sauri Abba yace.
“Kayi haƙuri Alhaji, barni in gaya musu gsky, kodan Rayyern da Ramadan, domin zuwa yanzu nagane cewa Riyyam-nsra kam da yar uwarsa Zaiton sun san komai”.
Da sauri Riyyam-nsra ya jinjina masa kai alamun eh.
Shi kuwa Barrister cikin sanyi ya kalli Hadi da Ari dake tsaye bakin ƙofar, yace.
“Da kun bamu wuri”.
Da sauri Baba Mauɗo yace.
“A’a barsu babu komai su mutanene masu aminci, ku shigo ciki ku zauna”.
To sukace kana suka shigo ciki suka zauna.
Barrister Kabeer ne ya kuma cewa.
“Abban Rayyern kai muke sauraro”.
Jin hakan ne yasa Abba Rayyern, sunkuyar da kansa, tare da rumtse idanunsa hawaye masu zafi suka silalo masa.
Sai kuma ya kalli Rayyern da Ramadan kana cikin tsananin rauni da tunowa da tsohon tabo mai ciwo a ransa ya buɗu baki a hankali ya fara basu lbrin da shine Tubalin komai cikin raunatacciyar murya yace.
*“Gembu Membilla”.*
Sai kuma ya sharce hawayensa kana yaci gaba da cewa.
“Shekaru ashirin da uku zuwa da huɗu baya, mun kasance a cikin garin Gembu da yake tushenmu asalin mahaifa mu ni da Rukayya.
Mu asalin fulanine, kuma makiyaya.
Alhaji Bashir Mai Gaskiya, gashi nan Baba Mauɗo kenan. kuwa baƙone a garinmi ba nanne asalin garinsaba.
Daga nan Kano yake a yadda ya sanar mana yanayin kasuwancinsa ne na binciken ma’adan ƙasa dana ruwane, da haɗa hannu da manoma wurin ganin sun bunƙasa harkarsu, ne ya kaisa Gembu.
Matarsa ɗaya Hajia Aicha.
Gata nan Mammyn Riyyam-nsra kenan.
A lokacin yaransu biyu ne, Rayyern da Ramadan”.
Cikin wani irin ɗimuwa da kaɗuwa, Rayyern da Ramadan suka zazzaro idanunsu waje tare da kallon Baba Mauɗo da Mammy kana suka kuma juyo suka kalli Abba cikin son tabbatarwa.
Shi kuwa Abba kai ya jinjina musu cikin tabbatarwa yace.
“Yesss Rayyern ku ɗindai kai da Ramadan, ku ƴaƴan sune na cikinsu. Sune suka haifeku”.
Ya salam tashin hankali da ba’a sa masa rana.
Gaba ɗaya Rayyern da Ramadan gigicewa sukayi.
Yayinda Jannart kuwa da Aunty Dijat da Dr Sajo suka zama kamar an dasasu ana basu labaran al’mara.
Yayinda Mamy kuwa ta saki wani irin raunataccen kuka.
Haka yasa Ramadan sa tafin hannunsa yana sharce mata hawayen.
Hafiz da Hafiza kuwa kwalamarsu kwai sukeci.
Alhaji Bala Tambari da Baba Mauɗo da Mammy kuwa Kai suke jinjina musu.
Barrister Kabeer kuwa zama ya gyara tare da cewa.
“Ci gaba”.
Numfashi Abba ya ɗan fesar kana yaci gaba da cewa.
“Lokacin dududu shekaruna sha 16, yayinda Ruƙayya kuwa lokacin shekarunta 12 ne kacal a duniya.
Rayyern kuwa lokacin shekarunsa 6 ne rak a duniya.
Kunga kenan da shekara 6 kacal nema Rukayya ta girmi Rayyanu ina tunawa lokuta da dama Rayyanu kan cewa.
Abba kayi Sa’a wlh Mamynmu bata tsufa, Ramadan kuwa lokacin shekaransa uku ne.”
Da sauri Rayyern ya riƙe kansa da hannu biyu kana cikin birkitaccen yanayi yace.
“Dan Allah kayi mgnar da zan iya ganewa, kaina bazai iya ɗaukaba tunanina zai hargitse”.
Ramadan kuwa shi zuru-zuru ma kawai yayi sa idanunsa.
Shi kuwa Abba murmushi mai ciwo yayin kana yace.
“Bari kuji yadda abun ya ya kasance, lokacin da suka ƙauro Gembu.
