Hausa novels

Halysaah Page 53 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 53…Jay na zaune dakinsa wajen karfe tara na dare yana rike da mug din coffee da yake ta stirring for almost 5 minutes now ya kasa sha, ya daga kai jin an bude kofar dakin, Ajay ne ya shigo ya nufi inda Laptop dinsa yake, shi dai Jay kawai bin sa yayi da ido har ya kunna laptop din ya duka yana dube dube a cikinsa, after almost 2 minute ba tare da Ajay ya kallesa ba yace “Resend me those files u sent yesterday via Email” Jay bai ce masa komai ba, hakan yasa Ajay ya juya yana kallonsa, mikewa yayi ya nufesa, ya cire masa head warmer din kansa ya saka a nasa kan yace “Hey is everything Okay? Me yasa baka fito ka ci abinci ba?” Jay ya mike ya fixge Head warmer dinsa sannan ya koma ya zauna yace “Kai dai ba ka ci ba, cire min Jacket dina Ajay, I can’t remember dashing you the Jacket….” Ajay na gyara Jacket din jikinsa ya koma ya ci gaba da abinda yake yi a laptop din Jay, after a while Jay ya ajiye Mug din hannunsa, speaking slowly yace “I spoke to Safiyyah not long ago” Ajay ya kallesa yace “Wacece haka?” Jay yace “My Housemate’s friend” Banza Ajay yayi masa ya ci gaba da duba abinda yake yi a laptop, calmly Jay yace “And she….” Ajay ya dakatar da shi sounding pissed off yace “Plss Jay, i am not interested, do not provoke me this night, banda file da nake nema a laptop dinka baza ma ka gan ni a dakin ka da daddaren nan ba” Jay ya mike yace “Whether you are interested or not, Safiyyah ta gaya min gayen ya saki Halysaah” Ajay ya juya ya kalli Jay babu ko kiftawa, after some seconds ya maida idonsa kan laptop din gabansa sai dai bai ci gaba da operating laptop din ba, Jay ya karasa kusa da window din dakinsa ya bude drape din ya rungume hannunsa yana kallon tiny snow din dake zuba kasa, Ajay yace “What did you expect? Were you expecting less? He’s satiated his craving, and that is all that he is after, yayi satisfying Lust dinsa” Yana kai wa nan ya rufe Laptop din kawai ya nufi kofa ya fice daga dakin, shi dai Jay da ido ya bi sa kawai, can ya sauke wani ajiyar zuciya ya karasa ya rufe kofarsa da Ajay ya bari a bude. Khaleesat na zaune gaban Coal pot wajen karfe sha biyun rana tana ta fifita gawayin da ta hura zata dora girkin rana at the same time tana gyara waken farantin dake cinyanta, Ummanta ce zata dora girkin don Aunty Farida ta fita kasuwa shi ne ta amshi girkin tace zata yi, shinkafa da wake da mai da yaji ne za su yi da rana, babu kowa a gidan sai ita da Umma don su Mama Zubaida da Mama Shatu sun tafi gidan biki ko girkin siyarwa basu yi ba ranan, Umma ma gidan Nenne take shirin zata je ta kai mata kubewan da ta tambayeta ranan friday, ɗaga kai Khaleesat tayi jin sallaman Safiyyah a compound din su, ta dinga kallonta bata ko kiftawa don bata ce mata zata dawo yau ba, Safiyyah tayi murmushi ta karasa har inda take sannan ta dau kujeran tsugunno da ta gani a tsakar gidan ta zauna tana kallon Khaleesat tace “Sannu da aiki” Khaleesat ta ɗan bude ido tana murmushi tace “You didn’t tell me you were coming today Safiyyah” Safiyyah tace “Eh nima ban zata zan zo yau ba, dama ranan Monday ko Tuesday nace maki zan dawo ai” Umma ce ta fito daga dakinta, Safiyyah ta gaisheta da ladabi, Umma ta amsa da fara’a tace “Ya su maman ku?” Safiyyah tace “Sun ce in gaishe ku Umma” Umma tace “Allah sarki, to ina amsawa, bari in je gidan Nenne in dawo yanxu” Safiyyah tace “To sai kin dawo Umma” A haka Umma ta fita daga gidan, Khaleesat ta dora ruwan girkin ta ajiye waken da ta gyara sannan suka shiga dakin Umma da Safiyyah, Safiyyah na kallonta tace “Don Allah ki daure ki dinga cin abinci Khaleesat, kin ga yanda kika rame kamar ba ke ba kuwa” Murmushi kawai Khaleesat tayi tace “To ni dama kiba gareni Sophie?” