Hausa novels

Wace ce ita (Who is she) Chapter 69 Hausa Novel

WACECE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SIXTY-NINE📍

Gudu kawai yake zubawa a shimfidadden titin da babu kowa kasancewar dare ya tsaga, imagining abinda ze yiwa baby tee kawai yake muddin ya sameta a gidansu khaleel, Allah ya sani in tana chan sai ya mata hukuncin da ko gidan wani bazata kara kallo ba next time dan be ga dalilin da zesa tayi tafiyarta kamar wacce aka yiwa wani abu ba, ba dai zatace dan ya bawa wata numbersa shine tayi zuciya ta tafi gidan saurayinta ba….
Cikin minti goma sha biyar ya karaso gidansu khaleel, parking yayi a kofar gidan dan zuciyarsa bazata iya jurewa ya shiga da mota ciki ba, karasawa jikin gate din gidan yayi ya shiga knocking da karfi, tasowa me gadi yayi da sauri yana fadin;
“Waye?”..
A tsawace deen yace;
“Zaka bude ko sai na ballaka kai da kofar!”….
Babu shiri ya bude yana bawa deen hanya ya shiga ciki, wani kallon banza deen ya masa yace;
“Ina ne part din khaleel?”…
Da sauri ya nuna masa da hannu dama shine part din farko a gidan…
Deen har yayi gaba wani abu yazo ransa, dawowa yayi inda me gadin yake cikin tsare gida yace;
“Zahrah na gidan nan?”….
A rikice yace masa;
“Bansan wacece zahrah ba yallabai”….
Kamar yace masa budurwar khaleel yaji baze iya bata bakinsa ya fadi wannan shirmen ba, kawai ya wuce part din khaleel din….
Baby tee na kwance a dakin data zabi kwana bayan tayi wanka ta chanja zuwa kayan baccin da tace khaleel ya fita ya siyo mata dazu, khaleel na zaune akan bedside drawer ya sata a gaba da kallo, kwata kwata hankalinsa be kwanta da kwanan a gidan ba saboda yasan dole ana chan ana nemanta, yanaso ya lallabata ya maida ita gida amma besan yanda ze mata ba…
Yana cikin wannan tinanin yaji ana buga kofa kamar zaa balla, kallon baby tee yayi yaga ta fara bacci, tashi yayi ya fita gabansa na faduwa, bugun kofan ne ya yawaita ko kafin ya karasa, bude kofar yayi yana fadin;
“Waye?”…
Shakosa deen yayi a harzuke yace;
“Ubanka ne! Ina zahrah take?”…
Wani irin tsoro ne yaji ya kamasa kamar ya rufe ido yaga ya bace agun, dama yasan za’a rina shiyasa zuciyarsa bata amince masa data zauna a gidan ba kawai dai bashi da yanda zeyi da ita ne, daurewa yayi saboda kashedin data masa yace;
“Bata nan”…
Shake masa wuya deen yayi cikin hargowa yace;
“Karya kakeyi!”…
Tsilli tsilli da ido khaleel yayi yace;
“Wallahi batanan”…
“Idan na shiga na ganta I will kill you”….
Sannan ya wurgar dashi a kasa ya shige cikin parlourn, khaleel na ganin ya shige ya fasa ihu yayi hanyar fita daga gidan a guje dan yasan inya zauna tashi ta kare yau, fita yayi yabi titi a guje sai ihu yake yana fadin;
“Allah sarki wifey, Allah ya kareki, zan dawo, wayyo wifeyyy”….
Gudu kawai yake yana ihun kiran sunanta, saida yaga yazo bakin unguwar sannan ya tsaida wani me mashin dayazo wucewa yace masa dan Allah ya gudu dashi za’a kashesa, me mashin na jin maganar kisa yace ya hau su tafi, a haka khaleel ya tsere abunsa yana yiwa wifey addu’a a ransa…..

