Halysaah Page 62 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 62…Sau daya Khaleesat ta kallesa ta dauke kai bayan tayi convincing kanta ba wajensu yake tahowa ba, Safiyyah tayi kasa da murya tace “Ni ban ma taɓa ganinsa a school din nan ba sai yau, gwara Housemate dinki shi dama ya saba zuwa ya same mu a nan sanda muke Exam, he is coming toward us fa” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba amma can kasan ranta ita ma tayi mugun mamakin ganinsa a department dinsu, how did he even know spot din da suke zama da Safiyyah, sai kawai tayi assuming hanya ce ta biyo da shi ta nan din, har ya iso inda suke zaune Khaleesat bata daga kai ba but she is surprise, Safiyyah na kallonsa tana murmushi tace “Good afternoon Ya Junaid” Ba tare da ya kalleta ba yana kallon different direction yace “Evening, can you excuse us… I want to have a word with ur Coursemate” Safiyyah dai bata fasa kallonsa ba tana gyada kai tace “Sure, why not….” Sai kuma ta dau jakanta ta mike tana kallon Khaleesat tace “Zan je wajensu Nora, if you are looking for me ina can…” Khaleesat ta gyada mata kai kawai, daga haka Safiyyah ta bar wajen, ita dai Khaleesat mamaki ma yasa ta kasa kallon Ajay dake tsaye kanta, he wants to have a word with her? To me zai ce mata da zai biyota har department din su, duk da under same faculty suke amma ko da wasa bata taɓa haduwa da shi a school ba in ba few days ago ba da suka shigo da Jay, ta kalli wayar da yake mika mata fuskarsa babu yabo babu fallasa, she was surprise, why is he giving her his phone? bata amshi wayar ba ta daga kai ta kallesa a karo na farko, ganin yanda ya daure fuska ya sa ta mika hannu ta amshi wayar tana kallon screen din, sosai gabanta ya fadi ganin hoton da suka yi da Aymaan jiya a get together, ta dinga kallon hoton babu ko kiftawa, gashi ba hoto daya ba ba kuma biyu ba, can ta kalli a ina yaga hoton sai taga a Instagram ne, bata san sanda ta gyara zama ba zuciyarta na bugawa sosai, Instagram kuma? Me ya kai hoton Instagram? ta shiga uku, ita da ko a screen din wayarta bata taɓa saka hotonta ba balle aje ga WhatsApp ko kuma facebook uwa uba Instagram, gaba daya hankalinta yayi mugun tashi ta kasa cewa komai, da kyar ta daga kai ta kallesa ta ga wani irin kallo yake mata, ta sauke idonta gabanta na ci gaba da faduwa ta kasa cewa komai, fixge wayarsa yayi daga hannunta yace “So you came back fully prepared to party in Baltimore Right? You came back to mingle with jobless guys following them to party up and down, Har kin ma mance abinda ya same ki, but wait… Baki taɓa zuwa islamiyya bane ko kuma kin je kin yi skipping classes? Ko kuma bayan mijin da kika ce a kyaleki kina son zama da shi ya sake ki baki zauna kin tambayi makusantan ki what next ba? Kawai saboda kina jin kanki on a different level yanxu shi yasa kika kama hanya kika tafi cikin kattin banza masu shaye shaye da sunan get together, har ki tsaya gefen wannan crook guy din ayi maku hoto kina dariya” Khaleesat ta kasa daurewa ta fashe da kukan da tun safe take son yi bata samu kwakkwaran reason din yin sa ba, shiru yayi yana kallonta irin kallon mamakin nan, after a minute ya zauna inda Safiyyah ta tashi amma bai ce mata komai ba, ita kuma bata fasa kukan da take ba kamar an aiko ta, tayi me isarta don kanta ta hakura ta fara