Page 65
Shiru ta yi masa, ta kasa magana, saboda yadda take jin wani iri a jikinta.
Ya janye hannunsa ya kalleta ya ce “Ba a bani abinci a plate”.
Ta kwaɓe fuska ta kalleshi, ta lura adam akwai saka aiki, ba gaira ba dalili.
Ta tashi ta ɗau plate ɗin, sai da ta zubo a flask, da cokali, da ruwa ta kawo masa, ya ce mata ta kunna masa tv.
Sai da ta ji kamar ta yi tsaki amma ta fasa, ta kunna ta dawo ta zauna, sai dai ta lura da yanayin sa, abincin ba wai daɗi yake yi masa ba, ci kawai yake yi.
“Papa maiyasa idonka yake hayaƙi, idan ka yi fushi?”
Yayi dariya ya ce “Sai ka ce generator, ko wani murhu, saboda gani jarababbe”
Ganin ya mayar da maganar shirme, ya sa ta yi shiri.
Kaɗan ya ci, ya rufe, a lokacin ta fara ƙoƙarin mayar da litatafan ta, ya ce “Ban gama da litattafan ba”.
Ya karɓa ya cigaba da duddubawa, a hankali ya din ga bi ɗaya bayan ɗaya, ya na sake yi mata bayanin darussan da aka koya mata, sai a lokacin ta ƙara ganewa ta kalleshi ta ce “Ai da za a din ga yi mini da hausa, da sai na fi ganewa”.
“No, da turanci suke magana, ni ma da turancin zan din ga yi miki magana”.
“Ashe za ayi zaman kurame, dan bai fi kalmomi, sha biyu na sani da turanci ba”
Bai bata amsa ba ya cigaba da cewa “Zan saka a ki islamiyya, ko ba na nan, sidi zai din ga kai ki yana ɗauko ki, sannan wannan zanen da ki ka yi, ki goge shi, ki rubuta wani abun”.
“Ba ka san ma’anar zanen nan ba, duk makin da na ci zan zo na nuna maka” ta ƙarasa maganar tana tattare litattafan ta, a cikin jakarta, daga nan ta mayar da hankali kan abun da yake kallo.
Film ne na Hollywood, sai dai yadda ake nuno matan, bai yi wa rumaisa ba, ta din ga kawar da kanta gefe, ba ta yi aune ba ta ga ana kiss, da sauri ta saka hannu ta rufe idanunta, ta sunkuyar da kai.
Sai dai ta ɗaga kanta, ta gefen ido, ta ga takawa ko a jikinsa, ya cigaba da kallo.
“Ka canza mana wannan tashar”
Ya ce “Saboda me?”.
“Ba ka ga abun da ake yi ba?”.
“A ina?”.
Cikin ƙulewa ta ce “Ka na gani ana abun da bai kamata ba, amma ka ke kallo, mama ta ce ba kyau, a gida ba a bari mu kalli irin wannan film ɗin ma fa, ka daina gani za ka makance”.
Ya kalli cikin ƙwayar idonta, iya gaskiyarta take gaya masa, bai ga alamar wasa a abun da take faɗa ba.
“Ko zamu gwada?” Yayi maganar yana tsareta da ido.
“Waro masa ido ta yi ta ce “Mu gwada me?”.
“Kiss ɗin”
Miƙewa tsaye ta yi, ta ce “Na shiga uku” har da haɗawa da gudu, ta bar masa falon.
Shi a zahiri ma ba film ɗin yake kallo ba, yanzun ma fitowa ya yi, domin ragewa kansa damuwa, da kaɗaici, atleast ya ɗan ji releif kaɗan, ya saka a ransa zai yi mai yiwu wa, wurin bin shawarar Bashir, ya saki jiki da rumaisa su samu kusanci sosai da sosai.
Har dare, ba ta sake yadda sun haɗu ba, dan ya gama ba ta kunya gaba ɗaya.
Har ɗaki Asiya, ta kawo mata uniform ɗin ta, an wanke wanda ta cire an goge mata su.
Ta karɓa ta yi wa Asiya godiya, ta cewa Asiya dan Allah ta dafa mata indomie, dan ba za ta fita ta haɗu da adam ba.
