Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Chapter 59 Complete Hausa Novel

WACE CE ITA (WHO IS SHE)

Unique Barakancy🌹

FIFTY-NINE📍

Wani irin tafi gurin ya dauka sai ihu akeyi because it came unexpected abu kamar a film, daga masu musu videos sai masu yin live a instagram a take……
Deen ko ajikinsa ya kara rungumota jikinsa yanda dole ta kifa kanta akan kirjinsa, yayi hakane kuma dan kartaga khaleel dan yasan bata san khaleel na gurin ba, gashi dai abu ne daya kamata yaji kunya saboda hakan ze iya ja masa raini amma wani dadi yakeji saboda khaleel dake gurin, shi bata taba rashin kunyar daya burgesa irin wannan ba and he’s looking forward to more of it in dai khaleel ze gani.

Ajiyar zuciya ya sauke ya cigaba da takawa da ita moving towards his apartment, wani irin iska me sanyi yaji yana shiga jikinsa lokacin dayaci rabin tafiya, ba komai bane kuma illa kayanta da suka tokaresa ta ko ina suka hanasa sukuni, ashe sudais beyi karya ba da yace komai yaji gaba da baya za’a huta a jikinta, shiko yasan komai yaji da yake rike da ita yanzu, ashe kallon tsoro yake mata all this while?

Abun mamaki kuma bata da weight ko kadan dan ji yake kamar be dauki komai ba, yasan dai duk kayan datasa sai yaga sun matseta suna kuma nuna surar jikinta amma be dauka abun haka yake ba saida ya mata irin wannan daukar, ba yau ya fara daukanta ba amma be taba mata irin wannan daukan ba sannan be taba daukanta cikin hayyacinta ba so baya bawa kansa daman yayi examining dinta sai yau, yau dinma maganar sudais ne yayi triggering dinshi har ya nitsu yaji komai, wato shiyasa kowani kare da doki yake hauka akanta kenan? He could remember haka sameer yace mata full package, ashe dagaske ne, hakan ya tabbatar masa shima khaleel dan abi yarima asha kida ne, it means ba tsakani da Allah yake sonta ba, they are all after her curves and beauty!

In ko hakanne ze kasa ya tsare yaga kowa be samu ba no matter what it will take him har sai yaga wanda ya dace da ita me sonta tsakani da Allah tinda kowa ya zama dan iska, right now gani yake kamar shi kadai ne mutumin kwarai a duniya cuz he’s not after all that, daurewa yayi ya shiga kokarin kauda yanayin dayake shiga, gashi duk step din daya kara sai yaji abubuwa sun kara tokareshi amma kuma yasamu kansa da kin yin sauri, a haka har Allah ya rufa masa asiri suka kai part dinsa…..

Sai da taga sun isa bakin part dinsa sannan idonta ya rena fata, taji kamar ta sauka ta gudu amma tasan bata isa ba dan dole sai ya tambayeta abinda yasameta ta rungumeshi..
Murda kofar yayi a hankali ya shiga makale da ita a jikinsa, direct bedroom dinsa ya wuce da ita gabanta sai faduwa yakeyi, shiga yayi ya tafi ya kwantar da ita akan gado a hankali kamar wanda ze ajye kwai sannan ya zauna a bedside drawer yana kallonta..….
Saurin juyamasa baya tayi tana rufe ido, murmushi yayi yabi bayanta da kallo na dan sakonni sannan murya chan kasa yace;
“Look at me baby girl”…..
Kin juyowa tayi tana kara kulle idonta…..
Hannunsa ya dora akanta ya cire dankwalinta, nan da nan gashinta data nannande da kyar ya biyo dankwalin da ribbon dinta ya zubo, kamar yanda yayi tinani batayi kitso ba kuwa, ajiyar zuciya ya sauke yana tura hannunsa cikin gashinta, lumshe ido yayi yana jindadin texture din a hannunsa, sai yaji gashin ya kara laushi da kyau, ga wani masifeffen kamshi da gashin ke fitarwa alamun ba karamin gyara ya sha ba…….
Sun fi 10mins a haka ita bata juyo ba shi kuma be dena tura hannunsa a cikin gashinta ba…….

Sunkuyowa yayi daidai kan gashin ya tura fuskarsa a ciki ya shiga shinshina gashin da hancinsa kamar ze koma cikin kanta…….
