Mijin Marigayiya Page 15 Hausa Novel
Haka Khadeeja ta kwana a asibitin karkashin kulawar Anti Iyami.Tun dare likita ya gama da ita aka bata duk wasu magungunanta, ya sanar da Anti Iyami za a iya tafiya da ita gida. Don haka gari yana wayewa karfe takwas na safe Anti Iyami ta gama aiki zata tafi gida ta shiga dakin da Khadeejan take. Bayan sun gaisa tace ‘Yanzu akwai inda yake miki ciwo Khadeeja.’Ta jijjiga kai tace ‘A’a, ko ina ya warware, yanzu ma na gama breakfast din da kika aiko min da shi.’‘Ok, so ki kirawo Mustapha kice masa zan wuce dake gida sai mu tafi na kaiki gidan Mommy din.’Bata son tayi magana da shi sai ta je gidansu don haka cikin sauri tace ‘Ai yanzu na kirawoshi bai dauka ba, ina jin yana bacci ko baya kusa da wayar amma na san da ya gani zai kira. Mu wuce kawai tunda tun jiya na gaya masa zamu wuce gidan.’‘Ohk, to tashi mu tattara kayan mu wuce. Nima tun dare na kirawo Mommyn naki na sanar da ita, da safe ma munyi waya. Na dai ce mata kada ta kirawoki ne don duk lokacin da na shigo sai na sameki kina bacci, shi yasa nace ta bari idan kin tashi zan kirawota kuyi magan. But ba komai idan mun je zata ganki tunda mun shirya.’Nan suka hada kayan Khadeejan wadanda daman ba yawa ne da su ba suka shiga motar Anti Iyami suka kama hanya.Khadeeja tana zama a mota ta lalubo wayarta ta ska ta a silent ta jefa a jaka don bata so Mustapha ya kirawota a gaban Anti Iyami domin bata san me zai ce ba idan ya ji ta wuce gidan Mommy. Duk inda suka je checkpoint aka tsayar da su da anga uniform din Anti Iyami kuma ta nuna ID card sai a barsu su wuce, haka har suka isa gidan Mommy.Tun suna asibitin Anti Iyami ta snar da Mommy zasu taho don haka kafin su isa an dorawa Khadeeja ruwan wanka, suna shiga ta wuce dakin Mommy inda Azumi mai aikinsu ta sirka mata ruwan a bandaki. Ba tare da bata lokaci ba ta fada wanka.A parlor Mommy suka zauna da Anty Iyami; bayan sun gaisa sun jajantawa juna Mommy tace ‘Ina Mustaphan? Ai na zata tare kuke da shi.’Ta gyara zama tace ‘Bai zo ba ma yau da safen duk da dai tace ta gaya masa nan zamu huto, amma don Allah kawata a duba yarinyar nan.’Cike da kulawa Mommy tace ‘In sha Allahu kuwa, kema kin san ba zan barta haka ba ko akwai wata matsala ne da ta samu ko rashin lafiya.’Ta jijjiga kai ‘Babu fa, kawai dai tace min tana son dawowa gida. Duk dai wasu tambayoyi da zan yi mata nayi ta nuna min babu komai, to amma kin ga akwai yaransa guda hudu. Watakila hidimar gida da ta yaran ce take mata yawa ga ciki shi yasa ta sume masa. Baccin da ta dinga yi kawai ya tabbatar min da cewa bata samun isasshen bacci wallahi, don shi yasa ma naki tashinta kuyi waya. Gaskiya ku bincika, ya nema mata mai aiki ko ya san yanda zai yi da yaransa.’‘Umm! To kinga dai idan ma da wata matsala bata fada ba, koda yake kwanaki tace mai aikinsu bata nana abata aron Nabila amma Baffansu yaki amincewa. Watakila saboda babu mai aikin ne abun yayi mata yawa ga laulayi.’