Hausa novels

Halysaah Page 175 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH 175…Mami na tsaye Bedroom dinta da Hajiya Shafa’atu wajen karfe tara na dare suna kallon Jay da yaki ce masu komai kansa a kasa duk da yana jin su, Hajiya Shafa’atu ta zauna gefen gado tana kallonsa a hankali tace “Jawwad” Ɗaga idanuwansa yayi yana kallonta, lokaci daya jikinta yayi sanyi ganin yanda ya koma, zaka ce yayi watanni ne bashi da lafiya tsabar yanda ya fita hayyacinsa ya dawo kamar ba shi ba, juyawa Mami tayi ta fita daga dakin jin hawaye sun fara taruwa idonta, tun bayan faruwan wannan abu Jawwad yayi bankwana da bacci da abinci, sallah ma don ya zame masa dole ne, Hajiya Shafa’atu tayi karfin halin cewa “Kayi hakuri ka daure ka je kaji Jawwad….” ita kanta hawayen take kokarin avoiding a moment din nan, Jay ya kasa cewa komai, tace “Ta shi mu je” Da kyar ya girgiza kai cike da karfin hali yace “Ban san me zan ce mata ba Mama, ko naje ban san me zan ce mata ba” Yana fadin haka sai ga hawaye idonsa, ya sunkuyar da kansa yana kokarin controlling kansa, Hajiya Shafa’atu was so emotional, ta kamo hannunsa tace “Tunda tana son ganinka ka tashi mu je, kaga bata dade da farfaɗowa ba, consider her condition Jawwad, muna lallabawa ne kar wani abu ya samu juna biyun da take dauke da, kayi hakuri ka daure, if you are not being strong ita ya kake son tayi?” Hajiya Shafa’atu na fadin juna biyun da Khaleesat ke dauke da shi Jay ya maza ya sauka daga kan gadon, haka nan ya bita yana tafiya a hankali yana jin kamar iska zai kadesa ya fadi, suka fita daga dakin, tun da aka dawo da shi masarauta sai yanxu ya fito daga dakin Maminsa, kansa na kasa har suka isa part din Ajay, lokaci daya yaji kansa na juya masa don duk wani waje da Ajay ya zauna ko kuma dai ya bar wani abun nasa to definitely sai kaji kamshin turarensa a wajen, parlon sai kamshin tsadadden turarensa yake, Jay ya zauna kan kujera a Main parlor yana jin wasu hawayen na taruwa idonsa ya rike kansa da suka masa nauyi, Hajiya Shafa’atu na kallonsa a hankali tace “She is inside the room Jawwad, ka tashi mu karasa can” After a while ya ɗaga kai da kyar yana kallonta cikin breaking voice yace “Wallahi Mama i don’t know what to say to her….” Kasa ci gaba yayi ya rufe fuskarsa with tears rolling down his cheek, he was really heartbroken, a wannan moment din ji yayi ina ma tare kawai aka harbesu a wajen da Ajay, he wish they left the world together, Yakumbo dake zaune can karshen parlon da carbinta a hannu sai goge hawayen dake zuba idonta take, a kwanaki biyun nan duk a wajen zaka sameta zaune sallah ne kawai ke tada ta, babu ci babu sha idonta duk sun kumbura tsabar kuka, Maryam da Khadijah dake parlon su ma hawayen suke gogewa, yawanci duk a parlon suke zama yanxu, Kilishi dake tsaye corridor duk tana kallon Jay ta karaso parlon tace “Kwantar mata da hankali kawai zaka yi Jawwad, that is what she needs right now, da bata da juna biyu ne sai ayi ta mata alluran bacci to calm her brain down ta dinga processing abun gradually har ta yi accepting reality din abinda ya faru, amma yanxu kam babu alamar zata yarda da duk abinda aka gaya mata, shi yasa ma ba a barin baƙi su shigo bangaren nan…” Jay dai bai dago kansa ba, shi kansa har yanxu ganin abun yake kamar a mafarki, he still can’t fathom the whole situation amma kuma a gabansa aka yi komai, he saw how Ajay gave up after struggling, bayan wasu sakwanni yayi karfin halin mikewa, Hajiya Shafa’atu ta fara tafiya zuwa second parlor, kansa a kasa ya bi bayanta walking slowly har suka tafi parlon Ajay, Jay yaki dago kansa cause he is trying so hard to control himself, gani yake kamar zai ji muryar Ajay a part din, Hajiya Shafa’atu ta bude kofar bedroom din sannan ta juya tana kallonsa, still not raising his head ya karasa bakin kofar dakin, Hadiyah dake zaune can karshen gado ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta sunkuyar da kanta a hankali, tun bai karasa ciki ba yake jin kukan Khaleesat tana ce ma Dr din da ke kokarin