Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 75 Complete Novel


_Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 400 ne,za’a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari sannan a kula wannan itace numbar wayata,Wasu suna ɗaukar numbar Wanda suka bani tallarsu kayansu suna kiransu a matsayin ni,bayan ni ga numbar dana bada nan itace numberta_

*Nagode sosai da addu’o’inku agare ni,da kuma uzurin da kukayimun,har zuwa wannan lokacin,Allah yabar zumunci a tsakaninmu daga nan har gidan aljanna💃*

*nace ba Masu satar littafi suna fitarwa ta bayan fage,mai yasa baku ƙarasa masu labarin ba?kuma kenan saida kuka jira ni?ae nayi tunanin cewa zaku ƙarasa masu labarin ne ashe dai sai anjira Boss*😂🤣😅

Bismillah

 

❤🤍❤

A hankali ya tura ƙopar bedroom ɗinsa tare da shigewa ciki,turus yayi ya tsaya yana kallon junaid dake manne da Mommynsu suna bacci yadda kasan wani jinjiri ya ƙanƙame ta sae faman sharar bacci suke yi atare,murmushi ya ɗan saki tare da wuce wa cikin bedroom ɗin,Rage kayan jikinshi yayi bayan ya kammala ya shige cikin toilet,Within 15mins yayi wanka,sae gashi ya fito ɗaure da towel,tsaf ya kammala gyara jikinshi agaban dressing mirror,kafin ya koma wurin Closet ɗinshi,ya ɗauko wasu lallausan kayan bacci riga da wando farare ya zura ajikinshi,bayan ya kammala shirin kwanciya,ya zagaya ta baya dai dai saitin da junaid yake manne da mommyntasu ya lalla6a tare da hayewa saman gadon,zuba mata ido yayi yana kallonta,kullum koma mashi takeyi tamkar sabuwar amarya,ji yake kamar ma ba’ajima da yin aurensu ba,saboda tsabar son da yake yi mata,ba ƙaramin kewar matar shi yayi ba,har yanzu bai kammala hucewa ba,tunda tadawo kullum da daddare suna manne da juna,a kwanakin nan ba ƙaramin kwanciyar hankali ya samu ba,ya zama cikakken mutun don rashin Alexandra ba ƙaramin gibi yayi mashi ba,kasa janye idanunshi yayi daga kallonta da yake yi,tayi wani irin haske mai kyan gaske,fatarta kamar ta jinjiri saboda tsabar sheƙin da takeyi da daukar ido,bin dogon gashin kanta yayi da kallo wanda ya baje agadon bayanta,a hankali ya mayar da idanunshi akan farar half vest ɗin dake ajikinta,nan take ya fara shiga yanayi na buƙatarta,ga kuma junaid ya riga shi,to ya kenan?
ƙasa ƙasa yayi da muryarshi dai dai saitin kunnan Junaid ya ambaci sunan shi a hankali”Junaid!junaid!tashi ka koma bedroom ɗinka,”yayi hakan ne saboda baison ya tashe ta,yasan inta farka ba lallai tabari ya rabata da junaid ba,jin shiru junaid bai motsa ba yasa shi ƙara ɗan ɗaga muryarshi yace”junaid!junaid!pls get up and go back to ur bedroom,inaso in kwanta ne!”
Shiru junaid ba alamun ma zai farka,hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarshi yace”Junaid!junaid!Ka tashi mana!!”
Duk wannan suratan da Abbansu keyi kaf a kunnan junaid,sarai yana jinshi yayi banza dashi,tun kiran farko da yayi mashi ya farka,koda yaji Abbansu na cewa ya tashi ya koma bedroom ɗinshi zai kwanta,sai ya ƙara ƙanƙame mommyn tasu,don yaci alwashin cewa yau fa abbansu bazai kwana tare da mommynsu ba,ba don komai ba sae don shi aganinshi Abbansu baiyi mashi adalci ba,don me zai dinga kwana tare da Mommynsu bayan shi ne ya dace su dinga kwana tare da ita,Saboda tafiyar da tayi ta barshi tun yana jinjiri,yanzu lokacin shi ne bana abbansu ba,dole ya haƙura yabar mashi,Tashin hankalin da ba’a sama shi date!
“Junaid!nafa son cewa kana ji na,kayi banza ka ƙyale ni!zaka tashi ko saina yi wurgi dakai,”a faɗace Abban nasu yayi maganar yana kallonshi,
turo baki junaid yayi cikin ƙunƙuni yace”Abba,wlh ba inda zani!yau kwana na ne,”
Har saida gaban Abbansu ya faɗi rass saboda yadda maganar ta junaid ta dirar mashi a kunnanshi,Cike da mamaki ya maimaita maganar “yau kwanana ne!”!
Junaid dake maƙale da Mommynsu yace”eh,abba kadaina ma wahalar da kanka,Allah yau ba inda zani,kullum sai kayimun wayau,kana kwana tare da mommy,fisabilillahi Ni da kai waye ya dace ace yana kwana tare da Mommy!!!?
Saboda tsabar takaici sam abbansu ya rasa me zaiyi ma junaid,gashi babu mabugi a kusa balle ya kwaɗe shi,ko ya samu sanyi aranshi,
Ganin junaid ya turje bilhaƙƙi dagaske yake bazai tashi ba,gashi kuma Alexandra tafara mutsu mutsu alamun suna takura mata,kuma baiso ta farka daga baccin saboda gudun karta hanashi kora junaid izuwa bedroom ɗinshi,hakan yasa ya yanke shawarar binshi ta lalama,
Sassauta muryarshi yayi tare da cewa”Pls babyn abbansa,abeg dan Allah ka tashi ka koma bedroom ɗinka,help ur dad pls,bakasan halin da nake ciki ba,pls junaid ɗin Abbansa,”
Ƙara ƙanƙame Mommynsu yayi tare da cewa”wlh Abba dama kadaina yi mun magiyar nan,ni yau tare da mommyna zan kwana,”
Muryarshi tamkar zaiyi kuka yace”to ni a ina kakeso na kwana?junaid baka tausayin Abbanka ko?meyasa zakayi mun haka?yau kuma rigimar akaina zata ƙare”?
ashagwa6e junaid yace”Abba,gaskiya kayi haƙuri nidai babu inda zani,kaje bedroom ɗina ka kwana mana,’yayi maganar tare da ƙara shigewa jikin Mommyn tasu,
Rai a6ace Abba yace”Don ubanka zaka tashi ko bazaka tashi ba!!”?
shiru yayi bai tanka mashi ba,sae ma minsharin ƙaryar da ya dinga ja,don abban nasu yasan cewa bacci ya ɗauke shi,
A daddafe Abbansu ya miƙe daga zaunen da yake gefen gadon,ranshi duk a jagule kamar ya aza hannu aka ya fasa ihu haka yake ji,shi kaɗae yasan halin da yake ciki,bai ta6a sanin cewa junaid bai da wayau ba sae yau,duk yasa ya zama abun ban tausayi,hawaye ne kawai bai zubar ba,amma ba ƙaramin 6ata mashi rai yayi ba,ya jima yana zagaye a cikin bedroom ɗin,yana kallonshi,a ƙarshe ya nufi ƙopar bedroom ɗin tare da buɗewa ya fuce waje,
“Gobe ma anan zan kwana,”junaid ne yayi maganar bayan jin fitar abban nasu daga ɗakin,

