Halysaah Page 145 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 145…Khaleesat ta sauke idonta ta karasa cikin parlon tana tafiya a hankali, ji take kamar kasa ya bude ta shige kawai, kwata kwata taki yarda su hada ide da Safiyyah, nan ta fara tunanin abinda zata ce mata, sai kuma tace “Maimakon ki kira ni Sophie, i slept off in his parlor ina jira ya bude kofar dakinsa in dau abinda zan dauka, kuma da na tashi yanxu sai naga kofar dakin a bude… Ko dai ya fita ne??” Bata jira cewar Safiyyah ba ta nufi kofar fita daga parlon tace “Ki taso mu je wajen Mamin mu gaisheta” Safiyyah ta cire mayafin jikinta a takaice tace “Ban zuwa, tafi ki ci gaba da baccin ki, nima baccin zan yi kawai” Sai a sannan Khaleesat ta juya ta kalleta suka hada ido, taga yanda Safiyyah ta cika saura kiris ta fashe, Khaleesat bata san sanda ta kwashe da dariya ba ta dawo parlon tace “Ke bacci fa nayi da gaske, baki ga idona ba, wallahi Allah bacci nayi” Safiyyah tace “Eh ai dole kiyi bacci kin je kin amshi sleeping pills a inda ya kamata, ai in kika kara ganin shegun kafafuwana a inda kike kiyi min fiye da haka, ni zaki walakanta ki shige dakin miji ki shanya ni parior for almost 2 hours kamar gantalalliya ina raba ido, ina lefin ki leko kice min ba yanxu zaki fito ba, mijin da ake ta mana iyayin ba a so ana koke koke ana an tsanesa har ba a son zama gida day shi….” Khaleesat ta wani harareta da sauri tace “Ji sharri yaushe nayi haka? Ni dai ban taba cewa haka ba, ai kema kinsan muna shiri da shi right from time he is not my enemy, kilan dai lokacin Abdul kike nufi, ni dai ki taso mu tafi” Tana fadin haka ta kara nufar kofa ta fita, Safiyyah ta bude baki ta bi ta da kallon mamaki, dariya sosai Khaleesat ta bata, wato har ta mance iskancin da ta dinga laftawa a Maryland akan bata son Ajay, eh lallai Ajay ya cika aiki dole Khaleesat ta mance duk cika bakin da ta dinga yi a America, Safiyyah ta girgiza kai tana murmushi, but deep down she is happy yanda taga kawarta ta folla ma Ajay lokaci daya kamar ba ita ba, even daga labarin da ta bata jiya na abinda aka yi masa a masarautar she could see the pain she was wearing on her face and even the pain in her voice gashi har da hawayenta, dama can tana sonsa ita ce bata gano hakan ba saboda taki kwantar da hankalinta tana ta hauka, amma fa ba don wajen Uwar Yaya Housemate za aje ba da babu abinda z Safiyyah ta bita don babu wanda ya taba wannan azababben walakancin da Khaleesat tayi mata sai Surayyah, ita ma haka take ta janye miji su shige daki a bar ta a gantale, barin in ta ganta zaune parlor da Ya Mustyn suna hira, abinda ya kara shock din Safiyyah yanda gogan ya zo wucewa yayi pretending bai ma san tana parlon ba cause he wasn’t expecting to see her there, har ya fita ya kulle kofa kamar bai ganta ba, ai ko gobe da sassafe zata tattara dan akwatinta ta karasa Gombe wajen Cousin sister dinta duk da ba shiri suke ba, don in ta ci gaba da zama a gidan nan bata san wani walakancin zata kara fuskanta ba tunda yanzu suke honeymoon dinsu, kwafa tayi ta yafa mayafinta ta mike ta bi bayan Khaleesat, tsabar Khaleesat ta raina mata hankalli haka ta dinga jan ta da hira kamar babu abinda ya faru har suka isa part din Mami, Khaleesat ta bude kofar a hankali ta shiga cikin parlon da sallama Safiyyah na biye da ita, Jay na zaune parlon ya jinginar da kansa da kujera idonsa a lumshe, Khaleesat tayi masa kallo daya ta karasa ta zauna kan. kujera, Safiyyah saura kadan ta tuntsire da darlya ganin ashe har yanxu yana bacci a duk inda ya samu, ita ma ta zauna kan kujera, after some seconds Khaleesat ta mike ta tafi hanyar