A ɗakin ta bar kwanun, ta yi sallar isha’i, ta hau aikin nata na bacci.
A cikin mafarke-mafarkenta, da ta saba yi, yau ta ga Mummy riƙe da sarƙar da take yawan ganin an ɗaɗɗaure adam da ita, yau ta ga mummy riƙe da sarƙar, ta hankaɗa adam cikin wani rami.
Ba ta san ya aka ƙare ba a mafarkin, ta tsinci kanta a tsaye, tana ta haki zuciyarta na bugawa da sauri.
Da sauri ta fita daga ɗakin, ta tafi na takawa, ta tarar da shi ya na bacci.
Kuka take yi sosai, tana dukan pillown sa, “Ka tashi”
Kasancewar baccin na sa ba nisa ya yi ba, ya farka, dan bai daɗe da yin baccin ba.
Da fari ya zata ko ciwon marar ne, ya tamabaye ta lafiya?.
“Ni tsoro nake ji”.
“Tsoron me kuma?”
“Ni dai tsoro nake ji” ta yi maganar tana kuka.
Ya tashi zaune ya ce “To zo ki kwanta a nan” ba musu ta haye gadon nasa, ta kwanta, ƙarshe dai har asuba bai samu ya yi bacci ba, ita ma kawai bakan ta yi, amma idonta biyu..
Sai dai tun lokacin da ya tashin, yake jin kamar an zare masa lakar jikinsa, ya fita masallaci, ta sauka daga kan gadon ta koma ɗakinta, tana ta addu’a a zuciyarta.
Sai dai kamar jiya da safe, walwalarsa ta sake ɗaukewa, bai ko karya ba, ya tafi kaita makaranta, sai dai a tuƙinsa kawai, ya isa ka fuskanci lallai akwai matsala. Ta yi masa a dawo lafiya ya jinjina mata kai ya tafi.
Sai dai ita ma ta shiga cikin tunani, tun da Allah ya sa ta ga Mummy, take yawan mafarkinsu tare da takawa.
Ikon Allah ne kawai ya kai shi wurin aiki, dan ko gani ba ya yi sosai.
Tun da ya shiga office, jiki yake nema ya rikice, ya rufe kansa a ciki, yake ta fama da matsanancin ciwon kai.
Bai iya aikata komai ba, ya kunna karatun Alkur’ani a wayarsa, ya ajiye dan idan ya shiga wannan yanayin ba ya iya karanta komai.
Ya daɗe a haka, kan a hankali ya fara samun nutsuwa, ya ɗau wayar, ya kira Jamil a waya, ya ce dan Allah ya zo office ɗin sa.
Ko mintuna biyar ba ayu ba sai ga Jamil, ya na ganin adam ya ruɗe ya ce “Lafiya kuwa? Ba ka da lafiya ne?”.
“Bana jin daɗi ne, dan Allah so nake ka kaini gida wurin ammi, ba na son kowa ya san halin da nake ciki, bana son ayi ta mun sannu, ko azo a zagayeni ban san me zai iya faruwa ba”.
Jamil ya jinjina kai, ya ɗaukar masa wayoyinsa, ya rungume shi suka fita.
Ko da suka je can gida, adam ya yi garajen buɗe ƙofa ya fita, ya faɗi a wurin. Dai-dai da shigowar motar hajiya jamila da Hajiya Lubabatu.
Saukkowa suka yi, suka nufi adam tare da ma’aikatan, suna tambayar ko lafiya.
Jamil ya ce “Bashi da lafiya, ya ce na dawo da shi gida, kuma ya faɗi”.
Haka aka kama adam, zuwa cikin gida sashin Ammi.
Ammi ba ƙaramin tsorata ta yi ba, rabon da haka ta faru an kwana biyu, dan an samu kyakkyawan cigaba a lamarin lafiyar Adam.
Kamar gawa haka aka kwantar da shi, a bedroom ɗin ammi, su Mummy suka je suka tsaya a kan sa suna yi masa sannu.
Tamkar wanda aka mintsuna, ya fara daddagewa jikinsa ya na rawa, yana danƙar bedsheet ɗin kan gadon, yana girgiza kai.