A bazata taji kamar mutum a cikin kanta, ba shiri ta janye ta juyo side din da yake, kawai taga mutum sai kyalli yake especially hancinsa da yafi ko ina kwasan man gashin, batasan sanda ta tashi zaune ta fashe da dariya tana nuna hancinsa ba….
Hannunsa ya dora a hancinsa yaji ya shafo maiko kamar wanda aka zubawa man gyada, yamutsa fuska yayi ya kalleta yace;
“Mangyada kika zuba a gashinki ne?”…..
Dariya ta sake fashewa dashi tace;
“Ni nace ka shinshina min gashi?”……
Marairaicewa yayi kamar gaske yace;
“But this is not fair zahrah, daga miki addu’a akai sai in kwasa maiko, gaskiya ki dena cika man nan”……
Dariyarta ta cigaba dayi, ya tashi ya lalubo tissue ya goge fuskarsa sannan ya shiga toilet ya wanke da sabulu ya fito ya sameta har lokacin bata dena masa dariya ba, hada rai yayi yana harararta yace;
“Kin ganki kuwa? Ina irin sababbin mahaukatan da basu yadda sun haukace ba? Toh you look like them with this your hair”….
Ya fada dan ya bakanta mata itama, ko a jikinta ta dauki ribbon dinta ta daure kanta sannan ta saka dankwali tana dariya abinta…….
Dawowa yayi ya zauna akan bedside drawern daya tashi ya kalleta sounding so serious yace;
“Meya sameki dazun?”…..
Daram! Taji gabanta yayi wani mugun faduwa, tin dazu take so tayi tinanin karyar da zata gilla masa amma gabadaya ya dagula mata lissafi ya hanata tinani bare ta samu kwakkwaran karya da zata masa ba, cikin rashin sanin abin fada tace;
“Kaina kemin ciwo”…..
“Shine bazaki iya min magana ba sai ki rungumeni a cikin mutane saboda gaki mara kunya?”…..
Wannan shine amsar dayayi niyar bata amma tuno da yanda khaleel ya gansu sai yaji baze iya mata magana mara dadi ba, kawai yace;
“Oh sorry baby girl, ashe kamar na sani na miki addu’a akan, so how’re you feeling now? In baki drugs?”…….
“A’a ai tinda kamin addu’a kan ya dena ciwo, basai ka bani komai ba”…..
Ta fada tana jindadin yanda be fassarata ba….
Dariyar da be shirya bace ta subuce masa, sai da yagama dariyarsa sannan yace;
“Kika sani ko ba addu’a na miki ba?”…..
Cikin rashin sanin abin dafawa tace;
“Koma me kamin nidai naji dadi kuma kaina ya dena ciwo”…..
Kasa yayi da muryarsa yace;
“Do you want more?”…..
Kasa tayi da tata muryar itama tace;
“Do you want more oil too?”….
Kawai suka kwashe da dariya a tare…….
Dariyar baby tee ce ta dauke dip saboda tuno da reward dinta na challenge din da sukayi da ilham, hankalinta ne ya koma kansu gabadaya taji babu abinda takeso illa taje ta karbi wayarta data ilham da kuma kudaden da sukayiwa siyama transfer duka, yau dai tasan ta gama da jin kan deen da kowa ke tsoronsa kamar wani Allah, basu san irin haushin da suke bata idan suna tsoronsa ba, kallonsa tayi tace;
“I need to go get something please”….
Wani irin kallo ya mata ganin yanda ta damu lokaci daya yace;
“Ko dai you need to go see someone?”….
Ita gabadaya ma ta manta da khaleel da introducing dinsa da tace zatayi tinda tasa wannan challenge din a gaba, girgiza kai tayi tace;
“No, gurinsu hassy zanje, abu zan karba”…
Cikin rashin yarda yace;
“Toh muje in raka ki”……
Bataso ba amma kuma datayi tinanin baze bita har gurinsu ba sai tace;
“Toh”….
Sannan ta tashi ta kara gyara daurin dankwalinta, bin bayanta yayi yana kallon cat working dinta daya dade da haddacewa, har sun kusa bakin kofa ya dakatar da ita da fadin;
“Hey! Dawo!”….
Dawowa tayi tace;
“Meya faru?”….
“Who is your stylist?”…
Ya tambaya batareda ya bata amsar tambayarta ba……
“Nima bansani ba”….
Ta fada da iyakar gaskiyarta….
“Karya kikeyi! How comes ake miki fitted kaya without measuring you?”……
“Bansani ba, umm da mami ke bani in saka”…..
“Well I’ll ask inji koma yaya ake miki dinkin”…….
