Uncategorized

Wace Ce Ita 9 Complete Hausa Novel

    WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

   Unique Barakancy

       NINE📍

          Kokarin zare nose mask dinta yake burinsa kawai yaga fuskarta dan ba karamin tada masa hankali idanuwanta sukayi ba,toh ido ma kenan inaga fuskarta?… Kauda fuskarta tayi kafin hannunshi ya sauka kan nose mask din,kara kai hannunsa yayi,kafin ma hannun ya karasa yaji saukar mari akan fuskarsa,kafin yagama tantance abunda ya faru ta sake sharara masa wani marin,sannan ta raba gefensa ta fita……….

Binta da kallon mamaki da al’ajabi yayi,bazai iya tina yaushe wani ya maresa ba tin yana yaro har izuwa girmansa,sai yau wata lady da ko saninta beyi ba,ta kalli tsabar idanunsa ta sharara masa maruka har guda biyu,shi kuma kamar shashasha ya kasa cewa komai,wai shi ‘the whole sameer’ wata ta mara? Unbelievable!……. “Toh WACECE ITA?” Ya fada yana karabin hanyar databi da kallo,ko alamunta be gani ba bare wata halitta me kama da ita….. Parlourn ya karasa cikin muryar fushi yana kwallawa khaleel kira,shiru ba amsa,sama ya nufa yana neman khaleel ido rufe dan yasan shi kadai ne ze basa amsar wacece ita,ganin khaleel baya bedroom dinshi yasashi  kiransa a waya,nanma haka wayar yayi ta ringing be dauka ba… Sai ya shiga hargitsa gidan yana duba ko ina na gidan kamar wanda akasa ya nemo wani abu,saida ya hargitsa ko ina na gidan sannan ya hakura ganin bega khaleel ba,fita yayi zuciyarsa ciki da san sanin wacece ita da kuma abinda takeyi a gidan khaleel……

      Tana fita ta mayar da shades dinta ta gyara zaman nose mask dinta,tafiya tayi me nisa kafin ta tsaya da nufin tsaida cab…….. Kamar daga sama taga mota ta parker a gabanta,whining glass din motar yayi yana mata murmushi,zaro ido tayi tana mamakin ganinsa,A hankali tace “How comes?”… Murmushi yayi yace “Ai kema kinsan ko ina kike ina nan,I can’t leave without you”…. Bude front sit tayi kawai ta shiga…… Tada motar yayi yana cewa “kin kyauta ai,shine tafiya babu sallama”….. Hmmm kawai tace…. Kallonta yayi ya kuma cewa “kinsan dole zan damu amma kikayi tafiyarki,kuma kika sauka a gidan saurayinki,is that right?”……. Hade rai kawai tayi bata ce komai ba….. Chan kuma sai tatuno da incident dinsu na jiya da khaleel,kwashewa da dariya tayi tana cire shades da nose mask…. Questioning look yamata yana binta da kallo,nan tashiga bashi labarin yanda sukayi da khaleel,dariya sosai suka shigayi,sannan yace “shi din banza,da so yake ya shiga hurumin daba nashi ba,lallai ma yaronnan,bari nima in baki labarin shashashan chan daya dinga binki a Nigeria” Nan ya shiga bata labarin yanda ya daki motar Deen,ya karasa da cewa “yana chan nasan yana jinya inma be mutuba tinda ya dauko ruwan dafa kansa,an fadamasa ana tabamin ke a zauna lfy ne?”…. Wata muguwar dariya suka saki me kunan rai wanda idan ace mutum na kusa dasu sai yaji ransa ya baci……

A wani hadadden restaurant yayi parking bayan ta sanar dashi tanajin yunwa,parking yayi ya umarceta data maida nose mask da shades dinta…. Mayarwa ko tayi sannan suka shiga ciki,VVIP section suka nufa,daga ita sai shi a wajan,menu aka kawo,yace su mayardashi kawai su kawo komai sai taci wanda takeso,haka ko a kayi aka cika musu table makil da abubuwa,dan tsatttsakura tayi tace mishi ta koshi kawai su tafi…….. 

So take taje tayi main mission din daya kawota amma ta hakura saboda bataso ya sani,yanzu kuma tinda yazo tasan ko ina tasa kafa saita ganshi…… Ganin kamar akwai abinda take sanyi ne yasashi tambayarta “yaushe zaki tafi?”… Kallonshi tayi tana ayyana yanda ya bata mata plan,tasan baze taba barinta tayi yawo ita kadai ba,ko waya basayi kwatsam saidai ta ganshi a inda take,har gwara a Nigeria akwai lokutan da suke planning haduwa,apart from that saidai kawai ta ganshi from no where…….

