Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 34 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

   THIRTY-FOUR📍

          “Dagaske Umm? Me suke shiryawa? Dan Allah ki sanar damu?”…..

Deen ya fada yana dawowa kusa da Umm…..

Umm zatayi magana kenan sukaga fatima zainab ta tashi da sauri tayi hanyar waje a guje…….

      “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”……

Mami da Umm suka hada baki wajan fadin haka at the same time suna bin bayan Deen daya bita da sauri…….

Gurin gate ta nufa a guje kamar wacce aka biyo, ganin haka yasa securities din gidan suka taso da sauri suna kokarin tareta dan basu manta da tashi hankalin da aka shiga last time data gudu ba…….

     “Don’t touch her! Kar wanda ya taba ta!!!”….

Deen ya fada cikin daga murya ganin kowa binta yake yana kokarin kamota…. 

     “Ku tabbatar ko ina a rufe yake!! Amma kar wanda ya sake ya tabata!!”……

Nan aka shiga duba gates din gidan ana tabbatar da cewa a rufe suke……

Shareta Deen yayi ya tafi gate din da tabi ta fita wanchan lokacin dan ya tabbatar ko shima a rufe yake, yana zuwa yagansa a rufe alamun angane an rufe kenan……

Dawowa harabar gidan yayi yaganta tsaye sai masifa take yiwa mai gadi wai ya bude mata kofa ta fita ita bazata zauna ba, mami da Umm na tsaye sai rarrashinta suke amma taki kulasu……

       “Saif anya bazaa kira malamai ba kuwa? Lokaci daya yarinya ta birgice haka?”……

Cewar mami tana dafe habarta…..

     “There’s no need for that, ku shiga ciki kawai, I’ll handle her!”……

     “A’a nidai hankalina be kwanta ba, let me go get my phone”…… 

    “Gaskiya dai gwara asan abinyi, this is not a small issue saif”…..

Umm ta fada tana bin bayan mami dan suyi shawarar abinda ya kamata ayi……

Hade rai Deen yayi ganin yanda securities din gidan suka zuba mata ido, yayi kwafa yace;

      “Before the count of three kowa ya bar compound dinnan nonsense!”…….

In a blink of an eye kowa yabar gurin saboda ba karamin tsoron bacin ransa suke ba dan yanda suke tsoronsa ko Mami basa tsoro haka, abu kadan sai ya yiwa mutum illa kuma ba yanda mutum ya iya, tsaki yaja yana harararta yace;

     “Kinzo kina yiwa mutane hauka ba dole ayita kallonki ba, yan iska kawai!”……

    “Please open the door for me”….

Ta fada a hankali kamar me tsoron magana, abinda takeji yau haryafi na rannan shiyasa har ta kasa fita a labe, ji take kome zaa mata wallahi saita fita daga gidan….

     “Get up!”….

Ba musu ta mike daga durkusan da tayi……

    “Ina zaki da kike cewa a bude miki kofa?”….

   “Zanje gidane”

    “Gidan wa?”….

  “Gidanmu!”….

   “Dama kunada gida? Ai na dauka a gidan saurayinki kike?”…..

Sunkuyar da kai tayi batace komai ba dan maganar ta daketa, cuz he’s right dan basu da gidan……

    “Me zaki jeyi a gidan”….

Ya sassauta murya ya tambayeta ganin kamar bataji dadin abinda ya fada ba….

     “Kai dallah ka budemin kofa in fita!!!”……

   “Karkimin rashin kunya! Sarai kinsa banasan raini! Gidan ubanwa zaki idan na bude miki?”…

Ya maida mata cikin tsawar data masa…….

     “Gidan ubanka zani! How many times will I tell you to go away from my life?!!”…

Yatsunsa guda biyu yasa ya bige mata lebe, a take gurin ya dan tsage saiga jini ya fito kadan……

Wani uban ihu ta rusa kamar wacce aka chakama wuka yayi saurin toshe mata baki da hannunsa…..

       “Kinga kinsa rashin kunyarki tasa na ji miki ciwo ko? Daga dan taba lips dinki shine zakiyi ihun munafurcin da kika saba salon su Mami suce na miki wani abu?”……

     “Meya sameta haka?”….

