Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 70 Complete Novel

*ASM070*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
……..bayan sallar isha gwaggo ta nufi gidan Hajiya, lokacin data isa a parlor ta isketa ta yi mata maraba, ganin tayi tsaye ta nuna mata kujerar gefen ta tace ta zauna mana, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta amsa tay mata ya aiki ta tambayeta Amadu kwana biyu bata gan shi ba tace yana nan, shiru sukai gwaggo ta d’an sunkuyar da kanta tama rasa ta ina zata fara, jin shirun nata yayi yawa yasa Hajiya cewa “Ya ya Dije, koda wani abu ne?” kallon ta tayi tay d’an murmushi kawai ba tare data ce komai, lokaci guda Hajiya ta fahimci abunda ya kawota tana murmushi tace mata ko itama Maryam d’in taje ta firgita ta, sai lokacin ta fara magana cikin sanyin murya tace “Hajiya dama zuwa nayi in rok’i Alfarma, don Allah tunda basu son auren ina ganin a hak’ura kawai don hankalin kowa ya kwanta, ban so silar hakan asamu rashin fahimta” d’an murmushi Hajiya tay ta d’an kya6e baki tace “to dawa dawa ye basu san Auren? Duka fa ita kad’ai ce ta nuna k’in amincewa kuma itama ba wani abu yasa ba face kishi da take taya yarta” shiru gwaggo tayi ita dai har cikin ranta tafi son a raba Auran kawae saidae bata iya yin jayayya da Hajiyar, ganin yanayin ta yasa Hajiya cigaba “ki kwantar da hankalin ki Dije ba abunda zai faru sai Alkhairi Fateema kuma tana nan Lafiya kuma ba abunda zai sameta in sha Allah, duk maganganun da taje ta fad’a maki barazana ce kawai ba wani abu ba” gyad’a kai gwaggo tayi tay shiru, can tace ma Hajiyar bari ta tafi tayi mata godiya Hajiya tace ta bari ta ci Abinci tana d’an murmushi tace mata a k’oshe bata jima da ci ba tace to bari a zubo mata ta kaima Amadu tace mashi tunda ya manta da matar ta shi gashi nan tana biko duk suka d’an yi dariya, Saude ta kira ta bata Umarnin zubo ma gwaggo Abinci, bayan ta kawo har zata bata Hajiya tace ta rakata part d’in Fateema ta ganta ko hankalin ta ya k’ara kwanciya ita dai gwaggo murmushi kawai take sukai sallama suka tafi Saude na ruk’e da Warmer d’in Abincin, Fatuu na cikin Bedroom ta fito daga wanka tana shiryawa da kayan bacci don tafiya part d’in Hajiya akai kopa ta nufeta ta bud’e, Saude ta gani sukai ma juna murmushi ta gaida ita tace mata ta zo ga bak’uwa ta kawo mata, d’an jimm Fatuu tay a ranta tana tunanin wace bak’uwa ce don rabonta da wani yazo tun cikin wanccan satin da Haulat tazo har take fad’i mata ta kusa komawa, juyawa tay ta d’aukko hula tasa ta fito, tana zuwa bakin corridor ta d’an wara ido tana son ganin wacece bak’uwar, gwaggo ta hango zaune akan armchair Saude na tsaye gefe aikuwa ta watso da gudu tana zuwa ta fad’a kanta cike da Farinciki take fad’in gwaggo dama ke ce bak’uwar, gaba d’aya dariya suke yi Saude na fad’in Fateema sai kace kin shekara baki ganta ba, ita dai gwaggo sai dariya take, sallama Saude tayi ma gwaggo tace ma Fatuu sai ta shigo ta juya ta nufi kopa, d’ago kai Fatuu tay suna kallon juna ita da gwaggo sai sakin murmushi suke, ganin gwaggon tak’i cewa komai yasa Fatuu tura baki a shagwa6e tace don Allah tayi magana mana, tana dariya tace taya zata yi Magana ta sakar mata nauyi jin haka yasa ta tashi maimakon ta zauna akan d’ayar armchair d’in sai ta haye saman hannun kujerar ta kama hannun gwaggon sai kace zata gudu, tambayar ta tana lafiya tayi tace mata eh sai lokacin ta tuna da bata gaishe da ita ba, shiru suka d’an yi Fatuu ta tambayeta Kawu Amadu tace ta wuto shi a shago yana gaishe da ita, shiru suka k’ara yi Fatuu nata wasi wasin ko ta fad’i mata abunda Hajiya Maryam tazo tayi mata, itama gwaggon tana son ta tambayeta ta rasa ta ina zata fara bata son Fatun ta fahimci taje gida kar ta tashi hankalin ta,
“Daga wurin Hajiya nike, naji tace Mahaifin d’ana Haisam da Hajiya Maryam sun zo har sun koma” yanayin fuskar Fatuu ne ya sauya a hankali tace mata eh, “Yanzu sun san da Maganar auren kenan?” Kai Fatuu ta d’aga tace mata eh, amfani tay da canzawar fuskar Fatun tace mata ya taga Fuskar ta ta sauya ko da matsala ne, shiru tay tana d’an kikkafta ido tana son fad’i mata amman bata son hankalin ta ya tashi gwaggo ta fahimci da wani abu hakan yasa ta kwantar da murya tace inda wani abu ta fad’i mata in ba ita ba wa zata fad’i mawa, labarin abunda ya faru ta bata harda yadda Senator ya kar6eta, Fuskar gwaggon da murmushi tace mata ta kwantar da hankalin ta komai zai daidaita in sha Allahu itama kar ta k’ullace ta tana gudun abunda ka iya faruwa da d’iyarta ne tunda bata san da Maganar ba sai suyi ta Addu’ar Allah ya kawo komai cikin sauk’i, tambayar Fatun tay koda wani abu tace mata a’a ta mik’e Fatuu ma ta saukko tana fad’in don Allah ta bari su tafi tare ta kwana a can ta d’an harareta tace to bari ta d’aukko mayafi su fita tare ta rakata ita kuma ta wuce part d’in Hajiya tace to ta juya da sauri sauri gudu gudu ta nufi hanyar corridor gwaggo ta bita da kallo tana Murmushi.