Ni ina yawan shiga cikin gari in mun dawo kiwo, in na shigo ina saida Su Fiya inabi da dai sauransu.
Kuma a bakin kwafar gidansu nake zama da ɗan teburunina.
Wannan dalilin yasa muka saba dasu sosai.
Har ya zama suna kwasa min aminci Alhaji Bashir amintaccen mai kuɗune mai mutunta talaka.
Haka nan Allah ya jarabceni da son yaransa Rayyern da Ramadan.
Mun shaƙu dasu sosai.
Har ya zama nike kaisu Makarantar boko, da islamiyya.
Sannan in zaune a ƙofar gidansu muddin suna gida to sai suzo wurina.
Wata rana Rayyern karatun Alqur’ani sai ya ɓata, nayi masa gyara, ashe Alhaji na jinmu.
Sai yake takvayata nayi karatun ne, nace mishi eh nayi na allo, sosaima.
Anan yake cemin ayyah ai babanshi ma na karantar da allaho dan haka in fara karantar masa dasu Rayyern mana.
Naji dadin hakan kuwa nan na fara karantar dasu, kuma Alhamdulillah kansu na ɗauka.
A lokacin
Ruƙayya kuma na tallan nono,kasan cewar gida, gida take shiga, shiyasa ta shiga gidansu.
A ranar forko suka saye nonon. ta duka to daga nanfa kullum sai tazo gidan.
Itama ta saba dasu Rayyanu sosai.
Muna cikin haka akayi faɗan ƙabilun Gembu da fulani.
A wannan faɗan ne na rasa kowa a duniya, nima din abinda yasa na tsira, dan ina cikin Gembu ne.
Ruƙayya ma haka abin ya kasance a wurinta.
Ta zama marainiya gaba da baya, dan gaba rugagenmu babu wanda ya tsira, sunyi mana illamafi muni a rayu warmu.
Mun shiga tashin hankali fiye da zaton ma sauraren.
Alhaji Bashir da matarsa, sun tausaya mana lokacin da abin ya lafa mukaje rugagenmu dasu, sosai Adda Aicha tayi ta kuka sabida ita macece mai rauni, ina tuna yadda ta ruggume Ruƙayya tana cewa.
Ruƙayya ki dena kuka ni zan zamemiki komai na duniya da kika rasa, ki kalleni matsayin tayarkin kuma mahaifiyarki, ki kalli su Rayyern kamar kanneki, ko kuma yayanki, ki kalli Babansu a matsayin babanki yayanki.
Zamu riƙeki dake da mai sunan Abban Rayyern”.
Da yake haka take kiran kasan cewar suna Bashiru sunan mijinta kenan.
To daga wannan ranarfa, muka dawo da zama gidansu.
Aka ware ɗaki akabi, ata waje.
Ita kuwa Ruƙayya daga ranan ɗaki ɗaya take kwana dasu Rayyanu.
Hakan ya sanar da wata iriyar amintacciyar shaƙuwa taban mamaki a tsakiyarsu.
Ni kuwa daga ranar Abba suke ƙirana dan karar inada sunan mahaifinsu.
Dan mahaifinsu da Baba suke kiransa.
Mahaifiyarsu kuma da Mammy suke kiranta.
Ramadan kuwa shiyasawa Ruƙayyah Mamy.
Daga nan muka zamo ahli ɗaya.
Cikin shekara ɗaya muka zamo tamkar yan uwa na jini.
Tuni Baba Mauɗo ya koya min mota,ya zama nazama kamar PA’nsa.
Sai dai banyi karatun bokoba,
Lokuta da dama, Baba Mauɗo sunayin baƙin musamman wani bawan Allah Barrister Abdulkareem Sale Dakata, yana yawan zuwa, kuma daga nan Kano yake tun forkon ƙauriwarsu da yazo ya fara soyayya da Zainab dudu cikin wata ɗaya akayi aurensu.
Na fahimci duk wani sirrin Alhaji Abdulkareem ya sani.
Kuma Alhaji yana ji dashi.
Sukayi duk mgnar sirrinsu a gabana ba tare da wani ɗarba.
Akwai wata ranar jumma’a da Barrister Abdulkareem yayi isowan dare, baima zo da motarsaba.
Da motar haya yazo, hana yasa Alhaji tadani mukaje ɗaukosa.
To muna dawowa a cikin motar.
“Barrster lafiya kuwa wannan zuwa na bazata”.
Kai jingina kana yace.
