Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 25 Complete Novel

 

🐅MATAR DAMISA🐅
(The Wife Of  Tiger)

Written and story by
Asma’u Muhammad Auwal

(ASMEETAH NOVEL✍️)

WhatsApp me 09065443871

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

 

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ——->69 & 70 <——-

____________________________
Ɗaga hannu tayi sama tana roƙon Allah “ya Allah ka temake ni, ka bani nasara akan ceton Junaid daga kogon hallaka…”
har ta gama Junaid bai motsa ba, ta tashi ta nufi gaban mirror, gabanta ne ya yi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ta tsaya cak ta zazzaro manya-manyan idanuwan ta waje ganin anyi rubutu a jikin mirror da jini, “Innalillahi wa inna’ilaihi raju’un..” abunda ta furta kenam, jikin ta na kakkarwa ta soma karanta rubutun da akayi da jini a jikin madubi…

{{ “kun munafurce ni Ɓingel ke da mahaifiyar ki, kun toshe mun kafar da zan sanya ku a idanuwa na balle nasan abubuwan da suke faruwa daga ɓangarenku, hakan yasa na ɗauki mummunan mataki akan shi wanda kike so ki rasa rayuwar ki akansa, kafin ki mutu ya rigaki mutuwa Ɓingel, daki rasa rayuwarki gwara shi ya rasa tasa rayuwar, kiyi hakuri na kashe Junaid har lahira, babu ta yanda zan ganki shiyasa nayi miki wannan rubutun BISSALAM” }}

tsabar firgita da tsoro Ayush har faɗuwa tayi ƙasi ƙafafunta bazasu iya ɗaukar ta ba, jiki na rawa tayi kan Junaid wanda yake kwance kan gado ƙafafunsa rabi suna ƙasi, jijjigar sa ta farayi tana ƙiran sunansa cikin yanayin kuka “wayyo dan Allah Junaid ka tashi, na shiga ukuna na lalace Junaidd! Junaidd!! Junaid ka tashi mana….” ta fashe da matsanancin kuka tana bubbugar ƙirjinsa, ta tashi da gudu ta nufi toilet ta fito hannun ta ɗauke da ruwa ta soma kwara masa amma Junaid ko motsi babu ido a rufe, tsabar kiɗimewa daga ita sai towel a jikinta haka ta jawo Junaid kanta suka faɗo ƙasin gado tare tana rungume dashi, ihu take na fitar hankali tana ƙara ƙanƙame shi a jikinta,
idonta sunyi jawur hatta fuskar ta shima ya yi jawur abinka da farar mace,
kanta ne ya soma juyawa ta soma kwashewa da dariya daga dariya ta koma kuka haka ta rinƙa haɗawa dariya da kuka, still tana ƙanƙame da Junaid!
Inta kwashe da dariya lokaci guda kuma sai dariyar ta juye ihu ta soma ihu kamar ranta zai fitaa,
Da haka har ta fara shiɗewa, ta soma magana ciki -ciki “Yaya Junaid bazaka mutu ka barni ba, bazan rayu ba…” lokaci guda kuma ta yi wani irin ƙaara na gaske har sai da madubin ɗakin ya dagargaje tsabar ƙarfin ƙarar ihun data yi, shine last ihun ta itama wuyan ta ya karye ta kwantar da kanta saman ƙirjin Junaid, numfashi ya tsaya cakk,
ihun nan har sai da ya daki dodon kunnen maigadi tsabar ƙarfin ƙaarar,
shi maigadin da yake can bakin gate mai shegen nisa.
Jin wannan ihun mai razanarwa yasa mai gadi tsorita jikinsa ne ya hau ɓari yana faɗin “innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, shikenam kwanan mu ya ƙare yau kam Junaidu ya koma Damusa ya kashe ƴar mutane, nasan yanzu kaina zai dawo bari na hau kan hanya na bar gidan nan tin kafin ya fito gare ni.
Da gudu Baba mai gadi ya buɗe gate ya fice a gidan…

(Shin mutuwa tayi ne ko suma Allahu A’alamu..).

