Hausa novels

Ruwan Zuma Page 6 Hausa Novel

(06) Kwananta goma da dawowa gidansu amma har lokacin hankalinta na kan Abul, ko wani hali yake ciki da ya kwana biyu bai ganta ba, sai Allah.  Bacci wannan gagararta yake yi sai dai kwakwalwarta ta sakata na dole. Abinci kuwa dama ba’a maganarsa, domin tun mutuwar Aliyu ta k’aurace masa shima sai dai ta ta6a kad’an don Sabrin ta samu abunda itama zata ci.  Ta k’ara ramewa ta fige kamar ba ita ba, ga wani duhu da tayi. In ka ganta baza ka d’auka Laila bace tsabar canjawar da tayi, babu wannan jiki mai kyau d’in, babu kwalliyar sannan uwa uba, babu kwanciyar hankali sam.   Ummii tana yawan mata fad’a Idan ta ga tayi zugum tana tunani, amma da ta kwatanta halin da itama zata shiga idan makamancin hakan ya sameta sai ta daina yiwa Laila fad’a, ya dawo itace mai rarrashinta da bata baki. Son dake tsakanin uwa da d’anta ba abun wasa bane.  Baba ma dattaku ne yasa tun farko ya barwa Umma Abul ba don yaso hakan ya faru ba, saboda shi kanshi ya sani ko a musulunce Laila ce ke da hak’k’in rik’e ‘yayanta ba mahaifiyar Aliyu ba. Yau tashi tayi cikin son ganin Abul, haka kawai taji hankalinta ba zai kwanta ba har sai ta ganshi, don haka tun kafin Baba ya fita ta fad’a masa zata je duboshi. “Ki jira idan na tafi shago sai Madu ya zo ya kaiki.”Bata so haka ba domin har yau Madu in banda gaisuwanta da yake amsawa babu maganar dake shiga tsakaninsu.  “Baba da ka bari kawai mu hau abun hawa ni da Mas’ud.””A’a baza ayi haka ba, ki shirya Madu zai zo ya d’aukeki da misalin k’arfe goma.” K’arfe goma da wasu mintuna Madu ya ajiyesu ita da Mas’ud a gaban gidan Umma. Da sallamarta ta shiga gidan shiru kamar babu kowa a ciki, d’akin Umma ta nufa tana mai cewa Mas’ud ya tsaya a waje sai an masa iso.  Sallama ta k’ara yi sannan ta kutsa kai cikin d’akin. A kwance ta samu Umma tana bacci a kan gado yayin da kuma Abul ke gefenta yana numfashi da kyar. Yayi wata muguwar rama kanshi ya fito sosai yana bud’e ido a hankali yana rufewa.  Ganin mamansa yasa ya saki wata kuka wacce da kyar take fita tsabar ya galabaita. Sannan ya d’ago hannu d’aya yana mik’a mata.  Kuka ne ya kwacewa Laila tayi saurin sa hannu ta d’aukesa, sai a lokacin Umma ta farka taga Laila a kanta. Salati ta fara yi sannan ta tashi zaune tana duban Lailan dake sauk’e Abul k’asa ba tare da ta sakashi a jikinta ba.  “Ni Nafisatu me zan gani haka? Yarinya ki shigo har d’akina babu sallama sannan ki tsaya a kaina kina kuka kamar ce miki aka yi mutuwa nayi.” “Umma ki duba Abul bashi da lafiya jikinshi yayi zafi, ga kuma kashi da yayi a jikinshi. Umma me ya sameshi ya rame haka?” Laila ta tambaya tana zubar da kwalla domin ko ita ba uwarsa bace zata tausaya mishi a halin da ta ganshi a ciki. “Kin tsaya kina tuhumata ne akan rashin lafiyar d’anki? Waye baya rashin lafiya? Kuma mak’on uwarsa da yake yi yasa ya rame har hakan ya jawo masa cuta. Kuma gashi har ya fara sabawa dani, yanzu ganinki da yayi kwana zai yi yana kuka kamar ranar da kika tafi.” Laila bata saurari Umma ba ta fita da Abul waje, Umma ta biyota da sauri tana tambayar ina zata kaishi. Sai dai ganin ta kaishi bakin band’aki yasa Umman ta tabbatar wanke masa kashin zata yi, hakan yasa ta koma cikin d’aki tana sababi ita d’aya.  