Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 26 Complete Novel

*ASM Bk2026*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

………Tana zaune kan darduma ta gama salla tana lazimi a d’akin Saude wayarta dake aje a gefen katifa ta fara ringing, a hankali taja jiki ta matsa ta kai hannu ta d’auki wayar ta duba mai kiran nata, Jim tay ganin sunan Ya Haisam ya bayyana kafin tayi picking ta kai kunne, shiru sukae gaba d’aya kaman bazasu yi Magana ba can Haisam d’in ya kira sunanta “Zaraah” har saida gabanta ya d’an fad’i jin yanayin da ya kira sunan nata cikin shaky voice tace “N..na’am Ya Haisam ina wuni” bai amsa mata ba ta sake cewa “Ya Aunty Fanan” sai lokacin yace “she’s fine” shiru suka d’an k’ara yi kafin yace “I heard u’r going to get married right?” Har saida ta had’iye abu cikin karewar murya tace mashi eh,

“Kin hak’ura da zama Doctor kenan?” d’an runtse ido tay lokaci guda kuka yazo mata tace “Ehhh.. ” yana jiyo sheshshekar da ta fara yi a hankali, d’an yamutsa baki yay kafin yace “Why are u crying, ba kina so ba shiyasa kika amince” cikin kuka tace “a’a Ya Haisam wllh bani so ba ni da yadda zan yi ne in ban amince ba Baffana zai shiga matsala ne Baban shi Ard’o zai tsine mashi yanzu haka ma duk yan gidan sun juya masu baya Saboda ya nuna bai so ayi man Auren shiyasa kawae na Amince don in taimake shi” sosae yake jiyo sheshshekar kukan nata yanzu slowly ya runtse idonshi ya d’age kan shi sama boiling from inside, ba k’aramin abu ke k’ona mashi rai ba amman wannan Al’amarin sosae ya ta6a mashi zuciya ba kamar yanzu da yake jiyo kukan ta ya fahimci itama abun ya ta6a mata zuciya sosae, sun dau d’an lokaci haka kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya kira sunanta ta amsa yace “is Ok, I get u so stop crying and pray for d best” jinjina kai tay kaman yana ganinta sai kuma tace to daga haka yace mata zai kwanta su dare ne yanzu tace mashi sai da safe, koda suka gama wayar zaune yay a wurin bai tashi ba still kan shi a d’age yake saidae ya bud’e idanunshi ya k’ura ma ceiling ido da alama tunani yake, suna gama wayar taci gaba da kukan da take yi wanda ba na komae bane face tabo da Haisam ya fama mata, a cikin ran ta take ayyana da ta aure shi duk da yanzu bata shiga wannan halin ba tunda ba wanda zai ce ai zai mata aure tana cikin haka Saude ta shigo don tace mata ta fito ta ci Abinci ta iske ta haka da sauri ta zauna gefen Katifar ta janyo kan Fatun saman cinyarta ta shiga tambayarta lafiya cikin kuka take fad’in ita bata son auren nan, sosae ta ba Saude tausayi don Hajiya ta fad’i mata zancen Auren da za’ai ma Fatun, lallashinta ta shiga yi tana mata Nasiha har sai da tayi shiru sannan ta kama ta ta kaita toilet don ta wanke face d’in ta bayan ta gama ne suka nufi Parlor. Kullum gidan Hajiya take wuni ba laifi gwaggo na d’an sake mata amman ba wani sosae ba, ranar Friday da safe Baffanta ya kirata ya sanar da ita game da zuwan shi ranar lahadi in Allah ya kaimu yace mata akwae wani Abokin shi da zai kawo shanaye kasuwar charanchi ranar lahadin in zai koma sai su tafi tare koda akwae kayan da za’a d’auka tunda Motar tashi babba ce, wata irin kyerma jikinta ya fara yi a dabarbarce take amsa mashi bayan sun gama wayar zaune tay tana ta zare ido ya dae tabbata auren za’ai mata ji take tamkar ana zare mata lakar jikinta ta d’au lokaci a haka kafin da k’yar ta mik’e taje ta sanar ma gwaggo to itama dae ta girgiza da jin zancen amman bata nuna ba kawae sai ce mata tay Allah ya kaimu bata ji komae ba da yanayin yadda gwaggon ta bata amsa don tama saba da yadda take mata Magana yanzu, bayan ta fito ta koma d’aki gyale ta yafa ta nufi gidan Hajiya lokacin da ta je hajiyar na bedroom d’inta da sallama ta shiga ta amsa mata da murmushi gefenta ta baza wasu takardu da alama tana duba wani abun ne, gaida ta Fatuu tayi ta nuna mata gefenta tace ta zo ta zauna bayan ta zauna ne hajiyar ta tambayeta lafiya ta ganta sukuku nan da nan idanunta suka kawo ruwa tana kyakkyafta idanu don kada su zubo murya na rawa ta fad’i mata game da zuwan baffan nata itama hajiyar Maganar ta dake ta tay shiru can kuma sai tace Allah ya kawo shi lafiya Fatuu ta amsa da Amin yayin da kwallan da take ruk’ewa suka fara zubowa Hajiya ta fara lallashinta had’i da yi mata Nasiha mai tsuma jiki sosae taji ta samu natsuwa.

