Mijin Marigayiya Page 43 Hausa Novel
Haka rayuwarsu ta cigaba; duk yanda ya so Khadeeja ta dinga binshi dakinsa gaba daya taki. Don haka bashi da zabi duk daren da yake bukatarta sai dai ya bita dakinta su kwana, idan bai je ba sai dai kawai ta leka dakin nasa tace masa sai da safe. Sau da dama ya sha kyaleta yaga ko zata biyo shi amma da zarar ta shiga dakin tace masa sai da safe sai tayi ficewarta. Da farko duk ranar kwananta idan bai ya bukatarta yayi kwanciyarsa a dakinsa haka yake kwana shi kadai, amma tunda Naja ta gane sai ta dinga bibiya; idan ta sameshi shi kadai sai tayi kwanciyarta a nan da uzirin laulayi. A zatonsu Khadeeja bata sani ba; sai dai ita din ta zabi tayi shirune tunda ta san yana yin hakan ne don ta hakura ta koma kwana dakinsa. Ita kuma har ga Allah gani take yi babu yanda za ayi ko wa take aure ta kwana gadon da yake kwana da wata matar; musamman Naja wadda bata tsanar wata mace kamar ita ba.……..Tunda Khadeeja ta dawo daga gida kuma sai laulayi ya saka Naja a gaba. Haka zata wuni jikinta babu kwari, abinci kuwa to idan dai itace ta dafa ba zata iya ci ba dole sai dai ya siyo mata wanda zata ci.Yau Khadeeja take fita daga girki don haka a wajenta shi da yara suka ci abincin rana. Ragowar abincin ranan shi ta diba ta zuba a flask ta ajiye musu ita da Hafsa saboda ta huta shiga kitchen da daddare.Tana zaune a parlor tana bawa Hammad nono ya shigo parlor din, bayan ta amsa sallamarsa ya zauna kusa da ita. Sai da ya gama kame-kamensa yace ‘Da-Allah kiyi abincin dare gaba daya saboda Naja bata da lafiya, kin san na gaya miki ciki ne da ita kuma yana bata wahala.’Ko da dai bata zata abinda ya zo fada kenan ba amma tana jiran wannan din ma domin tu tuni yara suka gaya mata Najan bata da lafiya kuma ta fahimci menene ciwon. Ta cire Hammad daga nono ta saka shi a kafada tana cewa ‘Ai kuwa ka ga yau ba girki zan yi ba ga ragowar abincin rana can shi na ajiye zamu ci da daddare. Allah ya bata lafiya.’Ya sake bata rai ‘Khadeeja, da-Allah ki bari. Yarinyar nan bata da lafiya ko abincin ma ita bata iya ci, kuma ba ita nace ki yiwa girki ba. Ni da yara zaki girkawa, idan ta sami lafiya zata karbi girkinta.’Ta kwantar da Hammad a gefenta sannan ta fuskanceshi gaba daya don bata cikin yanayi na son zance, tace ‘To ai cikin ba wani abu bane, ko ka manta ne? haka na dinga hadawa da cikin da komai duka da karancin shekaruna ga rashin mataimaki. Ita kuwa yanzu ka ga tana ma da mai aiki; ai babu wani abu da zai gagareta. Idan dai kwana ya zagayo kaina in sha Allahu zan yi kamar yanda muka saba.’A fusace ya kalleta na dan lokaci sannan yace ‘Yanzu kenan ke babu halin ace kiyi wani abu sai ki tuno abinda ya faru shekarun da suka wuce? Kuna zaune tare a gidan kina kallon bata da lafiya nace kiyi girkinta amma kina nema kice ba zaki yi ba? Wai ke me kike son zama ne? babu wanda ya isa ya tankwaraki kenan saboda zaman kanki kike yi ko me?’Ta sunkuyar da kai murya kasa-kasa tace ‘Ba haka bane, kawai dai nima mutum ce, yanda aka yi min na zata haka ake yiwa mutanen da ake so shi yasa nake so ko yaya ne ayi adalci.’Bata saurari abinda zai fada ba ta mike ta dauki Hammad a hankali saboda bata son ta tasheshi ya fara bacci, ta wuce dakinta ta barshi a nan.Yanda tayi wannan tafiyar ya tabbatar ko me zai yi ba zata saurareshi ba; wanda hakan yake nufin shi da yaransa zasu shiga halin rashin samun kulawa na tsawon wata takwas har Naja ta haihu, sai dai su sami kulawa kwana biyu kwana biyu kuma a barsu a gantale. Babu yanda za ayi ace ya dauki wannan kuma a halin yana da mata biyu. A yanda cikin nan yake wahalar da Naja kuma dole Khadeeja ce zata dauki wannan hidimar har zuwa lokacin da zata haihu.Sai da ya gama lissafinsa sannan ya mike ya fice, kai tsaye dakinsa ya wuce ya dauki mukullan motarsa. Bai zame ko ina ba sai gidansu Khadeeja; baya son kai kara don ya kulaita ko ya kai kararta ma goya mata baya zasuyi, sai dai yanzu bashi da wani zabi da ya wuce hakan.Ya ci sa a yana shiga gidan Baffa yana shirin fita, a nan bakin gate ya tsaya yayi masa bayanin halin da ake ciki.Cike da kulawa Baffa ya jijjiga kai yace ‘Subhanallahi, to Allah ya bata lafiya. Yanzu ka ga fita zanyi amma in sha Allahu idan na gama abinda nake zan zo har gidan na sami Khadeejan. Kada ma