Mas’ud da ya gaishe da Umma ta shareshi yaja tsaki bayan ta shige d’akinta, kana ya maida hankalinshi kan yayarsa dake kiciniyar cirewa Abul kayan jikinshi wanda ya ca6e da kashi.  Da sauri ya isa gurinta ya kunce mata goyan Sabrin sannan ya azata a bayanshi, yarinyar dake bacci ko farkawa bata yi ba taci gaba da baccinta. “Kalti yaron nan ya rame wallahi, dubeshi sai kace bashi ke da k’iba daa ba.” Mas’ud ya fad’a cikin tausayawa.”Ba’a bashi abinci ne, kaji mini yaro da kinibibi.” Suka jiyo muryar Umma daga d’aki wacce ke sauraron duk motsinsu sai dai babu wanda ya tanka mata. “Mama tafi dani, jan biki Mama.” Shine abunda Abul ke furtawa a hankali wanda Laila ce kad’ai ke jiyo sautin muryar tashi.  Kai kawai take d’aga mishi tana wanke masa kashin, ganin k’asusuwan jikinshi da tayi ne yasa ta fashe da kuka, tana gamawa ta ciro wani kayanshi dake kan igiyar shanya ta sanya mishi ta fita daga gidan da gudu rungume da d’anta.  Mas’ud da ke goye da Sabrin yayi saurin bin bayanta domin bai san hakan na cikin tsarinta na zuwa gidan ba. Umma kuma takun sawunsu yasa ta fito da sauri har zaninta na fad’uwa ta ga babu su a tsakar gida.  Wani kuwwa ta saka wanda yasa Muna farkawa daga baccin safe da take yi ta fito a tsorice don ta d’auka gobara ne ya tashi a gidan. Itama bin bayan Umma tayi zuwa zaure tana kwala nata kira, Umma kuma rik’e take da zani tana kiran sunan Laila tana tsine mata. Sai dai ko hangensu bata yi ba sakamakon gudun da suka yi bana wasa bane.  Tuni mutane suka taru a k’ofar gidan suna tambayar ba’asi amma Umma sai kuka take yi tana cewa Laila tsinanniya ce. Sai da aka kira Nazifi ya zo sannan ta fad’a masa yanda aka yi, har tana k’arin cewa Laila tunkud’eta ta yi ta fice da gudu.  Wasu laifin Laila suke gani yayinda wasu kuma ke Allah shi k’ara suna kuma goyan bayan Lailan. Saboda makwabtansu da suke amfani da katanga d’aya su suka san halin da Abul yake ciki, kullum cikin kuka yake, da dare haka zai hana kowa bacci da ihunsa yana kiran uwarsa ‘Mama, Mama’. Kwana biyu ne da suka ji shiru suka shigo yiwa Umma barka wacce bata samun bacci, shine take fad’a musu ai bashi da lafiya ne sannan muryarshi ta dashe tsabar kukan da yayi.  Wani abu da basu sani ba shine Abul bai daina kukan dare ba, dashewar muryarsa yasa su basa iya jinshi amma kuma haka suke kwana a zaune shi da Umma yana kiran sunan mamanshi. Idan abun ya bata haushi sosai sai ta gaggaura masa maruka wai don yaji tsoronta ya daina kukan. Sai dai hakan baya hanashi sai ma yaci gaba, dalilin hakan yasa take baccin safe kamar matacciya wanda yasa har Laila ta shigo d’akinta bata jita ba. Laila da Mas’ud sai da suka isa bakin titi sannan suka tsaya tana nishi tana rungume da Abul a k’irjinta wanda ke sauk’e ajiyar zuciya yana k’ank’ame da ita. D’ago fuskashi tayi tana kallonshi shima ya zuba mata ido, wata k’aramar murmushi yayi wanda yasa zuciyar Laila bugawa da k’arfi dalilin ganin fuskar Aliyu da tayi yana mata gizo shima yana murmushin.   A lokacin kuma a gurin ta sakawa ranta cewa ko duniya zasu taru don su rabata da Abul baza ta basu daman hakan ba.  