Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 30 Book 2 Complete Novel

 

Juyawa tayi ta fice da sauri tana goge hawaye, Ilham dataga duk abunda yafaru tayi wani tsallen farinciki, amma da tuna irin tonon sililin da Jalal yayi mata dazu se taji jikinta yayi sanyi ta juya da sauri ta koma gida.

Jalal bashida zabi da ya wuce ya bar gurin shima kamar wanda kwai ya fashewa a ciki yakoma part dinsa, zuciyarsa kaman an kunna masa wuta saboda bacin rai, side bed dinsa ya kalla yaga Alqur’anin nan da kuma teddyn Jalila a gurin, a hankali yace

“do she really mean what she said, zata barni gaba daya, bani ba ita? Jalila why? karkimin haka mana, nasan ba’a kyauta miki ba, Amma kar laifin Mummy ya shafeni”

 ya zauna a gefen gadon sa ya rintse ido, ya dinga tuno moments dinsu tare, da fitar da sukayi dazu, ji yayi kansa yana juyawa zuciyarsa ta masa nauyi, ya kunna sigari yafara sha, ya sha takai kara biyar amma beji yadda yakeso ba seda ya dakko merlot red wine ya sha ya fita daga hayyacinsa sannan ya yada kwalbar a gurin shima ya zube. 

Ita kuwa Jalila seda ta samu guri a cikin flowers tayi kukanta ta gode Allah sannan ta nufi palourn gidan, tunda ta shiga ita dai taji Abba yana bayani yayinda Yaya mairo keta haya gaga, sam Jalila bata gane me suke fada danji take kaman zata fadi ta wucesu ta shige daki ba tareda ta kula kowa ba, tana zuwa ta haye gado ta ja blanket ta cigaba da kuka da kuma tunani, shikenan yanzu kuma kallon mazinaciya mahaifiyar Jalal take mata? Gaskiya tsakanin ta da Ilham se Allah yasaka mata, amma ba komai zata rama ne, zatayi wa Ilham daurin da bata isa ta kwance ba”

Jawwad ya farka daga baccin dayake cike da farinciki ya tashi yayi salla, sannan ya nufi cikin gida dan ganin Maama dakuma ‘yan kannensa dan yasan zuwa yanzu sun dawo daga school. Yana fitowa manu direba ya shigo harabar gidan da mota, ya jira manu yayi parking Nana ta fito daga motar kallo daya zakayi mata kasan a gajiye take, se jefa kafa take kawai tana ganin Yaya Jawwad ta yalwata murmushinta tareda fadin “Oyoyo mutan Bauchi, Ashe kun dawo?” 

“Mun dawo Nana, ya school din? Naganki ke kadai ina Jalila?” 

“Yaya Jawwad kasan Jalila manyan kwarine, yau bataje school ba, amma ancemin angan ta dazu ta shiga zasuyi test” 

“Shikenan mukarasa ciki, yau Akwai Albishir masu dadin gaske, muje in gaida Maama tukuna” suka jero tare zuwa cikin gida. 

Abba yace “Hajiya mairo ban yanke wannan hukuncin dan cin mutuncin ki kona zuriyarki ba, sedai dan hakan shine masalaha  ga yarona, idan baki saniba yaka mata kikara sa ido da bincike akan yaranki, Amma dana san haka abun yake, da tunda fari ban yadda da batun hada Auren nan ba, nasamawa Jawwad wata yarinyar itama Naja, taje Allah ya hadata da rabonta dan binciken danayi akanta gaskiya bazan iya bari Jawwad ya aureta ba”

Yaya mairo tace “dama dai can ka shirya cin mutuncina nida yarinya ta, amma inda arziki da mutuci ita daudar gora ai a ciki ake shanyeta, koma me take aikatawa silar Auren ai sekaga ta shiryu” 

“Hajiya Mairo, da abunda ze yuwu ne da na hakura anyi auren nan amma baze yuwu ba, kuyi hakuri, sannan Naja ta koma gidan mahaifinta ta zauna” 

Maama da tun dazu batayi magana ba tace

“Dan girman Allah kayi hakuri mun yadda ya auresu su biyu ma bakomai, amma idan akayi haka kaman amci mutuncin gidanmune” 

Abba yace 

“Ni ban Janye batun Auren nan dan cin mutuncin wani ba, amma da abunda ze yuwu ne dana hakura anyi, zanje in samu mahaifinta muyi maganar, dan ba dake ma yakamata muyi wannan zancen ba” 

Naja kam se rusa uban kuka takeyi 

“Dan Allah ku kyale masa dansu, sekace shi kadaine namiji, kokuma mijin gold ne? Banda kaddara me zatayi da wani Jawwad mutum sam be waye ba waishi Ustaz, dalla kidena kuka kiyi rayuwar ki kamar kowa, ki manta dashi” 

Sa’adah ce ke wannan maganar cikin fitsara da rashin kunya, Abba ya mike yana kokarin bar musu palourn su Jawwad suka shigo jin hayaniya yasa

Jawwad yace “Abba lafiya kuwa?” 

“Rufe mana baki kasurgumin munafiki daga kai har ubannaka da waccan makirar jarababbiyar, kun shiga kunfita kafasa Auren yarinyata dan ku kunya tamu a duniya to ta Allah ba taku ba, Matsiyatan banza dana wofi hadda wai tabar gidan nan dadinta tanada gidan uba ba’a titi take kwana ba” 

Yaya mairoce ta wangale makogaro taketa zazzaga rashin mutunci san ranta, ta kalli Naja tace

“Jeki kwasomin kayanki mu tafi, Nina gayamiki sekin samu wanda ya fishi, Azzalumai kawai” 

Maama ke kokarin kwantarwa da Yaya mairo hankali ta hanyar cewa

“Yaya dan girman Allah kiyi hakuri, zan shawo kan matsalar nan, dan Allah” 

Naja tace “ba wani shawo kan matsala, ni bana son karya irin wadda kika saba yi, an kaimin kudi kin lallaba kun hada kai ze auri wata, kuma ana kokarin yimin sharri wallahi Allah ya isa ban yafe ba aikin banza kawai” 

A harzuke Jawwad yace 

“Wallahi kika kuma zagarmin uwa sena wanka miki mari, baza’a Aureki dinba, waze Auri mace irinki ace itace uwar yaransa, Kika kuma zagarmin iyaye sena bata miki rai” 

Aikuwa Yaya mairo tayi kansa ta hanyar cewa

“Rufemin baki mara mutunci, har kanada bakin magana, iyayennaka ba kananan mutane bane, masu baki biyu, matsiyacin ubannaka dan Allah ya bashi Arziki ze wulakanta munida yarana” 

A fusace Nana tace “A’a kinga Yaya mairo dakata, ubanmu fa ba sa’anki baneba, Maama ce ‘yar uwakki dan haka kuje kiyi keda ita, da kike kiran ubanmu matsiyaci ya gama muku komai, dawainiyar ku ba wadda baya dauka yayi muku rana, da tsiyar tasa da kike fada ya muku rana ya maganta muku abubuwa dayawa, meye ba’ ayi muku a gidan nan, wani abunma ku sata sann……… 

“Ke Nana rufemin baki, Yaya mairon Sa’ar kice? Maama ta katse ta, 

Jawwad juyawa yayi ya fice, dan a rayuwarsa baya son tashin hankali sam, 

Nana tace “Allah sarki Jalila baiwar Allah, dukda abubuwan dakike mata Maama nasan Jalila bazata taba kallon tsabar idonki takira ki da makaryaciya ba, yau sega wanda kikeso din suna zagin ki, dama Allah ai ba Azzalumin sarki bane, musamman Naja tazo gidan nan danta kori Jalila, ga reshe ya juye da mujiya ai, bata kori Jalila ba, bata auri Jawwad ba kuma ita an koreta” 

Nana tai wucewarta zuwa daki ta barsu a tsaye cirko2 suna cigaba da masifa. 

Nana na shiga dakin ta tarar da Jalila ta kima bargo akanta tanata bacci duk hayaniyar nan baccinta take, Nana ta tatttaro kayan Naja ta fito mata dasu palour ta ajiye, 

Tace “ga kayanki nan, daga nan bama bukatar ki a dakinmu” 

Ta juya takoma daki tasa key, ta barsu da Maama a gurin. 

