Halysaah Page 111 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 111Ajay na kallon football wajen karfe sha dayan dare kiran Mai martaba ya shigo wayarsa ya rage volume din TV din ya sauke kafafuwansa kasa daga kan kujera sannan yayi picking call din, cikin ladabi ya gaida Sarki, bayan sun gaisa sarki ya tambayesa Khaleesat, yace “Tayi bacci ranka shi dade” Sarki yace “Ohk, goben za ku tafi UK for Hadiyah’s Convocation which is on Tuesday?” Ajay yayi shiru, can yace “I thought Wednesday ne ranka shi dade….” Mai martaba yace “A’a, Jawwad din bai tura maka Invitation din bane?” Duk da bai tura masa ba Ajay yace “Ya tura, ban kula bane da date din” Mai martaba yace “It’s Tuesday not Wednesday” Ajay yace “Toh Allah ya kai mu lafiya ranka shi dade, nasan ba lallai ka samu daman karasowa ba ko?” Mai martaba yace “Za a wakilce ni, beside Hajja ma gobe za su tashi zuwa England din in sha Allah, Kai ma ya kamata kai da matar ka should leave tomorrow ba sai ranan talatar ba” Ajay yayi shiru at first, sai kuma a hankali yace “Abba i think ba sai na je da ita ba, she will stay with her friend kafin in dawo” Mai martaba yace “Ko saboda me?” Shiru Ajay yayi, Mai martaba yace “To ku je tare, she will get to meet most of ur relatives da basu san ta ba, there is no point leaving her behind shi yasa nasa ayi mata Visa” Ajay ya sauke idonsa yace “Toh Abba, we will go together in sha Allah” Mai martaba yace “Good, Walid ma tun shekaranjiya ya tafi England din” Ajay yace “Ehh he was here yesterday, amma ya tafi yau” Mai martaba yace “Really, America ya tafi dama?’ Ajay yace “Eh nan ya zo” Mai martaba yace “Wani irin tafiya ne wannan yayi? Shi da zai tafi England that is just 7 hours from Nigeria me ya kai sa America tafiyar kusan awa sha shidda?” Ajay yace “May be he have something to accomplish here, but ya tafi England din daxu da safe” Mai martaba yace “Ohk then, take care” Ajay yayi masa sallama sannan Mai martaba ya katse wayar, ajiye wayar yayi ya jinginar da kansa jikin kujera yana nazarin ta yanda zai fara tafiya England da Khaleesat, shi ma ba da son ransa zai je ba balle ya wani je da ita, mikewa yayi kawai ya kashe kayan kallon ya wuce sama. Safiyyah da ta rike haɓa tana kallon Khaleesat da mamaki tace “To hakan yana nufin kishi yake da ni kenan ko me? Banda haka me yasa zai hanaki zuwa wajena bayan tare ya gan mu? Ji min mutum, Ko don saboda yasan ni Team Housemate ce? To dole ne sai na goyi bayan cin amanar da yayi yake nufi ko me? Ni dama tun asali kowa yasan Housemate nake yi shine nawa, kuma bazan taɓa canza ra’ayina ba, har gobe bazan dena cewa ba a kyauta ma Housemate ba an ci amanarsa an cucesa, shekaranjiya ma naga ya saka status wai amaryarsa zata yi convocation a Oxford, caption dinsa ne yasa jikina kuma yayi sanyi qlau” Khaleesat ta daga ido tana kallonta, Safiyyah ta taɓe baki tace “Ko meye na wani sa wife dinsa a caption bayan kowa yasan wife dinsa ce ba sai ya gaya mana ba, ni dai kaddai fa ace har yayi move on ya bar ni nan da jiye masa takaici kullum ina babatu, su fa maza ba tabbas gare su ba, zuciyarsu ba shi da tabbas yanxun nan sai su canza in suka samu wata daban, tun da naga ya sa kalmar wife din nan a status jikina yayi sanyiiii, kinga alamar ya dirji amarcinsa yanda ya kamata kenan har da referring dinta to as his wife a status dinsa, to ai shikenan” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana jin zuciyarta na mata