Mas’ud da ke gefenta shima yana nishi yana gyara goyon Sabrin ya ce, “Kalti Ina tsoron abunda hakan zai haifar mana, amma ki sani duk rintsi ina tare dake.” “Nima ina cikin tsoro Mas’ud amma wannan karon duk abunda zai faru ba zan rabu da d’ana ba. Wallahi ba zan rabu dashi ba.” Ta fad’a tana mai mayar da Abul kan k’irjinta tana k’ank’ameshi. Taxi suka tara Laila tace ya kaisu Aminu Teaching Hospital. Suna shiga da kud’in hannunta ta sayi kati suka bi layin ganin Likitan yara. Ko da layi ya iso kansu tare da Mas’ud suka shiga wanda Sabrin ke hannunsa yana mata wasa.  Samun guri tayi ta zauna tana gaishe da Likitan wanda tun shigowanta bai d’ago ya kalleta ba yana rubutu a wata takarda. Sai da ya gama sannan ya d’ago idanunsa ya sauk’esu cikin nata. “Waye ba lafiya?” Likitan ya tambaya yana mai kallo tsakanin Abul da Sabrin. “Likita yarona ne bashi da lafiya, yau kwana goma rabona dashi sai zuwa nayi na samu yana zazza6i, ya rame, muryarshi ta dashe sannan yana gudawa.” Ta bashi amsa. “Juyoshi mu ganshi.” Ya umurceta yana mai saka na’urar dake gwada numfashi da bugun zuciya a kunnensa (stethoscope). Da haka ya manna abun a k’irjin Abul yana canja guri har sau uku. “Kika ce muryarshi ta dashe, shin mura yayi har hakan ya faru?” “Wallahi Likita bani da masaniya, amma kuma da alama ba mura yayi ba.” Gyad’a kai yayi sannan yayi d’an rubuce-rubuce a jikin katinsu kana ya k’ara d’ago kai yace, “Zan so inji yanda muryar tashi ta zama. Kisa yayi magana.” Ya k’ara umurtanta yana mai kallonta cikin nitsuwa. “Abul kayi magana.” Ta fad’a tana mai d’aga ha6arshi sama. “Kace Mama ko ka kira Sabrin Likita yaji muryarka, kaji d’ana?” Girgiza kai yayi ya mayar da kanshi k’irjinta. Laila ta k’ara d’ago fuskarshi tana masa magiyar yayi magana, bud’e baki yayi cikin dashewar da muryar tasa tayi yace, “Abba!” Tsayawa Laila tayi cak kamar jinin jikinta ya daina aiki, hawaye ne masu zafi suka sauk’o k’uncinta sannan ta fashe da kuka tana rungume Abul a jikinta. Likitan da yaji abunda ya Abul d’in ya fad’a ya gyara zamanshi cikin d’aurewar kai yana mamakin meya sakata kuka. “Yi hak’uri Hajiya, don Allah ki bar kukan nan.” Likitan ya fad’a cikin sauri. “Kalti ki daina kuka don Allah, yanzu Idan Abul ya ga kina yi shima zai fara.” Cewar Mas’ud wanda shima hawayen ne cike a idanunshi taff. Da kyar suka rarrashi Laila ta dawo tana goge fuskarta da kuma hancinta da mayafinta. “Ban san meya sakaki kuka don yaronki ya kira sunan mahaifinshi ba. Amma…”     Likitan bai kai ga k’arisa magananshi ba Mas’ud yace, “Babanshi ya rasu ko wata hud’u bai cika ba.” “Oh I see. Allah ya jik’anshi Hajiya. Sannu fa.” Yace da ita cikin tausayawa.  Gyad’a kai tayi ta amsa tana share fuskarta. A nan yasa ta d’aura Abul a kan sikelin gwada nauyi sannan ya k’ara mata wasu tambayoyi kana ya mik’a musu katin yana cewa, “Ga magunguna da zaku saya, sannan za’a masa k’arin ruwa dalilin rashinsa a jikinsa. Ku bawa Nurse katinku zata nuna muku in da zaku kwanta.”  