Uncategorized

Abban Sojoji Page 52 Book 2 Complete Novel

 

“`The father Of Soldiers“`

 

Story &  Written 

       By 

      Hafsat Bature

_💋Boss Bature💋_

Join this link to follow my tiktok acct👇

  

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

Lokaci guda Amal ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya,ashe magen hayam ce ta faɗo ɗakin,sai faman kuka takeyi miyauu miyauu,da alama yunwa take ji ne,Batare da 6ata lokaci ba Amal ta zuƙunna ta shiga tattara kuɗin da sauri da sauri jikinta na kerma,don a matuƙar firgice take saboda magen nan data tsorata ta oi,

  MiÆ™ewa tayi hannunta É—auke da kuÉ—in cikin sauri ta fice daga É—akin,komawa tayi cikin É—akinsu hayamm,jiki na rawa ta buÉ—e wardrobe É—in kayansu,doguwar riga ta É—auko ta Abra tare da mayafinta,

A hanzarce ta shiga zura rigar ajikinta,ba ƙaramin yawa rigar tayi mata ba har ƙasa take ja,ga wuyar rigar da yayi mata yawa,yafa mayafin tayi,

  Sannan cikin sauri ta fito daga cikin É—akin,a nan waje Æ™opar É—akin ta É—auki slippers tare da zura wa aÆ™afarta,

   Jiki na kerma AMAL ta kama hanyar fucewa daga cikin gidan,sai da takai baÆ™in Æ™opar fita sannan ta É—an tsaya tare da juyawa tana kallon cikin gidan yayin da hawaye ke shararowa daga idonunta,bazata ta6a mantawa da irin uÆ™ubar da tasha acikin gidan ba, ta dan jima a haka,daga bisani tasa kai cikin sauri tabar gidan,

   Kamar walk’iya haka Amal tabar santar gidan gaba É—aya,duk da bata jin kwarin jikinta,haka ta jure ta kama hanyar sauri sauri gudu gudu,ita kanta batasan ina zata dosa ba,amma tana da tabbacin cewa tasha zata nema domin ta hau motar zuwa Abuja,

…(Finally Amal taci nasarar barin gidan,saura fatan sauka lafiya)

DUBA WANNAN>> Yadda Zaki Magance Kaikayin Nono

*****************

Sosai jahan ke ta faman sakin dariya cike da nishaÉ—i,bakomai yasa shi dariya ba face Ayaan dake zayyana mashi irin halin daya shiga na barazanar da haroon ke masu,hankalin su kwance basu da wani sauran damuwa,suna a kwance cikin hotel room É—insu,basu jima da fitowa daga wanka ba,kowannansu na sanye da white shorts ajikinshi,suna rungume da juna cikin lallausan bargo,

  “Wlh jahan naji jiki sosai,wai ashe haka abun yake?sai gani a sume,gaskiya haroon ba Æ™aramin shaiÉ—ani bane,nasha Wahala a ranar nan,”

     “dama kai rago ne Ayaaan,nafi ka juriya shiyasa abun yazo maka ahaka,ranar naji kishi da baÆ™in ciki sosai,har yanxu in na tuna abun ba Æ™aramin Æ™una zuciyata ke yi mun ba,”acewar jahan,

   “Pls ni banaso muna tuna abunda ya wuce,hakan zai iya sanya mana damuwa acikin zuciyoyin mu,mubar maganar kawai,”

  Jahan yace”shikenan mu bar maganar amma inaso na tambayeka pls,yanzu kwatsam a lokacin nan da ace bamu ba haroon kuÉ—in nan ba,ya saki videon mu a social media har Abba da babban yayanmu suka gani,me kake tunanin zai biyo baya,”

  Da wasa jahan yayi maganar amma har sai da zuciyar Ayaan ta É—an buga,

   “Abunda zai faru shine,zuciyar Abban mu zata buga anan take ya yanke jiki ya faÉ—i,babban yayan mu kuma zai yi mana bugun mutuwa,abunda ba’a fata kenan,”Ayaan ya Æ™arasa maganar yana dariya, 

    Shima jahan dariyar yayi yana cigaba da sauraron shi kafin daga bisani suka É—aura daga inda suka tsaya,”