“Kamar yadda na gaya maka tun lwanaki, akan barazar da abokan tawagar abokanka sukeyi min, na in kasance cikinsu, in kuma basu dukkan bayananka na sirri, domin suna son mallakar wani sashi na musamman.
Bazan ɓoye maba harda ɗan uwana Yah Idi, shi yayi min barazana da raina dana Zainab”.
Cikin tashin hankali Alhaji yace masa.
“Zainab kuma to me tayi musu, da sayi maka barazana da ita, meyasa zasu sa mace a ciki, macema mai tsohon ciki”.
Cikin rauni yace.
“Nima sun raunatani dayin barazana da Zainab, domin cikinta ya tsufa haihuwa Yau ko gobe. Shiyasa na tattaro maka dukkan bayanka na sirri da dukkan takardunka da komai, na dawo maka dashi.
Sabida ina tsoron kada barazanar su ta raunata imanina su sani inci amanarka in basu shi”.
Cikin yanayin ɗumuwa.
Alhaji Bashir yace.
“Haba Barrister ya za’ayi kayi haka, bunada sama da iyalanmu, injidai akan Company da ake kafa Tubalinsa a kanone ya tada musu hankali.
Sukega kamar zan gurgunta musu basu da suke ganawa,
Toh kaje da takardu. Ka bawa Alhaji Bala Tambari, ya soke sa hannunsa, a dakatar da ginin, ko ma samu kwanciyar hankali.”
Haka kuwa akayi, washe gari da safe, nida kaina na kaishi gidan surkansa.
To yana gaida surkansa ya kama hanya ya koma kano da dukkan takardun sirrin dake hannunsa da komai na companyn.
Bayan ya koma da kwana biyune, kuma aka kira Alhaji taron a nan cikin Taraba.
Toni a lokacin duk inda zaije tare muke zuwa in muna gida kuwa, a bakin gate nake zama, wasu lokutan in anyi baƙi ina buɗe musu gate.
To wata rana da yamma, haka da sauri naga ya fito.
Ya shiga mota, koda na taso, sai cewa yayi in bari.
Rayyern kuwa dake gefena da sauri ya taso yaje ga mahaifin nasa, tare da cewa.
“Baba nima zanje”.
Ganin yadda yaron ya tsareshi da idanune yasashi cewa.
“Toh Mauɗo na muje”.
Da yake mafi akasarin lokuta haka yake kiransa.
Ramadan kuwa lokacin bacci takeyi.
Haka dai suka tafi tare,
Har zuwa ƙarfe sha ɗaya na dare basu dawoba, hakanne yasa.
Mammyn ta fito wajena ita da Ruƙayya, dan har lokacin Ramadan yana wurina.
Amsar Ramadan tayi a hannuna kana, ta juya tayi ciki.
Ita kuwa Mammynsu cikin fullacin da bata gama iyawaba, dan ita asalin ƴar ƙasar Ethiopia ce.
“Abba Rayyarn yau kuma lfy kuwa har yanzu Baban Mauɗo da Rayyern basu dawoba.
Gashi nayi ta kiransa yaƙi shiga”.
Cikin alhini nace mata.
“Toh kinsan kuna cewa, wannan abun shi neturom ne ko netyuk ɗin har yanzu baida ƙarfi a nan jihar tamu, naga shima kansa Alhajin wasu lokutan sai ya hau kan wancan dutsen yake samu yayi mgn”.
Shiru naga tayi sai kuma can ta ɗan kalleni tare da cewa.
“Nifa ina tsoro domin ya shaida min abokansa ne da sukeyin komai tare sun kuma san abubuwa da dama a kansan sun juya mishi baya, asalima har barazanar hallakashi sukeyi damu duka.
Gsky hankalina ya tashi, ina tsoron mutanen kasar nan”.
Da sauri nace to ta bani wayar inje in hau kan ɗan dutsen da nake ganin Alhaji na hawa yayi mgn da mutanensa, dan a lokacin duk faɗin Gembu membila mutun uku ne kacal keda wayar hannu kuma sai sun hau dutse suke kira, a lokacin kuma layi yafi waya tsada.
Koda na amshi wayar sai ta koma ciki.
Ni kuwa nayi ta gwada kiransa amman sam baya shiga.