Da jacket din daya saka mata ya fara cin karo akan kujera, sai mayafinta daya hango a kasa, rintse ido yayi yanajin wani daci a ransa, wato nan ta tawo dagaske, ya akayi brain dinsa be kawo masa nan ba tintini?, raba ido ya farayi yana nemanta a parlourn, ganin be ganta ba yasasa shiga dakin farko, sai da ya dafe bango saboda cin karo da rigarta da yayi a yashe a kan gado, gabadaya yaji zuciyarsa ta jagule tin kafin ya ganta, toh wannan wani kalan masifa ne yaga kayanta be ganta ba? Me hakan yake nufi? Me sukeyi? Meyasa ta cire kaya? Kansa ne yaji yana juyawa yayi saurin fita daga dakin, dayan dakin ya shiga hannunsa dafe da kansa, sai da ya dan tsaya a bakin kofa yaji ya dan dawo hayyacinsa sannan ya karasa ciki, hangota yayi kwance akan gado nannade a cikin bargo, ta juya baya iya kanta ne kawai a waje sai gashinta daya kwanta a bayanta….
A cikin baccinta taji alamun shigowar mutum duk a tinaninta khaleel ne, dama sanyi ya isheta tanaso a rage mata AC, cikin wata fitinanniyar murya irinta me bacci tace;
“Baby rage min AC’n nan, jikina ciwo yake”…..
“Ba AC za’a rage miki ba, bura uban Ac za’a rage”…
Kamar a mafarki taji muryar da bata fatan jinta a wannan yanayin, bata gama tantance mafarki take ko gaske bane ya fuzgota hade da bargon ya zabga mata wani lafiyayyen mari me gigita mutum sannan ya figeta suka fita daga dakin yana tambayarta..
“Uban me kukayi jikinki yake miki ciwo? Nace uban me kukeyi?”…
Kasa magana tayi saboda wutar data dauke mata na marin daya mata, gabadaya sai taji kamar jinta da ganinta sun dauke….
“Baza kiyi magana ba sai na ballaki? Bazaki gayamin abinda yasa kika cire kaya ba? Uban me kukayi?”….
Ya fada daidai sun fito daga part din khaleel, tsabar takaici ita da bargon yake ja dan bayasan gani ma koda kaya a jikinta ko babu….

Download>>> Surbajo Complete Novel Document

Daidai nan motar da aka dauko momma daga airport tashigo gidan, hango kamar hayaniya daga part din khaleel ta nufi chan direct, kicibus sukayi da deen daya fito da baby tee daga part din khaleel…
“Lafiya me ke faruwa anan?”…
Cewar momma tana kama haba…
“Sanin abinda yake faruwa bashi ze fissheki ba, inaso ki jawa danki kunne ya fita daga harkar yarinyarnan, inba haka ba sai na dauresa na har abada wallahi”….
“Dakata mallam! Ya fita harkarta ko ta fita harkanshi? Kai yanzu wannan makirar yarinyar kake karewa? Kasan wacece fatima zainab kuwa? Kodai kaima ta shanyeka ne kamar yanda ta shanye min da’ tinda ko wani dan iska ya ganta sai yace yanaso, toh bari in gayamaka wannan da kake gani kyan dan maciji gareta, kai da kake kareta tsap zata sareka ta baya baka sani ba”…
Ransa ne yayi mugun baci ya daga hannu da niyar marinta yayi saurin saukewa yana controlling kansa saboda be kamata ba saboda ko banza ta haifesa….
“Ni zaka mara deen? Dama haka kake? Ashe haukar khaleel akan yarinyar nan nafila ne akan naka”….
“Enough of all this shit talks Mr woman!”..
Ya dakatar da ita a tsawace, matsawa baya tayi saboda yanda taji tsawan har tsakiyar kanta…
Nuna ta da yatsa yayi yace;
“Wannan ba fatima zainab din da kuka gurbatawa rayuwa bace keda kishiyarki da mijinki, wannan ba fatima zainab din da kuka azabtar da yunwa da kunci bace, wannan ba fatima zainab din da kuke tinanin bata da asali da gata bace, wannan fatima ce me asali, gata da nasaba, wannan diyace ga Ambassador Muhammad Sa’id Me Kudi da Doctor Jamila Suleim Shuwa, nasan kinsansu, in ma baki sansu bama you can check google zaki samu enough information about them, sai ki auna ki gani if you can mess up with them”…
Sai kuma ya kada hannunsa a saman fuskarta yace;
“Lastly ki jawa shashashan danki kunne akan kanwata! Sannan idan kin isa dashi kinsan dan halak ne ba asaran nononki kikayi ba kice masa karya kara takowa inda fatima take, bissalam”….
Yana fadin haka ya sunkuci baby tee suka barta a tsaye a gurin, inda yayi parking ya tafi, ya bude back side ya wurgata a ciki sannan ya shiga yaja motar….