“Daughter”! ƙiris ya rage ta saki tray ɗin dake hannunta,don bata tsammaci jin muryar mutun a bayanta ba,bakowa bace wannan face Sehrish wadda ke tsaye a cikin kitchen tana shiryama Sgr fresh fruits tare da coffee,jikinta na sanye da doguwar riga ta bacci mara nauyi milk colour tayi rolling mayafi akanta launin baƙi,
Ganin daddynsu yasa ta sakin murmushi tare da cewa”daddy,dama idonka biyu bakayi bacci ba har wannan lokacin”?
ƙarasa shiga kitchen ɗin yayi yana cewa”taya zan iya baccin?bayan ɗaya daga cikin ƴa’ƴana idonta biyu bata runtsa ba,raina ne ya bani cewar akwai wadda batayi bacci ba acikinku shiyasa na fito don inga wacece ashe kece….”
fashewa da dariya sehrish tayi jin abunda yace,shima dariyar ce ɗauke a fuskarshi,
..tsayawa yayi dab da ita yana kallon kayan marmarin da ta kammala Jera ma sgr,ta gyare tsaf ta yayyanka mashi su,
“Yanzu wannan kayan daɗin duk na wanene?ko ke zaki sha”?yayi tambayar a yayin da yakai hannunshi cikin ƙayataccen tray din wanda ke ɗauke da plate na kayan marmarin ya ɗauki yankin abarba ɗaya tare da turata abakinsa yana sha,
“Bani zan sha ba,na babban yaya ne,”tunkan ta ƙarasa maganar taga ya dakata da taunar abarbar da yake yi yana kallonta fuskar shi ɗauke da mamaki yace”Kina nufin Rafayet kika shiryama wannan?shiya sanyaki ne”?
Jinjina kai tayi tare da cewa”eh daddy,shine ya buƙaci na dinga kai mashi fruit tare da coffee adai dai irin wannan lokacin ƙarfe sha biyu na dare in sun dawo daga aiki….’daƙyar ta ƙarasa maganar ganin yadda fuskarshi ta canza,alamar wani abu baiyi mashi daɗi ba,
“Daddy wani abu”?ta furta hakan tana kallonshi,
shiru yayi jimmm kamar mai nazarin wani abu,kafin daga bisani yace”da sanin Abbanku”?
girgiza kai tayi alamar a’a sannan ta ƙara da cewa”yasan cewa inayi mashi aiki daddy,amma banda tabbacin cewar ko yana da masaniya akan hakan,bansani ba ko babban yayanmu ya sanar dashi,’
ta6e baki Uncle abusufyan yayi kafin yace”Abba bazai ta6a bari ba,bana tunanin cewar ya sani,taya mace kamarki zata dinga zuwa ɗakin namiji a irin wannan lokacin!!?
Gabanta ne taji ya faɗi rass,sunnar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannnunta,
“That’s imposssible!!!Banaso gaskiya hakan bai kwantamin araina ba,duk da ɗan uwanki ne shi a yanzu,amma hakan bai dace ace kina zuwa ɗakinshi ba a irin wannan lokacin,in fact ba’a son mace da namiji suna ke6ewa,nasan kinsan da wannan!”
Muryarta na kerma tace”Hakane daddy,
Jinjina kanshi yayi tare da cewa”Yawwa,ɗauki kayan marmarin ki kai masa,kada ki makara,”
Hannunta na kerma ta ɗauki tray din da sauri da sauri ta nufi hanyar fita daga kitchen ɗin,har ta kusa fita daga cikinsa,muryarshi ta dakatar da ita,
“Sehrish,”
“Na’am daddy,”ta amsa mashi tare da ɗan juyawa ta baya tana kallonshi,
“daga yau!banaso ki ƙara zuwa don kiyi mashi aiki,koda da safe ne ko da rana,Azmee itace mai aikin gidan nan,idan ma da buƙatar masu aikin zansa a ƙaro wasu,amma ba zakuyi aiki wa kowa ba,ina fata kin fahimce ni,’
Tunda abusufyan ya fara maganar gabanta ya shiga faɗuwa,hankalinta yayi mugun tashi,tuni idanunta sun fara canza launi,
Fuskarta ɗauke da damuwa tace”daddy,inajin tsoran shi sosai,bansan taya zan sanar dashi hakan ba,’
Murmushi Abusufyan yayi tare da takawa kusa da ita suna fuskantar juna yace”Bance ki sanar mashi ba,kawai inaso daga yau ki ɗan ɗaga ƙafa daga zuwa part ɗinsa don kai mashi abinci ko yi masa gyara,nasan cewa bazai damu da hakan ba,tunda ga azmee,in ma yayi magana akan hakan ki sanar dashi cewa”NI NA HANAKI!”
wani irin wahalallen yawu Sehrish ta haɗiye a bakinta,sam bazata iya yima daddyn nasu gardama ba,tasan cewa yayi hakan ne saboda tausayinsu da yake ji,baison suna aikin wahala,amma wannan hukuncin da ya yanke mata ba ƙaramin horo bane agareta,Na farko hakan zai nisanta tsakaninta da SGR,ganinshi zaiyi mata ƙaranci,in har ba downstair ya sauko ba,Allah ya haɗasu to bafa zata samu damar ganinshi ba,Abu na biyu kuma hayaam zata samu damar shige masa,don tasan cewar daga ta daina yin aiki a ƙarƙashinsa,hayaam zata kunno kai,na uku kuma batasan me zai biyo baya ba,in har yasan cewar ta daina yi mashi aiki,Shin zai damu ko bazai damu ba…..’
“Zaki iya tafiya,kada ki jima a bedroom ɗin nashi,dare yana ƙara yi,da zarar kin kai mashi,kiyi hanzarin komawa cikin ƴan uwanki ki kwanta kiyi bacci ki huta,
“Toh Abba,zanyi duk yadda kace,”
Murmushi abusufyan ya saki tare da cewa”ki kulamin da kanki daughter,sai da safe,”
murmushin tayi itama bayan ta amsa mashi,batare da 6ata lokaci ba,ta wuce sashen Sgr,kamar wadda aka zare ma lakar jikinta haka take tafiya,ba don komai ba sai don Hukuncin da Daddy ɗinsu ya yanke,Taya zata iya rayuwa batare da tana sanya babban yaya acikin idanunta ba akai akai!anya kuwa zata iya jurewa?wa zai kula mata dashi kamar yadda take kula dashi?tashin hankalin da ba’a sama shi date,