Nima kaina hankali na ya tashi, haka yasa nayi ta zama a wurin har dare ya fara nisa har na yunƙura zan tashi sai kuma naji ƙaran wayar, da sauri na danna inda ta nuna min,
Ina kaiwa kunne kuwa naji murtar Alhaji cikin wani irin gigitaccen yanayi mai bayyana azabar da yake ciki, cikin yanayin wasiyya yace.
“Aicha!”. Da sauri nace.
Ba ita bace nine Bashiru”.
Cikin wani irin numfarfashin naji yace.
“Bashiru ina take?”.
“Tana gida, bari in kai mata”.
Na bashi amsa sai kuma naji yace.
“Da wuya ka isa inda take ina raye, kayi sauri dai kaje, ka ɗaukesu ku gudu, Bashiru ni bazan rayuwa, sun turani cikin ramin kogi, yanzuma ɗan zaren bakin gaba na samu na riƙe, kuma yaushe zai iya tsinkewa,
Rayyanuna kuwa na wurgashi can gefe, kazo ko ni ban rayuba Rayyern ya rayu.
Bashiru kayi maza kaje gudu dasu.
In in ka ɓoyesu ka kuma samu dama, kazo ka ɗauke Rayyern a daren nan.
Sannan ka tuna gidan da mukaje da kai a Kano, a wannan ƙaramin sashin na waje, gidan a ciki duk wasu takardun abinda na mallaka da duk wata dukiyana suna, ciki”.
A takaice dai anan ya gaya min dukkan sirrukansa tare da damƙa min amanar yaransa, ya shaidamin akwai tarin dukiyar ɗaya ware na aikin campanyn suna ciki wannan sashi, ya kuma roƙenin da in bawa su Rayyern kekkyawan ilimin boko, ya kuma cemin baya son yaransa suyi maraici.
Ya ɗaura da cemin tun ɗazu fa wanda ya turasa cikin ramin yayi nufi gidansa dan yaji yana cewa zaizo ya kashe sauran yaransa, yacemin ya goya Rayyern a jikin bishiyane a bakin gaɓar, kuma an bubbuga bishiyar amman dai baiga faɗowan Rayyern.
Ni kuwa dai-dai lokacin na iso ƙofar gidan.
Ga mamaki na sai naga gidan yanaci da wuta.
Makota duk sun fito sun tsaya cirko-cirko an rasa yadda za’ayi su shiga gidan.
Haka yasa na saki kuka ina cewa.
“Innalillahi wa innailaihi raji’un, sunbi sun kashe su”.
Dai-dai lokacin kuma naji Alhajin yayi mgn da ƙarfi a cikin wayar yace.
“Sun kashemin mata ɗan Bashiru?”.
Sai kuma naji suuuuuuu zinɗim alamun ya faɗa cikin azabebben ramin.
Wannan abun ya gigitani yasani.
Kurma ihu na nufi cikin gidan ina cewa.
“Sun kashe Alhaji da Rayyanu sannan sunzo sun bankawa gidan wuta, wayyo Adda Aicha.
Can najita, tana amsawa tana nufar ɗakin Ruƙayya tana cewa.
“Ruƙayya! Ruƙayya!! Fito keda Ramadan”.
Ina muna iso bakin ƙofar wuta ya rufe ɗakin nasu.
Ihu Adda Aicha tasa tare da juyawa ta fice daga gidan tana faɗin shike nan, sun hallaka min ahlina gaba ɗaya, mezanyi da Nigeria garin mugaye.
Daga nan ban kuma ganintaba, ban kuma jintaba.
Dai-dai lokacin kuma aka kece da ruwa kamar da bakin kwarya.
Duk da wannan ruwan wutan saida ya kara kusan awa biyu yanaci kafin ya mutu.
Washe gari da safe aka shiga ciki, toh fa nan muka samu Ruƙayya da Ramadan a sume a cikin Bathroom, bisa alamu hayakine ya sumar dasu,
hakane yasa muka tafi asibitin cikin taraba dasu.
Bayan an basu gado, ni kuwa na sake dawowa bakin gada, inata dube-dube cikin ikon Allah naga Rayyern a goye a jikin bishiya saidai a sume yake. Kuma kanshi ya fashe yanata zubda jini, har lokacin yayi wani irin fari fat alamun jininsa ya ƙare, kwancesa nayi na kaisa asibitin.
Sanin anyi gobarane yasa aka amsheshi a sibiti.
Watanmu ɗaya kafin suka samu lfy, cikin ikon Allah Sarkin Gembu shine ya ɗauki nauyin niyyar.
