Karfe A Wuta Chapter 13 By Ayshercool
Cike da takaici Walid ya nufeta da sauri, ya kalli Viper ya ce “Amma meyasa zaka yi haka? Da ka kasheta fa?”Aminu ya kalli saman tsinin wuƙarsa da take ɗauke da jinin Nabila, bai kalli Walid ba ya ce “Ban gaya maka kar ka kawo mini kowa ba?”Walid ya ce “Ka gaya mini, amma na tabatta ka ga abun da nake son ka gani, ai ko?””And so, me hakan zai amafana mini? Ka ƙaddara ban ga komai ba, kuma gargaɗi na yi mata a kaina, dole na san tana da manufar son haɗuwa da ni, wataƙila wata ƙulalliyar ce, sai dai amafani da mace ba zai hana in illata ta ba, idan ta shiga gonata”Walid ya ce “Yanzu abun da ka gani, ba shi da muhimmanci kenan?””Ko kaɗan” ya bashi amsa kai tsaye.Walid ya tsuguna a kanta, amma ya rasa abun da yakamata yayi.Wani irin numfashi Nabila ta fara fitarwa, mai sauti wanda hakan yake tabattar da, numfashin yana ba ta wahala.Ɗan mama ya ce “Mun shiga uku, wane irin numfashi ne wannan,ko mutuwa za ta yi ne?” Walid ya sake dirircewa ya rasa abun yi.Viper ya goge jinin Nabila da ke jikin wuƙarsa, a jikin rigarsa.Ya ɗaga kai, yana kallon yadda take jujjuya kanta, tana neman iska.Wata drower ya saka mukulli ya buɗe, ya ɗaukko wata ƴar ƙaramar akwati, ya ajiye, ya ƙarasa ya ɗauki jakar Nabila, ya zazzageta yana neman inhaler, amma bai gani ba, ya ja uban tsaki ya tashi, ya sake buɗe wardrobe, ya ɗaukko inhaler, sai dai sai da ya tsaya yayi ta kallon inhaler, yana kallon Nabila, sannan ya ƙarasa kanta, ya tsaya, ya ɗagota ya fesa mata a cikin bakinta.Kamar zata haɗiye inhaler, haka take sake buɗe bakinta, ya mayar da ita ya kwantar, ya ɗaga gefen rigarta, da wuƙarsa ta huda, ya saka auduga da spirit, ya goge jinin tsaf, ba wata huda ce ta kirki ba, kawai dai ta zubar da jini ne sosai.Gaba ɗaya suka zuba masa ido, ya zuba iodine a jikin audugar, ya saka a kan cikin nata, ya kawo plasta, ya saka. Dama ya saba yi musu dressing, idan suka je aka sare su, a wurin rashin jin su.Ya mayar da akwatin in da take, ya koma gefe ya kunna sigari. Mamaki yake da tunanin, uban me take nema a wurinsa, sai dai ya fi yarda da cewa, tarko ce ake son yi masa da ita.”Amma ya aka yi, aka samu wannan coincidence ɗin?” Ya tambayi kansa a cikin zuciyarsa.Duk suka koma gefe, suka zubawa sarautar Allah ido.Tari ta fara yi, ta yinƙura ta tashi zaune, ta kalli kayan cikin jakarta, da suke a watse, ta fara tattara abun ta, sai kuma ta dawo hayyacinta,bayan da suka yi ido huɗu da shi.A rikice tayi jifa da jakar, ta ƙwala wani uban ihu, nan take mafarkin da ta taɓa yi ya dawo mata, tabbas sai yanzu ta fuskanci inuwarsa take gani a mafarki.