 

Washe gari Asabar Fatuu da ta je islamiyya ta yi ma k’awayenta bankwana had’i da neman yafiyar su duk sunyi mamakin jin zancen Auren don ba wanda ya san da Maganar har Malaman su ma sun yi mamaki sun kuma yi mata Addu’oi har Malam Nazifi na cewa bata fad’i da wuri ba da an yi mata sauka amman ko bayan ta tafin in sha Allahu zai sa ayi mata bai amshi hadda ba a lokacin sai kawae yayi masu Wa’azi game da rayuwar gidan Aure da yin biyayya ga miji sun sha kuka ita da k’awayenta yan ajin su da aka tashi har saida suka rakota har gida, tunda ta dawo take k’umshe a cikin d’aki ko Abinci ta kasa ci Alwala kawae ke fiddo ta haka ma gwaggo kowa dae yana cikin matsananciyar damuwa, bayan sallar la’asar ne tana zaune kan abun salla wayarta tay ringing ta mik’e taje bakin gado inda take ajiye ganin hajiya ce yasa ta d’auka da sauri bayan ta gaishe ta ta tambayeta tana gida ko ta tafi islamiyya tace mata tana gida tace to ta zo yanzu ta amsa da to, dama akwae hijab a jikinta wucewa kawae tay bayan ta lek’a ta sanar ma gwaggo hajiya na kiranta ta d’aga mata kai kawae, a Parlor ta iskesu ita da Saude da Tk ga wasu manya manyan kwalaye guda biyu dake a bud’e shak”e da kayan amfanin kitchen gaida su tayi su duka suka amsa mata fuska a sake hajiya ta nuna mata kayan tace “Fateema ga kaya nan ki duba in akwae abunda kike so wanda babu sai ki yi Magana, can waje a bayan Mota akwae freezer da gas cooker ba’a shigo dasu ba kar ai wahalar sake fitar dasu kuma” mutuwar tsaye Fatuu tay tana ta zare ido ganin uban kayan dake gabanta wai kuma nata ne, ganin bata da niyyar dubawar yasa Hajiya ce ma Saude ta firfito mata da kayan ta gani ta amsa da to ta duk’a ta fara fiddo kayan, ba abunda babu da zaka samu a kitchen d’in yan gayu tun daga kan kaya masu amfani da wuta da sauran kayan amfani a cikin d’ayan kwalin harda rantsattsun zannuwan gado da labulaye sai daga baya ne ma Fatun ta lura da k’aton kwalin plasma TV dake can gefe itama Hajiyar tace tata ce she was completely speechless sai bin komae take da ido Hajiyar ta tambayeta akwae sauran abunda take so wanda babu girgiza mata kai kawae tay don ta kasa Magana ganin abun take tamkar a mafarki tana cikin hakan Hajiya ta mik’o mata kud’i tace “ga wannan kud’in da kika kawo man ne Yayan ki ne ya turo da kud’i aka siya maki komae sai ayi wani amfanin da su” idanu raurau ta kalli hajiyar tace ta kar6a mana sai kawae ta saka mata kuka Hajiya tace “Fateema wannan koke koken yayi yawa zai iya ja maki wata matsalar ina mun gama Magana dake?” Kai ta d’aga mata tace to tayi shiru sai lokacin ta yi mata godiya Hajiya tace ma Tk ya tashi su maida su cikin Mota a had’a da sauran akai can gidan ya amsa da to ya mik’e Saude ma ta tashi ta kama mashi suka fara fita da su, gaba d’aya da Sauden da Fatuu aka tafi lokacin Amadu na shago Tk ya parker hilux d’in Hajiyar duk suka fito Amadu na ganin su shima ya fito suka fara kai kayan ciki, jin anata kacaniyar shigo da kaya yasa gwaggo fitowa tana yin arba da kayan tay turus