Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 49 Complete Novel
*ASM Bk2049*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………tsaye tay a bakin kopar k’irjinta na ci gaba da bugawa da sauri da sauri ga tsoro da ya kamata ta d’an d’auki lokaci a haka kafin tay k’arfin halin kai hannu yana d’an rawa ta d’an kwankwasa shiru bata ji an yi magana ba hakan yasa ta k’ara d’an kwankwasawa da d’an k’arfi k’asa k’asa ta jiyo Muryar shi yace “Who is dat” shiru tay har saida ya sake tambaya amman ta kasa bud’e baki tace itace jiyo shi tay yace a shigo kopan a bud’e take da turanci d’an jimm tay kaman bazata shiga ba can ta d’an runtse ido kafin ta bud’e fuska a d’aure slowly ta tura kopar, tana shiga suka had’a ido da shi yana zauna akan kujera 3 seater yana operating system jikin shi sanye da jar armless gabanta anyi bak’in rubutu sai bak’in wando 3-quater abu dae sai dae ace Tubarkallah daga gefen shi c-table ne a saman table d’in kwalin lemu ne aje sai tumbler daga gefe kuma ledar take away ce mai d’auke da tambarin wani Eatery, bin ta da ido yay ya yi matuk’ar mamakin ganinta duk da fuskar shi bata nuna hakan ba itama tsaye tay tana mashi wani irin kallo cike da 6acin rai don bata tsammaci ganin shi haka ba wato dae zargin ta ya tabbata na bai damu da abunda ya aikata mata ba tunda gashi zaune ya warke har yana latse latsen computer ba tare daya nemeta ba tunda suka dawo,
“Come inside” taji cool voice d’in shi ta fad’a kaman bazata shigan ba ta d’aure fuska tamau can dae ta nufi cikin a gefen shiga inda kujerun suke ta ja ta tsaya tana kallon gefe kallonta kawae yake ya lura da yadda ta d’aure Fuska can yace “come and have a seat” banza ta mashi kuma bata kalle shi ba har saida ya k’ara mata magana kan taje ta zauna a d’an fusace ta kalle shi tace “ba shi ya kawo ni ba” still idon shi na a kanta ita kuma ta k’ara juyar da fuskarta can yay sigh yace “am listening miya kawo ki?” d’an yamutsa baki tay alamun mamakin jin yadda ya tambayeta seemed he doesn’t care at all aikuwa sosae ranta ya k’ara 6aci idanun ta suka ciko da k’walla ta juya cikin rawar murya ta fara magana “Zuwa nai in fad’a maka ka cuce ni, ka zalunce ni Ya Haisam, an yarda da kai amman kaci Amana kayi man abunda wani ma ban tunanin zai man hakan balle kai, kace ni matsayin k’anwar ka ta jini ka d’auke ni amman abunda kai man ya tabbatar da k’arya ne don in hakan ka d’auke ni baza ka ta6a son wani yayi man hakan ba balle kuma kai da kan ka, kowa nawa ya amince maka amman duk da haka ka ha’ince su kai man abunda na tabbatar ba kuskure bane da niyya ne tunda sai da na rok’e ka amman ka k’i saurare na Saboda dama kana neman dama ne don ka fara nuna alamomin kana son ta6a jikina….” dakatawa tay tana goge kwalla shidae sai kallonta kawae yake bazaka gane yanayin da yake ciki ba, tsayawa tay da goge kwallan cikin muryar kuka tace “..gashi nan sakamakon abunda kai man ka jawo mana abun kunya wanda na tabbatar gwaggo in taji zuciyarta na iya bugawa ta mutu….” dakatawa tay tana sheshsheka sai lokacin yanayin fuskar shi ya canza ya d’an k’ank’ance ido alamar tunani kan abunda ta fad’a kan shi ne ya d’aure gashi tak’i cigaba da Maganar sai kuka take faman yi tsam ya mik’e ya nufo ta ya tsaya gabanta Slowly