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya tace “Even though, yanxu raman tayi yawa wallahi, ji fa sai idanuwa da dogon hanci kawai” Dariya kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah na kallonta tace “Ba dadewa zan yi yau ba Khaleesat, aikoni aka yi wajen ki” Da mamaki Khaleesat ta dinga kallonta, sai kuma tace “Wajena kuma? Wa ya aiko ki” a hankali Safiyyah tace “Ur Housemate” Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta dinga kallon Safiyyah babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace “Sai dai kiyi hakuri, ni dai na gaya masa abinda ya faru, And….” Sai kuma Safiyyah tayi shiru, Ita dai Khaleesat kallonta kawai take don ta kasa cewa komai tana jin hawaye na taruwa gradually a idonta, a hankali Safiyyah tace “He sent me money for ur flight ticket back to America, and you tuition fee for this semester, ya ce zai samar maki wani apartment din for the one year that is remaining for us….” Hawayen dake makale idon Khaleesat ya zubo, ta kasa ce ma Safiyyah komai, bata san sanda ta fashe da kuka ba sosai, ita dai Safiyyah tayi shiru tana kallonta cause she wasn’t expecting less, sai da Khaleesat tayi kukanta me isarta sannan tana girgiza kai muryarta na rawa tace “I don’t think za a bari in koma in ci gaba da karatu Sophie” Safiyyah tace “Ban gane ba? Saboda me baza a bar ki ba?” Khaleesat na goge idonta da kyar tace “Saboda Abdul ma da aka bari ya kai ni karatu babu yanda za mu yi ne hakan ta faru, we had no choice then, dalilin haka har sai da Ummata ta samu hawan jini, kin ga yanxu kuwa ai babu wani hujjan da zai sa a sake barin wani ya ci gaba da sponsoring dina a wata kasar” Safiyyah tace “I don’t understand Khaleesat, yanxu me kike nufi? So kike kiyi asaran shekarun da kika yi a makarantar kenan?” Hawaye na zuba idon Khaleesat ta girgiza mata kai tace “A’a Sophie, but iyayena za su ji tsoron sake yarda wani ya dau dawainiyata try to understand me” Safiyyah tace “Zan jira har Umma ta dawo daga gidan Nenne in mata magana, ke kam bani da sauran magana dake, cause haushi zaki ci gaba da bani idan na biyeki, banda haka ta yaya ga dama ta samu amma kina neman misusing opportunity din, did you even know what you are saying?shekara daya kacal fa ya rage maki Khaleesat? Dropout kike son ki zama ko me? Ai wani abun mutum ba shi yake bargaining ma kansa hakan ba, you never bargained for all this Khaleesat, situation ne kawai, kina tunanin har a tashi duniya akwai ranan da Yaya Jawwad zai bude baki yace ai ya dau nauyinki a makaranta? Kina ganin Jawwad yayi kama da mutumin da zai maki gori wataran? Ai wallahi daga shi har Cousin dinsa sun girmi hakan, they are too classy for that, Kin zata kowa mahaukaci ne mara aikin yi kamar Abdul? Haba wallahi har kin bata min rai, ban taɓa tunanin zaki nemi kiyi turning down din offer dinsa ba, shi fa taimako kawai yayi saboda yana da halin yin hakan, duba da kin kusa gamawa kuma yasan duk abinda ya sameki, amma sbda rashin tunani irin naki kina neman gwalesa, i was thinking zaman da kika yi da Abdul zai sa ki ɗan canza wasu tunaninki marasu ma’ana, ko kuma in ce Childish tunani” Ita dai Khaleesat hawaye kawai take sosai ta kasa ce ma Safiyyah komai, tasan duk bayanin da zata mata bazata taɓa fahimtar ta ba, Safiyyah ta ciro wayarta ta fara dannawa