Ƙoƙarin tashi take ta gudu, cikin zafin nama, ya bar in da yake ya cafkota.Tausayinta ya kama Walid, tare da dana sanin kawo wa Viper ita, ko haɗa bakin aka yi da ita a cutar da shi, atleast ita macece ya ɗaga mata ƙafa, amma ya san in da ya matsa, sai Viper ya illata ta fiye da yanzu.”Waye ya aiko ki?” Yayi maganar a kausashe.Ta girgiza kai, amma ta kasa magana.”Waye ya turo ki na ce?” Yayi mata tsawa.A rikice ta ce “Wallahi ba kowa” tayi maganar tana zubar da hawayen tsoro.”Me ki ke nema a wurina?””Dan Allah ka yi mini rai, na tuba na bi Allah, ba zan sake ba, dan Allah kar ka kasheni, wallahi ni marainiya ce, tayi maganar tana kawar da kanta gefe, ta kasa kallonsa, sai azabar bugu da zuciyar ta take yi, cikin tsoro da fargaba.”Look up kalleni” muryarsa ba a iya kunnuwanta take jin ta ba, a tsakiyar zuciyarta take yi mata amsa kuwwa, gashi ya matso daf da ita, warin sigarin da yake yi, ya fara hautsina mata ciki.”Kalleni” ya sake maimaitawa.Ɗan mama ya ce “Ki bi umarninsa, ba ya maimaita magana, kan ki farka a lahira”.Cikin karkarwa, ta ɗaga kanta, da gefen idonta kawai ta kalleshi, amma ta fashe da kuka “Wallahi tsoronka nake ji, ba zan iya kallonka ba, idonka tsoro yake bani, dan Allah ka yi haƙuri kar……Tsit tayi, ta haɗiye wani irin mugun yawu, da ta ji tamkar ta haɗiyi wuta, biyo bayan ganin ya saita kaifin wuƙa a kwaroron maƙogwaronta.”Idan ki ka bari, na sake ganin fuskarki, ko a kan hanya, Wallahi sai na kashe ki!”Nabila ta gama saddaƙar da gumin da yake bin ƙafafuwanta, fitsari ne ba gumi ba, gashi tun daga goshinta, har cikin jikinta gumi ne kawai yake yanko mata ko ta ina.Ta jinjina masa kai, ya ja da baya, ya kalli Walid ya ce “Ta ƙara mintuna biyar a gabana, sai dai ka fita da gawarta”Walid ya kalleta ya ce “Zo in fitar da ke hanya””To in ɗauki jakata?” Tayi maganar cikin tsoro.Walid ya ce “Hanzarta ki kwashe kayanki mu tafi”Sai dai ta kasa motsawar, ta ƙame a jikin bangon ɗakin, jikinta sai tsuma yake yi.A fusace Walid ya ce “Ki tattaro mu tafi mana”Nabila ta fashe da kuka, ta ce “Wallahi tsoro nake ji, kar in durƙusa ya kashe ni, dan Allah ka bashi haƙuri, kar mu haɗu a wani wurin ban sani ba ya kasheni, ya rantse sai ya kasheni”.Walid ya ce “Na ji zan bashi, taho mu tafi””Wallahi na kasa motsi” tayi maganar hawaye na cigaba da zuba daga idonta.Gaban wardrobe ya je ya tsaya, ya juya musu baya, ya saka hannayensa, ya kama ƙasan rigarsa zai cire ya canza wata, kamar wadda ya kwance daga ɗauri, dama idanunsa ne igiyoyin da suka ɗaureta, ta durƙusa ta kwashi kayan jakarta, da jakar ta fita da gudu, ta kwashi takalmanta, ta fyalla a guje, ta bar gidan.Dariya ɗan mama ya ƙyaleƙyale da ita, ya yi wata irin ashariya ya buga ƙafa, sannan ya je gaban Viper yayi wata irin kururwa, cikin sara masa tare da kambama shi ya ce “Maza gumbar dutse, ina gwanin wani ga nawa, gaba salamun baya salamun mutumina, zaki ka ke sarki a gida sarki a dawa, ina mazan suke, ga fa uban ɗakina wanda ake kira namijin gaske. Sun buga da kai