ya furta “What is it?” d’ago kai tay ta kalle shi cikin kuka tace “CIKI gare ni!!!” yanayin kallon da yake mata ne ya sauya with surprise written boldly al over his face ya furta “U’r pregnant???” Kai ta d’aga mashi alamar eh kan shi ya d’aure ya ayyana taya hakan zai faru sai kallonta kawai yake ita kuma tana cigaba da yin kuka ta juyar da face d’inta gefe can taji yace “how did you know dat u’r pregnant?” shiru tay mashi don sai taji tambayar ma ta rainin wayau ce tunda ai yasan karatun da take, “am asking you Zarah” ya k’ara fad’a ba tare da ta kalli face d’in shi ba ta fara gaya mashi ciwon da take da yadda aka fara gulman ciwon da take a school har zuwa yadda taje ta siyo Pt strip ta auna tana gama fad’i mashi ta kai hannu ta bud’e yar purse d’in dake ruk’e a hannunta ta fiddo shi dama bayan ta shirya Fauzy ta saka mata shi tace in tazo ta nuna mashi mik’a mashi tay ya kai hannu ya amsa ya fara dubawa nan take ya tabbatar ma kan sa da gaske cikin gareta, d’agowa yay mamaki shimfid’e akan fuskar tashi ya kafeta da ido sai lokacin ma ya lura da canzar da tayi tay wani fayau dama gashi bak’ak’en kayane a jikinta, shiru ya rasa mi ma zaice abun ya matuk’ar bashi mamaki abun da akai just once amman ace har ciki ya shiga jin yayi shiru yak’i yace Komae yasata cewa “Dama nasan bazaka iya cewa komae ba, iya cuta dae ka cuce ni Ya Haisam yanzu da an san da wannan abun kunyan shikenan Mutuncin mu ni da gwaggota ya gama zubewa a idon mutane ga school ma da an sani korata za’ai ga dangin Baffana su bansan iya abunda zai faru ba in suka ji zasu ce dama abunda gwaggo ke sani ina aikatawa kenan shiyasa tai duk yadda zatayi ta hana in auri wanda suka za6a man Saboda manemin mata ne to gashi nan nima ashe abunda nike aikatawa kenan, wllh Ya Haisam ka zalunce mu kayi amfani da son zuciya wajen tarwatsa mana farinciki ko wanda a da za’a aura man da yake halin shi bai cutar da ni har haka ba don nasan Ya Abbas ya fad’a maka dalilin fasa auren mu sai kai da aka amince mawa kai da nake kallo matsayin Yayana uwa d’aya uba d’aya….” Kuka sosae take shi kam zuba mata ido kawae yay don a rayuwar shi wani bai ta6a tutsiye shi haka ba itace mutum ta farko, d’an tsagaitawa tayi tace “zuwa nayi dama in fad’a maka game da shi sannan in sanar da kai zubar dashi zan yi don bazan bar wannan abun kunyar a tare da ni ba ko don gwaggota da sauran dangi na kuma kai ma hakan zai rufa maka asiri duk da kai ka za6i zubar man da Mutunci to ni bazan so in zubar maka da naka ba don har yanzu kana da girma a idona sai dae ina k’ara tunasar da kai ka cuce ni ka ci amanar yarda” tana kai k’arshen Maganar tay gaba abunta fuu bai juya ya kalleta ba har ta fuce ya zuba ma abun hannun shi ido jikinshi yay weak sosae slowly ya d’an matsa ya zauna akan hannun kujera ya d’aura ha6ar shi akan hannun shi guda da ya dungule ya rasa ma murna zai yi ko kuwa don tunda yake bai ta6a jin fargabar wani abu ba irin wannan sosae kuma yay mamaki bai ta6a kawowa hakan Zai faru ba runtse ido yay ya shiga tariyo kalaman Fatuu har zuwa k’arshe da tayi zancen zubar da cikin tunanin abunda yakamata yayi ya fara zuciyar shi ta raya mashi yakamata yay saurin dakatar da ita fa don zata iya aikatawa wani abun kuma yazo ya sameta…..
