Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 17 Complete Novel

*ASM Bk2017*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

 

………..Kaman yadda ya kwanta da tunaninta haka itama tun bayan data kwanta tay lamo tana ta tunanin fuskarshi mai d’auke da kayataccen murmushin shi sai gizau take mata haka ma kunnuwanta tay ta jin muryarshi na ambaton Zaraah, shikenan ita tasan ta rasa Ya Haisam ji take dama ya dawo suci gaba da rayuwa koda bai Aureta ba, tunanin ko mi yake yanzu ko ya kwanta ta shiga yi can wata zuciyar ta raya mata k’ilan ma yana can tare da Fanan da sauri ta kauda tunanin ta kawo tunanin rungumar da yay mata d’azun irin natsuwa data ji har saida ta d’anyi murmushi tana ta tunane tunanenta a haka itama bacci ya sace ta dama gwaggo ta bata maganin ciwon kai ta sha, gaba d’aya baccin Haisam na ranar da mafarkin Fatuu yayi shi lokacin da ya tashi don tafiya sallar Asuba har saida ya d’an zauna gefen gado na wani lokaci hannunshi dafe da forehead d’inshi saboda wani nauyi da kan yay mashi da k’yar ya yunkura ya tashi don ya shirya, to itama dae Fatun d’aya ne da shi ba komae a cikin baccinta face Mafarkinshi gaba d’aya abunda ya faru ranar saida tay Mafarkinshi haka ta rink’a kuka cikin bacci tana kiran sunanshi ba don ita kadae ke kwana a d’akin ba da tabbas sai an ji ta, bayan ta gama sallar Asuba Al’qurani ta d’auka ta dingi karantawa gwaggo na jiyota duk da ba d’aga murya take ba sosae taji dad’in hakan ko banza tasan zata samu sauk’in zuciyarta, saida gari ya waye sosae sannan tayi Addu’oi harda yar kwallarta kafin ta shafa bayan ta maida Al’quranin ta nufi d’akin gwaggo Lokacin tana kwance saman gado ta shiga ta zauna kan kujera kafin ta kalli gwaggon a sanyaye tace “ina kwana” bata amsa ba saida ta yunkura ta tashi zaune sannan ta amsa Fatun tay shiru ta sunkuyar da kai gwaggo na d’an murmushi tace “Ya kwanan kewan Ya Handsome” da sauri ta kalleta suka had’a ido bata iya ce mata komae ba gwaggon tace “kiyi hakuri Fatuu haka sabo yake gaba d’aya rayuwarma haka take duk wanda muke tare dashi wataran zaki ga dole mu rabu sauk’in shine in Mutum na raye wataran zaka sa ran sake had’uwa dashi balle shi nasan sunan ba’a tare ne amman za’a rink’a ji da ganin juna to tunda haka ne kinga sai ki ma gode ma Allah ba kita kuka ba har kija ma kanki wani matsalan ga jarabawa a gabanki, ki rage damuwan nan koma in ce ki cire shi kin ji?” Kai ta d’aga mata sai kuma ta sadda kan k’asa jin kwalla sun tarar mata gwaggo ta fahimci hakan d’an murmushi tay ta girgiza kai can Fatuu taji tace “ko da wani abu ne?” Da sauri ta d’ago ta kalli gwaggon tana girgiza mata kai alamar a’a, gyad’a kai tay ta fara kokarin komawa ta kwanta Fatun ta mik’e har ta juya sai kuma ta kalli gwaggon tace “mi za’ayi na kalaci” d’ago kai tay tace “zaki islamiyya ne?” Shiru ta d’anyi sai kuma ta girgiza mata kai alamar bazata ba gwaggon tace taje ta kwanta zata tashi ta had’a ta juya idon gwaggo a kanta har ta fice daga d’akin.

