Ruwan Zuma Page 11 Hausa Novel
(11) “Abul baka iya gaisuwa bane?” Laila ta kwa6i d’anta tana mai masa ido kar ya kunyatata. Juyawa yayi ya kalli Haydar sama da k’asa sannan yace, “Sannu.” “Kana lafiya? Ina yawan jin labarinka a gurin Hajiya.” Fad’in Haydar yana mik’awa Abul hannu. “Mama waye shi? Wannan karon da 6acin rai yayi tambayar domin yaga saurayin na shige masa da yawa, kuma bai mik’a mishi hannu suka gaisa ba. “Abul behave, baka ganin yana mik’a maka hannu ne?” Ta k’ara kwa6arshi kamar k’aramin yaro. Bai k’ara magana ba ya juya a zuciye ya shige cikin gidan har yana buga k’ofar da k’arfi kamar zai cireta. Haydar da abun ya bashi mamaki ya kalli gefe kamar hakan bai faru ba. Laila kuma kunya ce ta kamata domin tana bawa Haydar labarin su Abul tana kuma yabon halinsu da kuma tarbiyyarsu, to gashi a had’uwarsu ta farko ya nuna ba hakan ba. “I’m sorry, Abul baya sabawa da mutum farat d’aya. Kuma wai don shirme baya son ya ganni tsaye da kowanne namiji balle in ce zanyi aure.” “To ai yin auren ma ba laifi bane.” Fad’in Haydar yana murmusawa. “Well….da wannan ma don wannan.” Haydar ya lura har lokacin abunda Abul yayi na damun Laila, domin hatta murmushin da take yi d’azu babu shi a fuskarta. Me zai yi ya sakata dariya domin ganinta cikin farinciki shine burinsa? Yaushe hakan ya zama burinsa? Ya tambayi kanshi. “Amma yanzu wannan babban saurayin d’anki ne?” Ya d’an nuna mamaki a fuskarsa. “D’ana ne, shekararshi ashirin da uku.” “Amma Hajiya in an ganku tare wallahi baza’a ce d’anki bane, sai dai ace k’aninki ne.” Ya fad’a tsantsar gaskiyarsa. Wata dariya Laila tayi mai dad’in sauti wacce tasa Haydar shagala da kallonta ba tare da ya gane abunda yake yi ba. “Hmm Haydar kenan. Wai haka kowa ke fad’i idan an ganmu tare.” Bai bar gurinta ba sai da ya k’ara sakata dariya kana suka yi sallama ya tafi mayar da motar kantinsu. “To ka aikomin da rabona mana.” Fad’in Nasir bayan Haydar ya shigo cikin kantin. “Kai kaga kud’in nan wallahi kayan abinci zan sayawa Ammi sauran kuma in bata na cefene. Ga dubu d’aya ka rik’e ko tsire ka sayawa Halima.” Ya mik’a mishi dubun wanda Nasir ya k’arba ba godiya sai ma ashar da ya narka masa. “Idan ta daina baka zamu zama d’aya ai.” “A rage hassada dai mutumina.” Cewar Aliyu yana dariya. Daga nan kasuwa ya nufa ya auno shinkafar tuwo, ta dafawa mai, manja da sauransu ya koma gida. “Allah abun godiya, sannu d’an nan. Allah ya k’ara bud’i ya k’ara maka arzik’i da zuciyar yi.” Haka Ammi tayita addu’a tana bud’e kayan abincin da Haydar ya kawo mata. Shi kuma yana zaune a gefe sai murmushi yake yi yana amsawa da Amin. “Ha’a, har da kayan shayi? Wai ina ka samu kud’i ne? Naga wata bai yi k’arshe ba.” “Wannan uward’akin nawa dai da nake baki labari, yau ma na kai mata kaya shine ta bani har dubu goma.” Ya bata amsa yana ciro kud’i a aljihunsa. “Ki rik’e dubu na cefene nima zan rik’e dubu na zuwa gurin aiki.” Ya fad’a yana mik’a mata kud’in. Da haka ya ciro wata leda a aljihunsa ya bud’e yana kallon