Also Download Namijin Duniya Book 2 Hausa Novel 

Wani irin farin cikine ya lullu6e hayaam dake la6e wurin kitchen ɗin tana sauraron abunda Uncle abusufyan ya tattauna tare da sehrish,kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha don tsabar farin ciki,ashe munafukar tana la6e ta kasa kunne tana sauraronsu,bakomai ya fito da ita ba daga ɗakinta face yunwar da taciyota,hakan yasa ta lalla6a ta fito don ta sama ma kanta abunda zata ci,anan ne fa tajiyo muryoyinsu suna magana acikin kitchen ɗin,shine tayi masu la6e,ta kwashe duk abunda suka tattauna acikin kunnanta,Lokaci guda ta manta ma da yunwar da take ji acikin cikinta,gudu gudu sauri sauri ta koma bedroom ɗinta,faɗawa tayi saman gadonta tana faman tiƙar dariya,bayan ta tsagaita da yin dariyar tashiga tufka da warwara acikin zuciyarta,
“Idan har inaso in samu nasarar cigaba da zama acikin gidan nan,dole saina haɗa kai da wani!wanda zai taimaka mun,wurin ganin na cimma burika na!tabbas ina bukatar shi,”ta ambaci hakan ayayin da take ƙoƙarin miƙewa daga zaune,
*WANENE SHI*!?

*Surgeon General Rafayet*

A ƙopar shiga bedroom ɗinshi ta tsaya,zuciyarta duk a ƙuntace take,don idanunta acike suke tab da hawaye ba don komai ba sai don hukuncin da daddynsu ya yanke agame da zuwanta part ɗin SGR,yanzu shikenan Yau zata kasance rana ta ƙarshe da zatayi aiki a sashen shi?shikenan bazata ƙara takowa ba da sunan ta kula dashi ba? 😥

Tamkar ta fashe da kuka haka ta dinga ji,dakyar ta daure ta cije tare da zuba sallama,shiru ba’a amsa mata ba hakan yasa ta ƙara daga muryarta,ta kuma zabga sallamar akaro na biyu,shima shiru bai amsa mata ba,hakan yasa ta fara tunanin cewa kodai yayi bacci ne ko kuma yana acikin toilet,don tasan shi akwai yin wankan dare duk in xai kwanta,

Tunani tayi ai shi muharraminta ne a yanzu hakan yasa ta kutsa kai tare da shigewa cikin bedroom ɗin nasa,wani irin daddaɗan kamshi ne ya daki hancinta,mai daɗin gaske,ga ratsa zuciya,lumshe idanunta tayi a hankali tare da sake buɗesu,tana ƙare ma shimfiɗeɗen gadon nashi kallo,kasa janye idanunta tayi daga kallon shi da takeyi,Yana a kwance saman gadon,yayi covering jikinshi da lallausan blanket ɗinsa,dai dai saitin stomach ɗinsa bargon ya tsaya,sumar kanshi ta rufe mashi fuskarshi da alama dae a gajiye suka dawo yau,baccin ma kamar bai shirya mashi ba ya ɗauke shi,duba da yadda yayi kwanciyar,right hand ɗinshi na asaman kanshi ya zagayo dashi ta dayan 6angaren,

