Halysaah Page 179 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 179…Ajay ya wanke hannunsa bayan ya gama cin kifi daya ya mike ya dau sauran kifin da bowl din ruwan wanke hannu ya fita daga Bukkan, matar da ‘yar ta suka daga kai suna kallonsa, yarinyar ta mike ta nufesa ta amshi Clay bowl din hannunsa da roba taje ta ajiye sannan ta dawo tana kallonsa ta bude masa palm dinta alamar me yake so, ya girgiza mata kai, ta juya ta koma ta zauna tana kallonsa, walking slowly ya nufi river din dake nesa da inda Huts dinsu yake, ta baya yaji an taɓo sa ya juya yarinyar ta nuna masa takalmin hannunta sannan ta ajiye masa kusa da ƙafarsa don babu takalmi kafarsa, yayi murmushi ya saka takalman sannan ya ci gaba da tafiyarsa zuwa bakin ruwan, yana isa ya zauna kan wani ƙaramin rock a bakin wajen yana kallon ruwan da bai hango iyakarsa ba, ko minti sha biyar bai yi zaune a wajen ba yaji taku a bayansa ya juya, wani magidanci ne da bazai wuce Shekaru arba’in da biyar ba ya nufosa yana murmushi da Hausan sa that is not fluent yace “Sannu abokina, jiki yayi kyau yau ko?” Ajay ya gyada masa kai yana mayar masa da murmushin yace “Da sauki” Mutumin yace “Toh muna godiya ma Allah, yanxu za mu tafi za a baka maganin ka na yau, za mu je wajen Mai magani din baza mu jira ya zo ba yau, ai kana iya tafiya” Ajay yace “Zan iya….” Mikewa mutumin yayi Ajay ma ya mike ya bi bayansa suka bar bank din river din, suna komawa inda Huts dinsu yake mutumin yayi ma matarsa magana da yare, hannu ta daga ma Ajay alamar su dawo lafiya, ya gyada mata kai yana murmushi, daga nan ya bi bayan mutumin suka tafi, da ido yake ta bin karamin garin wanda ke bakin ruwa, duk inda ka wuce zaka ga babban river din garin daga gefe da kwale kwalen fishermen a bakin ruwan, Bayan tafiyar minti talatin da kafa suka iso wani Bukka, shi ma dai a kusa da ruwa yake, mutumin yayi yarensu sannan ya shiga cikin bukkan, shi dai Ajay na tsaye gefen Bukkan yana bin ko ina da kallo, sai ga mutumin da ake kira da Ozhi ya leko yace masa “Shigo ciki aboki” dukawa Ajay yayi ya shiga Hut din, ya zauna kan tabarman dake shimfide yana kallon wanda ke zaune ya bar gemu kaca kaca a fuska ya daga masa hannu yace “Barka dai” Mutumin yace “Kana tuna tun yaushe ne baka da lafiya?” Ajay ya sauke idonsa bai ce komai ba, Ozhi yace “Shekara biyu kenan ba shi lafiya….” Mutumin yayi dariya yace “Ozhi ina son shi ya fada da bakinsa ne” Ozhi yace “To Dochu yaya shi zai sani yana kwance sai barci….” Mutumin yace “Amma yana jin kowa ai, ko baka ji?” Ajay ya sauke idonsa, Ozhi ya gyara zama yace “Mun gode ma Yesu kawai” Mutumin ya mike ya fita daga Bukkan, Ozhi yace “Allah mu ke godiya ma” Ajay ya ɗan yi murmushi yana bin Bukkan da kallo, kullin magunguna ne ƙashi ƙashi a dakin da tarkace irin dai na tsibbu, har da abubuwan da aka rataye a sama suna ta reto, Ozhi yace “Kana tuna sunan ka yanxu abokina?” Ajay ya daga kai ya kallesa yace “Sunana Ahmad” Mutumin na murmushi ya gyada kai alamar jin dadi, zai yi magana sai ga mutumin ya shigo dakin da clay bowl dauke da wani ruwa ya mika ma Ajay yace “Zaka shanye wannan zuwa cikin ka yanxu” Ajay ya kalli Clay bowl din sannan ya amsa yana kallon ruwan ciki da wasu particles ke ta yawo a ciki, Ozhi yace “Ka shanye, shi ne yana maka magani ai” Ajay ya lumshe idonsa ya kai clay bowl din baki ya fara shan ruwan cikin, Ozhi sai murmushi yake har ya shanye sannan ya ajiye Bowl din, mutumin ya mike ya debo wani ruwa ya shafa masa a kai da fuska yace “Saura gobe zaka sha kuma” Ozhi yayi masa godiya da yarensu sannan ya mike yana kallon Ajay yace “Za mu ta tafiya yanxu” Ajay ya mike shi ma yayi ma mutumin godiya sannan ya bi bayan Ozhi suka fita daga Bukkan suka dau hanyar gida, kamar dai sanda suka fito yanxu ma dai duk inda suka bi a garin kallon Ajay ake ana ɗaga masa hannu, shi ma yana masu haka, bayan sun yi nisa Ajay na kallonsa