Daga Makamai

Ladubban 25 Na Karbar Addu’a – Daga Sheik Aminu Ibrahim Daurawa

Ladubban 25 Na Karbar Addu’a 

Daga Sheik Aminu Ibrahim Daurawa

1. Tsarkake niyya, da yi don Allah.

2. Farawa da yabo ga Allah taala.

3. Yin salati ga Annabi saw.

4. Sakankancewa da amsawa .

5. Yin naci, wajan addua .

 

Karanta>>> Fassarar Mafarkin Ruwan Sama

 

6. Halarto da zuciya, da tara hankali.

7. Yin addua a halin kunci, da halin yalwa.

8. A roki Allah kawai,

9. A kiyayi mummunar addua ga iyali da ‘ya’ya da kai.

10. Sassauta murya, lokacin addua da nuna tawali’u.

 

Karanta>>> Fassarar Mafarkin Tashi Sama Kamar Tsuntsu

 

11. Tuba, da istigfari, da godiya, da sanin komai daga Allah ne.

12. Kiyaye yin shishigi, a cikin addua.

13. Nuna kwadayi da sa rai Allah bashi da rowa.

14. Mayarwa da wanda aka zalunta hakkinsa.

15. Maimaita addua sau uku .

 

Karanta>>> Fassarar Mafarkin Koren Macij

 

16. Fuskantar gabas.

17. Daga hannu a inda sharia tace a daga.

18. Yin alwala kafin fara addua, inda sarari.

19. Rashin nuna gwanintar harshe a cikin addua.

20. Ka fara rokawa kanka, kafin wani, sai inda wata masalaha.

 

Karanta>>> Ma’anar Mafarki A Mahangar Addinin Musulunci

 

21. Yin kamun kafa da sunayan allah, da
siffofinsa, ko wani aiki na kwarai, ko neman addua daga wani, rayayye, mai iko halatacce,

22. Cin halal,

23. Kiyaye mummunar addua ta yanke
zumunta.

24. Yin umarni da kyawawan aiyuka, da hani da mummuna.

25. Nisantar mugayen laifuffuka.

Allah Ya Ji Ka, Ya Sanka, Taskarsa Bata
Karewa, Kuma Bashi Da Rowa, Kuma Ya Bawa Wani Ka Gani, Mu Rokeshi Kuma Mu Sakankance Zai Amsa.

Back to top button