Hausa novels

Wace ce ita (who is she) Chapter 64 Hausa Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SIXTY-FOUR📍

Da mamaki suke kallon daddy da alhaji habibu da suketa sambatu kamar wasu zararru, idan alhaji habibu yace “gasu sun tawo” sai daddy yace “mu gudu mu gudu”…
Kana ganinsu dai kasan kan ba dadi sannan babu wanda ze ganesu inba wanda ya musu farin sani ba, gabadaya sun fita hayyacinsu sun tsomare, sun lalace, sun gigice, sun rikice, ga wani uban rama da sukayi kamar masu kanjamau, a haka sai ka dauka sun kai shekara dari, worse of it brain dinsu ya tabu, kwata kwata basu fahimtar komai sai shirmammun zantukan da sukeyi, sameer ne kawai yake da kyan gani a cikinsu in banda dan rama na wahala dayayi, hasalima shi yake kula dasu….
Cikin tausayawa da alhini bappa ya kalli sameer daya gaishesu babu wanda ya iya amsa masa yace;
“Ita rayuwarnan shiyasa akeso mutum ya shuka alkhairi sai yaga sakamako me kyau, how do you feel seeing them in this state?”…..
Be jira abinda sameer zece ba ya cigaba da fadin;
“duniyarnan ba tabbas komai na rayuwa takaitaccen ne, shiyasa akace idan zaka gina ramin mugunta ka ginashi daidai wanda zaka iya shiga saboda wataran dole kai zaka rufta a ciki, babu mahalukin da baya sharri a duniya amma anaso muyi saffa saffa yanda Allah baze daukemana tinaninmu kamar yanda ya musu ba, da yau tinaninsu yana tare dasu da tini sun nemi gafara amma yanzu ta ina zasu fara?, muda kanmu ganinsu a haka ya razanamu inaga su da zasuje su hadu da mahaliccinmu sarki Allah”…..
Dan numfasawa bappa yayi ya cigaba dacewa;
“Sameer duk abinda hakuri bai bamu ba toh tabbas rashinsa bazai bamu ba, yanzu ina amfanin rayuwa irin wanda suke ciki?, Allah yabaku dama kunbar damarku ta kubucemuku da son abun duniya da mutanan cikinta, ita fa rayuwarnan yau mune gobe bamu bane saboda haka yanada kyau mu aikata alkhairi saboda mu riskeshi a ranar gobe kiyama, da gatanku da komai yau kune kuka zama abun kyankyami hasalima bakusan ina kanku yake ba, Allah dai ya wadaran naka ya lalace! Duniyar duka guda nawa take? muda zamu koma lahira mai yakawo hadamar son duniya, subhanallah ya kamata mu guji duniya domin lahirarmu tayi kyau”…..
Baffa bai tsaya da maganar ba ya dora da nasiha;

Download>>> Miji Nagari Burin Ya Mace Complete Document

“kubi duniya a sannu karku yadda kucuci ko zalunci wani domin Allah baya barin wanda yayi zalunci, shi kuma sharri dan aikeni duk inda aka aikashi zaidawowa wanda ya aikeshi a lokacin da be shirya karbarsa ba, sannan duk sanda ya tashi dawowa ze dawo ne cikin mummunan yanayi fiye da yanda aka aikashi, ina kara jan kunnanku da ku zama masu aikata alkhairi komai kankantarsa domin alkhairi baya faduwa kasa banza, muzama masu aikata alkairi kozamu samu rabauta a ranar gobe kiyama, Allah yasa muzama mutane masu aikata alkhairi acikin al-ummar Annabi S.A.W, Allah yasa muzama salihan bayi masu tsarkake zukata akan kowa ,Allah yasa mufi karfin zukatanmu a duk lokacin da take masa sake saken banza, Allah ya yayemana son zuciya da fadawa hallaka, Allah yasa karshanmu yafi farkonmu kyau, Allah karkabarmu da iyawarmu ka iyamana dan darajar Annabi da al-qur’ani”……..
Baffa ya karashe da addu’a yana mikewa tsaye, kasa cewa komai sukayi suka mara masa baya suka fita daga gurin aka bar deen shi kadai…..
Suna fita deen ya kalli sameer daya kasa hada ido dashi, mika masa hannu yayi fuskarsa ba yabo ba fallasa yace;
“I’m sorry!”….
Kama hannunsa sameer yayi yana girgiza kai yace;
“Bakamin komai ba saif, infact I’m glad coming here kodan in kula dasu”……
Zare hannunsa deen yayi ya nufi hanyar fita, har ya kai bakin kofa ya tsaya, be juyo ba yace;

Download>>> Miji Nagari Burin Ya Mace Complete Document

“You can get out of here anytime you wish, and if you still want to fight for zahrah’s love you’re free to, goodbye”…..
Yayi wucewar shi batareda yaji amsar sameer ba…..
Guri sameer ya samu ya zauna yana tinanin abinda ya dace yayi, tabbas yana son baby tee har yanzu amma be san ta ina ze fara ba, sai kuma yake ganin kamar gatse deen ya masa….