yace “A ina zan samu Banki?” Ozhi ya bude ido ya kallesa yace “Bankin kudi?” Ajay ya gyada masa kai, Ozhi yace “Sai anyi tafiya zuwa Makurdi” Ajay yace “Awa nawa ne tafiyar?” Ozhi ya girgiza kai yace “Minti arba’in yayi yawa zuwa Makurdi” Ajay yace “Gobe ina son mu je Bankin” Ozhi yace “To sai mu tafi sassafe” Ajay ya gyada masa kai suna ci gaba da tafiya, sai kuma ya kallesa yace “Amma baza ka je fishing ba gobe?” Ozhi yace “Cikin dare ne zan je yau” Ajay ya gyada masa kai kawai…..Tana tsaye ta jingina da trunk din bishiya a babban lambun dake dauke da shukoki iri iri da suka kawata wajen, tsuntsaye sai shawagi suke a garden din happily making a chirping sound as the sun set slowly, the view was so beautiful and breathe taking, duk da yanda ta kafe view din da ido gaba daya hankalinta baya gun, she was just staring at the setting sun absentmindedly, tayi nisa cikin tunanin da take, likitan ta dake gefenta ta dafa ta tana kallonta cikin kwantar da murya tace “Magariba ya gabato mu je kiyi alwala ko” Kallon likitar kawai take babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda take cewa ba, sai ga hawaye ya fara taruwa idonta tana sauke numfashi a hankali, likitar ta kama hannunta ta jawota jikinta calmly tace “C’mon sweet heart, are you breaking another promise already?” ta kwantar da kanta jikin likitan hawaye wasu na bin wasu a fuskarta, likitan ta lumshe ido tana patting dinta duk jikinta a sanyaye, a tare suka juya jin footstep a lambun, ya tsaya daga inda yake bai karaso ba yana kallonsu, likitan ta fara gaishesa cikin girmamawa, zame jikinta tayi daga na likitan ta juya masa baya alamar bata son ganinsa hawaye na zuba idonta, ji take kamar numfashinta zai dauke kamar ko da yaushe, ta fashe da matsanancin kuka ta dafe trunk din bishiyar dake gefenta, ko amsa gaisuwan likitar bai yi ba ya juya ya fice daga garden din, da sauri likitan ta kamota ganin faduwa zata yi, ta fara kokarin zaunar da ita akan lallausan carpet dake shimfide wajen trying to calm her down tace “Haba kanwata, me yasa baza ki cika min alkawarin da kika daukar min ba?” Muryarta na rawa tace “Kiyi hakuri bazan iya ba wallahi” Rungumeta likitan tayi tana bubbuga bayanta a hankali wani mugun tausayinta na shigarta, tayi attending to different cases in her career as a medical Doctor amma babu wanda ya taɓa daga mata hankali ya tsaya mata a rai irin na baiwar Allahn nan, she wish she can take away her pains, she wish she can make her happy once more, she wish she can make her forget the past and face the present, a hankali likitar tace “Halysaah….” khaleesat ta daga rinannun idonta tana kallon likitan, likitan tace “Kiyi hakuri Halysaah, kiyi hakuri” Khaleesat ta sauke idonta bata ce komai ba hawaye na sauka idonta, likitan ta daga ta tana rike da hannunta suka bar lambun zuwa babban compound din gidan, yana tsaye jikin bango ya daga kai yana kallon faduwar rana babu ko kiftawa, ashe ba tafiya yayi ba bayan fitar sa daga garden din, har suka iso inda yake tsaye bai sani ba, Likitan na kallonsa tace “Ashe kana nan ranka shi dade, barka da yamma” Jay ya juya ya amsa mata a hankali, Ita dai Khaleesat bata kallesa ba ta zame hannunta daga na likitan ta bar wajen zuwa cikin gida, yana kallon likitan yace “Ya jikin nata yau Dr?” Likitan na murmushi tace “Yau kam Alhamdulillah da sauki, ba wani complication, kwata kwata bata yi kuka ba sai yanxun nan abun ya motsa mata, kuma anyi hira da ita sosai yau da su Kilishi, daxu da rana ma da Kilishi zata je gidan Hajja tare suka tafi har da Hadiyah, amma suna isa gidan Hajjan kuma tace zata dawo gida, shi ne aka sa driver ya maidota tare da Hadiyah, to da ta dawo bacci tayi don magungunan da ka rubuta mata last suna sa ta bacci sosai gaskiya, dab da la’asar ta tashi naga tana ta gyaran daki har da canza zanin Gado sannan ta wanke bandaki nace mata ai duk anyi da safe, shi