 

Wurin k’arfe 10 na safe gaba d’aya sun hallara a dining don yin breakfast harda Saude ta shiga cikin masu aikin girkin gidan guda biyu akayi Breakfast d’in da ita, abun burgewa gaba dayansu sunyi wanka suna sanye da kananun kaya wato English wears wasu riga da wando wasu da skirt dama haka Al’adar gidan take duk weekend irin shigan ake ita kanta mahaifiyar Haisam d’in sanye take da jeans da riga T-shirt ta d’aura bak’in Veil ya rufe iya saman kan yayinda doguwar bak’ar sumarta mai tsananin santsi ke zube a bayanta ta fito a Balarabiyarta ita kuwa Autynsu skirt d’in jeans da riga tasa sai hula data d’aura akan hajiya dae doguwar riga ce a jikinta shima mai gayya mai aikin wato Senator Jeans da t-shirt ne a jikinsa sun kar6eshi sosae kasancewarshi giant gashi sam baida irin mahaukacin tumbin nan don bai wasa da exercise tsaf tsaf dasu gwanin burgewa, yau Mubeen da Mubeena ne sukai Addu’ar bayan an shafa a nutse suka fara ci kowa abunda yake so yake zubawa don Senator ya hana mai aiki tayi tsaye da sunan serving nasu gaba d’aya har su gama, cewa yake suma suje su ci nasu hakan kuma ba k’aramin dad’i yay masu ba don ko ba komae ya nuna suna da daraja sa6anin wasu dake d’aukar yan aiki kaskantattu sam ba dae a gidan Senator ba don akwae wata iya dattijuwa ce yar Daura ita matsayin uwa ma suka dauketa don ko su twins ita ta raine su da ta nuna tana son hakan, yau Senator rike Haisam yay saida yaci Abinci sosae sai kace wani k’aramin yaro anata masu dariya, bayan sun gama Parlor duk suka koma a tsarin gidan duk bayan sallar Asuba ba’a komawa a nan Falo suke had’uwa ayi karatu kowacce rana da littafin da za’a karanta na Addini akwae malami musamman da yake zuwa daga Masallacin gidan Saboda ranakun aiki har yamma suke kai wa a Makaranta saboda suna yin extra lesson duk da acan ma ana koya abunda ya shafi Addini, in suka gama sai aje ai shirin tafiya skul amman weekend in aka gama karatun sai aje a k’ara kwanciya kafin lokacin da za’ai breakfast kowa yayi wanka ya shirya, bayan an gama kuma sai a zauna a Falo ana fira anan kuma duk mai wata matsala sai ya fad’a wasu kuma suyi kallo anan za’a zauna har sai anyi Azahar sai kowa ya tafi yin salla kafin lokacin kuma da za’ai lunch, da yamma gaba d’aya Sportswear suke sawa harda Matan a nufi Sport field inda suke wasanni daga gefen wurin kuma gym ne mai d’auke da kayan motsa jiki kala kala koda wasu basa nan kaman Senator da Aunty dake aiki Asibiti k’a’ida wad’anda ke a gidan sai sunyi hakan don ya zama Al’adan gidan, shima Haisam zama yay Parlon don duk tunanin shi lokacin Fatuu na islamiyya shiyasa bai kira ba ya bari sai lokacin tashi yayi, yau gaba d’aya hiran ta biki ce don a k’agare suke da a fara shagulgulan don shine biki na farko da za’ayi a gidan duk wani shiri tuni an gama shi sai abunda ba’a rasa ba lefe ma iyayen kud’i aka ba Hajiya Maryam don ita yar kasuwa ce sosae k’asashen da take zuwa sarin kaya taje ta had’o ma Fanan d’in har wasu daga cikin ankon da akayi ita ta kawo masu haka Aunty Zee ma ta Katsina yar gidan Fatuu mai shago itama sun bata ta fiddo wasu, ita kanta Fanan saida Haisam ya k’ara mata kud’i ta hado wasu kayan lefen daga India shima musamman lefen yay ma kanshi don kaf kayanshi na Katsina bayar dasu yay duka d’an trolley ne ya dawo dashi Abbas da kanshi ya za6i wad’anda yake so wasu ma basu wuce sawa d’aya zuwa biyu Haisam d’in yay masu ba sauran da suka rage ne ya kira Tk yace yasan yadda zai dasu don yasan kayan sun mashi yawa sai yace ai ana ragewa shine har ya kai ma Amadu wasu, komae a wadace ake yi ga Abokan Haisam sun mashi kara sosae ba kamar Najeeb da Saleem da Abbas duk wani wurin Event da za’ai amfani su suka kamashi haka duk wanda ke son ba Haisam d’in gudunmawa su yake ba don shi ansan ba amsa zaiyi ba.