Fada bappa yake musu me hade da nasiha tinda suka dauko hanyar dawowa asibitin da khaleel yake, sosai ya nuna musu bacin ransa akan kin waiwayar su daddy da sukayi kodan khaleel dake neman kashe kansa akan jininsu, ya kuma shaida baza abar su daddy a haka ba, da kansa zesa a musu magani…..
Hakuri kawai sukaita bashi har suka karasa asibitin…..
Da sallama suka shiga room din da khaleel yake, anna na zaune akan sallaya, baby tee da khaleel na daga gefe suna dan taba hira, gabadaya khaleel ya sake kamar ba shi suka zo suka tarar ranga ranga ba, hakan ya kara tabbar musu da baby tee itace mahadin rayuwar khaleel…..
Ya jiki daddy ya masa shida bezo dazu ba suma suka kara masa ya jiki sannan kowa ya samu guri ya zauna banda deen dake tsaye kusa da kofa ya fito da waya yanata danne danne, yanajin idon baby tee a kansa amma yayi kamar be gani ba..….
Gyaran murya bappa yayi yace;
“Khaleel munje munga mahaifinka ba kuma zan boye maka ba domin ba a yanayi me dadi muka gansa ba amma Insha Allahu ni nayi maka alkawari zanyi komai dan in tabbatar sun samu lafiya, sannan inaso ka kwantar da hankalinka domin fatima batada wani miji sai kai, zaka iya turo magabatanka inka shirya kafin Allah ya bawa mahaifinka lafiya kuma….”
Ko tsayawa jin karshen zancen deen beyi ba ya bude kofa a hankali ya fice daga dakin…….
Baby tee da hankalinta ke kansa kadai ce taga fitarsa, nan da nan zuciyarta ta kasa nitsuwa taji kamar ta bishi taji dalilin dayasa ya fita…..
Labari anna ta basu akan abinda ya samu khaleel dataji suna maganar shi da baby tee da basusan ma taji ba…..
Sosai suka kara tausaya masa, suka kuma fahimci son da yake yiwa baby tee ba karami bane……
Dafa kafadar khaleel da jikinsa yayi sanyi sosai bappa yayi yace;
“Kadena saurin yanke hukunci idan kaga abu, ka kasance me tsawaita bincike sannan, yanzu inda kayi hatsari ko wani abu ya sameka a hanya me akayi kenan? Sannan ka dena bari….”…
Kasa jurewa baby tee tayi hasalima maganganun da ake sam be dada ta da kasa ba kawai ta mike ta fice daga dakin a sace itama……