Jawwad sam ransa ba dadi, bangare daya yana cikin farinciki, bangare daya kuma ransa a bace yake ya tafi dakin Jalal domin suyi hira, yagaya masa halinda ake ciki, Amma abun haushin yana zuwa ya tarar da gogan yayi mankas baccin sa kawai yakeyi, dan dafe kai Jawwad yai ya zauna ya tattare kayan shaye2n gefe daya, ya zauna a gefen gadon Jalal, yana kallonsa garin da dan sanyi sanyi ga fanka ga A. C Amma Jalal gaban goshinsa se zufa yake, Jawwad ya dan girgiza kai, tareda fadin

“Allah ya shirye ka dan uwa” sannan yasa hannu ya daddaki pillow da Jalal yake kai, a hankali Jalal ya bude ido ya saukesu akan Jawwad ya mayar ya lumshe idonsa, Jawwad yace 

“Jalal ka tashi kai salla” dan karamin tsaki Jalal yayi yace “nika kyaleni please” 

“haba Jalal bakayi salla ba, ka daure ka tashi mana” 

Juyawa Jawwad baya yayi ya rungume pillow se ya tuna maganar Jalila  

“Inkaana Ibada, kana Addu’a Rage wasu Abubuwan” 

Sekuma ya danyi juyi ya mike da kyar yaje yai wanka da Alwala yazo ya gabatar da sallar Azahar da la’asar, fuskar nan tasa murtuk kaman be taba dariya ba. 

Jawwad ya dinga masa hira yana bashi labarin abubuwan da suka faru a Bauchi, da dramar da aka gama yi a gidansu yanzu, Amma se ya lura sam hankalin Jalal baya kansa yayi zurfafa a tunani ne, lokaci zuwa lokaci ya kanyi tsaki. 

Jawwad yace “Jalal wai me yake damunka ne? Ina ta magana hankalin ka baya kaina, se faman tsaki kake, menene?” 

Ajiyar zuciya Jalal yayi sannnan yace “Bakomai don’t mind me” 

“ban yadda bakomai ba, ka gayamin please” 

“Am serious bakomai, kawai yanayin ne bayamun dadi” 

“to Allah ya sawwake, Amma Jalal kwana biyu ina ta murna ka dena zuwa club, shaye shayen ma kaman ka dena amma nazo na tarar kasha giya, haba Jalal why” 

Dan shiru Jalal yayi dan yanajin muddin baze rabu da wannan damuwar ba akwai yuwuwar yakoma ruwa tsundum, dan maganganun Jalila sunyi matukar tasiri a zuciyarsa, a fili yace

 “Am sorry Jawwad, ina bakin kokarina, kasan wani lokacin halinda nake shiga idan ban shaba, Amma Insha Allah very soon zan dena gaba daya” 

“to Allah ya amince” 

Daga nan Jawwad ya lallaba Jalal ya jashi suka fita zaga gari da nufin ya debe masa kewa. 

Seda aka gama wannan tarzomar aka gama su Yaya mairo suka tafi sannan Allah ya nufi Jalila da tashi daga baccin da take, ta kalli Nana tace “Nana meyasa baki tasheni ba? Gaskiya na sha bacci tunda na dawo na kwanta se yanzu na tashi” 

Nana tace “Mhmm ke kinta bacci bakisan drama da’akayi ba yau” 

“Tame fa?” Jalila ta tambayi Nana irin bata san meyafaru ba, 

Nana ta labarta mata komai, Jalila ta jinjina kai ita babban abunda ya bata mata rai be wuce yadda Nana ta gaya mata irin cin mutuncin da suka dingayi wa Abba ba, hatta zagin da sukayi wa Maama yabata mamaki, bata taba zaton zasu yiwa Maama hakaba saboda yadda take kyautata musu. 

Nana ta gayawa Jalila cewar tunda Abba ya shige daki da wannan abun yafaru ko Abinci be ciba, ba karamin tausayin Abba ne yakamata ba takara tabattar da Yaya mairo daga ita har Yaranta basuda tarbiyya dan haka Jalila salla kawai tayi ta shiga kitchen ta dora Abincin dare saboda Abba ya samu yaci. 

Sunkuma waya da Ahmad ya gaya mata yauma tayi hakuri abubuwa ne sukayi masa yawa shiyasa baze samu zuwa ba, Jalila ta karbi uzurinsa saboda yanayin aikin nasa. 

Jalila ta shirya Abinci me rai da lafiya, bayan sallar magariba ta kaiwa Abba nasa har daki, Amma da mamakin ta ta same shi cikin fara’a, yace “‘yar gidan Abba Girki akayi min haka ne?” 

“Eh Abba, gashi nan kaci ka koshi sannan inzo inji Albishir din da zakayi min”

Yai murmushi yace “Ai Albishir din bana kine ke kadai ba, ki kira womin sauran’ yan uwanki muci Abincin tare” 

“to shikenan Abba yadda kace haka za’ayi” 

Haka kuwa akayi taje ta kira Nana, ta wuce dakin Jawwad dan kiransa, Amma Jawwad yanata rubuce2 shikuma Jalal yanata babbakawa cikinsa hayaki. 

Dauke kanta tayi kaman bata ganshi ba tace “Mutanen Bauchi, Yaya Jawwad ko kanemeni ko?” 

Haka nan jin muryar ta yasa gaban Jalal faduwa har yake kokarin boye sigarin hannunsa

Jawwad yace “nina isa, dazu na shiga cikin gidan amma na tarar ana fitina shiyasa na tafi” 

“to shikenan, Abba yace in kiraka duk tare zamuci Abinci saboda Akwai Albishir daze mana” 

Jawwad yace “Allah Auta, wane Albishir zeyi mana?” 

“Ahh kajika ai kai yakamata in tambaya, tunda tare kuka dawo” 

“to shikenan gani nan zuwa” Jalila ta mike ta fice, Sam Jalal beji dadin wannan dauke kan da tayi masa ba, Jawwad yace “Jalal zo muje” 

“A’a jeka seka dawo” Jalal ya bashi amsa, Jawwad yace 

“Wallahi baka isaba, tashi muje, Abban bakonka ne? Yakamata muje tare” 

Jawwad ya takurawa Jalal, badan yaso ba ya bishi, suna shiga palourn Abba Idon Jalal akan Jalila yafara sauka, tana sanye da riga da skirt na Atamfa, kaman ajikinta aka dinkasu cif dasu, tayi parking din gashin ta, ta kashe dauri ba kwalliya a fuskar ta amma tayi kyau matuka, bata kalli inda Jalal yake ba suka cigaba dayiwa Abba surutu ita da Nana, Su Jalal suka Zauna, Jalal suka gaisa da Abba, Abba yace Jalila zubawa su Jalal Abincin mana”

Ba tace komai ba ta fara zuzzuba musu Abinci, dakin yayi shiru suna Cin Abinci se surutun Nana dake tashi, gaba daya Jalila takasa sakewa taci Abinci saboda tsabar kallon da Jalal yake mata, bakowa ze gane ita yake kallo ba amma ita tasan ita yake kallo, shi kansa ba iya cin Abincin yake ba jujjuya cokali kawai yakeyi, Jalila tace “Abba ka gayamana Albishir din naka, nifa duk na kagu inji” 

Abba yayi murmushi ya kalli Jawwad yace

 “Jawwad gaya musu mana” sunkuyar da kai Jawwad yayi yana murmushi, Abba na yayi murmushi sannan yace “Na canza maganar Auren Naja da Jawwad, zuwa Jawwad da Hanan, nan da wata hudu Insha Allah” 

Wata irin Ajiyar zuciya Jalila tayi, Nana tace “dama ni zuciya ta tabani, Masha Allah, Allah yasanya Alkhairi ya nuna mana lokacin” 

Jalila tace

 “Abba ni na rasa abunda zance gaba daya, mungode Allah daya sa ka gano abunda nake ta maka nuni, Abba Allah yasaka da alkhairi wannan aini akayiwa ga Yayana Kuma ‘yar uwa ta, Amma shine Yaya Jawwad baka gaya mana ba, itama Hanan bata gayamin ba” 

Abba yace “Itama Hanan din bata sani ba ai, daddynta be gaya mata ba, sannan babban Albishir na biyu shine; Kakar Hanan itace yayar mahaifiyar mu, Inna Asma” au”