Umm da jin ihu yasata ta fito da sauri take tambaya…

    “Nothing much, ihu kawai takeyi”….

    “Meye haka? sake mata baki mana“….

Sai a lokacin ya tuna ashe ya garkame mata baki, hannunsa ya zare daga bakinta ya zaro handkerchief yana goge mata dan jinin daya fito…..

Wani ihun dayafi na dazu ta kara saki sai kuma ta zube kasa a sume….. Saura kadan takai kasa yayi saurin tareta, garin haka har bige hannunsa yayi be sani ba….

         “Ya Salam yarinyar nan na ganin rayuwa saif, muje ciki”…….

Karo sukayi da mami dake  shirin fitowa taga sun shigo saif rike da ita a hannunsa…. 

     “Yanzu nake shirin fitowa, yana ganku haka?”….

   “Suma tayi wallahi yaya”

   “Ikon Allah, yarinyar nan na ban tausayi wallahi”…

    “Kedai bari she’s really going a lot, Allah dai ya bata lafiya”….

    “Ameen ya Allah”…

    “But saif why is she always passing out? Anya babu rashin jini a lamarin yarinyarnan kuwa?” …..

Girgiza kai yayi cikin tausayawa yana kallon fatima zainab yace;

    “She had kidney failure!”….

   “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel! Kidney fa kace? How sure are you?”….

    “I’m very sure Doctor, namata general check up, duka kodanta is damaged, I don’t even know how”….

    “Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha, yanzu duk kasan da wannan shine kayi shiru?”……

Cewar Mami da take ta sallallami….

    “I just found out today”….

        “And what were you waiting for da bakayi proceeding da dialysis ba? Innalillahi this is too much for her”…..

Umm ta fada kamar zatayi kuka….

     “Transplant nakeso a mata, I want to give her my kidney!”……

Shiru ne ya biyo baya kamar wa’yenda aka daukewa wuta, su mami shock suka shiga jin ze bata kodarsa bayan ko sanin wacece ita beyiba, toh why is he willing to sacrifice this much for her?……

Ganin sunyi shiru yasa jikinsa yayi sanyi, durkusawa kasa yayi ya shiga rokonsu dan shi duk a tinaninsa basu amince bane…..

      “Mami, Umm pls don’t say no, wallahi she’s in a very critical condition and I don’t want to lose her, idan kuka cemin baku yarda ba wallahi komai ze iya faruwa”……

Shafa kansa mami tayi murmushi dauke akan fuskarta tace;

     “My son!”…..

Dagowa yayi da sauri yana addu’ar suce sun yarda dan shi a shirye yake ko yanzu a tafi a cire nasa asa mata….. 

     “I’m so proud of your kind heart! Ada nace I won’t come back to this conversation, but I’m asking you again today, are you in love with her?”……

      “No mami, Fisabilillahi zanyi badan komai ba trust me!”…..

    “Nayarda, we’re not against bata kidney dinka dakayi niya but the issue is kasan one of your kidney isn’t functioning well ko?”…..

    “Nasani, me lafiyan zan bata mami inyaso sai in cigaba da kula da kaina, I’m a medical doctor it’ll be easier for me”….. 

Jan hancinsa Umm tayi cikin barkwanci tace;

     “A’a gaskiya ban yarda ka bada naka ba, ina lefin mami tayi maka sacrifice din tinda duk ta fimu lafiya”…….

     “Sai in masa, meye a ciki? Sis haka ya kamata ma ayi”…..

Dariya tayi tace;

    “Ko kuma ni in bada nawa ba, amma gaskiya saida in siyar, saif nawa zaka siyan mata nawa?”…..

    “No duk ku rike naku nizan bata nawa, ku kun riga kun tsufa”…..

    “Kajimin yaro, daga abin arziki? Ko tsoro kake kar ince kaban 500m?”…..

Murmusawa yayi yana kallon fatima zainab da yaga kamar tana dan motsawa yace;

     “Gaskiya kin rena arziki na Umm, 500m dinne zanji tsoron baki, naaaaah”….

    “Nasani ko…….”….

