Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 24 Complete Novel

*ASM Bk2024*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

 

…………A kan kunnanta aka fara kiran farko na sallar Asuba ta yunk’ura ta saukko idanunta sun yi luhu luhu ta fita, Alwala ta d’auro tazo ta kabbara Nafila bayan ta gama tana kuka tana Addu’oi, lokacin da gari ya waye sosae ta fito don ta share gidan tayi wanke wanke kafin ta wuce islamiyya duk jinta take wani iri kaman wadda ta tashi daga ciwo jikinta sam ba k’arfi, d’akin gwaggo ta fara zuwa ta gaisheta amman ko kallon Arzik’i bata samu ba haka ta fito tana goge kwalla da gefen hannunta, tsintsiya ta d’aukko tana fara sharar gwaggon ta fito daga d’akinta fuskar ta a daure tamau da hannu tay mata alama ta aje tsintsiyar cikin muryar kuka tace “don Allah gwaggo ki yi hakuri ki bari in share” a fusace tace “to ban so ko gidanki ne, kuma daga yau ban amince ki k’ara ta6a komae da sunan aiki ba ki bar man kayana zan yi na riga na yaye ki wanda kikai kuma nagode” daga haka ta juya ta koma d’aki, kallon Amadu dake tsaye bakin kopar d’aki Fatun tay da fuskar kuka ya d’an girgiza mata kai alamar ta barin da sauri ta aje tsintsiyar ta shige d’aki sai gashi ya biyo ta ya zauna a gefen gado ya fara rarrashinta cikin kuka tace “Kawu Amadu ya zanyi gwaggo ta kasa fahimta ta ni wllh ba wai ban damu da damuwarta bane ko ban son abunda take so, nasan Saboda in yi karatu ne yasa bata son ayi man Auren to amman Baffana na cikin matsala in ban taimaka mashi ba kana iya ganin Allah ya ki bani sa’a ma a karatun amman inna taimaka mashi in da rabo sai kaga Allah nima ya taimaka man ya cika man buri na” ajiyar zuciya ya sauke kafin yace “na fahimce ki sosae ki yi hak’uri Kinji ki bi komae a hankali dole dama zata shiga damuwa kuma ranta ne ya 6aci sosae shiyasa take ta maganganu kar ki damu ki daina yawan kuka kar wani ciwon kuma ya kama ki” kai ta d’aga mashi alamar to yace taje ta de6o breakfast ta ci ta tafi islamiyyar cikin karyayyar murya tace “amman tace fa kar in k’ara ta6a mata komae” d’an murmushi yay yace “kar ki damu da hakan kije ki de6o bazata hana ki ba kuma aikin ma in bata nan sai ki yi in kuma ta nuna maki bata son abu a yanzu ki daina jayayya da ita tunda ranta a 6ace yake” tare suka fito ya tsaya a bakin kitchen d’in har ta zubo ta koma d’aki sannan shima ya nufi d’akinshi, sam tama kasa cin wani na kirki karshe d’auka tay ta mayar kicin d’in ta dawo ta shirya, koda ta fito saida taje bakin kopar d’akin gwaggon tace mata ta tafi islamiyya sanin ba amsa mata zatai ba ya sa ta tafi, lokacin da ta fito Kawu Amadu ya bud’e shago saida ya k’ara mata magana kan ta daina damuwa tace to kafin ta wuce, Koda taje islamiyyar duk takurewa tay wuri guda da ka kalleta zaka fahimci tana cikin damuwa har wasu na tambayarta sai dae tace ba komae sam hankalinta bai kan abunda ake koyawa a haka har Malaminsu na hadda ya shigo wato discipline d’in su Malam Nazifi, d’aya bayan d’aya ya rink’a bi yana amsar hadda da ya basu har aka zo kan Fatuu ya kira sunanta saidae kwata kwata bata ji shi ba har saida wata ta kusa da ita tay tapping nata sannan ta dawo cikin hankalinta k’awar ta nuna mata saitin Malam tace yana magana da sauri ta kai idonta kan shi ganin kallon da yake mata yasa tasha jinin jikinta ta kusa da itan tace mata haddar ki zaki bada, shiru tay sai zare ido take to inama ta ga kwanciyar hankali jiya da har zata yi hadda, ce mata Malam Nazifin yay ta mik’e tsaye bayan ta mik’e yace ta bashi haddar tay wuri wuri da ido sai faman mommotsa baki take ta rasa yadda zata yi kawae sai tasa mashi kuka dama so yake yay Nazarinta sosae shiyasa yay mata hakan alamu yay mata na ta zauna ta koma da sauri ta zauna duk jikin sauran daliban yay sanyi, cigaba da amsar haddar yayi har aka kammala ya basu wata bayan ya gama ya mik’e zai fita lokacin Fatuu ta d’ukar da kanta ya kira sunanta ta d’ago da jajayen idanu yace ta biyo shi daga haka ya fita ta mik’e ta bi bayan na shi tana fita yan ajin suka fara chapter kan ta.