zafi, Safiyyah ta taɓe baki tace “Duk da dai shi ma Ajay din ba mutumin banza bane mutum ne me shegen class da personalities masu kyau, kuma dama can yana burgeni yanda baya daukan wargi yanxun nan kana raina masa hankali zai kai maka naushi ya hada maka jini da majina, ba irin mijin Surayyah da Housemate ba masu ba namiji ɗan uwansu hakuri, tun daga nan suka sire min wallahi naga inaaa ba gwarzaye bane” Khaleesat ta kalli wayarta jin shigowar sako, sai kuma ta kalli Safiyyah a hankali tace “My driver is around Sophie, sai gobe” Safiyyah tace “Ni dai ki kwantar da hankalinki ki dena damun kanki wallahi, tun da Allah yayi Housemate ba mijinki bane don gashi can har ya rungume er matarsa to kema a gaskiya zan baki shawara kiyi hakuri ki fara kula mijinki duk da ɗan rainin hankali ne shi amma to ya za ki yi? Nasan shi ma wallahi daurewa kawai yake yana pretending amma ya gama macewa a kanki, yana zaune gida daya dake yana kallon ki matsayin halaliyarsa da wannan shape din naki da glowing skin har ya isa yace baya jin komai a ransa? Ai sai dai ya yaudari kansa wallahi, kawai daurewa za ku yi ku sauke hakkin juna a wuce wajen” Mikewa Khaleesat tayi without answering her fuskarta daure ta dau jakarta tace “Bani textbook dina zan tafi gida” Safiyyah tayi er dariya tace “Ranan da zai nuna maki ke halaliyarsa ce may be you will come back to ur senses that day, bar ganin yana kyaleki, ba dai namiji bane? wataran ko yace zai kyaleki bazai iya ba a sannan ne zaki dawo hankalin ki” Takaici yasa Khaleesat ta juya kawai tayi tafiyarta ta bar wajen, cikin bacin rai ta nufi inda driver ke parking yana jiranta. Khaleesat na isa gun motar ta bude back seat zata shiga, still tayi tana kallonsa, yana zaune driver seat ya saka Black glasses irin no respect din nan yana kallon gabansa kamar bai san ta bude motar ba, ta ɗan taɓe baki ta rufe back seat din ta bude front seat ta shiga motar, Without looking at him kamar ana tilasta ta tace “Good evening” Bata ji ya amsa ba ya ja motar suka bar wajen, ba hanyar gida taga ga nufa da ita ba, ita dai tana ta kallon hanya wondering where he is taking her to, sai da suka yi tafiyar kusan awa daya sannan yayi parking a wani babban Mall, ya kashe motar ya sauka, ganin bata sauko ba yace “Don’t waste my time” Bude motar tayi fuskarta babu walwala ta sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga wajen, Abayoyi masu tsadan gaske da dogayen riguna ta dinga gani, ita dai tana biye da shi a baya, without looking at her yace “Pick the ones u need” Ta daga kai ta kallesa, yana duba agogon wrist dinsa yace “Do not waste my time” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta daga wani Abaya da take ta kallo tun da suka shigo wajen, tana ganin price dinsa bata san sanda ta mayar da sauri ba, taga ya dau Abayan yana dubawa, ita dai kallonsa kawai take, ya duba size din, daga haka bai sake bin ta kanta ba ya ci gaba da duba Abaya da tsadaddun dogayen riguna yana daukan wanda yaga yayi kyau, sai da ya dau riguna biyar duk masu shegun tsada a wajen, don mamaki ma abun ya bata, yayi payment suka fita wajen ya shiga wajen takalma da jakunkuna designers, ta buda ido sosai tana kallonsa, nan ma duk shi ya zabar mata kala uku uku har tayi mamakin ta yaya yasan size din takalminta ga riga ma da ya siya yasan size dinta, sosai jikinta yayi sanyi ganin prices din items din da yake dauka ba na wasa bane, bayan yayi payment suka fita daga