Bayan sati guda da zuwan su Senator Fatuu na a parlon Hajiya bayan la’asar suna yin kallo tana sanye da riga da skirt na atampa, akai akai Hajiya ke mata magana akan film d’in da suke kallo wani wurin ta bata amsa wani wurin kuma tay dariya kawai don Hajiya bata iya in tana kallo tayi shiru, Sallama akai daga can bakin kopar duk suka juya suka kallo mai sallamar, Kawu Amadu ne daga bayan shi kuma wata ce tana sanye da doguwar rigar Atamfa da Hijab Fatuu na ta son ta gane ko wacece ta kasa don sun d’an masu nisa gashi Kawu Amadu ya d’an kare ta, Hajiya ce ta d’aga murya tace su shigo mana sun yi tsaye sai kace parlon bak’on shi ne ya nufo ciki yana murmushi wadda suka shigo tare na biye dashi, suna zuwa bakin kujerun Fatuu tay zumbur ta mik’e da alamun Al’ajabi idon ta akan wadda yazo da ita, ganin murmushin da take mata yasa da k’arfi ta furta “MINO” dariya minon tayi aikuwa Fatuu ta watsa da gudu tana zuwa ta kankame ta Amadu nata dariya Hajiya ma kallon nasu take ta cikin glasses tana murmushi, zama Kawu Amadu yay ya gaishe da ita ta amsa tace kace da babbar bak’uwa kake tafe yace aikuwa,
“To wai ni ba za’a bari in gaisa da k’awar tawa da ban sani ba sai a hoto” Hajiya tay Maganar idonta akan su Fatuu da suka saki juna suna ta ma juna dariya, kamo hannunta tayi suka nufo wurin Hajiya Mino na niyyar duk’awa ta gaishe da ita Hajiya ta mik’o mata hannu ta kama ta zaunar da ita a gefen ta, cikin hausar ta dake bayyana ita bafullatana ce sosae ta gaishe da Hajiyar tana fara’a ta amsa tay mata an zo lafiya da tambayar sauran yan’uwanta ta amsa Fatuu na tsaye gefe farinciki shimfid’e akan Fuskar tata, Hajiya ce tace mata ta zauna mana sannan ta zauna a kujerar kusa da su,
“Ita Dije wannan shine Fateema ta tafi ga wata Fateemar ta zo” ta fad’a idon ta akan Mino da ke ta washe baki in ka ganta baka ce daga k’auye take ba tsaf tsaf da ita ba irin kwalliyar yan k’auyen nan iya jan baki kawae ta shafa ko jagira batayi ba don tana da gashin gira sosae kaman Fatuu gashi sai d’an k’amshin turare take, “kusan ma tsawon su d’aya da Fateema kawai yanayin jiki ne ba d’aya ba” Hajiya ta fad’a tare da kallon Amadu yana dariya yace eh ita da gani ma sai tafi Fatuu tsawo tace ba shakka, Fatuu dai sai murmushi take saki farinciki fal ranta yar uwa tazo, hannu ta kai ta dafo Shoulder d’in mino ta juya ta kalleta, tambayar ta tayi su Yadikko tace mata zasu zo amman ba yanzu ba sai daga baya Baffa ne dai suka zo tare da shi,
“Kai haba! da Baffa kuka zo yana ina?” ce mata tay yana nan waje, kallon kopar shigowa Fatuu tayi ta nuna ta da yatsa tace bakin kopar nan ta d’aga mata kai alamar eh aikuwa zumbur ta mik’e ta nufi kopar da gudu, Kallon Amadu Hajiya tayi tace ya zai bar Mutum a waje yace mata shine yace ya fad’a tukun a bada izini, dariya Hajiya tay “wannan parlon na mutane har sai an nemi wani izini kaima Amadu ai da ka shigo dashi”, ce mashi tayi yaje ya shigo dashi yace to, Fatuu na fita ta ganshi a gefe yana sanye da manyan kaya riga da wando na shadda brown kusan sun saje da kalar fatar shi kanshi sanye da hula saidai karin ta bai fita da kyau ba shima tsaf dashi harda su Agogo anzo gidansu suruki, da sassarfa ta nufe shi tana fad’in sunan shi tana zuwa ta kankame shi sai kace zata shige cikin jikinshi, yana ta dariya yasa hannu guda ya dafa ta, d’agowa tay da tsantsar farinciki tana kallon shi sai washe baki take ta kasa yin Magana shima idon shi na a cikin nata suna ta yi ma juna murmushi, suna haka Amadu ya fito yace mashi ance su shigo yace to, Fatuu na ruk’e dashi tayi mashi side hug suka shiga, suna isa cikin parlon ya fara k’ok’arin duk’awa ya gaishe da Hajiya ta dakatar dashi tace don Allah ga wuri ya zauna sai a gaisa, bayan sun gaisa tayi mashi ya aka baro mutan gidan yana ta murmushi ya amsa, kallon Fatuu dake gefen shi har lokacin tana a jikin shi Hajiya tay tace su Fateema an ga Baba an hana mashi sakat tasa dariya Amadu ya kai hannu alamar zai bugeta yace ta sake shi ya huta ta mak’e mashi kafad’a shi dae sai murmushi yake, godiya Baffan ya shiga yi ma Hajiya kan abubuwan Alkhairi da aketa yi masu da Addu’oi tana murmushi tace mashi ai ba komai an zama d’aya,
