Hausa novels

Matar Damisa Book 1 Chapter 27 Complete Novel

 

🐅MATAR DAMISA🐅
(The Wife Of Tiger)

 

Written and Story by
Asma’u Muhammad Auwal*

( *ASMEETAH NOVEL* ✍️)

*WhatsApp me 09065443871*

*NASARA WRITERS ASSOCIATION*
___________________________________
{{ *_Nasara abin so ga kowa, domin marubuta da cigaban rubutu, alƙalaminmu ƴancinmu._* }}
___________________________________

https://www.facebook.com/103637491942644/

💫💫 *{{N W A}}* 💫💫

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم

*BOOK ONE*
🅿️ ——-> 75 & 76 <——-

____________________________
mommy tana zaune a bakin gadon da Ayush take kwance tana kallon ceiling, da alamun tana tunanin wani abu ne ga hawaye kwance a saman fuskar ta..
Doctor Hasheem ne ya shugo da sallama a bakinsa,
cikin yanayin damuwa Mommy ta ɗago tare da amsa masa sallama,
ya nemi ɗaya daga cikin kujerun wajen ya zauna yana faɗin “Ayush bacci take yi ne”
Mommy ta juya ta kalleta taga ta ɗora hannunta saman fuskarta, tace “eh tayi bacci, jiya bata samu yin bacci ba..” ita kuwa tana jinsu kawai ta sharesu, Doctor yace “Allah sarki ya jikin nasun! jiya ban fito aiki ba, sai yau nake jin labarin abunda ya faru da su…”
Mommy tana sharar hawaye tace “jikinsu da sauƙi, ba kamar jiya ba sai dai Junaid abun ƙaruwa masa yayi”
Doctor shima baiji daɗin ganin Junaid a wannan halin ba yace “hakane Momy, nima yanzu na dubo shi abun ba daɗin gani, amma gaskiya wannan ciwon Junaid bana asibity bane, ya kamata mu nemi wani babban malami wanda zai tsaya masa, insha Allahu za’a dace tinda shafin aljanu ne…”
Mommy tana kallon Doctor itama ta gamsu da bayanansa malami ya kamata a nemo, tace “hakane Doctor kaima kace wani abu, zamu koma gida yau, akwai wani babban malamin mahaifin Junaid shi zan nemo yazo ya duba mun shi..”

Ayush tana kwance jin abunda suke tattaunawa akai yasa ta zaro ido waje,
kamar wanda aka zabureta ta tashi zane tana faɗin “Mommy! Yayana Junaid bai mutu ba daman? dan Allah inason ganin Yaya Junaid, ku taimaka mun dan Allah..”
ta fashe da kuka tana magiya akan akai ta gun Junaid,
Mommy ce ta riƙe hannunta tana faɗin “Ayushert kiyi hakuri ganin Junaid a halin yanzu zai iya jefa ki cikin damuwa”
Ayush ce ta katse Mommy da cewa “Dan Allah ku taimaka mun, hankali na bazai kwanta ba indai banga Yaya Junaid ba….”

Doctor Hasheem yana zaune ƙololuwar baƙin ciki ne ya ziyarci zuciyarsa yana faɗin ” Allahumma ajurni bi musifatu ƙalu innalillahi wa inna’ilaihi raju’un, Allah ubangiji yasa ba wata ƙulalliyar alaƙa ce a tsakanin Ayush da Junaid domin inhar hakan ta faru shikenam walwala zata ƙaurace mun, nashiga uku Ayush kar kimun haka please..” duk waɗannan maganganun a ransa ya yi su yana fuskantar Ayush wacce ta rikice wai ita sai an kaita gurin Yaya Junaid..

Ganin hawaye sharɓe-sharɓe akan fuskar Ayush yasa shi cewa “kinga Ayush tashi na kaiki gurin Junaid kinji, banson ganin kukan ki, kar kiyi mun asarar hawayenki” Mommy juyowa tayi tana kallonsa domin tasan mai yake nufi,
Ayush da sauri ta sauƙa daga saman gadon, ita ta farayin gaba sai Doctor ya biyo bayanta yana faɗin “tafiya a hankali mana, kar ki sanya ni cikin matsala”
suna tafiya a tare har suka isa ƙofar room ɗin, hannu Doctor yasa ya ture, cikin rashin sa’a suka same shi yanata sharar baccinsa, da gudu Ayush ta nufi gurinsa tana kiran sunan sa “Yaya Junaid! Yaya Junaid!! na gode Allah da yasa baka mutu ba, domin na tabbata dana rasaka a rayuwata gwara ni na mutu…..”