bata sake ce ma Khaleesat komai ba don da gaske ta ɓata mata rai, after a while Khaleesat ta mike zata je ta wanke wake ta zuba a ruwan da to dora kan wuta, bayan ta gama wanke waken ta zuba ta rufe tukunyar tayi tagumi tana zaune gaban Coal pot din, a haka Umma ta shigo gidan ta sameta, Khaleesat ta sauke hannunta daga tagumin da tayi tana kallon Umma da ta nufota, tace “Umma kin dawo” Umma tace “Na dawo, ina Safiyyar?” Khaleesat tace “Tana ciki” Umma tace “Shi ne kika bar ta ita kadai” Khaleesat tace “Yanxu na fito in zuba wake ne” Aunty Farida ce ta shigo gidan da abubuwan da ta siyo a kasuwa, Umma tayi welcoming dinta sannan ta karasa dakinta ta shiga ciki da sallama, Safiyyah ta amsa tana mata sannu da zuwa, Umma ta cire Nikab da hijab dinta ta linke tace “Bata baki ko ruwa ba?” Safiyyah tayi murmushi tace “Umma ni ke nake jira ma tafiya zan yi” Umma ta zauna tana kallonta tace “To gani Safiyyah, lafiya dai ko?” Safiyyah tace “Lafiya lau Umma” Kafin Safiyyah ta ce komai Aunty Farida ta shigo dakin, Safiyyah ta gaisheta tana murmushi, Aunty Farida ta ajiye kayan hannunta tana amsa gaisuwan Safiyyah da fara’a, Umma dai kallon Safiyyah take tana jiran jin abinda zata ce, Babu bata lokaci Safiyyah ta fara yi ma Umma bayanin duk yanda suka yi da Housemate din Khaleesat, ita dai Aunty Farida na tsaye ita ma tana sauraron bayanin Safiyyah, Umma ta ɗan yi murmushi bayan Safiyyah tayi shiru tace “Allah sarki, mun gode sosai da kulawan sa, amma dai ki maida masa kudinsa Safiyyah, don ko babanta ma bana jin zai yarda, Abdul ma da ya kai ta karatun ba mu da yanda muka iya ne Safiyyah, Allah ya amfana abinda ta samu” Safiyyah was speechless, Aunty Farida ta dinga kallon Umma jin abinda tace, can tace “Allah ya amfana abinda aka samu kuma Umma? Shikenan fa tayi asaran karatun gaba daya idan bata karasa ba, kamar ka fara gini ne fa ya ruguje har kasa ya rage Foundation, ai kin ga kuwa baza kace Allah amfana abinda aka samu ba” Umma ta kalli Aunty Farida tace “Farida kin fi kowa sanin ban taɓa goyon bayan fitar Khaleesat karatu waje ba tun asali, daga ni har mahaifinta babu yanda muka iya ne, don haka Khaleesat bazata koma Amurka da sunan karasa karatu ba, ashe ma bamu dau darasin abinda ya faru a baya ba kenan” Aunty Farida bata sake ce ma Umma komai ba ta hau fiddo abubuwan da ta siyo a kasuwa, Ita ma Safiyyah tayi shiru don bata ma san me zata ce ba, Umma na kallon Safiyyah tace “Ki masa godiya kawai ki mayar masa da kudinsa Safiyyah, Allah ya dubi niyyarsa na alkhairi ya saka masa, ba wai ni kadai ba, hatta Mahaifinta ma ba yarda zai yi ba Safiyyah, cutar da ita da muka yi da farko ma da muna da wani dubaran da baza ayi haka ba, kin ga in mu iyayen arziki ne ai baza mu yarda ayi na biyu ba” Aunty Farida ta mike tace “To shi Umma ce maki yayi da wata manufa zai biya mata kudin karatun har kike tunanin za ayi na biyu? Shi fa Abdul duk abinda yayi yana da manufar yin hakan duk mun sani, ba haka kawai ya dauketa ya kai ta karatu ba….” Umma ta dakatar da ita tace “Ban ce shi wannan bawan Allahn yana da wata manufa ba amma dai kam Khaleesat bazata koma Amurka ba Farida” Aunty Farida bata sake tanka Umma ba ta fitar da albasan da ta siyo zata je ta shanya a bakin kofa, Safiyyah ta sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali tace “Toh shikenan Umma, ni zan koma gida, dama abinda ya kawo ni kenan” Umma tace “To ki gaida mutanen gidan Safiyyah mun gode kwarai, shi ma ki yi masa godiya don Allah” Safiyyah tace “To Umma” Jiki a sanyaye ta mike ta fita daga