“Ammi, Ammi! Jikina ki danne ni” ya din ga maganar cikin ɗaga murya.
Tuni hawaye ya cika idon ammi, ta ce “Sannu Allah ya baka lafiya”.
Mummy ta yi ajiyar zuciya ta ce “Kai wannnan lamari, ni abun nan na rasa gane kansa, Wannan wace irin larura ce?”.
“Ammi! Ana kakkarya ni fa, Ki zuba mini ruwan sanyi a jikina” yayi maganar yana neman abun da zai riƙe.
Jamil ya ce “Takawa, ka yi addu’a Allah ya baka lafiya”.
Hajiya Lubabatu ta ce “Jamil yo baya fa, kar ya yi maka illa, ko ka manta abun da yake yi, idan ciwon ya tashi haka?”
Gaba ɗaya suka tsaya daga baya, sai ammi ce ta zauna a kusa da shi, tana cigaba da yi masa sannu, su iman duk suna makaranta, da ma daga ita sai sabir.
Kan ka ce kwabo, sai ga samha ta shigo tare da Fauziyya, suna sashin Mummy, Mahmud ya gaya musu.
Samha na zuwa ta ganshi jikinta ya yi sanyi, ta na jin labarin rashin lafiyar sa, tun suna yara, wasu lokutan abun ya kan tayar masa, amma ba ta taɓa tunanin abun ya kai haka ba.
Ya na cikin wannan halin, ya koma cewa “Rumaisa! Ammi a ɗaukkota daga makaranta, kar wani abu ya sameta. Rumaisa! Ammi Rumaisa”.
Jamil ya ce “Ka kwnatar da hankalinka, wace makarantar ce, in je in ɗaukkota”.
Mummy ta ce “Takawa ka na ta kanka, kana ta wata daban, ka yi addu’a, fatanmu ka samu lafiya”
“Ammi rumaisa” ya sake nanatawa.
Haushi ne ya ƙule Samha, kamar ta buɗi baki, ta ce Allah ya tsinewa rumaisan.
Ammi ta gaya wa Jamil makarantar, ya fita da sauri ya ɗau mota.
Mahmud kuwa ya kasa zaune ya kasa tsaye, atleast ya na son jin ya jikin Adam, a wani situation yake, abun da bai taɓa ji ba sai yau.
Rumaisa kuwa tuni aka tashi, har ta fara ƙuluwa, ta ce “Lallai papa, zaton sa ba zan iya tafiya ba kamar yadda na ce masa ko? To wallahi tafiyata zan yi, in bi hanyar da ba ta gida ba, in ɓata sai ya nemo ni”. Ta na cikin mitar, ta ga motar adam, sai dai ta ga jamil a ciki, dan haka ta tsaya ta na kallonsa.
Ya sauke glashin ya ce “Zo mu tafi”
“Mu je ina?”.
“Can gida, takawa ba lafiya, ya ce na ɗaukkoki, ya na cikin gari wurin ammi”.
“Sai ka ce ba ni da hankali zan hau motar da ka ke tuƙawa, in je ka kasheni a banza, tun da na san ka tsaneni, saboda papa bai auri ƙanwarka ba, to ba zan hau ba”.
Ya kwantar da muryarsa ya ce “Da gaske nake yi miki, ni ba kasheki zan yi ba, ba dan shi ya ce na ɗaukko ki ba, ba abun da zai kawo ni”.
“Taɓ, ka isa ka gaya mini magana in yadda, ai ni yadda mutum yayi mini a haɗuwarmu ta farko da shi nake amfani. Ba ɗazu papan ya kawoni ba ka ce shi ya ce ya zo ya ɗauke ni, bayan a gabana ranar ka ke yi masa rashin mutunci, ka ce wai bai gaya maka anty aisha an sace ta ba, to ba zan hau ka kasheni ba, ba kai ne yayan anty aisha ba, duk na san komai, da ku ka din ga cin zalinta, tun tana ƙarama, sai da ta mutu za ku nuna kuna son ta. To wallahi ba zan hau ba, gara na tafi da ƙafata”.
