Hausa novels
Trending

Abban Sojoji Page 58 Book 2 Complete Novel

Abban Sojoji Page 58 Book 2

Father of soldiers (takun ƙarshe)

Written By Boss Bature

A tsananin tsorace take kallon fuskarshi ganin ya ware idanunshi yana kallon fuskarta,a hankali ya zame finger ɗinshi daga saman tausasan la66anta dake ta faman kerma,sai faman haɗiyar yawu take yi tsoranta wane hukunci zaiyi mata,sau biyu yana ƙoƙarin buɗe mouth ɗinsa zaiyi magana amma ya kasa,saboda ya rasa me zaiyi ma yarinyar,tun da yake wata ƴa mace bata ta6a ƙetare iyakar da yarinyar ta ƙetare ba,a matsayinta na wadda ba muharramarsa ba kuma ƴar aikin gidansu,ƙara matsawa yayi kusa da ita,cikin sauri sehrish ta ƙara ja da baya,tana faman girgiza mashi kai Alamar yayi haƙuri karya hukunta ta,tuni ta soma fitar da ƴan matan hawaye a idonta,ba komai take kallo ba face damtsen hannunshi da kuma wannan faffaɗan ƙirjin nashi,uwa uba yarda ya tsaya agabanta tamkar wani zaki.

 

Hannunshi yakai tare da ruƙe waist ɗinshi yana kallon yatsun hannunta dake ta faman kerma,

A natse ya soma magana”I will punish you for the mistake you made in my bedroom on my bed,so that you know under whom you are working,cos u crossed your boundary,”

Gabanta ne taji yayi wani irin bugu jin abunda sgr yace,hankali tashe take kallonshi,muryarta har kerma take wurin cewa”bazan ƙara ba,”

girgiza kanshi yayi alamar bai amince ba sannan yace”You are going to start frog jumping around the chairs without stopping, if you do that I will let you go, but if you dare stop,I will punish you badly,” yana ƙarasa maganar tashi ya juya tare da komawa saman sofa ɗin yana kallonta yace”Am watching u,”yayi maganar tare da nuna mata blue eyes ɗinshi da 2 fingers ɗinshi,alamar idonshi na akanta,

Tamkar ta fashe da kuka haka taji,ga matuƙar tsoranshi da take ji,ga punishment ɗin daya bata na tsallan kwaɗi abunda ta tsana arayuwarta saboda tasan wahalarshi,ba abune mai sauƙi ba bazata ta6a mantawa da lokacin da fawan ya sanyata frog jump ba har jini ya 6alle mata,saboda tsabar wuyar da tasha har suma tayi lokacin,

gyaran muryar da Sgr yayi mata ne yasa tayi saurin zuƙunnawa tare da kama kunnanta da hannayenta sannan a hankali ta soma yin tsallen kwaɗin,in da Allah yasota ma Wando ne ajikinta ba skirt ba da abun yafi muni,da sauri take yin tsallen har ta zagaya ta bayan sofas ɗin ta kuma dawowa ta gabansu duk yana kallonta,tun Sehrish tana yin tsallen kwaɗin cikin daɗin rai har ƙafafunta suka soma rurruƙewa,wani irin zogi suka shiga yi mata,nan take hawaye suka fara shararowa daga idanunta har da majina duka ta haɗa,

Yana jin shessheƙar kukanta amma ko ajikin shi,a ƙarshe ma sai ya ɗauki lemu mai sanyi ya tsiyaya acikin cup ya shiga kur6arshi a bakinsa yana sha,tun yana shan lemun daga zaune har ya ɗan kishingiɗa kafaɗarshi saman sofa hand ɗin,