 

Tun bayan data d’an yi breakfast take k’umshe a d’aki tay lamo kan gado duk kewar Haisam ta isheta gashi har zuciyarta ta fara raya mata kilan ma har ya fara mantawa da ita hakan yasa take zullumin kiranshi tana a haka har aka kira sallar Azahar taje tayo Alwala, bayan ta gama sallar kwance tay kan dardumar tana ta tunane tunanenta a haka bacci ya d’auketa, Su Haisam na dawowa daga Masallaci kowa yay part dinsa yana shiga Parlonshi ya nufi kujera ya zauna ya fara kokarin kiran Amadu don yasan ta isa dawowa yanzu ringing biyu zuwa ukku yay picking cike da girmamawa yana washe baki sai kace Haisam d’in na ganinshi ya gaishe dashi yay mashi an isa Lafiya don lokacin da suka tafi shi yana Makaranta shiyasa bai raka su ba, cikin cool voice d’inshi ya amsa mashi yace mashi Zaraah ta dawo ne Amadun yace mashi tana nan bata ma je Makarantar ba, shiru ya d’an yi sai kuma yace ya kai mata wayar ya amsa da to ya tashi da sauri ya nufi d’akinta yana d’aga labulen ya ganta a takure kan sallaya tana bacci shiga yay ya tsaya kanta yana fad’in “Fatuu, fatuu” a hankali ta bud’e idonta da sukai ja tana kallonshi yace “ya zaki kwanta a k’asa haka ba ga gado ba” duk Haisam na jin abunda yake ce mata, mik’a mata wayar yay yace “Ya Haisam ne” dammm kirjinta ya buga a hankali ta amshi wayar ya juya ya fita maimakon ta kara wayar sai ta rike tana ta kallonta hannunta na d’an rawa,

 

“ZARAAH” taji ya kira sunanta da sauri ta kai wayar kunnanta cikin shaky voice tace “Ya…. Haisam ina wuni” har saida ya lumshe ido jin voice d’inta duk da muryar tayi sanyi da yawa,

 

“Am Ok and u?” tace “lafiya lou”

 

“Kina kuka har yanzu ko?” girgiza kai tay sai kuma cikin karewar murya tace a’a, shiru ya d’anyi sai kuma yace “I will turn it to vid call” har saida ta d’an ji fad’uwar gaba don tasan in ya maida kiran Video call da yaga idonta zai gane ba ta daina kukan ba, batare da 6ata lokaci ba ya maida kiran na gani, sam ta kasa had’a ido dashi sai sussunar da kai take d’an murmushi yay don ya gane dalili Calmly ya furta “ba sai kin 6oye face en ki ba nasan kinci gaba da kukan don ina gani” da sauri ta d’ago ta kalleshi jin abunda yace suka had’a idanu yana kishingide jikin kujera,sai faman yan kyafce kyafcen ido take,

 

“Mi zai sa kukan nan ya k’are ne Zaraah?” Idanunta ne suka ciko da kwalla tace “ka dawo” tana yin Maganar suka zubo sharr, d’an guntun murmushi yay kafin yace “zan dawo” da sauri tace “Yaushe?” Jimm yay sun kafe juna da ido can yace “Wani rana amman sai kin daina kuka in ba haka ba bazan k’ara zuwa Katsina ba ko nazo 9ja” hannu takai tana goge kwallan tace ta bari,

 

“Kin 6ata happy face d’in ki look at ur eyes” d’an tura baki tay bata ce komae ba yay murmushi kafin yace “I think zan sa yawan kukan nan cikin yarjejeniyar glass in baki bari ba zan tada Maganan ne a biya ni kud’in shanu goma ko a bani shanun kinga sai in tafi dasu can in yi kiwo” waro ido tay sai kuma tay yar dariya har hakoranta suka bayyana taji yace “kinga kin fi kyau haka” sai kuma ta d’aure fuskar har baisan lokacin daya sa dariya ba hakanan yanzu komae nata burgeshi yake,