dakin Mami, tsaye tayi bakin kofa tayi sallama, Mami ta daga ciki, bata shiga ba har sai da Mami tas shigo sannan ta shiga dakin, ta karasa har gun Mami da ta mike zaune daga kwancen da take, ta duka kasa ta gaisheta Mami ta amsa tace “Kun tashi lafiya?” Khaleesat tace “Alhamdulillah, ya karfin jiki Mami?” Mami tace “Na ji sauki” Shiru Khaleesat tayi, Mami tace “Junaid ya tafi aiki ko?” Khaleesat ta gyada kai tace “Eh ya tafi daxu” Mami tace “To in dai baya nan ki dena zama can bangaren ke kadai, ki dinga dawowa nan, ko kuma Yakumbo ta koma can bangaren naki ta zauna da ke har sanda zai dawo” Khaleesat ta sauke kanta kasa a hankall tace “To in sha Allah Mami, dama tare muke da kawata ta zo zata gaisheki….” Mami tace “Kawarki daga Kano?” Khaleesat tace “Eh, tare muka yi karatu a Baltimore da ita, Coursemate dita ce” Mami tace “To maa sha Allah, bari in fito” Khaleesat tace “Toh Mami” Daga haka ta mike ta fita daga dakin ta koma parlor, dai dai sanda Jay ya bude idonsa a hankali, yana ganin Khaleesat ya gyara zamansa ita kuwa taki kallon inda yake ya bi ta da kallon gefen ido, ta tafi ta zauna kan kujera abun ta still not looking at his direction, Safiyyah dake washe baki ganin ya tashi tace “Ina kwana Yaya Housemate” Juyawa yayi da sauri zuwa side din kujeran dake gefen wanda yake zaune, ya dan bude ido yace “Ohh Safiyyah” Tana murmushi tace “Ai mun kana ta bacci abun ka” Da sauri yace “Ala bacci nake ba, i was just meditating” Dariya Safiyyah tayi tace “Saura kadan fa kayi minshari” Murmushi yayi yace “Na ji shigowar ku fa Safiyyah, kawai dai ban gama abinda nake yi bane shi yasa ban bude ido ba, zuwa Bauchi babu announcement?” Safiyyah tace “A’a ni da kayi blocking ta WhatsApp ta ina zan gaya maka, na dena ganin status dinka kwata kwata dama in an maka magana ba reply kake ba in ma an kiraka baka picking, nace to kilan ka goge number ta ne” Yayi er dariya yace “C’mon Safiyyah ta yaya zan goge numberki, i have ur number mana….” Wayarsa ya dauka ya bude ya shiga contact ya nemo number ta yana nuna mata screen din wayar yace “Isn’t it?” Ta mike ta tafi zata amshi wayar aka bude kofar parlon sai ga Hadiyah ta shigo cikin shiga ta alfarma ta sha gwala-gwalai, tun da aka ce title din Yarima ya zama na Jay yanxu ta fara ire iren shigar nan ita matar Yarima me jiran Gado, kallo daya Khaleesat tayi mata ta dauke kai, Safiyyah ma ta kalleta sannan ta maida dubanta kan Jay ta amshi wayar hannunsa tace “Ai kuwa ga number na nan, kilan network ne Jay dai yayi shiru bai ce komal ba may be because of Hadiyah, Hadiyah dake ta kallon Safiyyah babu ko kiftawa tana karasowa cikin parlon cikin wani expression tace “Ke wacece?” Safiyyah ta juva ta kalleta, Mami ce ta fito daga parlon, wa yasa Hadiyah ta fasa sauran maganganun Care makale bakinta ta fixge wayar Jay dake hannun Safiyyah, tana kallon Jay fuska daura tace “Ка tashi mu je, Ummi na son zata yi maka magana tun daxu” Jay ya sauke idonsa sai kuma ya mike, Mami dai kallonsu kawai take, Hadiyah ta tasa keyarsa fuska murtuke suka fita daga parion, rabonta da parlon Mami tun ranan da Mami ta koreta da ta nemi Khaleesat da fada, kuma tun ranan rabon da ta gaida Mami a gidan, yanxun ma taki yarda ta kalli inda Mamin ke tsaye ta tisa keyar Jay suka bar parlon, Mami ta karaso ta zauna kan kujera, saboda bakin ciki yasa tayi tafiyarta daki ta kwanta don tana parlon Jay ya shigo ya sameta tun dagal gaisuwar da yayi mata ta amsa a takaice bai sake ce mata komai ba sai ma ya bige da bacci abun sa a parlon, shine ta tafi dakinta cike da damuwa, Safiyyah ta zauna kan Carpet tana kallon Mami ta