A wani irin galabaice sehrish ke ɗaga kafafunta tana yin tsallen kwaɗin,a ƙalla ta zagaye kujerun kusan sau takwas amma sgr baice ta dakata ba,tun tana sa ran zai tsayar da ita harta fidda rai,saboda tsabar tsoro da firgicin da take ciki yasa ta gaza gane cewa sgr fa bacci ya kwashe shi asaman sofa ɗin,duk in ta zagayo ta wurinshi sai taga kamar idonshi biyu,batasan cewa tuni bacci yayi awon gaba dashi ba,har ya ajiye cup ɗin dayake shan lemun dashi,

 

Wani irin matsanancin ciwon kaine ya far mata,ga raɗaɗin da kafafunta keyi mata,lokacin da ta ƙara zagayo wa ta wurin shi,cikin shessheƙar kuka tace”…Am really sorry babban yaya,i ave realized my mistake,bazan ƙara ba nayi maka alƙwarin hakan,” tabbas yajiyo muryarta acikin ears ɗinshi amma sam bazai iya buɗe idanunshi ba,saboda nauyin baccin da yayi,

Ganin bai tanka mata ba,yasa sehrish cigaba da yin tsallen kwaɗayin da takeyi dakyar dakyar,tana cikin wannan yanayin wani irin stomach pain ya taso mata haikam,nan take ta yanke jiki ta faɗi saboda galabaitar da tayi,taji jiki sosai,

 

Sai faman zagaye hayam takeyi a tsakanin upstairs da kuma down,ba don komai ba sai don taga a wani yanayi Sehrish zata fito daga sashen sgr,har wani murmushin mugunta take saki don tasan cewa muddin Sgr yaga siraran gashi a cikin abincinsa dole ya kikkifa Mata mari,sannan ya kore ta daga yi mashi aiki,daganan  ita kuma zata samu shiga a wurin shi,gajiya ta fara yi da zagayen ganin cewa har ƙarfe sha biyu na dare tayi Sehrish bata fito daga part ɗinshi ba,hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,baƙin ciki kamar ya kashe ta,tsayawa tayi ruƙe da qugu tana cewa”Ko uban me yarinyar can takeyi a part ɗinsa har wannan lokacin bata fito ba!wlh na tsani yarinyar can,ko son ganinta bana yi,shisshiginta yayi yawa nasan yanzu haka tana can ta liƙe mashi tana kalle mun surar jikin mijina,Allah bazan ƙyaleta ba sai nayi maganinta mtssw,!”ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki sannan ta kama hanyar komawa bedroom ɗinta tana faman sambatu kamar wata zautacciya ,”

 

_💋Boss Bature💋_

 

Kwance yake asaman gadon Abbansu hannunshi rungume da pillow,yayin da idanunshi ke arufe tamkar mai bacci,

Yana jin lokacin da abbansu ya fito daga cikin toilet jikin shi sanye da Jallabiya,ƙarasowa yayi wurin gadon tare da samun wuri daga ɗan gefe ya zauna,sannan ya ɗan juya tare da kallon fuskar junaid da yayi likimo kamar mai bacci,hannu yasa tare da shafa sumar kanshi yace”sarkin rigima yayi bacci,”ya faɗi da murmushi a fuskarshi,janye hannunshi yayi daga saman sumar kan junaid,sannan ya miƙa hannu tare da ɗaukar wayarshi dake ajiye a saman bedside drawer,contact ɗinshi ya shiga ya lalubo numbar mommynsu junaid ya danna mata kira,nan take kiran ya shiga,cikin sa’a ta ɗaga kiran nashi,murmushi yayi tare da kara wayar a kunnanshi yace”Noorul ƙalbina”

On the other hand alexandra tace”yau kuma soyayyarce ta motsa?ni zaka yaudara da kalamanka saboda kaji cewa zanzo nigeria ko?to ae ba saboda kai zanzo ba,zanzo ne don naga Yarona kuma da zarar nazo zan ɗauke abuna na dawo Australlia dashi,don bazan barshi a hannunku ba don ban yarda da irin rainon da kake mashi ba,”

girgiza kai abbansu yayi tare da cewa”Yaushe zaki canza ne?ke ko tausayina bakya ji ne?baki damu da halin da nake ciki ba,na rashinki a kusa dani,ina fa sonki har yanzu kuma ban rabu dake ba,kece kika rabu dani kika kama hanya kika bar ƙasar nan batare da sani na ba,yanzu kinyi mun adalci”? Cikin sanyin murya ya ƙarasa maganar yana sauraron Amsarta