Download>>> Takari Complete Novel Document

Kuka momma ta fashe dashi bayan sun bar wajan, har wani daci daci takeji a bakinta saboda yanda maganganunsa suke mata yawo akai, ta dade ba’a gayamata maganar data tabbatar bazata iya bacci ba irin wannan, da tasan abinda zata zo ta tarar kenan da bata dawogarin ba, rashin samun flight din wuri ne kila da duk wannan abun bazai faru ba inda tazo da wuri, dama abun duniya ne ya isheta ganin duk space din data bawa khaleel ko waiwayarta beyiba, hasashenta ya kasance gaskiya kuma saboda tasan fatima zainab ce ta dauke masa hankali, sai kuma tazo ta tarar da wannan abun, inba asiri ta masa ba taya ze makale mata haka?, ga deen nan shima ya mata rashin kunya akan wannan tsinanniyar yarinyar har yana ce mata kanwarsa?, shi kuma khaleel yace me?, sai a lokacin ta gane ba karamin bacci tayi ba, taja gefe ta bari abubuwa sai wakana suke batasani ba, amma yanzu zata daura dammara tayi wannan yakin da dukkan karfinta, zata kuma tabbatarwa da fitsararren yarancen khaleel dan halak ne, kota wani hali zata bi sai ta tabbatar khaleel be kara bi takan fatima zainab ba…..
Shigewa part dinta tayi tana kwancewa da sakawa….

Ko gama daidaita parking beyiba ya fito ya bude motar ya fincikota, be tsaya a ko ina ba sai parlorn mami, babu kowa a cikin parlourn sai karar AC kawai dake tashi, sai a lokacin ya janye munafukin bargon dake jikinta, ganinta yayi daga ita sai wata light gown data wuce gwiwa da kadan kamar wacce take gidan mijinta, kasa controlling kansa yayi ya rufe ta da duka ta ko ina, ihu ta saka tana kiran mami da umm suzo su taimaketa…
A tare umm da twins suka sauko kasancewar mami na toilet ita batayi saurin jin ihun ba….
Umm bata dakatar dashi ba sai ma cewa datayi;
“A ina ka samota saif?”….
“Gidan wanchan wawan saurayin nata ta tafi kwana”…
Ya bata amsa yana furzar da wani iska me zafi…
Umm na jin haka tasa masa hannu suka shiga jibgarta kamar an aikosu…
Fashewa da kuka twins sukayi ganin sai dukan baby tee suke har tayi weak ta kasa kuka, wani lafiyayyen mari deen ya saukewa ko wannensu daya sasu yin sama a guje, haduwa sukayi da mami data sauko da sauri itama jin hayaniya daga kasa, cikin tashin hankali hassy tace;