******

Besty ce take kwance saman gadon Laila sai danna phone take tana watsa chiwgun a baki sai kara take tayi da su tana taunasu cikin salo, can saiga Laila ta fito daga toilet da ɗaurin
towel a ƙirjinta tana faɗin “my Besty yakamata kizo ki watsa ruwan musulunci a jikin ki koh, gashi time to pray sai ƙiraye-ƙirayen sallar la’asar ake.
Besty kuwa idon ta nakan wayar hannun ta tace ” kiyi sallar ki mana idan na tashi zanyi ai.” Laila ce ta taho gaban Besty tana faɗin “ke ki tashi nace kije kiyi wanka bazan zauna dake haka duk jikin ki ƙazanta” ta ƙarasa maganar tana fizge wayar hannun ta,
tashi tayi Besty tana ɗura ashar tace “kutumar bura uba, nice baza ki iya zama dani ba a haka? saboda nazo gidan ku ne yasa kike mun wulaƙanci son ranki, shikenam zan bar gidan ku yanzu ai nima muna da gidan, kuma ke bazaki nuna mun musulunci ba,” ta ƙarasa maganar tare da tashi ta fizgi wayar ta, ta jawo kayan ta zata saka suka ji bugan ƙofar ɗaki, a tsorace Laila tace “waye ne”
jin muryar Yayanta yana faɗin “Auta ki buɗe ƙofar mana” gaban ta ne yayi wani irin bugawa ta kalli Bestin ta murya ciki-ciki take cewa “ina kinga har Yayana ya dawo daga hospital shiyasa nake ta binki ki samu kiyi wankan kar yazo ya ganki a haka, gashi yanzu, ai saiki samu ki shige cikin toilet ɗin..”
wani irin harara Besty ta wurga wa Laila ta ja tsuka sannan ta shige toilet, itama Laila binta da kallo tayi kafin tayi ƙwafa ta nufi yanda wardrobe ɗinta yake ta ciro wata doguwar riga na material da gyalen ta mai ɗigon black and white ta ɗora su akan gado wannan ta fitar su ne wanda Besty zata saka..
itama ta ciro riga da skit blue da hular sa tayi saurin sanyasu, taji Yayanta yana faɗin “ke shanyar da kika yi fa ya bushe, wai mekike yi haka ne?”
“Yaya kayana dai nake sakawa nayi wanka ne…”
shuru yayi bai ce komai ba, sai da ta gama shirya wa tsab tukun tazo ta buɗe ƙofar da murmushi akan fuskar ta tace “your welcome my dearest bros” ɗan hararar ta yayi ta gefen ido yana faɗin “ni kike wa jan aji ko?”
taɓe baki tayi sannan tace “sorry my Bros….”
bakin gado ya samu ya zauna bakin sa cike da tambayoyi sai kalle-kalle yake ta yi a ɗakin kamar baƙonsa…

“waɗannan kayan waye…”
ya yi tambayar yana kallon Laila..

cikin ƙinƙina tace “Yaya! Aunty Maimoon ce tazo tinda rana, har bacci ya ɗauke mu yanzu tana wanka ne…”

Gabansa ne ya yanke jin an ambaci Maimoon, jinjina kai ya yi sannan yace “okay..”

tashi yayi zai fita Laila tace “Yaya meyasa ka tashi kuma?”
Murmushi ya yi sannan yace “bakomai inaso zanje nima nayi wanka yanzu dawowa ta, kinsan idan na dawo inhar banzo duba lafiyar ki ba hankalina baya kwanciya..”

Murmusawa tayi tace “proud of you my Bros, nagode da irin kulawar da kake nuna mun..”