Wani kuka da fatima zainab ta fashe dashi ne ya dawo da hankalinsu kanta banda Deen da tin dazu hankalinsa ke kanta…….

Daidai nan kuma malaman da Mami tasa a kirawo suka karaso, kiran landline din parlourn mami akayi mami ta dauka tace a shigo dasu cikin gidan……

     “Saif jeka taho dasu”…

   “Toh Umm, dan Allah kisa mata hijabi kafin mu shigo”……. 

    “Toh bappa gayamana abinda ya dace tinda mu bamu sani ba”…..

Bece komai ba ya fita, baa jima ba sai gashi ya dawo tare dasu…… 

Daidai shigowarsu ta sake kwalla wani kara me karfi da saida gidan ya amsa gabadaya…..

Babu bata lokaci suka fara mata karatun alqur’ani me girma, a take ta fara fizge fizge harsu mami suka kasa riketa, da sauri Deen ya rukota ganin daya malamin na neman kama hannunta, shifa shiyasa tin farko beso ankira malami ba kar azo garin rukiya ayita tabata….. 

kam kam ya riketa sannan ya shiga tayasu karatun…

Tin tana ihu muryarta na fita har muryarta ta dishe ta koma ihu a hankali, saida taga ba sarki sai Allah sannan ta fara magana;

     “Wayyo Karku kona ni, zan fita wallahi”….

      “Waye?”….

Daya daga cikin malamin ya tambaya…

    “Mijinta ne yusuf”…… 

    “Au dama baka rabu da ita ba? Yanzu ko zan kona ka dan iska kawai!”…..

Deen ya fada yana harararta kamar itace yusuf din….

     “Bazan iya rabuwa da ita ba, ni ba cutar da ita nake ba, sonta kawai nake”…..

      “Abinda yafi sonta kake banza mugu kawai, ta ina kataba ganin bil’adama da aljanu sunyi tarayya?”….

Dafashi mallamin dake kusa dashi yayi ganin yanda ya fusata ya kada masa kai alamun yayi shiru…..

Karatu suka cigaba da mata dan sun gano irin aljanunnan ne masu taurin kai gwara kawai a konashi shine zata samu salama……

      “Wayyo zan fita, dan Allah karku konani! Zan fita nace, na fita”……

Sai tayi wani atishawa wani nannauyen bacci na kwasheta a kirjinsa……

      “Kece mahaifiyarta?”….

Malamin dake daya gefen ya tambaya yana kallon Umm….

      “Eh nice”…

Ta amsa masa kawai…..

     “Garin yaya akayi sake akanta haka? Yanzu sai munyi da gaske kafin ya rabu da ita dan ya riga ya shiga jikinta sosai, alamun kuma sun nuna ya dade tare da ita”……

     “Ya hayyu ya kayyum, toh meye abunyi mallam?”…

Umm ta fada batareda ta bashi amsar saken dayace anyi ba dan batasan me zata fadamasa ba tinda itama batasan komai akanta ba…….

    “Ai wannan din karamin matsala ne akan sihirin dake jikinta!”….

    “Sihiri kuma? Oh Allah ka kawo mana dauki”….

    “Karku damu da yardar Allah komai ze daidaita, mu da Allah muka dogara!”…..

    “Hakane, yanzu ya zaayi toh?”….

Mami ta tambaya…

   “Yanzu zamuyi mata rukiya inta tashi sai a bata, zamu dawo gobe Insha Allah”……. 

      “Toh Allah ya kaimu, mungode sosai”…..

         Karfe takwas na dare ta bude ido tin bayan baccin daya dauketa, jinta tayi wani iri kamar wacce aka daukewa abu kamar dai ba itaba, juyi ta farayi a gadon kamar wata yar karamar yarinya, sai kuma chan ta tashi ta zauna……

     “Har kin gama wasan?”…..

Deen ya tambaya, yana zaune chan gefe akan couch yana aiki da system, tindazu yake zaman gadinta wai kar wani abu ya sameta, su mami sunyi sunyi ya tashi su zasu zauna da ita yaki, haka suka hakura suka kyalesa dan yanzu sunyarda genuinely yakesan taimakonta, koda ta tashi akan idonsa ne amma yayi kamar be gantaba ganin itama bata san yana dakin ba.. Sosai ya fara shiga yanayi da take juye juye nan, yanda komai nata yake kadawa kamar tanayi da gangan, sai yaji tsigar jikinsa na tashi……. Kauda tinanin yayi ya dauko tray din abinci da aka kawo masa tin dazu beci ba ya nufi gadon…..