Ammi wacce ke kallon ledar. “Kai Ali har da tsire? Wannan uward’aki taka Allah ya mata albarka ya k’ara bud’a mata k’ofofin arziki. Ni da zaka yadda ai da sai muje gidanta in mata godiya.” Ammi ta tura tsokar nama d’aya cikin bakinta. “Ai baki ma san babban abun farinciki ba, tace ranar litinin jibi kenan in je gidanta daga nan kuma zamu je wani ma’aikata da za’a d’aukeni a aiki.” Shakewa Ammi tayi da tsokar dake bakinta, ai kuwa ta hau tari ba kakkautawa. Da sauri Haydar ya d’auki ruwan zo6on daya saya mata ya bata ta kur6a yana mata sannu. Gyaran murya tayi tana sosa wuyanta tace, “Ali irin wannan labarin ai baza ka fad’awa mutum da tsokar nama a bakinshi ba. Yau naga farin rana jumma’a haji babbar rana. Allah mun gode maka.” Haka Ammi tayita godewa Allah cikin farinciki tana k’ara yiwa Laila addu’a. “Ammi kici naman kar yayi sanyi.” Ya fad’a yana had’iye yawu domin ita kad’ai ya sayawa saboda k’arancin kud’in hannunsa. “To sa hannu muci mana, naga kamar kaima baka ci ba.” “A’a Ammi, ai naman babu yawa ke kici kawai.” “Kaji mini maganar banza, ai bazan iya cin abu in hanaka ba Ali, maza d’auka.” Ta fad’a tana mai tura masa ledar gabansa. Dariya yayi kana yasa hannu ya fara ci yana bata labarin kalar kirkin uward’akinsa Laila. Bayan sun cinye Ammi ta had’a musu shayi suka sha da biredi, sai a lokacin da tuno da d’anwaken da Minat ta kawo masa. “Ali ga d’anwaken nan na ajiye maka.” Ta jawo kwanon a k’ark’ashin gadonta tana bud’ewa, duk yayi sanyi ya k’andare. “Nifa bazan ci ba, ji nayi na tsani d’anwake ma wallahi. In banda shirmenta ina naga kud’in yin soyayya ko aure? Yanda ubanta yake da tsananin nan ina fara kulata zai ce in turo! To me zan tura Ammi? Kema ki daina kar6an abunda ta kawo don wallahi ba biya zan yi ba.” Washe gari da safe Laila ta kira wayar kantin su Haydar. “Haydar nake so ku had’ani dashi.” Tace dasu tana kai kawo. “Hajiya bai fito ba sai da yamma yake da shift.” Cewar Eke manajan kantin. “Too, yanzu ya za’a yi in sameshi? Ko kana da numbernshi ka turo mini?” “Eh akwai, zan turo miki yanzu.” Haydar na kwance a d’akinsa yana kwance yaji k’arar wayarshi, tsaki yaja domin ya d’auka Nasir ne ko kuma Minat mai yawan masa text d’in safiya. Sai dai kuma wannan tunanin bai hanashi d’aukan wayar ba yaga suna ‘Hajiya Laila�? a jiki. Zumbur ya mik’e tsaye zuciyarshi na bugawa, a ina ta samu numbernshi sannan meyasa take kiranshi? Tun ba yau ba yayi saving numbernta amma bai ta6a kiranta ba, to in ya kira me zai ce mata? Baya son ya 6ata rawarshi da tsalle sannan baya son ya wuce inda Allah bai kaishi ba, alherin dake tsakaninsu ma ya wadatar. Har wayar ta kusa tsinkewa sannan ya d’auka yayi gyara murya. “Assalamu alaikum.” Ya mata sallama yana fita daga d’akinsa don yaji iskar d’akin bai isheshi ba. A can gefe Laila ta amsa tana cewa, “Da Haydar nake magana?” “Eh nine Hajiya, Ina kwana?” Bayan sun gaisa Laila ke cewa, “Don Allah in babu abunda zaka yi kazo gidana akwai wani aikin da zaka mini. That’s if in babu takura.