Karfe A Wuta Chapter 51 By Ayshercool
Kamar Nabila za ta yi hauka, tana kallon kiran Barrister Kabir yana shigowa wayarta, amma ta share, taƙi ɗagawa, ƙarshe ma rejecting kiran na sa ta din ga yi, taƙi ɗagawa babban burinta kawai Viper ya ɗaga wayarta, amma yaƙi ɗagawa.Kwana tayi cikin zullumi, da addu’a kar Allah ya bawa Nasir nasarar kama Ɗan mama, dan a labarin Viper ba ta ji yadda aka same shi ba, balle ta san ingancin kasancewar sa tare da shi, tare da tabbacin ba zai faɗi in da Viper yake ba, kodayeke ta san ba zasu taɓa janyo wanda zai cutar da su ba.***Abdul ne zaune a gaban Indabo, sai zazzaga masa faɗa yake yi, ya haɗe rai yana ta muzurai.”Ina magana kana shan kunu, Abdul ko ka ƙi, ko ka so dole ka yi aure, idan ba haka ba, babu yadda za ayi a ɗauki takara a baka, na gaya maka dan ba zaka yi mini asarar wahalar da na yi shekaru ina yi ba, dole ka je ka gano yarinyar party chairman ku daidaita, ko baka santa ayi, idan ya so daga baya sai ka auro wadda ka ke so”Cikin damuwa ya ce “Daddy, ya za ayi ace na auri wadda ba na so, ni tun ban ganta ba, ba na sonta wallahi, a bar ni zan kawo wadda nake so ɗin”Indabo ya ce “Inaa lokaci kuma ya ƙure maka, arranged marriage ɗin nan, duk cikin manufa ce irin ta siyasa, dan haka dole ka yi haƙuri, ka je ku daidaita” Abdul ya yi shiru bai ce komai ba.Indabo ya ɗora da cewa “Sannan za’a fara haɗa structures a kowacce mazaɓa, tun yanzu za ku fara campaign kafin ƙaddamar da takararku” Indabo har ya gama maganganun sa, Abdul bai saki fuska ba, yayi ya gama ya tashi ya bar office ɗin.Yana fita P.A ya shigo, ya ce “Distinguish yaya dai nake jiyo muryarka tun daga waje?”Indabo yayi tsaki ya ce “Abdul mana, gaba ɗaya yaron nan ba shi da hankali, wai shi ba zai yi aure yanzu ba, so yake yayi mini asarar wannan uwar wahalar da na sha muka kawo wannan matakin”P.A yayi murmushi ya ce “Rabu da shi, mu cigaba da dukkan shirye-shirye da suka dace, kuma a cigaba da bin malamai, dan Abdul akwai taurin kai, a kan auren nan zai iya fasa takarar amma a cigaba da matsawa”.Imdabo yayi tsaki ya ce “Yaya ake ciki? Ya batun yarinyar nan?””Mu na nan muna bibiyarta, sai dai bakin zaren gano in da Viper yake ne aiki, balle ayi masa tarkon da ita. A binciken da nake yi, shi wannan ɗan sandan ya kama liti, kwanansa kusan huɗu a hannunsa, aka ce lallai ya sake shi”Indabo cikin damuwa ya ce “Waye ya ce a sake shi ɗin?”P.A ya girgiza kai ya ce “Ban sani ba, haryanzu babu trace na wanda yake taimaka masa, kuma Viper yana nan a cikin garin nan yana yawonsa, sai dai gaskiya ƙarƙashin kulawar wani yake duk abin da yake yi “”Kaii wai wannan wane irin abu ne? Hankalina kullum a tashe yake, ban san ta ina zai ɓullo mini ya ce zai ɗauki fansa ba, ka san ba zai taɓa barina ba, shi ma wancan banzan da duk laifinsa ne, ya kasa komai ya kasa kamo shi ya kasa gano in da yake, duk shi ya ɓata lamarin, da bai tabattar da Viper ya mutu ba tun a wancan lokacin, ina cikin tashin hankali”.”Ka kwantar da hankalinka distinguish, Viper fa zai zo hannu, ko da me yake yawo, ka yi haƙuri in Allah ya yarda babu abun da zai faru sai alkhairi” yayi ajiyar zuciya ba dan ya gamsu da maganganun P.A ba.