Batace komai ta kara shirin fita…..
“Wait!”….
Ya sake dakatar da ita yana karasawa inda take, wani royal alkyabba me kyau sosai taga ya dora mata a kafada, nan da nan taji kamar an rufeta da bargo ta fara jin wani zafi yana shigarta, bata fuska tayi tace;
“Ni gaskiya bazan saka wannan alkyabban ba, bakaga yanda ya rufemin kwalliyata bane”..
Haderai shima yayi yace;
“Kin fiso kina yawo kawo na kallonki kenan, mala’ikun rahama na tsine miki, zahrah kinsan hukuncin wanda ya bari mutanen da ba muharramansa ba suka ga surarsa?”….
Turo baki tayi tace;
“Yawo nayi da ba kaya da za’a ga surar tawa?”…
Girgiza kansa yayi yana jinjina yarintarta…..
“Waya gaya miki sai babu kaya ake ganin jikin mutum?”…..
“Toh ni dai bazan saka wannan alkyabbar ba, kaji uban zafin dana keji kuwa, ba kaga yanda yake ja kasa ba kuma?”……
“Toh ba sai in rike miki yanda ake rikewa princess ba”……
“Nidai A’a”…
“Shikenan, cire ki jirani in dauko miki mayafi toh, I’ll be back now”…
Ya fada yana fita daga dakin, cire alkyabbar tayi ta samu guri ta zauna, tana ganin ya danyi mintina da fita ta tashi da niyar guduwa saidai tana zuwa taji kofar parlourn a garkame, deen na sane ya rufe saboda yasan zata iya guduwa, sai gashi tazo kuwa Allah ya kamata kofa a rufe, komawa tayi taje ta zauna inda ta tashi…..
Bata wani dade da zama ba taji ya turo kofar dakin, zaro ido tayi hango babban mayafin mami to match da kayan jikinta a hannunsa……
Tashi tayi tace;
“Wannan fa mayafin mami ne, ya za’ayi insa katon mayafinnan”….
Be kulata ba ya shiga yafa mata mayafin, tana ji tana gani ya lullubeta a cikin mayafi kamar wata matar aure, gashi ta kasa masa musu saboda yanda ya hade rai……
Kamo hannunta yayi suka fita daga dakin, ta dauka ze saki hannunta idan suka shigo cikin mutane amma taga ba haka ba sannan ta dauka baze bita har inda zataje ba taga yaki sakin hannunta har suka karasa gurinsu ilham, mutane sai kallonsu suke dayawa da ba family ba sun dauka matarshi ce musamman yanda ta dawo da lullubi, nan da nan wasu suka hau yi musu hoto a boye saboda yanda suka dace da juna…..
Suna zuwa sukaga sai fifita ake yiwa ilham da taketa zuba gumi kamar wacce aka shekawa ruwa, sai ihu take tana fadin;
“Wayyo kudina! Wayyo wayata! Na shiga uku, siyama dan Allah ki bani abu na”…..
Rufe ido siyama tayi ita kuma tana bata amsa da;
“Wallahi bazan baki ba, game kukayi kinyi losing sai ki dau na annabawa”……
Kawayenta kuwa sai fifita suke mata suna mata sannu, sauran su raihan kuma da suka san kan komai sai dariya suke mata, taimakonta daya Allah yasa suna daga chan gefe ne, so duk ba’a san abinda yake faruwa ba……
Kasa daurewa ilham tayi ta fashe da kuka tace;
“Wayyo na shiga uku da wanne zanji da soyayyar dake tsakaninsu koda rashin kadarorina, siyama dan Allah ki bani wayata da kudina kafin tazo, ki taimakeni ki bani inji da daya”……
“Wallahi kome zakiyi bazan baki ba, bayan kowa yasan kinyi losing kikeso na baki ni in kwan ciki? Inaa bazeyiwu ba”……
Mikewa tayi ta chakumo wuyar rigar siyama tace;
“wallahi sai kin bani kudina da wayata”…..
Daidai nan deen da baby tee suka karaso gurin rike da hannun juna, fizge hannunta daga na deen baby tee tayi ta fizge hannun ilham daga wuyar siyama tace;
“Wallahi ba za’a bayar ba, ko kin manta deal dinne? In baki gamsuba sai in maimaitawa yanzu ki gani”…….
Juyowa kan baby tee ilham tayi cikin masifa tace;
“Na fasa banayi ki gaya mata ta bani wayata tamin transfer din kudina”…..