   

**************Sehrish

Tun bayan da tadawo cikin bedroom É—inta,wanka tayi tare da É—auro alwala,bayan ta kammala sallar,ta koma wurin wardrobe É—inta,ta ciro kayan da zata sanya,dogon wando ne na roba,Army trouser tun lokacin da suka je siyayya,ta É—auke shi saboda ba Æ™aramin burgeta kayan sojoji suke yi ba,tare da farar shirt off shoulder ta zura ajikinta,ba Æ™aramin kyau tayi ba,komawa tayi gaban dressing mirror ta É—auki turarenta tabi ko’ina na jikinta ta feshe shi,wuri ta samu saman chair É—in da ke a front É—in madubin,ribbom É—inta ta É—auko tare da zura shi a hannunta,yau taci alwashin saita É—aure gashin kanta,

da iya ƙarfinta na ƙarshe ta tattare gashin ta haɗo shi wuri guda,tare da zura ribbom ɗin ta ɗaure shi sosai,ya sauko a gadon bayanta,

 • Also Download Abban Sojoji Book 2 Complete Hausa Novel Document
 •    Murmushi ta saki tana kallon kanta acikin mirror É—in kafin daga bisani ta miÆ™e tare da wuce wa gaban gadonta,within 15 mins ta kammala gyara bedroom É—inta,komawa tayi tare da hayewa saman gadon,takai hannu ta É—auko wayarta dake ajiye saman side drawer,

     Wi-fi ta kunna nan take messages É—in whatsapp dinta suka soma shigowa acikin wayarta,shiga whatsapp grp tayi na school É—insu,new student ne ke ta introducing É—in kansu tare da pics É—insu,tunani ta soma yi bata da hoto ko É—aya,gashi tana buÆ™atar pictures saboda ita ma tayi nata introduction din,

     tana cikin wannan tunanin kiran junaid ya shigo wayarta,cikin sauri tayi picking tare da karawa a kunnanta,

    Tun kafin tayi sallama yace”yunwa nake ji,”yana faÉ—in hakan ya katse kira,murmushi Sehrish tayi tare da cewa”shagwa6a66e kawai”

    Ajiye wayar tayi saman pillow sannan ta miÆ™e tare da saukowa daga saman gadon,sam ta manta bata yafa mayafi ba,saboda saurin da take yi nata kai mashi tadawo don tayi pictures din,takalmi kawai ta zura a Æ™afarta,sannan ta buÉ—e Æ™opar ta fita,

    A natse take tafiya hanyar kitchen ta nufa,wayam babu kowa a main palour É—in da alama duk suna cikin bedroom É—insu wasu kuma sun fita,

     Batare da 6ata lokaci ba ta haÉ—o mashi cornflakes tare da snacks acikin tray,kai tsaye ta wuce upstairs bedroom É—inshi,

    Tsayawa tayi tare da yin knocking Æ™opar bedroom É—in nashi,

    daga ciki tajiyo muryarshi yana cewa”a buÉ—e take fa,just come in,”

    a hankali ta tura door din tare da shiga cikin É—akin nashi,

    yana tsaye agaban mirror waist É—inshi na É—aure da farin towel da alama fitowarshi kenan daga wanka,

     Æ™arasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray É—in asaman table din dake kusa da gadon shi,

     Juyowa junaid yayi daga gaban mirror É—in da yake,zuba mata ido yayi yana kallon bayanta,wandon jikinta ba Æ™aramin fidda mata shape É—in jikinta yayi ba,

  KARANTA>> Cututtukan Dake Hana Mace Jin Dadin Jima’i

    takawa yayi a hankali ta bayanta ya tsaya sannan yakai hannunshi tare da ruÆ™o lallausan sumar kanta,a firgice Sehrish ta juya tana kallon shi,sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi yayi,

    A hankali ta ambaci sunan shi”junaid”!

    bai amsa mata kiran sunan shi da tayi ba,sai cewa yayi”reesh ina mayafin ki yake ne”?