 

Can k’ark’ashin wata k’atuwar bishiyar dalbejiya dake a cikin Makarantar ya nuna mata yace ta jira shi ya nufi Staffroom bada jimawa ba ya fito ruke da plastic chairs ya nufeta bayan ya aje su ya nuna mata d’aya yace ta zauna shima ya zauna kan d’aya ya zuba mata ido hakan yasa ta sunnar da kan ta can ya kira sunanta ta amsa ba tare da ta kalleshi ba yaci gaba “Fateema Muhammad Ardo na fahimci kina cikin damuwa ba tun yanzu ba tun wasu watanni can baya kin canja sosae akan yadda na san ki in ba damuwa ina son jin miye damuwarki ko da taimakon da zan iya yi maki kan hakan” Shiru tay tana sheshsheka har saida ya k’ara tambayarta sannan ta d’ago fuskarta duk hawaye ta fara Magana “Malam ba komae, ba abunda ke damuna” d’an murmushi yay kafin yace “sai dae in baki son in sani ne amman ai duk wanda ya sanki yasan kin canja Fateema yaushe rabon da ki yi laifin da na d’aga bulala na bugeki wanda inda da ne ba yadda za’ai a kwana biyu baki laifin da ban buge kin ba” shiru tay tana ta matse ido ya nisa yace ” in baki son in sani ne bazan takura maki ba zaki iya tafiya dama ina tunanin ko da shawara haka in kina buk’ata sai in baki watak’il ta taimaka maki”, shiru tayi can ta d’ago cikin muryar kuka tace “Malam abubuwa ne duk basu man daidai farko na rasa wani abu da nike tunanin nawa ne yanzu kuma wata matsala ce a gida na rasa yadda zan yi” sosae take kuka tana goge fuskarta da gefen hijab d’in ta, hanky ya fiddo daga cikin Aljihun shi ya mik’a mata yace ta goge kuma ta daina kukan zasu yi magana tace to, saida ya ga ta natsu sannan yay gyaran murya ya fara Magana,

 

“Wato Fateema ita rayuwa da kike gani dama cike take da k’alubale kala kala, dole kana musulmi mai cikakken imani ka rink’a fuskarta jarabawa kala kala ba kuma don Allah bai son bawan sa bane yake jarabashi sai don ya gwada imanin bawa ya ga zai yi hakuri ya cinye jarabawa ko kuwa zai butulce, wanda in bawa yay hakuri silar hakan Allah ubangiji zai daukaka shi, hakan na nufin duk abubuwan da suke faruwa da bawa marasa dad’i Alkhairi ne atare da shi matuk’ar yay hakuri, akwae ayoyi a cikin surorin Al’qur’ani da yawa da sukae Magana kan hakuri misali:

 

Suratul Ali Imran Aya ta 200 fad’inshi Allah SWT, Bismillahir Rahmanir Rahim “ya ku wad’anda suka yi imani ku yi hakuri,kuma ku jure kuma ku zama acikin shiri, kuma kuji tsoron Allah zaku rabauta”.

 

 

Suratul zumar Aya ta 10 fad’in SWT “hak’ika masu hak’uri ne kawae ake cikawa ladansu ba da lissafi ba”. Haka suratul Anfal Aya ta 46 fadinshi SWT “kuyi hakuri hak’ika Allah yana tare da masu hak’uri”.

Suratul Ali Imran karshen Aya ta 146 “…..Allah yana son masu hak’uri”.

