Mijin Marigayiya Page 23 Hausa Novel
Ta karasa ta zauna a kujerar gabansa, sannan ta dauki file a kan teburin ta mika masa. Nan take ya buda ya fara karantawa yana mata tambayoyi tana yi masa bayani. Bayan sun gama ya ajiye file din a gefe ya dubeta yace ‘To meye labari?’Tayi dariya ta sunkuyar da kai a kunyace tace ‘Komai normal.’‘Good. So nayi mana order din lunch ko? Don na san ko ance kizo muje mu ci a waje ba kya son zuwa eateries, sai shopping ko?’Tayi dariya tace ‘Gara dai ayi order din.’Tayi dariya tace ‘Gara dai ayi order din.’‘Ba damuwa, kiyi mana order din sai ki turo min account number na tura kudin.’‘Yes Boss, an gama.’Suka yi dariya gaba daya.Tana shirin tashi yace ‘Yauwa, gobe ana open daya a school din su Afaf, please idan kika shigo around 10am sai kije musu, ki jiyo min duk bayanasu da performances din su.’Ta gyara zama tace ‘Uhm, ok. But Madam ba ta nan ne ko bata jin dadi?’Ya gyara zama ya fara lilo a kujerar da yake kai yana kallonta sosai sanna yace ‘No, lafiyarta kalau but na dai fi son ke kije ki jiyo min komai.’Cike da farin ciki ta sake fadada murmushinta tace ‘Yes Sir, Allah ya kai mu. Kuma Allah ya sa kada kasa yayata ta bani query saboda na shiga aikinta duk da dai nima ‘yayana ne.’Yayi dariya ‘Kada ki damu, baki da matsala da ita.’Suka sake dan taba hira sannan ta fice ta koma office dinta cike da farin cikin yanda alakarsu take tafiya ita da ogan nata.Ba zata taba bari Mustapha ya kufce mata ba don ta ga mijin aure. Ta gama degree dinta har tayi masters, saurayinta na karshe har sun zo gaisuwa haka kawai ya daina zuwa sai ji kawai tayi ana bikinsa da ‘yar uwarsa. Duk da ta san ba wasu shekaru ne da ita masu yawa ba domin shekarunta 28 kacal, amma dai ta san an matsu tayi aure a gidansu; musammam ummanta wadda aikin ma so tayi ta hanata sai tayi aure. Sai gashi ahse mijin yana wajen aikin. A hankali suka saba, har suka kai yanzu da take jin zata iya cewa ta fi matarsa sanin halin da yake ciki da inda yake a kowanne lokaci; don haka ma take jin cewa kwaceshi a wajen Khadeeja kamar kwace goruba ne a hannun kuturu, domin tun yanzu tana jin ta fara samun nasara tunda kullum ita yake kawowa karar Khadeejan sai ta bashi hakuri, ta riga ta fahimci irin zaman da suke yi da Khadeejan don haka ta gama shirya musu; lokaci kawai take jira.____Karfe sha daya take da lecture don haka sai da ta gama shirya yaran dukansu suka fita makaranta sannan itama ta karasa ayyukanta ta shirya.Karfe goma da minti biyar tana zaune a gaban mudubi tana gayar fuska ta tuna jiya da daddare Shukra ta ce mata Anty tace kowa ya zo da Mommy dinsa open day 9am to 11am sannan sai a zarce da sports, kuma idan dai ba ta manta ba ma Afaf ta gaya mata duk da section din su Afaf din da ban da na su Shukra. Sai dai basu yi maganar da Abbansu ba, bai gaya mata itace zata je ko shine zai je ba gaba daya ta manta bata tambaye shi ba. Ta mike ta dauko wayarta wadda take ajiye a gefen gado ta dannan masa kira; sai da ta kirawo sau uku duka wayar bata shiga ba, don haka ta yanke hukuncin idan ta fita sai ta fara tsayawa a makarantar tasu tukunna kada taje sai ta wuce makaranta ya bugo waya yace itace zata je ya jika mata aiki.Nan da nan ta karasa shiryawa ta saka jilbab dinta me kalar lilac sanna ta saka bakin sneakers dinta