     Sai lokacin ta tuna cewa bata yafa komai ba ajikinta ta fito,

     “Mantawa nayi ban sanya ba,”ta bashi amsa tana kallon fuskarshi,

    “Kinyi kyau sosai,but pls kada ki Æ™ara fitowa haka batare da mayafinki atare da ke ba,”ya Æ™arasa maganar cikin sanyin murya,

    Har lokacin bai saki wutsiyar gashinta ba daga hannun shi,sai faman murza gashin yake acikin hannun shi,

    Sakin gashin yayi tare da zagayawa da hannun shi ta bayanta,ya zame ribbom É—in dake akanta,nan take sumar kan ta tarwatse abayanta,duk tana tsaye tana kallon shi batare da ta hana shi ba,

     tura hannunshi yayi acikin lallausan gashin kan nata,wasa ya shiga yi mata dashi,ganin abun nashi ba mai Æ™arewa bane yasa tace”junaid wai menene haka?kamar wata Æ´ar baby ka kama mun sumar kai sai murzawa kake yi,”

     Murmushi yayi tare da cewa”kwarkwata nake son cire maki,don nasan baza a rasa su acikin kan nan naki ba,abunda baki sani ba su suke saki yawan mantuwa,” 

    Buge hannun shi tayi tana dariya tace”wlh ka 6aci da Æ™arya junaid,bansan waya koya maka Æ™arya ba,” 

    tayi maganar tare da wuce wa tana nufar hanyar fita daga É—akin,cikin sauri yakai hannu tare da ruÆ™o nata acikin nashi yace”pls kada ki tafi,ki tsaya na kammala lunch É—in mana,inyaso sai mu fita atare,

      Batare da musu ba tace”bazan tafi ba amma zan fita daga waje,idan ka kammala sanya kayan saina shigo,”

      Æ™arasa maganar tayi tare da fucewa ta tsaya daga waje tana jiran shi,

  Shaf shaf ya kammala shirya wa cikin jeans da t shirt,sannan ya samu wuri daga gefen gadon ya zauna tare da kwala mata kira,

     dawowa ciki tayi tare da takawa zuwa gefenshi ta zauna,

     “Sehrish inason magana dake,”

        

  Yanayin yarda junaid yayi mata maganar da wata irin kasalalliyar murya yasa ta jin faÉ—uwar gaba batare da sanin dalilin hakan ba,

       Cikin sauri ta juyar da fuskarta tana kallon cikin idanunshi tace”menene junaid”

    Æ™ara matsawa yayi kusa da ita,fuskarsu ta kasance a kusa data juna,numfashinsu har harhaÉ—ewa yake dana juna don Æ™iris ya rage tsinin hancin shi ya ta6a nata,hakan ba Æ™aramin tsorata sehrish yayi ba,tun da take arayuwarta bata ta6a ganin fuskar junaid da irin wannan yanayin ba batare da Murmushi ba,sam babu murmushin nan a fuskarshi,

    Cikin en ina sehrish tace”..junaid wai menene haka?me yake faruwa ne”? 

    Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi tare da sake buÉ—esu a hankali ya furta”I LOVE U REESH,I wanna be with u,for the rest of my life,” in serious matter junaid yayi maganar,amma sai Sehrish ta fashe.da dariya kamar kamar me,

     Mamakine ya kamashi ganin tana yi mashi dariya,

    MiÆ™ewa tayi daga saman gadon nashi tana ci gaba da yin dariyar,dakyar ta tsagaita tare da kallon shi tace”gaskiya junaid ka iya wasan kwaikwayo,wlh ni har gabana ya faÉ—i duk atunanina wani abun kirki ne ashe zolayar taka ce ta motsa,”

    Hankali atashe junaid ya miÆ™e tsaye yana kallonta yace”reesh nifa ba wasa nake maki ba,inason bayyana maki irin tsananin son da nake maki ne,”

     Muryarta Æ™umshe da dariya tace”wlh junaid da ace kai actor ne acikin film ba Æ™aramin Æ™ayatarwa zaka yi ba,saboda ka iya tsara wasan kwaikwayo,”

     Tana kai Æ™arshen maganarta,ta kama hanya da sauri ta fuce daga cikin É—akin nashi tana Æ™arashe dariyarta,

    Jiki a mace junaid ya koma tare da zaunawa saman gadon,

     jinjina kai yayi tare da cewa”tashin hankali!ashe irin kallon da sehrish keyi mun kenan!yanzu taya za’ae na bayyana mata irin yarda nake ji a game da ita? 