Sannan akwae jerin ayoyi a Cikin Suratul baqara daga k’arshen Aya ta 155 zuwa Aya ta 157, fad’in shi SWT “…..kuma kuyi Albashir ga masu hak’uri(155) “sune wadanda idan wata musiba ta same su sai su ce, mu na Allah ne kuma mu wurinsa zamu koma” (156) “wad’ancan gafarar Allah ta tabbata a gare su da rahamarsa, kuma wadancan su ne shiryayyu”. Haka a cikin Suratul Ma’arij Aya ta 5 fad’inshi Allah SWT “ku yi hakuri, hakuri mai yawa”, da sauran dai Ayoyi da sukae Magana kan hakan,

 

“Sannan Magana ta farko da kika yi ta kin rasa wani abu akwae Aya ta 216 a cikin Suratul baqara da Allah SWT yay Magana akan hakan, “An wajabta maku yak’i a kan ku alhali kuwa shi abin k’i ne a gare ku, akwae fatar cewa ku k’i wani abu alhali shi ne mafi Alkhairi a gare ku, kuma akwae fatar cewa kuna son wani abu alhali kuwa shi ne mafi sharri a gare ku, kuma Allah ne yake sani kuma ku ba ku sani ba”

 

“Anan Fateema ina mai baki shawarar ki yi hakuri akan duk wani abu dake damunki ki fawwala ma Allah ki kuma d’age da yin Addu’a dare da rana in sha Allah zai yaye maki dukkan damuwar ki, sannan Jinkirin samun biyan buk’atar ki tare da naciyarki wajan Addu’a kada ya zama sanadiyyar debe kaunar ki. Allah ya laminta ne zai amsa Addu’ar bawa akan abun da ya za6a mashi ba akan abun da shi ya za6awa kan shi ba, a lokacin dashi ya ga dama ba a lokacin da kai ka ke so ba, jinkirin samun biyan bukata kan abunda mutum ke tsananin buri da fatan mallaka na daga jarabawa amman idan akayi hakuri sai Allah ya ba mutum wannan abun ko ma wanda ya fi shi ” Sosae Malam Nazifi yay mata Nasiha kuma ta ji sanyi a ranta harda Nafilolin da zata rink’a yi ya rubuta mata tay mashi godiya sosae.

 

(Abunda na fad’a daidai Allah ya bamu Ladan in da nayi kuskure Allah ka yafe man).

 

Tafe take bayan an tashi tana ta juya Maganganun Malam Nazifi tana fatan Allah ubangiji ya kawo mata k’arshen matsalolinta, tana gab da isa bakin lungun da zata bi wata budurwa da zata yi sa’an Fatun ko kuma ta d’an girme mata kad’an don ta fi Fatun tsawo ta 6ullo ta mik’o hanya tana sanye da pink Hijab Fatuu na ganin ta ta ayyana wani abu a ranta da sauri ta k’wala mata kira tace “Jamila” juyowa budurwar tayi sai lokacin ma ta lura da Fatun ta nufo ta tana mata murmushi a gabanta ta tsaya tace “Fatuu wllh bamma lura dake ba daga islamiyya kike” kai Fatun ta d’aga mata alamar eh ita kuma ta gyad’a kai har zata juya Fatun tace “Jamila don Allah ina son rok’on ki wani abu” tsayawa tayi da alamun mamaki kan fuskarta tace to, Fatuu taci gaba “dama so nike in rok’e ki abubuwan da nayi maki a can baya ki yafe man lokacin harda yarinta” dariya Jamila tayi tace “kai Fatuu abunda ya wuce ai ba wani abu kuma ma ni ai rigima dake Alkhairi ta zamar man wllh, zaki iya tuna wani lokaci can da kika 6arar man da awara har kafin ki zubar wani mutum ya raba mu?” Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai, taci gaba “to ai d’an gidan Hajiyar Sanata ne nasan k’ilan baki rasa sanin shi to ta silar hakan wata rana ya ganni ina tallan k’osai da safe da yake ranar da kika zubar man da awaran shi ya bani kud’i anan na fara sanin shi to shine ya tambayeni miyasa bana zuwa makaranta na fad’i mashi baban mu ne bai lpy….” Nan ta kwashe komae da Haisam yayi masu ta fad’i mata tace “kinga yanzu bamu da matsalan komae na bar tallan Saboda shi innata ke yin sana’ar a cikin gida babana kuma ya samu lafiya sosae Shima Yana yin sana’ar su hatsi da cefane anan k’opar gida kuma har yanzu suna gaisawa da babanmu da zai yi aure ma babanmu yaso zuwa shi yace ya barshi” Fatuu dake ta bin ta da idanu jin tayi shiru yasa ta gyad’a mata kai kawae Jamila tace “ko baki lpy ne na gan ki sukuku” a sanyaye tace “kai na ne ke ciwo” tayi mata Allah ya sawak’e daga haka tace bari ta wuce dama innarsu ce ta aikota cikin unguwa, ba k’aramin sanyi jikin Fatun yay ba jin abunda Haisam yayi ma su Jamilar a ranta ta rink’a ayyana “dama haka halin shi yake mu kuma Mu kai tunanin so na yake” wani irin k’una zuciyarta ta fara mata a fili ta ke fad’in “ina son ka Ya Haisam duk da nasan na rasa ka har Abada” cigaba da tafiya tay sukuku da ita abubuwa sun mata yawa gashi ba Haulat balle ta tausheta ko ta waya wuyar samu take mata don k’aramar waya ce a hannunta tun kafin ta tafi tata ta lalace aka ce bazata gyaru ba sai ta sayar ta amshi k’arama, farko da suka je Nijar da wayar Yayanta Usman suke chat yanzu kuma shi ya dawo dama rakata yay d’an sauk’inta shine Kawu Amadu sosae ya damu da halin da take ciki yake yawan bata baki gwaggo kuwa abun ba’a Magana, Washe gari da safe wurin karfe 11 na safe lokacin gwaggo ta tafi aiki Amadu ya isketa a d’aki ya bata kud’i Naira dubu d’ari yace Baffanta ne ya turo yace a bata daga haka ya fita, bin kud’in da Kallo Fatuu tay ganin abun take kamar almara wai kud’in da zata Siya kayan kicin d’in gidan auren ta ne ta rasa tunanin da zata yi kan kud’in ta san ko ta kai ma gwaggo ma ba amsa zata yi ba ita gashi ba iya zuwa kasuwa zatayi ba da sunan siyo wani abu kawae sai ta mik’e taje ta saka su cikin wardrobe, haka suka ci gaba da yin zaman doya da manja ita da gwaggo sam in tana ma gidan Fatun k’umshe wa take a d’aki bata samun sukuni sai in ta tafi aiki gashi ta kasa bin yadda gwaggon ke so na bijirewa Maganar auren Don har Baffanta ya sanar da ita sati mai zuwa zai zo ya d’auketa har tayi rama Saboda damuwa amman duk da hakan bata wasa da yin Addu’a,

