Fentin Zina Page 28 Hausa Novel
*****Na gaji da wulakancin ka Abdul! Na gaji!. Lokuta da dama kana jifana da miyagun kalamai ina yin shiru kana dauka tsoronka nike ji? Toh ina so ka sani babu wani tsoro naka ko wata soyayyarka data rage a cikin zuciyata, idan kaga zama dani takura ne a gareka Abdul ka sawwake mun zaifi mun sauki fiyeda kuntatawa rayuwata da kake yi dan Allah. Ta karasa tana hade hannayenta guda biyu.Kallonta yikeyi yama rasa me zaiyi tunani, zuciyarshi tana raya masa ka sake ta kawai, yayinda wani bangare na zuciyar ke gargadin shi da aikata hakan, ganin idan ya cigaba da tsayuwa a wajen zai iya aikata abunda zuciyarshi ke tunzura shi a kai yasa yaja kofa ya fice da sauri kamar guguwa ya banko kofar da karfin gaske.Ameena ta tabe baki tana fadin, idan ka balla kofar ai kaine wanda zai gyarata, ta koma ta zauna kan abincinta ta cigaba da ci tana watsar da duk wata damuwar dake kokarin kunno mata cikin kwakwalwar ta.Sam maryam bata lura da yadda fuskar shi ta sauya ba, sai ta hau cewa yawwa baby ka taso ta ko? Ganin zai wuce ta ya shiga daki ta kara fadin baby magana nike fah kasan yunwa nike ji sosai kuma bana jureta. Wani juyowan da yayi da irin kallon daya jefeta dashi nan take ta shiga natsuwarta saidai kuma ta lura da shatin yatsu a kumatunsa wanda da babu su.Wucewa yayi zuwa nashi dakin ya barta a tsaye a gurin, har tayi yunkurin binshi sai data isa kofar dakin shi taja ta tsaya ta kama baki sai ta canja akalar tafiyar nata zuwa dakin Ameena, babu sallama bare jiran izini ta tura kofar ta shiga bata tsaya a bakin kofaba sai da ta dangana da tsakiyar dakin ta kama kugu tana dube dube kamar mai son gano wani abu.Ameena da sai lokacin ta kammala cin abincin ta tattare su ta ajiye gefe sannan ta tashi ta zauna a gefen gado ta dubi maryam tana fadin ina fatan lafiya ko?Kamar wacce aka turo tace baki neme ta ba. Me kika ma mijina iye? Ya tashi da farin ciki shigowar shi dakin nan ya sauya masa fuska ta koma mara walwala shiyasa na biyo inji ba’asi, me kika masa? Ta tambaya tana kara jaddadawa da kai.Mikewa Ameena tayi ta saki murmushi sai ta taka ta zagayeta sau biyu sannan tayi madakata a gabanta wato sukayi fuska da fuska, sai ta dafa kafadarta still da murmushi a fuskarta tace shigowa yayi yana mun magiyar in bashi hadin kai domin a cewar shi bazai iya jira har kwana ya iso kaina ba saboda bai samu gamsuwa a tare dake ba shine yake so in taimake shi Kodak minti biyar ne zaiyi ya gama ba saikin gane ba, ni kuma gaskiya bazan iya shiga hakkin ‘yar uwata ba wannan dalilin ne yasa kika ga ya fita a fusace ai na dauka zaizo gareki ne ya huce haushi toh kinga tunda na ganki anan na tabbata lipton zai hada da lemun tsami yasha don rage radadi.Kuri maryam tayi mata zuciyarta na tafasa sai kuma shatin yatsun data gani ya fado mata tayi saurin cewa, amma naga shatin mari a fuskarsa ko taya hakan ta kasance? Ina bukatar karin bayani.Kara fadada murmushi Ameena tayi tace anan dai kamnayi kuskure, da naga yana magiya ne kamar zaiyi kuka kinsan su idan abun yazo musu kusan haukacewa suke don samun biyan bukata, shine nace mai zan amince amma bisa ga sharadi guda daya. Cikin sauri ya amince nan take, nace sai ka mari kanka sau biyu domin rama mun abunda kayi mun jiya, ba tare da wani tunaniba sai ya hau marin kansa wanda daga karshe ni kuma naki amincewa shinefa yayi fushi, amma nasan zai dawo ne. Ta karashe da marairaice fuska.Maryam tuni taja tsamayen kafafunta ta fita.Yana zaune saman one-seater dake dakinshi gefen shi kopin lipton ne ajiye wanda yasha jiya