saka mata drip “Ni wallahi lafiyata qlau, kawai ni dai a kai ni wajen mijina, shi nake son gani, babu abinda yake damuna, don Allah ku taimakeni kawai a kai ni wajensa” yana jin haka yayi halting yana son juyawa cause he can’t stand it, amma tuni Khaleesat ta gansa ta sauka daga kan gadon da sauri ta nufesa da gudu, hakan yasa ya kasa juyawa kawai ya tsaya amma kansa a kasa, tana isa gabansa ta sakar masa kuka sosai tace “Don Allah Ya Jawwad ka gaya min inda yake, ai tare ku ka yi tafiyar, me yasa ka dawo babu shi? Where did you leave him pls?” Jay ya kasa ci gaba da tsayuwa cause his legs couldn’t carry him any longer, a hankali ya duka kan knees dinsa feeling so emotional, at this point he couldn’t hold it anymore, ya dafe kansa da ya dinga juya masa with tears running down his eyes, Khaleesat ta tsaya tana kallonsa babu ko kiftawa with fear written all over her face, bata san sanda ta kurma wani uban ihu ba da sai da gidan ya amsa, action din Jay ne ya fara dawowa da ita reality din da taki amsa tuntuni, his actions explains everything to her, ta zube gabansa cikin wani irin shock jikinta na rawa tace “Na shiga uku, don Allah ka gaya min me ya samesa?” Jin yaki cewa komai ta Cakumosa da karfi cikin birkicewa tana zare ido tace “Ka gaya min me ya sami mijina don Allah, tell me what happened to him, da gaske ne an kashe min shi? Dama da gaske ne?” Jay couldn’t raise his head yana jin ihunta har tsakiyar kansa, ta sake kurma wani uban ihun ta dora hannu a ka, su Hajiya Shafa’atu da Hajiya A’isha da Kilishi duk suna parlor sun yi tagumi babu wanda ya iya shiga cikin dakin, Aunty Farida dake jingine da bango a parlor ita kanta bata iya ta shiga dakin ba hawaye kawai ke sauka idonta tana nanata Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un a zuciyarta, Khaleesat bata fasa jijjiga Jay ba ko ina na jikinta na rawa tace “Don Allah ka rufa min asiri ka dawo min da mijina Housemate, kar ka ce min ya mutu, wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba, me yasa zai tafi ya bar ni bayan kwana biyu kawai yace min zai yi ya dawo, na shiga uku, don Allah ku taimake ni” Hadiyah tayi karfin halin sauka daga kan gado ta nufeta zata dagota, Khaleesat ta riko hannunta cikin kuka tace “Don Allah ki tayani tambayarsa me ya samu mijina, don Allah ki tambayesa” Shi dai Jay yaki daga kansa, hakan yasa kawai Khaleesat ta mike ta warce hannunta daga rikon da Hadiyah tayi mata da nufin zata fita daga dakin ba tare da ta ma san ina zata je ba, sai a sannan Jay ya daga kai a hankali yana kallonta, lokaci daya tayi saurin dafa stool dake kusa saboda wani sharp pain da taji a maranta ta durkusa kasa da kyar, Jay bai san sanda ya mike da sauri ba ganin jini na diga daga kafarta yayi saurin dagota, Hadiyah tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Sosai hankalinsa yayi mugun tashi, kan kace me sai ga jini kamar an bude pampo har shi da Hadiyah dake kusa da ita sai da jinin ya ɓata masu kafa, tuni likitan dake tsaye dakin all this while cike da tausayin Khaleesat tayi hanzarin karasawa kusa da su tana cewa “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, Hasbunallah….” Wannan ne yasa su Hajiya Shafa’atu suka yi saurin shigowa dakin gaba dayansu, su ma duk suka saki salati cikin rikicewa, Hajiya Shafa’atu ta fashe da kuka tana girgiza kai, shikenan ɗan cikin ma da suke lallabawa gashi tayi ɓarinsa….. Kukan bakin ciki sosai Hajja tayi bayan an kai mata mummunan labarin miscarriage din da Khaleesat tayi na cikin yan biyun dake jikinta, gashi bata da lafiya ko fita bata iya yi balle taje ganin halin da Khaleesat din ke ciki, ta dai ce kar su gaya ma Mai martaba a bar sa yaji da abinda yake ji tukun, Nenne ma taci kuka ta gode Allah, haka ma Umma dake tausayin halin da er ta take ciki, gashi tunda dangin mijinta na kanta su sai dai su zauna a dakin da aka saukesu ita da Nenne da Aunty Murja sai Mama Zubaida, Aunty Farida ce kawai ke shiga wajen Khaleesat frequently…. Damuwa da tashin hankalin da Jay ke ciki ya ninku a