gaidata da fara’a, Mami ta amsa da murmushi tace “Sannu da zuwa yan mata” Safiyyah tace “Fatan mun same ku lafiya Mami” Mami tace “Alhamdulillah, ya hanya?” Safiyyah tace “Alhamdulillah Nan Safiyyah ta fara wondering ba ance Mami bata da kirki ba gashi kuma faram faram ta ganta, Mami ta kalli Khaleesat tace “Ki shiga kitchen Halysaah zaki ga cin cin da aka kawo min daxu da dublan ki debo mata da drinks” Khaleesat tace “To Mami” Mikewa tayi ta tafi kitchen din, after a wh fito da duk abubuwan da Mami tace ta ajiye Safiyyah, Mami ta mike ta bar masu parlon ta koma daki, Khaleesat tabi Mami dakı taji ko da wani aikin da za ayi mata duk da ko ina na part din fess fess ga kamshi dake tashi ta ko wani angle, Khaleesat sun fi minti arba’in bangaren Mami sannan tayi ma Mami sallama suka koma part dinta da Safiyyah, Safiyyah ta zauna kan kujera a Main parlor tana kallon Khaleesat tayi kasa da murya tace “In ji babu CCTV camera a parlon nan naki, gudun ko akwai a parlon Mami yasa na ja bakina na kume….” Khaleesat ta dan yi murmushi don tayi mamakin da Safiyyah bata ce komai ba duk zaman da suka yi a bangaren Mami, dama da tayi wata maganar ma zata yi maza ta kwabeta amma sai taga bata yi ba, Zaunawa Khaleesat tayi tace “Babu komai a nan Safiyyah tayi mitsi mitsi da ido tace “shanye Housemate din matar tasa tayi ko me???” A takaice Khaleesat tace “Ohon masu” Safiyyah tace Ji min er iskar yarinya, wallahi da Mami bata fito ba da taji ko ni wacece kamar yanda ta tambaya, kaina ya fi nata hayaki wallahi, ki ji fa har da fixge wayarsa a hannuna, kan bala’i bata fa san wacece ni ba yarinyar nan” Khaleesat tace “To ranan fa shakeni tayi kawai daga ta samu ni da mijinta a parlorn Mami Safiyyah ta hangame baki tace “Ta shake ki? Sai aka yi yaya?” Khaleesat ta tabe baki bata ce komai ba don wani bakin ciki tokareta tuno hakan da tayi, dai dal sanda bude kofar parlon sai ga Hadiyah da Iklima sun shigo parlon, daga Khaleesat har Safiyyah suka dinga kallonsu, Hadiyah na ma Khaleesat wani matsiyacin kallo har ta karaso tsakiyar parlon tace “Wato tun da na bi na toshe duk wata hanyar da zaki dinga bibiyan mijina da iskanci a gidan nan shi ne bari ki gayyato kawarki kwartuwa kamarki ta zo ta dora daga inda kika tsaya….” Safiyyah ta mike ta cillar da gyalenta ta nufi Hadiyah tana huci tace “Don ubanki ni kike ce ma kwartuwa? A gidan uwarki kika san ni zaki ce min kwartuwa? So kike in maki duka blue black a nan yanda ko mijin naki bazai gane ki ba??” Iklima na ganin haka tace “Kee hattara yarinya, kar ki ji ma kanki bala’in da baza ki iya fidda kanki ba, kin san wacece ita? So kike ki kare shegen rayuwarki a prison??” Tuni Khaleesat ta shiga tsakaninsu kafin a fara dambe ganin yanda Safiyyah ta hada Hadiyah da Iklima ta dinga kunduma masu zagi ba ji ba gani tana neman cakumosu, Khaleesat na jawo Safiyyah tace “Piss stop this Safiyyah, don Allah ki kyalesu mu shiga daki….” Hadiyah ta juya ta zabga ma Khaleesat wani wawan mari tace “Ke ce dai dai yina ba er tashar kawarki ba….” Khaleesát ta saki baki with shock ta dafe kuncinta tana kallon Hadiyah, bata san sanda ta gaura mata nata marin ba ta fincikota a fusace, nan dambe ya kacame tsakaninsu, Iklima t da gudu zata je kiran yan gidan yanda za ay Khaleesat da Safiyyah taron dangi ayi masu duka, dama duk yan matan gidan da iyayensu suna nan don Hajja na hanya yau, Safiyyah bata taba sanin Khaleesat na da karfi haka ba sai yau, don tuni ta kai Hadiyah kasa ta dinga lakada mata duka ba ji ba gani kamar an aikota tana gaggaura mata maruka Hadiyah na ihu tana kiran Ummi, Safiyyah taki rabasu ta koma gefe tana