Baki buɗe yake kallon rumaisa, ita ba ta manta abu, waye ma ya gaya mata wannan zancen, ita aishan ce ko adam ɗin ne ya gaya mata? Kuma ai ba shi ne ya nuna wa aisha ƙiyayya ba.
Ya dai-daita nutsuwarsa ya ce “ƙanwata ki na ji, shigo mota mu tafi, sai mu yi magana, duk wanda ya gaya miki zantukan nan ƙarya yake yi, na san dai aisha ba zata gaya miki ba”.
“Kai ni fa ba a lallaɓani, kuma ba a hantarata ko ayi mini dole, ka tambayi mijina ka ji” ta juya tayi tafiyarta, kan ya kunna motar, ya bita, ta haye a dai-daita sahu, ta ce a kaita gidan tsohon galadima.
Ana zuwa ta sauka abun ta, sai masu gadi ne suka biya kuɗin napep ɗin, ta nufi sashin Ammi, a ranta ta na raya idan ƙarya Jamil yake, sai ya gane ba shi da wayo.
Sai dai ga mamakinta ta ga baba uwani a falon ammi, bayan a gida suka bar ta.
Ta na ganin rumaisa ta hau kuka, ta ce “Tun ɗazu aka ce a zo a ɗaukko ki daga makaranta, yanzu aka kirani a waya, takawa babu lafiya”.
Ruma ba ta amsa mata ba, ta fara laluben a ina adam ya ke.
Ta na kaiwa bedroom ɗin ammi, ta ji tsigar jikin ta ta tashi, kanta ya wani sara.
Kamar ƙwai ya fashe mata a ciki, ta shiga ɗakin.
Duk ga su Mummy a gefe, har da Samha da su Fauziyya su na kuka.
Rumaisa ta ƙarasa kansa ta tsaya, sai fizge-fizge yake yi, kamar zai fita hayyacin sa.
Rumaisa ta waiwaya, ta ƙurawa mummy ido, a take jikin Mummy ya hau rawa, ta fara kame-kame “Rumaisa ko?, kin ga takawa ba lafiya ko? Dama yanzu yake ta kiran sunanki ya ce a ɗaukko ki”.
Ammi ta ce “Rumaisa, ashe jamil ɗin ya ɗaukko ki?”.
Rumaisa ta girgiza kai ta ce “Ni ba shi na biyo ba, saboda ya tsaneni, haka kawai in je ya kashe ni, ai haushina yake ji saboda takawa bai auri ƙanwarsa ba, na zata ma ƙarya yake yi, lafiyar papan ƙalau, yaudarata zai yi na hau adaidaita sahu na taho”.
“Yaya jamil ɗin ne yake yi miki ƙarya?” Samha ta yi maganar a ƙufule.
“Waye shi da ba zai yi ƙarya ba? Na faɗa na zata ƙarya yake yi, tun da a gabana yake yi wa papa rashin mutunci, wai bai gaya masa anty aisha ta ɓata ba. Sai kuma ya zo ya ce mini papa bashi da lafiya na yarda? Ai ni a ganin farko nake gane mutum”.
Ammi ta ce “Ruma ya isa haka, ki yi masa addu’a”
“Ammi ni fa rashin adalci ne da fuska biyu ba na so”.
Kallonta duk suke yi, ba tare da gane in da zamcenta ya dosa ba.
“Ammi ki danne ni, ƙasusuwana karyewa suke yi” maganar takawa ta sa suka mayar da hankalinsu kan shi”.
Iman ce ta yi sallama a bedroom ɗin, jikinta a sanyaye ita ma.
Rumaisa ba tare da jin kunyar wani ba, ta zauna a gefensa, ta riƙo hannunsa da yake cikin na ammi, ta ce “Papa meye yake maka ciwo?”
Ya riƙe hannunta sosai, cikin tsananin ciwo ya ce, “komai ma, Allah idan mutuwa za ta zama hutu a gareni, Allah ka sanya na mutu, da wannan azabar da nake ji” yayi maganar yana sake riƙeta tare da yin ƙara.
Duk ta na jin azabar riƙon da ya yi mata, ta sunkuya dai-dai kunnensa ta ce “Papa ba kyau fatan mutuwa fa, idan ka mutu sabir fa, ammi fa? Dan Allah ka daina, ka bari in cikawa anty aisha alƙawarin da na yi mata, zaka warke gaba ɗaya har abada” ta yi maganar tana zubar da hawaye.
