Gargadar So Chapter 114 By M Shakur
Hawwa tai maza ta ijiye wayan takoma sama tadauko hijabinta tasaka tafito daidai ana shigo da Ammi awani bespa moto na yawo agidan cus da nisa idan zakazo da kafa from asalin gate zuwa cikin gida, har gaban dakinta aka kawo Ammi, murmushi Hawwa keyi but ganin fuskan Ammi sai kawai taji gabanta na faduwa sosai amman ta daure takai hannunta zata karbi handbag na Ammi tace “sannu da zuwa Ammi” kala Ammi bata cemataba kawai tabude kofanta tashiga ciki Hawwa tabiyota tana maida kofan tarufe Ammi na kaiwa tsakiyan falo ta ijiye handbag nata babu wasa akan fuskanta tace “meke faruwa tsakaninki da mijinki Hawwa?” Khaleel ya sanar da Ammi ne? Tambayan da Hawwa tashigayima kanta kenan gabanta nafaduwa, yagayama Baba ne? Wannan da Ammi tazo daga Abuja, tabude baki zatai magana Ammi tace “wlh kikamin karya saina gauramiki mari! Sannan zan fita daga rayuwanki har abada this time around for good!” Shigowa cikin falon Hawwa tayi kawai saitai kneeling gaban Ammi takama kafafun Ammi bakinta har rawa yake tace “Ammi ki zauna zan fadamiki gaskiya wlh bazan miki karyaba nima daman inaso nakiraki, Please sit Ammi” da kyar Ammi ta zauna cus ta lura ayanda tama Hawwa maganan Hawwa ta dauka tasan wani abu ko maybe Khaleel ya sanar dasu komi, ahankali Hawwa tace “Ammi ni yarki ce Khaleel ba shine danku ba kafin nazo gidan nan nasanar daku kome kunki yarda dani, Ammi please believe me this time, bansan medame yafadan miki ba but I will not lie zan fadi komi nima nafadi abubuwan dana fadi” tadan sauke ijiyan zuciya gabanta na faduwa sosai wannan da Ammi tazo hala har sheri Khaleel yamata, tace “Ammi Khaleel na shaye shaye wlh!” Ammi tai shiru tana kallonta idanun Hawwa dasukai ja saita fara bama Ammi labarin komi daga farko tundaga kan auri saki da shaye shayen sa da abinda yahadasu da abinda tayi, da zagin, saikuma bakinta na rawa sosai tashiga bama Ammi labarin kotun da sammacin data kawomai jiya haba jikake tassssss!!! Ammi tadauketa da mari da saida Hawwa tai tumble ta tashi zaune da sauri tana dafe kuncinta ta bala’in tsorata da kalan marin da Ammi tamata, Ammi na mata wani kalan kallo tace “this slap is for zagin mijinki da rashin girmamashi” ko kadan Hawwa batai wani tunani Ammi zata kara mata mari ba, Ammi takara dauketa da mari tassssssss! Tace “this is for kai mijinki kotu” saikuma Ammi takama bakinta tana kallon Hawwa irin kallon Hawwa kece din nan tace “La’ilaha illalahu Muhammadu Ya Rasullullahi Sallallahu Alaihi Wa Sallama Hawwa kece da danyen aiki haka? Hawwa kin bani kunya! Wlh kin bani kunya! Tir da halin ki wannan halin gidahuman yan boko ne, Allah ya wadaran naka ya baci” Ammi tai shiru tace “inada tambaya dazan miki dudda nasan ayanda baki ambatoshi a labaran dakika bani ba hakan bai taba faruwa ba kenan but I will still ask you, Ibrahima yataba kai miki duka ko zaginki ko cimiki mutunci ko yimiki hauka idan yayi shaye shaye?” Idanun Hawwa sunyi jazur ta girgizama Ammi kai asanyaye, Ammi tasake dafa kanta kaman ta halaka Hawwa da duka takeji sabida tsabagen takaici dakuma haushi, sai kawai ta fuzar da iska Ammi is hurt very very hurt ganin yarta tasami miji but she’s too blind taga watake aure, cikin zafi da daci zuciya tace “Hawwa kin kira Khaleel fool in reality you are the fool! Hawwa kece dakikiyar kuma bakar jakama in particular!” Ammi ta fuzar da iska wlh takasa rike hawayen ta sai kukan yazubo takama bakin hijabinta tasaka akan idanunta tace “wlh sai ayau nakegani Ni’ima ma tafiki hankali Hawwa! Dan wlh tasan darajan mijinta! Baban Yaseer abin alfaharin Ni’ima ne! Ke bakisan darajan mijinki ba, bakisan kimansa ba ko value nasa, Hawwa you’ve disappointed me, bantaba expecting this behavior from you ba, wlh da wata tagayamin zance ba aloalo ba Hawwa na ba amman sai gata itane da halin nan” Ammi ta fuzar da iska ta sauke hijabinta tasa hannu ta goge fuskanta tasss sannan tamike tadauki jakanta jiki asanyaye tace “duk wani fada ko wa’azi dazan miki is too late kin riga ki dauki decision for kanki, kinkai kara kotu araba auren ku, bansani ba daban bata kudin motan zuwa Abuja ba bayan Babanki yakirani, bari naje zan sanar dashi komi