“Kinyi kadan yarinya! The deed had been done already! Kima daina bata bakin ki!”…..
“Wallahi sai kin bani abuna, ni zaki kasa, toh baki isa ba wallahi”….
“Kasawa na nawa kuma? Ai kinriga kinyi handover da abubuwanki tinda kikayi signing deal din, bari kiji na fi karfin chicken change dinki da akwalar wayarki amma da in baki gwara nayi kyauta dasu”…..
“Na rantse da Allah ko naira biyar baza kici min a kudina ba!”….
“Mu zuba mu gani! A gabanki zanyi rugurugu da kudinki babu abinda kika isa kiyi kuma! Shege ka fasa nida ke!”…..
Daka musu tsawa deen daya kasa gane kan maganganun da sukeyi yayi yace;
“Dalla kuyiwa mutane shuru! Baku da hankali ne zaku zo kuna hayaniya a cikin mutane, what’s even going on?”….
Ya karesa da tambayar abinda yake faruwa….
Rige rigen basa labari wayanda suka san kan abun sukayi saboda yanda kowa ya tsorata da tsawar dayayi, dakatar dasu yayi ya cewa siyama ta fada tinda yaga ita ake cewa kudi na hannunta…..
Labari ta basa tiryan tiryan yanda abun ya faru da duka abinda suka ce akansa har abu ya kai ga challenge dinnan, baby tee ta saka million biyar da wayarta, ita kuma ilham ta saka million daya da wayarta itama…….
Kallonsu daya bayan daya yayi especially baby tee data fi basa mamaki akan karyar data shirga masa ta karbi 5m din datayi challenge akansa kuma a gurinsa…..
Hararansu duka yayi yace;
“Cewa zakuyi chacha kukayi, ke ilham gani azara’ilu da har kikaji zaki iya betting irin wannan akaina ko? Ke kuma zahrah your case is worse! Wato gaki fitsararriyar karshen zamani shine zakiyi irin wannan chachar dani, sannan da yake baki da kunya kikazo kika sameni kikace na baki 5m din da kikayi chachar dani ko? Well tinda kinci sai ki dawo min da kudina ki kuma zo mu raba abinda kika samu”……
Sakin baki duka yan gurin sukayi suna binsa da kallon mamaki kadama ilham taji labari data sakankance tana jira yaci ubansu sannan yasa baby tee ta bata wayarta da kudinta dole shine kawai zebi bayanta wai su raba kudin, ashe kuma 5m din a hannunsa ta karba? Siyama ko da sauri ta shiga message dinta dan ta duba sunan da aka turo alert din 5m din dashi saboda dazu ko dubawa batayi ba saboda murna, tana dubawa kuwa taga SD and co ventures, da mamakin ganin sunan kampanin deen ta nunawa hassy dake gefenta, kallon juna sukayi suna jinjinawa baby tee, a take suka tabbatar da ita babban kai ce dan babu wanda ze iya abinda tayi a cikinsu……
Hade girar sama da kasa baby tee tayi tace;
“Ai kyauta ka bani wallahi bazan dawo dashi ba, ban ki in dan sammaka wani abu a cikin abinda na samu ba”……
Ilham na jin haka ta rushe da kuka ta zube a kasa tana rokan deen tace;
“Yaya saif kai kadai ne hope dina, dan Allah dan annabi kasa baki ta bani abu na, yaya saif dan Allah”…..
“Sanda zakuyi chachar na sani? Baki ga nima 5m dina ya tafi ba? Kina ji ance nima za’a dan sammin wani abu a cikin kudinki shine zakice insa baki a baki kuma? Bakin ciki kike min ne kome?”….
Ya fada with a straight face…..
Yana sane kuma yayi hakan saboda so yake ya koyawa kowa lesson in a different way yanda duka bazasu sake irin wannan shirmen ba….
“Yaya saif duka kudina fa na bata harda wayata kuma wallahi dakyar daddy ya siyamin wannan, kudin kuma dakyar na tarasu wallahi”……
“Ke kifa dena bata bakinki dan bazan bada komai ba!”….
Baby tee ta katseta….
Dawo da kallonsa kanta yayi yace;
“Toh ke zahrah me zakiyi da kudin da wayar?”…..
“Wayar already ina da wanda zan kyautar ma, kudin kuma balango zan siya in rabawa duka mutanen gidannan, ko baza kaci ba?”….
“Ci kai! Amma gashi ana barbecue anan, why not buy a different thing?”….