    Ya jima yana wannan tunnanin aranshi kafin daga bisani ya mayar da idanunshi akan cornflakes É—in da ta haÉ—o mashi,.  

    A sanyaye yakai hannu tare da É—aukar spoon É—in dake acikin cup din,ya fara É—ebowa yana kaiwa bakin shi,

  adai dai lokacin da  Sehrish ke gabda shiga Corridorn da É—akinta yake Sgr ya fito waya kare a kunnan shi,da alama waya yake yi,karaf idonshi ya sauka akan bayanta wanda lallausar gashin kanta  ke baje har wurin Æ™ugunta,don bata maida ribbom din da junaid ya cire mata ba dama dakyar ta É—aure shi É—axu,Æ™arasa fitowa yayi slowly ya dafa handrail da hannunsa guda har lokacin yana amsa wayan da yake yi, yayin da blue eyes dinsa ke bin bayanta da kallo, ba komae ne ya ja  hankalin shi ba face Army trouser din dake jikinta don ba Æ™aramin kyau yayi mata ba dama kuma favorite color dinsa ne……

  _💋Boss Bature💋_

  Wuraren biyu na rana hossana tafarka daga dogon baccin daya É—auketa,miÆ™ewa tayi daga kwancen da take asaman sofa,sai faman hamma takeyi tana murza idanunta, a hankali ta ware idanunta tana neman Omar da bacci yayi awon gaba dasu,wayam tagani babu shi alamar ya tafi bataso hakan ba, dakyar ta iya tashi daga saman sofa din,tana tafiya a hankali saboda jirin da take ji,ga wata irin Yunwa dake cin ta, 

    Bedroom É—insu ta shiga,a nan ta samu jahad zaune saman darduma ta jima da kammala sallar Azhar,amma bata bar saman sallayar ba,tana zaune zugum tana tunanin duniya,

    Jin alamar tafiyar mutum yasa ta juyowa tana kallon hossana dake tunkarato,

    Ƙarasawa tayi wurin jahad tare da zuÆ™unnawa kusa da ita tace”jahad ashe ya omar ya tafi bai tashe ni ba,ko sallama ba muyi ba,”murya a kasalance ta Æ™arasa maganar,

    murmushi jahad tayi tana kallon fuskarta tace”kada ki damu,in dae ya Omar ne zaki iya ganin shi da anjima ko da daddare ma,”

   Ta Æ™arasa maganar tare da cewa”ko kina jin yunwa ne?naga kina ta hamma”

     “E inaji sosai,’ta bata amsa,

  Jahad tace”Okey,yanzu nake shirin tashi na shiga kitchen in girka mana abunda zamu ci,amma kafin nan ki fara É—aukar fresh milk a fridge sai ki haÉ—a da wani abu kisha,sannan in kin kammala kiyi sallah,gashi har time ma ya wuce,’ 

    amsa mata tayi da toh,sannan ta miÆ™e tare da fucewa daga bedroom É—in,

   Murmushi jahad tayi tare da cewa”nan ba da jimawa ba zamu sha bikin Amarya hossana tare da bride É—inta ya Omar,”

  KA KARANTA>> Gyaran Nono A Mahangar Ilimi

   YunÆ™urawa tayi tare da miÆ™ewa daga saman sallayar, hannu takai zata cire hijabin jikinta, nan take ta tunano da maganar da mahaifiyarsu ta ta6a yi masu a lokacin da suke tare da ita,

    “Burin da nake dashi kafin nabar duniya Allah ya nuna mun ranar Aurenku,kamar yarda na haife ku arana É—aya haka nakeso na aurar daku ku duka ukun arana É—aya kuma a lokaci É—aya,zan cigaba da yi maku addu’a Allah ya baku mazaje nagari,”

    Cikin sauri jahad ta Æ™arasa cire hijabin tare da ajiyeta nan saman gadonsu,sannan cikin sauri ta fito cikin falon anan tasamu hossana zaune saman 3 seater hannunta É—auke da sinkin bread tare da fresh milk sai cusawa abaki takeyi tana haÉ—awa da madarar,

     jin alamar tafiyar mutum yasa ta É—agowa tana kallon jahad dake tunkarota,

       Ganin yanayinta yasa hossana cewa”jahad meya faru naga kamar kina cikin damuwa”?