Also Download Namijin Duniya Book 1 Hausa Novel 

A hankali sehrish ke nufar gadon nasa tana tafiya kamar wadda kwai ya fashe mawa akai,saboda rashin kwarin jikinta,ajiye mashi tray din tayi asaman side table ɗinsa,sannan tashiga tunanin,kodai ta tashe shi daga baccin kota ƙyale shi?ta jima tana nazari kafin zuciyarta ta bata shawarar cewa ta tashe shi kawai,ganin cewa ba kayan bacci ne ajikinsa ba,hakan na nufin baiyi night bath ɗin daya saba yi ba,tabbas bazaiji daɗin baccin shi ba,
Zuba mashi ido tayi tana ƙare mashi kallo,anan taga zufa na tsattsafowa a saman dogon hancinsa,da kuma wuyansa,mamakine ya kamata,aranta tace”Zufa kuma?duk da sanyin A.c dake akwai?karfa ace babban yaya bashi da lafiya”?cike da damuwa tayi tambayar,can kuma tace”kodan baiyi wankan daren daya saba yi bane?zai iya yiyuwa hakane,amma fa ina tsoran tashin shi daga bacci,
Bari dai kawai na haƙura kar in jama kaina,don na lura kwanan nan ɗaure mun fuska yake yi,kamar nayi masa wani laifi,’
Tana kai ƙarshen zancen zucin nata,tayi wani kwakkwaran juyi da nufin tabar wurin,cikin rashin sani tayi tuntu6e da doguwar ƙafarsa ɗaya data sauko ƙasan gadon,birkicewa tayi duk yadda taso ta ruƙe jikinta amma abun ya faskara,gaba ɗaya ta tafi ɗungurugum ta faɗa saman jikinshi,

Hankali a matuƙar tashe Sehrish ta zazzare idanunta tana kallon fuskarshi,gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,ganin ya fara motsa idanunshi yasa ta soma kiciniyar miƙewa daga saman jikinsa,sae dai kash bata samu wannan damar ba domin kuwa Sgr harya ware kyawawan idanuwanshi,biji-biji ya dinga ganinta acikin idanunshi,ita kuwa tuni jikinta ya shiga kerma,a hankali yakai hannunshi tare da ɗan Murza idanunshi,kafin ya ƙara ware su da kyau akanta,gaba ɗaya duk tabi ta rikice tuni zufa ta fara tsattsafo mata,ganin cewa dagaske dae ita yake kallo yasa ta ambaton nashiga uku,a hanzarce ta bar jikinshi ta sauka daga saman gadon,la66anta na rawa tace”dan Allah kayi haƙuri babban yaya,wlh ba yin kaina bane,na kawo maka fruits ne kuma banyi niyyar na tashe ka ba,tuntu6e nayi da ƙafarka na faɗo saman jikinka…..’kasa ƙarasa maganar tayi saboda wani irin kallo da taga yana jifarta da shi,sunnar da kai ƙasa tayi tana faman wasa da yatsun hannunta dake ta faman kerma,
“Kneel down,” ya furta da wata irin kasalalliyar murya ta wanda bacci bai ishe shi ba,
cikin sauri Sehrish ta zube saman guiwowinta agaban gadon nashi,
“Ur Hands up and close ur eyes,” yayi maganar yana yi mata nuni da hannunshi,
Jiki na rawa ta ɗaga hannayenta sama tare da kulle idanunta,sosai ta rufe su,tana matsar kwalla,
“Kada kiyi attempting buɗe idanunki,ko sauke hannayenki if not kinsan mai zai biyo baya,’
Muryarta na kerma tace”bazan buɗe ba,’
“Gud,” ya furta hakan a yayin da yake cire blanket ɗin dake rufe da jikinsa,a hankali ya sauko daga saman gadon,tsayawa yayi yana rage kayan jikinsa,sae da ya rage daga shi sae short,sannan ya wuce cikin toilet ya rufe ƙopar,
Saboda tsabar tsoro batama san cewa Sgr ya shiga toilet ba,sae faman shessheƙar kuka takeyi,after some minutes ya fito daga cikin toilet ɗin nasa,jikinshi sanye da bathrobe white colour,gaban dressing mirror ɗinshi ya zauna,ya shiga shafe jikinshi da mai,bayan ya kammala ya feshe ko’ina tass da tsadaddun tururrukan jikinshi,nan take ƙamshin ya gauraye ko’ina na cikin bedroom ɗin,ya jima agaban mirror ɗin kafin ya yunƙura tare da miƙewa ya nufi can cikin bedroom ɗin wurin Closet ɗinshi,
Almost 30mins Sehrish tayi zuƙunne saman guiwowinta jikinta na kerma,
dawowa yayi jikinshi sanye da nigh dress masu kyan gaske,
Wuri ya samu ya zauna daga gefen gadon yana fuskantarta,a hankali ya miƙa hannunshi tare da buɗe side drawer ya ɗauko wannan hoton da Uncle ɗinsu Abusufyan ya ta6a basu lokacin da suna ƴan shekara sha a duniya,zuba ma hoton ido yayi yana ƙare mashi kallo,kafin ya ɗago da idanunshi ya azasu akan fuskar sehrish yana kallonta,da alama nazarin wani abu yake yi a fuskarta da kuma fuskar ƙaramar yarinyar dake acikin hoton hannunsa,so yake ya gano wacece yarinyar dake acikin hoton nan,ƴar ƙaramar yarinya wata zararriya da ita,gashin kanta duk ya tarwatse ya yamutse yayi datti babu gyara,kayan jikinta duk sun fita hayyacinsu sun yage,ga ƙafafunta ko takalma babu,fuskarta kuwa duk tayi jaga jaga da majina,hoton yayi confusing ɗinshi,kokwanto ya shiga yi anya itace a cikin hoton?kodai ɗaya daga cikin ƴan uwanta ne,