‘Gaskiya dai ku duba, ko da zata koma ku barta ta huta ta sami natsuwa sannan kuma a daukar mata mai aiki.’Suka karasa hirarrakinsu daga baya suka yi sallama Anti Iyami ta kama hanya……..Bayan ta fito daga wanka ta tarar da farfesun kaza mai rai da lafiya wanda Mommy ta dafa mata sannan ga shayi mai kauri Azumi ta hada mata da burodi a gefe, cikin sauri ta gyarajikinta ta sa kaya sannan ta shimfida dadduma a gaban gado ta mike kafafu ta zauna ta fara ci.A nan Mommy ta shigo ta sameta itama ta zauna, sai da ta gama cin abinci sanna ta fara yi mata tambayoyi.Bata boyewa Mommy komai ba ta sanar da ita halin da ake ciki, ta tabbatar mata cewa idan dai da mai aiki musamman babba wadda ba zata sata surutu ba. Sai dai ta kasa gayawa Mommy cewa gaba daya ma ko da da mai aikin ita ji take kamar ma Mustaphan baya kaunarta, gani take kamar yanda take zama kullum cikin hidima ya sa bata gane kulawarsa a gareta. Don haka ta bar wannan a ranta tana fatan idan an sami mai aiki ya zama suna samun lokaci a tare to zata fuskanceshi.Muryar Mommy ce ta katseta tana cewa ‘To yanzu yaushe zai zo ya daukeki?’Ta kalleta suka hada ido ta sunkuyar da kai sanna cikin muryar shagwaba tace ‘Mommy kin ga yanzu mai aikin bata dawo ba, kuma na gaya miki shi ba zai tayani komai ba kuma ba zai bari yaransa su tayani ba. Kawai ki barni sai bayan sallah ko kuma duk lokacin da mai aikin ta dawo ko aka sami wata.’Mommy ta jijjiga kai tace ‘Na fahimceki, amma me kike so na gaywa Baffanku? Shi kuma Mustaphan wane dalili za a bashi na rike ki a nan din. Tunda dai ciki ya fice an riga an wake; kuma gaki nan kowa yana ganinki ras.’Ta karyar da kai kamar abin tausayi tace ‘Umma ni dai don Allah ki san yanda zaki yi a barni na huta.’‘To bari mu gani. Idan kuma akwai wani abun da Mustaphan yake yi miki wanda kike so a yi masa magan to kiyi gaya min.’‘Babu komai tunda ma bai hana a dauki mai aikin ba, in sha Allahu da ta dawo ko kika samo min wata zan koma.,Ta gyara zama ta kafa tagumi ‘Hmma, bari muga yanda zamuyi da Baffan naki tukunna.’………Sai da suka gama wannan hirar sanna ta tuna tunda suka shigo bata ma nemi wayarta ba, ta san yanzu haka Mustapha yana ta faman kiranta. Cikin sauri ta mike ta dauko wayarta daga jakarta, ai kuwa tana dubawa taga missed calls dinsa har guda goma sha daya.Tana gani danna masa kira, ko ringing bata yi ba ya dauka ‘Hello, wai ina kika shiga ne naje asibiti ina ta nemanki? Na rasa mai bani tsayayyiyar amsa, sai ce min kawai ake kin tafi da Anti Iyami, na zata gida zata kawo ki na dawo gidan kuma baku zo ba. Kin san ina neman haukacewa na rasa wanda zan kira don ban san me zan ce musu ba.’‘Subhanallah! Kayi hakuri Babe, wallahi ka ganni nan ai gidan Mommy ta kawo ni. Na kirawoka bata shiga ba kuma shine na jefe wayar a jaka na manta sai yanzu da na fito daga wanka na tuna.’‘Amma shine baki gaya min ba? Kin san wulakancin da aka dinga yi min a checkpoint kuwa?’Ta tausasa murya ‘Sorry Babe, wallahi laifina ne don tun a asibitin Anti Iyami tace na kirawoka sai wayar ta ki shiga.’Ya dan saki numfashi ‘To me yasa baku taho nan ba ko kuma a jirani na zo? Me ya sa za a kai ki gidan Mommy?’Ta dan yi shiru, shima bai yi magana ba yana sauraronta; ta murgude baki kamar yana kallonta tace ‘Ai ka san dai idan an haihu ana zuwa wanka gida, may be shi yasa da suka yi waya Mommy tace a kawoni gida.’