 

“Ya akai kika kwanta a k’asa ko duk kukan ne?” Girgiza mashi kai tay tace “da nagama salla shine bacci ya daukeni a nan” jinjina kai yay sai kuma yace “Abinci fa?” da budar bakinta sai cewa tay “kai Kaci?” Yar dariya yay a ranshi ya ayyana Zaraah rigima a fili kuma sai yace time d’in cin Abincin bai yi ba yace ta bashi amsa tunda ya amsa mata shima tace bata ci ba, umarnin taje ta zubo Abincin ya bata ba tare data katse kiran ba, ba yadda ta iya dole taje ta zubo ta dawo yace taci ya gani kaman zata sa kuka ta fara ci ya zuba mata ido koda tace ta k’oshi bayan ta d’an ci cewa yay bai yarda ba duka zata cinye shi tay kaman zata saka kuka yace bazai damu ba ko tayi dole saida ta cinye shi yace taje ta sha ruwa ta mik’e still yana kan waya taje ta shawo ruwan bayan ta maida plate din, tana niyyar ta koma k’asan ta zauna yace ta hau gado suka ci gaba da wayan yawanci shi ke Magana yana k’ara lallashinta, suna cikin haka landline d’in dake falon ya fara k’ara nan take ya gane Maganar ya fito cin Abinci ne za’ai mashi yace mata zai fita ta d’aga mashi kai ya sake cewa cikin akwatunan nan nata ta duba cikin babban daga k’asa akwae zip in ta bud’e zata ga abu nata ne tay amfani dasu tace to daga haka kiran ya yanke, bin wayan tayi da kallo sai kuma ta mik’e ta fita taje ta mayar ma Amadu tana dawowa ta kai hannu saman wardrobe d’inta ta janyo babban akwatin a hankali don akwae sauran kaya ciki sosae ba duka gwaggo tasa mata a cikin wardrobe ba, da k’yar ta sauke shi k’asa kafin ta zauna ta janyoshi gabanta ta bud’e ji take har ta k’agara taga abunda ke k’asan, fiddo kayan cikin tay sannan ta zuge zip d’in k’asan a nutse nan take idanunta sukai arba da wani k’aton abu kaman littafi mai d’an zanen flowers hannu ta kai ta fiddo shi saida ta juya taga ashe photo Album ne ganin da sauran abubuwa yasa ta ajeshi a gefe ba tare data bud’e ba ta kai hannu ta k’ara ciro wani abun Katon kwalin wayane Samsung Galaxy sabuwa dal har saida ta d’an waro ido alamar mamaki still akwae saura hakan yasa shima ta aje shi ta kai hannu ta ciro wata envelope brown babba a nutse ta bud’eta ta zaro wani had’addan card mai nuni da irin muhimmancin dake gareta a wurinshi tana karantawa tana sakin murmushi har ta gama sannan ta aje shi ta k’ara kai hannu cikin envelope d’in sai gashi ta fiddo da kud’i rafar yan dubu dubu na dari ganin kaman akwae saura ta k’ara kai hannu sai gashi ta k’ara fiddo wata ta dubu d’arin zaro ido tay sosae saboda Al’ajabi kafin ta aje ta duba cikin akwatin taga ba sauran komae sannan ta zuge zip din, gyara zama tay ta d’aukko Album d’in ta bude ta k’ura ma hoton farko ido saidae ta kasa tuna yaushe aka yi shi, a hoton idanuwanta a rufe suke ta d’an d’ukar da kanta k’asa da gani bacci take, kallon hoton dake k’asanshi tay nan take ta tuna inda aka yi shi wato a park din EE ranar da ta hau tread mill sai lokacin ta gane na saman ashe da tana bacci lokacin daya shiga camera yana duba fuskarta har yaga ashe tayi bacci ne da ta kwantar da kanta kan shoulder d’inshi to lokacin yay mata hoton ni kaina mai rubuta labarin ban ankare da ya d’auketa hoton ba kaji aikin miskilin Mutum, zuba ma na k’asan ido tay wanda sukai tare bayan data farka ta dafa shi tayi dariya shi kuma murmushi duk dimples dinsu sun lotsa, murmushi tay ta bud’e gaba hotunan