Dubawa tayi taga bata da mafita,zamanta a kasar kuma ya zama useless,sai kawai ta cemasa ”I’ll be leaving tomorrow”….. Murmushi yayi yace “okay,tare zamu koma kenan”… Gyada kai kawai tayi tana cigaba da kallonsa,zata iya cewa tinda take a rayuwarta bata taba ganin kyakkyawan namiji kamarsa ba,komansa is just perfect,karyar mace ta masa kallo daya ta dauke kai,gashi he has loved her right from day one,kawai dai wasu abubuwan nashi ne bata gane kansu…….. 

After few minutes tace masa ya mayarda ita gidan khaleel zataje tayi shirin tafiya,bece komai ba ya juya kan motar,ya dauki hanyar gidan khaleel……. “Won’t you ask for the address?”… Ta tambayesa….. Yar karamar dariya yayi yace “Karki damu ai indai akanki ne I need no direction”…… Batayi mamaki ba dan taga abinda yafi haka daga garesa……… 

Parking yayi a daidai cottage din khaleel,tabe baki yayi ya zira hannunshi a dashboard din motar ya zaro wani dan karamin box ya mika mata,karba tayi batace komai ba ta bude motar tana kokarin fita…. Binta da kallo yayi kamar ya hadiyeta yace “I love you”…. Batasan ya akayi ba kawai taji bakinta ya furta “I love you too”,sannan ta shige ciki da sauri…….

           Kwance ta tarar da khaleel yana bacci akan three sitter dake parlour,kana ganinsa kasan baccin bana kwanciyar hankali bane……. Takunta kawai yaji ya bude ido da sauri,dan dama baccin kusan kamar da ido daya yakeyi….. Fakan idonta yayi ya nufi sama a guje…. Binshi tayi tana dariya kasa kasa….. Karasawa kofar bedroom dinshi tayi ta murda saita jita a rufe,kwankwasawa ta farayi da karfi sannan tace “khaleel open this door now!”……

“Dan Allah kiyi hakuri,I’m sorry”….. 

“Ni babu abinda zan maka,magana zamuyi,I’m going back tomorrow”….. Sai kuma yaji beji dadi ba datace zata tafi,a tinaninshi kuma shine silar komai……. A hankali ya bude kofar ya fito,sai kuma yaji shi normal,duk wannan tsoron daya dingaji akanta ya kau…… “I’m really sorry wifey for everything,believe me sharrin shedan ne ki gafarce ni bazan sake ba,dan Allah karki tafi gobe”…… Ya fada kamar zeyi kuka…… Girgiza kai tayi tace “I’m leaving tomorrow,period!”…… “ To baki ce kin yafemin ba,pls forgive me”….. “I’ll think about that” Ta fada tana shigewa dayan bedroom din………

         It was a silent trip for both of them,kowa da abinda yake sakawa a ransa har suka iso Nigeria,suna karasowa parking lot ta nemeshi ta rasa as usual,karasawa inda drivernta yayi parking tayi,bude mata motar da sauri yayi tashige,wani book list na duk inda take zuwa ya mika mata,nuni ta mishi da school…… 

        Mama ce zaune a gaban wani mallamin tsubbu,dube dube yake mata kamar yanda ya saba mata a kwanakinnan…… Dubanta malamin yayi yace “yau tashigo kasar nan”…. Murmushi tayi tace “Yauwa,yanzu yaushe zaa fara aikin mallam?,so nake a hallakamin ita gabadaya tabar duniyar”….. “Hakan zeyi wahala kai tsaye dan wannan yarinya akwai rikici a al’amarinta,amma akwai wasu yan dabaru da zamu iya akan hakan,saidai mu miki aikin da ze cutar da ita a hankali har ta mutu”…… Wani mashahurin farin ciki mama hafsah taji a ranta,ita yanzu a duniyarnan babu wanda takesan ganin bayanta kamar fatima zainab,akan hakan kuma ba abinda bazata iya kashewa ba…….. “Hakanma yayi daidai mallam,in dai har wataran zata bar duniyar gabadaya shikenan,yanzu yaushe zaa fara aikin?”……

“Idan zamuyi aiki iri wannan muna duba lokaci ne,musamman in meshi ya kasance me ibada,saboda haka zamu bi abin a sannu”……. 

“Wacece me ibadar mallam?,nifa yarinyarnan wataran ma sai inga kamarfa bata sallah”…….

“Kece dai bakisani ba,amma a dubiyar da nayi ni naga hakan,kamar yadda nace miki zamubi komai a sannu”……

“Toh shikenan mallam,saura maganar alhaji,ina matukar so na koma dakina dan nasan komai sai yafi tafiya daidai in ina chan,ga bilkisu(Momma,mahaifiyar khaleel) nasan ta baje tana jin dadin an sakeni,shiyasa nakesan kamin aiki me karfin da ko na koma sai yanda nayi da alhaji”…..