    jiki asanyaye jahad tace”hossana mun manta ba muyi ma Ya Omar maganar SEHRISH ba!banji daÉ—i da muka manta da batun nemanta ba,baiwar Allah bamusan wani hali take ciki ba,”

    cike da damuwa Jahad ta Æ™arasa maganar tare da samun wuri saman hannun kujera ta zauna,

      Nan take yanayin hossana ya canza,lokaci guda taji komai ya fita ranta, ba don komai ba sai don tunawa da Sehrish,

     murya na rawa ta soma cewa”inason ganin sehrish sosai jahad, zan sanarwa ya Omar ya nemo mana ita,bazan Æ™ara mantawa ba insha Allah,”

     “Nima bazan manta ba, da zarar yazo zamu sanar dashi,”. a cewar jahad,

  Daga haka ta miƙe tare da wucewa kitchen,

  **********************

  Wuraren ƙarfe biyar na yamma,motar sofwan ta shigo layin gidan,tun a bakin Gate security guards suka tsayar da motar tasu,kamar wasu zakuna haka sojojin suka tunkari motar shi,hankali tashe ya juya tare da kallon hayaam dake manne ajikinshi tana bacci ta aza kanta asaman kafaɗarshi,jikinta na sanye da dogon hijabi har ƙasa ta sanya niƙab a fuskarta,kamar wata Malamar Addini,

    da Æ™arfi ya ambaci sunanta”Hayaam!!Hayaam!!”har cikin kanta ta dinga jin kiran nashi,daÆ™yar ta iya buÉ—e baki tare da cewa”wai menene”?

     “Mun Æ™araso gidan fa,dan Allah ki tashi kiyi ma waÉ—annan dakarun bayani,nifa a tsorace nake dasu,”.  

    guntun tsoki taja ta janye jikinta daga nashi,sannan tace”haba sofwan bafa yau ka fara zuwa gidan nan ba,menene abun tsoro aciki,sai kace ba namiji ba,”

     wani irin kallo yayi mata tare da cewa”ba yau na fara zuwa gidan ba,amma ae ko lokacin da na ta6a zuwa É—aukarki a iya bakin babban gate É—in nan nake tsaya……’

  Bai Æ™arasa maganar ba,saboda bugun glass É—in motar daya ji anyi daga waje,muryar wani basamudan soja ce ta karaÉ—e kunnansu da cewa”Oya wind down ur glass,”

    A hanzarce Sofwan ya sauke glass É—in motar,yana ta faman mazurai kamar wani mara gaskiya,

     tambayarsu yashiga yi”Su wanene ku!kuma wurin wa kuka zo,?

     Murya na rawa sofwan yashiga nuna hayaam yana cewa”am..yalla6ai..itace zatayi jawabi,bani ba,”

     girgiza kai hayaam tayi tare da kai hannu ta É—auko purse É—inta dake ajiye saman laps É—inta,cikin sauri ta ciro wayarta tare da ruÆ™e ta a hannunta,nan fa tashiga tunanin wa zata kira acikinsu don yayi masu magana subarsu su shiga,

    “Madam ke muke jira,bama son 6ata lokaci and remove dat thing u covered ur face with” muryar sojan ce ta sake katse ta,yana nuna nikab din da yatsansa.

    Tuni taji zufa ta soma karto mata a fuskarta da sauri tasa hannu ta cire nikab din,contact É—inta tashiga tare da dialing numbar Kanal Yousof,cikin rashin sa’a wayar tashiga ringing amma ba’a É—aga ba almost 3 times,cikin sauri ta kuma lalubo numbar Junaid,har ta gama ringing junaid bai É—aga kiran ba,da alama shima baya kusa da wayar tashi,

    Hankalin Hayaam ba Æ™aramin tashi yayi ba,dama su biyu kawai take da numbarsu a wayarta gashi duk sunÆ™i É—aga kiran,

      ganin zata 6ata masu lokaci yasa sojoji bashi umarnin yaja motar shi yabar wurin,