kallon Fatuu tay tace “to mage sai a tashi aje a had’a masu Abinci ko” tana dariya ta d’ago a kunyace baffan yace a bashshi sun ci Abinci Hajiya tace eh ai tasan sun ci shima na nan d’in sai aci duka sukai murmushi ta kai hannu ta dafa jikin Mino tace ita ai ta samu k’awa minon nata mata murmushi, cikin parlon ta kawo masu Abincin tare da Aunty Saude da bata san da zuwan nasu ba saida Fatun taje Kitchen take sanar mata, gaisawa tayi dasu tayi masu an zo lafiya, daga baya bayan sun gama cin Abincin suka yi ma Hajiya sallama ta tambayi yaushe Baffan zai koma yace mata gobe in Allah ya kaimu, tambayar Hajiya Fatuu tay wai ta bisu can gidan ta d’an ta6e baki ta girgiza mata kai alamar a’a, marairaice mata tayi tace mata don Allah tayi yar dariya tace taje in ma kwana zata yi ta kwana, zo kaga murna harda d’an tsallen murna. Bayan sun fito ne Fatuu tace ma Baffan suje yaga inda take yace mata ba sai yaje ba ta marairaice mashi ta kama hannun shi guda tana mashi magiya, Amadu ne yace mashi ai ba wani abu suje sannan suka nufi part d’in nasu, sosae yay farincikin ganin inda yar tashi take rayuwa har fuskar shi ta kasa 6oye farinciki nashi, Mino ma sai washe baki take tana fad’in yanzu Adda Fatuu nan gidan ki ne tana ta kalle kalle, matsa mashi Fatuu tay wai yazo yaga sauran wurare ya k’i yace ba sai yaje ba tunda yaga nan Mino ko ai tuni ta nufi ciki.
Bayan sun je can gidan mino tasa Fatuu ta kira mata Abbas tace ashe bata manta dashi ba tace ai suna waya dashi ta wayar yadikko, d’an waro ido Fatuu tay da d’an mamaki tace kodai wani abu ke tsakanin su ne da sauri Minon tace mata a’a wllh kawai yana kira yaji ya suke sai suyi hira wani lokacin har yasa tayi mashi magana da fulatanci har ma yace inta dawo nan zai siya mata waya kuma zata rink’a koya mashi fullanci jinjina kai kawae Fatuu tay, bayan ta kira shi sun gaisa taba Mino wayar ta sanar dashi game da zuwan su da alamun jin dad’i yace mata to yana nan zuwa, da daddare bayan sallar isha yazo a parlor suka zauna aka kira mashi Baffan Fatuu suka gaisa shima yayi mashi godiya sosae da Addu’oi yana ta fad’in ba komai, hira suka shiga yi gaba d’ayan su harda Kawu Amadu da gwaggo da Baffan Fatun Mino dai na a gefen Abbas, abun gwanin burgewa yadda suke yin hirar in akayi hausa wani lokacin sai a juye a koma fullanci Abbas yay ta murmushi har Mino nace mashi tunda tazo zata koya mashi ai, anan yake ma Gwaggo Maganar cigaba da karatun ta tace eh inda Fatuu tayi take son taci gaba in ta huta sai Amadu yayi mata cuku cukun samu Abbas d’in yace abar mashi komai, bayan Abbas ya tafi gwaggo tace ma Fatuu ita sai yaushe zata tafi dare yayi fa sosae tace ai anan zata kwana Hajiya ta amince tace a’a miya kai na wani kwana ta tashi ta koma ta marairaice kaman zata saka kuka gwaggon tace ko na jini zata yi sai ta tafi tace su tafi tare da Mino su kwana, jin hakan yasa ta washe ta basu tsarabar Hajiya da ta Fatun suka tafi, Bayan sun koma gida sun kaima Hajiya tsarabar suka dawo part d’in su, Bedroom suka nufa Mino sai faman washe baki take tana fad’in “Adda Fatuu wllh gidan ki Aljannar duniya ne” ita dai Fatuu sai dariya take, toilet ta jata don tayi wanka, a Laundary suka tsaya tasa ta cire kayanta ta d’aukko mata towel kanta yasha kitson fulani gwanin sha’awa, bud’e injin wanki tayi ta saka kayan data ciren nan fa Mino ta fara k’auyanci tana tatta6a shi cike da mamaki take fad’in ta ta6a ganin irin shi a kallo ashe tana da rabon ganin shi a fili har ta ta6a, gaba d’aya ta bi ta rurruk’e saman towel d’in da Fatuu ta bata ta d’aura, tana dariya tace mata in aka d’aure saki ake tace ai ji take kaman zai