Da Sauri Jalila ta waiwaya gurin Jalal dan in bata manta ba sunyi zancen da shi, amma kawai ta basar tace “Abba tunda naje tabani Labari nayu tunanin hakan, Amma nayi shiru ban fada ba saboda bani da tabbas, godiya ta tabatta ga Allah” 

Jalal yai karfin halin cewa “Abba kaga yadda Allah ke juya lamarin sa, a baya kayi ta bulayin neman danginka, ashe suna tare da kai baka sani ba, ina tayaku farinciki Abba, Allah yakara hada kan iyalanka” 

“Ameen Ya Allah ABDUL JALAL, Amma naji dadin wannan Addu’ar taka, kuma zance ka gaskiya ne, na dade ina bulayin nemansu amma ba zato ba tsammani na samesu ta silar ‘yar Auta ta” 

Sukayi murmushi gaaba daya. Abba ya dora da cewa ” munyi magana da daddynka, Jalal ranar Asabar Insha Allah zasu kawowa Mahmud kudin Aure, suma tareda na Jawwad za’ a hada, gaskiya zanso a hada da naka, yadda kuka taso tare ga aiki ya samu kamata yayi a hada da kai gaskiya” 

Dan guntun murmushi Jalal yayi wanda iyakarsa lebensa yace 

 “Abba Jawwad dai yayi, nikam se yadda Allah yayi, babu uba nagari da ze bawa ďan shaye2 auren ‘yarsa, koda za’ a bani saboda dukiya ta ne” 

Gaba daya tausayinsa seda yakama su

Abba yace

 “karka damu kaji Jalal, babu wanda ze hanaka ‘ya, kai mutumin kirki ne, wanda ya zauna da kai ne ze gane hakan, Insha Allah komai ze wuce, ka cigaba da Addu’a sannan ka dinga kokarin ka dena shaye2, babu abunda ze hana abaka’ ya Aure” jinjina kai Jalal yayi yace 

“to shikenan nagode Abba” 

Nana ta dan zumbura baki tace 

“Abba wai meyasa baza’a hada dana Jalila bane?” 

Abba yace “Saboda ban gaji da ganinta ba” 

“Auni ka gaji da ganina kenan?” Nana tai maganar kaman zatayi kuka. 

Abba yace “A’a Munyi maganar da Babanta, yace; Abari ta kammala karatu tukuna saboda yanayin Aikin Ahmad din, nan da shekara daya ne zata kammala in Allah yasa zamu gani itama zan Aurar da ita ga Ahmad” 

Gaba daya kunya ta kama Jalila ta mike tace

 “nikam seda safenku Abba” ta mike da sauri ta bar palourn, gaba daya Jalal ji yayi kaman Abba ya masa yayyafin wuta a kirjinsa, shima ya mike yai musu seda safe. 

Haka suka watse daga palourn Abba, babu wanda yabi takan Maama balle susan halin da take ciki, ta kule a daki ta rasa abunda yake mata dadi, bata taba zaton yaran yaya mairo zasu iya zaginta ba, gashi mijinta da yaranta ma sundena shiga harkar ta suna fushi da ita. 

Koda Jalal ya shiga gida, part din Daddy ya tafi, yana zuwa kaman wani karamin yaro ya tarar da daddy yana aiki akan system, Mummy na gefe suna hira, yana zuwa ba tareda ya cewa kowa komai ba ya zauna kusa da daddy ya kwanta akan cinyar sa yayi shiru kaman mara lafiya. 

Daddy yace “Jalal lafiya kuwa?” 

Jalal yace “daddy Anmin screening da interview, an turani Lagos zanyi wata uku acan, Jawwad ze tafi nasa gurin Aikin next week Monday ” 

Daddy yace “Eyya shiyasa ka damu haka? Kayi hakuri kaji yaron kirki, yasa haka shine mafi Alkhairi a gareku” 

Mummy tace “nifa gaskiya bana son wannan aikin da zeyi, meya nema ya rasa da ze tafi wani yawo daban” 

Mikewa Jalal yayi tareda yin tsaki yabar dakin, ya koma Part dinsa, koda ya koma ya sauya kaya ya kwanta domin yayi bacci amma abu ya ga gara, juyi kawai yakeyi idonsa ya bushe, ta shi yayi zaune ya kurawa teddy dinta da carbin da ta bashi ido, abubuwa da dama na masa yawo a kwakwalwa, Espicially lokutan da sukeyi tare, yana kallon teddy ya tuna lokacin da take rike da teddy ga sweet abakinta tana dariya, yana tuna tsiwarta, kwarin gwiwa, tausayinta, nasiha da murmushinta, ya tuno maganganun Abba dazu wai za’a Aurar da ita ga wani AHMAD!!! gaba daya yaji kansa yana juyawa, yazama dole ya nisanta kansa da duk wani abu da zazesa ya dinga tunata, Baze manta Alkhairan ta ba, tunani yakasa barinsa dan haka ya mike ya fice daga gidan gaba daya. 

Jalila ma juyi ta dingayi tana tunani da tausayin Jalal, tabbas Jalal abun tausayi ne, yana bukatar me jansa a jiki musamman yanzu da Jawwad zeyi nesa dashi, tana fargabar yakoma shaye2 kamar da, Amma a yanzu bazata iyayi masa komai ba, dan gudun kuma fadawa mummunan zargin da mahaifiyarsa ke mata. A takaice se gefin Asuba bacci ya dauke ta 

Jalal be dawo gida ba se Asuba, yaje club ya kwana yana shan giya, seda yayi mankas, da Asubar ma bata sake shi gaba daya ba ya dawo gida cike da maye. 

Yau tun bayan da Jalila ta dawo daga school, tayi waya da Ahmad ya gaya mata yau zezo, dan haka se shiri take domin tarbarsa. 

Jalal tunda giyar ta sake shi, yai wanka ya shirya kayansa daze bukata a Akwati, yaje cikin gida yai sallama da Daddy, yaita saka masa Albarka tareda fatan Nasara, tunda Ilham taji batun yasamu Aiki ta hanyar Jalila, kuma zeyi wannan tafiyar akan Aikin, hankalin ta ya tashi, wai se yayi wata uku acan, to in baya nan tayaya zata cigaba da gudanar da aikinta akansa?. 

Karfe biyar yagama shirinsa, saboda Jawwad ne ze kai shi Airport, ya sa hannu ya dauki teddyn Jalila da Alqur’anin nan da kuma carbin data bashi, ya nufi gidan su Jawwad, saboda so yake ya nesanta kanshi da dukkan wani abu daya shafe ta. 

Amma abunda yayi tozali dashi bayan ya shiga gidanne yasa yaji tamkar jijiyoyinsa sun dena harba jini yadda yakamata. 

Autar Ummi wato Jalila ya gani tayi kwalliya cikin wani dankareren leshi, tayi kyau matuka suna hira da Ahmad, kai da gani suna cikin shaukin soyayya, Jalal yaji wani Abu ya tsarga masa tun daga kansa zuwa tafin kafarsa, kirjinsa yai masa nauyi matuka A hankali yafara jan kafarsa dayake ji tamkar ba nasa ba ya nufi inda suke. 

Idonsa Akan Jalila har ya karasa inda suke, Jalila ce tafara daga kai tana kallon sa, gani tayi kamar ya danyi rama, yana zuwa Ahmad ya miko masa hannu da nufin su gaisa, kawai Jalal ya daga masa hannu, ya zubawa Jalila idanunsa da sukayi jawurr wanda yasa hantar cikinta kadawa, 

Ya ajiye mata Alqur’anin, a gabanta da teddyn, ya juya ya nufi hanyar fita

Shiru Jalila tayi ta kalli kayan daya ajiye mata sannan tabi bayansa da kallo har ya fice daga gate, din shiru tayi ta tafi tunani, Ahmad yace

“my queen, meya farune?”

Da sauri ta dawo hayyacinta tace “bakomai fa”

“Amma waye wanan?” ya tambayeta yana me kureta da ido, ta dan sauke numfashi tace “Yaya na ne”

“Yayanki queen, ba Jawwad ne kawai Yayanki ba?”

“Abokin Yaya Jawwad ne, dan haka Yayana ne kawai”

“Amma babu wani abu a tsakanin ku kuwa?”

“Meyasa kake min wannan tambayar? Ko baka yadda dani bane?”

