Fentin Zina Page 17 Hausa Novel
***Kallonta da kyau inna tayi daga sama har kasa tace waya baki kudi?.Kasa tayi da kanta tace tun lokacin can da baba malam ya bamu nida fateema ban taba su ba.Toh shikenan wuce ciki.Tayi iya kokari wajen boye yanayin tafiyarta amma duk da haka bata tsira ba don tana dap da shiga daki inna tace.Dingishin meye kike yi?.Bata juyo ba amma ta tsaya tace gurin fitowa daga shagon ne na buge kugu na a jikin wani karfe ta samu kanta da shararo karya.Jinjina kai inna tayi tace Allah ya kiyaye gaba.Fateema bata farka ba har yanzu hakan yasa ta zauna a gefen gadon tana sakin ajiyan zuciya yayinda take cike da fargaban abunda zai biyo bayan tarawar su da Ahmad.Har tsawon sati guda kenan rabon data yi waya dashi domin fateema tasanya matakan tsaro sosai a wayarta kasan pillon ta take saka shi idan zata yi bacci ta yadda da an taba zata ji mutum hakan ya matukar damun Ameena ta rasa wace hanya zata bi wajen yin magana da Ahmad din.Yau kuwa tayi sa’a fateema ta shiga wanka ta manta wayar a dakin kuma zata dan jima saboda har wanke kai zatayi.Daukar wayar tayi tayi dialing number shi.Lokacin yana wani wurin shakatawa da abokin shi flashing dinta ya shigo gajeren tsaki yaja kafin yace na riga da na gama da babinki domin bana amfani da abu so biyu.Abokin ya kalleshi yace kaddai wannan yarinyar daa kake fada mun ne?Itace in fada maka ai ban kyale taba har sai da ta fada tarkona yanzu kuma na gama da ita bata da wani sauran amfani a wajena barima kaga in kirata in mata kashedi mai girma kada ta sake gigin nema na.Ya fada daidai lokacin wani flashing din na Shigo wa yace ‘yar naci kana ya bi bayan kiran.Daga ta bangarenta tayi murmushi ta daga ta sa a kunne tace bakaji yanda zuciyata ta dinga bugu da sauri da sauri ina fargabar kada baka kira ba har mai wayar ta zo ta tadda ni.Dakata malama ba wannan ne yasa na biyo bayan kiran ki ba kin fahimta.Subhanallahi, innalillahi wa inna ilaihi raji’un dan Allah kada ka mun wasa da irin wannan abun ba shida hurumi anan.Ke bude kunnen ki ki saurare ni da kyau, ni ba sa’an wasan ki bane kucaka dake wawuya daga rana irinta yau kada ki sake yin gigin kiran numberna idan ba haka ba zanyi maganin ki sai kinyi dana sanin sanina a rayuwarki sai kinji inama ba’a haife ki a duniyar da ni Ahmad nike ciki ba.Dan Allah Ahmad ka tsaya ka saurare ni ka fada mun idan ma wani abu nayi maka sai in baka hakuri mu cigaba da rayuwar mu kamar da kasan zuciyata bazata iya jure rabuwa dakai ba dan Allah kada ka mun haka.Ke kin dauka wai son ki nake? Bari kiji ko matsayin mai aikin gidan mu bazan daukeki ba kazama dake bare ni na so ki Allah ya kiyaye, dama na rabeki ne domin cikar burina kuma na gama sai kuma ince umma ta gaida ashsha yaushe ma zanyi gangancin auren yarinyar da zata ba saurayinta jikinta saboda dadin soyayya kawai? Idan ma hakane tunaninki toh kinyi kuskure, bazaki sake ganina ba har abada, yana gama fadin haka ya kashe wayar.Kuka sosai Ameena ta fashe dashi yi takeyi kamar ance mata inna ko baba malam wani ya rasu.A haka fateema ta shigo ta sameta cikin sauri ta karaso cikin dakin ta zauna kusa da Ameenan tace adda lafiya meya faru? Me aka miki?.Kukanta ta cigaba dayi kamar zata shide, ganin haka yasa fateemar tashi tsaye tace barin kira inna kilan ita ki iya fada mata abunda ke damun ki, ta yunkura kamar zata fita Ameena ta capko hannunta ta zaunar da ita tace ki rufa mun asiri kada ki kirata fateema.Ta gyara zama tana kallon addan nata tace naji bazan kirata ba amma sai kin fada mun abunda ke damun ki.Ameena taja hanci ta goge hawayen dake tsiyayo mata tace fateema na cuci