dakin, Aunty Farida ta dau hijab dinta da ta rataye a igiya tayi ma Safiyyah alamar su je waje, ita dai Khaleesat na zaune inda take bata tashi ba don duk taji conversation din Safiyyah da Ummanta, Aunty Farida na fita kofar gida da Safiyyah tace “Safiyyah kar ki yarda ki gaya masa abinda Umma ta ce, ki bari Babanta in ya dawo anjima zan samesa in yi masa magana” Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace “To Aunty, don Allah ki yi convincing dinsa shi ma, It will be very sad idan aka ce bata karasa karatun nan ba, shekara daya fa kawai ya rage mana” Aunty Farida tace “In sha Allah zan yi bakin kokarina, kuma Khaleesat zata ci gaba da karatun ta” Safiyyah tace “To Aunty, gobe da safe zan kira ki sai inji yanda ku ka yi da Baba” Aunty Farida tace “To babu damuwa, ki gaida gida” a haka suka rabu Aunty Farida ta juya ta koma cikin gida… Khaleesat ta gama girkin da take bayan ta kashe gawayin tayi alwala ta shiga dakin Ummanta, tana idar da sallah ta kwanta, gaba daya taji damuwarta ya dawo sabo fil maganar Housemate dinta da Safiyyah ta kawo mata, Umma na kallonta tace “Baza ki ci abincin bane yanxu?” Khaleesat ta girgiza mata kai tace “Sai anjima” Ita dai Aunty Farida linke kayan su Islam take don tun bayan tafiyar Safiyyah bata ce ma Umma komai kan maganar da Safiyyah ta kawo ba sanin Umma bazata taɓa fahimta ba. Bayan Magrib Aunty Farida ta samu Malam Ali yana zaune kofar dakinsa, bayan sun gaisa yace “Amma ba Lagos kika zo gaya min zaki koma ba Farida?” Murmushi kawai Aunty Farida tayi don in akwai abinda ya tsana zamanta Lagos yayi fadan har ya gaji, ta kauda tambayar da yake mata tace “Magana na zo mu yi kan Khaleesat” Yayi shiru kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace “To ina sauraron ki” Cikin nutsuwa Aunty Farida ta sanar masa batun da Safiyyah ta zo da shi daxu da rana, Malam Ali ya girgiza kai yace “Ashe ban daddara ba kenan Farida, na yi tunanin duk mun dau darasi kan abinda ya faru wanda duk nafi kowa laifi a ciki….” Aunty Farida ta kwantar da murya tace “Ae wancan issue din da wannan ba daya bane Malam, shi fa Abdul da isa da gadara ya turata karatu Amurka kuma babu yanda muka iya haka duk muka sallama masa domin zaman lafiyanmu da naka, Abdul da manufarsa na tura ta karatu, shi ko wannan bawan Allahn babu wata manufa a ransa, saboda Allah zai biya mata ta karasa karatun kar tayi asaran shekarun da tayi, iya shekara daya fa ya rage mata Malam, ka san muhimmancin karatun nan balle ka kushe komawarta America ta karasa, in kowa zai kalubalanci haka ai banda kai Malam, don Allah ka duba wannan lamari, kuma shi wannan bawan Allahn da ya ce zai dau nauyin shekara dayan da ya rage mata su ne fa suka dau maka lauya har aka wanke ka a kotu aka kashe maganar bashin ka da Baban Abdul….” Malam Ali yayi murmushi yace “Ai nayi appreciating hakan da suka min kuma kullum ina saka su a addu’ata, amma babu zancen komawar Jiddah America karatu Farida, kiyi hakuri a bar batun nan gaba dayanta, we shouldn’t be a bad parent for the second time saboda son abun duniya, tayi hakuri in Allah ya hore min sai in biya mata tayi Jamb ta nemi ko BUK ko Northwest, duka duka shekarunta nawa suke? Ai lokaci bai kure mata na karatu ba Farida, kuma ko aro ne zan nema in biya mata in sha Allah, don haka bana son a sake tada zancen ci gaba da karatun ta a America” Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, after a while tace “To shikenan, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi” Yace “Ameen” Mikewa tayi ta bar wajen rai