Novel Document

Yankan Kauna Complete Novel

Yankan Kauna Complete Novel Document By Autar Manya

Description/Story:

 Yankan Kauna Complete Novel

Written By Autar Manya

 

Description

Birgima take tayi a ƙasan ɗakin su wanda bai sami arziƙin ledar ƙasa ba Hannunta dafe da Cikinta Idanun nan nata sun Kumbura sunyi luhu luhu fuskarta tai jajir Musamman saman Hancinta abin ka da Tubarkallah fara ce jajir kamar ka taɓa ta Jini ya fito

 

Sedai tsabar Rashi da Ƙuncin rayuwa yasa daidai da sutturar Jikinta idan ka kallah dab take da aga jikinta sabida yadda kayan suka Koɗe suka jeme wahala Sosai ta bayyana ga kayan na Jikinta wanda atamface amman tai shara shara kamar zata yage sedai a wanke take tas tsaf tsaf se ƙurar Ƙasar data kwasa wadda take kwance ne a ƙasan simintin ɗakin.

 

“Yaya Cikin naki? amman kina jin lafawar ciwon ko bari na leƙa ko mai chemist ɗin can ya fito na kira shi ya duba Ki seya baki magani”

 

“karki kiramin kowa ina jin marata kamar zata Ɓalle wayyo Hajiyata”

Hawaye Ummi ta share dama sun saba shiga wannan tashin hankalin Duk ƙarshen wata idan Sa’adah zatai period.

“To haka zaki yi ta Zama da ciwo Sa’adah ai dole inje wajan Mai Chemist ɗin can koya fito tunda shike baki magani se yazo ya ganki sabida ɗazu suman da kikai ya ɗaga mini hankali Ni kaɗai naita ihu agidannan wallahi su Umma Radio suka kunna damma kada suji Ihuna”

Cewar Ummi.

Sa’adatu ta cije baki tana Lumshe idanunta da suka ƙara Girma Fuskarta tai jajir musamman saman hancinta daya koma kamar Tumatur sabida ja abin ka da farar fata.

 

Kwantar da kanta tayi ajikin Ummi tana jan ajiyar zuciya hannunta guda takai saman Cikinta tana Jin yadda mararta ke ƙara ɗaurewa Jita ke dama akwai abin da zata sha wanda ze Lafa mata wannan Ciwon dake takurata a wannan Lokacin ba wai Kukan marar kaɗai take yiba harda Kukan talauci mai za’ayi da rashi abin da kake tunanin ka gagare shi Yazo kai ya gagare ka.

 

Baccine ya ɗauketa Ummi ta zame ta Tasanya mata ƙaramin matashi akanta Ummi uwar ɗaka ta shiga Gaba ɗaya Hajiyar su ta ɓata jikinta kasancewar tana da lalurar Shanyewar ɓarin Jikinta.

“Ya salam Hajiyarmu Ki min afuwa banzo na gyara ki ba abinne yayi Mini yawa”

Ummi ta faɗa da ƙarfinta ta ɗaga hajiya ta jinginar da ita ajikin bango ta soma cire mata zaninta wanda ya ɓaci ta fita dashi tsakar Gida a bakin Rijiya ta aje cikin bawo ta ɗibi ruwa a buta ta shiga uwar ɗakin Wanke wa Hajiya jikinta take tana zuba ruwan a wani ƙaton Bawo wanda suke yiwa Hajiya wanka aciki to yau basu sami Damar Yi mata wankan ba sabida Ciwon sa’adah Gashi kuma ba Ruwan ɗumi Dan yau har Kitso sa’adah tai Niyyar taiwa Hajiya to Kuma se Ciwon marar ta dake tashi duk ƙarshen wata ya tayar mata shiyasa gaba ɗaya basu da Nutsuwa.

 

Ummi ta kammala wanke wa Hajiya Jikinta ta ɗaga Bawon da Butar ta Fita tsakar gida.

 

“Kan uba! Ke Ummi uban wa yace ki ɗaukar mana butar mu ki wanke najasa wallahi bazan Ƙara taɓa ta ba”

Cewar Zainura wadda ta fito daga ɗakin Umman su har tana kama ƙugu sabida tsabar Neman Rigima.

 

Cikin kwantar da Muryar Ummi tace mata.

“Allah ya baki haƙuri tamu ce ta fashe amman In sha Allahu inna fita zan siyo Muku sabuwa dal! mu semu ɗauki mai najasa da ike ma ciwo yana kan kowa”

Ummi ta faɗa ta sunkuya tana wanke kayan cikin bawon duk wannan saukar da kan da Ummi tayi bai gamsar da Zainura ba, Kuma bawai Ummi tayi hakan dan tana shakkar suba hasalima tayi ne dan tasan ita ce bata da gaskiya don ita ce ta taɓa abun su.