kwance ne, tare suka shiga toilet d’in ta fara nuna mata yadda zata yi amfani da komae ta waro ido tana bin shi da kallo, had’a mata ruwa tayi cikin bathtub ta fara nuna mata yadda zata shiga tayi wanka tana cikin mata bayani Minon tace wai ko kaman yadda ake yi a tafki ta d’an harareta, bayan ta gama nuna mata tace zata tsaya a cikin d’akin waje in akwae abunda bata gane ba tayi mata Magana tace toh, da yake tana da fahimta kuma k’auyancin nata da Sauk’i bai yawa ba sai gashi tayi wankan lafiya lou ta fito sai shinshina jikinta take yi tana washe baki tana fad’in yau tayi wanka da ruwan turare, Fatuu dai saidae tay dariya ta girgiza kai, bayan sun koma cikin Bedroom tasata ta shafa mai ta daukko mata rigar bacci, saida ta gama shiryata ta nuna mata gado tace ta kwanta a d’arare ta hau gadon tana yi tana tatta6a jikin shi sai kace tana jin tsoron shi, bayan ta kwanta Fatuu ta wuce don tayo wankan itama, bayan ta fito a takure ta iske Mino sai faman rawar sanyi take ita tama d’auka tayi bacci, rage mata Ac d’in tayi ta nuna mata duvet tace da shi ake lullubewa tace ai ta d’aukka kwalliyan gado akai Fatun tay d’an guntun tsoki tare da murmushi.
Washe gari Baffan su Fatun ya tafi. A cikin satin Abbas ya gama yi ma Mino cuku cukun Makaranta ya kawo mata Uniform da su School back nan yake sanar da gwaggo Makarantar da zata cigaba wadda babbar private school ce da kusan duk an santa, da alamun damuwa gwaggo tace ya zai d’auki wannan babban nauyin ga dawainiyar iyalin shi nan yake sanar mata bashi ne zai d’auki nauyin Karatun ba Haisam ne shi yace akaita can tace to ai da ko wadda bata kaita ba tunda ita mai tsada ce yana murmushi yace mata tunda shi yace kar ta damu, bayan ya tafi tasa Amadu ya kira mata Haisam d’in bayan sun gaisa tayi mashi Maganar Makarantar tace dawainiyar zata yi yawa da asaka ta wadda bata kai ta ba yace mata ba wani abu, sosae tayi mashi godiya tare da Addu’oi. Cikin sati guda Mino har ta goge komai na part d’in Fatuu tasan yadda ake amfani dashi, anan take taya ta kwana da safe sai ta koma gida don taya gwaggo aiki, cikin satin daya kama ta fara zuwa Makaranta, sosae Uniform d’in suka kar6e ta kai kace itama d’iyar Senator d’in ce, Tk ne ke kaisu gaba d’aya kuma ya d’aukko su da yake kusan lokaci guda ake tashin su, duk wanda ya gan su sai yayi Maganar Kamannin su.
Ranar Juma’a daya kama wata guda da sati d’aya da tafiyar Haisam bayan Fatuu ta dawo daga Makaranta an sauke Mino ta nufi part d’in su, Bedroom ta wuce ta aje jakarta ta nufi toilet, bayan ta fito ta fara shiryawa ta saka riga da skirt na lace da yake period take bazata je Masallaci ba kaman yadda suke tafiya tare da su Hajiya, bari tayi a gama sallar sai ta tafi part d’in Hajiyar taci Abinci don bata son taje tayi mata Maganar zuwa Masallaci, tana kishingid’e tana latsa wayarta har aka gama sallan, da yake ba wata yunwa take ji sosae ba sai can bayan an dad’e da gamawa sannan ta tashi don ta tafi, saida ta yafa d’an gyale mahad’in kayan jikinta sannan ta tafi, Tana shiga parlon Hajiya ta hango ta zaune tayi kwalliyar Juma’a daga d’ayan bangaren kuma wata ce zaune wadda Fatun bata gane ko wacece ba, tana kaiwa bakin kujerun taja ta tsaya sakamakon wadda idanun ta suka gani, Farha ce zaune tana sanye da wasu matsattsun jeans da top kanta ba kallabi kunnuwan ta sak’ale da earpiece idanuwan ta na akan wayarta dake ruk’e a hannun ta tana d’an taunar cingam sam bata ji shigowar Fatun ba, kallonta Hajiya tay fuska a sake tace mata an dawo tace eh tun d’azu ma tace to taje ta ci Abinci, suna cikin Maganar Farha ta d’ago ta kalli Hajiya ganin tana Magana yasa ta kai idon ta kan wanda take Maganar da shi suka had’a ido da Fatuu, wani mugun kallo ta jefa mata nan take Fatuu tasha jinin jikinta, maida kanta tay kan wayar har Fatuu zata juya Hajiya tace mata bata gane Farha bane, dakatawa tayi da d’an murmushin yak’e tace ta ganeta