Samha wani uban tsaki ta doka, ta tashi ta fita, abun da babu wani take gaya mata game da zamansu daban, abun da take gani yanzu daban.
Mummy ma tashi ta yi ta ce “Giwa, Allah ya bashi lafiya, amma akawai buƙatar ki din ga kwaɓar sirikar ki, ta iya bakinta”.
Ammi ta ce “To na gode”.
Baba uwani ta kawo kai, suka haɗu da Mummy, Mummy ta yi mata sigina da ido, sannan ta tafi.
“Ki yi mini Addu’a” ya faɗa ya na sassauta riƙon da ya yi mata.
Baba uwani sai jera masa sannu take yi, iman ta kawo maganinsa, a shafa masa, ya ce ba ya so.
Iya abun da Allah ya sa rumaisa ta iya, ta din ga karanta masa, sai dai ta fi nanata la’iila ha illa anta subhanaka inni kuntu mina zalimin. Saboda tana da yaƙinin duk wahalar da ta shiga, idan ta karanta ta na samun mafita.
Lumshe idanunsa ya yi, ya daina hargowar da yake yi, ta kalli ammi ta ce “Wallahi ammi asiri aka yi masa, wai ku ba kwa ganin abun da nake gani?”.
Ammi ta ce “A’a rumaisa, Allah ne ya ɗora masa, muna fatan Allah ya yaye masa”.
“Ammi, wai baku ga matar da take zaune tare da su Mummy ba, tana kallonsa, wata baƙa, idonta ya na ci da wuta, haka fa wataran idonsa yake yi, idan ransa ya ɓaci, kuma wallahi ni ban yadda da babar mahmud ɗin nan ba…… Kamar daɗi take ji abun da ya samu baban sabir, sai murmushi fa take yi ku………
Hannun sa ya saka ya toshe mata baki, duk da idonsa ya na rufe.
Rumaisa baba uwani take kallo, idan har abun da Mahmud da kuma Asiya suka gaya mata a kan baba uwani gaske ne, to za ta yi amfani da shawarar yaya usman, dan ranar da suka je gida, ba abun da ba ta gaya masa ba, kuma shi ya bata shawarar ta faɗi wata maganar a gaban baba uwani, wadda ta san za ta iya zuwa kunnen Mummy.
A zahiri rumaisa ta ga matar da take faɗa, a tare da Mummy, sai dai a wannan karon ma, ta gane ita kaɗai take ganin ta.
Bacci ne ya ɗauke Adam, rumaisa ta tashi ta ce za ta yi salla.
Ammi sai sannu take yi mata, saboda ta san idan har ciwon adam ya tashi, duk wanda ya yi wa wannan riƙon sai ya ji jiki, amma ta ga rumaisa ras da ita.
Maimakon ta je ta yi sallar, sai ta fice harabar gidan.
Lelleƙawa take yi, ko za ta gano Mahmud, dan ta na da labarin gaya masa.
Bisa sa’a, ta ga yana tahowa daga waje, da alama masallaci ya je.
“Daddy” ta ƙwala masa kira.
Yana hangota ya yi murmushi, ya ce “Daughter, ina takwarana?”.
“Ya na wurin ammi, dama kai nake nema, Allah ya sa na ganka”.
“To gani ya aka yi? Amma ba kya tsoron kar mijinki ya ganki, ya kuma hantararki?”.
Ruma ta tura baki ta ce “Bashi da lafiya fa, kuma kowa ya zo duba shi, har da mamanka amma kai ba ka zo ba”
“To ai kin san ba shiri muke yi ba”
“Daddy meyasa?”.
Mahmud ya numfasa ya ce “Manta kawai, ya aka yi?”.
“Ka san maganar da muka yi ai ranar ko?, kuma ka ce zaka taimaka mini”.
Mahmud ya ce “Ko zan yi wa kowa ƙarya, ban da ƴa ta”.
Rumaisa ta ce “To ni fa na ce mamanka ce ta ke yi wa mijina asiri a gaban baba uwani”.