ne ba’a fitar ba ya jingine bayansa jikin jujerar ya lula tunanin irin hukuncin daya dace yawa Ameena domin bazata ci bulus din marin shi data yi ba.Banko kofar da akayine ya sashi duban kofar a zatonsa ko Ameenar ce ta biyo shi nan din don yaga rashin tsoro da kuma tsageranci a idonta, sai yaga ba haka bane maryam ce, baice komai ba har ta iso ciki ta tsaya akanshi lokacin da idonta ya sauka a kopin lipton tsabar masifar dake cinta bata fahimci na jiya bane daya hado lokacin suna tare a dakin nashi ta soma cewa.Abdul dama kasan kana son matarka ka aureni? Dama kasan baza ka iya adalci ba ka auroni ka kawoni gidan ka. Menene haka kayi, ranar girkina cikin ranakun amarcina kaje kana magiya kana rokonta saika kwanta da ita? Indai hakane baka mun adalci ba gara kawai ka sakeni in koma gidan mu don bazan iya rayuwa irin wanna ba a cikin gidan nan. Ta fada tana shewa da kukan da tayi ta rikewa.Tashin hankali ne ya riskeshi yana mai jin kukanta har can cikin karkashin zuciyarsa ya taso ya rungumeta ya soma rarrashinta da bata baki ya mata bayanin duk abunda ya faru daya shiga dakin Ameena bai boye mata komai ba gudun ya bar kofar zargi.Ajiyan zuciya ta sauke tana mai jin dadin bayanin daya mata wanda ya sanyaya zuciyarta daga tafasar da takeyi tayi guntun murmushi tace ka gafar ceni baby bisa ga rashin fahimtar da nayi a gare ka naji raahin dadi ne kan abunda matarka ta fada mun.Sakinta yayi ya gyara zama ya kalleta yace ta fada miki wani abu ne?Ta gyada kai tace kwarai kuwa, nan ta kwashe komai ta fada masa.Ya mike a fusace yace mata ina zuwa! Daga haka ya dauki belt din shi dake ajiye a gefen drawer ya fice bai saurari maryam dake ce masa ya dakata ba.Tana kwance kan gadonta tana chatting ya banko kofar a fusace yana fadin me kika fadawa matata?. Duk da ta tsorata dashi amma saita daure tahadiye tsoron ta mike zaune tace ni babu abunda na fada mata!. Ya nuna ta da belt din hannun shi yace kinga ki kiyayeni kada kija in miki lahani.Zuciya ne ya kawota wuya ta mike tsaye tace da nayi meye? Ko don kana ganin ina hakuri zaka shigo mun da rainin wayo, toh da kake nuna ni da wannan abun duka na zakayi ko meye? Wallahi ka kuskura hannunka ya sauka a jikina da sunan duka ka sani daga ranar ka daki aurenka.Mara kunyar banza mai bin maza har gida, ba saina dora hannuna a jikin ki ba kije na sake ki saki biyu…Dummm jinta ya dauke na wani lokaci kafin ta kalle shi cikin mamaki da tsoron furucin shi ta nuna kanta da yatsa cikin inina tace ka…ka…sake…ni kace?.Gyada kai yayi cike da rashin damuwa yace kwarai kuwa domin ba’ayi macen da zan rusuna mata ba ke din banza! Kuma ki gaggauta ficewa daga gida na idan ba haka ba wallahi na lahira sai ya fiki jin dadi ina fada miki. Daga haka ya ficewar shi, zama tayi kan gadon ta daf kuncinta tama rasa tunanin da zata yi, gaba daya kanta ya kulle saidai batayi dana sanin sakin daya mata ba domin dama wannan ranar ita take ta jira saidai kuma rashin jin dadin mutuwar aure, daukar wayarta tayi ta kira lambar fateema tana dagawa ta samu damar fashewa da kuka.Cikin rudu da tashin hankali fateema tace adda meya faru?.Fateema Abdul ne ya sake ni yanzunnan. Ajiyar zuciya fateema ta sake daga bangaren ta a boye don ta jima da gajiya da auren addanta dinnan wanda babu komai a cikinsa face cin zarafi da rashin kyautawa, amma a zahiri sai ta furta innalillahi wa inna ilaihi raji’un meya faru haka kuma garin ya?.Nan tayi briefing dinta abunda ya faru na yau din.Fateema cikin jin haushi tace dama can ya shirya rabuwa dake ne munafuki kuma sai yaga sakayya