sun barka mutumina, Allah ya baka duniya lahirar ma ka samu in sha Allah. Mahadi mai dogon zamani. Kai idan ba namijin gaske ba, kalli yadda ka mayar da mai hankali zararre cikin ƙanƙanin lokaci, kalli yadda yarinyar nan ta firgice ta koma zararriya lokaci ɗaya, ba gaba da gaba ba ko ta baya sai an shirya tararka uban gidana, mahadinmu mai dogon zamani, Allah ya baka tsawon rai, ya kaimu ranar da zamu ba da jininmu domin ɗaukar maka fansa”Geɓare baki Viper yayi kamar zai yi murmushi, dan kirarin ya tuna masa wasu abubuwa da dama da suka shuɗe.Walid kuwa gaba ɗaya daga Viper har ɗan mama haushi suka bashi, kamar ya ɗura musu ashar, Nabila ko da cunen aka yi musu da iya, shi yaƙi ai ɗan zamba ne, kuma ko ba komai mace ce, bai kamata ya razanata har haka ba, tun da ya san mazan ma razana su yake yi.Takalmansa ya saka, ya bi bayan Nabila, dan yadda ta fita a burkicen nan, komai zai iya faruwa, gashi ga dukkan alamu, ba ta da cikakkiyar lafiyar numfashi.Viper kuwa, rigar jikinsa ya canza, Ɗan mama ya ce “Boss, wai ka taɓa karatun likita ne? Na san dai ka iya wankin ciwo, to kuma na ga yau kayi aikin likita”.Al’amin ya girgiza kai ya ce “Ko ɗaya, na zauna da mai irin ciwon ta ne”Ɗan mama ya ce “Na fahimta, amma dai ba fita zaka yi ba ko?””Zaka hana ni ne?”Da sauri ya ce “A’a wane ni, ka san idan wannan jarababben ya dawo, ya tarar ka fita, masifa zai ta yi mini” bai saurari ɗin mama ba, ya bi ƙofa ya fita.Nabila kuwa tun da ta fita da gudu, ba ta tsaya a ko ina ba, sai da ta fita titi, shi ma babu ababen hawa, haka ta cigaba da tafiya tana waige-waige, sai a lokacin ta ji gefen cikinta, yana ta yi mata zugi, ta ɗaga rigarta ta ga plasta.Ga jikin rigarta da jini, a hankali ta furta “Na shiga uku”Addu’a ta din ga yi, tana cigaba da tafiya, cikin ikon Allah, Allah ya kawo mai a daidaita sahu, ta kama ta shiga, tana ta haki.Sumayya tamkar yau ta shiga harkar aikin jarida, haka tattaunawar ta su da honorable Indabo take kasancewa, saboda yadda ya tsatstsareta da manya-manyan jajayen idanunsa, yana yi mata wani irin kallo, gashi daga shi sai ita a wurin.Ajiyar zuciya ya yi ya ce “Meyake damunki ne? Ki nutsu mana”Ta jinjina masa ta kai, ta cigaba da yi masa tambayoyin da su aka yarje mata ta yi masa.Sai dai ita kanta ta san amsoshin da yake bayarwa, na son zuciyarsa ne kawai, ba wani abu ba.Jin ta yi shiru, ya sanya ya kalleta ya ce “Ya dai?”Cikin girmamawa ta ce “Tambayoyin sun ƙare sir””Kamar bakinki akwai magana, akwai tambayoyin da ki ke son yi mini ko? Mu je zuwa ina saurarenki”Ƙasan zuciyarta ta ce, ina ma da gaske ka ke, da ka ji ruwan tambayoyin da ko ka ƙi Allah, sai ka dangana da faɗar gaskiya, a zahiri kuwa ta girgiza kai ta ce “Babu sir”Ya kalli kofunan gabansu, ɗauke da shayi, wanda shi yana yi yana shan nasa, ita kuwa ko taɓawa