***Daga wurin Indabo Abdul gidansa ya wuce, ya tarar da Ramma na ta uban bacci, motsinsa a ɗakin ne ya saka ta farka, ya kalleta ya ce “Baccin nan ba ya isarki ne?” Ta ɗaga masa gira alamar eh.”Ko ki na da ciki ne?””Allah ya kiyaye, ya tsari mahaifata da ƙara ɗaukar ƙazantarka”Ya ce “Hmm, ki bari cika baki, ki bari ayi gwaji tukuna”Ramma ta ce “Ba abun da za a gwada”Lambar saif ya kira, ya ɗaga ya ce “Yeah””Saif daddy ya ɓallo ruwa fa”Saif ya ce “Zancen auren dai?””Shi fa, wai wata ‘yar party chairman, ni tun ban ganta ba, ba na sonta wallahi dan kawai zan yi takara, sai na auri wata wadda ba na so, ya dage ya dage, kamar na gudu wallahi”.”Kai fa ka fiye gaggawa, ka bi su a sannu tukuna, ka je ka ga yarinyar “Abdul ya ce “Ba ma wannan ba, Nina ta ga yarinyar nan a gidan nan, tana ta yi mini hauka, ga maganar auren nan idan ta ji, ban san haukan da za ta yi ba, ni gaba ɗaya na rasa abun yi ma”.Saif ya ce “Lallai ma Abdul, ba ka mayar musu da yarinya ba, kai baka kasheta ba, ka bar ta to yaya zaka yi da ita?”.”Mu haɗu in anjima a joint kawai”Saif ya ce “Shikenan, Allah ya kaimu anjiman” yana kashe wayar ramma ta kalleshi ta ce “Bariki babu riba, dama duk wata hanya idan ba ta Allah, ai ba mai ɓullewa ba ce ba your excellency, na ga ku duniyar kawai ku ka saka a gaba, lahira kuma kun bar mana mu talakawa mu nema. Allah ya bamu a can.Ni dai in an tashi, a taimakawa ‘yan garinmu da hanya, a gyara mana babban asibitin garinmu, sai kuma makarantunmu, dan Allah kar a manta da mu”Yayi murmushi ya ce “Ki na yi mini rashin kunyar za ayi abun da ki ke so?””To ba ma so, dama kuɗin haram bana halal ba” bai ji haushi ba, ya kwanta a jikinta, yana kashe mata murya, yana kiran sunanta.”Rahmaaaa” ture shi tayi a fusace ta ce “Ni ka daina yi mini wannan abun ‘yan iskan ba na so””Her excellency rahammaaa” yayi maganar kamar mai shirin yin shagwaɓa.Wani uban takaici ya cika mata zuciya, ta kasa ture shi, sai ma cakulkuli da ya fara yi mata, ta dunƙule hannunta tana kai masa duka, amma ko a jikinsa, dariya ma yake yi, abun nata gwanin ban dariya.***Tun da aka idar da sallar asuba, Nabila ba ta koma bacci ba, ta shirya, gari na yin haske, ta ɗauki jakarta ta fice daga gidan, fuskarta sanye da niƙabi.A hanya gari ya ƙarasa waye mata, ta tafi gidan su Viper.Duk da akwai tafiyar ƙafa sosai, daga titi zuwa gidan, amma yanzu idan tayi bulayin, tana iya gano gidan. Kasancewar wurin da nisa, gari yayi haske sosai ta isa gidan.Ta tarar da su suna ta shirin ɗora karin kumallo.Walid ya kalleta da mamaki ya ce “Lafiya?”Ɗan mama ya ce “Mun shiga uku, wannan akwai mayya wallahi, idan ba kama mu aka yi ba, hankalinta ba zai kwanta ba”.Liti ya miƙe a fusace, ya ɗauki wuƙa a kan taga, ya ce “Ke ware dan kazakazanki, ko shi bai kashe ki ba sai na kashe ki ni, jarababbiya kai, uban me ki ke nema a wurinmu? Ke bayan haushinki da nake ji, har da wannan banzan saurayin naki ɗan sanda da ya din ga azabtar da ni, sai na yi masa ido ɗaya, ba zai bar aikin ɗan sanda ba sai da tabona”.Walid ya ce “Meya dawo da ke kuma? Me ki ke nema?”Ta ce “Viper””Me zai yi miki?””Ina son ganinsa ne””Yana