“Eh ai tsire akeyi, ni kuma balango nake sha’awar rabawa”….
Murmushi me ma’ana yayi yace;
“Yayi hajajju, yanzu a ina zamu siyo? Ko muyi order kawai?”…..
Cikin jindadi tace;
“Yauwa ka kawo shawara me kyau, kasan wayenda suka iya balango me dadi da zamu iya order toh?”….
“Eh nasani, let me chat them up”….
Zaro wayarsa yayi ya kunna data yayi searching account din wasu “house of balango” me dadin gaske, yana magana sukayi replying without wasting time, juyowa yayi yace;
“Sunyi responding, na nawa za’a ce musu?”….
Wani irin ihu ilham tasa nan da nan hankalin mutane ya dawo kansu, ko kulata basuyi ba baby tee tace;
“Kana ganin mutanen gidannan zasu kai dari uku?”….
“Zasu kai”….
“Kace su sa na 3000 guda dari uku!”……
“Angama hajjaju”…
Deen ya fada yana danne dariyar dake taso masa……
“Gashi ya turo account waye zeyi transfer din?”…..
Karban wayarsa tayi taga dagaske yayi chat da masu balango, kallon siyama tayi tace;
“Siyama zan karanto miki account din ki musu transfer din nine hundred thousand”…..
“Okay karanto”….
Siyama ta fada tana shiga bank app dinta….
A take siyama tayi transfer din kudin cikin account din masu balango sannan ta mikawa baby tee taga receipt din, karba tayi tayi sharing receipt din zuwa wayar deen sannan ta turawa masu balango, nan da nan sukayi verifying payment din sukace zasuyi delivering in the next one hour……….
Burgima a kasa ilham ta hau yi tana ihu tana kuka, daka mata tsawa deen yayi ta nitsu ba shiri, sauran mutane kuma suka saki baki da hanci suna jira a kawo balango, amma babu wanda beyi mamakin yanda deen ya biyewa baby tee ba saidai babu me bakin magana sai zubawa sarautar Allah ido……..
Zama sukayi suna jiran kawo balango, guri deen ya samu ya zauna ya kalli siyama yace;
“Toh ina wayar zahrah?”…..
Bude jaka siyama tayi ta mika masa da sauri, baby tee na shirin magana Deen ya rigata da fadin;
“Ajye miki zanyi and dubu darin daya saura kuma ya zakiyi dashi?”……
“Zan baka dubu hamsin sauran kati zansa”…..
Dariyar da beyi niya ba yayi yace;
“It’s alright baby girl”…..
Kallon juna siyama da raihan sukayi dariya da gulma na cinsu na abubuwan da suka faru, har wani kaguwa sukayi su kebe a maida zance…
Kamar yanda sukace within an hour aka kawo balango kamshi sai tashi yake, su siyama ne masa rabo akabi kowa aka basa, har ilham saida baby tee tace a bata itama tasa albarka a kudinta, ana bata ta cillar tana kuka kamar tayi hauka, karban nasu anna deen yayi ya tafi kai musu yanata dariyar mugunta, shi kadai yasan me yake shiryawa ko wannensu…….
Sai da ake rabon balango baby tee ta tina da eesha, zata kirata a waya kuma ta tina wayarta na hannun deen, iphone dinta shima ta barshi a part dinsa, dole ta kyale idan ta hadu dashi…….
Da sallama deen ya shiga parlourn, mutane ne burjik a parlourn sunata hira suna cin balango, dariya yayi aransa yace ashe suma balangon har ya karaso musu kenan…….
Tambayarsu anna da su mami yayi sukace suna parlourn sama, haurawa yayi ya samesu su hudu a zaune, anna, mami, umm sai ummi matar uncle A…. Gaishesu yayi yana kin hada ido da umm, sannan ya ajyewa kowa balango a gabansa, juyawa yayi da niyar komawa saboda ganin umm yasa yaji baze iya zama ba, anna ce ta dakatar dashi da tambayar inda ya siyo balango me dadi haka saboda harta bude ta fara ci……
Dariya yayi yace;
“Jikarki da kike ji da ita ce tayi giveaway”…
“Bangane giveaway ba? Zahra’u keke nufin ta siya ma kowa balango?”…..
“Eh ita”…
A bazata sukaji anna ta fara masifa…..
“Yanzu saboda rashin tausayi sai a bari ta siya ma duka kattin dake gidannan nama? A rasa waye ze bada kudi sai ita? Saifu ka bani mamaki, fatima, Jamila kuma na gode”…..