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

“Open ur eyes,”
Jin muryarshi yasa tayi saurin buɗe idanunta wanda ke fitar da kwalla,muryarta na rawa tace”babban yaya dan Allah kayi haƙuri bazan ƙara ba,”tayi maganar tana faman shassheƙar kuka,
Miƙa mata hoton hannunshi yayi tare da cewa”Who is she”?
hannunta na kerma ta kar6i hoton daya miƙa mata,Ƙura ido tayi tana kallon hoton,nan take tashiga tambayar kanta ina Sgr ya samu hoton ɗaya daga cikinsu?ita kanta bazata iya tuna waya ɗauki hoton ba,kuma haka zalika bazata iya tantance wacece acikin hoton ba,saboda abun yayi confusing ɗinta,Kamar ita kamar kuma hossana,saboda gashin kan daya harmutse kamar na Mahaukaciya,tasan cewa hosana ce kawai keda irin wannan hargitsastsen gashin,
“Ina sauraranki,”ya furta hakan a yayin da yakai hannunshi tare da ɗaukar cup of cofeen da takawo mashi,ya shiga kur6ar shi anatse,
Cikin en ena tace”Wannan kamar hosana ce,bazan iya tantance wacece ba,’
ɗaure fuskarshi yayi tare da cewa”Oh ba zaki iya tantance wacece acikin hoton ba?what does that mean”
Muryarta tamkar zatayi kuka tace”Inaji hosana ce,wannan itace gashin kanta yake a haka,”
Hannu Sgr yasa tare da kar6e hoton ya ajiye shi a gefen shi,’
Tsuru tsuru tayi da idanunta,cike da tsoran kar ace ta ƙara wani laifin,
“I want u to tell me..,wannan bastard ɗin menene ma sunan shi?
“Ya sayyadi,” ta bashi amsa,
“akwai wasu mahimman bayanai da nakeso naji daga gare ki,hope zaki natsu kiban amsa,” jinjina kai tayi tare da cewa”in sha Allah,”
“Awani area kuka zauna a kano?”
“A hotoro ne” ta bashi amsa,
Jinjina kai yayi tare da ajiye cup ɗin dake hannunshi,then ya ɗauki banana yana 6areta a hankali yace”zaki iya tuna address ɗin gidanku kenan”?
“Eh,”

Also Download Banana Island Book 2 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

“Okey,’ ya ɗanyi shiru bayan yakai ayabar abakinsa ya ɗan gutsireta acikin bakinshi,kafin ya kuma cewa”a labarin da sister ɗinki ta bayar,ta faɗi cewa shi wannan mutumin ya ta6a nemanku,a cikinku akwai wadda ya ta6ayin raping”?
Daram!!!taji gabanta ya faɗi,girgiza kai tashiga yi muryarta har tana harɗewa wurin saurin cewa”babu…bai ta6a samun nasarar yin hakan ba,yadai ta6a yunkurin hakan,”

Shiru Sgr ya ɗanyi sae lokacin ya ɗan ɗago da idanunshi ya kalli fuskarta,gaba daya duk tabi ta rikice jikinta sae faman kerma yakeyi,yanayinta kuma kamar akwai wani abu data 6oye masa,
“Tell me the truth!kinsan bana son ƙarya,even if u hide it to me i will find out soon,so its better ki sanar dani,before naji a wurin wani!!”
Hawaye taji sun wanke mata fuskarta,ji take kamar ta tashi ta watsa da gudu,saboda ta tsani taji ana zancen Ya sayyadi,
ɗagowa tayi da idanunta waɗanda suka rune suka canza launi,kai tsaye suka sauka acikin nashi,cikin shessheƙar kuka tace”bazan maka ƙarya ba,yaso yayi hakan amma Allah bai bashi dama ba,’
“In har dagaske ne abunda kika faɗa,to meyasa kike kuka”?
“Saboda banason ana mun maganar shi,hakan yana tunamin rayuwar da mukayi a baya,”
kawar da idanunshi yayi daga kan fuskarta,sannan yace”Its okey,u can wipe ur tears,amma ba hakan yana nufin za’a daina maki maganar shi bane!dole ta hanyarku ne zamu samu dukkan bayanan da mukeso,before muci nasarar kama shi,’
Hannu tasa tana share hawayenta tace”Allah ya bani ikon Amsawa,”
“U can leave,”ya bata umarnin tafiya,
Tashi tayi jikinta asanyaye ta juya tana nufar hanyar fita daga bedroom ɗin nashi,gaba ɗaya duk jikinta yayi mugun sanyi,wata irin kasala ta lullu6eta,har ta kusa fita daga bedroom ɗin nashi ta ɗan tsaya tare da juyowa a hankali don tayi ma ɗakinshi kallon karshe tunda daga yau bazata ƙara zuwa sashen shi ba,da sunan yi mashi aiki,

Juyowarta keda wuya,idanunta suka shiga acikin nashi,har saida gabanta ya faɗi,kasa tafiya tayi kallonshi kawai takeyi,a yayin da shima yake kallonta,
Kusan 8 mins sannan taji muryarshi acikin kunnanta yace”Lafiya”?
girgiza kai tayi alamar ba komai,kafin tasa kai ta fuce daga bedroom ɗin nashi,