cikin yanayi mara daɗi, ki yi haƙuri ki tafi kawai, ba zaki ji daɗin abun da zaki gani ba”Nabila ta ce “Komai munin abun zan gani, zan jure””Kin ga, ba mutuncinki bane ba, kina ‘ya mace, ki dinga sintiri a gidan nan, wurin mutane irinmu ma, yakamata ki daina zuwa””Zan daina, idan na samu abun da nake so, ka ƙarasa mini labarin jauhar, ni lawyer ce, ina son ya ɗauki fansa ta hanyar da ta dace ne, kuma niyyar da nake da ita ta alkhairi ce, dan haka na san ba zaku cutar da ni ba” tayi maganar tana nuna wa Walid id card ɗin ta.Walid ya ce “Na san ke lawyer ce”Cikin mamaki ta ce “Ta yaya?””A ina na saka aka ɗaukko mini ke?” Sai kuma tayi shiru tana kallonsa.”Baki isa na bari ki raɓi Viper ba, muddin ban san wacce ke ba. Hatta gidanku na sani”.Tayi ajiyar zuciya ta ce “Nayi mamaki, dama jiya na kira Viper ya ƙi ɗagawa, wanda ya kama ka, ba saurayina bane ba, yayana ne. Kuma da shi nake taimakawa a kan neman Viper, yanzu haka ya tabbatar mini da yi wa wani ɗan mama tarko, ya ce idan ya kama shi, an ce zai samu Viper, sai dai ban san waye ɗan maman a cikinku ba”Walid ya ce “Wani tabbaci muke da shi, ba zaki cutar da mu ba, ko ki ci amanar mu ba, duba da yadda ki ke zambatar ɗan uwanki cikin aminci”Nabila ta jinjina kai ta ce “Haka ne, ni zan tsaya a tsakiya ne, na bi ɓangaren gaskiya, and no matter what, ina da ikon tsayawa duk wanda nake ra’ayin tsayawa. Amma dan Allah ku bari na ganshi na yi magana da shi.Walid ya ce “To”Liti ya ce “Ni fa ban yadda da yarinyar nan ba mai laya, ya ya za ayi ta ci amanar ɗan uwanta kuma, ta ce tana tare da mu?”Walid bai kula shi ba, ya buɗe mata ɗakin da Viper yake ciki, yana zaune daga shi sai gajeren wando, ko riga babu a jikinsa.Jiki a sanyaye ya ce “Maganar da ki ka faɗa gaskiya ce, ƙwaƙwalwar viper ta fara samun matsala, a dalilin damuwa da ta’amalli da miyagun ƙwayoyi, yana buƙatar ganin likita, amma tayaya? Ina tsoron mu fita da shi a samu matsala”.Duk ganin ƙirarsa ta razanata, yana zaune, daga zaunen ma maye kawai yake yi, ga uban karan taba guntu-guntu a wurin.Kawai ta shiga ɗakin ta nufe shi kai tsaye.Walid ya ce “Ki daina gangancin tunkararsa yadda ki ka ga dama, ba ya cikin hayyacinsa fa”Nabila ba ta saurare shi ba, ta je gaban Viper ta durƙusa, ya ɗago ya kalleta ya ce “Ban ce ki daina zuwa ba?””Ba zan iya ba ne, na fara jin abun da ‘yar madara take ji, idan ta ganka a yanayi mara daɗi, yaya za ta ji idan ta tsinceka a yanayin da ya fi na baya muni?” Ya zuba wa Nabila ido, wanda hakan ya tilasta mata kawar da kanta daga kallonsa.Ta cigaba da cewa “Yakamata ka ƙarasa mini labarin jauhar, kar na je na sakankance, ta dawo ta ƙwace mijinta, dan a labarinta na ga daga tausayi soyayya ta ƙullu, kuma nima dai gashi ba na son shaye-shayen nan, kar na je sai na yi nisa ta ƙwace mini kai, tana ina ne yanzu?” Tayi maganar tana jiran amsar da zai ba ta.Ya ƙura mata ido, har sai da gabanta ya faɗi, ta fara tunanin ko shaƙetan zai yi.Amma ya jingina da bango yana lumshe ido.”Talk mana” tayi maganar da sigar rarrashi.Su liti duk suna window suna ganin ikon Allah, su ihu yake ta yi musu, yana kiran matarsa, amma yanzu ya nutsu, ko hargowar