tace to basu gaisa ba, ce mata tay taga kaman bazata ji ba tunda ta saka earpiece shiyasa bata yi mata magana ba Hajiya tace ina ruwan uwar son kad’e kad’e, ce mata tayi taje sun gaisa daga baya hakan ba K’aramin dad’i yay ma Fatuu ba ta juya, ji tay kaman ta koma part d’inta kawai ba sai ta ci Abincin ba saidae ta san Hajiya dole tayi Magana, bayan ta shiga Kitchen tsaye tay gaba d’aya ta rasa mike mata dad’i don tana zargin ba hakanan Farhar tazo ba ba kamar data ganta ita kadae, ita dake dad’ewa bata zo ba kuma saidai suzo gaba d’aya, zuciyar ta ce ta raya mata k’ilan ma yanzu d’in ba ita kad’ai tazo ba sai kuma ta sake raya ai kuma da taga sauran a parlorn, yanke tafiya da Abincin part d’in su tayi ta ci acan, bayan ta zuba har saida tay d’an jimm a bakin k’opa kafin ta fito, ganin hankalin Hajiya na akan tv yasa ta bi ta kopar baya idanun Farha a kanta, bayan fitar Fatun da d’an lokaci Farha ta mik’e ta nufi Hanyar Bedroom, tana zuwa ta d’an juyo ta kalli Hajiya ganin bata ganinta ta wuce itama ta bi ta kopar bayan ta fuce,
Bayan ta koma part d’in nasu kitchen ta wuce ta zubo Abincin a plate ta dawo parlor ta d’aura akan c-table ta fara ci, bata dad’e sosae da fara ci ba taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta, Farha ce ta shigo har saida gaban Fatun ya Fad’i ta dakata da cin Abincin tana kallon ta, nufo cikin falon tay tana tafiya cike da isa ta tsaya daga gaban Fatun suka fara kallon kallo ta wani kalan had’e rai can ta ja wani dogon tsoki ta nuna Fatuu da yatsa a fusace tace “You bastard! how dare u married my sister’s Husband!!!” Shiru Fatuu tay tana kallonta, a hasale ta matsa ta kai duka hannuwanta jikin c-table d’in ta d’ago shi ta kifa ma Fatun shi Abincin ya 6aro a jikinta da sauri ta mik’e don yana da d’an zafi ga c-table d’in ya dakar mata gwuiwa, hannu ta kai ta maida table d’in ta d’ago tana kallon Farhar tana fitar da numfashi da sauri da sauri ita kuma Farhar sai huci take, a zafafe taci gaba “U must leave dis house tunda ba gidan uban ki bane, wllh sai kin bar shi talakan banza talakan wofi a gold digger” tsoki ta k’ara ja ta juya har tayi d’an taku ta juya tana nuna Fatun tace “in na k’ara ganin kin je d’aukar Abinci sai na saka maki poison kin mutu kuma ba abunda za’ai man na kashe Banzaaa” tana fad’in hakan ta juya ta tafi, tsaye Fatuu tay a wurin tamkar an dasa ta zuciyarta sai harbawa take da k’arfi k’afafuwanta na d’an yin rawa, ta d’auki lokaci a hana kafin jiki a mace ta zauna kan kujera, sosae Maganar Farhar ta k’arshe tay tasiri a kanta don yadda take nuna mata tsana tasan zata iya aikata mata hakan, da k’yar ta mik’e gwuiwowinta a sanyaye ta nufi Kitchen don ta d’aukko abunda zata gyara wurin, bayan ta gama gyarawa Bedroom ta shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay tsuru, in tace taji dad’in zuwan Farha tayi k’arya don tasan yanzu kwanciyar hankalinta ya k’are ba kamar data gane dalilin zuwan nata, k’arshe dai Abincin da bata ci ba kenan. Da daddare bata je part d’in ba balle taci Abinci sai kawae ta yanke ta dafa indomie taci, bayan ta gama dafawar bedroom ta wuce da ita, sam tama kasa sakin jiki taci indomie d’in don har bakinta ba dad’i take jin shi, yar kad’an taci ta mik’e ta maida ta kitchen, komawa tay Bedroom ta haye gado ta zauna ta shiga duniyar tunani, a ranta take raya ita bata ga amfanin wannan auren ba dama su rabu kawai ta huta don ba komai a cikin shi sai tashin hankali gashi wanda take zaune don shi ya yi tafiyar shi ya barta ko damuwa bai yi da ita ba, daga tafiyar shi zuwa yanzu zata iya k’irga sau nawa suka yi waya itama ba wani Magana mai tsawo ba iyaka ya tambayi yadda take ko chat basu yi, idanunta ne suka ciko da k’walla saidai bata bari sun zubo ba don itama yanzu har ta gaji da yin kuka, tana haka Mino ta shigo ta k’ak’alo murmushi tayi mata ta nufo ta itama tana murmushin, a bakin gadon ta zauna ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata gwaggo na gaishe da ita ta d’aga kai, tambayar ta tay ko bata lafiya ne ko wani abu na damunta taga kaman fuskarta ta canza tana murmushi tace mata lafiyar ta lau ta tambayi taci Abinci tace eh bata dad’e data gama ci ba, ce mata tay akwae sauran indomie data rage a Kitchen in zata ci, mik’ewa tay tace to bari ta d’aukko. Bayan sun gama shirin kwanciya Mino ta kwanta ita kuma ta d’aukko jakar ta don tayi karatun test da suke cikin yi Saboda exam d’in su ta matso, tana zaune a kan gadon tana karatun aka turo kopar ta kai idon ta da sauri don bata tsammaci wani ba a lokacin mantawa ma tayi bata kulle kopar ba, Farha ce ta shigo tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa kanta sanye da hula, nufo cikin d’akin tay cikin d’acin rai ta tsaya bakin gadon tana masu kallon rashin Arzik’i, nuna Mino tay a wulakance tace “Who is she?” shiru Fatuu tay kaman bazata tanka mata ba sai kuma ta bata amsa da kanwarta ce, tafa hannuwa Farhar ta shiga yi da alamun mamaki tace wato har talakawan yan’uwanta ke zuwa kwakwa suma kenan” banza Fatuu tay mata tay k’wafa a fili ta furta duk zata yi maganin su, ce mata tay anan zata kwana don haka ta tasheta ta bata wuri, Fatuu dake kallon ta tace mata ai ga wuri nan sosae ba sai ta kwanta ba, yamutsa Fuska tay ta furta “God forbid! ni zan kwanta da pauper kina son ta goga man talauci ne” ta d’age ma Fatun gira tana kallon ta shek’ek’e, tasan fitina take nemanta da ita hakan yasa ta kai hannu ta fara tada Mino d’in, bayan ta farka tace mata ta saukko daga kan gadon, tambayar ta tayi lafiya tace mata eh kawai, saukkowa tayi ta tsaya sai lokacin ta lura da Farha dake mata kallon k’ask’anci, ganin yanayin fuskar ta yasa bata ce mata komai ba, wardrobe Fatuu ta bud’e ta fiddo bargo tazo ta shimfid’a ma Mino a saman Carpet ta d’aukko mata filo, bayan ta gama tace mata ta kwanta anan, da alamun rashin fahimta tace mata miya faru bazata kwanta a gadon ba kafin ta bata amsa a fusace Farha tace daga gidan uban su aka kawo shi ne, waro ido Mino tayi baki a d’an bud’e take kallonta ba tare data ce komai ba dama ita bata da rigima Fatuu ce mai rigimar yanzu kuma tayi sanyi lakwas, kwantawa Mino tayi itama Fatuun ta zauna a gefenta taci gaba da karatun, bata dad’e da zama ba taji Farhar ta watso mata zanin gadon dake shimfid’e a kan gadon da duvet harda pillows, hannu ta kai ta cire bedsheet d’in daya rufe mata fuska rai a 6ace tace mata ba gadon take so a bar mata ba kuma gashi nan an bar mata miyasa zata watso mata kaya tana yatsina tace ta d’aukko mata wasu wad’annan an goga masu talauci, sosae ran Fatuu ya 6aci bata dai ce mata komai ba kaman bazata d’aukko ba sai kuma ta mik’e taje ta fiddo wasu ta kawo mata ta aje akan gadon ganin zata juya tace mata bazata shimfid’a mata ba ko banda gadon rashin Arzik’i harda gadon rashin iya tarbar bak’o tayi, bata ce mata komai ba ta shiga shimfid’a mata, bayan ta gama ta koma ta kwashe wanda ta watso ta linke su ta kai Wardrobe, gaba d’aya Fatuu ta kasa yin karatun don tun bayan data kwanta ta fara kunna wak’ok’i gashi ta k’ure volume, k’arshe mik’ewa tay ta d’auki books da jakar tata ta fita daga d’akin ta koma parlor, bata dad’e sosae da komawa ba sai ga Mino ta fito a gigice tana kuka jikinta sharkaf da ruwa sai kerma take ta nufo cikin parlon, da sauri Fatuu ta mik’e ta tarbeta tun kafin ta tambaye ta abunda ya faru ta shaida, rai 6ace ta tambayi mi tayi mata ta watsa mata ruwa tace itama bata sani ba kawai tana cikin bacci taji ta watsa mata su da yawa, duk yadda Fatuu ta so kar tayi kuka ta kasa jurewa sosae Mino ta bata tausayi, zaunar da ita tayi kan kujera tace tana zuwa, Bedroom ta nufa saida ta tsaya a bakin k’opa ta goge Fuskar ta sosae sannan ta shiga, tsayawa tay daga bakin gado rai 6ace take kallon Farha dake latsa waya tace “mi tayi maki kika watsa mata ruwa