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Saukowa downstair tayi,hawaye nata faman zarya a fuskarta,sai da ta goge tears ɗin sannan ta wuce  bedroom ɗinsu, a hankali ta tura door ɗin ɗakin ta shiga,Samun Jahad tayi zaune daga gefen gadon ta zabga tagumi,yayin da hosana ke ta faman sharar bacci,
Bayan ta rufe masu ƙopar ɗakin ta koma daga gefen jahad ta zauna tare da ambaton sunanta”Jahad,”
A razane ta ɗago tana kallon Sehrish,sam bataji shigowarta ba,
“Mekike tunani ne”?
Murmushi jahad ta ɗanyi tare da cewa”Ashe kin fita,na farka ban ganki ba,acikin ɗakin,’
Sehrish tace”Naje part ɗin babban yayanmu ne,’
“Wannan mai blue eyes ɗin”? Jahad ta tambaya yayin da take kallonta,
“Eh,Sunan shi RAFAYET,amma suna kiranshi da BABBAN YAYA,”
“Shine babbansu kenan”?acewar jahad,
“A’a bashi bane babbansu gaba ɗaya ba,Akwai wanda suka girme shi sosai,Sunan ne ya dace dashi shiyasa suke kiranshi da haka,”
Jahad tace”kamar bazaiyi sauƙin kai ba,na lura ko magana baisan yi,ni in inama kallonshi tsoro yake bani,araina har cewa nake yi wai shima nan ɗan uwanmu ne,ƙwayar idonshi daban koda yake ga Ayaan nan shima idanunshi ash ne,mommynsu ma nata kalar na babban yaya ne,amma Mommynsu fa kamar bata son ganinmu nake gani ko kin lura da haka”?
Sehrish tace”eh hakane,amma kada kisa ma ranki wannan,idan kika lura abun kamar a jininsu yake ita da babban yaya,in ka biye ta yanayinsu toh bazakayi rayuwa asake ba,duk zaka takure kanka ne,kayi tunanin cewa kamar sun tsani mutane basa son ganinsu bayan ba haka bane,kawai basu cika son magana ba,ko kallon mutane basa son yi,’
Cike da mamaki jahad tace”tofa su kuma haka suke?shiyasa junaid shima baison ganina,har yau fa junaid ko son haɗa ido baiyi dani,in kuwa muka haɗa ido dashi har hararata yake yi ya kuma murguɗa mun baki,Wlh bana jin daɗin abunda yake yi mun,sai inga kamar ya tsane ni ne,abun ba ƙaramin damuna yake yi ba,gashi inason nasamu kusanci sosai dashi,kamar yadda naga kuna shiri a tsakaninki dashi,bansan meyasa ni yake mun haka ba,’
Tayi maganar fuskarta ɗauke da damuwa,
Sehrish tace”kai junaid ɗin keyi maki hakan?to ae duk gidan nan babu kamar shi,indai wurin son mutane ne,yafi kowa faran faran da mutane kullum cikin fara’a yake,Junaid fa ko yau kuka fara haɗuwa dashi zai nuna tamkar kun ta6a haɗuwa a baya,kuma yadda zai saki jiki da mutun zaisa kayi tunanin kamar kun share shekaru kuna atare,”
Sosai Sehrish ta shiga kora mata bayani agame da junaid,
Abun ba ƙaramin ɗaure ma jahad kai yayi ba,cike da mamaki tace”To Amma meyasa ni yake mun haka”?
Murmushi sehrish tayi tare da cewa”dole akwai dalili,amma ki barni dashi in sha Allah zan tambaye shi inji,”
gyaɗa kai jahad tayi tare da cewa”Shikenan,dan Allah duk yadda kikayi dashi ki sanar mun,”
sun jima suna fira atsakaninsu kafin bacci yayi awon gaba dasu,ƴan ukun Abusufyan,

Wuraren ƙarfe biyu daidai na dare,wata irin guguwar iska,ta shigo ta cikin windown ɗakin su Sehrish mai matuƙar tsoratarwa da kuma razanarwa baƙi wulik mai tafe da wani irin sauti,wanda ya ciccika kunnuwansu,a firgice hosana ta farka tare da fasa wata irin razananniyar ƙara,wanda yayi silar tashin Sehrish,ita kanta ta tsorata da ganin guguwar iskar nan,ta tattare wuri guda yadda kasan kwarangwal din mutun haka shape ɗinta ya koma bayan ta sauka a dakin nasu,ga yayi ajikinta,
Ƙanƙame Sehrish hosana tayi sosai tana cewa”Wayyo Allahna,mun shigo uku,ina daddynmu yake,menene wannan abun,’
Babu abunda Sehrish ke ambato face”innalillahi wa’inna ilaihirraji’una,yayin da ta ƙura idanunta akan guguwar nan data saukar masu acikin ɗakinsu,
jikinsu sae faman kerma yake yi gaba ɗayansu,hakoransu sae faman rawar ɗari suke yi kaf kaf kaf,saboda wani irin sanyi daya ziyarce su,

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 2 Complete Document

ganin guguwar ta tsaya agefen gadonsu,kamar su take kallo don harda ƴan idanu gare ta hakan yasa suka ƙara fashewa da kuka suna faɗin”Wayyo Allah mun shiga uku!”
A firgice jahad ta farka,jin ihun da su hosana keyi,adai dai lokacin hosana na cewa”wlh hada ƴan idanu ke gare ta,mun shiga uku,”
Zuba masu ido jahad tayi tana kallonsu ganin yadda suka kware baki suna kuka,Ga bargo a hannunsu,sun rurruƙe,
A hankali ta mayar da idanunta kan abunda suke kallo,guguwar nan ta gani tsaye da suffar kwarangwal tayi masu ƙuru da ido,
“Jahad kina ganin abunda muke gani kuwa”?Sehrish ce tayi mata maganar,
Jinjina kai jahad tayi tare da cewa”Nagani,mutun ne wannan ba guguwar gaske ba,koma waye yazo ne don ya tsoratar damu ne kawai babu abunda zai iyayi mana,”
Hankali atashe hosana da sehrish suke kallon jahad,jin abunda tace,babu alamun jin tsoro atattare da ita,hankalinta kwance tayi maganar,ganin haka yasa suma suka dakatar da kukan da sukeyi,
“Wama ya sani,ko ya sayyadi ne yazo da suffar guguwar nan don yazo yaga yadda muka koma,” jahad ce tayi maganar fuskarta ɗauke da dariya,