kace mata zan zo, ka kyaleni da ita zan zo na sameta ka ji. Ai daya daga cikin amfanin karin auren kenan daya ta taimakawa daya a irin wannan yanayin.’Suka yi sallama kowa ya nufi inda zai je.Ba shi da tabbacin abinda Baffa zai yi a kan wannan matsalar amma dai yana saka ran Baffan zai fahimceshi ya saka Khadeeja ta dinga taimakawa Naja, a kalla a lokutan da bata da lafiya; idan ba haka ba menene ribar mata biyun ga namiji.Bata samu tayi sallar isha’i a kan lokaci ba don haka har wajen 8:30pm tana zaune a kan dadduma, Hammad yana wajen Habib wanda yake zaune a parlor dinta yana kallon TV. Ta so ta jiyo muryar Baffanta suna gaisawa da Mustapha a tsakar gida, amma da yake bata sa rai da zuwan Baffan ba sai kawai ta zata kunnenta ne ya jiye mata ba daidai ba.Tana nan zaune Mustapha ya turo kofar dakin ya shigo da sallama, bayan ta amsa sallamarsa yace ‘Baffan Mommy ne yazo, gashi nan a parlor na.’Da mamaki ta kalli Mustaphan da alamomin tambaya a fuskarta, tace ‘Baffana?’Yayi ‘yar dariya saboda yanda ta tambaya sannan yace ‘Baffan Nabeela dai.’Itama sai ta dan yi dariya tare da mikewa tsaye; kwata-kwata bata yi zaton kararta Mustapha ya kai wajen Baffa ba. Ta yi zaton zuwa yayi ya ga sabon gidansu kamar yanda take ta faman rokonsa tunda suka tare yazo ya ga gidan. Nan da nan ta tashi ta fice don zuwa ta taryi Baffan nata. Sai da ta shiga kitchen ta jera ruwa da lemo a faranti sanna ta fito, ta dubi Habib wanda yake zaune a parlor din yana rike da Hammad tace ‘Yaya ku taso ku gaida Baffa gashi nan a parlor din Abbanku.’Tana shiga parlor din ta sameshi da Shukra da Nasreen yayin da Abban nasu yake zaune daga gefe a kan kafet; yanayi zaman da Mustaphan yayi kawai ta kalla ta sha jinin jikinta. Ko da bai kai kararta gida ba to tabbas ta san a wannan dan zaman da Baffan yayi ya gaya masa laifinta. Ta karasa ta ajiye ruwan a gaban Baffa a daidai lokacin da Naja wadda itama ta shigo ta gaisheshi take ficewa daga parlor din. Ta zauna daga gefen kafarsa sannan ta gaisheshi ya amsa cike da girmamawa.Sai da ya gama raha da yaran sannan ya zaro sababbin kudi a aljihunsa ya bawa kowa naira dubu sannan ya sallamesu suka wuce suka barsu daga shi sai Khadeejan da Mustapha.Ya dubi Khadeeja yayi gyaran murya sannan yace ‘Deeje, garin yaya kika ce ba zaki taimaka ki karbarwa abokiyar zamanki hidimar gida ba bayan bata da lafiya? Haba Khadeeja, hakan ai shine zaman tare tunda dai Allah ya hadaku.’Ta yi shiru ta sunkuyar da kai tana tunanin ta inda zata fara, inama da Baffa ya zo da Mommy. To ta ina zata fara gayawa Baffa yanda Mustapha yayi mata lokacin tana nata laulayin? Kuma ya za ayi ta gayawa Baffa cewa ita bata bin Mustapha dakinsa kuma duk ranar da bata bishi dakinsa ba Naje yake kira ta tayashi kwana? To ai Baffa ma sai dai ya sake yi mata fadan kin zuwa dakin miji domin tabbas abu ne da haka aka saba; kuma ta sani mata biyu ne da kakanta mahaifin baffa. Wanda da wayonta kafin dukansu su rasa ta san matan ne suke zuwa dakinsa. Wannan kam ai sai dai ta kara kai karar kanta.Muryar Baffa ce ta katseta yana cewa ‘Deeje me yasa ba zaki taimakawa abokiyar zamanki ba?’Ta dan yi firgigit kamar wadda aka tasa daga bacci sannan tace ‘Uhm Baffa wallahi nima daurewa nake ina yin hidimar ranar girkina, tunda ga jego ina yi sannan kuma ina zuwa aiki.’‘Eh, ai wannan ba zai gagareki ba tunda kinga da ace ke kadai ce a gidan ai duka zaki hada ko?’Suka yi shiru na dan lokaci sannan daga baya tace ‘Baffa nima fa haka nake hada nawa laulayin da aikin gidan babu wwanda yake tayani. Kuma ka ga Baffa akwai mai aiki fa wadda zata iya yi mata duk abinda take so idan tayi mata bayani.’Baffa ya dan yi murmushi sannan yace ‘Na fahimceki Khadeeja, amma dai kiyi hakuri ki karbar mata aikin. Tunda kin ga yanzu kema idan kika kuma samun wani cikin ai zata karbar miki ko? Kiyi hakuri Deeje, bana son taurin kai da yawa. Allah zai baki lada har kashi biyu, ladan biyayya wa miji da kuma ladan taimakon ‘yar uwarki musulma wadda take neman taimakon naki. Kiyi hakuri kin ji, tunda ga yarinyarki nan tana taimaka miki ki zauna lafiya tunda dama yara duka naki ne tun kafin ma a aurota.’Haka Baffa ya dauki lokaci yana bata hakuri, daga karshe kuma ya bata umarnin lallai ta taimakawa Naja ta karbi hidimar gidan…
