Uncategorized

An bada bellin matar Gwamnan jihar Kano Hafsah Ganduje

 

A safiyar jiya kafafen yada labarai suka karade da batun kamun da Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa da ta’annati da dukiyar kasa ta EFCC tayi ga uwar dakin Gwamnan jahar Kano Wato Hafsat Ganduje, sai dai labaran na cike da kwangaba kwan afe baya, domin kuwa da zarar wani labari ya fito na batun kamun wani akasin sa shima ya fito daga gwamati  da ke cin karo da wannan.

Idan baku manta ba dai a kwanakin baya labarai sun bayyanar da cewa babban dan gwamnan jahar ta kano wato Abdul’aziz Ganduje ya kai koke ga hukumar EFCC kan ta biciki mahaifiyar sa kan zargin almundahana da tarawa kanta dukiya ba bisa ka’ida ba, wanda dai shima aka musan ta batun inda aka bayana a lokacin da ake wannan cece kuce  ita tunima bata ƙasar, tana wajen murnar kammala karatun ɗanta Muhammad.

Sai dai kwatsam! A jiya sai aka ji cewa biyo bayan kin amsa kiran da hukumar tayi wa matar gwamnan jami’an hukumar sunyi ram da ita inda sai bayan sun share wasu awanni tana amsa tambayoyi kafin mijin ta gwamna Abdullahi Umar Ganduje yaje yayi belin ta, wanda aka ga hotunan su suna sakkowa daga jirgi, a safiyar talata inda matar Gwamnan ta lulluɓe fuskar ta da mayafi.

Kafin zuwan wannan labari anji cewa shi mai karar wato Abdul’aziz Ganduje tuni ya cika wandonsa da iska, ya fice daga kasar a cewar rahotannani ya bayyana bazai dawo ba har sai mahaifin sa ya sauka daga mulki . sai dai kuma hadimin gwamnan jahar kano Abubakwar Aminu Ibrahim a wata wallafa da yayi a shafinsa ya musanta labarin inda ya bayyana cewa wani taro gwamnan ya halatta a Abuja tare da mai ɗakinsa kuma sun dawo lafiya.

Labarin dai da yafi rijaye shine Hukumar ta kama matar gwamnan amma an sake ta bisa matakin beli domin kasancewar bata da rigar kariya irin wacce Gwamna ko shugaban ƙasa ke da ita idan ta kama har Shari’a za’a iya yi da ita, indan aka kama ta da laifi kuma a yanke mata hukunci daidai da laifin ta.

Back to top button