goge idonta tana sauke ajiyar zuciya, sai a sannan ya kalleta yace “Ohk i understand, kin dawo America ne kiyi abinda ranki yake so ba kuma kya bukatar wani yace zai yi questioning din ki ko kuma yayi correcting din ki” Wani sabon kukan ta fara yi kamar ana tunzurata, ya mike trying to control himself yace “Get up” ganin taki tashi ya hade rai yace “Baza ki tashi ba?” A hankali ta mike tana ci gaba da goge hawayen dake zuba idonta tana shesshekan kuka, babu yabo babu fallasa yace “Mu je” Bata masa musu ba ta fara bin sa har sannan tana goge hawayen idonta, after almost 10 minutes walk suka iso inda yayi parking motarsa, yana bude motar ta daga kai ta kallesa a hankali tace “Ni ban ce ma Safiyyah zan tafi ba” Ya mata wani irin kallo yace “Baza ki ce mata ba, get in the car” Bata ce komai ba ta zaga ta bude gaban motar ta shiga, bata taɓa shiga motarsa a America ba sai ranan, har suka isa Apartment dinta babu abinda yace mata, bayan yayi parking without looking at her yace “Leave my car” Sauke idonta tayi, ta bude motar a hankali ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace “Don Allah tunda ka san sa kayi masa magana ya goge hotona a Instagram” Ya jefa mata wani kallo yace “Zan gaura maki mari, ni na hada ku nayi maku hoton da zan ce masa ya goge?” Daga haka yayi Reverse yayi zoom off daga Neighborhood din, wasu sabbin hawaye suka cika idonta ta juya tana tafiya a hankali ta nufi kofar apartment dinta ta bude ta shiga, zaunawa tayi a parlor ta fara tunanin to ko shi ma Housemate dinta ya ga hoton ne a Instagram bayan status din Safiyyah, bata taɓa jin haushin Safiyyah irin yau ba, Allah kadai yasan mutane nawa ne suka ga hoton nan daga jiya zuwa yau, ta goge idonta ta bude handbag dinta ta ciro wayarta ta fara kiran Safiyyah, yana fara ring Safiyyah ta daga tace “Ya tafi ne in fito?” Trying to be calm Khaleesat tace “Kin ga Safiyyah kije kiyi ma wannan mutumin magana ya cire hotona a Instagram, who does that? Ta yaya daga hoto zai je yayi posting a Instagram kamar mun san juna from anywhere da shi? Meye hadina da shi da zai min haka? Har wani dogon magana muka yi da shi da har zai dau hotona tare da shi yayi posting a Instagram dinsa?” Muryarta na rawa ta kare maganar, Safiyyah tace “Innalillahi, Instagram yayi posting hotunan? Kinsan ni ba wani damuwa da IG nayi ba, kuma fa Aymaan ban taɓa ganin yayi posting mace a Instagram ba, sai gashi yayi posting na ki, amma how did you know his Handle da har kika ga yayi posting din ku?” A fusace Khaleesat tace “Ina ruwana da wani handle dinsa, kawai daga haduwa ko maganar minti daya ban yi da mutum ba ya kama hotona yayi posting duk duniya su gani, is he even okay? Ko ba shi da hankali ne? To wallahi ki je kiyi masa magana ya goge min hotona” Safiyyah tace “Ni ma dai nayi mamaki gaskiya, wallahi ban taɓa ganin yayi posting mace ba sai gashi yayi posting din ki, kar dai shi yasa Ajay ya zo wajen ki yau? Don definitely za su iya sanin juna kilan ma suna following juna, kinsan akwai association na Nigeria student a makarantar mu dole ma za su sun san juna, ɗan Deputy governor ne fa Aymaan, he is also popular on IG” Takaici ya sa Khaleesat ta katse kiran ta jefar da wayarta kan kujera, wani mugun haushin Aymaan da Safiyyah ta dinga ji a ranta, da tana da numbersa babu abinda zai