       Wani irin Æ™ululun baÆ™in ciki ne ya tokare mata maÆ™oshinta,ba Æ™aramin 6acin rai tashiga ba,amma babu yarda zatayi dolenta su koma,

    Sofwan na Æ™oÆ™arin tashin motar su bar wurin,sai ga motar Sgr ta kunno kai daga cikin babban gate É—in gidan,

       Zuba ma motar ido sukayi gaba É—ayansu musamman hayaam da take jin cewa sauÆ™i yazo mata,don tasan kowanene zai bada Umarnin abarsu su shiga ciki ne,

    “Sir I think something is wrong here,” Amstrong ne yayi mashi magana,

  Don haka sgr ya bashi command É—in ya tsayar da motar tasu don jin meke wakana,

   A daidai saitin motarsu Hayaam Amstrong ya dakatar da tasu motar,sannan a hankali a wani irin slow glass É—in motar suka soma saukewa atare,

     Waro ido waje hayaam tayi nan take zuciyarta tayi wani irin bugun bazata,ba don komai ba sai don ganin mutumin da tajima bata sashi a idonta ba,wato abun harinta,

     A hakimce yake zaune a back seat É—in motar,ba Æ™aramin kyau yayi ba yayi wani fresh dashi,musamman wankan daya É—auka,Red shirt ce ajikinshi,tare da black trouser,

  launin rigar ya ƙara fito da wannan hasken fatar nashi sosai fari sol kamar ka ta6a jini ya zuba,sumar kan nan kuwa tana ɗaure abayanshi,yayin da idanunshi ke lumshe tamkar mai jin bacci,

    Cikin sauri sojan ya Æ™arasa inda yake tare da buga Æ™afa ya sara mashi sannan yace”Sir,wasu baÆ™in fuska ne ke son shiga cikin gidan,kuma basu da shaidar da zamu iya barinsu su shiga cikin gidan,shiyasa muka dakatar dasu,

    kusan 5 mins bai buÉ—e bakin shi ba,babu alamar cewa zaiyi magana ma,kowa yayi tsit yana jiran jin ta bakin shi,kai har sai da sojan ya fidda rai da zaiyi magana sannan Calmly yace”What about asking their details?

     Sojan yace”ban tambaye su wannan ba,amma bari naje na tambaye su,”

    juyawa yayi tare da É—an matsawa kusa da motar Sofwan yace”yana buÆ™atar bayani a wurinku,ku gabatar da kanku don yasan su wanene ku,”

    jin shiru hayaam bata ce komai ba yasa sofwan juyawa zaiyi mata magana,sakin baki yayi yana kallon ikon Allah,gaba É—aya hankalinta ya tafi kan Sgr,ba Æ™aramin tafiya da imaninta yayi ba,

    Nan take yaji wani irin kishi ya rufe shi,acikin ranshi yace”haba no wonder,sai yanzu na gane dalilin dayasa hayaam ta haukace mun akan wannan Namijin,mutum kullum Æ™ara kyau yake yi,kamar shi yayi kanshi don kyau,muddin irin wannan na yawo agari tofa bazamu ta6a yin kasuwa ba,”

     “Don’t waste our time”! muryar sojan ce ta katse mashi tunanin nashi,

    Cikin sauri yace”Hayaam!magana fa ake maki,kiyi masu bayanin alaÆ™arki da mutanen gidan,”

    Ajiyar zuciya hayaam tasaki,sannan anatse ta soma magana”ka sanar dashi cewa Æ™anwar matar yayansu ce hayaam,” 

    Juyawa sojan yayi tare da komawa wurin motarsu Sgr yace”yalla6ai tace ita Æ™anwar matar yayanku ce kuma sunanta Hayaam,”

     a hankali sgr ya É—an buÉ—e idanun shi,

    Hakan yasa Hayaam dake hangen shi ta soma washe baki,ba don komai ba sai don ita atunainta sgr ya gane jawabin da Sojan yayi mashi,

    Cike da Æ™asaita yace”sam wannan bayanin bai kwantamin araina ba!infact,I don’t know any person wit dat name hayaam or what…,ban ta6a jin sunan ba,Sergeant!!a sallamesu su koma,nd add more security!!”

