Sassaƙe na nufin yin amfani da fatanya ko magirbi ko dai wani abin wajen ciro ɓawo ko jikin wata bishiya domin a sarrafa ta a yi magani misalan kaɗan daga cikinsu sun haɗa da:
SASSAKEN KIRYA
Ana Amfani da sassaƙen ƙirya ana jiƙa shi da ruwa a sha yana maganin ciwon jiki.
Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah
SASSAKEN TAURA
Ana amfani da sassaƙen taura a jiƙa a sha yana maganin (Tamama) jin-kashi wanda yara ke fama da shi.
SASSAKEN MARKE
Ana jiƙa sassaƙen marke a ruwa a ba mata masu ciki wata huɗu idan yana yi musu ciwo domin samun lafiyar cikinsu da jaririn da suke ɗauke da shi. Bayana haka ana shanya sassaƙen marke ya bushe a daka a haɗa da irin gero idan za a shuka domin samun kyakkyawan sakamako, sannan kuma baya burtuntuna, har ila yau ana haɗa sassaƙen marked a jar-kanwa a sha maganin tari.
Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya
SASSAKEN SHIRINYA
Ana jiƙa sassaƙen shirinya da ruwa a rinƙa ba yara suna sha maganin mafarkin yara. Kinkiba.
SASSAKEN TUMFAFIYA
Ana kankare sassaƙen tumfafiya a haɗa da nono a sha maganin shawara.
Karanta>>> Sirrin Gyaran Nono Kashi Na Daya.
SASSAKEN BAKIN MAKARHO
Ana sassaƙar baƙin-maƙarho a jiƙa da ruwa har tsawon kwana uku, a rinƙa sha maganin basir mai tsiro.
SASSAKEN MARKE
Ana sassaƙo bishiyar marke a dafa idan ya huce sai a ɗiba a haɗa da lemon tsami a rinƙa sha yana maganin tari.
Karanta>>> Maganin Amosani, Karyewar Gashi Da Kuma Zubewarshi Kyauta
Sassaƙen Farar Ɗorawa da Sassaƙen Mangwaro:
Ana amfani da sassaƙen farar ɗorawa da sassaƙen mangwaron a jiƙa da jar-kanwa a sha maganin basir.
SASSAKEN KWANARYA
Ana dafawa da nonon saniya a riƙa sha yana maganin shawara, bayan an sha ana yin amai, ana warkewa sarai.
Karanta>>> Dalilan Dake Sawa Nonuwa Suke Zama Kanana
SASSAKEN GAWO
Ana jiƙa sassaƙen gawo da ruwa a sha yana maganin taurin kai, musamman ‘yan tauri ko ‘yan daba.
Sassaƙen Goba da Mangwaro da Lemon Tsami:
Ana amfani da su wajen maganin ciki, ana shanya su, su bushe sannan a daka a rinƙa jiƙawa ana sha yana maganin ciwon ciki.
Karanta>>> Amfanin Zobo Ga Lafiyar Jikinmu
Karanta>>> Tsumin Matan Aure Don Inganta Auratayya
Karanta>>> Tasirin Da Tazargade Ke Yi Ga Lafiyar Mata
SASSAKEN ARARRABI
Ana jiƙa sassaƙen Ararraɓi a rinƙa sha yana maganin tau-tau, bayan haka ana shanyawa ya bushe a daka a rinƙa barbaɗawa a kan tau-tau ɗin.
SAIWOWI
Saiwoyi na nufin wasu jijiyoyi ne ƙananan da manya waɗanda su ke riƙe da bishiya ko tsirrai. A koda yaushe saiwoyi kan kasance ne a ƙarƙashin ƙasa amma a wani lokacin sukan fito waje ma’ana su kan turo ƙasa. A ɓangaren magungunan Hausawa na gargajiya su ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa suna bayar da gudunmawa ta musamman wajen warkar ko kwantar da cuta a jikin Ɗan-Adam ko dabba. Wasu daga cikin saiwoyin da ake haɗa magungunan Hausawa na gargajiya sun haɗa:
Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam
SAIWAR KUKA
Ana haƙo saiwar kuka wadda ta ratsa kan hanya, ana haɗa maganin kwarce da kuma maganin soyayya. Akan haɗa abinci da ita a ba yarinya ta ci, maganin mallakar zuciyarta domin soyayya.
SAIWAR TAFASHIYA
Mata masu ciki na amfani da saiwar tafashiya, su jiƙa su sha domin samun lafiya cikinsu.
Karanta>>> Amfanin Zobo Ga Lafiyar Jiki Da Kuma Illolinsa
SAIWAR GAUDE
Ana haƙo saiwar Gauɗe a jiƙa a rinƙa sha, yana maganin ƙarfin jiki.
SAIWAR RAWAYA
Ana jiƙa saiwar rawaya a sha, ko kuma a shanya ta bushe a daka a rinƙa soyawa da ƙwai ana ci yana maganin shawara.
Karanta>>> Hanyoyin Da Zaku Bi Domin Karin Kiba Ba Tare Da Kunsha Maganin ba
SAIWAR BAKIN GAGAI
Ana jiƙa saiwar baƙin gagai da kayana ƙanshi a riƙa sha maganin ƙarfin maza.
SAIWAR SABARA
Ana ɗebo ko haƙo saiwar sabara da saiwar lemon tsami da ganyen tsamiya a haɗa a daka, sannan a jiƙa rinƙa sha, yana magann tamama (shawara) kamar yankan wuƙa.
Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata
SAIWAR JEMA
Ana haƙon saiwar jema a wanke a zuba a randa ko ruwan sha, tana maganin mayu.
SAIWAR DAYI
Ana haɗa saiwar dayi da farin goro a tauna sannan a haɗiye ruwan, tana maganin farin jinni. Bugu da ƙari idan aka tauna saiwar dayi ita kaɗai aka haɗiye ruwan maganin sammu (Makaru).
SAIWAR TAFASA
Ana haƙo saiwar tafasa a dafa da jar kanwa tana maganin ciwon nono
Karanta>>> Illolin Kwanciyar Ruf Da Ciki Ga Lafiyar Mu
SAIWAR ZOGALA
Ana haƙo saiwar zogala a haɗa da saiwar bini da zugu da lemon tsami da kuma barkono a jiƙa a sha, yana maganin sanyi mai kumbura jiki.
SAIWAR KUKA.
Ana haƙo saiwar kuka ta ɓangaren gabas sai a jiƙa a sha tana maganin ƙarfin maza ….
Karanta>>> Ko Kunsan Amfanin Shan Kunun Aya Lokacin Shan Ruwan Azumin Watan Ramadan Kuwa?