gaban Doctor Hasheem ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske, kafin kace me har gumi ya wanke masa fuska…
ita kuwa Ayush tana zaune a bakin gado ta rirriƙe hannunsa ɗayan hannun kuma tana shafa sajen fuskarsa mai shegen kyau da sheƙi,
Doctor Hasheem gani yayi bazai iya juran ganin wannan takwaicin ba, shawara ɗaya ya yanke cewa gwara shima ya sanar mata yana mutuwan sonta, domin yasan indai bai tara da wuri ba tabbas yana gaf da rasa Ayush duk da yasan Junaid ba Aure zaiyi ba…

gaban Ayush yaje ya tsaya sannan ya furta sunanta a hankali “Ayushhh..”
ɗagowa tayi da rinanan eyes ɗinta tana kallonsa bata ce komai ba tana sauraron mai zaice mata ne,
ganin ya ƙura mata ido kuma bashida abun cewa yasa ta kawar da fuskar ta gefe tana kallon kyakykyawan fuskar Junaid still hannunta na kan saman fuskarsa,
Hannu Doctor yasa ya riƙo hannun Ayush wanda yake kan fuskar Junaid sannan ya zamar da ɗayan hannun da take riƙe da hannunsa, ya miƙar da ita tsaye, yana mata wani irin kallo, ido cikin ido suke kallon juna ita dai Ayush abun mamaki ya bata a cikin ranta tace “wannan bawan Allah kuwa lafiyansa ƙalau? a gaban Yaya Junaid zai mun haka duk da yana bacci..”
haɗiyar yawu Ayush tayi sannan tace “Doctor ina jinka, kana riƙe da hannaye na sannan ka tasar dani daga zaune, shin wani irin kallo kake mun ne haka…”

Doctor Hasheem yana kallon cikin idanuwan ta yace “becouse i love you, I love you Ayushert, ke rayuwata ce sannan kuma mafarki na, ki cika mun burina na Auren ki dan Allah my Ayushert…”
Ajiyar zuciya Ayush tayi sannan tace “bai kamata ace munyi maganar soyayya a nan ba, saboda majinyaci ne a gaban mu..

“No Ayushert idan kika amince da soyayyata ni kin gama mun komai, inaso Junaid ya zame mun shaida duk da nasan baya cikin hayyacinsa, please my Ayush…”

yana murza mata lallausar hannayenta yana ƙara matsowa daff da ita,
a tunaninsa zata dakatar da shi sai kuma yaga akasin haka, farin ciki ne ya fara wanzuwa a zuciyarsa, hakan ya bashi daman rugumarta jikinsa yana faɗin “sorry my Ayush, keɗin farin ciki nane”
Itama kwantar da kanta tayi akan kafaɗarsa tana zubda hawaye ta kasa cewa komai,
ita dai hankalin ta yana kan Junaid, Doctor ne ya ɗago ta suna fuskantar juna, bakinsa yake shirin kaiwa nata saitin bakin, ganin lokaci guda Junaid ya buɗe idonsa, da sauri Ayush ta kawar da fuskarta ta nufi gurinsa tana faɗin Yaya Junaid ka tashi ne Alhamdulillah, ta zauna daf dashi tana shafar suman kansa…

shi kuwa Junaid yayi shuru baya iya cewa komai, sai binta da ido yake yi, ita kuwa hawayen farin ciki take zubar wa tana wasa da sajen fuskarsa da hannunta,

Doctor Hasheem kuwa zuba mata ido yayi, shi dai takaicinsa Ayush tafi nuna damuwa akan Junaid sosai ma..

ganin ransa yana shirin ɓaci yasa yayi saurin fice wa daga cikin room ɗin…

( ta wani ɓangare Ayush ta magance matsala Junaid a rashin sani, domin tinda Ayush ta taɓa shi, shikenam jaririn Aljani ya bar jikin Junaid sai dai an toshe masa bakin magana, bazai iya aikata komai ba…))

suna cikin wannan halin Ayush taga bai kulata ba, ta ɗago da kanta tana kallonsa tace “Yaya Junaid kayi shuru kayi mun magana mana ko zanji sanyi a raina, insha Allahu zaka samu sauƙi..”
tana kaiwa ƙarshen maganar ta saiga Mommy ta shugo da sauri tana faɗin “Ayush na karɓi takardar sallama, Junaid maganin gida yake buƙata bana hospital ba..”
cikin rashin fahimta Ayush take kallon Mommy tace “meya samu Yaya Junaid ɗin har sai an nemi maganin gida..?”