bai yi mata ba.”Na ga haryanzu baka gama dawowa dai-dai ba, bari na je zan dawo, sai mu yi magana ka din ga ɗaga wayata amma, sunana Nabila Yusuf maitama. Amma babanmu arfa yake ce mini, ranar arfa aka haife ni, shiyasa nake da sa’a sosai kuma yana son mamana sosai da sosai, kamar dai yadda ka ke son ‘yar madara. Amma dan Allah ka gaya mini da wuri tana ina, kar in zo daga baya, ka ce baka san zance ba baka sanni ba”. Tayi masa maganar cikin sigar shagwaɓa.Yayi shiru, ko tari bai yi ba.Har ta gama surutanta, bai yi magana ba, ta tashi a hankali ta fito, ta kalli Walid ta ce “Zan je gidan masu rangwamen hankali, na yi magana sa likitocin ƙwaƙwalwa, idan ta kama dole ayi arranging yadda zai ga likita, ina matuƙar buƙatar hankalinsa, kafin komai ya yiwu, sannan ku rage zirga-zirga an matsawa yayana lamba a kan kama shi, kuma ya dage by any means sai ya kama shi”.Walid ya ce “Shikenan, mun gode da gudunmawarki, sai anjima” ya jinjina kai ta fice ta tafi.Suka sake leƙa Al’amin, ya kwanta a wurin, yayi ruf da ciki, wanda tun bayan sallar asuba suke fama da shi, sai ya fita ya kashe madaki da Indabo, da ƙyar suka rufe shi a ɗaki, da kokowa, dan kuwa sun sha wahala, duk da su uku ne, shikaɗai neman gagararsu yayi, amma da Nabila ta zo tana yi masa magana bai yi wannan hargagin ba.Sai kusan sha biyu saura ta isa wurin aikinsu, mai yi musu goge-goge ne ya sanar da ita, Barrister kabir yana ta nemanta, ta ce masa to, sai da ta shiga office ɗin ta, ta dafa tea a dispenser tana da biscuit a office ɗin ta, ta haɗa ta karya.Sai da ta kammala, sannan ta tafi office ɗin Barrister kabir, yana ta shiri zai fita yana da wani meeting, duk yadda yake yi mata wasa, idan suka haɗu yau sai ya sha kunu ya ɗaure fuska tamau.”Sir an ce kana nemana?”A ƙule ya ce “Au an ce nema? Tun jiya nake kiran wayarki, baki ɗaga ba, baki biyo ba ki ji dalilin kiran”Cikin ko in kula ta ce “Sir ban taɓa yin hakan ba, yakamata ayi mini afuwa ayi mini uzuri””Shut up, ba zaki janyo mana magana ba, kin san wacece matar nan kuwa?””But sir, this is my personal trial, ba under law firm ɗin nan zan yi shari’ar nan ba”.”Ina magana kina magana? Amma da ID card ɗinmu ki ke amfani ko? You better watch what you are doing, faɗa da matar nan tamkar faɗa da manyan mutanen nan ne, dan su take yi wa aiki”Barrister Habib ne ya ƙaraso, yana faɗin “Subhanallah, lafiya kuwa meyake faruwa?”Barrister kabir ya ce “Ka san yarinyar nan office ɗin Naja’atu Bunkure ta je neman magana, wai tayi mata bayanin wani case da yake hannunta, ina ruwan Nabila da Bunkure?” Idanun Nabila ya cika da hawaye, tamkar ta fashe da kuka, kowa ya santa da barrister Kabir, suna good time sosai, amma yau yayi mata ihu a gaban mutane.Barrister Habib ya ce “Barrister Nabila, garin yaya, meyasa ba kya shawara waye ya aike ki? Kin san wacece Bunkure kuwa? Gaskiya kin yi wauta, mu je in ji ya aka yi, barrister yau da kai da daughter taka mu ganku a rana, amma ayi mana afuwa, ka san yanzu nine abun koyinta, mun shirya tana son aiki tana ƙoƙari. Ayi mata afuwa”.Kabir ya girgiza kabir ya ce “Rigimarta tayi yawa””Ayi haƙuri ke kuma wuce mu je” Barrister Habib ya