haka!” banza ta mata sai kace bada ita take ba, k’ara maimaita tambayar Fatuu tayi saida ta mula sannan ta d’ago ido cike da isa tace snoring take mata daga haka ta maida idon kan waya, shiru Fatuu tay tana mata wani kallo jin sharrin data ja ma Mino na wai munshari take mata ita tasan bata yin shi tunda tare suke kwana, tunowa da ta baro Minon a jik’e yasa ta juya ta nufi wardrobe, kayan da zata canza ta d’aukko da su bedsheet d’in da Farha ta watso ta kinkima ta fita, bayan ta bata kayan ta canza tayi mata shimfid’a akan Carpet d’in parlon tace ta kwanta, kallon Fatun tayi ta tambaye ta wacece Farha nan ta bata labarin ta harda dalilin daya sa take mata hakan,
“to ki fad’a ma Hajiya abunda take mana” shiru Fatuu tay tana nazari can tace mata suyi hak’uri kawai yanzu in ta fad’i ma Hajiya ta d’auki mataki akanta Mamar ta itama tana iya yi mata wani abun, kamar Mino zata yi kuka tace to yanzu haka zasu cigaba da zama tana masu haka, shiru Fatuu tay gaba d’aya ta rasa mike mata dad’i can tasa Kuka bak’in cikinta wanda duk ake mata haka Saboda shi baima damu da ita ba ganin tana kukan yasa Mino d’in ma cigaba da yi, daina yin kukan Fatuu tayi tace itama ta daina komai zai wuce bada dad’ewa ba, rok’onta tayi akan Kada ta fad’i ma gwaggo tace to tace ta kwanta, zaune Fatuu tayi ta kasa cigaba da yin karatun ma idon ta akan Mino dake kwance ta lullube, wani irin tausayin ta take ji tunani take ko tace ta daina zuwa kwanan saidae tasan dole gwaggo zata tambayi dalili, haka tay zaune tsawon lokaci sai can dare ya nitsa sannan ta kwanta,
Washe gari da wuri Fatuu tace ma Mino taje gida sai ta k’ara yin baccin acan tace to baiwar Allah harda ce mata to tazo suje tare tunda ba Makaranta itama tayi baccin tace mata a’a ko taje gwaggo korota zata yi, kaman bazata tafi ba tsoronta kada ta tafi Farhar tayi ma Fatun wani abu haka dai ta tafi, bayan tafiyarta Fatuu ta kwashe kayan shimfid’ar ta maida d’aki Farha na kwance baje baje ko salla bata tashi tayi ba, dawowa parlor Fatuu tay ta zauna tama rasa mi yakamata tayi, tsawon lokaci tana anan saiga Saude tazo kawo mata breakfast, akan c-table ta d’aura suka gaisa ganin yadda Fatun tayi tsuru yasa ta zauna tana tambayar ta miya faru a sanyaye tace mata ba komai, tana shirin k’ara yi mata magana sai ga Farhar ta fito duk suka kalleta ta wurga masu wata uwar harara ta wuce, bayan ta fita da alamun mamaki Aunty Saude ta kalli Fatuu tace mata mi tazo yi nan ne taga ta fito daga Bedroom, shiru Fatuu tay ta sunkuyar da kanta nan take Aunty Saude ta gane da wani abu dama gashi ta isketa tsuru a parlor, matsa mata tayi kan ta fad’i mata Fatun ta fara fad’i mata duk abunda tayi masu da cewar da tayi zata saka mata poison a Abinci tana yi tana goge kwalla, ran Saude ne ya 6aci tace aikuwa yanzu zata je ta fad’i ma Hajiya dama ita tasan ba abun Arziki ya kawo ta ba, rik’eta Fatuu tay ta hau yi mata Magiya kan karta fad’i na Hajiya tunda tasan ba dundundun ta zo ba ta k’yaleta tayi ta gama yanzu in aka fad’i ma Hajiya tana iya cewa ta koma gida kuma Hajiya Maryam zata ga an korar mata D’iya Saboda ita koma bata yi niyyar yi mata wani abu ba hakan na iya sawa ta cutar da ita tunda dama gani take suma kamar asiri sukai ma Hajiyar, shiru Aunty Saude tayi tana nazarin Maganar, da damuwa tace to yanzu haka zata k’yaleta tay ta mata rashin mutunci, d’an murmushi mai cin rai Fatuu tay tace mata ba komai kawae dai tana son ta taimaka mata zata daina zuwa cin Abinci bata son Hajiya ta gane koda tayi mata Magana tace tana zuwa amsa ala bashshi sai ta rink’a dafawa kawai, cewa Saude tay ta bari zata rink’a kawo mata tasan yadda zatayi Hajiyar bazata tuhumi dalilin daina zuwan nata ba Fatun tace ta barshi kawae tunda akwae kayan Abincin tace amman ya za’ai ace sai ta dawo daga Makaranta sannan ta dafa kawai zata cigaba da kawo matan in yaso randa ba Makarantar sai ta dafa tayi mata godiya.