Ya ɗan yi shiru ya ce “Ke waye ya gaya miki haka?”
“Haka nake tunani, kuma nake son tabattarwa, amma so nake na kama baba Uwani, yaya usman ne ya bani shawara. Ni fa ban yadda matar nan mamanka ba ce, jiya mafarki na yi tana tura papa rami, yau kuma na ganta da wata mata, ba wanda yake iya ganinta sai ni, baƙa mummuna, idonta sai wuta yake yi, abar tsoro kawai dai ni ba ta tsorata ni ba. Papa sai ihu yake yi, abun tausayi”
Yayi zuru da ido yana kallon rumaisa, sai kuma ya ce “Da gaske ki ke ko da wasa?”.
“Ni ba kullum nake yin ƙarya ba” ta bashi amsa.
“So, you want expose my mother daughter?”.
Ta yi shiru, tare da zuba masa ido.
Ya ce “Shikenan, ni na yi alƙawari ai kuma zan cika in sha Allah, duk wani support da ki ke nema, i will assist in sha Allah, zan taimaka miki, ki cika alƙawarin da ki ka yi wa fulani, amma yaushe zaki bashi bayani a kan abun da yake nema na binciken? Ya na son aisha sosai, a yanzu ba shi da burin da ya wuce, ya gano wanda suka saceta”.
Rumaisa ta ce “Kamar ka na son takawa? Tun da har ka san abubuwa a kan sa, amma meyasa ba kwa shiri?”
Jiki a sanyaye ya ce “Kar ki damu, lambar wayata na nan, na rubuta miki, a bayan sashin su mijinki, duk lokacin da ki ke buƙata ki kirani, idan har ina Nigeria” yana gama faɗa ya juya zai tafi ta ce “Idan kuma na gane ka zaɓi uwar riƙon ka, ka yaudareni, zan yi maka abun da ba ka zata ba, zan iya yin komai a kan uban ɗa na”
Cak ya tsaya, ya waiwaya ya kalleta, kawai ta kwashe da dariya, ta ce “Kamar a film ko? Zan iya acting ashe, ai na san ba zaka yi mini haka ba”
Tun da ya dawo ƙasar nan, suka haɗu da rumaisa, suka yi magana, yake jin kamar wani abu ya sauya a tare da shi, sosai yake jin tausayin Adam, kuma a jikinsa yake jin, lokaci ya yi, da yakamata Mummy ta tuba, shekaru sun fara ja, ko ba komai ta mutu ta samu rahamar Allah, sarautar da take yi masa ƙuzu kuma, shi ba a gabansa take ba ma.
A ɗakin Iman rumaisa ta yi salla, iman ta baya doguwar rigarta ta saka, suka zauna su na ɗan taɓa hira, iman ta ɗan bata labarin, irin wahalar da yake sha, idan yana ciwon nan, da kuma wahalar neman magani da ammi take yi, ba yau ba gobe”.
Iman ta ɗora da cewa “Anty rumaisa, da kin sani ba ki faɗi maganar nan ta ɗazu a gaban mutane ba, ba zan musa miki mummy ba ta asiri ba, amma idan maganar ta koma kunnenta fa? Zai iya haddasa wata rigimar”.
“Ai na ga duk wanda yake wurin, amintacce ne. Waye zai je ya faɗa? Ammi ce za ta gaya mata, ko kuma ke? Ko kuma baba uwani, da dama dan ita na faɗa”
Iman ta kalli rumaisa da mamaki, rumaisa ta yi dariya, ta ce “Iman, ina da wayo fa, kawai dai ba na ji ne, amma dan Allah Meyasa papa suke gaba da daddyna? Ko da ba ammi ce ta haifesu duka ba, amma ai ƴan uwa ne”
Iman ta ce “Duk ƴaƴan ammi ne”
Rumaisa ta ce “Ai na zata kema zaki raina mini hankali ne, ai na sani, na san duk ammi ce ta haifesu, amma daddy ya dage wai waccan matar ce babarsa, amma dan Allah meyasa gaba ɗaya gidan nan naku, a hargitse yake? Kowa ba shi da gaskiya”.
Iman ta rausayar da kai ta ce “Ai ba abun da ki ka gani, family ne mai cike da rikici da ƙulla-ƙulla”.
