Ruwan Zuma Page 12 Hausa Novel
(12) Da dare misalin k’arfe bakwai da rabi Haydar ya iso gidan Laila. Waya ya mata cewa ya iso sannan ya shiga falon bayan ta masa iso. Babu kowa a falon, hakan yasa ya nemi guri a k’asan carpet ya zauna yana ajiye wani large envelope daya shigo dashi a gefe. Laila ce ta fito daga d’akinta fuskarta d’auke da murmushi ta zauna a kujera mai fuskantar Haydar. “Me haka Haydar? Don Allah ka tashi ka zauna a sama.�? Ta umurceshi tana mai nuna mishi kujeran da yake jingine da ita. “A’a Hajiya, nan ma ya isa.�? Ya bata amsa yana sosa k’eya. Babu yanda bata yi dashi ya dawo saman kujera ba amma ya k’i, da kanta ta hak’ura ta barshi. “Kayi k’ok’ari sosai na had’o abincin nan cikin k’ank’anin lokaci. Komai yayi daidai nagode.�? “Babu komai Hajiya, ai ba wani abun wahala bane. D’azu naga kina tare da bak’i shiyasa ban baki sauran canjinki ba.�? Ya tashi daga inda yake zaune ya ajiye mata kud’in a gefenta wanda zai kai dubu hud’u. “Ka barshi kawai.�? Ta d’auki kud’in zata mik’a mishi amma har ya koma gurin zamanshi. “Wallahi Hajiya nagode, ai jiya ma kin bani kuma har yanzu akwai saura.�? Laila tayi d’an jimm tana kallon yanda yake mata magana cikin girmamawa, yana sunkuyar da kai k’asa baya son saka idanunsa cikin nata. Farar fuskarsa mai d’auke da sajen da bai gama had’uwa ba take kallo, innocence d’insa na d’aya daga cikin abunda ya d’auki hankalinta a farkon had’uwarsu. Sannan baza ta manta ba yayi wata tsayuwa, tsayuwa irin ta Aliyunta. Kuma a yanda ta lura dashi Haydar mutum ne mai tsafta da son ado, ita har yau mutum mai tsafta yana saurin shiga ranta. Zata taimaka mishi ba wai don ta samu wani abu a gaba ba, sai don tana ji a zuciyarta ya cancanci hakan. “Bani takardun naka in gani.�? Haydar ya tashi ya mik’a mata large envelope d’in yana mai duk’awa kad’an. Laila ta bud’e ciki ta ciro takardun cikin tana dubawa. “Aliyu Haydar.�? Ta furta a hankali tana mamakin yanda sunansa ya zama haka. Shi kuma Haydar addu’a yake yi a ransa kar ta tambayi dalilin hakan domin bai shirya bawa kowa amsar ba. “Yayi kyau, baka da matsala Insha Allahu. Gobe k’arfe takwas na safe ta maka a gidan nan sai mu tafi ko?�? “In Allah ya yarda Hajiya, nagode Allah ya k’ara girma da d’aukaka.�? Ya fad’a yana mik’ewa tsaye. Laila ta kwalawa Nana mai aikinta kira fito rik’e da leda a hannunta, ta mik’awa Haydar ya kar6a tare da yin godiya kana ya mata sallama ya fita. Wata nannauyar ajiyar zuciya Laila ta sauk’e kana ta mayar da takardun cikin large envelope d’in sannan ta mik’e da niyyar komawa d’akinta. Abul ta gani tsaye a k’ofar d’akinsa fuskarsa a had’e yana mata kallon rashin fahimta. “Mama waye wannan yaron?�? Shine tambayarsa ta yau kuma ta jiya wacce yayi bata amsa masa ba. “Sunanshi Haydar.�? Ta bashi amsa don bata son ya d’auki abun da wata manufa.“Me yake zuwa yi a gidan nan?�? “Aiki zan nema masa ubana Abul. Sai kuma wace tambayar tunda kai ka ajiyeni?