kaina na shiga uku na lalace bana jin zan ci gaba da rayuwa a duniyar nan dan Allah idan na mutu ki rokar mun yafiya gurin inna da baba malam ta fada tana kara rushewa da kuka.Wannan karon fateema ta tsorata sosai itama hawayen ta fara yi tana cewa adda ki fada mun meke faruwa dan Allah duk kin tsoratani kina neman zautar dani kinsan bana son damuwan ki.Fateema ina cikin halin ibtila’i, yanzu na dauki wayarki na gwada kiran Ahmad domin inji ya yake amma ya rasa me zaice mun sai shi ya daina soyayya dani bazai iya aure na ba, bayan duk wuyar dana sha akan shi gurin inna da baba malam.Ajiyar zuciya fateema ta sauke tana fadin Alhamdulillah nagode wa Allah dajin wannan labarin aike adda bai kamata kiji kin damu ba Allah ne ya cece ki daga fadawa tarkonsa shiyasa da kanshi ya ce ya fasa auren naki, Allah zai kawo miki wanda yafi shi.Girgiza kai Ameena tayi tace abunda ciwo wanda ka yarda dashi yaci amanar ka, amma a zuciyarta tace bazaki gane girman cutan da Ahmad ya mun bane a rayuwata.Anan fateema tayi ta bata baki har dai taga ta sake, ita kuma Ameena ta sake dinne don kada fateema ta matsa mata da tambayoyi har dai ta gane gaskiya.Kwanaki sunata tafiya wata rana Ameena ta tashi da matsanancin zazzabi sai dai taki barin kowa ya gane harta fateema da suke yini su kwana daki daya, tambayar inna tayi akan tana son zuwa gidan wata ‘yar ajinsu anan kusa dasu, inna bata hana ba tunda lokacin an cire mata takunkumin da aka mata ganin bata nuna alamun Ahmad na tare da ita ba kuma ita yarinyar tana yawan zuwa gurin Ameenan.Ta shirya ta fito tama inna sallama, inna tace kada ki dade dai ki dawo da wuri.Toh inna, tasa kai ta fice, wani almariji ta gani ta rokeshi ta nuna masa chemist din gabansu tace dan Allah ko zaka iya siya mun abu a shagon nan.Yace eh kawo.Dari Biyar ta ciro ta bashi ta bashi wata karamar paper tace in kaje kace a baka abunda ke rubuce a nan.Karba yayi yaje bai jimaba ya siya ya dawo ya bata ya mika mata chanjin tace kabar shi kawai ka rike a hannunka.Godiya ya mata ya wuce yana jin dadi.Sallama tayi a kofar gidansu zulaihat, mamarta ta amsa ta karasa ciki ta tsugunna ta gaida maman zulaihat din.Ki shiga tana ciki yanzu ma ta shiga.Ok kawai tace ta shiga, duk abunnan jikinta a matukar sanyaye yake da tarin tunanuka a cikin kwakwalwar ta.A falo sukayi kicibis da zulaihat din, tsalle zulaihat tayi ta rungumeta tace kamar kinsan ina ta tunanin ki kuwa dazuma nike fadawa mummy insha Allah gone zanje gurinki.Ai kuwa gani nazo kin huta zuwa.Mu shiga ciki mana.Tare suka shiga dakin da yake mallakin zulaihat din.Zama sukayi zulaihat taki daina fara’a tace gaskiya naji dadin zuwan nan naki sosai.Murmushin yake tayi tace nima naji dadi dana zo, zaman gidan ne ya isheni kinsan ni ban ciki mu’amala da mutane ba duk cikin ajin mu dake kadai na yarda saboda tarbiyyarki.Hakane nima baki ga ke kadai na likewa ba, ta mike tsaye tace ina zuwa dan Allah minti biyu.Bata jima da fita ba ta dawo dauke da plate din fried rice da lemun exotic.Tana ganinshi taji ranta ya biya, zulaihat ta ajiye tace bismillah ta nuna mata abincin ta tsiyaya mata exotic din a kopi.Ta cinye kusan rabi da kwatan abincin tana godiya a zuciyarta don rabon data ci abincin daya mata dadi tun kafin awkuwar lamarin su da Ahmad.Zulaihat tana kallonta ta fahimci akwai abunda ke damunta domin ba haka take ba, yanayinta ya nuna hakan ga fuskarta tayi fayau kamar wacce tayi wata tana ciwo.Saida ta bari ta gama ci ta natsu tukun tace zan iya tambayar ki? Amma kada kice na shiga al’amarin da bai shafeni ba.Kallonta Ameena tayi tace kada ki damu, ina sauraren ki.Tunda