�? “Haba Hajiya, kinfi gaban haka wallahi. Gani nan zuwa.�? Wanka yayi ya fita cikin sauri Ammi na cewa, “Ali ka tsaya ka karya.�? “Ammi na k’oshi.�? Acha6a ya tara zuwa gidan Laila, yana shiga ya kira wayarta ta d’auka tace ya shigo cikin falon. Wannan karo na uku kenan da yake shiga falonta, k’amshin turaren wuta ne ya fara bugar hancinsa kafin idanunsa su haska masa tsaruwar falon wanda babu wasu tarkacen banza. Mata ya gani a zazzaune kusan su ashirin ya gaishesu daga bakin k’ofar kanshi a k’asa. Laila ce ta fito ta wata k’ofa wanda yake tunanin kitchen ne. Sanye take cikin doguwar riga blue irin masu taushin nan, kanta kuma kamar kullum yana lullu6e da d’ankwalin rigar. Haydar shagala yayi da kallonta don zai iya rantsewa bai ta6a kallonta haka ba, kullum a lullu6e take koda kuwa aika ya kawo mata. ‘Me maraban Hajiya da budurwa?�? Shine tambayan da ya yiwa zuciyarshi yana mai kawar da kanshi gefe ganin har ta iso gurinshi. Gaisheta ya k’ara yi yana kallon fuskarta wacce bata yiwa kwalliya ba, sai yaga tafi masa kyau ma a haka domin fatar fuskarta ta fito natural tarr. K’asa k’asa tayi da murya yanda ‘yan falon baza su ji ba ta fara masa magana yana kad’a kai. Da haka ta mik’a masa key kana tace, “Zan tura maka, amma zaka iya yin komai kai d’aya ko in had’aka da Abul?�? Saurin girgiza kai yayi domin bai manta da irin kallon tsanar da Abul d’in ya masa jiya ba. “Zan iya Hajiya.�? Ya mata sallama ya fita waje ita kuma ta isa gurin matan tana k’ak’alo murmushi. Muna matar Nazifi ta kalleta a wulak’ance tace, “Wannan ma k’aninki ne?�? “Me kike gani?�? Laila ta tambaya tana tsayawa a bayan kujeran Munan. “Naga duk kalarku d’aya irin na sadaka yallan nan.�? Matan gurin suka kwashe da dariya Muna ma ta tayasu. Sosai hakan ya bak’anta ran Laila domin dama ranta a 6ace yake tun zuwansu, sai dai bata nuna a fuska ba illa ma murmushin da tayi tamkar bata ji me aka ce ba. Tun ranar da Maman Salman (saurayin Sabrin) ta saka ranar da za’a kawo kayan auren Laila tasa Abul ya fad’awa Umma da Nazifi, kuma ta k’ara da cewa baza suyi taro sosai ba saboda su dangin mijin ma basu fi su shida zasu zo ba. Abul ya dawo yake fad’a mata wai Maman Sani (Muna) ce kad’ai zata zo wanda hakan yayiwa Laila dad’i domin har ranta bata son taron yayi yawa. Ta gurinta wanda zasu zo daga yayarta Ajidde, Marwa, k’awayenta biyu Hajiya Maryam da Hajiya Shatu sai matar Madu Hajja ne kawai. Dama bak’in sunyi k’arfe sha d’aya zasu zo, su kuma suka tsara akan zasu had’u k’arfe tara a gidan Laila don k’arishe shirin taryan bak’i. Bayan kowa yazo ana jiran Muna kawai suka jiyo hayaniyar mata kamar ana k’aramin biki. Laila bata tsinke da al’amarin ba sai da taga mata na shigowa kamar wanda ake hankad’osu, kuma kowacce rik’e da yara d’aya ko biyu. Haka ta sakewa fuskarta fara’a tana musu barka da zuwa a ranta kuma tambaya take meyasa Muna ta mata haka. Su Ajidde da suke d’akin Lailan suka fito gaishesu, ganinsu yasa Hajiya Maryam wacce dama babu sakata a bakinta tace, “Ha’aa Muna amma daga nan garinku zaku je biki ko?