hanata kiransa ta gaggaya masa magana, ko an gaya masa ita irin wa ennan matan ne da har zai yi posting din ta duniya su gani, Abdul ne ya fado mata, nan da nan jikinta yayi mugun sanyi, don babu uban da ya kai sa zama active a Instagram gashi da uban followers, wa ma ya sani ko yasan Aymaan din, sosai taji hankalinta ya tashi ta jinginar da kanta da kujera wasu hawayen na zuba idonta, bata taɓa jin Safiyyah bata kyauta mata irin yau ba, da kyar ta mike ta dau jakarta da waya ta wuce sama. Meemah ce ta shigo dakin Momy tana mika mata wayar hannunta hankali tashe tace “Momy kin gane wacece wannan kuwa?” Momy ta ajiye bowl din farfesun hannunta ta amshi wayar tana kallon screen din, can ta kalli Meemah tace “Wannan ba er matsiyatan can bace? Khaleesat take ko wa” Meemah ta zauna gefen gado har sannan fuskarta dauke da tashin hankali tace “Ita ce Momy, ita da Aymaan” Momy ta ajiye wayar ta dau bowl din farfesunta ta ci gaba da ci tace “Waye kuma Aymaan?” Meemah tace “Aymaan din kuma kika manta yau Momy, Muhammad Aymaan ɗan mataimakin gwamna fa” Momy ta kalleta tace “Wai tsohon saurayin ki Muhammad?” Meemah ta hade rai tace “Tsohon saurayi fa kika ce Momy, Aymaan din ne tsohon saurayina?” Momy tace “To in ban ce maki tsohon saurayin ki ba ya zan ce, yaron da ba ɗaga kiranki yake ba yanxu, yaushe rabon ki da shi? kin ga kuwa ai sai in ce tsohon saurayin ki Meemah, dama ai a titin Instagram din ku ka hadu da shi, ba sai da na dinga hada maki da rokon Allah ba kika samu sassaucin son sa da kika dora ma kanki, dama su biyu zuciyarki ta makale ma da shi da wani ɗan sarki yake ko wa shi ma kullum sai kin isheni da zancensa bana ma tunanin kina da numbersa, duk samarin ki a Instagram din ku ke haduwa kuma a can ku ke rabuwa, ni na taɓa ganin wannan wahala” cike da damuwa Meemah tace “Wallahi mace ce ta shiga tsakaninmu da Aymaan Momy, amma ai ya so ni kamar ran sa, ki tuna har fa kano ya sha zuwa wajena” Momy ta tabe baki tace “Amma ai ba gidan ubanki yake zuwa ba sai dai yace ku hadu gidan cin abinci ko wani wajen, bai taɓa biyo ki yaga gidan ku ba, shekara kusan takwas ana abu daya in da gaske son naki yake me ya hanasa fitowa har yau, ni dama tun da Malam Tasi’u yace min bazai fa aureki ba na hakura da kashe kudina a iska, amma ai na kashe kudi kan wannan Aymaan din, bayan Malam Tasi’u ma akwai wani malamin da yace min mu hakura ba auren ki zai yi ba bata maki lokaci kawai yake, kuma uwarsa ma a tsaye take kyam” Meemah tace “Momy duk ba wannan ba, a ina yasan yarinyar nan har suka yi hoto tare? Kinsan shi ma a Amurka yake kuma makarantar su daya amma ya gama degree dinsa tuntuni in dai ba masters ya koma yi ba, kuma wnn hoton daga gani a Amurka aka yi sa” Momy tace “Atoh kika san ko tsohon hoto ne, dama ai kin ce iskanci ta dinga yi a Amurkan don haka ba abun mamaki bane don kin ga hotonsu tare, yanxu kuwa ai sai dai tayi karuwancinta da yan Mariri” Meemah dai ta kasa cewa komai amma kana ganinta kasan hankalinta ya tashi sosai, Momy ta kalleta tace “Ai kun ma fi shekara biyu baku yi waya da shi ba ko?” Meemah ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Yanxun ma ina ganin hoton na kirasa bai daga ba, amma ni abinda ya bani mamaki duk yanda yake da mace fa baya posting dinta ko a WhatsApp balle har Instagram” Momy tace “Ɗan