Alhamdulillah duk sun samu lfy, sai daifa Rayyern ya samu matsalar kwakwalwarsa ta mance baya.
Shiyasa ya taso bai iya tuna abinda ya faru dashi daga haihuwarsa zuwa shekara bakwai.
Ramadan kuma a hankali ya mance iyayensa.
Haka nayi ta zama dasu a Gembu cikin gidan Sarkin Gembu.
Harda Ruƙayya, wacce nai tunanin ita kaɗai ce zata tayani rike amanar da aka bani domin munyi neman duniya babu lbrin Adda Aicha.
Nan nace ina son muyi aure da ita, dan mu rani yaran.
Haka yasa aka ɗaura mana aure.
Daga baya muka shirya muka taho kano, koda mukaje Kano kai tsaye wannan gidan muka nufa.
Kasan cewar gidane da ya ginawa a sirri dan ko iyayensa basu saniba.
Kuma dama takardun gidan da key ɗin duk da wasu tarin takardunsa nasan inda yake ajesu.
Shiyasa na ɗauka mukaje muka zauna a ciki.
Nasa Rayyern da Ramadan a Kekkyawar makaranta, na kuma saya mana motar da nakeyi musu dukkan hidima dasu.
Ni kuwa na zama kamar mai gadin gidan Ruƙayya kuwa mai gyaran gidan da rainon, aikin da muke ne muka warewa kanmu albashi kamar yadda mukaji ake biyan masu irin aikimu da wannan kuɗin nakeyi mana komai na aiki.
Su kuwa su Rayyern inayi musu komai da dukiyar mahaifinsu. Dan ko mota dana saya dan kaisu makarantane.
Su kuwa sun taso a duniya su basu san kowaba sai mu.
Dan ko gambu bana kaisu.
Na kuma ƙi kaisu wurin dengin mahaifinsu wato gidan Kakansu Malam Mai Nasara ne sabida inaga kamar magautan zasu iya ganesu ta sanadin zuwan su biyomu su kashesu.
Gashi mukuma Allah bai bamu haihuwa ba, sai suka zame mana yayanmu.
Bana harka da kowa dan gudun kada a ganomu, na hanasu yin abota da kowa.
Saida suka girmane Sanadin karatu dole Rayyern yayi abota da Dr Sulaiman.
Ramadan kuwa har yau baida abokin ko ɗaya.
Usman PA maigadin maƙocinmu ne ya haɗani dashi da wutanmu ya ɓaci ya gyara man sanadin haka suka saba da Rayyern har ya zama PA’nsa.
Na gina su Rayyern kan ƙin yarda da kowa, shiyasa baya sakin jiki da kowa a rayuwarsa.
Baya amsa gayyatan hiran yan jarida ko ta inane.
Sunyi kekkyawan karatun likitanci, dan nasan burin mahaifinsu ne dan shima likitane, to amman yafi bawa kasuwanci himma.
Nasan idan su Rayyern suka gane Malam Mai Nasara kakansune to gaba ɗaya ko wanne asirin zai tonu.
To amman duk da haka inada niyar dole watan-wata rana zan gaya musu gsky.
Ɗan tsagaitawa yayi tare da sauƙe numfashi.
Yayinda saura kuma kab sukayi shiru.
Rayyern da Ramadan kuwa,
Hawaye kawai suke zubdawa.
Shi kuwa Abba Barrister Kabeer ya fuskata a hankali yace.
“Tun randa kazo min da batun zaka bawa Rayyern auren Jannart ka kuma gaya min sunanka, na gane tabbas kanada alaƙa da Barrister Abdulkareem Sale Dakata, domin ksunanku.
Koda na kwakkwafi Jannart bayan aure kuma na gane ɗan uwanka ne.
Yanayin yadda bada auren Jannart da yadda komai ke tafiya, da tuno kalaman Barrister Abdulkareem, na gane duk abinda kake boyewa akan Jannarr, na kuma gane akwai wani abinda ka sani a kanmu shiyasa na amince a sauƙaƙe”.
Cikin sauƙe Numfashi Dr Sajo yace.
“Barrister Kabir shaida musu”.
Cikin sanyi yace.
“A’a muji yadda akayi Alhaji Bashir ya rayuye dai tukun da yadda Hajia Aicha ta rayu”.