�? Muna ta gane habaici aka mata saboda da gayya ta gayyato k’auyawan ‘unguwarsu domin ta 6atawa Laila tsari. Sai dai tun kafin aje ko’ina ta fara jin bak’in cikin abunda tayi dalilin alak’antata dasu da Hajiya Maryam tayi. “Ko zaki yi rakiya ne?�? Ta mayar mata don ta nuna abun bai dameta ba. “Ai ina shiga cikinku za’a gane ni d’in gayyar sod’i ce.�? Laila na jin hakan taja hannun Hajiya Maryam zuwa d’akinta yayinda Muna wacce ke rik’e ta d’anta Sani ta fara magana wanda Laila bata ji sosai ba. “Ya kamar ba’a farin ciki da zuwanmu ne? Idan dama ba’a buk’atar zuwanmu sai tun farko a fad’a mana kuma kar a gayyacemu.�? “Hajiya Maryam meyasa kika tanka mata? Kinsan dama fad’a take nema idan kuma aka biye mata ta samu abunda take so kenan.�? Fad’in Laila tana zama a bakin gado. “Shikenan, amma ko yanzu na d’ana bakina. Mace sai shegen neman magana da tada zaune tsaye! Nice ke wallahi sai na auri mijin nata kuma in mallakeshi muga k’arshen tsiya da fad’in rai. Iskancin banza kawai, an ce ba’a son taro shine zata bi kaf danginta ta kwaso?�? “Ni dai in kina yiwa Allah karki k’ara tanka mata domin bana son bak’in nan su zo su fahimci wani abun.�? Laila ta k’ara kwantarta. “To yanzu ya zamu yi da abinci? Kinsan sakwaran da aka yi ba zai ishemu dukanmu ba.�? D’aga kai Laila tayi tana tunani domin abincin da masu aikinta suka yi wanda za’a ci bayan bak’i sun tafi bazai ishesu tare da tawagar Muna ba. “Ki barsu su tafi haka ai bamu san da zuwansu ba.�? Hajiya Maryam ta bada shawara. “A’a baza ayi haka ba, in muka yi haka kuma bamu kyauta ba. Abinci bazai had’a fad’a ba, nasan me zan yi.�? Da haka ta d’auki waya ta kira kantin su Haydar har aka bata numbernshi, tasan babu mai mata irin wannan aiki cikin sauri sai shi, domin Abul har yanzu yana fushi ganinta da yayi da Haydar d’in. Mas’ud kuma bata son damunshi domin jiya ya dawo daga tafiya yana baccin gajiya. Haydar yana fita tsakar gida ya bud’e motar Laila ya shiga ya rufe. K’ashin turarenta ne a ciki tamkar tana nan tare dashi. Kalle-kalle ya tsaya yi yana ganin ko’ina tsaf-tsaf tamkar mai motar. Maigadi da ya ganshi cikin motar yak’i ya bud’e gate sai da ya kira Laila ta fad’a mishi cewa ita tace Haydar yaje mata aika da mota. Shi kuma yana fita yayi hanyar kasuwa. Sai da ya gama duk abunda Laila ta sakashi sannan ya dawo gidan wajen k’arfe sha biyu. Bayan tafiyar Haydar Laila ta koma d’akinta tayi wanka domin bak’in sun kusa zuwa. Lace mai zafi ta sanya kalar maroon wacce ta yiwa golden skin d’inta kyau bana kad’an ba. Kwalliyar data saba yiwa fuskarta shi tayi sannan tabi jikinta da turaruka kana ta kafa d’auri had’e da yafa gyale. Kyau tayi bana wasa ba wanda har Hajiya Maryam na tsokanarta, “Duk wannan kyau da had’uwan babu miji, kash.�? Dariya Laila tayi wanda dama ta saba jin hakan daga bakin Hajiya Maryam amma baya 6ata mata rai saboda tasan wasa take mata. “Naji a barni a haka.