Junaid daya kasa kunne yana sauraransu sai faman murmushi yake yi idonshi a rufe,

Shiru Alexandra tayi yayin da idanunta ke kallon sararin samaniya ta cikin windown katafaren bedroom ɗinta,kunnanta na kare da wayarta tana sauraron shi,muryarshi ta kuma ji yana cewa”kinyi shiru baki ce komai ba”?

Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗan jinjina kai tace”me kake so yanzu”?

Runtse ido abbansu yayi saboda ya rasa yarda zai fahimtar da ita,wata irin bauɗaɗɗiyar mace ce,ko don tayi aikin soja ne yasa ta kasance haka,saboda a tsaye take ba irin raunin zuciyar nan na mata,

“Hossein in baka da abun cewa,Ni zan aje waya ne,”

Muryarta ce ta kuma katse shi,a lokacin ranshi ya gama 6aci a faɗace yace”Fatima na gaji da irin wulaƙancin da kikeyi mun,nayi danasanin haɗuwata dake tun farko,kuma nayi danasanin haɗa zuri’a dake,saboda kin cutar da rayuwata,sam baki respecting ɗina a matsayina na mijinki,kuma uban ya’yanki,idan kinsan zaki tafi kibarni meyasa tunfarko kika sanyamun soyayyarki acikin zuciyata?

Muryarshi araunace yayi maganar yanayin sautin kamar zai fashe mata da kuka,

 

Jin tayi shiru bata ce mashi uffan ba yasa shi cewa”banaso ki dawo ƙasar nan!ki cigaba da zama acan,saboda zuwan naki baida amfani awurina,kuma babu ruwanki da ƴa’ƴana  dama can baki damu dasu ba,tun da har zaki iya tafiya kibarsu,batare da tunanin yaya rayuwarsu zata kasance ba”!

Jin wannan maganar ta Abban nasu yasa hawaye suka soma gangarowa a idanun junaid,sam baiji daɗin yarda mommynsu ke 6ata ma Abbanshi rai ba,

Bai jira Alexandra ta bashi amsa ba ya katse kiran nata tare da yin wurgi da wayar gefe guda,jiki amace ya kifa kanshi asaman gadon,idanunshi sunyi jawur sun cicciko da kwalla,

a hankali hawayen suka soma gangarowa,kamar daga sama yaji tafin hannu a fuskarshi,cikin sauri yakai idonshi akan junaid dake share mashi hawayen fuskarshi,

Cikin shessheƙar kuka yace”Abba don Allah kadaina zubar da hawayenka akan mommynmu,ba dole sai da ita zaka samu farin ciki ba Abba,Ni na isheka duk wani farin cikin duniyar nan,Abba ka ta6a faɗamun cewa ko kallona kayi kanajin sanyi aranka,why zaka Sanya ma kanka damuwa akan mommynmu?ka rabu da ita kawai Abba,akwai mata da yawa agari waɗanda suka fi ta hankali………’

Murmushi Abban nasu yayi jin abunda junaid yace,

Miƙewa yayi daga zaune suna fuskantar juna yace”junaid bazaka gane ba!mommynku ba kamar sauran mata take ba,idon har tana raye ni bazan iya kula wata ƴa’ mace ba,”

ɗaure fuska junaid yayi tare da zum6ura baki yace”Saboda me Abba?me tafi sauran matan?duk yarda take 6ata maka rai?