 

Ranar Laraba tana fitowa don tafiya islamiyya sai ga Tk ya taho kan mashin d’in shi zai nufi gida yana ganinta ya tsaya yana murmushi itama d’an Murmushin ta ke mashi yace “Manyan gari kwana biyu ina kika 6oye?” itama tambayarshi tay a sanyaye tace “Tk ashe ka dawo?” Yace “eh tunda uwar d’akina ta dawo ai kinga dole in dawo” d’an bud’a ido tay tace “Hajiya ta dawo ne?” Yace “eh tun ranar Monday ma ashe baki sani ba” girgiza kai tay tace bata sani ba yace to ta dawo, har zai ja mashin d’in sai kuma ya dakata yace “Amman dae baki lpy ko” d’an cije lip d’inta na k’asa tay kafin ta d’aga mashi kai alamar eh yace ai ga alama nan Allah ya sawak’e daga haka ya ja ya tafi, tsaye tayi tana tunanin zuwa gun Hajiyar yanzu ko sai ta dawo can ta yanke bari ta koma gida ta aje jakar ta canja kaya sai ta je kawae, doguwar rigar material da mayafinta ta sa bayan ta koma gidan ta fito ta nufi gidan Hajiya, lokacin da ta shige gate bin part d’in Haisam da kallo tay rabon da ta shigo gidan tun kafin yay aure d’an girgiza kai kawae tay ta wuce, Hajiya na zaune a Falo idanunta sanye da glasses tana kallon tv Fatun tay sallama ta shiga har saida gabanta ya fad’i don tana shiga tay arba da wasu manyan hotuna wanda a da babu su, d’aya Haisam ne da Fanan da ganin yanayin shigar da suka yi da bikin su ne sunyi matuk’ar kyau shine a tsakiya sai gefe d’aya kuma Hajiya da su ne sun sakata a tsakiya duk sunyi dariya sai d’ayan gefen kuma hoton Fatun ne ita da Haisam wanda aka yi masu da kayan Fulani a cikin falon Hajiyan yayi kyau sosae, juyowa Hajiya tayi tana kallonta ta cikin gilashin har ta k’arasa ciki ta zauna kujerar kusa da ita da d’an murmushi tace “Hajiya ina wuni an dawo lpy” d’an kya6e baki Hajiyar tay kafin tace “idon ki kenan Fateema, ai nayi zaton sai na nemo ki da kaina ace kwana biyu na dawo amman baki zo kikai man sannu da zuwa ba har Dije dae ta shigo, ko don yayan ki ya bar gidan shiyasa za’ai man tawaye ko da yake tun ma kafin ya tafi ai kika d’auke man k’afa” ita dae d’an murmushi kawae tayi Hajiyan tayi mata murnar gama Makaranta da fatan sa’a a hankali ta amsa mata, shiru ya biyo baya can taji Hajiyar tace “Wai Fateema ko dae har yanzu ba ki jin dad’i ne naga duk kin yi wani iri gashi har rama ma naga kin yi sosae” sadda kanta tay ba tare da tace mata komae ba hakan yasa Hajiya k’ara tambayar tata aikuwa kawae sai tasa mata kuka, bin ta da ido hajiyar kawae tayi with mouth agape ganin bata da niyyar dainawa yasa ta kai hannu kan shoulder d’inta tace “shikenan ya isa hakanan kuka ai bai magani in baki lafiyan ne ko wani abu na damun ki ai sai ki fad’a man ba kita kuka ba, fad’a man miye?” Shanye kukan tay ta d’ago fuskarta duk hawaye cikin shaky voice tace “Gwaggo ce….” Sai kuma tayi shiru tana motsa baki Hajiyar tace tana saurarenta mi dijen tayi mata Fatun taci gaba “f…fushi take da ni, bata man magana, bata kula ni ta hana ko aikin gida in rink’a yi….” Cigaba da kukan tayi da tsananin mamaki Hajiya tace “Dijen ce ke maki haka harda gaba da girmanta to mi ki kai mata Fateema da har yay zafi haka?” Cikin muryar kuka Fatun ta bata labarin duk abun da ke faruwa, jinjina kai Hajiya ta shiga yi ita kanta ta girgiza da jin batun auren har ta kasa magana Fatuu nata sheshsheka can tace mata ya isa haka tayi shiru kafin tace “Amman Dije bata kyauta ba gaskiya to da mi zaki ji ne, ni Sam koda ta shigo bata man Maganar ba kuma komae ai a hankali ake bin shi ko ba ta dau zafi haka ba hakan zai samar da mafita ne, ki k’yale ni da ita” ta k’arasa ta sigar lallashi kai kawae Fatun ta d’aga mata tace ta daina kukan ta share hawayenta, bayan ta goge Hajiyar tace bari a zuba mata Abinci ta ci farko cewa tay ta k’oshi amman hajiyar tace a’a sai ta ci, bayan ta k’wala ma Saude kira ta bata umarnin ta kawo ma Fatun Abinci a nan cikin Falon bayan ta kawo mata har saida Saude ta tambayi Fatun bata lpy ne lokacin da ta gaisheta tay shiru sai Hajiya ce cikin 6acin rai tace mata ita da Dije ne, sai da Hajiya tasa ta taci sosae bayan ta gama tace taje d’akinta ta watsa ruwa ta kwanta tace to ta mik’e ta d’auki plate d’in Abincin walking slowly ta kai Kitchen kafin ta wuce d’akin Hajiya, bayan tayo wankan ta kwanta a k’asa kan carpet tana ta tunani bada jimawa ba bacci ya kwashe ta, sosae Fatuu tasha bacci don har Hajiya ta shigo don yin sallar Magrib da ake kira bacci take ta yi saida ta tasheta kafin ta tashi tayi salla bayan ta idar saida ta jira Hajiya ta gama don tana dad’ewa in tana yin salla sannan tace mata zata tafi amman Hajiyar tace tay zamanta a nan bayan sallar Isha zata je ta samu Dijen a hankali Fatun tace to, ganin kaman ta k’i sakin jiki yasa Hajiya ce mata taje d’akin Saude tace to ta mik’e ta nufi hanyar fita idon hajiya a kanta tana kallonta cike da tausayi yarinyar da koda yaushe take cikin nishad’i ce ta koma sukuku da ita, bayan sallar Isha hajiya ko cire hijab bata yi ba ta nufi gidansu Fatun baiwar Allah bata ma jin dad’in k’afafunta ciwo suke mata dama tana da ciwon shiyasa ma Senator ya hana ta dawo don sai da suka je US checkup daga can suka biya gurin su Haisam tare da Mahaifiyarshi harda Aunty da Hajiya maryam da mahaifin Fanan d’in duk aka je ganin d’aki, lokacin data isa da sallama ta shiga gwaggo ta fito daga d’akinta tana ganin hajiyar ta fara mata fara’a ta nufo ta tana yi mata sannu da zuwa…….

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button