�? Ta bata amsa suna fita falo gurin da kowa ke zaune. Sai dai saboda kujerun sun musu kad’an yasa suka shimfid’a darduma a k’asa wasu suka zauna a nan. Itama Laila a darduman ta zauna tana bin bak’in da murmushi wanda suka zuba mata ido kamar zasu cinyeta. Hakan ba k’aramin 6atawa Muna rai yayi ba domin sun barta a kan kujera cikin gayyarta su kuma sun zauna a k’asa kamar ba sune masu gidan ba. Ita kanta ta sani a kyau ko ado Laila ta fita, a take ta rainawa nata adon tana kawar da kai cikin bak’in ciki. “Yau gane mini madarar kyau! Kai amma matan nan balarabiya ce ko?�? D’aya daga cikin matan ta tambayi Muna. “Ban sani ba. Kuma don Allah ku daina kallonta, haba wannan wani irin k’auyanci ne?�? Shine amsar da Muna ta bata. Bak’i sun zo su Ajidde suka bud’e musu d’ayan falon wanda dama na Mas’ud ne suka zauna a ciki. Laila dai cewa tayi baza taje ba tayi zamanta a falon. Tawagar Muna ma suka k’i bin su Ajidde suna cewa ai wanda suka tafi ma sun isa, alhali nan ganin babu tsaransu yasa suka kama kansu. Muna dai haka ta tashi ita kad’ai tabi bayansu tana ayyana irin 6acin ranta da zata nunawa wanda tazo dasu, domin sun wargaza mata tsarinta na duk su taru suje kan bak’in. Haka aka k’ar6i kayan aure aka cika bak’i da abun arzik’i suka tafi. A nan ne Laila ta yiwa gayyar Muna iso wai suje su ga kayan auren. Suna shiga falon shi kuma Haydar ya shigo gidan da kulolin abinci, “Na shigo.�? Ya sanarwa Laila zuwanshi ta text message. “Yauwa, maigadi ya tayaka shigo da abincin kitchen ta k’ofar baya.�? Ta mayar masa da amsa. Sai da suka gama ganin kayan sannan suka dawo falon Laila suka zauna ana santin kaya. “Kai kaya sun yi kyau, kamar wanda za’a bud’e shago!�? Fad’in bak’uwar Muna. “Alhamdulillah sun yi k’ok’ari kam.�? Marwa ta bata amsa tana murmusawa. Wata hamma Muna tayi sannan tace, “Ya kamata muci abinci kafin mu tafi ko?�? Ta k’arisa maganan tana kallon tawagarta. Dariya kawai suka yi suna gyara zama domin dama Muna ta fad’a musu zasu ci abinci mai dad’i. “Bari a fito muku dashi.�? Fad’in Laila tana tashi zuwa kitchen. Wata dariyar gefen baki Muna tayi tana ganin inda za’a fito da abincin da bazai ishi tawagarta ba ta samu abun yayatawa da zagi. Laila ce ta fito bayanta kuma masu aikinta biyu ne d’auke da k’aton kula suka dire a gaban Muna. Suka k’ara komawa suka d’auko wasu kuloli biyu tare da cartons na drinks guda biyar duk a gaban Muna. “To bismilla jama’a aci abinci.�? Fad’in Laila tana komawa mazauninta. Masu aikinta ne suka fara rabiyan abincin, had’eddiyar fried rice da jollof rice za’a saka a plate sai a d’aura pepper chicken da samosa a sama a bawa mutum, daga nan kuma sai su fad’i drink d’in da zasu sha a mik’a musu. Sai da suka gama bawa bak’in Muna kaff sannan suka dawo kan su Hajiya Maryam, abinci dai har ya rage amma Muna tace tana azumi. Masu k’ari suka yi k’ari ciki har da d’an Muna wato Sani, wasu kuma har da neman leda wai zasu yi guziri. Ai kuwa Muna ta cika tayi fam kamar zata fashe tsabar takaici. Ganin zasu cigaba da kunyatata ta mik’e tace su tafi zata yi bak’i. Suka juye abincinsu a leda suka yi haramar tafiya Laila ta tsayar dasu. D’ari biyar-biyar ta mik’awa kowacce mata sannan tayita musu godiya murmushi bai bar fuskarta ba. “Ai Hajiya idan auren ma yazo zamu zo wallahi. Allah yasa d’akinta ne na har abada.