bi izinillah, yanzu dai ki fara tahowa gida ki dauki kayan sawanki kawai kafin wata kila ayi muku sulhu! Fateema ta fadi hakane saboda ta san iyakar hukuncin da baba malam zai yanke kenan sai dai idan shi Abdul din ne ya turje yaki.Toh tace tana mai jin baby dadi kuma, koba komai akwai sabo da shakuwa a da tsakaninsu.Shirya kayanta tayi cikin trolley ta hada duk abunda zata bukata taja tayi waje, daidai bakin kofar gidan su ta samu abun hawa ta shige.Abdul kam Koda ya fita daga dakin nata nashi dakin ya koma yana jin kanshi na sara mishi kamar zai rabe biyu kuma baya jin hukuncin daya yanke yayi tsauri, amma kasan zuciyarshi harya fara kewa da begenta domin yasan ba karamar wahala zai sha ba koda ta bangaren abinci da sauran abubuwa na kulawa saidai ya dau hakan komai zai wuce bada dadewa ba yama san dole ta kira ta bashi hakuri anan ne kuma zaiyi maganinta ya nuna mata matsayinsa. Maryam bata dakin ta koma dakinta saboda ta samu damar sauraran duk abunda zai wakana a tsakanin su, ilai kuma taji komai murna a wurinta kamar ta zuba ruwa a kasa tasha.Ameena tana isa kofar gida ta biya mai adaidaita ta shige gida.Babu kowa a tsakar gidan don haka dakinsu ta wuce ta samu fateema zaune tana danna waya shureim a gefenta yana ganin abunda take yi.Da gudu yaron ya taso ya rungumeta yana fadin momma na sannu da zuwa.Shafa kanshi tayi tayi murmushi tace sannu my boy ina inna?Tana wajen baba malam.Ta maida kallonta kan fateema tace kin fada mata abunda ya faru ne?Eh muna gama waya ta shigo shine na sanar mata kafin ki karaso.Huci Ameena ta fitar ta zauna gefen gadon tana rike da shureim ta furta Allah yasa kada baba malam ya kira wancan mutumin a waya domin ko kadan bana kaunar wani zama ya kara kaini gidan shi.Toh Allah yasa! Daidai inna ta dago labule ta shigo da sallama suka amsa ta dubi Ameena daga tsayen da take tace Ameenatu ya akayi haka? Yanzu malam ya gama waya da shi mai gidan naki amma banji dadin abunda kikayi ba, ai ba’a biyewa zuciya da kinyi hakuri! Kada ki sake kinji ko?Fateema ta riga yin magana tace inna dan Allah kada ki dorawa adda duka laifin domin na tabbata da zaki ji irin zaman da adda takeyi a gidan da baza kiga laifinta ba ko kusa akan abunda ya faru dinnan.Hum fateema kenan! Koma dai menene kije mahaifinku na kiran ki domin munji shigarki gidan.Toh inna, tace tana mikewa tace da shureim zauna ina zuwa ko?. Ya gyada kai ya koma wajen fateema ya zauna gefenta ita kuma ta fice inna ta bita a baya, fateema ta bisu da kallo tana cewa a zuciyarta, dama nasan a rina.Gurfane take gaban iyayen nata, baba malam yana mata nasihu masu shiga jiki daga karshe ya dora da cewa tunda ya tabbatar mana daya maidake dakin ki don haka bai kamta ki dau lokaci kafin ki koma ba, kamata yayi ki tattara yanzu ki koma gidan mijin ki ina kuma fata wannan ya zama na farko na karshe da irin haka zata faru a tsakaninku, ki kama kanki ki kama aurenki, babu wanda yake zaman aure don dadinsa kawai, kowa hakuri yake yi hatta damu iyayen ku ai kina ganin rayuwar da muke ciki, don haka ya zama dole Ko koyawa kanki karbar ko wane irin kalubale da kuma jarabawar dake cikin zaman aure ina mai tabbatar miki dadin na gaba, shima na mishi fada sosai kuma insha Allah zai gyara kusakuran shi, don haka ki kara hakuri kinji ko?.Ta gyada kai tana hawaye, har zuciyarta tana jin radadi sosai taso tayi zamanta a gidan su domin kwata kwata shi Abdul din ya fice mata a rai tana dai kokarin kyautata masa ne kawai don sauke hakkin aure.Insha Allah baba zanyi iya kokarina wajen gyara rayuwar aurena kuma