Ficewa ya yi daga cikin ɗakin
ita kuwa Laila murmushi tayi tasan saboda Maimoon yabar ɗakin….

zama tayi a bakin gado tayi tagumi wasu siraran hawaye ne suke gangaro mata daga gani kasan tana cikin damuwa.
dai den lokacin da Maimoon ta fito daga toilet ɗaure da towel a ƙirjin ta, ganin Laila a cikin wani hali yasa tazo itama ta zauna kusa da ita ta zauna jikinta duk a mace tace “Laila what’s wrong with you? kina kuka akan meye?…”

Laila ta juyo tana kallon Maimoon tace “ke ma ai kuka kika yi, ganan eyes ɗinki sun canza launin jaa, nasan ke kukan ki akan Doctor Hasheem ne wato Yayana.”
Jinjina kai Maimoon tayi sannan tace “haka ne a duk lokacin dana ci karo da Yaya Hasheem gabana faɗuwa yake tsabar tsananin sonsa da nake yi, muna son junan mu amma narasa meyasa Yaya Hasheem lokaci guda ya canza mun,
ga halin da muke ciki ni da ke, abun kunya ne ace ni ina lesbian da ƙanwar mijin da nake sa ran zan Aura, tirr da wannan rayuwar kuma hakan ma a iya junan mu muke wannan ƙazantar, ni na lura Laila a duk sanda muka yi wannan abun akwai rashin jituwar da yake shiga tsakanin mu, dole sai munyi faɗa, shin meya jawo hakan?..”

Ajiyar zuciya Laila ta ja sannan tace “nima ban saniba Aunty Maimoon, a koda yaushe ina kuka akan wannan al’amarin, sai dai mu cigaba da addu’a domin muna cikin babban masifa ina tsoron kar wata rana a kama mu..”

gaba ɗayan su kuka suke yi,
“Aunty Maimoon Oga Junaid ciwon sonsa zai hallaka ni wallahi, amma
shi baya sona..”

Maimoon ta juyo tana kallon Laila tace “Laila ke ma kin ɗora ranki akan Junaid wanda shi ba mace bane a gabansa, mutumin da bashi da lafiya, ba cikakken mutum bane, shin ina zaki kai shi?..”

Laila hura iskar bakin ta tayi tana faɗin “insha Allah Oga Junaid shine mijina kuma uban ƴa ƴana,..”

Murmushi Maimoon tayi sannan tace “Allah ya temaka ya bada sa’a..” ta tashi tana ƙoƙarin zura rigar da Laila ta fitar mata..

ita kuma Laila kallon Maimoon take tana maganar zuci “ina tausaya miki Maimoon domin nasan duk lokacin da kika ji Yaya Hasheem ya samu new budurwa haƙiƙa zuciyar ki bugawa zata yi, Yaya Hasheem yanzu ba kece a gabansa ba, amma shima ya yi rashin adalci sai da kuka shaƙu soyayyarku tayi ƙarko tukun zai bar ki ya koma gurin wata wai Ayush…”
tsuka taja ta tashi ta saka hijabi tare da shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah…

jin yanda Laila tayi tsuka yasa Maimoon yin murmushi ta girgiza kai a tunanin ta tsukar da Laila tayi da ita take…..

*****

Zaune yake a bakin gado ya yi tagumi yana magana ciki-ciki “kiyi hakuri Maimoon nasan nayi miki babban laifi, kece mace ta farko dana so a rayuwata kuma nake da burin Aura amma tinda naci karo da Ayush komai na jefar shi gefe, nasan kina matuƙar ƙauna ta fiye da yanda nake tunani, amma yanzu na canza Ayush nake gani a gabana ita ce ta maye gurbinki Maimoon duk da kema har yanzu kina raina..”
haka ya cigaba da maganganun sa shi kaɗai.