�? Wata ta fad’a Laila ta amsa da Amin, Muna kuma a ranta tace ‘sai dai ki mutu amma bake ba k’ara zuwa gidan nan�?. Ko tsayawa ayi sallama Muna bata yi ba ta fice daga gidan, haka kuma bata jira tawagar tata ba ta shige napep ta kama hanyar gida. Ko da suka fito suka ga bata nan jikinsu ya basu cewa tafiya tayi ta barsu. Daga nan kuma reshe ya juye da mujiya, a maimakon a zagi Laila kamar yanda taso tun farko sai ya kasance ita suke zagi. “Yanzu dama wannan mata mai kirkin ne take zagi?�? Fad’in d’aya daga cikinsu. “Hassada ce kawai da kyashi ganin ta fita komai.�? “Munafuka tana son ta mana bak’in cikin cin gara, ai guzirin da nayi wallahi bazan yi abinci rana ba yau.�? Wata ma ta tofa tata. Da haka suka biya talatin-talatin suka cika napep biyar suka koma gida. “Alhamdulillah komai ya tafi yanda ake buk’ata.�? Fad’in Laila tana zama a falon Mas’ud bayan sun bar nata falon masu aikinta na gyarawa, carpet d’inta kam nad’eshi aka yi domin dottin da yayi da abinci. “Kinga fuskar matar nan kuwa? Yanda kika san zata mutu!�? Fad’in Hajiya Maryam. “Wai har yanzu kishin balbalin ne tsakaninku bayan ke naki mijin ya rasu?�? Ajidde ta tambaya tana ta6e baki. “Shi Baffan su Abul, mijin Muna ai har yau yana son aurenta, mutumiyar tawa ce tak’i amma da tuni mun je suna.�? Fad’in Hajiya Shatu suna tafawa da Hajiya Maryam. Ajidde da dama tana da labarin tayi dariya tace, “Wai ita akan wannan mijin nata take haka? Mutumin da ko a k’afa aka d’auramin zan kwance.�? “Ah to, yau dai kema kin fad’i gaskiya.�? Cewar Laila, domin bata manta ba kwanaki har da Ajidden ake bata bakin ta auri Nazifi. “Amma ai bashi zai hana ki k’i yin aure ba. Kina da manema Laila, manyan mutane masu sonki da aure amma duk kin koresu. Ni kuna fad’a mata gaskiya kuwa?�? Ajidde ta maida dubanta ga su Hajiya Maryam. “Yanzu kam mu bar maganan auren Laila domin ta Sabrin muke. Amma ni ya akayi kika samu abunci da yawa haka cikin k’ank’anin lokaci?�? Hajiya Shatu ta canja maganar ganin har Laila ta had’e rai. Sai a lokacin Laila ta tuno da Haydar wanda duk shi yayi wannan k’ok’arin. “Kinga d’an Adam da mantuwa ko ? Wallahi yaron nan Haydar shi ya sayo a restaurant, ni ban ma san ya akayi ya had’o haka ba, amma dai na kashe kud’i kam.�? Dariya suka saka dukansu Marwa na cewa, “Ai yanzu kika fara kashe kud’i domin aure na gaba.�? “A kawo muku sakwaran ne?�? Fad’in Laila tana tashi tsaye. “Dama daa shi zamu ci ko? Ki bari kawai zuwa anjima kafin nan shinkafar ta sauk’a.�? Da haka ta fita daga falon tana danna wayarta. Tana shiga d’akinta Haydar ya d’auki wayar yana sallama. “Sannu da k’okari fa Haydar. Ka tafi ne?…. Ok, da dare zaka tashi?….Shikenan kazo Ina nemanka. Nagode.�?
Mum Fateey👌