“Ahh haba waneni ince ban yadda da gimbiyata ba, ina so ne in tabattar da abunda ke tsakaninku, dan da idonsa yana shaye2”

Ba karamin haushi maganar Ahmad ta bata ba, kenan shima yanayi, in ba yanayi ba, ba abunda idon Jalal yayi dayake nuna yana shaye2, dan haka tace

“baya shan komai, kawai bashi da son magana ne, baya kula mutane”

Kyaleta Ahmad yayi yaga alamar bata son zancen suka cigaba da hira, Jawwad ne ya fito ze wuce su Jalila ya tsaya suka kuma gaisawa da Ahmad dayake dazu sun gaisa, Jawwad yace “to sirikina zan iya ce maka se anjima, ni zan tafi kai Jalal airport ne”

Da sauri Jalila tace “Ina zashi?”

Jawwad yayi murmushi yace “Aiki mana, an tura shi Lagos, se lokacin biki inaga ze dawo, bari inje karyai ta jirana, kin san baya son jira, se anjimanku” Sukayi sallama da Ahmad ya fita.

Ahmad ya maida idonsa kan Jalila yace “Gimbiya naso a haďa bikin nan hada namu, na kagu in mallakeki”

Murmushi kawai tayi amma hankalinta baya kansa, tanata zancen zuci ne, dayaga haka yace “queen naga kaman Akwai abunda yake damunki, bari in tafi semunyi waya”

Ta mike ta rakashi har bakin gate sannan ta dawo ta zauna akan kujerun tana nazari

“At least yakamata ace sunyi sallama da Jalal, tayi masa nasiha, Amma bata tunanin zata iya kuma rabarsa ba saboda mahaifiyarsa.

Jawwad ya ga sam fuskar Jalal a daure take, babu alamar walwala ko fara’a, Jawwad yai masa magana yafi a kirga, amma ko daya be bashi amsa ba, dan haka ya kyleshi suka cigaba da tafiya a haka kaman kurame. 

Gajiya Jalila tayi da zaman tunanin ta mike ta tafi cikin gida, Nana tana zaune a palour suna waya da Mahmud,

“Nana waike dan Allah ba kya gajiya da wannan wayar ne? Kuyita surutu tun ana fadar gaskiya se an koma fadan karya” 

Nana taki kula ta seda ta gama wayarta sannnan tace 

“waike Baby an gaya miki kowa irin kine me tsarin tsiya, ke yadda ba kya son yawan waya kowa ma hakane, ai a rana inji muryar Mahmud sau hamsin bazan gajiba, musamman mu da muke distance relationship, ai Ahmad din nan ma ban wani yadda kina sonsa ba” 

“Inasonshi sosai, amma hakan bashi ke nufin a dinga uzzuramin da surutu ba” 

“Hajiya Jalila, kyaji da shi dai” 

Hanan ca ta kira Jalila a waya, ta daga tasa a kunnenta 

“hello Baby, ‘yar uwata rabin jikina ashe Family dinmu daya Baby? Narasa inda zan sa kaina dan farinciki, dazu Abba yake gayamin kuma wai an kawo kudin Aurena da Haidar, Baby na rasa me zanyi dan farinciki”

Murmushi Jalila tayi tace “na riga ki ji ai, kiyi Azumi ki godewa Allah” 

“queen na rasa inda zan saka raina dan farinciki, daddy yace zasuzo karbar kudin Nana, narasa yadda zanyi dan murna” 

“haka Al’amarin ubangiji yake Hanan, yana juya komai yadda ya so” 

“Hakane Queen, amma naji haushi da baza’a hada da nakiba, ni ina Jalal ne ma?” 

“yaje interview din nan ai, an turashi lagos zeyi wata uku”

“Allah sarki bawan Allah, wallahi Jalila bana kaunar Aurenki da Abokin Yaya Yusuf din nan, in duniya da gaskiya Jalal ya kamata ki Aura” 

Wani dogon tsaki Jalila tayi ta kashe wayarta, dan bata son Hanan ta bata mata rai. 

Jalila ta mike har zata bar palourn taga Maama tazo ta wuce kitchen, gaba daya Jalila bata jin dadin yadda kowa ya fita harkar Maama, dukda abubuwan da Maaman tayi mata, Akwai lokutan da ta kyautata mata, dan haka taga be dace ta mata hukunci da laifin da take mata ba, dan haka tabita kitchen din, Maama na kokarin kunna gas Jalila tayi maza taje ta karbi lighter tace “Maama kawo in kunna miki, me zaki dafa?” 

“barmin Abina zanyi” 

“A’a Maama, tunda ba abunda nake ki barshi in dora miki” 

Jalila ta karbi lighter ta kunna gas, dan jimm Maama tayi tana Kallon Jalila, yadda Jalilan ke Acting kaman Maama bata taba yi mata wani abu na bacin rai ba. 

Jawwad suka isa airport yayiwa Jalal Sallama amma ya amsa masa a ciki, sam baya walwala, yasan halin Jalal baya son takura, tunda be niyyar gaya masa meke damunsa ba, ya ja Akwatinsa yayi gaba yabar Jawwad. 

Haka Jawwad ya taho yanata tunanin me akayiwa Jalal yake wannan bacin ran haka? 

Bayan Jalila ta gana yiwa Maama girki, ta koma daki, ta dauki Alqur’anin nan tana ta jujjuyawa, Kamshin turaren Jalal yakeyi, hakama dan teddyn ta, tasa hannu ta ta dinga duba Alqur’anin nan page by page, amma sam bata ga komai a ciki ba, kodai Jalal dama yana son raina mata hankali ne kawai? 

Shiru tayi ta tuna yadda taga yana yinsa bayan ya gansu tareda Ahmad, Fuskar nan tasa a daure babu alamun sassauci, tayi shiru ta cigaba da zancen zuci, ;yanzu ze tafi lagos bashi da kowa a can, babu me kula dashi, Allah kadai yasan meze aikata, 

“kinfi so in cigaba da shaye2 na ko? Ke Garkuwa ce a gareni” ire iren wannan maganganun nasa da Maganganun Antynsa da take gaya mata tabata amanar Jalal ne yasa take tunanin Anya hukuncin data yanke yayi dai2 kuwa? 

To Amma nikuma mutuncina fa? ” gaba daya ta rasa me yakamata tayi? Yanzu tana gaya Hanan, tasan Hanan zata canza mata magana tafara kawo wani abu daban, dan haka tabar Abun a ranta ta cigaba da Yiwa Jalal Addu’a. 

‘yan kwanakin nan sam Abba ya dena shiga harkar Maama, har gara Jawwad ma yana zuwa gaisheta, Nana kuwa seda Jalila tasata a gaba ta nuna mata be dace ba abunda take yiwa Maama, wannan abunda yafaru tsakanin ta da Abba ne da kuma’ yan uwan ta, sannan ta samu Nana ma take shiga sabgar Maaman, Abba ya gayawa Maama ranar Lahadi zasuyi baki, za’a kawo kudin Auren Nana, abakin su Nana taji batun haduwa da ‘yan uwan Abba a Bauchi, ba tayi mamaki sosai ba jin ance su Hanan’ yan uwansu Abba ne ba, sakamakon matukar kamannin dake tsakanin Jalila da Hanan, sedai taji haushin rashin sanar da ita da Abba beba. 

Tun ranar Juma’a suke shirye2 domin bakin daza’ayi, Jalila ce jagorar girke2 da shirin yadda za’a karbi baki. 

Gefe guda Jawwad yana ta shirye2 Ranar litinin shima ze tafi gurin nasa Aikin, ba karamin kulawa Hanan take bashi ba, da soyayya da kuma shagwabarta, yanayin yadda take nuna yarinta  a wasu bangaren ba karamin birge shi yake ba. 

Kamar yadda aka saka ranar lahadi daddyn Hanan yazo Kano aka karbi kudin Auren Nana, itama lokaci dayane dana Jawwad dakuma Abdallah Yayan Hanan, ranar har mutan bauchi seda sukazo garin kano karbar kudin, da kuma kara taya juna murnar haduwar su a matsayin ‘yan uwa. Jalila taji dadi da akazo hadda Hanan da Mummynta, Maama seda ta sha jinin jikinta ta raina kanta ganin manyan mutanen da sukazo gidan, Abun Arziki ya hadu dana Arziki, dangin Su Jawwad dana Su Jalal, Ranar anci ansha, kai ka dauka bikin Aure akeyi rana ce me matukar tarihi da wannan Ahali bazasu manta ba. Jalila sam bata samu kebewa da Hanan ba, saboda Hanan na manne da Jawwad, sam bata jin kunyar kowa take nuna masa soyayya. 