wani gari ne ma?” Meemah tace “Gusau” Momy tace “Abdul ya san sa ne?” Meemah tace “Oho, shi wannan ana sanin cikinsa ne, ni ban san ko sun san juna ba, kuma ai Abdul bai san ni da Aymaan ba tunda kinga ba wai ya taɓa zuwa gidanmu bane Aymaan din, sai dai su san juna a Instagram amma ba a sarari ba” Meemah ta kara Zooming din hoton da kyau tana kallon tsadadden Abayan jikin Khaleesat ga wani kallo da Aymaan ya kafeta da shi, ita kuwa tana dariya with her beautiful set of teeth, Meemah ta fice daga wajen hoton ta sake dialing number Aymaan amma har ya katse bai daga ba, mikewa tayi ta nufi kofa, Momy ta tabe baki tace “To ke banda abunki me zai yi da er talakawa aka ce maki, in kin bibiya hoton ya dade, yanxu kuwa ina taga hanyar zuwa Amurka, ai uwarsa ma ta fi mu ƙin talakawa bari ki ji in gaya maki, a zamanin yanxu dai ko wani me kudi ya waye baya yarda ya hada zuri’a da talaka, yanxu kwarya tabi kwarya kawai, haka abun yake” Ita dai Meemah ta fice daga dakin tana sake dialing number Aymaan with confusion. Tana zaune usual spot din da suke zama a school tana jiran Safiyyah da taje kai ma wani coursemate dinsu laptop dinsa, tun daxu take zaune wajen tana danna wayar hannunta with full concentration, lkci daya ta dakata da abinda take yi a wayarta jin wani kamshin turaren da ta sani ya doki hancinta, waige waigen wajen ta fara yi suna hada ido bata san sanda ta saki wayar hannunta ba zuciyarta na bugawa tana kallonsa babu ko kiftawa, he was the least person she is expecting to see in her life, lkci daya taji wani courage ya zo mata ta dau wayarta fuskarta a daure ta mike da nufin barin wajen, ya fixgo gyalen jikinta yana kallonta da kyau yana murmushi yace “You think i will let you just like that Khaleesat? Har kin samu masu ci gaba da sponsoring din ki an dawo dake America, ga shi har ana hoto dake ana dora ki a Instagram, u snapped a picture together with Aymaan har yayi posting din ki duniya ta gani, ko wani ɗan iskan gaye kin sani a Amurka and they are all ready to go through any mile for you, to ki sani na maida aurenmu da ke, you are still my wife….” A firgice Khaleesat ta farka daga baccin da take ta mike zaune jikinta na rawa, tun da uwarta ta haifeta bata taɓa mummunan mafarki irin wannan ba, ta sauka daga saman gadonta har sannan jikinta na rawa, bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba tana ganin abun kamar ba mafarki bane gaske ne, ba karamin tashin hankali ta shiga ba ta fara karanto duk addu’an da ya zo bakinta tana kuka, duk yanda ta so ta samu nutsuwa hakan ya gagare ta, she was really shock, da kyar ta daure ta dauko wayarta ta kunna data hannunta na rawa, kawai taji she wants to speak with her Housemate, tana bude data taga Aunty Farida ta ajiye mata sako, ta shiga DM dinta taga hoton da suka yi da Aymaan ta turo mata tana tambayar wanene shi, kuma me yasa zata yi hoto da shi…. Tashin hankalin Khaleesat ya ninku akan wanda take ciki da, she was so confuse and shock, gashi jikinta sai rawa yake, a ina kuma Aunty Farida taga hoton nan, ta shiga uku, shikenan kilan Abdul ma zai gani kenan mafarkinta ya tabbata ya zamto gaskiya? Ta fashe da matsanancin kuka tana jin zuciyarta kamar zai fito tsabar tashin hankali, ko reply din Aunty Farida bata yi ba ta fita daga WhatsApp din ta fara dialing number