Sirrin Rike Miji

Namijin Da Mace Bata Iya Mantawa Da Shi Duk Tsawon Zamani

NAMIJIN DA MACE BATA IYA MANTAWA DA SHI DUK TSAWON ZAMANI……..

 

✍ Wanda ya iya sauraro, zai saurari zancen ta kuma yana maraba da shi na daidai da rashin daidai, cikin kulawa da biye mata, baya kushe ta ko gwasale ta.

✍ Wanda baya wasa da abin da ya shafe ta me daďi ko mara dadi sai inda qarfinsa ya qare.

 

Karanta>>> Abubuwan Da Yakamata Ace Kayi Bankwana Da Su Bayan Kayi Aure

 

✍ Namiji me juriya da Haquri da ita sosai kan daidai da rashin daidai dinta, me mata fada da nasiha cikin kulawa.

✍ Me yawan kyauta, me fara’a me iya bayar da kulawa, kamar yi mata tausa idan mijinta ne lokacin da ta gaji, yi mata sannu da zuwa idan ta dawo daga unguwa da tambayar ta hanya, kiranta idan tayi tafiya yaji ya ta sauqa ko ya ta kwana? Idan tayi wasu kwanaki zata dawo har yayi mata girki idan yana Gida ko ya ajiye wani abu domin ta, wanda baya son ya bata mata Rai da ganganci yana kula da motsinta sosai na farinciki ko damuwa, yayi iya yinsa wurin ganin tayi nishadi idan damuwa ce.

 

Karanta>>> Zafafan Kalaman Soyayya Don Samari Da Yan Mata Har Ma Da Ma’aurata

 

✍ Wanda zaiyi wasa da ita, ya tattauna da ita, ya shiga Lamuranta sosai da sosai.

✍ Wanda ko yaushe yake son cigabanta da ganin Burinta me kyau ya cika indai yana da yanda zaiyi.

 

Karanta>>> Hadin Sabuwar Mace – Malama Juwariyya

 

✍ Me girmama komai nata da kowa nata, me girmama ta da Daraja ta, da tsayuwa kan tsare mutuncinta.

Duk macen da ta Rayu da irin wannan Namijin da wuya ta qara jin dadin Rayuwa da wani a Duniya, wasu sun samu suna wasa da irinsa, wasu basu samu ba suna neman irinsa.

 

Karanta>>> cikakken Tarihi  Malama Juwariyya (phone number)

 

Allah ya zaba Alkhairi . Ameeen. Kada ku manta da Sharing domin yan uwa su

Back to top button