‘To kuma shine aka rasa wanda zai gaya min.’Cikin kosawa tace ‘To ba gashi na gaya maka ba, kuma ai nace maka mantawa nayi.’Ya dan ja numfashi ‘Uhm! To ya jikin naki? Shike nan an gama yi miki alluran?’‘Na sami sauki, ga ragowar magungunana na taho da su daman yawanci na kwana bakwai ne. amma na sami sauki.’‘To idan an bude gari sai na zo na daukeki, inaga ranar Saturday zasu dan bude mu, nan da kwana uku kenan.’‘Uhm, to ka dai zo amma gaskiya sai bayan sallah zan dawo kafin nan na dan huta na gama arba’in tunda ka san shima barin ai sai an yi wanka.’‘Barin, gaskiya ban taba ji ba. Ma’u ma fa su biyu tana yin barin amma na biyun babu wanda ma amuka gayawa a nan tayi zamanta ta cigaba da hidimarta. Hutawa kawai tayi na kwana biyu.’‘idan ka zo dai mayi maganar.’Ta tamabye shi yaran ya bata su suka gaisa sannan suka yi sallama suka ajiye waya.……….Tunda yake bai taba ganin son zuciya irin wannan ba, ya za ayi a dauke masa mata kuma ace sai bayan sallah zata dawo? Kawai saboda tayi bari. Asma’u ma ai tayi bari har sau biyu ma;Asma’u ma ai tayi bari har sau biyu ma; na farkon shine bayan haihuwar Habib, bayan anyi mata wankin ciki a ranar suka dawo gida. Ko maganar taje gidansu ma ba a yi ba kawai dai an kawo mata kanwarta tunda dama tana da mai aiki. Na biyun kuwa ma bayan haihuwar Nasreen babu wanda suka gayawa, suna zuwa asibiti aka ce musu ya fice gaba daya ba sai an yi wankin ciki ba aka basu magunguna suka dawo gida. Kawai dai ya san ba zata koma dakinsa ba sai bayan kwana arba’in, kuma bashi da matsala da wannan. Amma su iyayen Khadeeja saboda son zuciya sai akwai su dauke ‘yarsu? Kuma ko gaya masa ba za ayi ba.Haka ya gaji da sake-sakensa ya sake daga wayar ya kirawo Alhaji ya gaya masa, don bai gaya musu cewar a asibiti ma ta kwana ba yana so yaje da safen ya gani tukunna. Shima Abban ya nuna rashin jin dadinsa da aka tafi da ita, musamman da ya gaya masa basu ma tambaye shi ba suka tafi da ita. Bayan sun gama waya da Alhaji ya kirawo Ummansu itama ya sanar da ita.Suma su Afaf saida yayi musu bayani don tunda ya dawo basu ganshi tare da Khadeeja ba suke ta faman yi masa tambayoyi.Babu yanda za ayi ya iaya brin Khadeeja ta zauna a gidansu, ya suke so yayi? Ga lockdown an hana mutane fita sannan kuma su dauke masa mata. Kwana ukun nan ma da zai yi da yaran bai san ta ina zai fara ba don yana tuna yanda a kwana dayan nan suka gama firgitashi; ga gari a kulle balle ya kaisu gidan Umma. Gaskiya da an bude gari ranar asabar zai je ya dauko ta tunda dai ko shi ya tambayeta jiki ta ce da sauki.Sai can da yamma dabara ta fado masa; ya dauki waya ya kirawo Baffan Khadija, bayan sun gaisa ya jajanta masa jikin Khadeejan sannan ya sanar da shi cewa ranar asabar idan aka bude gari zai zo ya dauki Khadeejan. Ba tare da matsala ba kuma Baffan ya amsa masa da hakan yayi, don haka cikin walwala ya karasa wuninsa. Bayan Ummi ta gama hada musu kayan shan ruwa shi da yara ta wuce ta tafi gidansu ta barsu.———