tana bin su da ido Fatuu ce ta nufe ta ta tsaya a kusa da ita a sanyaye tace “wai Hajiya ce tace a kawo Ya Haisam ne ya turo da kud’i aka siya ga wanda na kai mata tace a yi wani abun da su” ta kai Maganar tana mik’a ma gwaggo kud’in hannunta a hankali tace ta ruk’e a hannunta, lokacin Saude ta k’araso ta gaishe da gwaggon da d’an murmushi ta amsa mata tayi mata godiya, bayan an gama shigo da komae su Tk d’in sun tafi Amadu ya fara firfito da komae cike da mamaki yana dubawa itama gwaggo idonta na akai lokacin da ya gama ya d’ago ya kalli Gwaggo yace “Naira dae tasha kashi a wurin nan wannan ai an kashe million koma fi, ji wannan k’atuwar freezer da gas cooker don Allah ga plasma ma babbar” ajiyar zuciya kawae gwaggo ta sauke kafin a hankali tace an gode Allah ya saka da Alkhairi Amadu ya amsa da Amin ganin tana niyyar juyawa ta koma d’aki yace ba za’a shiga dasu bane ta dakata tace tunda tafiya za ai dasu su kauda su gefe daga haka ta shige d’aki bada jimawa ba kuma sai gata ta fito sanye da hijab ta nufi gidan Hajiya don yin godiya, da daddare lokacin Fatuu ta gama komae ta kwanta tay tunanin yakamata tayi ma Ya Haisam godiya duk da bata son Auren taji dad’in kayan don ko d’iyar wasu masu kud’in ce iyakar abunda za’a mata kenan, lokacin da ta kira dawowar shi kenan daga Masallaci sallar Asuba a edge d’in gado ya zauna yay picking call d’in bayan ta gaida shi ya amsa ta shiga yi mashi godiya yace ba wani abu shiru suka d’an yi jin kaman tana kuka yasa shi fara lallashinta suna cikin hakan Fanan ta shigo jikinta sanye da jalbab da alama itama sallar tayi zama tayi kusa da shi tana sauraran yadda yake Magana cikin kwantar da murya har saida ta d’an yi mamakin da wa yake Magana haka, sosae ya kwantar mata da hankali kafin sukae sallama yay mata Allah ya tsare hanya yace sai ya sake kira, yana cire wayar Fanan ta tambaye shi wacece yake lallashi haka bin ta da ido yay ganin ta kafe shi da idanu alamar amsa take jira yasa shi d’age mata gira yace “kishiyar da zan maki ce” wani kalan kallo ta jefa mashi ta d’aure fuska tamau can kuma sai ta ce “Babe I hate dis kind of jokes” murmushin gefen baki yay ya ja jiki ya jingina bayanshi da heardboard yana cigaba da kallonta ta wani sha murr ita ala dole bata son zancen kishiya ganin baida niyyar yi mata bayani yasa ta k’ara tambayarshi da wa yake wayan sannan yace mata Zaraah ce with surprise tace to mi ya faru taji yana lallashinta haka sai lokacin ya sanar mata zancen Auren da za’ai mata itama ta nuna bata ji dad’in hakan ba k’arshe tace Allah yasa hakan yafi zama Alkhairi. Washe gari da safe lokacin da ta je gaida gwaggo tace mata ta shiga makwabta tay masu sallama tace to, duk inda taje da an ji zancen Auren sai anyi mamaki jin abun kwatsam akai tayi mata fatan Alkhairi harda masu bata kud’i amman ta k’i amsa daga baya ta wuce gidan su Haulat lokacin da ta sanar ma innarsu haulat batun Auren sosae ta girgiza don abu ne da ba wanda ya ta6a tunani Fatun harda kwallarta innar ta shiga bata