Mummyn Hanan se mita take tace “Ni gaskiya naso a hada abun nan hada na Jalila, in aurar da ‘ya’ ya uku, amma in shirya da kyau, amma bakomai anata se nafi shiri ko Jalila?” 

Ita dai Jalila sedai tayi murmushi ta sunkuyar da kai. 

Duk yadda Maama take jin kanta take kuma jin haushin Auren Hanan da Jawwad boyewa tayi, Saboda sam bata da makusa, ‘yar dangi ce, kuma’ yar uwar dan tace, tana da kyau dai2 gwargwado kuma tana da Ilimi, yanayin kyau da gayun mahaifiyar Hanan ya isa ya nuna maka ‘yar ta ma hakan take. Koda ta hasko Naja seta ga abun se A hankali, kuma tun abun nan da sukayi mata ta tabattar da Ko Auren akayi Naja zata iya wulakanta ta. 

Da ire iren wannan tunanin yasa ta ajiye duk wani bacin rai aka shiga hada2. Tareda tsara yadda suke ganin bikin ze kasance, Ba laifi Mummyn Hanan ta saki jiki Maama, Sunyi hira sosai kaman sun saba, sannan suka tattauna akan yadda harkar bikin yaran nasu ze kasance. Se la’asar Suka tafi, mutanen Bauchi suka tafi, Su Hanan ma a ranar suka juya kaduna saboda Su Hanan suna jarrabawa, su kuwa danginsu Mahmud, suna kawowa Mahmud kudin Aure sukaci Abinci suka juya Borno. 

Wasa2 sosai tunanin Jalila ya hana Jalal sukuni, da yafara aiki in ya tuna da ita gaba daya se yaji duniyar tayi masa zafi, yarasa inda zesa kansa, meyasa Mummy tayi masa haka? Idan yaji abun ya dameshi se ya tafi club yaje ya cika cikinsabda giya, dukda wasu lokutan yana bawa aikin da yaje yi mahimmanci, Sam Jalal bashi da sakewa da mutane, dan haka be saba da kowa ba, sedai yana girmama shugabanninsa na gurin aiki, girmamasun da yake besa sunga alamar ze bari su taka shi ba, inda yake burgesu yana maida hankali akan aikinsa sosai. 

Duk lokacin da yaje Club mata da suke damun sa ne ga kuma shigar tsirara da suke yasa shi dakatar da kansa ga zuwa Club, idan yaji ba yadda zeyi se yayi shaye2 se yayi abunsa a dakinsa na hotel da yake ciki. 

Amma duk da haka yarasa dalilin da yasa mata ke binsa, sedai in baze fito ba. 

Hannah ce zaune akan kujera tana kwalliya, Sa’ada na kwance akan gado tana danna waya, dan dakatawa da kwalliyar Hannah tayi ta dan kurawa madubi ido, sekuma can ta daki kan mirror tace “Impossible baze yuwu ba wallahi” 

Sa’adah ta waigo ta Kalle ta tace “lafiya kuwa?” 

“Akwai matsala Sa’ada” Hannah ta bata amsa

“matsalar me fa?” 

“Sa’ada ki kalleni ki kara, kimin kallon tsaf tun daga sama har kasa, ki kalli yadda nake gara kan maza, in taka wanda naso in wanke wanda naso, amma a hakan har rububina wasu suke, in sauke Ajina in cewa Jalal idan ya Aureni zan dena bariki, Amma ya watsa min kasa a ido”

Wani dogon tsaki Sa’ada tayi tareda fadin “Nina dauka ma wani mutumin kirkin ne, A she akan wannan mashayin ne, ni ba wannaan ya dameni ba a yanzu” 

Hannah tace “Mutumin kirki ne mana, ki kalleshi kallon tsaf Sa’ada Namiji ne irin wanda duk wata mace zatayi burin Aure, shaye2 ne kawai matsalar sa, da farko da nakewa su Jeje aiki, nna zata zan samo kansa ta sauki ya yadda dani, Amma duk wata dabara da kisisina ta matan bariki nayi amma yaki amincewa dani”

“to kibi wani mana, ko shine kawai namiji?” 

“bazaki gane ba Sa’ada, bakiga irin kirar da Allah yayi masa bane, kuma da kike ganinsa a haka, dukiya ce dashi kaman abun banza” 

“Ya akayi kika sani, nasan dai babansa yana da kudi, amma shikam ko aikinyi ba shida shi” Sa’ada tayi maganar tana yatsina fuska

“Hmm to wallahi har ki mutu in ba wani ikon Allah ba, kaf danginku daku da abunda kuka mallaka, bazaku kaishi dukiya ba, yana da kudi da mahaifinsa yasa ake juya masa, Jeje yaso ganin bayan dukiyar nan shida mai gidansa amma abun be yuwu ba suka kare a prison”

Sa’ada ta tashi zaune tace “to ke yanzu meye abunyi, ni ban taba sani ba, kin san ya taba kusa tonamin Asiri ina zuwa club agaban babarmu” 

Dariya Hannah tayi tace “Abune mawuyaci ya tona miki Asiri, bar ganinsa a haka, yasan abunda yakeyi, naje har gidansu na dana masa tarko, amma ga dukkan alamu ya tsallake shi, wannan karon zan masa tarkon da zan rike shi a wuya, be isa ya kuma subuce min ba” 

“Yakamata kam, Amma ni nan tunanin yadda zan huce abunda abokinsa Jawwad yayiwa Naja nake, kiri2 yafasa Auren ta, yarinyar nan duk ta shiga damuwa” 

“Allah sarki, to wai ya’akayi aka fasa Auren? Waye yaje yai mata gulma a gurin baban nasa?” 

“ya za’ayi in sani, Amma da nafi kyautata zaton wannan munafukar kanwar tasa ce” 

“Wace kanwar tasa ya’akayi tasan abunda Naja take? Ko dai itama tana ta bawa?” 

“Ke bari, wata yarinyace yadda kika san boka haka take, ni dai ban san tana wani biye biye ba, Amma kina zaune in taso seta nemo waye ubanki koda ke baki sani ba, wai ita Jalila makirace ta bala’i, idan tace bata san abu seta ga bayansa, tasa Jawwad ya fasa auren Naja se kawarta” 

Jin an ambaci Jalila yasa Hannah zare ido tace

“Kan bala’i ai nasan wannan yarinyar, tabdijan ni zan gaya miki makira ce, ke wallahi keda kike bariki tafi ki iya rashin mutunci, ke zata iya yuwu wa ita tasa aka hana, bari in gayamiki yarinyar nan tafiki bala’i, dan koni tasa min ido akan Jalal, ita take rusa min komai “

Cikin mamaki Sa’ada ta kalli Hannah tace” wai kin santa ne? “

” Nikuwa na santa, kuma nasan illar ta, munyi Arranging da Jeje mun gama komai, zamu sace Jalal ranar birthday din sa, idonta na kanmu, muka bugar da shi da giya ta shammace mu tasa aka dauke shi daga gurin, ke ina jin kishin cewa ita tasa aka kama Oga KB” 

Zaro ido Sa’ada tayi cike da mamaki tace “Ke haba dai? Shikuwa oga KB yana me,duk iya kuri da gadarar rashin mutuncin nasa, yarinya ce fa karama” 

Hannah tace “hmm ke dai bari, mace kenan, kaidin wata yafi wata, irinsu kuma sa’a ce dasu a rayuwa, kibi a sannu kawai” 

“Tabdijan amma babu kama, dan bakiga cin mutuncin da muke mata ba mu da babarmu, kin san uwarta tsohuwar arniya ce, bakiga cin mutuncin da muke mata ba” 

Hannah tace “Yawwa kuma ga cin mutuncin da tayi muku nan, kuma ta gama daku ba” 

“Sosai makuwa ta gama damu” 

“shiyasa wannan karon shirina ita da Jalal ne, dan bana ta wannan Ilham din dan wannan ba mace bace, wannan tafi hatsari, baze tsallake wannan tarkon ba a yanzu, na duba mashayar da yake zuwa ba adadi amma ance ya dena zuwa, duk da haka zan nemoshi” 

Yauma duk da tarin farinciki da Jalila ta tsinci kanta a ciki yau, amma bacci ya kauracewa idanuwanta, jikinta na bata Jalal yakoma shan giya, da kyar ta samu bacci ya dauke ta, amma mafarkin Jalal a cikin wani yanayi na shaye2, yasata farkawa, gabanta na wata irin mummunar faduwa, wayarta ta dakko ta duba karfe biyu da rabi na dare, ga shi ita ba lambar Jalal ce da ita ba, tarasa mema zatayi gallery dinta ta shiga tana dubawa, tsofaffin ajiyayyun hotunan ta take dubawa, hotunan da sukayi da Jalal tun wani zuwa da Hanan sukayi, haka taita kallon hotunan, a haka har ta kawo kan hotunan birthday dinsa, cin karo tayi da wani hoto da’akayi harda Hannah a ciki, take gaban Jalila ya fadi, dan sam ta manta da Hannah, kuma barin Hanna ba tareda daukar wani mataji ba tamkar kashe maciji ne ba’a sare kansa ba a rayuwar Jalal. 