Baki asake suke kallonta,sehrish tace”Anya jahad ba macanzarki akayi mana ba?na fara kokwanto anya kece?taya zaki ga wannan tashin hankalin amma ki nuna baki damu ba?guguwa face tayi suffar kwarangwal kuma hada ƴan idanu kuru tana kallonmu ki kalla dakyau,”
Tsoki jahad taja tare da cewa”Nice mana,nifa Allah kaɗai nake tsoro,dashi na dogara,wannan koma menene yazo wlh ni dariya ma halittar take bani,ji idon fa yadda yake jujjuyawa kamar an ɗorashi,’ fashewa da dariya jahad ta kuma yi,Kafin ta kalli su hosana tace”abunda za’ae yanzu muja bargo mu lullu6e,mu rabu da ita,idan ta gaji da tsayuwa ta tafi,koda yake ba ƙafafu gareta ba,fiffike zatayi ta tashi,’
Ta ƙarasa maganar cike da nishaɗi,jan bargon nasu tayi,cikin sauri suka gyara kwanciyarsu ta lullu6esu da bargon,saboda tsabar tsoro Bargon da suka lullu6a dashi sae faman kerma yake yi,
“Jahad dagaske,baki ji tsoron wannan abun ba”?kasa-kasa Sehrish ta tambaye ta,

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Murya na kerma jahad tace”yanzu haka ma kuka nake yi,wlh atsorace nake,ƙarfin hali kawai nayi,saboda na ta6a jin wani malami yace idan ka nuna kana jin tsoran Aljani shine yake cin nasara akan mutun,shi har faɗama yake yi da aljanu shine nima na jaraba yin irin nashi,’
Duk da halin da Sehrish ke ciki sai da ta fashe da dariya tana kumshe baki,
“Jahad kinja mana bala’e,koma meye yanzu kin ƙara fusata shi da kalamanki,bansan me zai biyo baya ba,”acewar sehrish,
Jahad tace”Addu’a zamuyi kawai,insha Allah ba abunda zasu iya yi mana,’
Muryar hosana suka jiyo abayansu tana cewa”Sehrish dan Allah kuyimun addu’a,ko fatiha bazan iya karantawa ba a halin da nake ciki a yanzu,ga fitsari ya matse ni,’muryarta tamkar zatayi kuka tayi maganar,
Jahad tace”ki tashi ki shiga toilet mana!kinsan Allah kada kiyi mana fitsarin kwance,’
Fashewa da kuka hosana tayi tana cewa”taya zaki ce in shiga toilet bayan wannan halittar na nan ta ƙura mana ƴan idanunta,Allah ba inda zanje,sai dae ki tashi ki rakani ko kuma inyi shi a wando,’
Har haɗa baki sukeyi wurin cewa”Wai wa zai raka ki”?
“Ke ko sehrish daya daga cikinku ta rakani,”
“Tab,wlh nidai ba inda zanje,sai dai ko Sehrish,” jahad nakai ƙarshen maganarta sehrish tace”Ke baki je ba sai ni kike tunanin cewa zan rakata,Ae wlh sai dae tayi shi a wando,ba inda zanje,”
Ganin basu ɗauki maganarta serious ba yasa ta ƙara fashewa da wani kukan mai sauti,
“Dawo tsakiyarmu ki kwanta,zanyi maki addu’ar ɗaukewar fitsari,ae na iya,Oumma ta ta6a koya mana,”fashewa da dariya sehrish tayi tana cewa”kai jahad,ni ban ta6a jin wata addu’a ta ɗauke fitsari ba,’
Tashi hosana tayi tare da komawa tsakiyarsu ta kwanta,tana jiran Jahad tayi mata addu’a kamar yadda tace’
“Rufe idanunki”jahad ta fadi hakan fuskarta ƙumshe da dariya,runtse ido hosana tayi tare da cewa”Na rufe,”
Tofa mata addu’a jahad ta shiga yi a fuskarta,ita kanta me addu’ar batasan me take fadi ba,sae faman motsi take da baki,intayi sosai saita tofa ma hosana a fuskarta,
A ƙule hosana tace”waini sai tofa mun miyau kike a fuskata,kuma ni banji kina addu’ar ba,’
“Ita addu’ar a sirrance akeyinta,ba a bayyanata,kiyi shiru kawai zanci gaba da karanta maki har a samu fitsarin ya ɗauke,
Shiru hosana tayi tana faman sauke ajiyar zuciya,yayin da jahad taci gaba da karanta mata addu’ar,duk sehrish na sauraronsu,
Abu kamar wasa,bacci ya ɗauki hosana,
“Kamar tayi bacci”?sehrish ta tambaya,
Jahad tace”eh,tayi bacci yanzu saura mu ya rage muyi bacci,’
Sehrish tace”taya zamu iya bacci da waccen halittar a ɗakinmu?inta cutar damu fa”?
Jahad tace”Insha Allah ba abunda zata iya yi mana,muyi addu’a kawai mu kwanta,mu ɗauka kamar mafarki ma mukeyi,”
Kamar yadda jahad tace haka suka haɗa baki suna karanta addu’oi,bayan sun kammala kuma suka shiga karanta ayoyin alkur’ani mai girma atare,cikin lokaci ƙankani bacci ya ɗaukesu,
Yin baccinsu keda wuya wannan guguwar ta disashe daga wurin ta 6ace 6aat.

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete

Tashin hankali,kowaye yazo masu da wannan suffar?

Abunda ya faru bayan fitar abbansu daga bedroom ɗinshi,kai tsaye ya wuce upstairs part ɗin Marshal Omar,jikinshi duk asanyaye haƙika junaid ba ƙaramin 6ata mashi rai yayi ba,da alama sakin fuskar da yake yi mashi ne yana wasa dashi kamar tsaranshi,hakanne yasa raini ya fara shiga tsakaninsu,