sakata a gaba, suna zuwa Office ɗin sa, ta fashe da kuka.Ya ce “Ahhh ya haka? Kuka kuma karaya tun yanzu?”Cikin kuka ta ce “Kana ganin abun da yayi mini, ita wacece Naja’atun ba mutum ba ce ba? She’s just my senior kuma ni ba rashin kunya na yi mata ba, ajiye masa aikinsa zan yi nayi zaman kaina”Barrister Habib ya yi dariya ya ce “Kin bani kunya, waye ya ce miki ana gwagwarmaya babu ƙalubale ne? Dole ki shiryawa ƙalubale, and ki bar maganar resigning ɗin nan ba mafita ba ce ba. Yanzu yaya ku ka yi da ita?”Cikin tura baki ta ce “Ni sai na bar wurin nan””Kar ki ga laifinsa, maybe kiransa aka yi, aka ja masa kunne, dan haka ki yi masa uzuri ai bai taɓa yi miki haka ba ai, haba ‘yar ƙwalisa”.Ta zumɓura baki, tana goge hawayenta.”Yanzu yaya ku ka yi da ita?”Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce “Nothing much, alamu sun nuna babu gaskiya a lamarin nata, dan idan tana da gaskiya, zata gaya mini aka tsaya a lamarin yarinyar, amma ta kore ni, ta ɓuge da kiran sa.Sai dai an hana ni ganin shi wanda nake karewar ma, amma dai ya kwatanta mini gidan ɗaya mai aikin, na je an ce ta tashi ta koma garinsu. Amma ya tabattar mini da yarinyar ‘yar tofa ce, wai wani gari yaloko, amma bai san ina ba a tofa. Ni ban san ina ne ma tofan ba, balle na nemi gidan su yarinyar”.Barrister Habib ya yi shiru sannan ya ce “Kin tabattar a tofan ya ce miki take? A yalokon?”Ta jinjina masa kai alamar eh.”To shikenan, ki bani kwanaki i will get back to you. Amma ki daina garaje, ki din ga bin komai a hankali”Ta ce “To” ya din ga rarrashinta, har ta huce, ta tashi ta koma office ɗin ta”.***Tun da Abdul ya dawo, yake cika yana batsewa, ramma ko kallo bai isheta ba, ta cigaba da sabgoginta, ko abinci bai ci ba, ya nemi wuri ya kwanta.Haushi ya ishe shi, gaba ɗaya ba ta tasa take yi ba, karatun littafinta ne kawai a gabanta, babu tsammani ta ji ya fizge littafin hannunta.Ta kalleshi ta ce “Lafiya?””Wai ke wace iri ce ne?”Ta kalleshi ta ce “Kamar yaya?””Ke baki damu da ki ga mutum cikin damuwa ba, ki tambayi meyafaru ba?”Ramma ta ce “To ina ruwana da abun da ya dameka? Ni banda damuwar da ka saka ni a ciki? Bani littafina malam”.Abdul ya ƙura mata ido, ta tashi zaune ta miƙa masa hannu ta ce “Bani dan Allah”.”Me ki ke ganewa a ciki ne?”Ramma ta ce “Ko ba na ganewa, ai gara na karanta littafin, da kallon fuskarka ma, bani littafina malam” ta yi maganar tana haɗe rai.Wayarsa da take vibrating ya ciro, ya saka a kunnensa.”Yau Yakamata ka shigo Asibiti, yau zaka yi wa patient ɗin ka tiyata fa”Ya ɓata fuska ya ce “Yau ne amma baku tuna mini ba, ni na manta gaba ɗaya”.”An yi booking ɗin su, da wanda za su ganka, kusan wata biyu suna jira, ba su samu ganinka ba””Zan kira Doctor Anas,ya je yayi am sick, ba zan iya tiyata ba””Amma doctor… Cikin hargowa ya ce “Shut up, abun da na ce za ayi””To shikenan” ya ajiye wayar, ramma ta ce “Dama kai likita ne?””Ban sani ba, sai yanzu ki ga damar kula ni, saboda baki da imani, ki na kallo ko abinci na kasa ci”.”Kar Allah ya sa ka ci mana, kai har ka na bakin cewa wani bashi da imani Abdul yasar? Hala tsabar imanin ne ya sa kazo ka yi mini kurkuku a nan?””Ke fa