“Baki da matsala da wannan in dai zaki saki kudi hajiya”…….

“Kudi ba matsala bane,indai bukatata zata biya mallam”…….. 

(wa iya zubillah,Allah ya tsaremu da kishiyoyi irinsu mama da duk wasu masu bin malamai,wayanda sukeyi suma Allah ya ganar dasu sudaina tin kafin duniya ta musu karantun ta nitsu)

          Sosai Dad yakewa likitocin asibitin bala’i rai a bace,tin jiya ya shigar da kara akan case din,kasancewarsa me mugun kudi kuma masu fada aji a Nigeria yasa aka kama Doctors din dake on duty ranar,ya kuma rantse bazaa sakesu ba sai yaga danshi sai kace deen din wani karamin yaro ne,ya kuma dage akan insecurity dinsu ne da har patient ze fita baa ganshi ba,tabbas yasan Deen da kafafuwansa ze gudu amma kuma harda sakacin hospital din,lallai haduwarsu da Deen bazeyi kyau ba…….. 

        A hankali take takowa cikin hostel,saitaga yadan chanja mata,kodan kusan two weeks kenan rabanta da hostel din,binta da kallo suka shigayi kamar yadda suga saba itako ko a kwalar rigarta,tafiya ta cigaba dayi harta karasa room dinsu,da sallama ciki ciki tashiga…… 

Eesha dake zaune tana tinanin datasaba,kamar a mafarki ta hangota dukda ba irin shigar data sabayi bane amma tasan babu wanda zeyi irin wannan shigar inba itaba…..,

Tashi tayi ta nufeta da sauri ta rungumeta tace “I miss you so much,kullum da tinaninki nake kwana nake tashi,where have you been for more than a week?,bansani ba ko sabida ni kikaki dawowa,toh kiyi hakuri”….. Janye eesha fatima zainab tayi tana mamakin yaushe suka fara wannan wasan da wannan yarinyar,wai hardasu ko sabodani kikaki dawowa,to ita a wa zataji tsoron dawowa dan ita……

Bata kulata ba ta karasa bed dinta,binta eesha tayi tace “Yanzu nagama girki,in zubo miki sis?”…….. Dauke kai kawai tayi surutun yarinyar harya fara takura mata,Itako eesha ko a jikinta sai zuba take dukda taki kulata,dama batasa ran zata kulata ba…..

Ganin abun ya isheta yasa ta dibi wasu abubuwa ta nufi hanyar fita,riko hannunta da sauri eesha tayi tace”Dan Allah kiyi hakuri karki kuma tafiya,indai nice nayi shiru,bazan kara damunki ba”….. Haka kawai ta samu kanta da girgizawa eesha kai alamun ba saboda ita zata tafi ba sannan ta fice da sauri gudin kar eesha ta kuma cewa wani abu…….

Eesha ko wani dadi ne ya kasheta ganin yau bata tureta ba duk uban surutun data mata,gashi harda body language ta mata magana,meaning there’s a good improvement…… “Yessss!” Ta fada tana dialing number aminiyar mom dinta…….

         Transcorp ta nufa straightly tanajin yanda gajiya kebin duk ilahirin jikinta,sai a lokacin tayi danasanin zuwa hostel,gashi wanchan yarinyar hartasa mata ciwon kai,wanka da sallah tayi sannan tasha abunda ta saba,nan da nan ko bacci ya dauketa…

     The next day

   Around 10am yana zaune a cikin motarsa kamar yanda ya maida hakan farilla a yan kwanakin nan,kullum saiya zauna a parking space for hours ko Allah zesa ya ganta,har gidan daddy ya kuma zuwa,yace kawai ya kawo masa ziyara ne amma deep down shi kadai yasan dalilin dayaje,tinani kawai yake ze ganta achan,kusan kullum se yayi lecturing a class dinsu,nan ma shiru bata zuwa class,a yan kwanakinnan ya mayarda duka inda ya taba ganinta gurin zuwansa,amma ko irin abinda yakeji in tana guri be jiba sam,sosai ya zama frustrated,yayi zuciya so ba adadi amma anjima kadan sai yaji ya huce,burinsa kawai ya ganta ya tambayeta WACECE ITA?……

A hankali ya farajin kirjinsa na bugawa,dafe kirjinsa yayi ya fito daga motar ya shiga bin harabar gurin da kallo,haka yakeji,tabbas irin abinda yakeji ne a duk sanda take guri,amma kuma be ganta ba gashi zuciyarsa ta tabbatar masa da tana kusa….. Kamar ance dago ya hangota ta fita daga harabar hotel din,binta yayi da sauri ganin ta nufi next street a kafa,yasan dai ba abin hawa take nema ba cuz duk wanda yake zuwa gurinnan yasan babu public transport a area,gashi ko ina very silent kamar ba mutane……….