Godiya Laila ta masa sannan suka fito wajen ofis d’in tana tunanin yanda zata d’auko kud’i a gidansu, domin na hannunta ko magani ba zai saya ba balle kud’in gado. “Mas’ud bana son na koma gida a yanzu ba tare da na nemawa Abul lafiya ba, kuma gashi babu kud’i a hannuna. Ya zamu yi?” Ta tambayeshi cikin d’aurewar kai. “Ina da kud’i har naira hamsin da nake tarawa, zan iya zuwa gida na d’auko, Ina ganin zai ishemu biyan kud’in magani.” Kallonshi tayi cike da k’aunarshi tace, “Allah ya biyaka da aljanna Mas’ud. Amma nima ina da kud’i wanda abokan Baba dana Babanshi suke bani Idan sun zo ta’aziyya.”  Da haka ta masa kwantance inda ta 6oye ya fita bayan ya tabbatar an kwantar da Abul a gadon da aka basu.  Mas’ud kai tsaye ya shige cikin gidansu yayi hanyar d’akin Laila. Sai dai bai kai ga isa ba ya ji an jawo kwalar rigarsa yayi baya-baya kamar zai fad’i amma ya tsaya.  Juyawan da zai yi ya ga fuskar yayansu Madu wacce tayi jaja zir, yana rik’e da kwalar Mas’ud yana huci ya fara magana. “Ina Laila?” Sosai Mas’ud ya tsorita yana zare ido amma kuma yak’i magana. Fitowan Ummii daga d’akinta yasa Madu ya sassauto da shak’eshi da yayi yaci gaba da tambayarshi in da Laila take. “Kai Madu me haka? Kasheshi zaka yi ne? Sakar masa wuya maza-maza.” Ummii ta fad’a tana mai jawo Mas’ud gefenta. “Ko da wasa bana son irin wannan gangancin. Kai Mas’ud Ina Laila?” Ta dawo da hankalinta kanshi, sosai yaga 6acin rai a fuskarta, a nan ya tabbatar abunda suka aikata ya iso gida.   Sai dai ko da wasa bazai fad’i in da Laila take ba domin yasan ba k’aramin aikin Madu bane yaje asibitin ya d’aukota ba tare da an yiwa Abul magani ba. Shi Idan ranshi ya 6aci baya aiki da tunaninsa. “Ummii nima ban san in da take ba, tun da muka fita ta tari Taxi tace in koma gida tana zuwa. Na d’auka ta dawo ne shiyasa zan je d’akinta in duba.” “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.” Shine kawai abunda Ummii ke nanatawa tana ayyanawa a ranta cewa Laila ta shiga duniya ne tare da ‘yayanta. Madu kuma fita yayi waje cikin sauri don bai yi tsammanin abun zai kai haka ba, kasuwa ya nufa domin sanar da Babansu abunda yake faruwa.   Bayan gudun su Laila da minti talatin Madu ya iso k’ofar gidan Umma domin d’aukarsu. Sai dai tashin hankalin da ya samu ‘yan unguwar a ciki yasa ranshi ya 6aci sosai da abunda Laila ta yi. Cikin k’unar rai ya tafi bayan Umma ta cikashi da k’arya da gaskiya akan abunda Laila ta mata duk akan Abul.  Dawowanshi gida ya samu basa nan, shine ya samu Ummii yake fad’a mata abunda ya faru. Ya fito zai tafi kasuwa domin ya sanar da Baba sai ga Mas’ud ya fad’o cikin gidan. Wannan kenan. Ummii shigewa tayi d’akinta tana dafe da kanta. Ganin duk sun watse yasa Mas’ud ya wuce d’akin Laila cikin sand’a, ya d’auki duk abunda yake buk’ata ya fita daga gidan. Sai da ya sayi magungunan sannan ya shiga asibitin zuwa gurinsu Laila. Ganinshi d’auke da akwati yasa Laila ta tsaya kallonshi cikin mamaki. “Mas’ud ba kwana fa zamu yi ba, Idan ruwan ya k’are sun ce zamu iya komawa gida yaci gaba da shan maganinshi.” Tace dashi tana kallo yana ajiye jakar makarantarshi wacce take a cike tam. “Komawa gida na nufin rabaki da Abul, yanzu haka a gida an san me muka yi.” Ya bata amsa fuskarshi a kwaye. “Kalti ki zo mu gudu wani gari, ni zan nemi sana’a in dinga ciyar daku har Allah yasa su girma a hannunki kamar yanda kike so. Don Allah Kar kice a’a.”

Mum Fateey👌

Back to top button