taimakonki nayi, haka ki ka zo kalli yadda ki ka yi ƙiba, ki ka yi kyau, sai ma mun ci gwamnati, zaki fi haka ƙiba” yayi maganar yana taɓa damtsenta.”Ni meye nawa idan ma kun ci gwamantin, in sha Allah ma ba zaku ci ba, ace a rasa wanda za su jagoranci al’umma, sai mutanen banza masu lalata yaran mutane ” ya ce “Ok, Ai ba a wurinki muke nema ba””In sha Allah ba zaka ci ba, ko ƙuri’a ɗaya ba zaka samu ba”Abdul ya ce “Ke ki ka sani, na je na ga yarinyar da aka ce zan aura, kyakykyawa nutsatiyya, tabbatar Allah ba ya karɓar addu’arki”Da sauri ramma ta kalleshi ta ce “Nutsatiyya, ai ba zaka taɓa auren macen kirki ba, sai wadda wani ya lalata kamar yadda ka yi. Ai ko ka ganta a nutse ma, in sha Allah irinka ce zaka aura. Ba zan yi fatan Allah ya baka lalatacciyar ‘ya ba, dan ba ita tayi mini ba, amma in sha Allah sai ka auri lalatacciya” tayi maganar tana hawaye.Abdul ya ce “A’a gaskiya ba lalatacciya kamar ke ba, Nutsatiyya ce sosai, idan na aureta kar ki damu, ba zamu rabu ba, ai ana mugun tare tun da kin zama ‘yar hannu kema.Ta ce “Kai da Allah, kuma in sha Allah sauran wani zaka aura”Abdul ya ce “Nima saurana wani zai aura, balle ba zamu iya rabuwa da juna ba, mun riga mun saba, ni zan iya aure, amma ke ba zaki iya ba, kawai mu cigaba da rayuwarmu a haka rahma”.Hawaye wani na bin wani ta ce “In sha Allah, sai Allah ya kuɓutar da ni daga hannunka azzalumi kawai” Abdul tamkar jin daɗin tsinuwar da ramma take yi masa yake ji, ta zage shi tayi masa Allah ya isa, amma hakan ko a jikinsa, sai ma cigaba da tunzurata da yake yi ya ce “Ohhh kishi a fili, ki dai yi a hankali, kar ki yi zurfi a soyayyata, ‘yan mata ne da ni burjik””Eh tun da ga ka bunsuru ba” ta tashi tsaye tana kuka.Ya ƙyaƙyace da dariya ya ce “Bunsuru ya ajiye akuya ta mussaman a gidansa ba” kalmar akuyar tayi mata ciwo, kawai ta fita daga ɗakin ta bar shi, yana ƙyaƙyata dariya.***Indabo yana ta shiri zai koma Abuja, hutunsu na majalissa ya ƙare, ga shirye-shiryen da ake yi na fara zaɓen fidda gwani, wanda yake ta fafutuka a tabattar da yarjejeniyar da suka yi na ba wa Abdul takarar mataimakin gwamna. Sai dai sai fama yake da shi, idan yayi nan sai yayi can.Naja’atu Bunkure ce ta kira shi a waya, ta ce masa tana office ɗin sa na gidansa, tana son ganinsa.Ya san muddin ta yi masa zuwan gaggawa ba bu sanarwa, akwai damuwa ne, dan haka ya ajiye abun da yake yi, ya fita.Ya shiga ya zauna yana faɗin “Naja’atu masu ƙasa ya ake ciki ne?”Ta kalleshi ta ce “Ina Abdul?””Oho masa, yana can tasa shiririta ya tattara ya koma gidansa da zama””Akwai ƙura fa”Indabo ya ce “Wace irin ƙura kuma?””Yaya yayi da yarinyar da ya yi wa fyaɗe?”Indabo ya ce “Mun yi magana da shi, ya ce mini ya kasheta””Ka tabattar da hakan kuma? Akwai matsala fa. Wata shegiyar yarinya ta zo office ɗina, wai na bata bayanan in da aka tsaya da maganar yarinyar, wai zata tsayawa mai gadin nan, hankalina ya kasa kwanciya jikina yana bani, ba itakaɗai take wannan abun ba, akwai abun da ta taka, duk da na kira law firm ɗin su na yi musu warning, amma jikina yana bani akwai wata a ƙasa, kar ta zurafafa ta gano wani abu, dan yarinyar a tsaye take babu alamar