Zama yayi yana facing dinta ya debo abincin yakai bakinta, saurin kauda kanta tayi tana kallon gefe…

      “Come on baby girl!, juyo mana”…..

    “Banaso!”….

    “Toh me kike so in dafa miki?”…

       “Bazaka iya dafawa ba!”…

Bakinta daya fashe dazu ya dan shafa yace;

     “Ance miki kowa lazy ne irinki?”…..

Batarai tayi tace;

    “And who said I’m lazy?”….

Dogon hancinta dayake bashi sha’awa yaja yana fadin;

    “Your body said it all, your skin is so soft da an tabaki sai kisawa mutum kuka, harna fara tausayawa wanda ze aure ki wallahi zesha fama”….

Haushi maganarsa ta bata taji kamar ta dakesa, wai har kura yace da kare maye? Dama ance lefi tudu ne saika take naka kaga na wani, in banda haka duk muguntarshi be gani ba sai nata?….. Murguda baki tayi tace;

      “Khaleel baze taba gajiya dani ba!”….

    ‘Taraaassss’…..

Taji karar fashewar kwanukan daya zubar dasu a kasa harda abincin gabadaya, da gudu ta fita daga dakin karya shaketa……

Huci ya shigayi kamar mayunwacin zaki, ya daga murya yace;

     “I’ll get hold of you bitch!!”……

Sai kuma ya tashi ya bita da sauri….

Da gudu ta shige dakin mami, Umm dake zaune akan gado taji kamar an jeho mutum, rungumeta fatima zainab tayi tana boyewa a cikin jikinta…..

     “Lafiya! Lafiya kuke guje guje haka? Da katawo nan ina zakayi?”….

Umm dataga Deen na kokarin hawowa gadon ta dakatar dashi…..

Kwafa yayi yace;

     “Wallahi zan kamaki, sai kin maimaita abinda kika fada”…….

    “Basai kazo ka kamata mugani ba, ko kunya bakaji kayita cin zalin yarinya, my friend get out!”….

Mami da fitowarta kenan daga toilet ta fada tana nuna masa hanyar waje……

       “Ikon Allah sai kace wasu jarirai”…..

    “Kema dai kya tayani fada, kome tayi ai be kamata ya biyeta ba tinda ba lafiya ne da ita ba”….

    “Ni mamaki ma ya bani, Allah ya kyauta kawai”….

    “Ameen”….

Dagota Umm tayi tana tambayarta me zataci, cewa tayi batajin yunwa ita bazataci komai ba, lallabata Umm tayi da kyar ta yarda taci kadan, shi dinma saida ta bata a baki…. 

Sata tayi tayi wanka sannan ta rama sallolin dake kanta…. Haka ta zamewa Umm kamar jela, duk inda tasa kafa saita bita wai karyazo ya kamata, kuma duk a tinaninta Umm ce mamansa shiyasa take binta tinda da kunya ya mata abu a gaban mamanshi…..

Suna zaune a parlor suna kallo gurin tara da rabi Deen ya shigo da sallama……

     “Kuna kallon film da wannan me almatsutsan? Ai qur’ani ya kamata kuyita kunna mata ko shedanun kanta zasu sauka”…..

    “Zaka fara ko, toh ba ruwanka da ita”….

      “Umm nayi shiru”…..

    “Sweetheart mu cigaba da hirarmu kinji?”…..

       “Kice mishi ya dena kallona toh”…..

Harararsa Umm tayi batace komai ba……

     “Ni yaushe na kalleta, wannan yarinyar akwai sharri wallahi, ni bari kuga news zan kalla”….

      “Better for you, ina jinki”….

     “Iya abinda nasani ko?”……

     “Yes ina jinki”……

Numfasawa tayi tashiga basu labarin WACECE ITA!!!………

    

Finally we’re getting to WACECE ITA lol

Back to top button