 

Sunku yon da Ummi tayi ya bawa zainura damar hayewa bayan ummi ta shaƙo mata wuya Ummi ta fara Nishin wahala Nan da nan idanun ummi suka firfito Tana haki da wani irin zafin nama ummi ta wurgo zainura ta haye saman cikinta ta dinga Dukanta dama ummi ƙarfi ne da ita kamar talauci masifaffiya ce ta ƙarshe dan ita ke ƙwatar musu ƴanci agidan.

 

Ihun zainura ya cika gidan tana neman ɗauki Umma da Jamila ne suka fito dan umma zaninta har Kuncewa yake sabida sauri.

 

“Kan uban can Ummi ke Ummi kashe mini ƴata zaki lallai dana ɗaure ki wallahi dase kin ƙare rayuwarki a kurkuku shegu masu baƙin halin tsiya in banda zalunci ina ke mai ƙirar samudawa da Zainura”

Umma ta faɗa tana fincikar Ummi daga saman Cikin zainura Ummi Huci take tana karkaɗa Jikinta Idanunta sunyi jajir Duk kaushin farcen Zainura ya Fito a wuyanta abin ka da farar fata Nishi Ummi take tama kasa magana kawai ta tsaya tana kallon Cin Mutuncin da Umma take yi mata tana aibata ta.

 

“Aikin banza aikin Wofi bari Inusan yazo nagaji da wannan cin mutunci Ke ga ƙarfi kamar talauci Kin kama mini yarinya kina duka dan tsabar Ganin faraga to bari yazo ayi mana tsakani daku sabida babu ɗan iskan daya isa ya takura mana acikin Gidannan”

 

Ummi sunkuyawa tai tana ɗauraye kayan Hajiya Tana jin zuciyarta na sauka ko banza ta Jibgi banza dama ta jima tana Jin haushin zainura sabida Cin fuskar data ke akan hajiya In tai Yunƙurin Magana ko ɗaukar mataki se Sa’adah ta hanata inta Bijire se sa’adah tahau kuka tana Suji da abin da ke gaban su mana.

 

Ta kammala Komai ta shanya kayan Har ta shanya su, Umma tana Kumbar baki ta wanke wajan tai alwala ta Nufi ɗaki.

 

Lokacin sa’adah ta tashi zaune da alamun kuma sauraron maganganun Umma take yi.

 

“Ummi mai yasa bakya Jine so kike ciwon hajiya ya tashi ina ruwanki da matar Gidannan Meye zaki daki zainura sa’ar kice koni ta girma bare ke wai ya kike so nayi da rayuwata ne Ummi na gaya miki ni bana son tashin hankali duk abin da zai janyo Mini fitina bana so”

 

Sa’adah ta faɗa muryarta na rawa zatai halin wato kuka Ummi tai mata banza ta nuna kamar bata ji abin da take faɗi ba dan idan ta biye ta sa’adah tabbas zaman Borancin da zasu yi agidannan bana ƙare bane.

 

“Ummi kina jina kika mini banza wato raini ya soma shiga tsakanina dake Ko me?”

Dariya Ummi ta ƙunshe kafin ta Nemi guri ta zauna Cikin tsokana tace.

“To Aunty sa’a bazan kuma ba yaya babba yau son girman ya tashi kenan amman dai Kinsan Hajiya tace shekara Ɗaya kika bani”

 

Dukan wasa sa’adah ta kawowa Ummi ita kuma ta zille tana Ƙunshe baki.

 

Tashi sa’adah tayi Duk zaninta ya ɓaci Ummi ta miƙa mata hijabin Jikin Ƙofa ta sanya zata fita waje se Kuma taja ta tsaya tana Ƙifta idanu.

“Kije mana ki wanke Jikin ki sabida duk kayan ki sun ɓaci”

Cewar Ummi.

 

“Wallahi Ummi tsoro nake ji karsu dake ni Umma fa har yanzu faɗa take yi”

Tsaki! ummi taja mai ƙarfi tare da shigewa Cikin ɗaki wajan Hajiya tana ce wa sa’adah.

“To lallai zaki Bushe a wajan dan Wata gardiya seki kasa sakewa agidan ku Allah dai ya yaye maki wannan tsoro……..

Yankan Kauna Complete Novel Txt

File Name   Yankan Kauna… Hausa Novel Doc.
Title Yankan Kauna Complete Novel
Author    Autar Manya 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    01/11/2024
File Size    210KB
Format Size    TXT
Book Price    500
Phone No   09022260850
Download Yankan Kauna Complete Novel By Autar Manya 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button