Tana ta faman goge k’walla ta fito daga cikin gidan ko kallon inda su Officer suke zaune bata yi ba ta nufi Keke Napep d’in bayan ta shige tace mashi su tafi bai tanka mata Maganar lemun da ya ce ta fito mashi da shi ba ganin halin da take ciki, bayan ya ja Napep d’in sun bar wurin d’ayan Officer wanda bai san Fatun ba ya kalli abokin aikin nashi yace “ita waccan d’in wacece naga kaman kasan ta” yana murmushi yace “nima ban san wacece ba kwanaki ne Yalla6ai yazo tare da ita” da alamun mamaki yace “nan gidan suka zo?” Kai ya d’aga yace “eh da daddare inaga wurin k’arfe 11 ma” jinjina kai d’ayan ya hau yi alamar mamaki kafin yace “wato ya fara kawo mata kenan amman nayi mamaki koda yake dama irin Mutanen nan sun fi bada mamaki” yar dariya d’ayan yay yace “nidae ban ce maka ya fara kawo mata ba ka sani ko yar uwarsu ce”
“Kai tunda kake aiki a gidan nan ka ta6a ganinta koda in masu gidan na nan kuma koda yar uwarsu ce mi zaisa ya zo da ita a wannan lokacin tunda yasan gidan ba kowa kai dai Allah ya kyauta kawae gata ma ta fito tana goge fuska da gani kuka take” da alamun mamaki d’ayan yace “na gani wllh kasan ko rannan ma haka ta fito tana kukan wurin d’ayan dare…..” Katse shi yay ya maimaita lokacin da ya fad’an had’i da ruk’e ha6a d’ayan yace “wllh amman dae tace ya tsaya yin wani aiki ne a computer sai bacci ya kwashe ta lokacin da ta farka kuma shima ya riga yay bacci” d’ayan yace “to in haka ne miye na ta fito tana kukan?” Still da murmushi yace “zazza6i ne ya rufeta tace dalilin farkawar tata kenan amman dae…..kawai muyi mashi kyakkyawan zato kaman ko yaushe” dan ta6e baki d’ayan yay yana wani murmushi.
Tana cikin Napep d’in wayarta ta fara ringing duk a tunanin ta Fauzy ce ta bud’e purse d’inta ta fiddo wayar tana kallon screen d’in taga sunan Haisam ya bayyana wani irin tamke Fuska tay tak’i yin picking ta d’aura wayar a kan laps d’inta har ta katse can sai ga wani kiran ya sake shigowa still tak’i d’auka saida ya kira na ukku mai Napep d’in yace mata ana waya cikin disasshiyar murya tace mashi tana ji ya jinjina kai yana kallonta ta side mirror ganin tana ta goge kwalla yasa shi ce mata tayi hakuri ta d’aga mashi kai kawae. Tsaye yake wayar shi ruk’e a hannu ganin ya kira har sau ukku bata d’aga ba yasa shi yin shiru kaman mai yin tunani can ya juya ya nufi inda bed d’in shi yake ya zauna a edge d’in gadon ya kai hannu ya d’auki wayar landline dake aje a saman bedside ya kira gate saidae har ta tsinke itama ba’a d’aga ba don su Officer d’in na wajen gate maidawa yay ya aje ya fara k’ok’arin kiran shi ta wayar dake hannun shi ringing biyu Officer d’in ya d’aga tun kafin yace wani abu Haisam yace mashi akwae wata da ta fita yanzu ya bita ya tsaidata gashi nan fitowa Officer na jin haka ya gane wadda yake magana akai yace mashi ai tare da mai Keke Napep take kuma tana fitowa suka tafi yanzu ma yasan sun yi nisa tun kafin ma ya k’arasa Haisam ya katse kiran yay zaune jigum ya rasa miya kamata ma yayi gaba d’aya ya shiga damuwa har fuskar shi ta nuna sanin abortion ba k’aramin hadari ne dashi ba komai zai iya faruwa gashi yasan halinta har yanzu she’s stubborn tunda ta fad’a abunda zatai kenan, k’ara kiranta yay still ba ta d’aga ba bayan kiran ya yanke d’an shiru yay can kuma sai ya shiga cikin messages ya tura mata sak’o kamar haka,
Don’t do anything Zarah, pick my call now.