kunya a tare da ita”.Indabo ya ce “Kin daɗe kina magance matsaloli da rigingimun da Abdul yake ɗaukkowa, amma ya aka yi na ga karaya a tare da ke yau?””Ba karaya nayi ba, ka san hausawa sun ce, rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya, na so ƙarasa aikin da kaina, amma ka ce na bari zai yi maganin abun, ka nemo ɗanka ka tabattar da bai bar wani trace ba, gobe in Allah ya kaimu zan tafi conference ɗin da shugaban ƙasa ya tura mu, dan haka ba zan samu damar zuwa gidan su yarinyar ba, dan haka ka nemo shi”Indabo ya ce “Naja’atu, idan aka samu matsala the blame will be on you, sakacinki ne”Naja ta girgiza kai ta ce “Sakacinku dai, na yi iya yi na ni, yadda ku ka yi da shi, ka sanar da ni” Indabo cikin hanzari, ya ɗauki wayarsa yana kiran Abdul, sai dai wayar taƙi shiga gaba ɗaya.Nabila har wata ramar dole tayi, saboda zirga-zirga, gashi kwana biyu ba ta je wurin Viper ba, gashi tana cikin damuwa da tsananin son ganinsa.Gaba ɗaya yanzu ba ta doguwar shawara, kafin ta tafi gidan Viper, yau ma haka babu tsammani sai ganinta suka yi rana tsaka.Duk suka bi ta da kallo, ta kalli Walid ta ce “Ina wuni””Lafiya ƙalau””Ya mutumina, ina fatan yana lafiya?”Walid ya ce “To da sauƙi dai, yana ciki”Liti ya ce “Wallahi ba zata shiga ba, ke ware, ni fa ban yarda da yarinyar nan ba”.Nabila ta kalli liti ta ce “Ka kiyaye ni fa, ba ruwanka da ni, ba wurinka na zo ba, wurin Viper na zo, zan duba lafiyar sa kuma mu yi magana”Walid ya ce “Dan Allah liti ka daina haka, mana wai me ta yi maka ne, ta bayar da haƙurin abun da tayi ai”Liti ya ce “Ni fa ba a iya yaudarata cikin sauƙi, fita malama, ba zaki ganshi ba””Ba zan tafi ba sai na ganshi, ba ruwanka da ni”.Ya zazzaro mata ido zai yi magana, ya ji an hankaɗe shi daga bakin ƙofa, Viper ya fito yana ƙanƙance idanunsa.Suna haɗa ido, ta sakar masa murmushi, mai cike da nuna farincikin ganinsa, duk kallon na sa tsoro yake bata.Liti ya ce “Mai zamani mai hakan yake nufi? Kai ma ka yarda da wannan munafukar, ita fa ta saka aka kama maka ni, aka rufe ni so take sai an kama ka fa”.Walid ya ce “Kai ɗin uwar me ka ke tsinana masa?”Duk bai kula su ba, ya taka ya fito ya ɗauki brush da toothpaste, ya matsa.”Ina kwana” tayi maganar tana bin bayansa. Bai amsa ba, ya durƙusa yana wanke bakinsa.Wayarta da take ta vibrating ta ciro, ta saka a kunnenta ta ce “Hello””Ke Sumayya ce””Ohh sumy, kullum cikin sauya lamba kamar ‘yar yahoo?””Malama kwana nawa ina nemanki a waya ban same ki ba, kuma baki neme ni ba”Nabila ta ce “Sorry na yi laifi”Sumayya ta ce “Yaya ku ka yi da Naja’atu baki gaya mini ba”Nabila ta ce “Ke zan zo gida na baki labari, ina wani abun ne yanzu, dan na kusa rubuta resigning na ajiye musu tsiyar su, na fuskanci Naja’atu Bunkure gaba da gaba, naga gani take ita wata jan wuya ce, ko ban kaita ƙasa ba sai na razanata” gaba ɗaya suka zuba wa Nabila ido, cikin hanzari Viper ya ɗago ya zubawa Nabila ido, ta katse wayar ta ce”Meyafaru ku ke kallona ne?””Naja’atu Bunkure” ya maimaita yana kallon idon Nabila.Cikin rawar baki, saboda tsorata da kallon da yake yi mata ta ce “Ka santa ne?””Mu je waje mu yi magana”
Ayshercool 08081012143