da sukayi ne ranar Salla a Banu Commassie nan ma dae Murmushin tay ta kalli d’ayan side d’in sauran hotunan da tasa Tk ya tura mashi ne lokacin daya kaita yawon salla na gaba kuma wanda tayi dashi ne da babba salla daya d’inko mata shadda daga Abuja, k’ara bud’ewa tay taci gaba da kallon hotunan harda wanda suka yi lokacin dasu Jidderh suka zo da kayan Fulani ita dashi a hankali har ta zo kan Na Ajiwa Dam nan da nan yanayinta ya canja a fili ta furta “Ranar bak’in ciki” daga su sai wadanda tay da Fanan lokacin data gyara mata gashi tayi matuk’ar mamakin ganinsu daga su sai wanda yay masu a falonsu lokacin da sukae rigen cinye Abinci sai na fitar da sukae cin Abinci shekaranjiya a Zoo and Pack lokacin da ta bud’e hoton k’arshe har bata san lokacin data kyalkyace da dariya ba shiri, ba kowanne hoto bane face wanda ya kaita Salon ashe lokacin data amince zata koma ai mata har ya fito daga cikin Mota yana kallonta tana nufar shagon tana waiwayenshi lokacin yay mata shi kanta kaman an kifa mata kwando gata wata yar gajera da ita daidai ta waigo yayi mata shi sosae take ta dariya tunawa da lokacin can ta kwashi kayan ta mik’e ta nufi d’akin gwaggo lokacin tana kwance tana bacci amman saida ta tasheta ganin tana dariya yasa gwaggon tashi ba shiri Fatun ta aje kayan a gefen gado ta fara nuna ma gwaggon, baki bud’e take kallon abubuwan da tsananin mamaki tace a ina ta samo su nan ta fad’i mata yadda sukae da Haisam kasa ma Magana gwaggon tay can tace “shi wai bai gajiya ne duk da uwar hidimar dake gabanshi shine ya baki wannan uwayen kaya haka harda uban kud’i, ni ai da yayi man Maganar waya banyi zaton harda kud’i haka ba ai da sai na gardama mashi gaskia yaji da hidiman gabansa kudi har 200k sannan wayan ma wayasan kudinta da gani itama zata yi kudi sosae ga kuma iyayen Akwatunan kaya suma sai kace lefe” ita dae Fatuu shiru tay tana binta da ido can tace ta kira mata Amadu tace to ta mik’e, bada jimawa ba sai gasu sun dawo tare daman yana d’aki yana danne dannen waya, gaban gadon suka nufa idonshi akan kayan tun kafin ma gwaggo tace wani abu ya kai hannu ya d’auki kwalin wayan da mamaki yace “wannan fa ina aka sameta?” d’an ta6e baki gwaggo tay ta fad’a mashi game dasu, bud’a ido yay yana jinjina kai yace “tabbb wannan hidima haka bata yi yawa ba kinsan fa wayan nan mai tsada ce sosae zatayi dubu dari da wani abu fa in ma bata kai d’ari biyun ba” ba shiri gwaggo tasa hannu ta rufe baki itama fatun gwalo ido tay sai kuma yace “ta gode tunda ai ba rokonshi tay ba” cire hannun gwaggo tay tace “amman gaskiya abun yay yawa Allah” d’an murmushi yay yace “to za’a maida mashi ne, rabonta ne kawae” sai kuma ya juya kan Fatun yace “enye ta Romeo za’a Faso gari gaskia bazan yarda ba ki fara ruke babbar waya ni inata fama da rugwagwa macanza zamuyi” tura mashi baki tay gwaggo data saki baki tana kallonshi tace mashi waye kuma Romeo kallon Fatuu yay yana dariya ta d’an yamutsa fuska yace ma gwaggo ba kowa wani d’an kwallo ne d’an k’asan waje mai kama da Ya Haisam d’in Fatuu bata san lokacin da tasa dariya ba gwaggon ta ta6e baki, zama yay suka fara kallon hotunan tare da gwaggo sosae suka yaba wani wurin suyi dariya ba kaman na wurin salon d’in suma sunyi dariya sosae bayan sun gama Amadu ya kunna wayar ya fara nunnuna mata yadda zata yi amfani da ita.