wani tsumuwa tana kara gingering Khaleesat, sai da taga Khaleesat ta shake Hadiyah da gaske har idanuwanta sun fito, kuma exactly yanda Hadiyah tayi mata a parlon Mami sannan Safiyyah tayi saurin janyeta daga kan Hadiyah tace “Bar shegiya haka, bar ta haka nan kar ta suma a hannunki, gobe ko burkutun arna ta kwankwada bazata sake shigo maki bangarenki ba, er iska mara tarbiyya kawai” Ihu kawai Hadiyah take tana birgima a parlon tana kiran Ummi, Khaleesat na huci tace “Don uwarki gobe ki sake wanke shegun kafufuwanki ki zo bangarena ki gani, wallahi sai na maki fiye da haka don jina jina zan maki, mijin ki din banza naga sanda yake tare dake tani yake ba take ba, kuma da bakinsa ya gaya min ke din zabin Maminsa ce ba zabinsa ba kawai ya rasa yanda zai yi ne da aurenki da aka kakaba maki, abinda Mijina aka so makala maki yaki shi ne aka makala ma Jawwad din, to burgar uwar me zaki ma mutane bayan mun san komai, yaush ya fara baki attention dinsa? Ina ce a rashine ya hakura yayi accepting dinki har yake maki kallon mace? Ke da kike matar chushe har kina da bakin magana mara kunya kawai” Hadiyah was more than shock, kukan ma ta kasa tana kallon Khaleesat jin abubuwan da take cewa, Hayaniyar matan gidan da ‘ya yansu Khaleesat ta fara jiyo alamar sun iso bangaren nata, ai ko ta ja hannun Safiyyah da sauri suka shige parlon Ajay tun da akwai key a jikin kofar, suna shiga ta kulle kofar da makulli, Safiyyah na zare ido jin hayaniya sosai a Main parlor tace “To kira mana Ajay ya zo ya kai ni tasha” Khaleesat ta zauna kan kujera tana huci tace “Wallahi kadan nayi mata, ni ma ai haka ta min ranan a parlon Mami ta shakeni, babu wanda yayi kokarin stopping dinta sai Mami da Ya Junaid da ya mareta, but at the end Jawwad was questioning Ya Junaid akan me zai marar masa mata, bayan yana tsaye komai ya faru he couldn’t even save me” Safiyyah ta bude baki da mamaki tana kallon Khaleesat tace “Shi Housemate din??” Khaleesat tace “Kuma babu wanda yace inyi hakuri a gidan nan sai Mami, don haka nima yau na rama sai in ga me za a ce” Safiyyah tace “Har Mai martaban?” Khaleesat taki ce mata komai døn ita Mami ce kawai bata jin haushi a fadin gidan nan, mikewa tayi ta tafi dakin Ajay ta dau wayarta ta kunna sannan tayi dialing numbersa, yana fara ringing ya daga amm ce komai ba, ta turo baki tace “Kana gan zaman zamana zaman zamana Hadiyah ta biyoni har part din nan ta mareni ko?” Shiru yayi for some seconds, har tayi tunanin baya kan layin, ta kalli screen din wayar taga yana kai har sannan, sai kuma taji yace “Ta mare ki? Ke kuma sai kika zauna ta mareki ko?” Khaleesat tace “A’a na rama, sannan nayi mata duka” Yace “Kika mata duka?” Khaleesat ta kara turo baki tace “Enh mana….” Yace “Good, hope kin shiga ciki kin kulle kofa?” Tace “En” Yace “Kuma Kawarki bata yi involving kanta ba?” Khaleesat tace “A’a ni kadai na doketa, ita ce ma ta raba mu” Yace “Good, duk me za su ce kar ku bude kofar” Katse wayar yayi daga haka, Khaleesat ta koma parlor, Safiyyah sai zare ido take jin uban zage zagen da mata ke laftawa a parlor kamar maguzawa suna cewa sal sun yi ma ita da Khaleesat lahani, kai baka ce sun hada komai da Sarauta ba yanda suka dinga maganganu kamar yan tasha, gashi sal Bazawara suke kiranta da shi wai aurota masarautar ma Taboo ne at the first place shi yasa daga shigowarta komai ya rikice a masarautar, maganganu marasu dadi sai wanda suka manta ne basu ma Khaleesat da iyayenta ba, Khaleesat ta kunna TV din parion Ajay ta kure volume yanda ma bazata dinga jin su ba, kuma zuciyarta ko dar, as far as Aj yi blaming dinta kan abinda tayi ba…….