babu dadi. Washegari wajen karfe tara Aunty Farida ta gama shirin da take, Umma dake kallonta tace “Ina za ki ne?” Aunty Farida na dora Nikab dinta kan Hijabin jikinta tace “Ba nace maki zan je gidan Abida ba shekaranjiya” Umma tace “Shi ne zaki mata sammako?” Aunty Farida tace “Jiya tace min bata da lafiya ne, kuma ina son in dawo da wuri in wanke kai na” Umma ta tabe baki tace “To sai kin dawo” Ita dai Khaleesat juya kokon gabanta take a hankali tana sha ga dumamen tuwo shi ma a gabanta, da kyar take shan kokon, dumamen kuwa ta kasa ci, dama jiya da daddare ma bata wani ci tuwon ba, Aunty Farida tayi ma Umma sallama ta fita daga dakin. Nenne na gyara daurin dankwalinta tayi kasa da murya tace “To ke banda abun ki ai Zahra’u Jahila ce Parida, matar da har yau bata da wayewa kanta a murfi yake kamar matar kauye, ita ta wani san maki muhimmancin karatu kina ganin mata haka kara zube, gashi sai yanda kazaman kishiyoyi suka yi da ita sun mayar da ita Bora? Ai bari ki ji Parida, Zahra’u a yanxu dai ita daga tuwo sai bautan Allah kawai ta saka a gaba, babu ruwanta da wani ci gaba na duniya ko kyale kyalin duniya, ta riga ta amince ta kare rayuwar ta a haka in dai zata ci tuwo tayi bautar Allah, shi yasa kullum zaki ganta rike da carbi a kuturin dakinta da ko Ceiling din arziki babu, ni bana ma jin Zahra’u na yi ma Ali addu’an Allah ya dawo masa da arzikinsa don in tayi hakan gani zata yi kamar ta butulce ma Allah, duk tunaninta fa haka Allah ya so ganinsu cikin baƙin talauci, gani zata yi in tayi ta ma Allah magiyan ya yaye masu talauci kamar butulci tayi bata gode da ni’imarsa ba tunda tana samun tuwo ta ci, to irin tunanin yayarki kenan Parida, in ba haka ba ta yaya zaki dinga yi ma er cikinki bakin cikin karasa karatu ta taimake ku a rayuwa ta cire ku daga kangin talauci? shikenan kuma don kai jahili ne sai ka rasa sanin abinda ya kamata? Har wani kwambo fa take da jahilcin ta da rashin wayewa, ki bar ni da su kawai zan yi maganinsu daga Alin har Zahra’un, da can uban me yasa suka bari aka kai ta Amurkan in har da tsoron Allah a lamarinsu daga ita har Alin? Wato sai yanxu suka zama iyayen kirki masu tsoron Allah ko? To zan yi maganinsu gaba daya, in dai karatu ne kamar Khaleesah taje Amurka ta karasa in har ina numfashi, Allah ya kai mu anjima da yamma, Alin ai zai dawo daga zaman kashe wandon da yake yi a kasuwa, zan je har gidan in samesa inji ko na tauye masa karatunsa duk da talauci na, in de ni na amince taje to ko wani ɗan iska ma kar ya amince” Nenne na kai wa nan ta mike ta jawo kofar dakinta ta kulle da kwado, sannan ta dau mayafinta sabo dake rataye saman igiya ta yafa, ta dau handbag dinta ta saka makullin kofar a ciki, ta zura takalmanta ta nufi kofar fita daga gidan tana taku dai dai don sabuwar atamfa ce a jikinta, Aunty Farida ta bi ta da kallon mamaki tace “Wai fita zaki yi ne Nenne?” Ba tare da Nenne ta juyo ba tace “To me zan maki, anguwa har uku zan je yau da kika gan ni, bazan zauna a banza ki bata min lokaci ba, in ba gulma ba ganinki nake yi a gidana, ni dai in kin gama zaman kin fito ki ja min kyauren gidana kar almajirai su shiga su min sata” Daga haka Nenne ta fice daga gidan, murmushi Aunty Farida tayi ta mike ta nannade mata tabarmanta ta ajiye sannan ta daura nikab dinta, bin bayanta tayi da sauri don jadadda mata kar tace ita ta zo ta gaya mata maganar don tasan tsaf sai yayarta ta kullace ta._Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via 0902 469 2720_*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button