ta sallami Rashida sannan ta wuce.Tana zuwa makarantar kai tsaye ajinsu Shukra ta wuce, duk malaman nasu sun santa saboda zuwa daukansu don haka ba tare da bata lokaci ba aka bayanan Shukra da kuma results dinta na CA. tana gamawa ta ja hannun Shukra suka wuce ajinsu Nasreen inda nan ma aka hada mata komai, Nasreen tana cikin wadanda zasuyi wasan tsere don haka bata samu ta fita daga aji ba Khadeeja ta ja Shukra suka nufi secondary section don ta karbo sakamakon Afaf da Habib.Tun kafin su karasa kofar secondary section din ta hango Afaf tare da wata mata sanye da bakar abaya da brown envelops a hannunta, suna tafe suna hira; ga dukkan alamu a dai malama ce a nan makarantar duk da ita Khadeeja bata taba ganinta ba. Da suka kara matsowa kusa Shukra ta zare hannunta daga na Khadeeja tana cewa ‘La, Anti Naja ce gasu nan ita da Yaya Afaf.’ Ta karasa wajensu da gudu.Da fara’arta ta cimmusu, suna haduwa ta kara fadada murmushinta cike da girmamawa tace ‘Sannu Anti.’Cike da mamaki itama ta dan yage baki mai kama da murmushi tace ‘Yauwa, sannunmu.’‘Ya aiki ya yaran?’ ta kula da yanda ta ke magana kamar da kyara don haka kafin ma ta bata amsa ta mayar da hankalinta ga Afaf tace ‘Yaya Afafa muje na karbo muku CA report dinku ke da Habib na wuce don nima school zan je.’Ta dan daga gira cikin halin ko in kula tace ‘Anti Naja ta karbar mana ai, dama na su Shukra zata je ta karba yanzu.’Ta kalli Afaf din sannan ta kalli malamar da aka kira Anti Naja tana mamaki tace ‘Me yasa? Anti ai da kin barshi na zo gashi sun saka ki aiki.’Ta kawar da kai ta daga gira tana cewa ‘No ba wani aiki, ai Abbansu ne yace na karbar musu.’Itama Khadeeja ta dan zaro ido tace ‘Oh, ya zo kenan ko yaushe yace a karbar musu?’Afaf ta fahimci Khadeeja bata san Naja ba kuma bata ma san da zamanta ba, sabanin ita da kannenta wadanda a cikinsu zata iya cewa Shukra ce kawai bata san Naja ba ko kuma ta santa amma bata san wacece ita ba. Ta dan yi gyaran murya tace ‘Anti ba fa malamarmu bace, sakatariyar Abba ce kuma shine ya turota daga office ta zo mana open day din.’Mamakin Khaddeja ya karu, ta sake karewa Naja kallo na dan takaitaccen lokaci sannan ta bude baki zata yi magana sai kuma ta fasa. Ta dan yi murmushi da gefen baki sannan ta kalli kasa ta dago suka hada ido da Najan wadda take mata kallon da ta kasa fassarawa sanna tace ‘Oh, ok, Umm.’Kafin ta ce wani abu Habib ya karaso wajen yace ‘Yauwa Anti kin karaso? Dama ke nake jira; don Allah zo muje ki cewa uncle ni bana son basket ball team ya barni na shiga football team. Haka kawai wai saboda ni dogo ne sai nayi basketball.’Kafin Khadeeja tayi magana Najan tace ‘Au shine baka gaya min ba Habib, ai da ka gaya min nayi masa magana.’‘Dama Anti nake jira.’ Ya fada cikin halin ko in kula ya zari envelop guda daya daga hannun Najan ya mikawa Khadija yana dariya yace ‘Anti guess what?’Ta dan yi murmushi yayinda suka bar Naja da baki bude, tace ‘What?’Ya zaro takarda daya ya mika mata yana cewa 38 naci a Hausa yau don haka yau da shawarma zan yi dinner ko?’Ta karba tana dariya sannan ta bashi hannu suka tafa tace ‘Iyye, ai dole kaci shawarma tunda yau ka wuce gori. Haba ko kai fa, kullum komai kaci A da B amma a Hasua ka dinga cin D da F.’Ya mikawa Khaddeja envelop din yana cewa ‘To zaki ga Uncle din?’Tace ‘No, tunda yanzu ka ga kun riga kun fara games ina jin ka bari sai gobe sai na zo na ganshi. Kafin nan munyi tattauna a kan football da basketball din kuma mun yi magana da Abbanka ko?’Ya gyada kai ‘Eh, hakane.’Naja tayi sauri tace ‘Idan kina sauri ne ai sai naje naga Uncle din.’Tace ‘No ba sauri nake ba, kamar dai goben zai fi dacewa kawai.’Habib ya katsesu yana mikawa Khadeeja envelope din yana cewa ‘Anti sai mun dawo, goben kya zo kawai.’ Ya wuce ya barsu a nan.Naja ta mikawa Khadeeja hannu tana cewa ‘Ki kawo na tafiwa da yallabai takardun tunda office zan koma.’Ta dan yi murmushi tace ‘No ina ga gara ni na tafi masa dasu tunda a gidansa zan kwana.’Ta bata rai tace ‘Um, sai an jima.’Ta wuce rike da takardun Afaf da suke hannunta Afafa din tana biye da ita suna hira.Khadeeja ta bi bayansu da kallo tana mamaki; to yaushe yayi sabuwar sakatariya? Tunda da dai ta san sakatarensa namiji ne. kuma har yaushe sakatariyar ta kai matsayin tazowa yara open day har tana wani cewa a bata takardu ta kai masa? Tukunna ma; kamar dai yaran nan sun sa wannan sakatariyar, itace bata santa ba. To kenan har yayi introducing dinta a wajen yaransa a matsayinta na wa? Me yasa suka kwana tare bai ce mata tazo open daya ba kuma bayan ya fita ma ya kasa kiranta? Wanda tunda ta aureshi duk wata harkar makarantar yara itace take zuwa kuma shi yake saka ta ta zo. To me yasa wannan ya sa sakatariya? Naja? Bata son ta yanke hukunci cewa akwai wani abu tsakanin Mustapha da Naja amma dai tabbas tana da tarin tambayin da zai amsa mata.Sai da ta raka Shukra aji sannan ta nufi fita daga makarantar.Tun kafin ta gama fitowa daga cikin ginin makarantar zuwa farfajiyar wajen da ake ajiye motoci ta hangosu, tana rike da hannun Afaf suna magana har suka karasa bakin motar gefen direba ta sa mukulli ta buda motar; ta dan ja baya ta labe. Me take gani ne? Motar Mustapha? To shine ya kawota ko me?Tana nan a labe ta hangosu; Naja ta bude motar ta zauna a kujerar direba sannan ta yiwa Afaf sallama ta ja motar.Sai da ta karanta lambar motar a fili domin kara tabbatarwa motar Mustapha ce; kanta ya daure gaba daya. To me hakan yake nufi? Ya aiko sakatariyarsa ta zo wa yara open day kuma a motarsa. To hada kudi sukayi suka sayi motar a tare? Ko kuwa dai tsabar kauna ce ko rashin hankali ya sa suke sharing motarsa da sakatariya? Me yasa bai aikota a motar haya ba ko a motar office? Wato motar da ita idan dai makaranta zata ko arage mata hanya bata isa yayi ba itace ya bawa sakatariya take yawo a gari.Kai! Gaskiya Mustapha ya rainata.Tayi sauri ta fito daga inda ta rabe lokacin da ta hango Afaf ta nufo wajen.Tayi mata sallama sannan ta wuce ta fice daga harabar makarantar.A bakin titi ta tsaya, motocin haya sai tsayawa suke ba tare da ta hau ba; gaba daya ma ta manta inda zata saboda yanda zuciyarta take zafi; me Mustapha yake nufi da ita?Har ta juya zata koma gida saboda yanda take jin ba zata iya zuwa lecture din ba sai kuma ta tuna idan taje gidan me zata yi? Rufe kanta kawai zata yi a daki tayi kukan da ba zai mata maganin komai ba; don haka ta sake juyawa ta koma bakin titi ta hau motar BUK. Ta kalli waje ta tagar motar, tayi murmushi ita kadai; wai itace a motar haya yayinda ga wata can tana yawo a motar mijinta. Takawar da kai ta share kwalla…