Jin hakane yasa Baba Mauɗo gyara zama tare da fara basu lbi
“Ni a waccar naran koda naje, cikin Gembu membila sai na samu, ashe harda su Alhaji Bala Tambari dasu Alhaji Audu Tababa da kuma Alhaji Ahmed Tinkau da Alhaji Idi Sale Dakata, da kuma Dr Lukman, da dai sauransu za’ayi zaman. Nayi mamaki domin wannan taron iya na mutanen tarabane.
Sunyi duk yadda zasuyi da in haɗa hannu dasu naƙi, wanda hakan ya tunzurasu, sukayi ta gayamin duk abinda sukaga dama.
A karshe dai da faɗa aka tashi, yayinda duk abinda mukeyi Rayyern na kan cinyarta.
Ina fita wurin Alhaji Idi yace.
Ba sai na rayuba kan inyi musu turji, yace dani da Lawyer na duk sai su ɗai-ɗai tamu.
Furucin daya bani tsoro kenan.
Saidai ban kulaba na shiga mota na kama hanyar Gembu, duk da dare yayi.
Ina tafiya Alhaji Bala Tambari ya kirani a sirrance kamar kullum shike sanar dani duk shirinsu.
Ya shaida min cewa fa, an turo mai babbar mota kan ya takani, ya kasheni ya kuma je da fetur ya ƙona min gida.
Hakan yasa na ƙara gudun mota, ga kuma hadarin da iska da akeyi.
Tafiya kaɗan kuwa nayi Baga mai babbar mota na bina, duk inda nayi sai ya bini hakan yasa na gane shi aka turo
A haka dai ya samu ya turani cikin ramin to kafin in faɗa sai na fita cikin motar lokacin daya tokareta da bishi.
Gaba ɗaya naji ciwo, hakama Rayyern to sai na cire rigata na goya Rayyern a jikin wata bishiyar dake ɗan gefe kaɗan da wacce ta tokari motata.
Na juyo zan dawo bayan Rayyern ɗinne kuma, tsantsin ya ɗebeni na tafi cikin ramin to ban faɗaba, na riƙe sirarun jijiyoyi bishiyar.
A haka ina reto na kira Bashiru nayi mishi dukkan bayanan sirri na.
Hankalina ya tashi lokacin da naji yana cewa, an bankawa gudana wuta, babu wanda na tuna sai Ramadan da Ruƙayya, dan sai nakeji Aicha zata iya tsaratar da kanta, amman su yarane.
Wannan kaɗuwanne tasa na faɗa cikin ruwan Kogi mai masifar zurfi, daga nan kuma ban sake sanin inda nakeba, sai farkawar nayi na ganni a wani babban asibiti Alhaji Bala Tambari na gefena.”
Shiru yayi alamun ya gama.
Murmushi Alhaji Bala Tambari yayi ganin yadda duk suka zuba mishi idanu alamun neman ƙarin bayani.
Zamanshi ya gyara tare da kurɓan ruwa kana yace.
“Tun da na gaya masa ana binsa nima na biyo bayansu ba tare dana gayawa munafukan banzanba da nufin in dakatar da direban babbar mota sai dai ina na makara.
Domin ina zuwa motar na faɗawa, cikin ramin shi kuwa ya wuce cikin gari,
Tashin hankali yasa na kasa tuna ya dace in bisa in tseretar da yaran.
Sai daga baya na tuna hakan.
To koda naje cikin garin sai na samu tuni an ƙona gidan.
Haka yasa kawai na wuce cikin jama’ar ina cewa a nuna min gidan Sarkin ruwa.
Nayi sava kuwa aka kaini, dan duk a tunani an rigada an gama da waɗannan kam, shiyasa nake son a ceto Alhaji Bashir da yaƙinin nasan yana da baiwar iya riƙe numfashinsa na wasu lokutan.
Koda aka haɗani da Sarkin ruwa, ce masa nayi motar ɗan uwanane ta faɗa cikin ruwa muna zuwa, dan Allah ya taimaka min.
A nan yacemin gsky baya tsammanin ɗan uwana zai rayu, domin babu wani wanda ya taɓa faɗawa cikin ramin nan ya tsira, domin ruwan bai cika gudu Bama.
Amman irin ranar ruwan zai iya gudu ya amayar da abin cikin ramin sabida yadda ake ruwa kamar da bakin kwarya.
Anan yace min, sai dai a tsammaci gawar ɗan uwan nawa, dan haka inje in sanar a matatar ruwan kiri dam.
Kana ya haɗa da kiramin Sarkin ruwan dake can ya sanar musu da gashi-gashi abinda ke faru ya ƙara da cemin.