A hankali ta ajiye wayar, ta sakko daga kan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tada salla. 

Ranar litinin Jawwad shima yayi nasa shirin tsaf domin tafiya Gurin nasa aikin dake birnin tarayya, Abba yayi masa Nasiha sosai tareda sa masa Albarka, haka ma bangaren Maama, tayi masa Addu’a da sa Albarka, dukda marin da Maama tayi masa akan Naja, hakan besa ya nuna mata har yanzu yana fushi ba, Bangaren Jalila kuwa har kuka tayi, saboda zatayi kewar Yayan nata sosai 

Abba yace “Jalila kina kuka dan zeyi tafiya, kuda kwanan nan zeyi Aure gaba daya zasu bar gidan, su barki seke kadai” 

Kara fashewa da Kuka Jalila tayi, Nana tace “Abba ka gani ko? Wannan yar taka ta fiye shagwaba wallahi” 

Jawwad yace “haba babyn Abba, sekace ba jaruma ba, zan dawo ai kidena kuka” 

Sukayi ta tsokanarta ita kuwa dagaske take kukanta. 

Haka sukayi sallama da Jawwad shima yakama hanyar tafiyar sa. 

Jalal yana waya da daddyn sa sosai, sannan suna waya ds Jawwad, suna shirye2 yadda biki ze kasance a tsakanin su. 

Abban su Jawwad yana kasuwanci ne a tsakanin Kano da lagos, dan haka in yaje suka haduwa da Jalal. 

Jalila Nason sanin halin da Jalal yake ciki, amma babu wata hanya da zata san hakan, dan haka taketa kokarin boye damuwarta. 

Maama Allah ya temaketa Abba ya sakko daga fushin dayake da ita, sannan tunda abun nan ya faru Su Yaya mairo ko a waya basu kara neman Maama ba, abun ya dameta sosai dan haka ta shirya da kanta taje gidan su. 

Tunda tayi sallama suka amsa suka shareta suka ki kulata, ita tayiwa kanta gurin zama, ta gaida Yaya mairo amma taki kulata, seda ta bata ‘yan kayan data saba kaimusu, shine Yaya mairo ta dan saki rai suka gaisa, Naja ta gani a lullube tana bacci, Maama tace “Yaya, Naja ba lafiya ne?” 

Kafin Yaya mairo ta amsa Naja ta fara magana cikin maye “Ni… Ni.. Ba… Wallahi baaaaani da…. Da lafiya, Shiyasa naiwa kaina caaajiii, baaaa danki yaki Aure na baaaaaa, wallahi…. 

Cikin tsawa Yaya mairo tace” yimin shiru dan ubanki, ciwon mara take, shine ta sha magani fiye da ka’ida”

Gaba daya jikin Maama yayi sanyi saboda babu tantama Naja maye takeyi. Shiru tayi takasa cewa komai, Naja ta cigaba da surutai, can kuma ta kwalla uwar kar, sega jini na gudu a tsakar dakin daga karkashin Naja. 

Se bayan la’asar su Jalila suka gama lectures ta gaji matuka, haka kurum tun suna lectures takejin gabanta yana faduwa, da kyar ta tsaya aka gama lectures ta fito, danma manu direba ne yaje dakko ta daga school, abunda yabata mamaki be wuce ganin motar Hannah a gabansu ba, tana tsala gudun wuce sa’a, kuma da alama layinsu zata shiga, Jalila tasa Manu direba yayi parking a farkon layinsu, ta sauka ta shiga layin da kafarta, aikuwa tana zuwa taga Hannah tayi parking din motarta ta shiga gidansu Jalal, Jalila batayi shawarar komai ba ko tunani tabi bayan Hannah zuwa cikin gidan. 

A hankali Jalila ta cigaba da bin bayan Hannah, ba tareda ita Hannah ta sani ba, Hannah ta bude kofar babban palourn ta shiga, Jalila ta biyo bayanta amma ta tsaya a corridor yadda ba wanda ze ganta, Hannah ba karamin mamakin kyai da tsaruwar gidansu Jalal tayi ba, an kashe masa dukiya matuka, tun daga harabar gidan zaka gane mzauna gidan na cikin ni’imar ubangiji ta dukiya da yake bada ita ga wanda yaso a lokacin da yaga dama. 

Koda ta shiga palourn ba kowa, seda ta tsaya ta karewa tangamemen palourn kallo, sannan ta jinjina kai tareda yin ajiyar zuciya, ta fara sallama, Mummy dake kitchen ta amsa tareda fitowa da jug a hannunta, suka gaisa da Hannah, Mummy na mata kallon rashin sani,

Mummy tace “bari in kira miki Ilham din, dan a zatonta kawarta ce” Hannah tace “A’a ba gurinta nazo ba, Mummy dan Allah Jalal fa?” 

Mamakine yakama Mummy amma ta dake tace “Ai kusan watansa guda baya gari, yana lagos” 

Hannah tace “Ai dole ya lallaba ya gudu lagos mana, Ina fatan mahaifinsa yana nan” 

Mummy tace “lafiya kuwa?” 

“Ina fa lafiya, ina son ganin mahaifinsa tunda shi baya nan” 

“me mahaifinsa ze miki ne? Ki gayamin menene?” hakan yayi daidai da fitowar Ilham da alama fita zatayi, kawai taga Hannah, take gabanta yayi mummunar faduwa, kirjinta yafara dukan goma2, ta wani hade rai, ta karaso palourn cikin kasaita kaman gidan father dinta, tazo ta tsaya tareda kama kugu tanawa Hannah kallon da wacce kika zo?. 

Kallo daya Hannah tayi mata ta dauke kai, tareda yin murmushi a ranta ta kalli Mummy tace “Gara in gayawa mahaifin Sa abunda ake ciki, na gaya masa wancan karon be dau mataki ba, shi namjine ke ba lallai ki iya daukar abunda zan fada ba” 

“ki Fadamin bakomai ni mahaifiyarsa ce ai” 

Hannah ta gyara zama, sannan ta kalli Mummy tace “wancan karon da nazo nayiwa mahaifinsa magana, nace yayi yadda zeyi a hadu mu rufawa juna asiri amma ba’ace min komai ba, nikuma asirina yana daf da tonuwa, Ina dauke da cikin Jalal na watanni uku a yanzu” 

Da sauri Jalila tasa hannu ta toshe bakinta tana zare ido, gaba daya taji kafafuwanta suna rawa. 

Hannah ta cigaba da cewa “muna haduwa da Jalal a hotels, kokuma idan yake night clubs, yasaba yimin ciki yace in zubar, wannan karon likita yace  rayuwata na shirin fadawa hatsari muddin na zubar da cikin nan, ga iyayena na kokarin ganewa, soyayyar Jalal ce tasa na bashi kaina, wallahi koya aureni ko nayi kararsa ya kula dani da dansa”

Hannah ta karasa maganar cikin kukan kisisina, kasa magana Ilham tayi saboda mamaki. 

Hatta Mummy kasa motsawa tayi daga inda take, se ido da take bin Hanna dashi

Hakan yayi dai2 da fitowar Daddy sakamakon jin hayaniya sama2

“lafiya me yake faruwa haka?” 

Kafin su bashi amsa, ya sauke idonsa akan Hannah, be manta ta ba, ya kalleta yace “yarinya lafiya kuwa? 