     Yana Æ™arasa maganar tashi,glass É—in motar ya É—aga sama sannan a hankali Amstrong ya tashi motar,anatse yake driving É—inshi har suka bar wurin gaba É—aya,

     dariya ce Æ™umshe abakin sofwan amma ya gaza fitar da ita saboda tsoran 6acin ran hayaam,sam yaÆ™i yarda su haÉ—a ido da ita,saboda tsoran karta huce akanshi,

     Kamar ta aza hannu akai ta fasa ihu haka taji,zuciyarta har wani boiling take tana burning saboda tsantsar 6acin rai da baÆ™in ciki,ashe duk haukan nata ma abanxa ne Sgr baisanta ba,baisan wacece ita ba duk zuwan da takeyi gidan a lokacin baya, 

       daÆ™yar sofwan ya daure ya cije tare da ce mata”mu juya ko”?

    A tsiwace tace”bansani ba!!mtswww” ta Æ™arasa maganar tare da jan dogon tsoki,

   Can kuma tace”babu inda zanje wlh,kota tsiya kota arziÆ™i wlh saina shiga cikin gidan koda kuwa zamu kwana anan ne,don bazanyi tafiyar banza ba,”

    Cikin sanyin murya sofwan yace”Hayam ki bi komai a hankali!su fa waÉ—annan mutanen da kika gani ba kamar sofwan É—in da kika raina bane,muddin kikace zakiyi masu rashin kunya wlh dukan tsiya zaki sha,kakkarya Æ™asusuwan jikinki zasu yi,kuma kada kiyi tunanin cewa zakiyi masu kwarkwasa ko kija hankalinsu da kyanki,don wlh babu ruwansu da mace,su ba mayin mata bane irina,so u ave to be very careful,”

    ya Æ™arasa maganar fuskarshi É—auke da dariya,don yau ba Æ™aramin nishaÉ—i yasamu a wurin Sgr ba,ba Æ™aramin burge shi yayi ba yanayin acting É—insa babu wasa aciki,Namijin ne dae na gaske,

     Tsuke fuska hayaam tayi,harara ta watsa mashi tare da jan dogon tsoki batare da tace komai ba,

     tunani tashiga yi akan yadda za’ae su shiga cikin gidan,nan take zuciyarta ta bata shawarar ta kira Aunty babba ta sanar mata,tana Æ™oÆ™arin kiran nata sai ga Motar Haroon ta shararo da gudun gaske cikin layin,

    tunkan ya Æ™araso wurinsu ya rage gudun motar tashi,sai da yazo dai dai bakin gate É—in gidan sannan yayi parking É—in motar tare da sauke glass É—inta,da alama yasha ya bugu har takai mashi karo,saboda yarda idanunshi ke ta faman rurrufewa sunyi luhu luhu dasu,

     dakyar ya iya tsayar da idanunshi akan Motar sofwan,nan take suka hango mashi kyakkyawar fuskar hayaam,É—aga murya yayi tare da kwala ma sojojin kira,cikin sauri suka tunkari motar tashi tare da sara mashi,

    Yatsina fuska yayi ya  kallesu a wulaÆ™ance yace”Meke faruwa anan ne?su wanene acikin motar can”?

     É—aya daga cikinsu ne yace “Yalla6ai,ba mu san ko su wanene ba,mun hana su shiga ciki ne saboda basu da shaidar da zamu iya barinsu shiga cikin……’

   Tunkan ya Æ™arasa maganar haroon ya katse shi da cewa”Saboda gidan na ubanku ne!wai ma uban wanene ya kafa wannan dokar ta hana mutane shiga cikin gidan nan ne!”?ni banga amfanin takurawa mutane ba,idan tsaro ne ba Allah ke tsarewa ba mtswwww,

     Shiru sojojin sukayi suna sauraron faÉ—an nashi kamar ubansu,hayaam kuwa tunda taji yana zazzaga masifa yasata É—agowa tana kallonsu,ganin yarda yake banbamin bala’e akan an hanasu shiga yasa ta soma sakin murmushin jin daÉ—i,

    Sofwan kuwa jinjina kai yayi tare da cewa”ikon Allah,kowanene wancan jarababben da yake ta faman tada jijiyoyin wuya,da alama ba Æ™aramin hatsabibi bane,’

         Cikin lallashi sojojin suka haÉ—a baki wurin cewa”Sorry sir!Allah ya huci zuciyarka!”