�? Takowa yayi zuwa gurinta yana sassauto da fuskarsa domin yaga itama ranta ya fara 6aci. “Mama bana son kina shiga harkar yara irinshi, wallahi a gabanki ne zasu nuna miki suna da hankali amma suna fita zaki ga sa6anin hakan. Kuma ni tun ganinshi da nayi bai kwanta mini ba, haka kawai naji ina zarginsa. Don Allah kiyi taka tsan-tsan ba don na fiki sanin me ya dace ba, a’a, saboda I care ne Mama. Please.�? Ya dafa kafad’unta duka biyu yana kallon cikin idanunta. Laila taji kamar wacce aka tsare domin Abul ya fita tsayi sai ta zama kamar wata k’arama a gabansa. “Naji.�? Kawai ta fad’a tana mai ratsewa ta gefenshi tayi hanyar d’akinta. “Mama.�? Ta jiyo Abul ya kirata da wata sauti wanda bata ta6a jin irin hakan daga gareshi ba. “I’m sorry da abunda na miki jiya, amma don Allah karki saki jiki dashi. Naga yanda yake kallonki and I hate it Mama.�? Ya k’arisa maganan kwalla na taruwa a idanunshi. “Abul kenan kaima zargina kake yi kamar yanda sauran mutane suke yi ko?�? Wannan karon Laila ce tayi maganan rai a 6ace. Girgiza kai yayi sannan yace, “Har abada bazan ta6a zarginki ba domin nafi kowa sanin halinki Mama.�? “Good.�? Kawai tace dashi tayi shigewarta d’aki tana jin komai ya daina mata dad’i. Addu’arta a kullum shine Allah ya ragewa Abul zafin zuciya da d’aukan k’aramin abu har rai. Me Haydar zai iya yi mata? Cutarta zai yi ko kisa? A zaman da suka yi tasan baya d’aya daga cikin mutane masu mugayen halaye. Kuma idan abun da Abul yake tunani ne ita babu shi tsakaninta da Haydar kuma har abada hakan bazai ta6a faruwa ba, domin a matsayin k’ani ko d’a ta d’aukeshi. Haydar yana komawa gida ya samu Ammi a d’akinta tana gyangyad’i. Tana ganinshi ta tashi tana wartsake ido. “Ka dawo?�? “Na dawo, tace tana gaisheki.�? Ya zauna yana ajiye mata leda a gabanta. “To ina amsawa. Wannan fa?�? Ta jawo ledar ta bud’e tana kallo. “Abun taryar bak’in ne nima aka bani.�? “Kai kullum kaje gidanta sai ka dawo da abun arzik’i? To masha Allahu.�? K’arfe sha d’aya na dare Haydar ne kwance a d’akinshi kan katifa ya shiga whatsapp yana duba sak’onnin da aka aiko mishi wanda yawanci daga wanda suka yi makaranta tare ne. Bayan ya gama amsa na amsawa ya koma kallon status wanda a nan yaci karo dana Laila. “Kenan tayi saving d’in numberna?�? Ya furtawa kanshi yana mai duba hoto d’aya rak data saka. Hoto ne na taron mata hud’u wanda Laila ce cikon na biyar. Kowacce sanye take da shiga ta mutunci suna dariya. A take yayi saving hoton sannan ya koma cikin hotunansa ya bud’e, a haka yasan yanda zai yi ya cire sauran matan a hoton ya rage Laila ita kad’ai. Murmushi yayi mai sauti ya cigaba da kallon hoton har bacci ya d’aukesa ba tare da ya gane meyasa yayi hakan ba. Washe gari litinin da sassafe Haydar ya gama shiryawa ya yiwa Ammi sallama kana ta bishi da addu’ar samun nasara. Black Suit da yayi bikin gama makaranta da ita yau ma ya sanya domin da ita yake zuwa neman aiki idan aka samu wani vacancy. K’arfe takwas daidai Laila ta fito daga falonta cikin laffaya fara sol mai adon silver stones. Hannunta rik’e da silver pos kalar takalminta mai