Cikeda karfin hali Hannah ta korawa daddy bayani kamar yadda tayi wa Mummy 

“Karya kikeyi, Wallahi Jalal baya neman mata, mata basa gaban shi, yana shaye2 amma be yadda da neman mata ba, Jalal ba mazinaci bane ba” Ilham tayi maganar ilahirin jikinta yana rawa

“Masha Allah, dukkan yabo ya tabatta ga Allah, kin fadi magana kuma kin karyata kanki Ilham, tunda kinsan Jalal ba mazinaci bane, ta yaya kika san ina bashi kaina?” 

Jalila ce ke maganar cike da kwarin gwiwa, gaba daya suka juyo inda Jalila take, kanta tsaye ta tako har gaban Ilham ta Kalle ta ido cikin ido tace 

“Nagode Allah, kinyiwa Jalal kyakyawar sheda, yadda baya neman mata nima ba’a haifi namijin da Jalila zata bashi kanta a titi ba, Wallahi Ilham kinji kunya, tun wuri ki canza hali, tun kafin ki kaini bango in miki abunda se kin kasa shiga mutane” 

Ta juya ta kalli Hannah tace

“Ni na manta da ke a doron kasa, in ban manta ba haduwar mu ta karshe yafi shekara, katsam jiya kika fadomin a rai, da irin abubuwan da kike aikatawa, haka nan naji kasa sakewa, zuciya ta tanata bani wani abu zw faru, katsam akan hanyata naga motarki na kokarin shigowa layinmu, shiyasa na biyoki dan duk inda kikaje babu Alkhairi Hannah “

Gaba daya kan Hannah ya kwance bata taba tunanin zata hadu da Jalila a wannan lokacin da take shirin hurawa Jalal wutar da babu me iya kashe masa ba. 

Jalila ta kalli daddy tace

“Wallahi daddy karya take yiwa Jalal, ba wani abu dayake tsakanin ta dashi, sema ita da take kokarin cutar da shi”

With full confidence Hannah tace

“Karya kike inyiwa Jalal karya, ina dauke da cikinsa ne, kuma wallahi wannan karon bazan zubar ba, kamar yadda yasaba sani ina zubarwa” 

Cikin tashin hankali daddy yace “Jalal din nawa ne yai miki ciki? Kiji tsoron Allah, bana tunanin hakan ze faru, wancan karon akan wannan maganar yayi fushi har ya nemi ya bar kasar nan, narasa waye me gaskiya a tsakaninku” 

Jalila tace “Daddy ka kyale ta taje ta kai duk inda zata kai, Kai ka haifi Jalal kasan abunda ze iya da wanda baze iya ba, kasan baya shakkar kowa, idan ya aikata baze ji tsoron gaya maka ba, Daddy karya takeyi wallahi, I dan ba haka ba, taje ta shigar da karar” 

Sosai Jalila take kokarin kare Jalal, abunda yabawa daddy mamaki, dan agabansa ya sha ganin irin artabun da sukeyi da Jalal, amma wani tabbaci take da shi akan Jalal haka, kuma y’a kayi tasan Hannah? 

Ilham kam harar Jalila kawai takeyi ji take tamkar taje ta maketa a gurin, sekace Jalal din ubanta ne, ita so take tayi amfani da wannan damar, a tirsasawa Jalal yin Aure, amma Jalila nata karewa. 

Mummy tace “Waike meye haka? Ban hanaki shiga duk wani shirgi daya shafi dana ba, banda munafunci da son jin kwakwaf hada biyo ta kizo kiji me ze faru, kina……. 

“Rufe min baki khadija, Kinsan meyasa take kokarin kareshi, meye da dannaki da kike wani kumfar bakin adena shiga harkarsa”? 

Daddy ya kalli Jalila yace “Jalila a ina kika san wannan yarinyar?” 

Jalila ta kalli Hannah tace “daddy nasanta a gurin birthday din Jalal ne, Kuma sannan” 

Sekuma tayi shiru, “Sannan kuma me?” 

Daddy ya tambayeta, Jalila tace “bakomai daddy, amma makaryaciya ce” 

Hannah ta fashe da kuka tace “Shikenan tunda ba ‘yar kuce niba kun zabi zubewar mutuncina, wallahi mutuncina baze zube ni kadai ba, ku saurari sammaci, wallahi karar Jalal zanyi” 

“Karki fasa sekin dawo, Amma idan har karya kike abunda ya faru da iyayen gidanki ze faru dake, idan har kin iya makirci za’ a nuna miki ranar dukiya, ki fice kibar gidan nan da kafafuwanki kafin insa akama min ke” 

Hannah ta tsorata da gadar zaren da Jalila tayiwa su Jeje suka rufta, dan haka ba kunya ta juya zata fice, daddy yace “Amma ta tafi ba’a gano bakin zaren ba” 

Jalila tace “daddy ka rabu da ita, ko ta kai kara, kota bari ya dawo ayi maganar amma babu dalilin da zesa ta dinga maka karya tana bata maka rai akan danka” 

Ta juya ta kalli Mummy tace “Mummy Allah ya huci zuciyarki, ban biyo Hannah dan shiga cikin lamarin iyalinki ba, sedan sanin hatsarin Hannah ga rayuwar Jalal, Amma Insha Allah kome ze faru bazan kuma shiga lamarin ba, in dai ya shafi gidan nan” 

Ta juya zata fice, daddy yace “Jalila ita wannan yarinyar wacece? Sannan meye hatsarin ta ga Jalal? Menen alakarsu?” 

Jalila tace “Daddy ba a bakina yakamata kaji ba, amma dai nasan babu wata alaka ta kusa dake tsakaninsu, na tafi se an jima” ta juya ta fice zuciyarta cike da bacin rai. 

Maama ta dubi Yaya mairo tace “Yaya wannan jinin kuwa na lafiya ne?” 

“Al’adace haka yake zuwar mata” 

“haba Yaya, kalli guda gudan dayake zuba kice min Al’adace, yakama tunda nazo da mota mu kaita Asibiti” 

“ba wani Asibiti da zamu kaita” yaya mairo ta bata amsa tana kokarin temakawa Naja ta mike zaune, amma tana tabata taga bata motsi, numfashinta da kyar yake fita, ga jini se cigaba da fita yake daga jikin Naja, ba shiri Yaya mairo ta mike, Maama ta temaka mata suka gyara Naja, suka sata a mota se Asibiti, 

Sunkai awa biyu suna jira, Yaya mairo takira Naja a waya, tazo suka hadu a Asibiti, likita ya fito ya tambayesu alakarsu da Naja, sukayi masa bayani, yace su bishi office dinsa, haka suka bishi sukaje suka zazzauna suka zubawa likita ido, ya danyi gyaran murya sannan ya kallesu yace

“To kun san duk abunda yasamu bawa mu kaddarine daga Allah, kuma Allah yana jarrabar bayinsa ta ko ina, kuma dukkan musulmi se yayu Imani da kaddara sannan Imaninsa ze cika, Hakikanin gaskiya mara lafiyar ku tana dauke da ciki karami, kuma tayi Amfani da miyagun kwayoyi wanda hakan yayi sanadiyar zubewar cikin jikinta da kuma lalacewar mahaifarta”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji un” shine abunda suka dinga nanatawa, gaba daya Maama taji jikinta yafara rawa, Yaya mairo ta dora hannu aka tafara ihu, likita yace “Haba baiwar Allah kamar ba yanzu nagama yi miki nasiha ba, ba wannan bama, yarinyar nan ta zubar da jini da yawa, Akwai bukatar a sama ta jini, kuma a bincike da mukayi tana da cutar Hepatitis B, (ciwon Hanta), dan haka ku gaggauta nemo Jini, a duba a ‘yan uwa wanda jininsu yayi dai2 se a samata” 

Haka suka fiti office din nan suna salallami, jiki a sanyaye Yaya mairo tace “bari a kira yayanta a waya, Zainab kira Jawwad suzo a duba in jininsu zeyi a samata” 

Da sauri Maama tace “Wane Jawwad din? Jawwad yana Abuja ya samu Aiki ai, nikam Yaya mairo ga wannan” tasa hannu a Aljihu ta dakko kudi tabata sannan tace “ga wannan ku sai magani, zan koma gida magariba tayi, se na dawo dubiya, Amma yakamata kunemo wanda yake da alhakin cikin nan, yazo ya dauki nauyin ta, se anjimanku” 

Maama ta juya ta fito daga ward din, tana ta tunani tareda mamaki, da kyar Maama ta kai kanta gida, saboda tunani da Mamaki, da tuno marin da tayiwa Jawwad saboda Naja se taji gaba daya jikinta yayi sanyi. 