ba ta yi ba.”Ya ba ki sha shayin ba? Ki sha mana”Sumayya ta sake risunar da kai ta ce “A ƙoshe nake ne”Ya ce “I see, amma na yi mamaki da ki ka ce mini baki da tambaya a gare ni, duk da yadda ki ka ƙaryata hirar da na yi kwanaki, ki ka ce ban yi ayyukan da na ce na yi ba, na ƙyale ki ne kawai saboda managernku yayi ta bani haƙuri, kuma ke mace ce yarinya ƙara ƴar cikina.Siyasa mu tamkar business take a wurinmu baby girl, we invest to make a profit, ita kanta gidan radiyon da ki ke aiki da su, nike hannun jari mafi tsoka a cikinta, dan haka abun da nake so shi ake yi, kuma domin yi mini campaign ya sanya na zuba kuɗina a harkar gidan radiyon”Sumayya dai ta yi shiru, ba ta ce komai ba.Ya miƙe tsam, ya zagaya ya zauna a kan kujerar da take kai, wanda hakan ya sanya ja da baya, tana maƙale jikinta.”Mun gama abun da ya kawo ki, sai kuma abun da ya sa na ce a turo mini ke”Da sauri ta ɗaga ido ta kalle shi, tana mamakin abun da ya faɗa.Ya ɗauki kofin shayinta ya sha, sannan ya ce “Yarinyar da na ganku tare, ranar da na yi zuwan ƙarshe, ita nake nema ba ke ba, amma ke ce tsanin da yakamata na taka na kai gare ta, wacece ita?”A tsorace take kallonsa, ya ce “Ki amsa mini mana”.”Nabila ce, ƙawata ce, she’s like a sister to me” ta faɗa a tsorace.”Ba wannan nake son ji ba” yayi maganar yana sunkuyowa daf da fuskarta.”Wacece ita?”Sumayya ta ce “Ƴar wani tsohon soja ce, dan Allah idan wani laifin tayi maka ka yi haƙuri, ba zata ƙara ba, idan ma dan ba ta gaisheka bane ranar, dan Allah ka yi haƙuri ba zata sake ba, ba ta da lafiya ne ranar”Ya girgiza kai ya ce “Ko ɗaya, tarko nake son na yi da ita, aiki za ta yi mini”Jiki na tsuma Sumayya ta ce “Wane irin aiki kuma?”Ya gyara zamansa ya ce “Kin san wani ɗan daba Aminu Viper?””A’a ban san shi ba wallahi”Indabo ya ce “Kina ƴar jarida, ki ce mini ba ki san shi ba, jami’an tsaro na neman sa ruwa a jallo, na yi niyyar shafe tarihinsa, aka samu wani ya yi mini zagon ƙasa, ya rusa mini komai.Har a yanzu ana ta ƙoƙarin kama shi, kwatsam na ganku, kuma na ga tana da wani abu da zan iya yi masa tarko da shi ya zo hannuna, dan haka ƙawarki za ta yi mini aiki”Hankali tashe ta ce “Dan Allah ka yi haƙuri, mutumin da yake kashe mutane, tana mace ina ita ina ɗan daba, ba jami’an tsaro suna nemansa ba? Za su kama shi dan Allah ka ƙyale mu”Yayi wata muguwar dariya ya ce “Kin san waye indabo kuwa? Kama Aminu ya zama gawa ne kaɗai zai samar mini da nutsuwa da kwanciyar hankali, dan haka dole ƙawarki za ta yi mini aiki”Ta buɗe baki za ta yi magana, wayarta ta fara ringing, ta ɗauka ta duba, ta ga nabila ce take kiranta.Ya ƙureta da idonsa ya ce “Ɗaga mana, ɗaga wayarki”Jiki na rawa ta ɗaga, ta kara a kunnenta.”Sumayya kina ina ne?” Muryar Nabila ta fito raɗau a wayar.Sumayya ta ce “Ina nan ƙalau, lafiya kuwa? Na ji