“Ai shi ne wannan yayan anty aishan, zai raina mini hankali, ni kuma wallahi yadda mutum ya mu’amalance ni a farko, haka nake tafiya da shi, kin ga rashin mutuncin da suka yi mini ranar da muka je gidan su, da shi, da wannan masifaffiyar mai jan kaya ta ɗazu, da wannan jabir ɗin, shi ma jabir ɗin da babarsa, wadda ta riga Mummy tafiya ɗazu.
Wai takawa ya turo shi ya ɗauke ni daga makaranta, na ce ba zan hau motarsa ya kashe ni ba, dan na san haushina yake ji, saboda takawa bai auri ƙanwarsa ba, wai ni zai yi wa dabara, a gabana fa ya yi wa papan wulaƙanci, wai an sace ƙanwarsa bai gaya masa ba, shi a wa? Sai ka ce son anty aishar suke yi”.
Iman ta ce “Ke dai kawai ki ce, an taɓa miki miji kin ji haushi. In dai yaya jamil ne sun saba, faɗa da takawa kuma daga baya su zo su shirya. Amma duk da haka na yi mamakin yadda ki ka iya kawo, yaya Mahmud sashen nan, ba ya son ammi da abun da ya shafe ta, balle adam. Lokaci na ƙarshe da ya zo, shi ne lokacin da aka fasa aurena, saboda rashin asali, ammi ta roƙe shi ya aureni, har da kukanta, ya ce ba ya so na, ba zai aureni ba”. Ta yi maganar hawaye fal idonta.
Rumaisa ta yi shiru, ta ce “Wane irin abu ne wannan kuma? To duk saboda me? Ban gane ba ki da asali ba”
Iman ta share hawayen da ya zubo mata, ta ce “Zan yi miki bayani, yanzu mu cigaba da addu’a papan mimi ya warke” ta yi maganar cikin ƙarfin hali tana murmushi.
“Shikenan, ara mini wayarki, na kira gida na gaya musu papa ba lafiya”.
Iman ta ce “Amma idan mai sunan baba zaki kira, ki yi masa magana ta what’s app, ya hana ni kiransa a waya”.
Ruma ta ce “Au kuna waya ne dama?” Ta yi maganar tana dariya.
Da sauri Iman ta ce “A’a, ba waya muke yi ba, ke ce da ki ka kira rannan bai ɗaga ba”.
Ruma ta yi dariya ta ce “Buɗe mini data mu yi magana da shi”.
Iman ta karɓa ta kunna mata data, ta ba ta, yaya umar ta ga iman ta yi saving number.
Ruma ba ta ce komai ba, ta yi masa voice message “Mai sunan baba, ni ce, ka gaya wa mama mijina ba shi da lafiya, mu na gidan ammi, idan ka ga message ɗin dan Allah ka yi mini magana, rumaisa ce”.
Iman ta zare ido ta ce “Ba kya jin kunya, ki ke cewa ace da ammi mijinki babu lafiya”
Rumaisa ta miƙe tsaye ta ce “To me zan ce? Ai maman ma mijina take ce masa, bari na je na gani ko ya tashi, idan mai sunan baba ya yi magana, sai ki kira ni” ta fita daga ɗakin, ta tafi na ammi.
Ammi ba ta ɗakin, ta tarar da adam a zaune, sai dai ta ga samha a zaune a gefen sa, da flask ɗin abinci.
Wani abu ne mai nauyi, ya daki zuciyar rumaisa, da ba za ta iya tantance ko menene ba.
Iman kuwa ta cigaba da chatting ɗin ta, sai ga video call na mai sunan baba.
Gudun kar ta yi laifi, kan ta kai wa ruma wayar ta katse, ya sanya ta ɗaga, gabanta ya na faɗuwa.
Maimakon ya ga rumaisa, ya ga kyakywar fuskar iman, ta bayyana a kan screen ɗin wayarsa.
Ta ɗan sunkuyar da kai ta ce “Barka da yamma yaya umar”
Sunkuyar da kanta da ta yi ne, ya bashi damar ƙare mata kallo, ya na jin releif na abun da yake damun ruhinsa.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.