Haka ta koma gida jiki a sanyaye, tunda ta koma take tunani, Nana ta lura da Yadda Maama jikinta yake a sanyaye dan haka taje ta sameta a daki take tambayar ta “Maama wai me yake damunki ne? Tukuna ma ina kikaje?” 

Dan shiruu Maama tayi, sannan tace “Nana naso inyi ganganci da rayuwar dana” 

“gangancin menene?” 

Nan ta kwashe komai ta gayawa Nana, Nana tayi murmushi tace 

“Allah sarki Rayuwa, Maama kinga wannan abun to izina ne a gareki, Allah yasa kar alhakin marainiyar Allah ya kamaku, kunsaka Jalila kuka ta zubda hawaye ba a dadi, ku zageta ku mata cin mutunci, ku mata gori amma se gashi su sunyi Abun kunyar da ‘yar arnan ba tayi ba, Maama lokaci yayi da yakamata ki gane su waye ke kaunar ki, Yaya mairo’ yar uwakki ce amma abun hannun ki takeso, ki duba irin biyayya da Jalila tayi miki tsawon lokaci, duk fitsararta da kuke fada, ke dai bata taba yimiki ba, se dai Yaya mairo, Maama a ci zarafin iyayen mutum dacin abun ya wuce yadda kike tunani, kun cutar da ita gaskiya, fatan Allah ya yafe muku, yanzu seki gane, Ummi da take ba musulma ba da farko, tayiwa ‘yarta tarbiyar da wanda aka haifa a musulinci bata yiwa’ yatta ba, Allah yasa hakan ya zama izina a gareku”

Maama kasa cewa komai tayi, se jujjuya maganganun Nana da takeyi, tabbas Maganganun Nana gaskiya ne, 

Nana tace “Maama bari inje daki inada Assignment da zanyi” 

Gyada mata kai kawai Maama tayi, Nana kuma ta fice, koda taje dakinsu Jalila tana kwance idonta a rufe, kaman me bacci, amma ba baccin take ba, tunanin abubuwa da dama ne ke zagayawa a cikin kwakwalwarta. 

Daddy yakasa samun sukunibda abunda ya faru, gaba daya hankalin sa yaki daidaituwa, yarasa maganar wa zebi, ta Jalila kokuma ta Wannan yarinyar, Amma yakasa bawa kansa amsar wani tabacci Jalila take da shi akan Jalal, Mummy ta lura da yadda daddy ya dami kansa dan haka tace

“Ni dai a ganina wannan yarinyar da gaske take, ba’a shedar mutum, shiyasa nake son mu aurar da Jalal, shekarunsa ya kai ya ajiye iyali, ita kuma wannan yarinyar da tazo da wannan maganar, indai da gaske take, a lallabata abata kudi tayi hakuri” 

“bana tunanin Jalal ze aikata haka, kuma tunda Jalila ta bada sheda akan Jalal, abun dubawa ne, amma yazama dole in bincika, lamarin yaron nan na ma rasa yazanyi, Allah ya shiryamana zuri’a” 

Dadd yasa hannu ya dau wayarsa ya kira Jalal a waya, seda ta kusa katsewa sannan Jalal ya daga, koda ya daga ma beyi magana ba, shiru ya gudana na wani dan lokaci sannan daddy yace “Jalal kana jina?” 

“Ina jinka daddy” 

“ya kake ya aikin kuma?” 

“lafiya kalau Alhamdilillah daddy, kana Nigeria kenan?” 

“Eh ina nan, nakira ka ne, ina so muyi magana” 

“ina jinka” 

“Wace ce Hannah?” 

Gaba daya Jalal ya manta da wata Hannah a rayuwarsa, Amma ya maze yace “Ban Santa ba” 

“Jalal ban sanka da karya ba, wannan yarinyar itace kwanaki tazo min da waccan maganar, wannan karon tazo min da maganar wai tana dauke da ciki kuma nakane, Amma Jalila ta karyata ta, sannan tacemin Yarinyar tana da matukar hatsari ga rayuwarka, kamin bayani “

Ba abunda ya farantawa Jalal rai sama da jin batun Jalila ta kare shi, duk da furucin da tayi na bashi ba ita, daddy yace” Jalal ya naji kayi shiru? “

“to me zance maka daddy? Duk hukuncin daka ga dauka akaina dai2 ne, inma ka yadda gaske ne ko karya, dan Allah ni ku kyaleni hankali na ya kwanta, ina jin dadin zamana a inda nake karku daga min hankali” 

“Amma Jalal meye hadinka da yarinyar nan har take bibiyar ka? Tana ikrarin zata kai kararka” 

“Daddy in dai har bana nan, a bayan idona yarinyar data tsaneni zata bada shedar kirki akaina me kake so ince maka, kana so inta rantsuwa ne seka yadda dani? Kasan ba haka nake ba, Idan bata kai karata ba ni zan dau mataki akanta” 

“Amma meye hatsarin yarinyar ga Rayuwar ka? Kamar yadda Jalila ta fada?” 

“ka tambaye ta mana, tunda a bakinta kaji” 

“Jalal yaushe zaka dawo?” 

“ba yanzu ba, se nan gaba, nifa zamana anan yafi min zaman gidan nan, da za’adinga takura min” 

“to shikenan tunda haka kace” 

Haka sukayi sallama ya kashe wayar. 

Mummy tace “wai nifa nakasa gane wannan maganar, ita Jalila wacece dinsa da za ta fadi abu ka yadda, ya akayi tasan abunda mu bamu sani ba akan danmu, haka akeyi?” 

Murmushi daddy yayi ya dan kashe mata ido  yace “haba deejat to meye a ciki? Kin samu me kulamiki da son, you have to thank her, har gida tazo dan kare shi” 

Kara kunna Mummy yayi, dan haka ta tashi fuuu ta bar masa dakin. 

Ilham tayi safa da marwa yafi sau Ashirin a dakinta, tana son ta tabbatar da Hannah dagaske take koda wasa, yanzu abun ya kuma kwabe mata, da ta manta da batun Hannah, amma yanzu yakin ya kuma zame mata biyu, ga Jalila ga Hannah, da tana tunanin tayi maganin Jalila, tunda tayi mata makirci a gurin Mummy, “Amma Jalila nan naci ne da ita bata da zuciya, shegiya se nayi maganin ta, sena kuma kunna mata wata wutar, to amma in dagaske Jalal yayiwa Hannah ciki fa? Da sauri tace” kai karyane, da Jalila yayiwa Hannah ciki da yanzu wani zancen ake ba wannan ba, karya takeyi”

Ilham ta fito daga dakinta har tana tuntube ta tafi daki Mummy, tana zuwa ta tarar Mummy ta cika tayi fam, fuskarta sam babu walwala, Ilham taje ta zauna a kusa da Mummy tace

“Mummy lafiya kuwa?” 

“ke rabu dani, ni zancen wannan yarinyar mana, gaba daya daga Jalal din har ubansa naga hankalin su ya karkata kan wannan yarinyar Jalila, ga itama wannan wadda tazo din da wannan maganar cikin” 

“mhmm wallahi Mummy in bakiyi wasa ba yarinyar nan se ta hana Jalal din ma shigowa gurinki, ta ne Santa shi dake, meye nata na sawa anema masa aiki a nesa? Kuma ga daddy yafara biyewa maganganun ta, wallahi Mummy da sannu zata janye miki shi gaba daya” 

Mummy ta numfasa tace “ni Ilham gaba daya kaina ya kwance akan lamarin Yaron nan, narasa yadda zanyi” 

“to Mummy kiyiwa daddy maganar, ayi mana Auren mana, saboda ayi maganin abun, tunda har ya fara bin mata” 

A fusace Mummy tace” Ke dan Allah ki rabu dani, kina gani ba irin kokarin da banyi ba, Amma abu ya ga gara, ni ki kyaleni nace ki bani lokaci, sena fara shawo kan matsalar, ni na miki alkawarin Auren nan, ki karamin lokaci in gama da wannan matsalar mana”

Ilham ba tace komai ba ta mike ta bar dakin, tana fita tayi kwafa tace “Wallahi zaki gane kuskuren ki Mummy, zanyi maganinki, sena Auri Jalal din na mallake shi, ke da shi sedai kallo” 

Back to top button