“Sarkin Ruwan kiri dam dashi da aljanu marabarsu kaɗan, domin shi yakan iya yin kwana hamsin cikin ruwa, kuma babu matatan ruwa da baya zuwa, zai iya taimaka min sai dai zai cajeni kuɗi da yawa, jin haka yasa nace babu komai ko nawa ne zan biya.
Toh a daren na kama hanyar kiri.
Cikin ikon Allah kuwa kafin asuba na isa.
Kai tsaye bakin dam ɗin na wuce.
Allah mai yin yadda yaso a lokacin da yaso.
Kafin in isama an tsamoshi a cikin ruwan saidai baya da maraba da gawa.
Kwanana goma sha ɗaya a can, kafin muka samu ya farfaɗo daga dogon sunan da yayi,
To sai dai fa ya rasa tunaninsa.
Haka yasa a sirrance na ɗaukoshi na dawo dashi, gidana dake Gombe acan akayi ta jinyarsa har ya samu lfy, amman tunaninsa bai dawoba.
Kasan cewar yana yawan zama da Mai gadin gidama na can da yake buzune suka saba sosai.
Har da zai tafi garinsu sulaje tare,
Saida yayi shekara Goba sha uku acan amman ni ina zuwa ni kuwa naji daɗin zamansa can sabida yafi sirri zamansa acan yasa ya koyi duk yarukansu da kuma shigarsu d ta zame masa jiki.
Sai shekaru goma baya ya dawo, nan mukaci gaba da zama dashi, har tsawon shekara ashirin ba ɗaya.
Kawai ranar ya fita yaje masallaci yana dawowa mota ta bugeshi.
Bugunma bana kirkiba sai dai ya suma, tofa yana farfaɗowa ya farfaɗo da tunaninsa kwakwalwarsa ta dawo ras.
Babu abinda yake cewa sai.
Rayyanuna Ramadan ɗina, Bashiru ka kula min dasu, ka kula da maraicinsu dana Ruƙayya kada ka bar Aicha ta ƙasarsu da yarana”.
Wannan abun shi yafi komai yimin daɗi.
Daga nan aka sallamemu nan nayi masa bayanin komai.
Tofa daga ranar ta tada hankali sai munzo Kano.
Yayinda a wurin su Alhaji Idi Sale Dakata kuwa, nake cikinsu dan sanin duk ƙullinsu.
To koda muka zo Kano kai tsaye nan gidan yace muzo.
Muna zuwa kuwa ya ganka a ƙofar gidan kaida Rayyern da Ramadan bisa alamu masallaci zaku tafi.
Yana ganinku yace ga yayansa.
To kuma ni kaina na gamsu dan tsananin kamar da Rayyern keyi dashi.
Ramadan kuma da an ganta ansan Aicha ce ta haifesa.
To dole muka koma mukayi sabon shiri, haka yasa yazo muku a suffan buzu yana neman aikin gadi. Kai kana ganinsa sai kayi ta kallonsa har saida yayi ta maimaita maka mgn cikin muryar buzaye sannnan ka girgiza masa kai, da alamun jikinka na rawa a lokacin.
Rayyern kuwa sai yayi saurin cewa.
“Dan Allah Abba mu ɗaukehsi aiki ka dena buɗe mana gate dayi gadin ƙofar gida bamajin daɗin haka.”
Ni kuwa duk mgnar da kukeyi a waya nake jinta.
A karshe dai yaran ne suka dage dole ka ɗaukeshi. Shi kuwa ya rayu cikinku domin ya gane wanne yanayi kuke ciki.
Yasha zuwa wajena a boye muyi mgnar sirri.
Kai kuwa ka yarda dashi yasa har ka nemi shawarsa kan aikin campanyn, ya baka shawarar a fara ginisa kuma ka yarda, cikin hikima yasa akeyin komai cikin gaggawa.
Koda Riyyam-nsra yazo kawai cemin yayi wallahi ɗansa ne”.
Ya ƙare mgnar yana dariya.
Cikin sanyi Mamyn Rayyern ta kalli Mammyn tare da cewa.
“Dan Allah Aicha ya akayi kika bar ƙasar nan”.
Cikin sauƙe numfashi farin ciki Mammy tace.
“Lokacin da naji Abinda Bashiru ke cewa sanda gidan yaketa ƙonewa yana cewa.
An kashe Alhaji da Rayyanu sannan an kashe su Ramadan.