Bayan ya tura da yan mintuna ya sake kira still bata d’aga ba tafin hannun shi ya kai ya rufe daga hancin shi zuwa ha6arshi yana breathing heavily yasan shi yay mata laifi amman bai yi tunanin zata iya mashi haka ba, lokacin da sak’on ya shigo wayar ta ta duba d’an ta6e baki tay a ranta tace ko na d’auka ba abunda zaka fad’a man k’arshe kace kar na zubar tunda ba kai ne a matsala ba dama ance komi namiji yay ado ne to wllh sai na zubar dashi k’arshe ma sai ta saka wayar a silent kawae, suna hawa titi mai Napep d’in ya tambayeta ina zai kaita ta ce babban Asibiti suka d’auki hanya,
Yanata zaune can ya yanke yabi bayanta ya mik’e da sauri ya nufi cikin Corridor bada Jimawa ba ya fito ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt bayan ya d’auki wayar shi da car key ya fice da sauri, parking space ya nufa ya bud’e Motar da zai hau ya shiga bayan yayi mata key ya fito ya tunkari gate yana sakin horn da k’arfi tuni su Officer suka mik’e aka zuge mashi Gate d’in ya fice ko ta kan d’aga mashi hannun da suke bai bi ba, bayan wanda ya bud’e gate d’in ya rufe ya dawo yace ma abokin aikin ka lura da yadda ya fita kaman akwae abunda ke faruwa yace mashi eh shima ya lura kuma yana tunanin game da yarinyar nan ne da ta zo tunda ya kira yana a tsaidata d’ayan ya d’an jinjina kai yace Allah ya kyauta to ya amsa mashi da Amin, Har ya fito daga Unguwar bai ganta ba dama bai yi tunanin zai gantan ba tunda ance a Napep take tunanin inda yakamata ya nufa ya shiga yi ganin ranar Juma’a ce yasan tana komawa gida Weekend yasa ya yanke zuwa can,
Suna zuwa gab da Asibitin tace ma mai Keke Napep d’in ya d’an tsaya wanccan Pharmacy d’in zata amshi abu yace to ta ciro gyalen jallabiyar ta ta nad’a shi kaman nikab ta yadda ba za’a gane face d’in ta ba bayan ta gama ta bud’e purse ta fiddo yar takardar data rubuta sunan allurar da zata siyan dama tun kafin ta fito ta rubuta ko Fauzy bata sani ba, nufar cikin pharmacy d’in tay mai Keke Napep d’in nata kallonta cikin d’aurewar kai ganin tayi basaja wanda da ba haka take ba, bayan ta shiga ta mik’a ma d’aya daga cikin yan shagon takardar tace ita take so in akwae ya amsa yana dubawa can ya d’ago ya kalleta yace akwae amman basu yi ma Mutane da sauri tace Owk dama ba yi mata za’ai ba ya juya bayan ya d’aukko yace taje ta biya ta nufi cashier d’in ta biya aka bata receipt ta dawo ta amshi allurar ta juya yana ta kallonta har ta fice k’arshe ya d’an girgiza kai kawae, bayan ta koma cikin Napep d’in yaja suka nufi cikin asibitin, a daidai gate d’in School d’in su ya tsaya bayan ta fito ta bud’e purse d’inta ta fiddo 1500 ta mik’a mashi ya amsa ya duba da mamaki ya kalleta ganin kud’in sunyi yawa tun kafin yace wani abu tace yasha lemun da bata d’aukko mashi ba da sauran ta juya ta nufi ciki yana ta washe baki yana mata godiya, tana shigewa tasa hannu ta kwance gyalen ta nufi Hostel. Sosae yay gudu nan da nan ya iso kopar gidan su bayan ya parker ya bud’e ya fito lokacin Amadu na cikin shago