shima yadena damuwa dan babu amfani” Ammi ta tashi tai hanyar kofa dasauri Hawwa ta bita tana kama kafafunta tace “Ammi ina zaki dan Allah karki tafi” wani kalan juyowa Ammi tayi ta hankada Hawwa da kafafu tamata wani ihu sosai tace “kinci ubanki Hawwa cikani! Karki kara kirana Ammi sunana Zainabu! Ni ba mahaifiyar ki bane yau kin gwadamin haka, Hawwa kin nunamin I was never your Mom and I will never be, kin nunamin bani na dauki cikinki ba na wata tara! Hawwa idan har zaki iya tashi kin wanke jiki kitafi kotu baki kirani ba, baki kira Baban ki ba, ai bamuda ragowan amfani arayuwanki, bamu da daraja bamu da kima we are nothing! Damu da babu duk daya dan haka nabarki lafiya” kai Ammi taji zafin abinda Hawwa tayi ba kadanba, dawani kalan gudu Hawwa ta tashi tashiga gaban Ammi tafashe da kuka, maganganun Ammi yakarasa tayi nadaman actions nata a hundred million times, cikin kuka maiban tausayi tace “Ammi dan Allah kiyakuri karki banni da halina, Ammi I’m confuse, banda natsuwa, I can’t think straight, bansan menakeyi ba, bansan yanda ake nurturing relationship ba, Ammi wlh na yaga takardan sammacin jiya da daddare nayi flushing a toilet, i will call them nagaya musu na janye case din, Ammi dan Allah i need you now more than ever to guide me bansan menakeyi ba” Ammi na wani irin kallonta ta nunata da yatsa sabida yanda Hawwa ke bata bakinciki tace “yarinya kinyi karya you don’t need me!” Zata wuce Hawwa takama hannunta tace “Ammi sabida Mamana karki rabudani! Naji ni nayi laifi kiyi fushi dani ki hukuntani but sabida Mamana karki rabudani, rayuwana zai lalace, ke kadai gareni Ammi banda any friend, guide me Ammi nayi kuskure, kiyakuri Ammi dan Allah, dan Allah, Ammi Mamana na kallonmu kiji tausayina Ammi” Hawwa is seriously crying kana ganinta kasan she’s scared itama to loose mijinta, Mamanta data kira kadai ne abinda ya kashema Ammi jiki not Hawwa dan tana matukar fushi da Hawwa, tanason yayarta sosai, ta tsaya tana kallon Hawwa dake kuka sosai sai kawai ta wuce ta xauna tanunama Hawwa gabanta akan carpet tace “zoki zauna”Zuwa Hawwa tayi ta zauna tana kuka still Ammi tace “the only laifi na Khaleel danaji na dauka is shaye shaye! But yaron nan da bakinki kika fadi yana kokarin chanzawa ba kullum kikaga yakeyi ba, banda haka Hawwa yana sanar dake gaskiyan abu sabida yana sonki!” Ammi tai shiru chan tace “Hawwa yaron nan saida ya sanar da Malam mahaifiyarshi namai aure tun yana yaro yana sakinsu sabida baya sonsu, kece mace ta farko daya taba gani da idanunsa yaji kece ra’ayinsa yakuma aure ki akanme zaki dinga hada kanki dasu? Idan ma ya auresu kaman yanda ya aureki ne ai mace data isa tasan kanta tasan yanda zata mu’amalanci mijinta ta yanda bazai taba iya sakinta ba ko a mafarki” Ammi tace “Hawwa yau wani yatareki yaji kinyi wannan haukan yace bamu baki tarbiya da kyau ba yazakiji? Iyaye is no no koyaya suke ke ko bokaye ne su fadanki da Khaleel ya tsaya tsakanin ke da shi babu dalilin kawo iyayensa! Hakan zagi ne da disrespect, yaron nan koda baya girmama iyayensa ke bakida hurumin kice bazaki girmamasu ba!” Ammi tai shiru tace “zagin sa, Hawwa kina gorantamai ilimin addini ke rawa kikayi Allah yabaki? Shida baidashi yama fiki hankali da hikima da sanin yakamata da ahaka ake dawo da mutane hanyar gaskiya da babu wanda ya karbi addinin musulunci da manzon ma’aiki yakawo! Kinada labarin karuwa karuwa Hawwa data shiga aljanna sabida ta shayar da kare dakejin kishi ruwa? Kin dauka ita tanada ilimin addini ne? Kinsan Malamai nawa zasu wuta? An gayamiki sabida wane malam ne shikenan dan aljanna ne? Kinada labarin wanda yayi kashe kashen mutane Allah ya yafemai yasashi a aljanna?? Hawwa mata sunfi yawa a wuta inji Annabi and yawanci wayanda suke wutan sabida mazajensu suke ciki! Kinsan maisa akace wanda ke koyon Al Qur’ani idan yana karantawa yafi wanda ya iya karatu samin lada, bar gani kaman kinfi Khaleel ilimin addini yaron nan saiya iya shiga aljanna yabarki a gate din jahannama sabida abubuwan dakikamai, wat is wrong with you Hawwa harxakiyi tunanin kai aurenki kotu ki kashe? Kin manta kuka da rashin bacci, sleepless night dakike having sabida rashin aure???