wajen takalman kuma duk shi ke rike da kwalayen da aka zuba masu kayan, ta wani zaro ido ganin wajen designers jewelries zai shiga, ita dai a hankali take tafiya tana bin sa a baya, nan ma set din jewelries lafiyayyu uku ya daukar mata ita dai tana ta kallon ikon Allah, taga ya kara mata da zobuna biyu duk designers, sai wristwatch, zoben ne ma ya bata ta gwada without looking at her, daga nan ya biya kudaden suka fita daga wajen, inda ake siyar da hair accessories irin na turawa ya gani ya shiga wajen tana dai biye da shi cikin sanyin jiki, hadaddun ribbons din gashi ya siya mata iri iri bayan ya biya suka bar wajen sannan suka fita babban Mall din gaba daya, she don’t even want to start calculating the amount he spent in just this shopping cause the money was huge especially when converted to Naira, millions masu dama kenan fa in anyi lissafi, bayan mota ya bude ya ajiye kwalayen kayan hannunsa sannan ya bude driver seat ya shiga, ita ma ta shiga gaban motar ta kulle, sae da suka kusa gida after almost an hour and 15 mins ride sannan ya tsaya wani eatry ya siya abinci takeaway biyu, daga nan kuma suka wuce gida wajen karfe bakwai na dare…. A nan parlor Ajay ya bar mata kayan a takaice yace “Get ready za mu yi tafiya gobe karfe biyar na asuba, iya wa ennan kayan zaki tafi da” Yana kai wa nan ya wuce sama ta bi sa da kallo, a hankali ta dau package din kayan gaba daya ta wuce sama ta kai daki, kara fitowa da kayan daya bayan daya ta dinga yi tana duba su, ya subhanallah… they were soo beautiful and unique, the designer bags and shoes where more than gorgeous, har cikin ranta suka yi mata kyau sosai, gashi ya iya zabe ya ma fi wata macen iya zaban kaya, ta gwada takalman taga kamar don kafanta aka halitto su, ta zaune gefen gado ta fito da jewelries din su ma tana duba su, they were screaming nothing but luxury, ta gwada 2 rings din dake ta kyalli ta ɗan yi murmushi sai kuma murmushin yayi fading daga fuskarta ta cire su a hankali ta ajiye bayan ta tuna zoben da Housemate dinta ya siya maya, lokaci daya duk mood dinta ya canza, ɗan farin cikin kayayyakin da take yi yayi disappearing at once daga ran ta, tafi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike a hankali ta goge hawayen dake makale idonta ta nufi banɗaki zata yi alwala, sae da tayi sallan magrib sannan ta fita daga dakin, ta jima tsaye corridor as if contemplating on what she is about to do, at the end kawai ta karasa ɓangarensa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta shiga kamar munafuka, yana zaune parlor ta samesa yana duba wayarsa, taki barin su hada ido ta tsaya jikin kujera a hankali tace “Thank you so much for the wears, Allah ya kara budi” Bai daga kai ya kalleta ba, bayan few seconds taji yace “Thank God instead” Still not looking at him tace “Okay” Daga haka ta juya ta fita daga parlon ta kullo masa kofa, sai bayan da ta koma daki ta fara tunanin kaddai fa convocation din Hadiyah za su je gobe, sosai gabanta ya fadi bayan wannan tunanin ya zo mata rai, lokaci daya jikinta yayi mugun sanyi taji ƙafafuwanta sun mata nauyi sun ma kasa ci gaba da daukan ta, anya zata amince ta bi sa kuwa? da kyar ta karasa edge din gadon dakin ta zauna kamar warce ruwa ya cinye tunani iri iri na yawo a ranta, after some minutes ta jawo wayarta cikin sanyin jiki zata kira Safiyyah ta gaya mata.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah, ur evidence via 07087865788*