yana hango shi da sauri ya bud’e ya fito ya nufo shi suka had’e ya gaishe dashi bayan ya amsa mashi yace “Zaraah na ciki?” d’an shiru Amadu yay alamar tunani can yace “gaskiya kaman bata nan don tunda na dawo daga school ban ganta ba kuma da ina cikin shago ban ga ta zo ba, shiru Haisam d’in yayi Amadu ya lura yanayin shi ya canza hakan yasa yace mashi bari dae yaje ya tambaya ko ta dawo da bai nan ta fita kai kawae Haisam ya d’aga mashi ya juya da sauri ya nufi cikin gidan, d’akin gwaggo ya nufa lokacin tana kwance kan gado tana bacci tayi wankan juma’a wurin kanta ya tsaya ya fara kiran sunanta a hankali ta ware idonta akan shi tana ganin shi ta yunk’ura ta tashi zaune tace mashi lafiya tambayarta yay Fatuu ta dawo ne tace “a’a lafiya?” Yace “dama Ya Haisam ne yazo yana tambayarta yana waje” tace “ba ta kaiga dawowa ba har yanzu kace mashi tana Makaranta k’ilan zuwa zai ya d’aukko ta” d’an shiru Amadu yay sai kuma yace mata k’ilan to daga haka ya juya yana fad’in bari ya fad’i mashi, bayan ya fito ya sanar dashi har yanzu bata dawo ba kai kawae ya d’aga mashi ya juya ya koma Motar bayan ya juyata ya koma ta hanyar da ya biyo da gudu.
Lokacin da ta shiga d’akin nasu Fauzy na kwance tana bacci ta yi wanka tasa kaya a bakin gadon da take Fatuu ta zauna ji tay kamar karta tasheta ta bari sai ta tashi amman kuma bata iya hakuri don ta k’osa ai komae a gama hannu ta kai ta fara dan bubbuga jikinta a hankali ta fara motsawa kafin ta bud’e idonta tana ganin Fatuu da sauri ta yunk’ura tana murza ido ta jingina da bango cikin muryar wanda ya tashi daga bacci tace “kin dawo Zarah” kai Fatuu ta d’aga mata d’an shiru Fauzy tay tana ta kallonta can tace “kin gan shi?” nan ma kan ta sake daga mata ta k’ara cewa “to ya ku kai dashi?” d’an ta6e baki tay yanayin fuskar ta ya canza cikin bacin rai tace “bai ce komai ba sai faman bi na da ido kawae, ni dama nasan fa ba abunda zai iya cewa shi kanshi daga yanayin fuskar shi na fahimce ya rud’e da jin zancen cikin ba kamar dana nuna mashi pt strip d’in” shiru Fauzy tay saidae a ranta ta matuk’ar yin mamakin jin wai bai ce komae ba can tace “to da ya ji Maganar zaki zubar da shi miya ce??” tace “dana fad’a mashi shima tsaye yay man yana bina da ido har na baro mashi d’akin saida ina kan hanya ne naga ya kira ni ni kuma ban d’aga ba” Fauzy tace “to Saboda mi Zarah ba sai Kiji mi zai ce ba” yamutsa fuska ta fara yi idanunta suka ciko da k’walla cikin rawar murya tace “Fauzy da akwae abunda zai fad’a man tun ina can da ya fad’i man kawai nasan bai wuce yace kar in zubar ba zai handling komae kuma wllh wannan ba yar k’aramar matsala zai jawo ba ni gwaggota nafi ji Fauzy tun ina k’arama take bani labarin wata d’iyar yar wajen aikin su da tay cikin shege a koda yaushe tana man misali da ita in tana gargad’i na koda na fara period saida tay ta gargade ni akan kada na bari wani ko hannuna ya kama in ba haka ba zan samu ciki Fauzy ki taimake ni ko don ita da karatu na da kuma kallon da za’a koma