tsini. Kyau tayi bana wasa ba, ga wani walwalin da take yi tamkar wata a daren sha hud’u, sai dai fuskarta babu walwala kamar kullum dalilin wani abu da ya faru kafin ta fito. Wannan karon Haydar sake baki yayi yana kallon tsarin halitta irin ta uward’akinsa. A zuciyarsa kuma mamaki yake yi yanda ta zauna tsawon shekaru ashirin babu mijin aure. Shi ya isa gurinta ya kar6i file d’in hannunta kana ya gaisheta cikin girmamawa. A sanyaye ta amsa ta shiga motarta, ganin haka yasa shima Haydar ya shiga gaba ya kulle k’ofar yana zare ido. Ko dai kallonta da yayi ta yi ne ya 6ata mata rai? Me yake damunshi ne? Shiru suka yi na kusan minti d’aya sannan tace, “Zo kayi driving.�? Kana ta fita daga cikin motar ta koma baya ta zauna. “To Hajiya.�? Shima ya fita ya shiga driver seat ya kunna motar. Da haka suka fita daga gidan Laila na fad’a masa inda zai kaisu. Wata ma’aikata suka isa wanda tunda Haydar yaga tsarin ginin da kuma mutanen da suke shiga ciki ya gane cewa ba k’aramin ma’aikata bane. Laila ce ta fita kana ta sanyawa idonta blue sunglasses wanda ba’a iya hango kwayar idonta. Kai tsaye ta shiga cikin ma’aikatar mutane na binta da kallo duk inda ta ratsa. Haydar dake binta a baya wani tuk’uk’in bak’in ciki yazo ya tsaya a mak’ogwaronsa da yaga wani mutum ya zubawa bayan Laila ido. Ita kuma ko a jikinta domin ta saba da hakan shiyasa ma ta sakawa idanunta tabarau. Bayanta ya koma yana hararan duk wanda yaga idonsa a kanta. Da haka suka isa wani office a hawa na biyu. A bakin office d’in Laila ta tsaya tana amsa gaisuwar wata mata wacce aka rubuta Secretary a kan teburinta dake kusa dasu. Kwankwasawa tayi sau biyu aka musu izini suka shiga Haydar yana shiga sanyin Ac ya fara dukansa tamkar wanda ya shiga kankara. Mantawa yayi da 6oye bayan Laila da yake yi ya hau kalle-kalle yana jinjina tsaruwar Office d’in da yake ganin irinsu a fina-finan turawa. “Gimbiya Laila.�? Haydar yaji an kira wacce tasa ya dawo da kallonshi kan mamallakin ma’aikatar wanda ke zaune a kan office chair yana juyawa gefe da gefe. “Alhaji Abdul.�? Itama Laila ta kirashi tana zama a d’aya daga cikin kujeru masu fuskatar tasa. “Kina tsufar dani Laila, ki kirani da sunana yanda kika saba.�? Ya k’arishe maganan yana murmushi mai bayyana fararen hakwaransa. Haydar dake tsaye har yanzu ba’a bashi izinin zama ba ya lura akwai sanayya tsakanin mutanen nan biyu. Kuma a yanda yaga mutumin na aika mata kallo na k’auna da kuma wani abu kamar obsession yasa yaji kamar kar yayi aiki a k’ark’ashinsa. “Sit down young man.�? Yace da Haydar dake k’ok’arin saisaita nitsuwarsa. Zama yayi ba tare da yace komai ba yana kallon mutumin. Bak’i ne amma ba har can ba, yana da k’iba daidai irin ta manyan masu kud’i. A kalla zai yi shekara hamsin ko k’asa da haka, sannan ganinsa kad’ai da Haydar yayi ya gane cewa mutumin ya gogi duniya itama ta gogesa. Gyaran muryar da Laila ke yi yasa ya dawo daga tunanin da yake yi ya kalleta yaga tana masa ido, amma bai gane me take son fad’a ba. Zare masa ido tayi kana ta juya idonta kad’an gurin Alhaji Abdul. Sai a lokacin ya gane ya had’e bakinsa alamar ‘O�? kana ya maida dubansa ga mutumin wanda ya d’aga gira d’aya sama yana kallonsu duka. “Good morning Sir.