kan wanda yake ciki, gaba daya ya dawo kamar wanda ya fara samun issues da brain dinsa, miscarriage din da Khaleesat tayi ya kara destabilizing dinsa yana ganin shi ne ya ja hakan, just like that the twins are gone too, yayi da ya sanin amincewa da yayi har yaje wajenta tunda zuwansa ne ya ja har cikin ya zube, all this while taki yarda da cewar abu ya samu mijinta amma ganin hawayensa yasa ta gaskata abinda taki yarda for days shi ne har ta shiga shock din da ya ja mata miscarriage, Hajiya Shafa’atu da Mami duk sai da suka yi da sun sanin tilasta Jay yaje wajenta, kuma duk tunaninsu idan ta gansa zata sa ma kanta salama ta nutsu ashe ba haka bane, Har kusan asuba Mami na zaune gefen Khaleesat don ciwon mara mai tsanani take yi tun bayan fitar pregnancy tissues din, sai wajen karfe hudun asuba ta samu bacci ya dauketa, sannan Mami ma ta samu tayi shimfida nan kasan carpet ta kwanta, ita kanta Mamin karfin hali kawai take don zazzaɓi take ji sosai a jikinta, ko minti talatin Khaleesat bata yi ba da fara baccin ta farka a firgice, Mami na jin motsinta ta mike zaune, Khaleesat ta sauko kusa da ita tana kallonta cikin wani yanayi tace “Mami da gaske fa bai mutu ba, wallahi nayi mafarkinsa yanxu yace min zai dawo” Mami dai ta sauke ido tayi shiru bata ce komai ba, Cikin rawan murya Khaleesat tace “Mami ki ce wani abu don Allah, wallahi yace min zai dawo” Mami ta kasa kallonta, cike da karfin hali ta gyada mata kai kawai tace “Na sani Halysaah, amma mu yi ta addu’a kin Ji?” Khaleesat tace “Ina son in ga Ummata” Mami tace “To bari in kira maki ita yanxu” Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin, ko da tayi sallama dakin da su Umma suke daga Umma har Nenne idonsu biyu suna zaune kan darduma kusan yanda suke ganin rana haka suka ganin dare tun zuwan su, Nenne na ta sallah kan darduma, Mami ta karasa ciki tana kallon Umma dake rike da carbi tace “Maman Halysaah ki zo” Sosai gaban Umma ya fadi tana kallon Mami, ita kanta Nenne daburcewa tayi a sallahn da take, Mami taga tashin hankalin dake kwance fuskar Umma tace “Ki kwantar da hankalinki babu komai, Halysaah ce take tambayarki yanxu ta farka bacci” Umma tace “Toh” Daga haka ta mike ta bi bayan Mami suka fita daga dakin zuwa wajen Khaleesat….. Washegari Khaleesat na zaune ta jinginar da kanta da gado hannunta rike da carbin da Mami ta bata, ba komai yasa Mami ta bata carbin ba tace ta dinga ja sai don yayi distracting dinta ta dena maganganun da take kamar warce ke neman zaucewa, yanxun ma dai tana rike da carbin ne amma tayi nisa tunanin da take, Hadiyah da su Iklima da Shahuda suna can zaune far end of the room, sai Khadeejan Aunty dake zaune bakin kofa, Ummi kuma na daga gefen Khaleesat tana jan nata carbin a hannu, Hajiya Shafa’atu da Kilishi ma duk suna dakin zaune kan Carpet babu me cewa komai, aka murda kofar dakin, sai a sannan Khaleesat tayi firgit ta dawo duniyar tunanin da ta tafi ta sauke ƙafafuwanta daga kan gadon da sauri tana kallon kofar dakin jin exactly irin yanda Ajay yake bude kofa ne, don sau da yawa idan ya murda kofa sai yayi jim before gently pushing the door open, Ummi ta daga kai ta kalleta ganin wajen kofar take son tafiya da sauri, tuni Kilishi ta mike ta tareta zata maidata inda take zaune, Ummi ma ta tashi duk suka yi preventing dinta from going further, Khaleesat ta fashe da kuka tace “Wallahi nasan shi ne, don Allah ku bar ni in je….” Bata rufe baki ba Sophie ta karasa tura kofar dakin amma ta kasa shigowa ciki, Khaleesat ta dinga kallonta, kawai Safiyyah ta juya zata fita saboda hawayen da suka fara sauka idonta, da gudu Khaleesat ta bita ta rikota ta fashe da kuka sosai cikin rawan murya tace “Don Allah Sophie ki gaya min ko kun yi waya da shi, he is still not yet back” Safiyyah ta kasa cewa komai hawaye na zuba idonta, instead kawai ta rungumeta jikinta trying hard to control her self, Khaleesat ta dinga kuka kamar ranta zai fita tana cewa “Sophie nasan he is not dead, nasan zai dawo, and i will wait for him”

Back to top button