Dariya deen ya kwashe dashi yace;
“Kudin banza ta samu fa Anna”…..
“In kudin banza ta samu a barta ta kashewa kanta a banza mana, sai a bari ta siyawa kowa balango babu wanda ya hanata, toh wallahi sai an mayar mata da kudinta, kuna jina ko”…..
“Allah ya wuci zuciyarki anna za’a maida mata”…..
Cewar umm tana ture balangon daga gabanta…
“Bawani za’a maida mata, kai saifu wuce kaje ka kirata yanzu a maida mata da kudinta a gabana”…..
Anna ta fada maganarta ko fitowa batayi sosai saboda yanda ta cika balango a baki……
Mikewa deen yayi yace;
“Toh shikenan ni zan bata”….
Anna zatayi magana mami ta rigata da fadin:
“Go and call her now”….
Fita deen yayi ya barsu anna sai loma balango take tana cigaba da fadan meyasa aka bari baby tee ta biya…..
Dawowa sukayi tana biye dashi a baya, Anna na hangosu tayi murmushi tace;
“Tawo an zara’u zara’u wannan balango yayi dadi amma gaskiya ba’a kyautamin da aka barki da biya ba”……
Karasawa gurinta baby tee tayi tana zama a kusa da ita…..
Janyo na umm data ture anna tayi ta bude ta faraci sannan ta kalli baby tee tace;
“Nawa kika kashe duka?”….
“Dubu dari tara”….
Baby tee ta bata amsa batareda tinanin komai ba…..
Dakatawa anna tayi tana kallonsu mami tace;
“Yanzu saboda rashin tsoron Allah sai a barta ta kashe har dubu dari tara akan siyawa mutane balango? Toh wallahi a maida mata kudinta yanzu yanzu, in baza’a mayar ba kuma a gayamin ni in bata”…..
“Za’a mayar mata yanzu anna”….
Cewar mami tana dauko wayarta dake gefenta…
Kallon baby tee umm tayi strictly tace;
“Where did you get the money from?”….
Karap Anna tace;
“Million dayan ce baku fi karfinta ba da sai an tsareta da tambayoyi? Ni bari in bata toh”….
Ta fada tana cigaba da cin namanta…..
Da sauri mami tace;
“Yi hakuri Anna, baby tee call your account in miki transfer yanzu”….
Sunkuyar da kai tayi tace;
“Mami ki barshi nayi niya ne”…..
“Just call your account details please!”….
Mami ta dakatar da ita saboda tasan halin anna dole sai an bada kudin nan kafin a samu zaman lafiya, kuma su masu bata kudin da yafi haka kyauta ne dama so it’s not a big deal……
Tashi baby tee tayi ta koma kusa da deen, yana ganin tazo yayi saurin kashe wayarta da yaketa rejecting din call din khaleel tin dazu, ba’a hakura ba kuma aka cigaba da kira kusan so goma kenan, kasa tayi da murya tace;
“I don’t even know my account number”….
Harararta yayi sannan kasa kasa shima yace;
“Olodo! Yanzu account dina kikeso in bayar asa miki kenan?”….
“Yes please, ai nasan zaka bani ko?”…..
“Au karban kudin zakiyi kenan”…
“Toh ya zanyi, bakaji anna tace sai na karba ba”….
“Mallama jiranki akeyi”…..
Cewar umm da takasa gane kus kus din me suke…..
Da sauri Deen daya sha jinin jikinsa yace;
“Mami tace kisa mata a account dina sai na bata cash”….
Wani irin kallo umm ta musu tace;
“Batada baki kenan”…..
“It’s not a problem jam, maybe cash takeso, kuma ina dashi ma, tashi ka dauko mata ai kasan inda yake”…..
Tashi Deen yayi yaje ya dauko cash din, yana dawowa daidai nan sultan da dawowarsa kenan yaji labarin scene din da aka buga tsakanin saif da baby tee dazu, saida ya tsaya aka tura masa videos da komai sannan ya tawo a guje dan yazo ya bawa mamansa labari saboda irin mutanennan da komai sai sun bada labari a gida….. Da gudu ya shigo ko kula da deen da baby tee dake zaune beyi ba yace;
“Ummi kunga abinda ya faru dazun kuwa, wani scene me zafi aka buga between yaya saif and baby tee, kunga videos”…..
Karba ummi tayi ta kunna videon farko suka fara kallo ita da umm dake gefenta…..

Back to top button