Housemate dinta da sauri, ta kirasa har sau biyu bai daga ba, rasa yanda zata yi tayi tana kuka, can kawai ta fara dialing number Safiyyah har sannan jikinta bai dena rawa ba, yana fara ring Safiyyah tayi picking, cikin rawan murya Khaleesat tace “Safiyyah baki ce ma mutumin nan ya goge hotona a Instagram ba dama??” Safiyyah tace “A’a na masa message ta WhatsApp he is not online fa, na kuma kirasa bai yi picking ba, kuka kike yi ko me? Haba Khaleesat sai kace warce tayi wani mugun abu? Get together fa kawai muka je aka yi hoto ba wai club ba, kuma shigar ki ta mutunci kika yi fa, Aymaan kuma left a reasonable distance tsakanin ku balle ace ko manne maki yayi a jiki” Khaleesat taki bata amsa tace “Kina da number Ya Junaid pls?” Safiyyah tace “Eh kamar ta numbersa Jawwad yayi min fowarding receipt din 10M da aka tura ma su Maman Abdul” Da sauri Khaleesat tace “Don Allah ki turo min yanxun nan” Safiyyah tace “Ohk bari in duba, amma ni dai wallahi ban ga abun damuwa ba don kawai Aymaan ya daura hoton ki a Instagram, sanannen Celebrity ne shi fa, kawai don bama Instagram ne shi yasa baza mu sani ba, kuma kawai don dai kina Iddah ne da ace kin gama so what?? Ai kin isa ne yasa ya dora ki” Khaleesat ta katse wayarta don bata son ta gaya ma Safiyyah magana she is just controlling her self all this while, ba a dau lokaci ba sai ga Safiyyah tayi mata fowarding number Ajay, Khaleesat tayi dialing number da sauri, gaba daya zafi ta dinga ji duk da uban sanyin da ake har da snow, don Ajay na dropping dinta daxu babu dadewa aka fara snow shi ne har ta kwanta bacci tayi wnn mummunan mafarkin, sai da ta kira sau biyu sannan Ajay ya daga, ta kasa daurewa ta fashe masa da kuka muryarta na rawa tace “Don girman Allah idan kasan mutumin nan ka taimaka min kayi masa magana ya cire hotona a Instagram page dinsa, wallahi ni ban san sa ba pls talk to him” Tana kuka sosai ta kare maganar, Ajay dake sauraronta kamar bazai ce komai ba sai kuma yace “Ni na ajiye ki a gefensa aka yi maku hoton da zan masa magana ya cire?” Ta kara fashe masa da matsanancin kuka tace “Na shiga uku, don Allah ni dai ka taimake ni wallahi ban san waye shi ba” Ajay ya ki cewa komai daga karshe ma ya katse wayarsa, ta mike ta koma kan gado ta dinga rera kuka, ita babban tashin hankalinta ace Abdul ya ga hoton nan, tsaf attention dinsa zai iya dawowa kanta kuma ba da good Intention zai dawo ba, tana rayuwarta low key gashi Safiyyah ta ja mata fitina, ji tayi kamar zazzabi na neman rufeta tsabar tashin hankali, ta kwanta saman gado tana sauke ajiyar zuciya hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, ta kusa awa daya a haka daga karshe tayi karfin halin tashi ta tafi bandaki zata yi alwala don yin sallan magrib, ko da ta fito ta kasa yin sallan ta kwanta ta lulluba da duvet saboda rawan sanyin da take, ba karamin kidimar da ita wnn mafarkin da tayi yayi ba, after like 15 mins ta ji ana danna bell din gidan, ta mike zaune da sauri har lkcn tana rawan sanyi, gaba daya a tsorace take kamar mara gaskiya, after some minutes aka sake ringing bell din gidan, ta fara tunanin ko dai Housemate dinta ne ya dawo, tunanin hakan yasa ta daure ta sauka daga saman gadon ta fita daga dakin, har a sannan kuma snow bai dena zuba ba…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