Download>>> Matar Makaho Complete Novel Document

“Mami dan Allah kije ki taimaketa, sunata dukanta”…
Ko tsayawa jin karshen zancen mami batayi ba tayi parlourn da sauri, turus tayi ganin sun saka yarinya a gaba sai duka sukeyi, hankali tashe tace;
“Me zan gani haka? Kai saifff! Jamila!! Kasheta zakuyi ne, ku bari mana”….
Babu wanda ya kulata a cikinsu sai ma yi sukayi kamar basujita ba, kokarin janye baby tee tayi rai a bace tana fadin;
“Jamila baki da hankali ne? Kai kuma inka kara taba yarinyarnan Allah ya isa ban yafe ba”….
Janyewa deen yayi umm kuma ta cigaba da dukanta, sai da mami tayi da gaske kafin ta kwace baby tee daga hannun umm lokacin baby tee ko hannunta bata iya dagawa….
“Wani irin rashin hankali ne wannan jamila? Sai ki biyemasa ku daki yarinyar da ko ishesshen lafiya bata dashi?”…
Mami ta fada tana bubbuga bayan baby tee data fara baccin wahala a jikinta….
“Tinda ta iya bin saurayi gida ai ta samu lafiya, kalli yanda aka samota fa yaya, kalli suturar dake jikinta dan Allah, aure ne in tanaso ai basai ta fara kwana gidan saurayi ba sannan za’a mata”….
“Ya isa haka, abar zancen haka”…
“Wallahi ba za’a barsa ba, abinda takeso ne kuma za’a mata”…
Umm ta fada tana barin parlourn…
Wani irin kallon banza mami tayiwa deen tace;
“Hankalinka ya kwanta kun hadu kun duketa? Fisabilillahi in taje gidan khaleel din ba sai ka rufa mata asiri ba ka mata fada? To kasani ba ita kadai za’a yiwa auren ba kaima me kawo gulma sai ka shirya yin auren a ranar, wuce ka bani guri mara mutunci kawai”…
Juyawa yayi ya fice yana magana kasa kasa yanda baza taji ba…
Da kyar mami ta lallaba baby tee suka hau sama lokacin jikinta yayi wani mugun zafi, ko ina jikinta yayi ja abunka da farar mace, jikinta ne ya fara rawa bayan mami ta kwantar da ita, hankali tashe mami tayi kanta tana tinanin taimakon daya kamata ta bata ita ba likita ba, gashi likitocin gidan su suka sata ciwon ta ina zasu bata taimako especially umm yanda ta zuciya dinnan ta san wallahi bazata tabata ba, ita kanta fushi takeyi dasu bazata iya cewa suzo su dubata ba, gashi kuma dare yayi sosai, tunowa tayi da wata kawarta likita dake cikin unguwar tayi saurin daukan waya ta kirata, Allah ya taimaketa bugu biyu ta dauka, ba musu tace gatanan zuwa, ba’ayi minti goma ba kuwa sai gata tazo bayan mami ta bada izini a shigo da ita..
Allura tayiwa baby sannan tasa mata ruwa shine aka samu jikinta ya daina rawa, magani ta bawa mami tace a bata inta tashi sannan sukayi sallama ta tafi, duk yanda mami tayi ta karba kudi ki tayi….
Umm na shigewa ciki ta hau kiran abby a waya dukda tasan dare yayi amma zuciyarta bazata iya hakura sai gobe ba, sai da ta mishi missed calls biyu sannan ya dauka ana ukun hade da yin sallama…
Ko amsa sallamar dayayi batayi ba tace;
“Dama na kira ka ne in fadamaka ka shirya aurar da yarka nan da sati biyu”…..
Cikin rashin fahimta abby yace;
“Ban fahimci abinda kike nufi ba boddi?”….

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji [Domin Magance Matsalolin Ma’aurata]

“Ta fara kwana a gidan saurayi, tun kafin ta kwaso mana abun kunya gwara a musu auren suje chan su karata”…..
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wannan magana ba magana bace ta waya boddi, insha Allahu zan shigo gobe sai muyi maganar”…
“Ah toh na dai fadamaka”…..
“Babu abinda ze faru da yardar Allah, zan zo gobe kinji ko”…
Kashe wayarta tayi ta cilla kan gado, zama tayi a bakin gadon tana dafe kanta, gabadaya ta rasa me zata kama, mamaki take yanda akayi baby tee ta fita daga gidan ta tafi gurin saurayi bayan ba’a mata komai ba, ko dazu da safe kin cin abinci tayi sai da ta lallabata ta bata a baki, daga ita har mami biyemata sukeyi a cikin gidannan tinda ta fara jinya shine rana tsaka zata zo musu da iskanci, toh wallahi bazata dauka ba……
Sai da ya koma part dinsa sannan yaji hankalinsa ya tashi, tinanin halin da take kawai yake saboda yasan ta daku, amma kuma inya tuna abubuwan daya gani sai yaji haushinta yake ji ma, haka yayita tinani sai bayan asuba ya kwanta….
Karfe bakwai na safe ta farka da wani mugun ciwon kai, gabadaya ji tayi ta tsani duniyar da kowa ma, khaleel ko tsakaninta dashi sai dai Allah ya isa tinda ya fadawa wannan mugun inda take bayan tace masa karya fada, in ba shi ya fada ba ya akayi ta nemesa ta rasa? Yanaji deen na janta kuma yaki fitowa, yanzu ta gane mami kadai ke kaunarta a gidannan kuma ba wani aure da zatayi sai dai suyi duk abinda zasuyi..
Da kyar ta iya tashi ta zauna kasancewar jikinta na ciwo har lokacin, hawaye ne ya zubo mata tana jin kamar lokacin suke dukanta….
A hankali deen ya turo kofar dakin idonsa ya sauka akanta…

Back to top button