�? Haydar ya gaisheshi. A gefe kuma Laila ta sauk’e ajiyar zuciya, me Haydar yake tunani da ya kasa yin abunda ya dace? “Hmm, me sunanka?�? Alhaji Abdul ya tambayi Haydar yana masa wani irin kallo mai wuyar fassara. “Aliyu Haydar.�? “Just Aliyu Haydar ko akwai wani suna a gaba?�? “No sir, Aliyu Haydar kad’ai.�? “But suna Haydar is part of Aliyu, ko ba haka ba?�? Gyara zama Haydar yayi cikin rashin nitsuwa da kuma k’osawa da tambayoyin yace, “Hakane Sir.�? “Please can we proceed? Saboda akwai inda zanje daga nan.�? Laila ta fad’a don ta lura Haydar bai ji dad’in tambayar ba. Haydar mutum ne mai amsa tambaya kai tsaye amma ta lura baya son tambaya akan sunansa. Hannu Alhaji Abdul ya mik’awa Haydar amma kuma hankalinsa na kan Laila wacce ke murmusawa tana masa magana. Haydar ya mik’a file d’inshi ga Alhaji Abdul, shi kuma ya ajiye a gefe suka cigaba da hira shi da Laila akan wata kwangila. “Bana son harkar da zai sa shiga da ficena ko hark’allana da mutane yayi yawa. So a hakan ma Alhamdulillah, Laila Beauty da kuma Pharmacy da Mas’ud ke rik’e dashi sun isheni yin rayuwa.�? “Ni dai ke zan bawa wannan kwangila, kuma bazan daina miki tayinta ba har sai kin yarda kin kar6a.�? Fad’in Alhaji Abdul yana bud’e large envelope d’in Haydar. Nitsuwa yayi sosai tamkar bashi ke cakalar Laila da tsokana d’azu ba. Wasu rubuce-rubuce yayi a jikin wata takarda kana ya mik’awa Haydar yace, “You are one lucky lad Aliyu Haydar, zaka fara zuwa aiki rana ita yau. So, anjima kad’an my secretary Jenny zata had’aka da wanda zai nuna maka kan aikinka ko?�? Kad’a kai Haydar yayi cikin farinciki don bai d’auka abun zai zo da sauk’i haka ba. “Thank you sir nagode sosai. Thank you Hajiya. Zan yi iya bakin k’ok’arina domin in ga nayi aikina.�? “You better do, sign here.�? Bayan wasu mintuna Laila ta mik’e tsaye tana cewa, “Ni zan tafi zan barka a nan, da fatan babu wata matsala ko?�? “Babu komai Hajiya. Nagode.�? “D’an uwanku ne shi ko?�? Alhaji Abdul ya tambayi Laila wacce ke saka sunglasses d’inta. “D’an uwa ne, me ka gani?�? “Akwai ruwan Shuwa Arab a tattare dashi amma kuma kamar ya had’a ruwa damu Hausawa, I don’t know ko idona ne. Kana mini kama da wani wanda na sani but na rasa gane waye.�? Shiru Haydar yayi ya k’ame jikinshi guri d’aya tamkar bai ji maganar da akayi a kansa ba, ba tambaya bace balle ya bada amsa ko da kuwa ya sani. Alhaji Abdul da Laila suka zuba masa ido suna kallonshi wanda hakan yasa Haydar yaji duk ya tsargu. Dariya sosai Alhaji Abdul ya saka wacce tasa hankalin kowa ya dawo kanshi kana ya tashi tsaye ya mik’awa Haydar hannu yana cewa, “Welcome to Lu’a Ventures.�? “Thank you Sir.�? Fad’in Haydar shima ya mik’e tsaye suka yi musabaha, a ranshi kuma yana mamakin yanda suka sakawa ma’aikatarsu wannan suna wanda ya tashi dashi a bakinsa.
Mum Fateey 👌