Mommy ce tayo kan Junaid tana faɗin “kukan luɗa yake yi amma yanzu kuma naga baya cewa komai,”
ta dudduba shi naga jijiyoyin kwakwalwarsa basa motsi, kallonsa tayi cike da mamaki tace “Junaid meyake damunka ne haka?”
shi kuwa still idanuwansa suna kan Ayush ko ƙibta idon baya yi,
wasu likitoci ne suka shugo da keken guragu na asibity yanda zasu ɗora Junaid akai,

Ayush ganin yanda aka ɗauki Junaid aka ɗora shi akan keken yasa ta faɗin “wai meyake faruwa ne da Yayana Junaid, Mommy inadai ba gurguncewa yayi ba, dan Allah Mommy ki sanar mun mana..!

Mommy ce ta zauna ta sanar da Ayush abunda ya faru har zuwa wannan lokacin…
Ayush ba abunda take sai kuka, idon nan ya yi jawur tsabar kuka har kayinta ya soma ciwo….

Da haka aka fitar da Junaid har harabar asibitin suna tura shi, sannan suka saka shi a cikin mota, Ayush ce ta zagayo ta ɗayan ɓangaren ta shugo,
Junaid ta kwantar a saman cinyarta, Mommy kuma ta zauna a gaban motar,
Doctor Hasheem ne ya shugo cikin motar yana draving ɗinsu yana kallon Ayush ta cikin madubin motar….

isar su gidan sukayi horn da ƙarfi,
Mommy tana faɗin “bansani ba ko Baba mai gadi ya dawo..” kafin ta rufe baki sukaji an buɗe gate, direct miƙar hanyar da zai sada su da harabar gidan suka nufa,
bayan Baba mai gadi ya rufe gate yana gudu ya biyo motarsu Doctor, cikin ƙanƙanin lokaci ya iso gare su yana faɗin “Hajiya ashe Junaidu ne ba lafiya..?”
tsayawa Mommy tayi tana kallonsa tace “Baba ina kaje? ka barmun gate a buɗe, sannan meya samu yarana?..”

Baba mai gadi murya na rawa yake cewa “wallahi Hajiya bansan meya faru dasu ba, nidai abunda na sani shine ina zaune akan dadduma na sai najiyo ƙaran ihu daga cikin gidan, wallahi tsoro ne yasa na gudu, nayi tunanin Damusan sa ne ya motsa shiyasa…”

Ajiyar zuciya Mommy tasau tana kallon Baba mai gadi tace “Baba kaifa namiji ne, bayan Junaid kai kaɗai ne namiji kuma baza kaso wani abun cutarwa ya cutar dasu ba, dan Allah Baba a kiyaye dokar aiki…”

Baba jiki na ɓari ya amsa da “toh shikenam hakan bazai sake faruwa ba”
tace “Allah yasa”
ta shige cikin falo tana kara waya a kunnenta, tareda faɗin “Assalamu Alaikum Malam ya gajiya, dan Allah ina nemanka ne a gidana akwai babban matsala..”
sun gama waya ta katse kiran,
Upstairs ta haura yanda Doctor Hasheem ya kai Junaid wato ɗakinsa tare da Ayush, itama zuwa tayi ta samesu har an kwantar da Junaid akan gadonsa, daga nan Doctor ya yi wa Momy sallama yayi tafiyarsa domin bazai iya juran ganin Ayush tana manne da Junaid, hakan ba ƙaramin ɓata masa rai yake ba….

After 1 hour
Sai ga Malam har yayi parking motarsa a harabar gidan, sannan ya nufi cikin falo kai tsaye,
jin tsayar da motor yasa Mommy sauƙowa downstairs tana ƙiran malam tare da cewa “Dan Allah Mallam kazo ka duba mun jikin Junaid abu yayi tsanani ko tashi baya iya yi balle magana..”
Mallam da sauri ya haura upstair yana faɗin “subhanallah meya faru haka?”
Mommy fashewa tayi da kuka itama tabi bayan Malam, ɗakin Junaid suka shiga gaba ɗayansu, da sallama a bakin malam ya shiga tareda jera wasu add’o’i, yana shiga kuwa idonsa ya sauƙa akan Ayush a razane malam ya tsaya cak yana faɗin “Ayshert…”
itama Ayush tashi tayi tsaye ta zaro ido waje tace “Baba Malam…” lokaci guda tasau murmushi a saman fuskarta,
Mommy ce ta katse su da cewa “ha’aa daman kunsan juna ne?”