Da sallama abakinsa ya shiga bedroom ɗin Marshal,samunshi yayi a kwance yana sharar bacci,bedside lamps ɗinsa ne suka haskaka wurin bed ɗinsa,
Shiga ciki abbansu yayi tare da hayewa saman gadon,ya jingina bayanshi a jikin headboard ɗin gadan,Ranshi duk a jagule yama kasa kwanciyar saboda yasan cewa koya kwanta bazai iya runtsawa ba,ba ƙaramin ƙuntata yayi ba,junaid ya fusata shi sosai,
Kwakkwaran juyi marshal yayi zai gyara kwanciyarshi,karaf idanunshi suka sauka akan Abban nasu,cike da mamaki ya ambaci sunanshi”Abba!”
fuskarshi ɗauke da damuwa yakai idanunshi akan fuskar Marshal yace”Omar,dama ba bacci kakeyi ba ne?”yayi maganar ayayin da yake ƙoƙarin 6oye damuwarshi,
Yunƙurawa Omar yayi tare da tashi daga zaune yana fuskantar abban nasu yace”Abba!meya faru naganka anan?kuma fuskarka da alamun damuwa attare dakai,”?
shiru abbansu yayi na wani lokaci yana deciding akan ya faɗa ma Omar halin da yake ciki ko kuwa ya ƙyale zancem kawai,
“Omar,ashe junaid bai da wayau har yanzu yaro ne shi”?
aɗan ruɗe omar yace”me junaid ya aikata,”?
“Hmmm,ya hanani sakat Omar,ƙiri ƙiri junaid ya shige mun ɗakina,yana can rungume da mommynsa,nayi nayi dashi ya tashi in kwanta amma ya ƙiya,wai har ni yake ce ma Yau kwanan sa ne!”?
Murmushi marshal Omar yayi jin shiriritar junaid,wato yau da Abbansu yake kishi,
“Abba,just calm down ur mind,ka bani 5 minutes yanzu zan dawo,just wait,”
Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya kama hanyar fucewa daga bedroom ɗin,
Zugudum abbansu yayi yana jiran dawowar Marshal,

Saukowa downstairs yayi kai tsaye ya wuce bedroom ɗin Abban nasu,a hankali ya tura door tare da shigewa ciki,koda junaid yaji an tura ƙofa sae ya ɗan ɗago da kanshi don yaga wanene,ashe baiyi bacci ba damuwar jahad ta hana shi sak har yanzu a tsorace yake,duk a tunaninsa abbansu ne,karaf idanunsa suka sauka akan Marshal Omar dake shigowa ciki,ae yana ganin Marshal Omar ya qara ƙanƙame mommynshi,don yasan cewa abbansu ne yakai shi qara shine akazo a ɗauke shi,
Omar na ƙarasawa wurin gadon ya Shiga tattara hannun jallabiyar jikinshi,muryar junaid kamar zai kuka yace”Ya omar dan Allah kada ka ɗauke ni,wai ni mai yasa akeso a takuramin…..’bai ƙarasa maganar ba Omar ya ɗaukesa gaba ɗaya ya aza a kafaɗarshi,ya fuce tare dashi daga ɗakin,
Suna tafiya yana kuka kamar ƙaramin yaro,Omar yace”rufe mun baki junaid,banason ƙara jin wani sounds daga bakinka stupid,wai har abba kake cema Yau kwananka ne!tsaran wasan ka ne!ko don kaga yana wasa dakai ne shiyasa ka raina shi?
Ya ƙarasa maganar a lokacin da yake hawa upstairs,
Cikin shessheƙar kuka junaid yace”Ya omar,ni fa ban raina shi ba,saboda me zai dinga zuwa yana kwana tare da mommy,bayan ni ya dace ace ina kwana a wurinta,abba baiyi mun adalci….’
Katse shi omar yayi da cewa”Shut up junaid,’
Tsit junaid yayi yana faman hura hanci,
“Tunda har ka fara kishi da mahaifinka,hakan na nufin cewar zaka Iya aikin Soja!yadda zaka ji daɗin kishin ƙasarka,”
Hankali tashe junaid yace”Am sorry ya Omar,bazan ƙara ba,Zan daina hanashi kwana,’
girgiza kai Omar yayi yana cewa”Ban amince ba,zuwa aikin Soja ba fashi junaid,U.S ma zamu turaka,zanyi ma sgr magana,dama abba kawai muke jira ya amince,kaga yanzu ka 6ata mashi rai nasan cewar a shirye yake daya miƙa ka wurinsu koya huta da shiriritarka,
Turo kopar bedroom ɗinsu yayi ya shige da junaid ciki,Abba na ganin shi ɗauke da junaid,ya ɗaure fuska a cikin zuciyarshi kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba,
Sauke shi saman gadon Omar yayi tare da cewa”Maza ka kwanta,”
turo baki junaid yayi yana kallon Abbansu,zuba mashi ido abban yayi yana kallon ikon Allah,
Kwantawa junaid yayi tare da Lullu6ewa da bargo,yayi ƙasa ƙasa da muryarshi yana cewa”abba hankalinka ya kwanta,ka rabani da mommyna,kuma gobe can zan kwana,in kuma aka hanani ɗakinsu sehrish zan dinga kwana,”
Saukowa abba yayi daga saman gadon ya kalli Omar tare da cewa”ngde ssae Omar,Ni zan wuce,mu kwana lpy,”
Fuskar Marshal ɗauke da Murmushi yace”Gud night abbana,”
Har yakai bakin ƙopar fita daga ɗakin ya juyo yana kallon Omar ɗin dake tsaye yana kallon bayansa yace”Omar wai cikin triplet ɗin nan Wacece taka acikinsu”?
Sunnar dakai ƙas Omar yayi yana faman sakin Murmushi,daƙyar ya iya furta sunanta”Hosana,”

Jinjina kai abbansu yayi fuskar nan ɗauke da murmushi yace”batare da 6ata lokaci ba,bayan an kammala walimar jibi zan nema maka auranta a wurin mahaifinta,saboda banason wani daga waje ya gansu yace yana so,nafison dukansu su auri na gida,saboda na yadda sosai da irin tarbiyar dana baku,zaku kula da rayuwarsu sosai,”
“But….Abba Rafayet fa,?shima zaka nema mashi auren ɗaya daga cikinsu in yaso sai a haɗa auren atare!!!!?

Back to top button