Ji kawai tayi an ruko hijab dinta ta gefe,kasancewar ta koma normal shigarta na hijab da niqab,mamaki ne ya kamata ganinsa,bata manta da fuskarsa ba dan tariga tayi marking dinshi as wanda yasa mata ido gashi ta kudirta a ranta lallai third encounter dinsu bazeyi kyau ba……… 

Tsayawa Deen yayi yana binta da kallo still hannunshi rike da hijab dinta,he couldn’t believe he has been looking for this unknown human being,wani mixed feeling yakeji daya kasa tantance ko na menene,sai kuma yaji ya zama speechless duk irin tarin tambayoyin daya shirya mata….

Itama on her side hakan ta kasance,so take ta masa rashin mutunci dan taci alwashin third encounter dinsu bazeyi kyau ba,amma sai ta kasa cewa komai,ko motsi ta kasayi bare ta janye hannunsa daga hijab dinta……

Shiya fara breaking silence din yace “My worse night mare,finally got you,now tell me WACECE KE?…….

Wani courage ne yazo mata ta daga hannu da nufin marinsa kamar yadda ta saba ga duk wanda ya mata abinda be mata ba,karap taji ya rike hannun,ya shiga bin hangloves dinta da kallo yace “karki kuskura,don’t make a bloody mistake!,wai ni zaki mara?,who the hell do you think you are?”…. Ya fada da dan karfi……. Kokarin kwace hannunta take amma yaki saki,saima kamo dayan da yayi yana kokarin cire hangloves din hannunta,wani sassayan kukan munafurci ta saki da saida ya daki zuciyarsa,da sauri ya danja gefe still yana rike da hannunta amma be cire gloves dinba “ke me namiki kike kuka,wani in yazo wucewa basai ya dauka wani abu zanmiki ba,wait ke bakya magana ne?”………… 

Rikicewa yayi ganin jikinta sai kakkarwa yake kamar wacce aljanu suka shafa,rasa me zeyi yayi…..Mamaki ne ya kamasa ganin abun nata ya tsananta ya sashi rungumeta kyam batareda yasan yayi hakan ba… 

A hankali yayi bisimillah ya fara karanto mata suratul baqarah a kunnanta rungume da ita kamar wacce zaa kwace masa ita……. 

Yana fara karantun yaga ta nitsu,jikinta ya dena rawan ma,kin sakinta yayi yanaji kamar su dawwama a haka,shi kadai yasan irin dauriyar da yayi da yake rungume da ita,wai a hakama da hijabi,how can someone skin be so soft?,wannan anya ta taba aiki a rayuwarta kuwa,wannan daga gani bazata iya komai na aikin mata ba….. Haka dai ya daure ya cigaba da mata karatun……

Yazo daidai  ‘أُوْلَٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدًى مِّن رَّبِّهِمْ ۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلْمُفْلِحُونَ’…. Kawai sai yaji ta kama,besan sanda yayi shiru ba yana sauraran daddadar muryarta da tinda yake be tabajin sassanyar murya me dadi irin haka ba,shida yayi tinanin yana yiwa me aljanu karatu,sai ta koma ita kemasa…. Tuni ya fita daga duniyar mutane tsabar yanda ya nitsu…… A hankali ya fara sassauta rikon daya mata tsabar yanda muryarta ta saukar masa da wani mugun kasala,ya lumshe ido yana cigaba da sauraran yanda take fitar da tajwid a karantunta,kamar wacce ke musabaka…..

Bude ido yayi kawai yaga ba mutum ba karatun kuma,dube dube ya farayi amma ko alamunta babu,da gudu ya nufi harabar hotel din yana nemanta amma be gantaba,describing dinta ya shigayi yana tambayar mutane ko sun ganta,kowa sai yace be gantaba….. Wani abu ne ya daki zuciyarsa yace “Damn it!,She fooled me,she seduced me with her voice and ran away”…… Dafe kanshi yayi yana jin kamar ya dawo da moment dinsu baya,sai a lokacin yaga wautarsa dabe tsige niqab din yaga fuskarta ba,ya biye mata thinking ko aljanu ne da ita ashe wayo ta masa!……… “Wayyo Allah,she betrayed me!”…. Ya fada kamar zararre😹

~Unique Barakancy~

Back to top button