“Junaid she’s special saboda ta bani babbar kyautar da har yau in na kalleta nake jin farin ciki araina,”

Cike da mamaki junaid yace”Wata irin babbar kyautace wannan? Ya tambaya yana kallon Abban nasu,

Murmushi Abbanshi yayi tare da nuna shi da yatsanshi yace”Am talking about u junaid!Matar da ta haifamun lu’u lu’u kamarka taya zan iya rabuwa da ita junaid?ta bani farin cikin da har na bar duniyar nan bazan ta6a samun makamancinshi ba,kyakkyawan yaron da kowa ke alfahari dashi,kowa yake so kuma yake ƙauna,Junaid bani da burin da ya wuce in farka in ganka akusa dani da ranka da lafiyarka………..’

Tsagaitawa yayi da maganar yana kallon junaid da bakinsa yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha,sai faman washe baki yake yi,kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna,ya ma rasa mai zaiyi don tsabar farin ciki,a ƙarshe ya faɗa jikin Abban nasu tare da rungumeshi ya ƙankame shi sosai ajikinshi yana faman dariya,

Zagayo da hannunshi yayi yana ɗan bubbuga Bayan junaid yaci gaba da cewa”I love u so much my baby boy,Allah ya nuna mun ranar auranka kafin nabar duniya,koda ace shine abu na ƙarshe da zan gani kafin na koma ga mahalicci na,Ina rokon Allah ya nuna min wannan ranar,da shagwa6a66an yarona zaiyi aure,zanso naga yaron da matarka zata haifa mana,wanda zamu dinga kira da Babyn baby,”

Fashewa sukayi da dariya, suka dinga yi atare,har lokacin basu raba jikinsu ba,

Ƙarar shigowar message a wayar Abban nasu ce,yasa junaid janye jikinshi daga na abban nasu sannan ya rarrafa tare da kai hannu ya ɗauko mashi wayar,ya miƙa mashi,

Kar6a Abba yayi tare da duba message ɗin da aka turo mashi yana karantawa kamar haka

“Forgive  me my love…….nasan na 6ata maka rai sosae,kayi haƙuri ka yafe mun kuma inaso kasan cewa nima ina sonka sosai har yanzu ba abunda ya sauya na sonka acikin zuciyata,zan dawo nigeria ne saboda na gyara alaƙata da uban ƴa’ƴana,da kuma ƴa’ƴan nawa,ka shirya tarbar amaryarka Alexandra………..’

gaba ɗaya ya rikice saboda tsabar farin cikin saƙon da ya shigo mashi,saboda ruɗu har hannu yasa yana goge idanunshi wai ko badaidai ya karanta bane,saboda tunda yake arayuwarshi alexandra bata ta6a bashi hakuri ba,bai ta6ajin kalmar sorry daga bakinta ba,koda ace tayi mashi laifi sai dai shiya bata haƙuri ya rarrashe ta amma badai ita ba ae tafi ƙarfin wannan,amma yau ita da kanta take bashi hakuri!?_

Ganin yarda Abban nasu ke ta sakin murmushi yasa junaid cewa”Abba menene naga kamar farin ciki a fuskarka,”

Miƙa mashi wayar abban nasu yayi dama tsakaninsu babu 6oye 6oye,

“Junaid dubamin ka gani,kodai idona ne ke nunamin ba daidai ba,wai mommynku ce ke ban haƙuri da kanta,”

hannu junaid yasa ya kar6i wayar daga hannun Abban nasu ya shiga karanta saƙon,nan take yaji wani irin sanyi aranshi,

“Junaid baka ji farin cikin dana ji ba wlh,naji daɗin saƙon nan na mommynku,da ace bataban haƙuri ba da bansan a wani yanayi zan kwana ba yau,”

Murmushi junaid yayi bayan ya kammala karanta saƙon cike da zolaya yace”Su Abba an kusa angwancewa,amarya mommyn junaid zata dawo,amma dai Abba idan tadawo nigeria ba zaka kore ni daga kwana bedroom ɗinka ba ko?