Download>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Deen na fita be nufi ko ina ba sai garden din asibitin ya samu guri ya zauna, zaro wayarsa yayi ya kira sudais, ringing daya sudais ya dauka da sallama ya dora da fadin;
“Na kiraka dazu ban sameka ba, I wanted telling you na aiwatar da sakonka”…..
“Good! Sudais I can’t fulfil your wishes”….
Deen ya bashi amsa a sanyaye…..
“Bangane you can’t ba? Meya faru?”……
Dan shiru deen yayi kafin ya fara bashi labarin duka abinda ya faru daga zuwansu asibiti har zuwa barrack da yanda bappa ya nuna interest dinsa sosai akan khaleel da ita baby tee data tabbatar masa da khaleel take so…..
Cikin rashin jindadi sudais yace;
“I still believe in kace kanaso ko ciwon mutuwa ne dashi sai anbaka wallahi”…….
Kada kai deen yayi yace;
“Na riga na fadawa bappa babu komai a tsakaninmu and I’m aware of soyayyar dake tsakaninsu da khaleel”…..
“Amma meyasa zakayi haka? Haba saif ba haka muka tsara ba”…….
“So kake in kwanta kamar shi ince sai sun bani ita bayan ba sonta nake ba ma? Ko so kake in mata dole ta kasance dani bayan bataso na bana sonta? Ko so kake inyi stopping low in tsaya ina musu yar murya? Bari kaji sudais at this point ko ganin zahrah banasan yi, wallahi kome kama da ita banasan gani, I just want to get over her completely”…..
“You want to get over her fa kace? Kai da baka sonta meya kawo maganar get over her?”.
“Yes bana sonta amma I always want to her to be under my care, toh yanzu kuma banaso, I don’t care any longer, I don’t love….
Wani kara deen yaji anyi daga gefensa, juyowa yayi da sauri idonsa ya sauka akan baby tee data zube kasa a sume saboda maganganunsa da suka bigeta, ba shiri ya mike yayi kanta, sunkayawa yayi ya dagota jikinsa yana dora hannunsa akan hancinta yaji bata numfashi, sosai hankalinsa ya tashi ya dauketa a rude yayi emergency ward da ita….
Suna ganin yanda ya shigo likitoci sukayi kanta a rikice, ID card dinsa ya nuna musu suka shiga emergency room din har dashi, dukufa sukayi akanta sunata kokarin ceto numfashinta da kuma san gano sanadin abun…….
Sai da sukayi kusan hour daya akanta kafin Allah yasa numfashinta ya daidaita, ba karamin tashi hankalin deen yayi ba saboda a binciken da sukayi rayuwarta is at danger saboda situation dinta ya zama crucial, gabadaya kidney dinta yayi damaging completely, she’s just living under ikon Allah sannan a binciken da sukayi sun gano tasha wani abu me karfi da yayi triggering faruwar hakan…….
Kai da kowawa deen ya farayi a cikin emergency room din yana tinanin yanda ze bullowa al’amarin, sam bayaso su umm su sani saboda yasan panicking zasuyi su daga hankalinsu a bata lokaci ana jimami instead a nemo solution…. Gwara ya nemo solution shi kadai idan komai yayi normal sai ya sanar musu….
Hamdala yayi tuno da sunada appointment da Dr.Max saket akan implant din saidai in few days ne ba ranar ba, zaro wayarsa yayi ya shiga neman number Dr Max ko Allah zesa ya samesa a waya ya fada masa halin da ake ciki, kuma koda be samesa ba yasan dole ya bar kasar da ita a yau sannan at all cost he has to save her life…..

Download>>> Boddiya Complete Hausa Novel Document

Luckily yana kiran Dr Max number yayi going through, Allah ya taimakesa kuma ya dauka, babu bata lokaci deen ya masa bayanin halin da ake ciki ya kumayi requesting yayi musu shifting appointment dinsu zuwa yau, a take Dr Max ya amince jin yanda lamarin ya tsananta ya kuma cewa deen su tawo as soon as possible a samu ayi mata implant din a yau in Allah yasa batayi passing out ba saboda idan mutum ya kai stage dinnan it’s rare ya dade be mutu ba inba wani ikon Allah ba……..
Godiya deen da yake ta daure zuciyarsa yayiwa Dr Max ya kuma ce masa zasu tawo as soon as possible……
Fita yayi daga ward din yana tinanin fastest route da zasuyi getting to India yanzu, abby ne ya fadomasa a rai tino da yanda yake yayawan tafiye tafiye hakan yasa an bashi license yana shiga ko wacce kasa, amma kuma besani ba ko haryanzu license din is available, yasan kuma jet din abby kadai ne zaa samu fully lubricated a yanzu……
Wayarsa ya zaro yayiwa Abby text message kamar haka;
“Can I see you please? It’s so urgent abby”..
Abby da wayarsa ke rike a hannunsa yaji karar text message, dubawa yayi ya karanta content din, kamar ya kirawo deen yaji sai kuma yayi tinanin da magana yakeso suyi a waya ze kirashi, kawai ya mishi reply da;
“Of course saif, where are you?”…..
A take deen ya mishi reply da;
“I’m in the hospital garden, thank you”….
Abby be sake mishi reply ba yayi excusing kansa ya fita daga dakin, direct garden din ya nufa tin kafin ya karasa ya hango deen a tsaye…..
Deen na ganin karasowar abby ya sake saita kansa yanda baze gane yanayin da yake ciki ba……
“Abby do you still have the license to go any country?”……
Ya tambaya kai tsaye making it look like a business discussion…..
“Yes son, do you need anything?”…..
Abby ya bashi amsa cike da kulawa…..
“Dan Allah so nake ka ara min licensed jet dinka, I need to fly out now, it’s very urgent”…….
Abby be tambayesa ina zeje ba kome zeyi ba saboda he believes deen ba yaro bane da ze tsaya yana mishi irin wannan tambayoyin kawai yace;
“Why not? Kayi sa’a yana nan abuja kuwa, let me make a call”….
Ya fada yana zaro wayarsa……
Air crew din ya kira ya basu order a shirya emergency flight yanzu yanzu…..
Basu fi 10mins ba kuwa sai gashi sun kira sun fadamasa everything is set, kallon deen yayi yace;
“Son everything is set”…..
Murmushi deen ya kakalo yace;
“Thank you so much abby”…
“You’re welcome dear, insa a kaika port dinne?”……

Download>>> Sexxy Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

“No need Abby, da mota nazo”….
“Okay, Allah ya kiyaye hanya ya bada nasara”…….
“Ameen Abby, I really appreciate”….