ne take gaya min mafarkin da tayi….” Jay ya katse likitan don bai ma son jin mafarkin don it is always the same sad dream everyday, cikin sanyin murya yace “But did she complain of chest pain today?” Likitan ta girgiza masa kai tace “A’a ta kwana biyu ma bata yi complain ba gaskiya, duk kwana biyun nan ma akwai improvement fa” Yace “Ohk” Da damuwa likitan tace “Amma ranka shi dade an fito da ɗan uwan naka da theatre din kuwa? And I am hoping the operation was successful” Jay yace “Mu ma bamu samu wani feedback ba tukunna, i don’t think an fito da shi” Likitan tace “To Allah Ubangiji ya sa mu ji alkhairi, Allah ya tashi kafadunsa, Allah yasa karshen wahalan kenan” Jay yace “Ameen” Daga haka ya juya ya bar wajen, Likitan ta bi bayansa tana girgiza kai cike da tausayin Walid a ranta, operation a spinal cord kusan na hudu kenan duk babu success sai kara tabarbarewa abun yake, asibiti yafi uku da aka canza masa in different countries, ana kuma tunanin wannan operation din ne na karshe idan kuma ba ayi nasara ba shikenan a haka zai dawwama with complete paralysis for life, even though the success rate of the operation is just 5 percent dama, gashi baya iya rikon fitsari don complications din Surgery din yayi affecting bladder function dinsa, Aunty duk ta fita hayyacinta saboda ita da Jakadiyarta da Mukhtar ke tare da shi a asibiti, sai dai ta dawo gida Nigeria ta huta kwana biyu sannan ta koma, duk mutanen da take harka da su babu wanda yace bari ya tayata jinya ko na rana daya, har aminiyarta Hajiya Nafisah warce sau daya taje dubo Walid a sanda suke India shi ma kwana biyu tayi ta juya kamar ana koranta, daga haka kuma bata sake komawa ba, ko kiran waya bata yi ba, a dangin Aunty ma babu wanda yaje tunda ba harka take da su ba tun bayan da tayi aure gidan Sarauta ta dinga walakanta su, shi ne kowa ya kama kansa aka kyaleta, tafi shekara ashirin rabonta da garinsu bata kuma neman kowa har wa enda suke uwa daya uba daya, a masarauta kuwa sai dai su je dubiya jefi jefi su yi kwana daya zuwa biyu su dawo, Mami ce kadai ke yin kwana biyar zuwa sati daya in dai taje, ita ma saboda Khaleesat ne yasa zaman nata baya wuce haka, sai Ummi warce ita dama kwana uku take cewa mijinta yace tayi, su Kilishi kuwa idan suka je to yawon bude ido suke yi a gari su gama kwanakinsu su koma Nigeria, Hajja rashin lafiya ya sakota gaba sai dai kiran waya, kullum sai ta kirasu video call don duba jikin Walid, duniyar tayi ma Aunty zafi, ta rasa me ke mata dadi taga kamar kowa ya juya mata baya, Mai martaba duk karshen wata yake zuwa duba Walid yayi kwanaki uku ya dawo Nigeria, haka Aunty ke raya dare tana sallah tana kuka tana addu’an Allah ya tashi ɗan ta, duk ta rame saboda damuwa….. Likitan Khaleesat na komawa ta zauna Main parlor bayan wani tunani ya zo mata rai, da ace ba iya aikin likitanci aka dauketa for Khaleesat ba da zata yi karambanin bada shawaran why not kawai a bari Jay da Halysaah su auri juna, to amma me yasa har yanzu babu wanda yayi tunanin hadasu aure a gidan, hadasu aure ne kawai zai basu daman consoling junansu su hakura su yi facing rayuwa kuma haka, ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta shiga bangaren Ajay ta tarar Khaleesat ta shiga bandaki tana alwala, ta zauna parlor tana jiran fitowarta sai ga Mami ta shigo Parlon, da ladabi likitan ta gaisheta Mami ta amsa tace “Kin hada kayan nata kuwa?” Likitan tayi murmushi tace “Ranki shi dade ita bata yarda Abuja za ku ba har yanxu tana ganin kamar Kano za ki kai ta, na hada kayan da safe kan in shiga kitchen in fito har ta mayar cikin wardrobe dinta” Murmushi kawai Mami tayi tace “To zan hadata da Ammin su yi waya kilan zata yarda ta haka, amma ta ci abinci daxu?” Likitan:,: tace “Ta ci ranki shi dade” mami tace “Idan tayi sallah ki taho da ita bangarena” Likitan tace “To ranki shi dade” Juyawa Mami tayi ta fita daga parlon.