Wani irin kallo abban nasu ya jefa mashi tare da cewa”Ae aranar da tadawo,zaka tattara yanaka yanaka kabarmin ɗakina,dama nagaji da kwana tare da ƙato a ɗakina…..’kasa ƙarasa maganar yayi saboda dariyar daya kwashe da ita,junaid kuwa tsuke fuska yayi yace”Allah Abba ba inda zanje ko mommy ta dawo,sai dai mu rinka kwana tare daku,ku sanyani a tsakiyarku muyi bacci atare,” ashagwa6e ya ƙarasa maganar tashi,

harara abba ya watsa mashi tare da cewa”Allah ya kiyaye mu kwana tare da kai,”

Da buɗar bakin junaid sai cewa yayi”Abba kaima ya haramta a musulunce ka kwana tare da mommynmu……’tunkan ya ƙarasa maganar tashi,Abban nasu ya wawuro pillow tare da buga mashi asaman kanshi yana cewa”gidan ubanwa ka ta6a jin haka junaid?waya koya maka wannan kalamin ƙabihin?

dariya junaid ya shiga yi yana tarbe pillown da yake bugun shi dashi,gaba daya suka shiga yin wasan bugu da pillow shi da abban nasu,yarda kasan wasu ƙananun yara,sun jima suna shiririta kafin daga bisani bacci ya kwashe su gaba ɗayansu kowa hannun shi ruke da pillow,

 

_💋Boss Bature💋_

 

Tun bayan da Jahad ta haɗo mashi abincin a tray,ta kawo mashi anan ƙasa ya sauko tare da hossana suka zauna,da kanshi ya dinga ɗebo abincin yana bata abaki tana ci,sai da ya tabbatar da taci ta ƙoshi sannan ya ƙyaleta,ya jima a wurinsu suna fira atare gwanin ban sha’awa kafin daga bisani wurin sallar isha’e yayi masu sallama da nufin zaije yayi sallah ya dawo kafin ya wuce gida,

 

Lokacin da Omar ya dawo,bai same su a palourn ba babu kowa aciki,hakan ya tabbatar mashi da cewa sunyi bacci don yadan jima daya fita masallacin,tsayawa yayi yana tunanin ya tafi ko ya tsaya,harya juya yaji cewa bazai iya tafiya batare daya ƙara sanya Hossana a idanunshi ba,

juyawa yayi tare da nufar bedroom ɗinsu,a hankali ya tura door ɗin ɗakin,sannan yasa kai ya shiga da sallama abakin shi,

Sunyi nisa acikin baccinsu,hankalinsu kwance sai faman sharara bacci suke yi,kowaccen su na sanye cikin kayan baccinsu,jahad riga da wando farare,hossana kuma ƴar riga ce dai dai guiwa pink colour,sharara rigar take,saboda daɗin bacci ta hankaɗe rigar tayi sama hakan ya bayyana santala santalan cinyoyinta da suka ji hutu,dama bata iya kwanciyar bacci ba,

tsayawa Omar yayi yana kallonsu ta hanyar hasken Bedside lamps ɗin da suka kunna,sun haskaka wurin gadon nasu,yarda suke bacci cikin kwanciyar hankali ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,har ya yanke shawarar ya juya yabar bedroom din idonshi suka sauka akan laps ɗin hossana dake dan  kerma alamar sanyi ya kama kafafunta,kafin su kwanta sai da Jahad ta lullu6esu,cikin bacci hossana tayi wurgi da bargon gaba ɗaya,ya yi gefe guda can ƙasan ƙafafunsu,