Hak’uri anan ta tambayeta Haulat kuwa ta sani tace mata a’a bata samun ta a waya innar tace in sha Allahu zata kirata ta sanar mata, da zata tafi ta d’aukko wani glass jug da kwalin set d’in Warmers da unbreakable plates cikin kayan Auren haulat ta bata Fatun na ta bassu tace sai ta amsa in ba haka ba zata aika mata dasu gida dole ta amsa tay mata godiya ta tafi innar nata jajanta abun a ran ta, Sai wuraren La’asar Baffan Fatun ya iso sosae taji dad’in ganin shi sai dae tana kallon shi ta fahimci ya rame sosae har duhu ma yayi hakan ya tabbatar mata da duk abunda ya fad’a na halin da yake ciki dama kuma ta gasgata shi tun da ya fad’i mata, a d’akin Kawu Amadu ya sauka bayan sun gaisa Amadun ya fita ya rage daga shi sai Fatuu dake gefenshi tana mashi murmushi yace “inna wuro an saka ki cikin damuwa ko?” d’an girgiza mashi kai tayi yace “ah kar ki man k’arya da ganin ki kina cikin damuwa fuskar ki ya nuna” tana murmushi tace “Baffana kai ma ai ka rame sosae” d’an murmushi shima yay yace “Ya za’ai sai Addu’a kawae, ki yi hakuri don Allah” da sauri tace “ba komae Baffa na rungumi hakan a matsayin kaddara ta” jinjina kai yay lokacin gwaggo ta shigo da sauri ya tsugunna itama ta duk’a daga can wurin bakin kopa ya shiga gaidata cikin harshen fulatanci tana amsawa fuskarta ba yabo ba fallasa tay mashi an zo lpy ya amsa da lafiya lou suka d’an yi shiru sai kuma ta mik’e tace Allah huta gajiya ta fita, a sanyaye ya kalli Fatuu suka had’a ido ya tambayeta har yanzu bata hak’ura ba ne tace mashi kar ya damu ta hak’ura ya dae yi shiru kawae amman daga yanayin da yaga gwaggon yasan tana cikin fushi don yadda suka saba gaisawa ma ba haka tay mashi ba duk da yasan dama dole tay fushi sosae don ba’a kyauta mata ba ita tasan wahalar inna wuro gashi an nuna mata fin k’arfi, da k’yar Fatuu ta sa ya d’an ci Abincin da aka kawo mashi ba sosae ba bayan ya gama tace yazo yaga kayan da Ya Haisam ya siya mata farko cewa yay ba sai ya gani ba tunda dasu zasu tafi amman ta matsa mashi saida ya fita duk da ya hana ta bud’a amman shima yayi mamakin uwayen kayan, bayan sallar Isha tare da Fatun yaje gidan Hajiya yin godiya lokacin tana Bedroom Fatuu taje ta kirata da fara’a ta fito tana mashi maraba lale shima ya mik’e yana mata dariya bayan ta iso ta zauna har k’asa ya duk’a ya gaishe da ita tana ya mik’e haba ya zauna, sosae suka shiga tattaunawa game da batun Auren da za’a ma Fatun bawan Allah harda kukan shi ya nuna bai ji dad’in hakan ba Hajiyar ce ta nuna mashi ya daina damuwa ya bita da Addu’a Allah yasa haka yafi zama Alkhairi daga baya suka hau yabon Fatun irin sadaukarwar da tayi ta hak’ura da karatun ta ita dai d’an murmushi kawae take, da zasu tafi sosae yayi mata godiyar kaya da abun Arziki da ake masu ta nuna mashi ai an zama d’aya su kai sallama Hajiyar ta tambaye shi lokacin da zasu tafi yace gobe bayan an gama sallar Asuba har hajiyar na cewa bazai bari ya k’ara hutawa ba yace ai da Abokin shi ne zasu tafi Saboda kaya kuma Abokin nashi gobe