Abby na tafiya deen ya koma emergency room din, be bi takan doctors din ba kawai ya sunkuceta yayi hanyar waje da ita, wani daga cikinsu ne ya taso yace;
“Ya zaga fita da ita without a discharge letter and you didn’t even pay for the bills”……
Wani banzan kallo deen ya masa ya zaro bandir din one thousand dake aljihunsa ya cilla masa ya fita…..
A back seat ya sata sannan ya shiga ya tada motar ya bar asibitin a guje…….
In few minutes ya isa port din Abby saboda gudin da yake tsugawa, yana zuwa ya gansu all set kamar yanda Abby ya fada, har pilot din yana cikin jirgin shima, sai da suka tambayesa inda zasu yace musu India sannan suka bude masa ya shiga dauke da ita a hannunsa, yana shiga jirgin yayi taking off a take……
Ajiyar zuciya deen ya sauke yana kankameta yace;
“Alhamdulillah, I can’t wait for us to get there, I just want you to be alright baby girl”….
Sake gyara mata zamanta a jikinsa yayi yayi kissing lips dinta lightly murya chan kasa yace;
“If it takes giving you my two kidneys I’ll do that, I can’t afford losing you beautiful”……
A haka yanata dan kananun surutansa har bacci ya daukesa shima…..

Sai da suka tashi tafiya sannan sukayi noticing babu baby tee ba deen, khaleel dama tin fitarta yaji hankalinsa be kwanta ba amma ya daure beyi magana ba saboda bappa dake masa nasiha amma hankalinsa gaba daya yana kan time, har aka ci one hour babu wanda ya gane basanan shi kuma kunya ta hanashi magana musamman yanda bappa ya masa fada akan zargi kar yayi magana yanzu su dauka zarginsu yake shiyasa ya daure be nuna ba……
Rikicewa su umm sukayi suna nemansu lokacin kuma akayi rashin sa’a Abby ya fita receiving wani business call, fita umm da mami sukayi suka shiga duba lunu da sako na asibitin amma babu su babu alamarsu, har gida suka kira ko sun koma aka tabbatar musu basu dawo ba, gashi sai kiran wayoyinsu ake duka akashe, hakan sai ya tabbatarwa umm da mami tare suka tafi koma ina ne……
Karo sukaci da abby daya tawo ze koma cikin ward din, a gigice umm tace;
“Kaga saif da baby tee dan Allah?”……
Gyada kai abby yayi yace;
“Na dai ga saif boddi, baby tee kuma ai tana ciki”…..
Da sauri tace;
“Dan Allah yana ina? Bata ciki and I’m very sure duk inda yake suna tare”……
“I don’t think suna tare because saif baya kasar nan”……
“Bangane baya kasarnan ba?”…..
“Eh dazu fitan danayi shi yayi texting dina, yace na ara mishi licensed jet dina he needs to fly out urgently, and I did”…..
Cikin rashin fahimta umm tace;
“Fly out to where? Ina yaje?”…..
“Wallahi bansani ba boddi, ban tambayeshi ba”……
“Yanzu Muhammad har yanzu baka chanza da wannan ridiculous habit din naka na biyewa yara ba? How can someone borrow your jet bazaka tambayeshi ina zashi ba? Kai wani irin mutum ne wai? Who even does that?”…..
Umm ta fada cikin masifa hade da kiran sunansa kai tsaye abinda bata tabayi ba…..
A nitse kasancewarsa mara hayaniya yace;
“Relax boddi, babu abinda ze faru da yardar Allah”….
Dakatar dashi tayi da fadin;
“Relax fa kace inyi Muhammad? What on earth is going on with your brain?, kacemin be gayamaka kasar da zasu ba amma kake cewa I should relax? Impossible! I won’t even listen you! See na baka one hour kayi finding out ina yarana suke! And if you can’t provide their whereabout within an hour I will hold you responsible for everything!”…….

Download>>> Anya Baiwa Ce Complete Document

Back to top button