yi man ba kamar dangin mu har ma dashi Ya Haisam d’in gara mu kawo k’arshen komai ba tare da kowa ya sani ba” ta k’arasa hawaye na zuba daga idanunta had’i da kai hannu ta kamo hannun Fauzy shiru tay tana bin ta da ido wani irin fad’uwa gabanta ke yi hakanan ita dae bata son a zubar da cikin ga fargabar mi zai iya zuwa ya dawo magiya Fatuu taci gaba da yi mata can ta ja dogon numfashi cikin karyayyar murya tace “Zarah tsoro nike wllh kada wani abu ya faru sakamakon yin allurar nan kinsan tana da illa fa” da sauri Fatuu tace “in sha Allahu ba abunda zai faru raina na bani hakan kuma nayi maki Alk’awarin koda wani abun ma ya faru bazan mentioning d’in ki ba zan d’aura ma kaina alhakin duk abunda zai faru pls k’awata wadda bata son damuwata ki taimaka man” hannu Fauzy ta kai baki ta d’an cije yatsun ta tana nazari Fatun na cigaba da kallon ta a marairaice can ta cire hannun cikin disashewar murya tace mata ta had’a allurar nan da nan Fatuu tay d’an murmushin farin ciki ta fara kokarin had’a allurar………
Sosae yake gudu yana driving d’in yana kai hannu bakin shi ya d’an ciza had’i da d’an bugun steering d’in cikin lokaci kankani ya iso bakin gate d’in Makarantar su ya Parker sai lokacin ya fara tunanin yadda za’ai ya samu ganinta in ma tana a cikin school d’in hannu ya kai gefe ya d’auki phone d’in shi ya fara kiranta sai dae har ta katse bata d’aga ba haka saida ya kira sau biyar amman bata d’aga ba cikin tashin hankali ya kai hannu ya d’aki steering d’in da k’arfi ya furta “ZARAH….!!!” shiru yay yana numfashi da sauri da sauri kan shi ya gama k’ullewa bai san taya zai gan ta ba gashi bai san number d’in Fauzy ba balle ya kirata zuciyarshi ce ta raya mashi the more yake 6ata lokaci the more rayuwar ta ke shiga hadari he has to do something quickly hannu ya kai da sauri ya tashi Motar bayan ya juya ta ya jata da gudu ya tafi, yana ta sak’e sak’en abunda yakamata yayi a ranshi k’arshe zuciyar shi ta yanke mashi kawae yaje ya sanar ma Hajiya, bai d’au tsawon lokaci ba duk da da yar tazara ya iso Unguwar taso tun da ya karya kwanar gate ya fara latsa horn wani na bin wani Officer na jin hakan ya tashi da sauri ya zuge mashi Gate d’in ya shige fuuu bai nufi parking space ba ya wuce da Motar har kusa da part d’in Hajiya sannan ya parker ta ya fito ko rufe kopar bai yi ba ya wuce ciki, lokacin da ya shiga Parlon kwalam ba kowa da sauri ya nufi Bedroom d’in Hajiya yana shiga nan ma ya ga ba kowa har toilet ya nufa yay knocking tsit bai ji anyi alamun da mutum ba hakan yasa ya juyo da sauri ya fito Parlor ya nufi hanyar fita har ya kusa kaiwa k’opar fitan yaji motsi a bayan shi ya juya da sauri Amarya Saude ce don an d’aura mata aure da Officer tarewa ce kawai ta rage, daga kopar baya ta shigo hannunta ruk’e da yar roba mai fad’i Haisam na ganinta ya tunkare ta yana tambayarta Hajiya ko amsa gaisuwar da take mashi bai yi ba da hannu tay mashi nuni da inda ta fito tace mashi tana baya wurin su d’awisu ya amsa da Ok ya nufi kopar