kamar kina numfashi da ƙyar, ciwon ne ya tashi””Sumayya na kusa mutuwa yau” tayi maganar tana sauke numfashi.A rikice sumayya ta ce “Mutuwa kuma, lafiya””Na haɗu da Viper, ya kusa kashe ni”Ras gaban sumayya ya faɗi, indabo ya ƙura mata ido, yayi mata alama ta cigaba da wayar.Jiki a sanyaye Sumayya ta ce “To maƙaryaciya, ni zaki jirga?””Wallahi ba ƙarya nake yi ba, ya na ji muryarki kamar wadda aka ritsa, kin je hirar ne? Ko wani abun ya faru ne?”Sumayya ta ce “A’a, maƙaryaciya, mutumin da ake nema ruwa a jallo ki ka gani bai kashe ki ba?””Ban sani ba, tun da kin ƙaryata ni ki je ki ƙarata, ina fatan dai mutumin nan bai yi miki wani abun ba, dan mutumin nan yayi ruwan ƴan iska”Kallonsa sumayya ta yi, sannan ta ce “Mu haɗu a gida”Nabila ta ce “Ai dole mu haɗu yau, akwai magana, zan biya asibiti numfashin zai ɗauke, ki kula da kanki dan Allah, jikina yana bani kamar akwai matsala a in da ki ke, idan da wani abu, ki sanar da ni” “Ke normal ne, sai mun haɗu” ta kashe wayar tare da kallon honorable Indabo ta ce “Wallahi ƙarya take yi, ba wani Viper da ta haɗu da shi, yayanta ne jami’in tsaron da yake bincikensa, amma wallahi ƙarya take yi”Cikin ko in kula, indabo yayi dariya ya ce ce “Wato na yi zubin ƴan iska, wato a rayuwata ni mutum ne mai sa’a, na tsinci dami a kala, yanzu ke zaki yi mini aikin ba ita ba.Dole ki tabattar idan da gaske take ko akasin haka ki sanar mini, duk wani aiki ko bayanai da nake son samu, ke zaki nemo shi a wurinta, idan ki ka saɓa umarnina kuma, zan saka a kawar mini da ke da ita baki ɗaya!”Sumayya gabanta ya faɗi, ta rasa abun yi, kamar ta kurma ihu, wannan wace irin ƙaddara ce, ace babban mutum kamar wannan da ake ji da shi a kujerun iko, na ƙasa da jihar nan, ya rasa wanda zai saka a gaba sai su ƴaƴan cikin sa.Ya ce “Buɗe wayarki ki bani” tamkar shashasha, haka ta cire password ta miƙa masa, yayi ƴan danne danne a jiki.Wani mutum ne yayi sallama, ya shigo, ya ce “Gani sir””Wannan wayar zaka yi wa aiki”Ya ce “Ok sir” ya karɓi wayar yana daddanawa, sannan ya miƙowa Indabo.Ya ce masa “You can leave”Ya miƙa wa Sumayya wayar ya ce”Daga yanzu za ki din ga karɓar umarnin, abun da ake buƙatar ki yi, idan ki ka saɓa umarnin, zaki yi dana sani mara amfani, dan sai na fara da wulaƙanta rayuwarki, na tozarta ki, kodayeke dama wulaƙantacciyar ce. Dan ku ƴaƴan talakawa baku da wani amfani, kuma babu wani abu da zai faru idan na salwantar da rayuwarki, da kuma ta ta”.Sumayya ta sunkuyar da kanta ƙasa, ƙirjinta na cigaba da bugawa.”Tashi ki je sakatariyata zata sallame ki”Sumayya ta tashi jiki babu ƙwari, ta bar ɗakin, tana tunanin wace masifar suke shirin shiga ita da Nabila. Allah wadaran bakin Nabila da bashi da saiti wasu lokutan.Shi kuma yana babban mutum, menene alaƙarsa da wani Viper, wai shi waye ma wannan vipern, da