 

Sai dare bayan sallar Isha sai gashi ya kirata ba laifi ta saki jiki tana kwance kan gado bayan tayi mashi godiya suka shiga yin hira sosae ya saki baki hakan yasa itama ta washe sai gata harda su dariya can yace mata ta kwanta dare yayi kuma ta tabbatar taje islamiyya gobe kar ta zauna yin kuka tana yar dariya tace mashi toh daga haka sukai sallama, gallery d’in wayar ta shiga dayake duk hotunan yasa mata a ciki ta fara kallo yawanci duk nashi take kalla cike da shauki wani lokacin har rungume wayar take ko ta kai baki ta manna ma hoton shi kiss sai kuma tasa hannu ta rufe fuskarta alamar kunya daga baya bacci yay awon gaba da ita. Washe gari lahadi danginsu Haisam yan kasar Ethiopia suka iso harda dangin kakansu Larabawa da d’an yawansu suka zo yawancinsu duk basu ta6a zuwa Nigeria ba sai yanzu, Jama’a kuzo Kuga ruwan kyau gasu duk yan gayu ne dangin sarauta ko iya su ka kalla a bikin Haisam dole zaka k’ayatu Farar fata da uban gashi kawae ka ke gani Malam sai faman farincikin ganin juna ake baka jin komae sai Larabci da yarensu na Ethiopia dake tashi, kakanninsu yan tsofaffi kyam kyam dasu basu tsufa ba sosae suka ragwa6e irin yadda fararen fata ke yi in suka tsufa , Washe gari Monday sai kuma ga danginsu Hajiya daga Daura wasu kuma daga Katsina nan da nan gida ya d’au haramar fara hidiman biki a ranar kuma sai ga First Lady ta Jihar Nasarawa wato twin sister d’in Mahaifiyar Haisam Her Excellency Hajiya Zainab ita da yaranta don ta kasa hakuri tana son ganin iyayenta, wohoho sha’anin manya daban yake nan fa gida ya kara kacamewa securities ta ko ina Jama’a da k’yar nike lalla6awa ina rubuto maku labari kar in ci na jaki, in ka ganta kaman an tsaga kara an karya ita da mahaifiyarsu Haisam abu d’aya ne kesa ana ganesu shima sai Mutum ya lura shine kwayar idonsu ta mahaifiyarsu Haisam bak’in yafi cijawa,a cikin yaranta da suka zo harda babban d’anta sa’an Haisam wato Sameer sak kamaninsu d’aya da Haisam har yanayin jikin kai kace suma twins d’inne don yafi kama dashi ma akan Nameer saidae shi Sameer bak’i ne ko in ce chocolate wato kala mai tsada sannan a yanayin sumarsu ma akwae bambanci ta Haisam tudu gareta shi kuma tashi ta d’an kwanta har wuyanshi sannan ko a halayya ma sun bambanta don sam Sameer bai dariya cikin sauk’i ba k’aramin abu ne ke saka shi dariya ba unlike Haisam shi in yaso yana yi kuma yana murmushi amman Sameer ko Murmushin ma sai an kai ruwa rana kafin ya d’anyi, suna matuk’ar kaunar junansu shida Haisam ko karatu ma tare sukae a Kasar waje amman ba abu d’aya suka karanta ba suna ganin juna suka rungume juna Haisam na fad’in “U’r welcome My Man” cikin muryarshi mai cike da izza ya furta “Thanks Bro” kai kace dole aka masa wai a haka ma don Haisam ne tabd’i da gani dai ba’a rasa girman kai tattare da shi uhm ba dae ruwana………..

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button