Daga lokacin na fita gidan to a ganina Meta rage min da Nigeria, da a mahaifiyata batason aurena da Abbansu Rayyarn wanda kasuwancine ya kaisa ƙasarmu Ethiopia har muka kulla soyyaya, kasan cewar dama mahaifina ya rasu, kuna Ni kaɗai suka haifa shiyasa Didi na batason auremu, a ƙarshe dai bada yardarta akayi aure ba, randa muka taho Nigeria tayi kuka kamar zata mutu niko son da nakewa mijina yasa na daure muka zo.
Alhamdulillah ahlinsa kab suna sona. Cikin aminci muke zama da kekkyawan zaman lfy.
Har na haifi Rayyern da Ramadan kafin mukaje Ethiopia lokacin shekaran Ramadan biyu a duniya.
Muna dawowa ne muka koma Gembu membila.
To shiyasa wannan abin na faruwa na tattara na koma ƙasata ta haihuwa kuma a lokacin inada cikin Riyyam-nsra da Zaiton har na wata huɗu.
Shi ya sani.
Naƙi in sallami iyayensa ne dan naji gaba ɗaya ƙasar na tssneta bana son komai ma ƙasar gani nake ƙasace da babu amana, a nan diganmu dake can bayan gida babanshi naje na ɗauki E password na da komai nawa, a ciki kuma nayi ta zama ba tare da sanin kowaba, har komai na tafiyana ya kammala.
Na tafi, gidan babansa kuwa duk sun shiga tashin hankali jin labarin rasuwarsa dan har can ƙaninsa Mustahpa yaje to amman dan ba’a sansaba anki a sauraresa. Dole ya dawo sukayi ta zaman makoki, amman Malam yaƙi amincewa shi cewa yake shifa Ɗansa da jikokinsa na raye, su kuwa yaransa sai dukega mutuwarce ta gigitashi.
Nima a zatona su Rayyern basa raye, shiyasa banda bin ta kan Nigeria ba sai dai ina yawan gayawa su Riyyam-nsra cewa su asalin ƴan Nigeria ne ina basu lbrin komai.
Sai ranar da naga gidajen tv’n da jaridun ƙasarmu suka rinƙa haska hoton fuskar Rayyern ne a matsayin wanda ya taimaki ƴar wani babban ƙusam gwamnati, ina ganinsa naji a jikina ɗanane, ganin sunansa ya ƙara bani ƙarfin guiwa, musamman in na duba kamarsa da Riyyam-nsra da kuma kamannin mahaifinsu, haka yasa na amince da nacin Riyyam-nsra na son zuwa.
Kana shi kuwa dake ɗan rawan kaine yana bibiyan mutanen ƙasarnan a shafukan sada zumunta.
Anan yaga Ahmad Nasir har suka saba, sai daga baya muka gane shi ɗan ƙawar babansune.
Shi yan ywansane shiyasa nace muku.
Ta ƙare mgnar tana shafa kansa.
Jannart kam har yanzu hawaye take zubdawa.
Shi kuwa Baba Mauɗo cikin fargaba yace.
“Alhaji Bala Tambari kullum tambayarka nake ina Barrister Abdulkareem Sale Dakata amman kaƙi gaya min komai a kansa yau tsawon shekara uku kenan ina tambaya, tunda kaƙi sanarmin barin in tambayi Kabiru”.
Ya kare mgnar yana fuskantar Barrister Kabeer.
Shi kuwa Alhaji Bala Tambari wani irin raunataccen kukane mai sassayan sauti ne ya subce mishi.
Shima Barrister Kabeer kukane mai sassayan sauti ya saki.
Yayinda tuni Aunty Dijat ma ta kife kanta bisa cinyarta.
Cikin tsananin tashin hankali Baba Mauɗo ya matso gaban Barrister Kabeer murya na rawa yace.
“Kabir ka tunani ko?”.
Kai kawai ya gyaɗa masa yana mai sakin shessheƙan kukan da yasa jikin Jannart fara wani rawa mai haɗe da tasowar kuka.
Shi kuwa Baba Mauɗo cikin taraddadi yace.
“Kabiru ina Barrister Abdulkareem inayake? Ina Zainab? Me ta haifa?”.
Cikin tsananin kuka Barrister Kabeer ya ɗago kansa tare da nuna masa Jannart…!
Ban samu nayi editing ba sabida zazzaɓin mura ɗaya rufeni, zakuga kurakurai da yawa, duk na san zaku kage in sha Allah.
By