A daddafe tayi Weekend d’in nan, Ranar Monday tunda taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta tana cikin damuwa don har fad’awa fuskarta tayi, bayan anyi break ne ta tambaye ta abunda ke damunta nan ta kwashe game da abubuwan da Farha take mata ta fad’i mata, tun kafin ta gama yanayin fuskar Fauzy ya canza bayan ta gama fad’i mata rai a matuk’ar 6ace tace “inta fasa kashe ki bata haihu K’wara ba don ubanta! ke kika k’yaleta wllh” yamutsa Fuska Fatuu tay tace to ya zatayi, a hasale Fauzy tace “wane ya zaki yi, ba ita take neman ki da rigima ba, kamata zaki ki lakad’a mata shegen duka kinsan dama irin haka sai kun had’a jiki mutum yaji a jikinshi sannan yake shiga taitayin shi” sakin baki Fatuu tay tana kallonta Fauzyn tace “ko tafi k’arfin ki ne? In tafi k’arfin ki ni ki bari in zo mu had’u mu had’a mata jini da mijina wllh zaki ga ta kiyaye ki” da sauri Fatuu ta hau girgiza mata kai tace ba zasu yi haka ba a kyaleta kawai, a hasale Fauzy tace “Wato kin fi son tay ta cusa maki bak’in ciki ko har wani ciwon yazo ya kamaki ga jarabawa a gaban mu” watsa hannu Fatun tay ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tace “Fauzy ko mi zatai man tayi ba kowa yaja man ba face Ya Haisam, duk abunda ake man Saboda shi ne kuma shi bai damu dani ba ya tafi ya barni Saboda bai sona, na tabbatar da yana sona ba yadda za’ai ya tafi tsawon wata guda da rabi ba tare da ya waiwaye ni ba tunda yana da halin ko duk sati yaso zuwa nan hakan ba wani abu bane a wurin shi, ni na rasa gane kan wannan Auren namu da yasan haka zai man da tun farko bai amince yaci gaba da zama dani ba, in don abunda ya faru ne naje na bashi hakuri kuma yace ya hak’ura to miyasa ya canza man, miyasa bai damu dani ba…., miyasa son shi yak’i barina kwata kwata, miyasa nike tunanin shi tunda shi bai damu dani ba….miyasa ba zai sake ni ba kawai in San ban tare dashi ko na cire shi daga cikin zuciya ta…..” tana Maganar k’walla na zubo mata har tazo ga6ar da ta saki kukan mai cin rai ta fad’a jikin Fauzy da itama kwallan ne suka fara zubo mata, wani irin tausayin ta da bata ta6a ji ba ya kamata ta shiga d’an bubbuga bayanta tana rarrashin ta, ita kanta ta fara kokonton anya Ya Haisam na son Zarah kaman yadda suke hasashe kuwa, zuciyar ta ce ta fara raya mata aikata wani abu……
Kafin a tashi tace ma Fauzy zata rink’a bin ta Hostel sai yamma ta koma gidan don gaba d’aya bata jin dad’in gidan tace to Hajiya fa ba matsala taga bata komawa da wuri tace zata fad’i mata suna tsayawa karatun jarabawa ne tasan zata fahimta tace to, kiran Tk tayi ta sanar dashi kada yazo d’aukar ta ya d’aukko Mino kawai ita sai yamma zata dawo kuma ba sai yayi wahalar zuwa d’aukarta ba zata hau Keke Napep, bayan an tashi suka nufi Hostel, suna zuwa salla suka fara yi bayan sun gama Fauzy ta had’a mata Madara da biscuit tace ta fara sha bari ta dafa masu Abinci, tana gama sha lokacin Fauzy na cikin dafa masu Abincin ta mik’e tace bari taje ta watso ruwa har Fauzy nace mata zata iya shiga toilet d’in su kuwa tana yar dariya tace mi zai hana, cire kayanta tayi ta d’aura towel Fauzy ta kalleta tace mata wllh duk tayi d’an wuya tay murmushi kawai, bayan fitar ta Fauzy ta mik’e ta nufi inda ta tashi ta zauna ta kai hannu ta d’auki wayarta, zurfin tunanin anya Ya kamata tayi abunda take tunanin yi kuwa ta shiga, fargaba ce tay mata yawa ta maida wayar ta aje ta bar wurin, bayan Fatun ta fito tace ma Fauzy ta bata yar riga mara nauyi tasha iska kafin ta tashi tafiya ta d’aukko mata, bayan ta gama saka rigar hayewa tay saman gado ta kwanta suna d’an yin hira da Fauzy, a hankali ta fara lumshe ido Fauzy na fad’in kada tayi bacci bata ci Abincin ba tace ai ba yunwa take ji ba in ma tayi sai ta ci in ta tashi, baccin ne ya dauketa Fauzy ta zuba mata ido tana ta wasi wasin abunda take son yi acikin zuciyar ta can ta mik’e ta nufi gadon da take ta kai hannu ta d’aukko wayarta ta dawo ta haye saman gadon zuciyarta nata harbawa hannuwanta har d’an kerma suke ta shiga daddana ta…….”
____________________
Fanan zaune asaman doguwar kujerar dake a cikin parlon su ta haye saman ta gaba d’aya tana sanye da yar fingilar riga da iyakarta tsakiyar cinyoyinta hannun ta kuma irin na vest kaman dai rigar bacci ce ta d’an rankwafa tana lallatsa computer d’in dake gabanta hakan yaba brown gashin ta damar zubowa ta gefe da gefen fuskar ta, daga gefen ta kuma takardu ne lokacin su can dare ne don har anyi sallar isha, tun bayan da Haisam ya aje wayar shi ya tafi had’o masu Coffee take ta damun ta da k’arar notifications, dakatawa tay ta kai hannu ta d’aukko wayar don ta kashe Wi-fi d’in wayar ko sakonnin sun daina shigowa, tana latsa power haske ya kawo jikin Screen d’in idon ta ya sauka akan sunan da tasan ya saka ma Fatuu alamar ta turo mashi sako, d’an murmushi Fanan d’in tayi a ranta ta raya wato da ita ne ta daina zumunci kenan, bayan ta kashe ta maida wayar ta aje, har taci gaba da abunda take kawai taji tana son ganin sak’on miye Zarah ta turo mashi, hannu ta kai ta d’aukko wayar ta sake kunna hasken ta bud’e, kan sakonnin WhatsApp ta danna ta shiga ciki, sak’on Fatuu ne last da aka turo hakan yasa ya kasance a sama ta kai hannu ta ta6a ya bud’e, gyara zama tayi ta fara Karantawa……………….
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 da 3 Naira 400 ne za’a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za’a turo shedar biya ta wad’annan nos din 09013804524 ko 08169856268
…
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.