zai tafi tace ta fahimta sai Allah ya kaimu zata lek’o in zasu tafi, suna komawa gida Baffan nata yace taje ta kwanta tunda da wuri zasu tafi ta amsa da to tayi mashi sai da safe, tana komawa d’akin ta wayarta ta fara ringing taga Abbas ne bayan ta d’aga ta gaishe dashi yace ashe abunda ke faruwa kenan shi bai sani ba tunda bai nan sai yanzu Haisam ke fad’i mashi tace eh ga ma Baffanta har ya zo gobe da Asuba zasu tafi, sosae ya jinjina Al’amarin ya nuna baiji dad’in hakan ba daga baya yay fatan Allah ya za6a abunda yafi zama Alkhairi tace Amin yace in sha Allahu zai zo d’aurin Auren ta fad’a mashi Date d’in tace yanzu dae bata sani ba amman in ta tambayi Baffanta zata turo mashi yace Ok, suna gama yin wayar saiga Alert na 50k daga Abbas d’in ya turo mata text message cewa tayi amfani da su ba yawa har saida tay yar kwalla, a wannan Daren dai tsakanin Fatuu da gwaggo ba wanda ya runtsa har gwara Fatun tana d’an yin baccin sai kuma ta farka ta fara tunane tunane, yanzu abunda yafi damunta shine waye zata aura??? Wace irin rayuwar Aure zasu yi ita bata son shi kuma shima ta san ba son ta yake ba tunda dae Auren had’i ne ko ganin juna basu ta6a yi ba.

 

Washe gari kiran sallar farko Abokin baffan nata ya iso ba 6ata lokaci suka fitar da kayan aka shirya su a bayan babbar Motar suna gamawa suka nufi Masallaci don yin sallar Asuba lokacin itama Fatuu taje tayo wanka tazo ta kabbara sallar dama tuni ta gama shirya kayanta da zata tafi dasu don ba komae zata d’auka ba k’aton Akwatin da Haisam ya bata ne sai trolley d’inshi anan ta shirya kayanta na sawa ta bar ma gwaggo na tsakiyan sai wata jaka da ta zuba littattafanta da sauran abubuwan ta da take so, tana zaune Kawu Amadu ya shigo yace ta gama shiryawa tace eh ya fara fitar mata da kayanta lokacin da ya dawo zai d’auki na k’arshe ne Fatuu dake tsaye ta kira sunan shi ya kalleta kaman zata sa kuka ta mik’a mashi wayarta tace ” gata kaci gaba da amfani da ita sai ka bani taka” waro ido yay baki bud’e alamar mamaki kafin yace “a’a ki bar abun ki can ma ai zaki iya amfani da ita” da sauri tace “ai shiyasa nace ka bani taka kaga can bama wani Network ke da akwae ba mai kyau ko naje da ita bazata yi man amfani ba sosae kaman yadda kai zata maka don Allah ka amsa” ta k’arasa hawaye na zubo mata hannu ya kai yana goge mata yana cewa tayi shiru zai amsa, dama ta goge abunda zata goge tace ya tura mata abubuwan da ta bari kafin su tafi yace to ya amshi wayar ya d’auki d’ayar jakar da yazo d’auka ya fita, gari na fara wayewa suka fito don tafiya har lokacin Fatuu bata ga fuskar gwaggo ba lokacin da ta shiga don yi mata sallama a zaune kan abun salla ta isketa ta d’ukar da kanta k’asa, duk’awa tay gefenta ta gaishe da ita ta d’aga mata kai kawae shiru Fatun tayi can kuma tay k’arfin halin cewa “G…gwaggo zamu tafi” farko shiru tay sai kuma murya a disashe taji tace “Allah ya tsare hanya yasa Alkhairi Amadu zai kawo maki sak’o” daga haka tay shiru sosae gaban Fatuu ya fad’i don daga jin muryarta