    Hura hanci haroon ya shiga yi kafin daga bisani yace”Ban amince abarsu su shiga da motar da suka zo da ita ba!shi namijin yaja motar ya koma gidan ubansa,ita kuma budurwar kuce mata tashigo daga cikin motata na sauke ta cikin gidan,idan har bata amince ba to su tattara su koma inda suka fito,”. 

     “An gama yalla6ai,”atare suka amsa mashi,sannan suka juya tare da tunkarar motar sofwan,tun kafin su Æ™araso hayaam ta buÉ—e motar jiki na rawa ta fito saboda taji duk bayaninshi acikin kunnanta,

    Hankali tashe sofwan yace”Hayaam ni kuma awani matsayi kika ajiye ni ne”?

    Batare da ta waigo ta kalleshi ba tace”Zan kiraka a waya,in nasamu lokaci,ta bude back door ta dau jakanta”

    Jiki asanyaye Sofwan yaja motar,yayin da zuciyarshi ke cike da 6acin ran abunda tayi mashi,yasha wahalar kawota,amma ko godiya babu balle yayi tunanin sake samun wani abu awurinta,tuni yaji hawaye sun cika mashi idanunshi,tabbas hayam ta cuce shi sosai ba Æ™aramar wahala yasha akanta ba,duk don ya mallake ta amma gashi nan ya tashi a tutar babu!dashi da Zero basu da bambanci Æ™wara ma zero yana da amfani wurin yin lissafi,

     Shu’umin murmushi haroon ya saki lokacin da hayaam ta Æ™araso jikin motar tashi,hannu tasa tare da buÉ—e gaban motar tashiga ta zauna tare da rufe motar,sannan ta mayar da idonta akan haroon daya zuba mata ido ko kyaftawa baiyi,

    ita kanta saida tasha jinin jikinta da ganin irin zubin shi,cikin sanyin murya tace”Sannu ko,”

     É—an ta6e la66ansa yayi tare da cewa”Yawwa,amma naga baÆ™uwar fuska ina buÆ™atar Æ™arin haske,”

      Cike da kwarkwasa tace”Sunana Hayaaam,ni Æ™anwar Aunty laila ce da kuma Aunty Amani,”

     murmushin gefen fuska haroon yasaki kafin yace”Wow,no wonder that’s why naga kamanceceniyar ki da Aunty laila,ashe ke Æ™anwarsu ce,amma fa am really sorry game da abunda ya faru,securities É—in gidan nan basu son ciwon kansu ba,in ba haka ba taya zasu ga mace kamila irinki sanye cikin dogon hijab kuma su hanaki shiga?

    Sunnar dakai Hayaam tayi tana faman sakin shu’umin murmushi,aranta tace”dalilin dayasa na sanya dogon hijabi kenan saboda nasan cewa kowa zaiyi tunanin ni mutuniyar kirki ce,hmmmmm basu san cewa da fuska biyu nazo masu ba,” 

     (Rashin sani yafi dare duhu!hayaam batasan da wa take magana ba,”

     “Kada na cika ki da surutu,bari nashiga dake cikin gidan,”

    Ya faÉ—i tare da jan motar da gudun gaske ya shige cikin babban gate din gidan

    (Finally hayaam ta samu nasarar shiga cikin gidan)  

  *SANARWA SANARWA*💃💃💃💃

  *ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*

  *MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI.  MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*

  *LOCATION KANO*

  08062073990

  Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

  Wadrobe balls 

  Madarar kulleccham 

  Vaseline kulleccham 

  Kajiji

  Halut

  Couscous 

  Khumrah 

  Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

  Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka 

  Wadrobe balls 

  Madarar kulleccham 

  Vaseline kulleccham 

  Kajiji

  Halut

  Couscous 

  Khumrah 

  Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

  It’s not just good …it’s finger linking good faster than fast food, better fine dining.

  Snack

  Awarah 

  Farah

  Zobo

  Samosa

  Cup cake etc 

  Contact me 09063302182or 09012179727.

  Back to top button