Malam ne ya dubi Mommy sannan yace “ai wannan…..” Ayush tayi saurin katse shi da cewa “am am daman maƙwabcin mu ne, shi yayi magani a mahaifiyata har Allah yayi mata rasuwa, bamuda kowa shi ya temake mu, daga baya muka tashi a unguwar da yake..”
Ayush ta ƙarisa maganar tana girgiza wa malam kayi.

shima biye mata yayi da cewa “eh hakane..” yana kuma mamakin yanda ta iya zura ƙarya har haka, a cikin ransa yana faɗin “duk yanda akayi yarinyar nan tana ɓoye musu wani abu a cikin gidan nan, toh ma ya akayi tazo gidan nan bayan mahaifiyar ta Bara’at ta zauna har suka kore ta….” ya ƙarasa maganar zuci yana kallon Ayush wacce tin tinin gumi ya wanke mata fuska, tsoro ne ya bayyana akan fuskarta yau ta haɗu da wanda yasan labarinsu da mahaifiyarta kuma yanada alaƙa da gidan nan,
a cikin ranta kuwa cewa tayi “wayyo Allah na, asiri na ya kusan tonuwa idan har suka san cewa ni ɗiyar Bara’at ce shikenam kasheni Yaya Junaid zaiyi…” itama ta ƙarasa maganar tana zubda hawaye..

shima kansa malam ya fahimci Ayush tana cikin damuwa kuma zai temaka mata, yanada wannan niyar a ransa..
nufar gurin da Junaid yake kwance yayi, sannan ya zauna a bakin gado ya riƙe hannunsa sosai tareda rufe idonsa yana karanta wasu abubuwa,
cikin ƙanƙanin lokaci ya buɗe idonsa yana kallon fuskar Junaid, ga hawaye yanda yake gangaro masa daga cikin ƙayar idanunsa,
sannan ya juyo ya kalli Ayush ya karkaɗa kayi tareda yin murmushi, ya buɗe cikin jakar daya zo da ita ya ɗauko turare mai ruwa anyi rubutu ta larabci a jikin turaren,
yace “Hmmm! Aljanu aka turo masa, wanda zasu hanashi yin komai,”
Mommy tace “to malam daga farko kukan jariri yake yi yanzu kuma ya daina” malam yace “waɗannan ƙananun aljanu ne kuma suna matuƙar jin shakkar wata yarinya ce mai ƙarfin iko, wanda raɓarsa tayi ne yasa suka gudu, yanzu wani Aljani ne a jikinsa wanda bansan dalilin zamansa a jikinsa ba, amma yanzu zamuji abunda zai ce.
Wannan turaren ne malam ya watsa a saman fuskar Junaid,
nan take fuskarsa ta koma yellow ya kanne idonsa sosai!

Malam yana fuskantar Junaid yace “inason sanin meya kawo ka jikin bawan Allah nan..?”

Junaid ne ya buɗe baki kamar shine mai maganar, wata ƙatuwar murya ne yake magana kamar
“NI SUNANA ALJANI ƘUDDUS, AN TURO NI NE DOMIN NAZO NA KASHE JUNAID DAGA MASARAUTAR RAAMUD, TAUSAYINSA DA NAKE JI NE YASA BAN KASHE SHI BA, SHINE NA RAƁI JIKINSA, BAZAN TAƁA BARIN JIKIN JUNAID BA SAI AN CIRE ZOBEN DISH DAKE JIKIN CIBIYAR ƳAR SARKI RAAMUD…”

daga nan Aljanin yayi shuru,
kallon Ayush malam yayi sannan yayi murmushi,
yace wa Mommy “kindai ji abunda yace, amma insha Allahu zai samu lafiya….”

Mommy ce tayo kan Junaid tana kuka,
shi kuwa ganin haka yasa yayi wa Ayush magana yace “inaso zanyi magana dake Ayush, ki isoni a cikin motata ina harabar gidan…..

Domin sauke CikakkenLittafin Sai Ku Danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Matar Damisa Book 1 Complete Novel Document 

 

*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝*
*MTN* . *Airtel*
1GB = ₦300. 1GB = ₦300
2GB = ₦600. 2GB = ₦600
3GB = ₦900. 3GB = ₦900
4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200
5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = ₦350. 500Mb ₦500
2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100
3GB = ₦1050. 2GB ₦1600
4GB = ₦1400. 3GB ₦2000
5GB = ₦1750. 4GB ₦2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
*🪀08066268951*

*ASMEETAH NOVEL✍️✍️*

Back to top button