kuka tayi cikin rawar murya Fatun tace “to gwaggo ke bazaki zo ba?”shiru tay mata ta k’ara tambayarta nan ma tay mata shiru kawae sai tasa mata kuka tana fad’in “Don Allah gwaggo ki yi hakuri ki yafe man kar ki ce bazaki zo ba, kowa in za’a mata aure Mahaifiyarta na mata fad’a da nasiha ni waye zai man in kika k’i zuwa??” sai lokacin ta d’ago idanunta sun yi jawur cike tabb da k’walla tay d’an guntun murmushin takaici kafin tace “ga yadikkon ki ga kuma wasu iyayen naki cike da gida Fatuu” sosae take kuka tana rok’onta ita dae don Allah ta zo suna cikin haka Hajiya ta shigo gidan da sallama jiyo kukan Fatun yasa ta nufi d’akin gwaggon tana fad’in “koke koken ne har yanzu ba’a gama ba an bar mutane nata jira a waje tafiya bata kusa ba” d’aga labulan kopar tayi ta shiga ganin yadda fatun ke kuka ta tambayeta abunda ya faru cikin kuka ta sanar mata, wani kallo tay ma gwaggon rai 6ace tace “haba Dije wai miyasa kike haka ne don Allah, yarinya zata tafi baza kuyi rabuwar Arziki ba ki faranta mata rai sai ki fad’a mata abunda zaki tada mata hankali haka” girgiza kai gwaggon tayi tace “nifa ban ce mata bazan je ba ita ta yanke hukunci” Hajiya ta kai hannu ta mik’ar da Fatun tsaye tana ce mata tayi shiru tama isa tace bazata je bikin ba suna nan zuwa harda ita sai lokacin taji sanyi a ranta suka nufi hanyar fita tana ta waiwayen gwaggo da tayi zaune bata da niyyar mik’ewa bare ta rakata, waje suka fito dama ita kawae ake jira Hajiya ta kaita har bakin Motar tace ma Baffanta gata nan su tafi kar suyi dare a hanya cike da girmamawa ya amsa mata da to ya bud’e ma Fatuu kopar Motar ta baya ta haye ta lek’o da kanta tana kallon su Tk da Amadu da Saude harda wasu daga cikin makwabta da suka fito sai kuka take Amadu ma ya kasa jurewa saida ya yi kwalla da k’yar ya matsa ya mik’a mata wayar tashi cikin kuka tace “Kawu Amadu zaka zo ko?” Da sauri ya jinjina mata kai ya kamo hannunta guda yace “in sha Allahu tun kafin bikin ina nan zuwa ki yi hakuri don Allah ki kwantar da hankalin ki kin ji” kai ta d’aga mashi lokacin Baffanta yace ma Amadu ya rufe mata kopar yace to ya saki hannunta ta maida kan ta ciki ya rufe sannan ta sake lek’o da kan ta windown kopar, zagayowa Baffanta yay ya yi masu sallama ya k’ara ma Hajiya godiya duk suka yi masu Allah ya tsare ya kai su lafiya ya amsa masu daga haka ya juya ya nufi gaban Motar ya shige shima Abokin nashi wanda shine driver d’in da zai tuk’a Motar ya lek’o yay masu sallama daga haka ya maida kan nashi ya tashi Motar wani bugu gaban Fatuu yay ta d’aga hannu tana masu bye bye tana ta kuka suma duk suka d’aga mata Tk da Saude ma duk kasa jurewa su kai sai da suka zubar da kwalla Motar na fara tafiya kawae sai ganin fuskar gwaggo tay ta lek’o sosae ta d’aga mata hannu ta kira sunanta da k’arfi “Gwaggo!!!” hakan yasa duk aka waiga ana kallon gwaggon don ba wanda ya lura da ta fito da k’yar ta d’aga ma Fatun hannu guda itama tay mata bye bye……….

 

 

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button