dukkan kuskuren da nasan inayi zan gyara ku taya ni da addu’ah.Baba Malam ya Nina Mata kusa dashi yace zo nan ki zauna, babu musu tayi kamr yadda ya umurceta, ya shafa kanta cikin tsananin sonta da kaunar ta yace Allah ya muku albarka, kije fateema ta raka ki ki koma yanzun nan kafin azahar tayi, ta kuma dawo kada ta bari magriba tayi ta a waje.Toh baba nagode Allah ya kara nisan kwana.Inna dai batace komai ba illa Allah ya muku albarka kije maza ku hanzarta.Ameen tace ta mike ta fita tana matsar kwalla, tana shiga dakin tace da fateema baba malam yace ki rakani gida kuma kada kikai magriba a waje.Toh kawai fateema tace ta tashi ta dau hijab ta dau akwatin tace ke ki daga shureim.*****Abdul bayan sun gama waya da baba malam sai yaji wani tukuki ya tokare masa makoshi yace a kasan labbansa, kaji tsoho da iya tsara zance, ya sakani aikata abunda banyi niyya ba.Har yanzu maryam na dakinta, fitowa yayi ya nufi dakinta ya fada mata bari yaje gaida su mama, da toh kawai ta bishi.Bayan ya fita ta dawo falo ta zauna tayi kiran baby kawarta a waya tana dagawa tace kawata albishirin ki!Daga ta can bangaren baby tace goro fari kal!Ke in fada miki Abdul ya saki wannan ballagazar matar tashi dazu yanzu zanci duniyata sabuwa.Ke da gaske kike?.Kwarai wallahi yanzu haka ta bar gidan ta tafi gidan su.Baby ta kwashe da dariya tace na tayaki murna lallai umma ta gaida aisha kice ina nan zuwa gobe insha labari.Toh sai kinzo goben ina jiran ki.Ai kuwa da wuri zaki ganni.Toh shikenan bye….Tana sauke wayar aka turo kofar falon a zatonta Abdul ne har ta soma cewa babyyy baka tafi din ba.Sai tayi shiru sakamakon ganin Ameena da fateema da shureim rike da akwati, tsabar kaduwa da mamaki baki bude take kallon su ta kasa furta koda kalma daya ne.Haka Suka wuceta suma ba tare da sunce mata komai ba suka shige dakin Ameena.Suna zama fateema tace adda wallahi ba don ina tsoron fadan baba malam da inna dana taushe tsinanniyar nan a cikin gidan nan wata pigaggiya da ita wai har shela takewa kawayenta akan kin bar Mata gida wato, toh koni ada bana farin cikin dawowarki amma yanzu dan Allah adda ki koda mana wannan matar muga ta tsiya.Girgiza kai Ameena tayi tace baki san zuciyar Abdul dinnan bane akan wacce kike kira pigaggiya, sai ya iya komai akanta.Tabe baki tayi tace Allah ya kyauta.Nan dai suka cigaba da hira tare suka dora abinci, shinkafa da miyar data ji kifi danye. Da yawa suka yi domin zata ci gaba da yin girkin dasu har kwanaki bakwai din su cika.Bayan fateema tayi sallahr la’asar sai ta wuce gida, ita kuma ta kara wani wankan tasa kananun kaya wanda suka zauna a jikinta sosai daga saman cinyoyinta zuwa idon sawayenta duka net ne hakan yabaiwa fararen cinyoyinta bayyana.Ta gabatar da sallahr isha data ji ana kira kana ta mike ta dau wayarta ta koma falo ta daura kafa daya kan daya.Abdul ne ya turo kofar, ya tsaya a bakin kofar yana kallonta irin mayataccen kallonnan don ba karamin tafiya dashi wankantayayi ba tare da debe duk wani bacin rai daya kunsa game da ita yana jin soyayyarta na huda duk wata tsoka ta jikinshi tana shigewa zuciyar shi. A yadda ya tsaya yana kallonta shi kanshi baisan adadin lokutan daya dauka yana tsaye ba, har sai da maryam ta fito daga dakinta ta tsaya tana kallon irin kallon daya ke bin Ameena dashi,take wani kululu yatokare mata makoshi ta kalle ahi ta kalli Ameena.Ameena a jikinta taji idanu suna mata yawo haka yasa ta dan juyar da kai tana dagowa, nan fa aka shiga kallon kallo tsakanin su ukun……….. *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️