kika shigo gidan nan kallo daya na miki na fahimci akwai abunda ke damunki shiyasa zan rokeki dan Allah idan zai yiwu in kina ganin babu matsala zaki iya fada mun meke damun ki?.Shiru Ameena tayi tana tunani, hakika a wannan halin da take ciki bazata iya solving matsalarta ita kadai ba, tana da bukatar mai bata shawara ga yanzu da tazo gurin zulaihat data kawo mata maganar taji ta gamsu da zulaihat ta yarda zata iya rufa mata asiri don haka ta sauke ajiyan zuciya ta kalli zulaihat idanunta na tara kwalla tace zulaihat naji na yarda dake na kuma amince dake zaki rike mun sirri bazaki bari wani yaji koda kadan daga sashen maganar ne sai dai ina bukatar jin tabbaci daga gare ki ina so ki daukar mun alkawari babu wanda zaiji koda tsakanin kanki da kanki ne.Na miki alkawarin rike miki amana da alkawari zan rike sirrinki zan hana shi bayyana sai in kece da kanki kikaji cewar ya dace ki fadawa wani kada ki manta duk wanda ya rufawa wani asiri shima Allah zai rufa masa nasa asirin.Na yarda dake zulaihat.Nan ta soma bata labari tiryan tiryan tun daga farkon haduwar su a fagen da ita zulaihat din bata sani ba ta bata har zuwa yau.Salati zulaihat tayi tace gaskiya kinyi kuskure mafi girman kuskure ma kuwa, har yaushe zaki sakankance ki saki jikinki ga na miji har kikai ga aikata zina don kawai tsoron kada ki rasa shi, wannan ba daidai bane sai dai kaddara ta riga fata abunda ya faru ya riga ya faru saidai mu nemi mafita kawai.Na sani zulaihat! Wallahi na san na tabka kuskure a rayuwata sai dai addu’ah ta Allah yasa kada abunda nike zargin ya kasance idan ba haka ba na shiga uku wallahi inna kashe ni zatayi bare kuma baba malam ki taimake ni.Kinga Ameena ki natsu musan abunyi don idan baki cikin natsuwarki baza mu iya zartar da ko wani irin hukinci ba, yanzu dai abunda ya kamata shine kiyi gwajin ciki.Ta numfasa tace nayi tunanin haka shiyasa dana fito na siya wannan PT strip din karfin in karaso nan.Ta fada tana nuna mata shi a ledar data siyo shi.Kinsan yadda ake yin gwajin ne? Zulaihat ta tambayeta tana tsire ta da ido.Ban sani ba, ban taba mu’amala da abun ba amma dai basan zasuyi prescribed din yadda za’a yi amfani da shi sai muyi yadda suka ce.Toh shikenan.Nan ko suka bi duk irin procedures din da suka gani a jikin takardar abun suka tusa tsinken a gaba suna jiran ganin sakamako.Gabana faduwa yakeyi inama ace mafarki nakeyi wani ya tasheni yanzu.Daidai lokacin da ta karasa wannan maganar daidai lokacin da mararta ta murda sakamakon ganin layi biyu a jikin tsinken wanda ke nuni da cewar lallai tana da juna biyu.Salati kawai ko waccensu keyi a zuciya musamman ma Ameena da numfashinta, jinta da ganinta suka dauke gaba daya na wucin gadi.Jijjigata zulaihat tayi ganin kamar batama cikin duniyar.A firgice ta daga ido ta dubi zulaihat din tace zulaihat kice mun mafarki nakeyi, wayyo Allah na, na shiga uku na lalace wayyo na bonu, Allah ya isa tsakanina da kai Ahmad bazan taba yafe maka ba har abada ka cutar da rayuwata Allah kadai ne zaiyi sakayya da hisabi a tsakanin mu.Dafa kafadarta zulaihat tayi tace ki kwantar da hankalin ki mu nemi mafita tun da wuri, me kike ganin ya kamata muyi.Share majina tayi tana jan hanci tace zulaihat har sai ma kin tambayi me zanyi? Ai banida wani abun rufin asiri yanzu daya wuce in zubar da wannan cikin domin zaman shi a jikina zai iya zama silar abubuwa da yawa.Kada kice haka, kada kiyi yunkurin aikata wani laifin bayan wanda ke kanki bai goge ba, zubar da ciki ba shine mafita ba, mu kira shi Ahmad din in yaso zamu san abunyi na gaba daga nan. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️