ƙarasawa ciki omar yayi da nufin ya rufe su da bargon,amma tunda ya isa wurin gadon,ya gaza janye idanunshi daga kallon surar jikin hossana,abun da bai ta6a yi ba,tamkar ana ingiza shi zuwa gare ta haka ya dinga ji,nan take yaji wata irin ƙishirwar sha’awarta ta kama shi lokaci guda,gaba daya ya makance akanta har baisan lokacin da ya faɗa jikinta ba gaba ɗaya,ya shiga ƙoƙarin biyan buƙatarshi,tuni ya zame hannun rigar jikinta,ya sulale ta izuwa kasa har wurin stomach ɗinta,ba ƙaramin rikicewa yayi da gani booobs ɗinta ba,a cike fam suke tuni suka tsone mashi ido,gaba daya omar ya farmasu kyakkyawar damƙa yayi masu ya shiga murzasu a hannunshi,jikin shi har kerma yake yi,laushin su ba ƙaramin gigita shi su kayi ba hakan yasa yakai bakinsa gaba ɗaya,

A wani irin firgice hossana ta farka saboda raɗaɗin da taji kan nipples ɗinta,jin mutum asaman jikinta yasa ta fasa wata irin razananniyar ƙara mai sautin gaske tana faɗin”Jahad!!jahad!!nashiga uku!Abba zai cutar dani!dan Allah kadaina !ka bari!kada ka kashe ni mutuwa zanyi!dan Allah kabari Abba banso!!!!!gaba daya Omar baya a hayyacinsa ƙoƙarin zame belt ɗin wandonshi yake yi don ya cimma inda yake son zuwa,

Wannan ihun da hossana keyi ne ya farkar da jahad,a wani irin gigice ta yunƙura tare da miƙewa zaune tana kallon wannan tashin hankalin,kamar a mafarki haka take kallon Lamarin,saboda tsabar ruɗu bata gane fuskar waye ba,da hanzarin gaske ta dunƙule hannayenta tare da daddagewa ta ɗuma mashi dundu abayanshi,amma ko gizau Omar baiyi ba sai faman cigaba da abunda yake ƙoƙarin yi yake,

Fasa ihu jahad tayi tana faɗin”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!”gaba daya ta rasa ta yarda zata iya ceton Hossana,ƙoƙarin ruƙo shi ta shiga yi,aikuwa gaba ɗaya Omar yayi wurgi da ita,gaba ɗaya jahad ta gangara ta faɗa ƙasan gadon,kanta ba ƙaramin buguwa yayi ba,kafin jahad ta yunkura ta taso daga faɗawar nan da tayi,hossana ta daddage ta gartsa mashi cizo asaman damtse hannunshi,kusan sau uku tana cizon shi amma ko gezau baiyi ba,gashi harta fasa mashi fatar jikinshi,shaidar jinin harya fara fitowa ajikin farar shirt ɗin dake ajikinshi,

Ganin yana ƙoƙarin zame pant ɗin jikinta daya rage mata,yasa Hossana fashewa da wani irin sabon kuka tana cewa”Jahad kizo ki taimakeni!zai kashe ni!Abba zai cutar da rayuwata!Ya Omar bazai barka ba sai ya kashe ka……..”idanunta na arufe take ambaton hakan yayin da hawaye ke 6ulbulowa daga cikinsu kamar an kunna fanfo,

Lokaci guda tunaninshi yadawo cikin hayyacinshi ta dalilin sunan shi da hossana ta ambata,zaro ido Omar yayi hankalinshi a matukar tashe yake kallon hossana daya raba ta da kayan jikinta,innalillahi wa’inna ilaihirraji’un,A uzubillahi minasshaiɗanin rajim!!!shine abunda ya shiga ambata abakinshi,gaba ɗaya yabi ya gigice kanshi yashiga sara mashi da wani irin matsanancin ciwon kai,kunyar duniya tabi ta baibaiye shi,a hanzarce ya miƙe da saurin gaske ya fuce yabar bedroom ɗin,cikin sa’a batare da Hossana ta buɗe idanunta ba,kuma batare da jahad taganshi ba,dukansu babu wanda ya shaida shi,ƙaramin kuskure kan iya jefa mutum faɗawa tarkon shaiɗan,omar yayi danasanin dawowarshi cikin gidan,yayi danasanin shiga bedroom ɗinsu,in banda tsautsai da ƙaddara bai ta6a gigin shiga ɗakinsu ba sai yau,