*WACECE MAIMOON*

wata yarinya ce ƴar shekara 21 mai ilimin gaske na boko dana arabic, sau uku Maimoon tana sauƙe Alqur’ani mai girma, hadisai ne da Ahlari a kwakwalwar ta,
Itace ta ɗaya a gasar karatun qur’an a cikin ɗalibai na ƙasashe..

asalin iyayen Maimoon larabawan makkah ne, suka baro makka zuwa nan nigeria garin Abuja,
Maimoon fara ce tas itama ga gashi tana da dirin jiki domin tafi Ayush dirin jiki gaskiya
sai dai bayan nan bata fi Ayush da komai ba,

Ayush da Maimoon farare ne sai dai launin fata ta banbanta,
ita Ayush fara ce tasss, Maimoon kuma farin ta launin jaa ne.
gashin Ayush mai murɗi-murɗi ne ga laushi gaban goshinta kuwa gashi ne a kwance har yaso ya haɗe da girar ta, yanada tsayi sosai zuwa tudun bayanta,
ita kuma Maimoon gashin ta tsantsi ne dashi a ware gashin yake itama ya rufe gadon bayan ta,
Ayush ta fi Maimoon Eyes da ƙaramin baki,
Maimoon kuma tafi Ayush tsayin hanci duk da itama Ayush tana da tsayin hanci,
Amma kuma Ayush tafi Maimoon tsayi nesa ba kusa ba domin ita fa Ayush da kaɗan Junaid ya ɗarata tsayi..

kowa da kalar suffar ƙasar daya ɗauko,
zuriyar mahaifin Ayush ƴan fulanin indiyawa ne dake ƙasar Oromia daganan kakanta ya samu mulkin ƙasar California….

Ita kuma Maimoon balarabiya ce ciki da waje,
duk ɗin su ba laifi ta ɓangaren kyau…

Mahaifin Maimoon babban abokin mahaifin Doctor Hasheem ne marigayi alhaji Bukar,
tin suna ƙananan yara suka fara soyayya da Dr Hasheem da kuma Maimoon, har Allah yasa suka mallaki hankalin kansu yanzu kuma Docter Hasheem yake so ya juyar da soyayyarsa kan Ayush haɗuwar sama…

*DALILIN YIN LESBIAN TSAKANIN MAIMOON DA LAILA…*

Akwai wata rana Maimoon da Laila suna tafe kan hanyar su ta zuwa hospital zasu je gurin Doctor Hasheem to daman Maimoon ita take draving motar ta suna tafe suna hira, kwatsam sai suka bugi wata tsohuwar mata da baƙaƙen kaya a jikin ta,
da gudu suka fito daga cikin motar suna faɗin “innalillahi wa inna ilaihi raju’un, ta mutu ko?”
ita ko Laila fashe wa tayi da kuka dake lokacin yarinya ce bazata wuce 15years ba, ita kuma Maimoon ta kai 18years suna ƙoƙarin ɗaga tsohuwar nan suka ji ta tintsire da dariya ta ɗago tana musu wani irin kallo, lokaci guda kuwa ta rungumo su jikinta kowanne sai data zura harshenta a cikin bakin su, cikin lokaci ƙanƙani kuwa ta ɓace ɓatt, tin daga lokacin ta juyar musu da kwakwalwa wanda idan basu kusanci juna ba basa jin daɗi duniyar zafi take musu,
to tin daga wannan lokacin suke wannan harkar ba tare da son ransu ba, sai bayan sun kammala suke dana sanin aikatawa kuma suke faɗa a junan su, tsawon shekara uku yanzu kenam….

idan har ba tsafi bane ai Maimoon tafi ƙarfin zuciyar ta saboda kullum a cikin karatun kur’ani take, a yanzu ta kammala N.C.E, Laila kuma ta kammala S.S.E, shaƙuwar dake tsakanin su ne yasa Laila take ƙiran Maimoon da Besty ita kuma Maimoon ta ƙirata da ƙawas amma ai Maimoon ta girmi Laila sosai….

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

*MASHA ALLAH*

Rashin comments ɗinku ne yasa zamu tsaya anam.

ku gyara dan Allah🙏🙏

 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

Back to top button