ita kaita saida tay mamakin ganin yanayin shi, yana fita bayan ya hango ta can a zaune akan kujera a gefen wurin Aku da alama fira suke hannunta d’aya ruk’e da sandar ta ta alfarma da take amfani da ita yanzu wurin yin tafiya, tun kan ya isa Aku yace ma Hajiya wai ga d’an ta nan jin haka yasa ta juya ta kalli Haisam dake tunkaro ta kafin ta juyo tana dariya tace ma Akun bata fad’a mashi jikan ta bane ba d’anta ba Akun ya dae yi shiru tamkar bai fahimci mi take nufi ba lokacin Haisam ya iso ya tsaya gefenta ta d’aga kai ta kalle shi sai yama kasa ko gaida ita sai d’an motsa baki yake lokaci guda ta gane akwai abunda ke damun shi tace mashi miya faru d’an shiru yay har saida ta maimaita sannan yace yana son yin Magana da ita ne tace to ta taso ne ko anan zasu yi yace suje Parlor tace Ok ta fara kokarin mik’ewa Aku na fad’in sai kin dawo Hajiyata tace to ya jirata suka nufi parlon tana gaba Haisam na bin ta a baya, bayan sun iso wurin kujeru akan 3 seater ta zauna shima ya zauna daga can gefenta idanunta akan shi yay shiru yana kallon carpet ganin haka yasa tace mashi shi take sauraro ya akai, shirun dae yaci gaba da yi ya rasa ta ina ma zai fara tunda yake bai ta6a jin fargabar gaya ma wani magana ba irin yau saida Hajiya ta k’ara tambayar shi da d’an k’arfi tace “miye wai ka fad’a in wani abu ya faru kayi man shiru zaka tada man hankali!” Sauke ajiyar zuciya yay ya d’an kalleta idanun shi har sun canza sai kuma ya maida su yana kallon gefe cikin raunanniyar murya ya fara cewa “…I want to tell u dat Zarah is pregnant and a…..am responsible for it” daga haka ya dakata wani kallo Hajiya ke bin shi dashi baki bud’e cikin rashin fahimta tace “Fanan nada ciki shine abun damuwa kai da zaka yi farinciki kiran ka tay ta sanar maka?” Tayi tambayar tana murmushi ya fahimci bata fahimci sunan da ya fad’i ba gashi ta kafe shi da ido alamar tana jiran amsa juyawa yay yayi facing d’in ta sosae cike da k’arfin hali yace “I said Zarah Not Fanan” lokaci guda yanayin fuskarta ya canza ta tsuketa cikin d’aurewar kai tace “Wace zarar?” Jimm yay sosae yake jin fargaba can dae ya dake yace “Zarah our neighbor I impregnated her yanzu haka tana d’auke da ciki na a jikinta” da alama mutuwar zaune Hajiya tay baki bud’e take kallon shi shima kallon nata yake sun dan d’auki lokaci a haka kafin ta kai hannu ta gyara zaman gilashin ta wai taga in shi ne da kyau a rud’e tace “Haisam kana da hankali kuwa kasan mi kake fad’a kuwa dama ashe ciwon da kake ba wani abu bane shaye shaye ka koya wurin turawan shine yanzu ka shawo abunda ya fi k’arfin ka kazo kana man zancen hauka to Allah ubangiji ya tsare mu da irin wannan abun kunyan ka bari muji dana shaye shayen da ka fara, yanzu kai Haisam duk yadda muke d’aukar ka mai hankali kowa na yaba halin ka nagari shine har ka bari turawa sukai galaba a kan ka wannan wane irin abun kunya ne ni Hauwa!” tana k’arasawa ta kai hannu ta ruk’e ha6a tay mashi zugudum tana mashi kallon bak’on mutum ba Haisam ba still