Fucewarshi ke da wuya,jahad ta ɗago da kanta daga buguwar da tayi a ƙasa wurin harya ɗan fashe kaɗan,da saurin gaske ta haye saman gadon tana faman shessheƙar kuka,tsayawa tayi tana faman wurga ido cike da mamaki ganin babu mutumin nan dake ƙoƙarin keta haddin hossana,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,6aat babu shi babu alamar shi,

Cikin sauri ta ƙarasa wurin hossana dake a kwance babu kaya ajikinta,da alama suma tayi saboda tsabar firgicin data shiga,

Hannu jahad takai tare da janyo bargo ta lullu6e mata jikinta,sannan ta rungumota ajikinta tana faman ambaton sunanta”Hossana!!hossana!!!”ganin ko motsi taƙiyi yasa hankalin jahad tashi,jijjigata tashiga yi tana cewa”Hossana ki farka dan Allah!!ki tashi!Allah yasa bai kaiga cutar dake ba!nashiga ukuna ni yau!meyasa haka ke faruwa dake ne?burin kowa yaga ya lalata maki rayuwarki hossana!meyasa bazasu barki kiji da abunda ke damunki ba!meyasa bai tunkare ni ba sai ke……..’kasa karasa maganar tayi saboda kukan daya ciyota,mai raɗaɗin gaske,gaba daya ta fashe da matsanancin kuka tana cewa”Ya Allah kasa mafarki nake ba gaske ba!!Allah karka nunamin wannan ranar da zan rasa ƴar uwata!!hossana dan Allah ki tashi kada ki mutu kibarni…….’

Ganin ko motsi hossana taƙiyi yasa jahad sakinta tare da yin saurin saukowa daga saman gadon,da gudun gaske ta fito cikin falon tare da nufar telephone don ta kira Ya omar ɗinsu ta sanar dashi abunda ke faruwa cewa wani ya shigo musu cikin gidansu,

Hannunta har kerma suke yi wurin daukar telephone ɗin tare da danna numbers ɗinsa ta buga mashi kira,Allah Allah take akan ya ɗaga kiran ta sanar mashi saboda tsoran Kada mutumin ya ƙara dawowa,ga kuma hossana dake kwance araye ko amace,

Lokacin da kiran Jahad ya shigo wayar Marshall Omar,yana acikin motar shi bawan Allah,duk yabi ya takure yaji ya tsani rayuwarshi gaba ɗaya,kamar ya binne kanshi haka yake ji,wasu irin zafafan hawaye ne ke gangarowa daga idanunshi sai faman cizon la66anshi yake yi,idanunshi sunyi jawur,

Jikin Major ba ƙaramin sanyi yayi ba,saboda ya gane halin da Ogan nashi yake ciki,ga wayarsa sai faman ringing takeyi amma yaƙi ɗaukota bare yayi picking call ɗin,

A hankali major yayi parking ɗin motar tasu agefen titi ba don komai ba sai don baijin zai iya cigaba da driving yayin da oganshi ke cikin wani yanayi,

Ganin ya tsayar da Motar yasa Omar cewa”major meyasa ka tsayar da motar”?

Cikin sanyin murya major yace”ka gafarce yalla6ai,bazan iya driving ɗin bane,saboda gaba daya jikina amace yake,guiwowina sun sage tamkar anzare lakar jikina haka nake ji,bansan me ya faru dakaiba amma ina da tabbacin cewa wani abu mara daɗi ne yasaka shiga wannan halin da kake ciki,”

Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace”Major yau nayi abun kunya,naji kunya sosai kamar na binne kaine,ashe dama shaiɗan baida tabbas”?yayi tambayar yayin da zuciyarshi ke cigaba dayi mashi ƙuna,

Cigaba da magana yayi”major yau ni da kaina nayi attempting rape,kuma ba kowa nayi yunkurin aikata ma hakan ba face hossana…..’

 

Domin Sauke Littafin book 3 Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button