ya fi kuɗi wahalar samu?Tana fita sakatariyar ta miƙe tana murmushi ta ce “Har kun gama?”Sumayya ta ce “Eh”Ta miƙa mata envelope ta ce “Ga wannan ya ce “A baki”Sumayya ta karɓa ta duba, kuɗi ne maƙudai a ciki, gabanta ya faɗi, tabbas idan ta karɓi kuɗin nan, ta tabatta sai ta din ga bin umarninsa, gashi ba ta san wane irin umarni za a bata ba.Ajiye envelope ɗin ta yi ta ce “Ba na so”Ta nufi hanyar fita, tana tuna yadda ya kirata da wulaƙantacciya.Tana gaggawa ta kai ga ƙofar da zata fitar da ita waje, mutumin da ya karɓi wayarta ɗazu, ya sha gabanta, wanda hakan ya tilasta mata tsayawa.Ya ƙare mata kallo sannan ya ce “Kamar yadda honorable ya gaya miki, ke zaki yi mana aiki a zahiri, bama buƙatar ta san kina yi mana aiki, dan haka ko kin karɓi kuɗi, ko baki karɓa ba, baki da zaɓi dole sai kin yi komai kasadarsa, ko da kuwa yana nufin sanya rayuwar ƙawarki a siraɗin rasa ranta, zamu yi amfani da ita, idan kuma kin zaɓeta zaki iya rasa taki rayuwar”Cikin matsananciyar damuwa Sumayya ta ce “Muna mata, menene alaƙarmu da ƴan daba, wannan ba aikin hukuma bane ba?”Yayi murmushi ya ce “Shi zaki gayawa hakan ai tun a ciki, idan kuma zaki kai wa hukumar ne, ga fili ga mai doki”Wani abu mai ɗaci, ya tokarewa sumayya a ƙirji.Cikin ɓacin rai ta ce “Amma dai ba ku yi mana adalci ba, wannan tamkar rusa mana rayuwa ne, tayaya muna ƴaƴa mata zaku yi tarkon kama mutum mai irin wannan hatsarin da mu””Ai ba ke aka ce ba, ƙawarki aka ce, dan haka ina kina son lafiyarki, da mutuncinki, kiyi abun da aka umarce ki, ita ranar biyan buƙata, rai ba a bakin komai yake ba. Ki yi ta kanki kawai, idan har ki ka yi abun da aka buƙata, babu wata alfarma da zaki nema a ƙasar nan ki kasa samu, zaki zama ɗaya daga cikin yaran honorable, za ki yi kuɗi, zaki ɗaukaka za kuma ki shahara, ki nutsu ki yi tunani da kyau, kar ki yi wawanci, ki je aikinki ya fara daga yanzu”Shiru ta yi tana kallonsa, har ya gama maganganun da zai yi, sai dai gaba ɗaya ta rasa wani tunani ma yakamata ta yi.Ba ga ce uffan ba, ta raɓa shi ta buɗe ƙofar ta fice.A cikin mota, direban gidan radiyon, da wanda suka rakota suke tambayarta, yaya program ɗin ya kasance?.Cike da basarwa ta ce musu lafiya ƙalau.Kafin su ƙarasa gidan radiyon, ta ce su sauketa, tana da uzuri, dan haka ta sauka, ta kira Nabila a waya.Tana kira Nabila ta ɗaga, “Yaya kina ina ne? Kina asibitin ko kin tafi gida?”Nabila ta ce “Ina can, wai sai bayan 2-5hrs za su sallame ni, idan na zama stable, haryanzu numfashi yana bani wahala””Ok to gani nan zuwa””To masoyiyya Allah ya kawo ki lafiya”Sumayya ta sauke wayar, kamar ta fashe da kuka, duk yadda take da Nabila, ace ta ha’inceta, ta saka rayuwarta a hatsari, anya amana ta ce haka kuwa?.A haka ta ƙarasa Asibitin, ta tambayi ɗakin da Nabilan take, aka nuna mata.Nabila na ganinta