yana ta kallon ta yasan dama bazata fahimta ba cikin sauk’i d’an matsawa yay kusa da ita yace “ni fa ba wani abu da nake sha ko kuma na sha yafi k’arfi na what am telling u is true Zarah da kika sani tana da ciki 1 month and nawa ne yanzu taje G.r.a ta sanar mani don nima ban san tana dashi ba….” Nan ya kwashe yadda sukai da Fatuu data same shi yanzu harda K’in d’aukar wayar shi da tayi da neman ta daya zo da kuma makarantar su da ya je duk ya fad’a mata, tana ta kallon shi har ya gama mata bayani tay shiru kawae, zuciyarta ta fara gasgata mata zancen shi Saboda yanayin da ta ga Fatun a d’azun tabbas yanayin ta ya nuna kaman na mai d’auke da yaron ciki iya girgiza Hajiya ta girgiza cikin tsananin tashin hankali murya na rawa tace “K.. kenan kana nufin raping d’in yar mutane kai???” d’an cije lips d’in shi yay ya d’aga mata kai alamar eh ta zabga uban salati tana tafa hannuwa ta shiga fad’in “…..Wannan wace irin musiba ce Haisam ya jawo mana, duk yadda nike Addu’ar Allah ya raba mu da mugun ji da mugun gani ashe kai ne zaka jawo hakan Haisam, miya faru da kai ne ka aikata ma Yarinyar Mutane wannan d’anyen aikin yarinyar da take tamkar k’anwa a gare ka, mika sha ne ka aikata mata hakan, ka fad’a man ko don ance matar ka nada matsala shi ne kai tunanin samun d’a ta wannan hanyar kasan mi ka aikata kuwa???” Sigh yay ya kai hannu ya dafa goshin shi kafin ya cire yace “I ave told you ba wani abu dana sha fa abunda ya faru wasn’t intentionally kema kin san bazan aikata hakan da wani niyya ba ko don wai Fanan na da matsala nasan nayi kuskure na biye ma son zuciya wannan dalilin ne ma yasa na kasa natsuwa har na dawo nan ban wuce Us ba” kallon dae kawai take bin shi dashi tsananin tashin hankali yasa ko kuka ta kasa yi ganin shi take a matsayin wanda ba daidai yake ba don kuwa da alama ya manta girman laifin da ya akaita da wadda ya aikata mawa, cigaba yay “Yanzu dae isn’t the right time da zamu cigaba da Maganan ya kamata ai stopping nata daga aikata abunda tace zata yi u know abortion nada matsala and nayi k’ok’arin in tsaidata but she refused to pick my calls kuma kinsan tunda karatun ta ne zata iya aikatawa pls do something in ya kama ko gidansu ne muje sai a fad’a ma Grandma d’inta” wannan karon kallon mahaukaci Hajiya ta koma yi mashi mahaukacin ma mai hauka tuburan don Maganar k’arshe da yayi a wurinta ta mara hankali ko miskala zarratin ce kaman yasan mi take ayyanawa yasa shi fad’in “nasan abun nada tashin hankali but bai kai na in aka samu Matsala ba don she may lose her life fa in hakan ya faru kuma ya tashin hankalin zai kasance so is better a sanar mata ta dakatar da ita and I will take responsible of everything” bakin Hajiya dai ya gama mutuwa sai ido kawae can ta yunk’ura ta mik’e shima ya mik’e ta nufi kopar fita daga parlon ganin zata fita haka yasa shi cewa veil d’in ta fa banza tay mashi tana dogara sandar ta har ta fice daga parlon shima haka………..
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.