ta ce “Oyoyo sumyna”Sumayya tayi murmushin yaƙe ta ce “Ya jikin?””Alhamdilillah da sauƙi””Baki kira kowa a gida ba, na ganki ke kaɗai?”Nabila ta ce “Rabu da ni, ba wanda na kira, ƙarshe dai walida ko baba magajiya ne za su zo, dama da DSP yana gari ne, to shi ma wai ya tafi workshop ko me oho dai, Abuja ya tafi, dama da zai zo, to sai anty, ni kuma bana son takura musu, sai dai ba yadda na iya, na gaya wa Abba, kar su ji ni shiru. Amma ya na ga kamar kin yi kuka? yaya program ɗin?”Sumayya ta ce “Wani irin kuka ana zaune ƙalau, program lafiya ƙalau, ga recording ɗin ma ban kai ba, na ce bari na zo na fara ganinki tukuna”.Nabila ta haɗe fuska ta ce “Ki gaya mini idan wani abun yayi miki, mu san abun yi, na gaya miki ni gaba ɗaya mutumin nan bai yi mini ba, dai-dai nake da shi idan wani abun yayi miki, in yi fito na fito da shi, sai in da ƙarfina ya ƙare.”Sumayya ta haɗe rai ta ce “Ke da ya yi mini wani abu kya gannin a haka, ba wannan ba, maganar da ki ka gaya mini a waya, da gaske ki ke ko kuwa?”Nabila ta yi murmushi ta ce “Baki yadda ba ko?””Yaya za ayi na yadda, mutumin da ake ta fafatukar yaya za a kama shi, ki ce mini kin haɗu da shi, kawai in yadda ta yaya?”Nabila ta kaɗa kai ta ce “Kusan watana guda zuwa na biyu ma, kawai ina fafutukar yaya zan ganshi, na san dama zaki ƙaryata ni, ban gaya miki ba ma balle ki hana ni ko ki yi mini masifa. Amma cikin ikon Allah, viper ya bar mini shaidar da zai tabattar da ya ganni”Cikin rashin fahimta, sumayya ta ce “Kamar yaya?”Nabila ta ɗaga rigarta, sai ga plasta a gefen cikinta, ta saka hannu ta cire plastan, sai ga rauni a wurin.Sumayya ta waro ido, tare da rufe baki, ta ce “Na shiga uku, Nabila kin haukace ne? Wai dama da gaske ki ke?”Ta saki rigar ta ce “Ai kafin yayi mini haka, rannan karnuka sun kusa yin watanda ta. Sunayya gayen nan ya wuce duk yadda nake tunani, ashe faɗar sunansa ne a baki kawai mai sauƙi, wallahi idanunsa sun kusa sakani fitsari a wando, sumayya yaya zan kwatanta miki yadda yake ne ki gane abun da na gani? Kwarjininsa ya wuce duk yadda zan kwatanta miki, wallahi da ya shaƙe ni, na ɗauka mutuwa na yi””Har shaƙe ki yayi, kin ga Nabila ki rufa mana asiri, amma yaya aka yi ki ka samu in da yake?””Na gaya miki kusan watanni biyu kenan ina nemansa, na san idan na gaya miki, hana ni zaki yi, duk ba wannan ne ya dame ni ba, yayi alwashin idan ya sake ganin fuskata, sai ya kashe ni, kuma mummunar kasada na kuma tafkawa Sumayya”.”Ta me kuma?!”Wayarsa na sato, kan na taho!”.Alhamdilillah, duka duka a nan mu ka kawo ƙarshen free pages, mu kasance a cikin paid pages, domin jin ainihin gundarin labarin *ƘARFE A WUTA*.
₦500 ne kacal ta wannan account ɗin, masu so ta private special group 1k zasu saka a wannan account ɗin.
0009450228 Aisha Adam jaiz bank
Ayshercool.
08081012143
